nasa haka ya ɗauke su, dalili kenan da ya sa ya sake mamaye zuciyar Inno tun bai furta mata kalmar so ba. Laraba ganin Inno ta tafi ɗakin Mai Yasin ya sa ta yi zaraf ta ɗauki hijabinta ta nufi wurin mai daban-daban, a lokacin da ta je ya gama gashe mata zabin sun yi jar suya gwanin birgewa. Laraba ta basar kamar gaske ta ce masa.
"Mai daban-daban Inno ta ce na tambaye ka, nawa ne kuɗin aikin naman sai a biya ka."
Mai daban-daban ya washe baki cikin jin daɗin ganin Laraba tana sakar masa fuska ya ce.
"Haba Laraba, yanzu saboda ni na fi kowa rashin kara sai na karɓi kuɗin Inno don na yi mata aikin zabi, ai a kanki Laraba babu abin da ba zan iya sadaukar miki ba." Laraba ta fakaice shi ta ɗan taɓe fuska sannan ta ce.
"Ashe haka kake sona ban sani ba Mai daban-daban?"
Mai daban-daban ya miƙa mata ledar da ya zuba zabin a ciki ya ce, "Tun farko dama ai ke ce kika ƙi ba ni haɗin kai Laraba, amma bakina ai ba zai iya furta irin soyayyar da nake yi miki ba."
Laraba ta yi masa murmushi sannan ta tafi gida, sai dai fargaba ce fal a ranta tana tunanin me za ta ce wa Inno, idan ta tambaye ta a inda ta samo nama mai yawa haka. Tun da ta doshi kwanar layinsu ta ga wani matashin saurayi yana biye da ita, ita mamaki ma abin ya ba ta don idan aka cire Mai daban-daban babu namijin da ya taɓa cewa yana sonta, saboda duka mutanen garin kallon marar hankali suke yi mata.
"Yan mata, don Allah ki tsaya ina da magana da ke." Matashin ya furta yana shan gabanta, Laraba ta ɗan haɗe fuska kamar ba ta fahimci me yake son faɗa mata ba ta ce.
"Malam lafiya kuwa?"
Sai da ya gyara gaban rigarsa ya saki murmushi sannan ya ce.
"Tun ɗazu da kika wuce na ji kin kwanta mini a zuciyata, to na ga bai da ce na tsayar da ke a can ba shi ya sa na biyo ki zan ga gidanku."
Laraba ta ɗan maƙale murya ta ce, "To gaskiya ni dai ina da masoya da yawa, amma ka san dai an ce mace allurar cikin ruwa ce. Kuma yanzu aike na aka yi, sai dai idan na kai aiken ka tsaya na fito."
A fili ta lura da yadda matashin ya ɗan tsora ta jin ta ce tana da masoya, amma da ya ga ta ba shi dama sai ya sauke ajiyar zuciya. Laraba zuciyarta ƙal, don ita ma so take ta gwada yadda ta ga su Bushira yayyanta da suke uba ɗaya suke yi kafin su yi aure ko ta ji abin da ake ji. A ƙofar gida matashin ya tsaya Laraba tana shiga cikin gida ta zura da gudu ta nufi sashen Inno, har a ranta tana fargabar kada ya gudu kafin ta shiga ta fito. A uwar ɗakin ta ajiye ledar ta sake zurowa da gudu ta koma, sai da ta je soro sannan ta tsaya ta ɗan daidaita nutsuwarta tana mayar da numfashi.
"Ɗan samari na dawo!"
Laraba ta furta tana wani kanne ido.
Martanin murmushi ya mayar mata ya ce, "Barkanki da dawowa sarauniyata, ni dai sunana Habu kuma ba a ƙauyen nan nake ba. Na zo ne daga maƙotan garin nan, ban sani ba ko kin san gidan Malam Lado mai itace?" Laraba ta yi murmushi ta ce.
"Wallahi na gane shi, sam-sam ba shi da mutumci. Sau ɗaya na taɓa tsinkar masa mangwaro ya kai ƙarata har gaban mai gari, kawai dai na raga masa ne saboda na ga ƙafa ɗaya gare shi."
Habu ya saka hanu ya rufe bakinsa ya ce, "Yayan mahaifina ne fa!"
Cikin halin ko'in kula Laraba ta ce, "Ita gaskiya ai dama ɗaci gare ta." Shiru ya yi yana tsoron kada ya sake wata maganar ta ce ta fasa son shi, don ya lura kamar ba ta rufa-rufa. Don haka ya basar ya ce.
"Na tambayi sunanki an ce sunanki Laraba, amma Laraba ai ba sunan ainahi ba ne."
Laraba ta yi fuskar tausayi ta ce, "Sunana Aminatu, sunan mahaifiyata na ci kasan tana haihuwata ta mutu. Ana kirana da Laraba ne saboda ranar Laraba aka haife ni, ga kuma sunan Innata da na ci." Cike da tausayawa ya yi wa mahaifiyarta addu'a, sannan suka ci gaba da hira duk da mafi yawan hirar da Laraba take yi masa shirme da shirirta ne, amma haka kawai ya ji tana birge shi.
Tun da ya shawo kwanar layin hasken fitilar motarsa ta haske su Laraba da ke tsaye a ƙofar gida, suna hira ita da Habu tana ta sheƙa dariya. Ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, cike da ɓacin rai ya ja dogon tsaki har sai da matarsa Nabila da ke gefe ta kalle shi ta ce.
"Baby lafiya?"
Kamar ba zai tanka mata ba, sai kuma ya furzar da iska mai zafi ya ce.
"Nothing!"
Shiru suka yi har suka ƙarasa ƙofar gidan, sai da ya fita ya buɗe gate ya koma cikin motar ya shiga da ita cikin harabar gidan, sannan ya yi hanyar fita a zafafe. Saboda ya lura koda Laraba ta gan shi babu wani tsoro ko shakku a tattare da ita.
"Baby ina za ka je kuma?"
Nabila ta furta, don ta lura da sauyinsa.
"Get inside, i am coming back righ now."
Bai jira cewarta ba ya fice. Shiru ta yi tana nazari, haka kawai ta ji ƙirjinta ya buga da wani tunani ya faɗo mata. Cikin sauri ta ce.
"No! It can't be happen!"
Ta buɗe motar ta ɗauko lapcoat ɗinta da jaka ta rataya sannan ta shige sashensu.
"Shiga gida!"
Dr Fadil ya furta wa Laraba a tsawace, ta wani kwaɓe fuska ganin zai yarfa ta a gaban saurayi ta ce, "Zance fa nake yi Ya Fadil."
Ɗan zaro ido waje ya yi jin abin da Laraba ta faɗa masa babu ko shakku.
"Idan na sake magana ranki zai ɓaci."
Laraba ta fara hawaye rai a ɓace ta ce, "Wallahi Ya Fadil ka fiye shiga haƙƙina, kai lokacin da kake soyewarka wa ye ya hana..."
Marin da ya sauke mata ne ya sa ta katse ragowar kalamanta, gefen bakinta ya fashe ganin irin ƙasƙancin da ya yi mata ya sa ta fashe da kuka tana faɗawa cikin gida da gudu.
"Haba Malam wannan wane irin abu ne haka? Mene ne aibu a maganganun da ta yi da za ka mare ta..."
A fusace Dr Fadil ya ɗauke Habu da mari, ya nuna shi da yatse cike da masifa ya ce.
"Dama ku ne irin 'yan iskan samarin da suke hurewa ƙananan yara kunne ko? Idan na sake ganinka a ƙofar gidan nan, sai na karairayaka na watsar a ƙasa." Daga haka Fadil ya shige gida ya bar Habu riƙe da kunci, ƙwafa ya yi ya ja ƙafafuwansa ya bar ƙofar gidan, a ransa yana jin idan sama da ƙasa za ta haɗe ba zai daina zuwa wurinta ba saboda soyayyarta ta yi masa mummunan kamu.
A harabar gidan Laraba ta yi zaman 'yan bori ta fasa ihu, kamar wacce ake ƙwaƙwalewa idanu. Mutane suka shiga fitowa daga ɓangare-ɓangare ciki har da su Inno, takaici ne ya cika Fadil ya yi tsaye ya harɗe hannuwa a ƙirji yana kallonta.
"Ke Laraba lafiya kike ihu da daren nan kamar wacce ta taka 'ya'yan shaiɗanu?" Inno ta faɗa a ruɗe. Laraba ta sharce majina da ɗan kwalinta fuska shaɓe-shaɓe da hawaye ta ce.
"Ba Ya Fadil ba ne ya koro ni ina zance da saurayina, haka kawai ya dinga falla mini mari duk ya zubar mini da aji a gabansa."
Inno ta yi kicin-kicin ta haɗe rai ta ce.
"Kai Boka ka fita idona na rufe, Larabar ce ba ta isa zance ko mene ne nufinka? Ina ce saba'ar watannan ta cika shekara goma sha biyar? Ga Lantan nan sa'arta ce haihuwa biyu za ta yi a ɗakin miji."
"Wallahi idan na sake ganin Laraba a ƙofar guda sai na ci mutumcinta, dama duk iskancin da yarinyar nan take yi ke ce kike ɗaure mata Inno. Ni da ita za mu ga mai taurin kai."
Dr Fadil ya furta a zafafe yana barin wurin, a daidai lokacin Nabila ta ƙarasa tana jin abin da yake faruwa. Inno tana shirin yin magana suka ji wani sabon kukan daga ƙofar shigowa. Salame 'yar gidan Larai ce ta ƙarasa cikin kuka, kowannesu fuska ɗauke da mamaki suka wurga mata tambaya.
"Lafiya Salame?"
Sai da ta share hawaye sannan ta ce, "Jamilu ne ya sake ni."
Kusan lokaci ɗaya suka ɗauki salati, cikin kumfar baki Yaya Inu ya ce.
"Uban me kika yi masa da zai sake ki a daren nan ga tsohon ciki a jikinki."
Salame ta ja majina ta ce, "Saboda ya sayo shayi ruwan bunu da awara zai sha, ni kuma na ji sha'awarsu na ɗauki ƙwaya biyu da shayin na sha. Shi ne kawai ya sake ni."
Ta ƙarasa maganar cikin kuka, takaici ya mamaye mutanen da suke tsaye. Yaya Inu a ƙufule ya ce.
"Shayin banza da wofi da har zai sake ki a kansa, wannan ai rashin hankali ne. Bai ga halin da kike ciki ba ne?"
Larai da ke tsaye ta saki murmushin takaici ta ce.
"Dama gwano ai ba ya taɓa jin warin jikinsa, yanzu mai gida har kana da bakin magana don an sako maka 'yarka, kuma a kan dalilin da bai taka kara ya karya ba? Ai na sha faɗa maka, wannan auri sakin da kake yi ba zai haifar mana da samun ɗa mai ido ba, domin kai ma uba ne kuma duk abin da ka yi wa 'yar wani sai an yi wa ta ka. Idan ba ka manta ba fa, Raliya a kan ƙosai ka sake ta. Mariya kuma a kan man shanu, ga Abu kuma a kan kai yara almajiranci. Ni ma da kake zaune da ni saboda na zama kujera ce, duk tarkacen yaran da ake tafiya a bar maka ni nake riƙe su. Ka ga yanzu kai ma kana da zaurawa uku kenan a gida, wannan kaɗai ya isa ya zame maka izina..."
A fusace ya katse ta. "Larai ni za ki yi wa rashin mutumci a gaban mutane?"
Baba Ibrahim ya ce, "A duk maganganun Larai babu cin mutumci, sai zallar gaskiyar da har yau ka gagara gane ta Yaya Inu, ya kamata ka dawo cikin hayyacinka. Aure-auren da kake yi ya yi yawa wallahi, yanzu ko wuƙa aka saka mini ba zan iya lissafa adadin mata nawa ka aura ba. Ka gyara zamantakewarka da iyalinka, sai ka ga Allah Ya daidaita lamuranka. Duk da dama aure da mutuwa yana wurinsa, amma ka sani akwai jarabtar da Allah yake yi wa bawa a kan abin da yake aikatawa."
Mai Yasin da ke gefe ya zuba wa Salame da kuka idanu yana lashe baki, saboda fara ce tas kamar Yaya Inu sai dai 'yar ƙibar mahaifiyarta da ta ɗauko.
'Yanzu wannan danƙwaleliyar aka saki, ai kuwa wannan mijin nata an yi sakarai.'
Malam ya furta a cikin ransa.
"To tsohon munafuki, ai babu kuɗin kowa a cikin auren da nake yi, kuma babu ƙaton da yake ciyar mini da su idan sun dawo gida. Ke shige gida muje." Yaya Inu ya ƙarasa maganar yana tasa ƙeyar Salame shi ma ya shige ciki, daga haka kowa ya watse.
CIKIN DARE
Tun da Mai Yasin ya ci karo da Salame ya kasa zaune ya kasa tsaye, haka kawai ya ji wani abu yana fisgarsa a kanta. Duk da tana yanayin kama da Laraba amma ta fi Labara zama cikakkiyar mace 'yar duma-duma kamar yadda yake muradi, Inno da ke gefensa ta miƙe za ta yi masa sallama ta ce.
"To Malam ni zan wuce ɗaki ko akwai abin da kake buƙata a yanzu?"
Wani munin Inno ya gani saboda yadda Salame ta mamaye zuciyarsa, haushinta ya kama shi don haka ya ɗan yi tsaki a hankali ya ce.
"Babu komai za ki iya tafiya!"
Inno ta yi mamakin yanayin furucin da ya yi mata, ganin haka ya sa Mai Yasin ya wayance da cewa.
"Raina ne duk a ɓace wallahi, a ce ka saki mace da tsohon ciki wannan ai hauka ne."
A fili Inno ta saki ajiyar zuciya cikin jin daɗi, don yadda Mai Yasin yake nuna wa zuri'arta kulawa abin yana burge ta.
"Lamarin babu daɗi dai sam malam, ni bari na wuce sai da safe."
Mai Yasin ya amsa mata yana alla-alla ta fice, shi kaɗai ya dinga zarya a ɗaki yana tunanin yadda zai ɓullowa halin da yake ciki. Wata dabara ce ta faɗo masa ya saki murmushi mai sauti, kamar wanda aka yi wa dole haka Mai Yasin ya zauna tunkur har ƙarfe biyun dare ta cika. Daga shi sai gajeren wando ya zare sakatar ƙofa ya nufi sashen Yaya Inu, wannan ne zuwansa na farko sashen don haka cikin sanɗa ya kama gajeriyar katangar ya dira. Sakatar ƙofar ya zare ya bar ƙofar a buɗe saboda koda rana ta ƙwace masa ba zai sha wahalar guduwa ba.
Da yake da ɗan hasken farin wata, cikin sanɗa ya dinga bin ɗakuna yana leƙe, sai dai idan ya zura kai ba ya iya hango komai ta ciki. A haka har ya nufi ɗakin da Yaya Inu yake kwance ya shiga, domin jikinsa ya ba shi a nan Salame take a kwance. Tun dag bakin ƙofa Mai Yasin ya kwanta ya fara jan jiki a hankali, don kada a ji motsinsa a haka har ya haye kan katifar da Yaya Inu yake kwance.
Cikin bacci Yaya Inu ya ji ana shafa masa jiki, da ɗan magagin bacci ya ce.
"Hansatu ce!"
Jin muryar Yaya Inu ya sa ƙirjin Mai Yasin ya buga da ƙarfi, amma don kar ya yi saurin gano shi sai ya ce.
"Ummm."
Tsaki Yaya Inu ya yi ya ce, "Ke dai kin cika jabara Hansatu, don masifa na ce miki zazzaɓi ne a jikina amma saboda ƙalata sai kin zo kin tsotse ragowar ruwan jikina."
Mai Yasin ya yi shiru ya cigaba da kai hannun yana laluben Yaya Inu, shiru Yaya Inu ya yi yana mamakin yadda Hansatu ta iya irin waɗannan abubuwan don bai taɓa jin haka daga gare ta ba. Don haka sai abin ya birge shi duk da yana jin zazzaɓin jikinsa, ya shiga mayarwa da Mai Yasin martani yana faɗin.
"Ke dai Hansatu wannan jarabar Allah Ya yaye miki, duk halin da mutum yake ciki ba za ki..."
Maganar Yaya Inu ta maƙale, ƙirjinsa ya buga da ƙarfi jin ya shafo gashin baki da gemu buzu-buzu, sai kuma ya kai hannu ya shafo kai ya ji wayam babu gashi sai ma wani sulɓi da ya ji kan yana yi kamar bayan sulba. Mai Yasin kusan mutuwar tsaye ya yi, Yaya Inu ya yi kukan kura ya ce.
"Ƙundun uba, jama'a kwarto a ɗakina zai haike mini."
A yi mini afuwa da rashin update kwana biyu, na shiga rububi amma yanzu na dawo free.
07062062624
Ummou Aslam Bint Adam
[01/01, 17:08] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd
Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻
SHAFI NA TARA
A madadin Mai Yasin ya saki Yaya Inu ya yi ta kansa, sai ma ya sake ƙanƙame shi ta baya ya maƙale murya cikin ƙarfin hali ya ce.
"Haba Mai gida me kake son mayar da ni?"
Sororo Yaya Inu ya yi jin abin da Mai Yasin ya faɗa, sai ya fara zargin ko dai shi ne bai shafo daidai ba, ko kuma hannuwansa ne suke yi masa gizo. Don haka ya sake lalubo Mai Yasin ya ji ƙasunbarsa ta masa ƙabe-ƙabe, ya shafa gefen cinyarsa ya ji gajeren wando. A zafafe cikin zafin nama, ya kai masa naushi a fuska yana faɗin, "Mai gidan ubanka, ɗan iskan kwarto. Jama'a a kawo ɗauki." Ganin da gaske asirin Mai Yasin yana shirin tonuwa, ya sa shi fita a guje; shi ma Yaya Inu ya rufa masa baya. Sai da suka je tsakar gida Yaya Inu ya fisgo gajeren wandon Mai yasin, saboda babu riga a jikinsa idan ba haka ya yi ba zai iya kama shi har ya cim masa ba. Ganin dumu-dumu ya shiga hannu sai Mai Yasin ya zage iya ƙarfinsa ya barke wandon ya rabe biyu, ya fita a guje saboda tashin hankali a tsammaninsa sashen Inno ya nufa. Ba tare da ya ankara ba, ya haye katangar sashen Labaran ya dira. Cikin ɗakin ya faɗa a guje jikinsa har karkarwa yake yi, yana jin sa a kan katifa ya ja bargo ya rufa gumi yana keto masa.
Labaran ne ya fito daga zagayen wurin da suke tsugunno, sai da ya ajiye butar a ƙofar ɗaki sannan ya shiga ya buɗe randa ya sha ruwa, ya ƙarasa gefen gadon Rahinatu.
Murmushi ya saki a fili ganin mutum ya gangaro wurin kwanciyarsa, a tsammaninsa Rahinatu ce. Cike da shauƙin soyayya ya furta.
"Rahinatuwa kenan! Bari na gyara ki da kaina, don kada na katse miki bacci mai daɗi." Ya ƙarasa maganar cikin tattausan lafazi mai haɗe da soyayya, sannan ya saka hannu ya gyara hannun Mai Yasin da gumi ya gama wanke shi, ya yi mamaki sosai da ya ji hannun kamar ba na Rahina ba saboda ita mace ce mai ƙiba sosai. Da yake ɗakin babu haske sai ya bar abin a ransa ya raɓa ta gefe ya kwanta, sauke hannunsa da zai yi a gefen Rahinatu ya ji ana karkarwa ga gumi ya jiƙe shi. Ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi, a sanyaye ya ce.
"Rahinatu lafiya kuwa? Me yake damunki na ji kamar kina rawar ɗari "
Daga can gaban Mai Yasin, Rahina ta ɗago tana ɗan yanutsa fuska ta ce, "Baby lafiya kake magana da tsohon daren nan?"
Da sauri Labaran ya zaro ido waje, saboda Mai Yasin a tsakiyarsu yake. Labaran shiru ya yi ya sake saɗaɗa hannu ta cikin bargo ya shafo ƙafar Mai Yasin ya ji, don ya tabbatar da ba aljani ne ya jawo masa hari ba. Saboda a fitar da ya yi fitsari a tsammaninsa indai ba aljani ba, babu wanda zai shigo masa ba tare da ya ji ƙarar buɗe ƙofa.
Ƙafar Mai yasin ya shafo ya ji 'yan yatsu irin na shi saɓanin kofato da ya yi tsammani, sai ya kai hannu ya shafo kansa. Mai Yasin ya maƙale murya ya ce, "Masoyi kada ka yarda da ita ni ce ainihin matarka."
Ware ido Rahinatu ta yi don sai a lokacin ta lura da mutum a kusa da ita, jin furucin Mai Yasin ya sa Labaran ya shafo ƙasunbarsa, ya lalubo ƙirjinsa sai ya ji shi wayam.
"Kai la'ananne sai na kashe ka, garsamemen ƙato a gefen Rahinatuna! weeeeeeeeee huuuuuuu."
Labaran ya furta a haukace haɗe da yin gurnanin da ya razana Mai Yasin, hakan ya sa ya bankaɗe bargo ya fita da gudu Labaran ya rufa masa baya. Cikin shammata Mai Yasin ya juyo ya yi masa mahangurɓa a fuska, cikin tsananin jin azaba ya zube a wurin. Rahinatu ta fito tana ihu da kururuwa, a haka Mai Yasin ya samu ya cire sakata ya fice. Ya fita kenan Yaya Inu ya sako kai cikin sashen Labaran, ya shiga wuri-wuri hannunsa ɗauke da barandami da kokara.
A haukace Labaran ya fisge daga hannun Rahinatu ya cakumi wuyan Yaya Inu yana faɗin, "Wallahi yau ko ni ko kai a gidan nan, tun da ka nemi gwada mini kwartanci." Yana faɗin haka ya kai wa Yaya Inu naushi a baki, jin zafin haka ya sa Yaya Inu ya watsar da kokarar hannunsa ya falla wa Labaran mari, nan take suka shiga kiciniya Rahinatu ban da ihu babu abin da take yi. Kafin wani lokaci tuni iyalan Yaya Inu sun cika sashen Labaran, da ƙyar aka raba su kowannensu yana mayar da numfashi.
"Kai Labaran idan ka bari na riƙe ka wallahi sai na sumar da kai, shashasha wanda bai san ciwon kansa ba."
Yaya Inu ya yi furucin yana buga tsalle, kamar zai ƙwace daga hannun su Bashar. Labaran ya ji wani takaici ya lulluɓe shi, don gani yake Yaya Inu ya gama cin tuwo a kansa, saboda maganar da yake yi masa kamar an dake shi ne kuma aka hana shi kuka. Ya zabura a hassale ya ce.
"Ka dai yi asara Inusa, ka ajiye riɗa-riɗan mata amma kana bibiyar matan wasu, wallahi idan gabaɗaya mutanen garin nan gatanka ne, sai na ɗauki haƙƙin iyalina da ka shiga har cikin turakar sunna kake ƙoƙarin aikata fasadi."
Shiru kowa ya yi, cike da mamaki Hansatu ta ce.
"Kai Labaran kana nufin bayan sashenmu kai ma an shigo maka? Yanzu fa ihun Mai gida ne ya taso mu."
Yaya Inu ya ɗago gajeren wandon Mai Yasin ya ce, "Wannan shi ne abin da na samu daga jikin kwarton, kuma wallahi sai na kai wa Mai gobe da nisa ya saka shi a bala'in da bai taɓa zato ba."
Sai a lokacin jikin Labaran ya yi sanyi, kunyar yayansa ta kama shi, suna shirin watsewa suka jiyo ihun Inno a ɓangarenta. Kamar haɗin baki lokaci ɗaya suka bi sashenta sai dai ƙofar a rufe suka same ta, Yaya Inu ne ya kama katangar ya dire sannan ya buɗe wa ragowar ƙofa. A tsaye suka samu Inno butar hannunta ta tuntsire a bakin ƙofa ruwan cikinta ya zube, Inno tana ganin su Yaya Inu ta riƙe su jiki yana rawa ta ce.
"Inusa wani ya shigo gidan nan, don yanzu haka na fita fitsari na ga giftawarsa da gudu. Babban tashin hankalin ma, gamo na yi domin zir ɗinsa haka yake ko bante babu." Ba su saurari jin ta bakin Inno ba suka fita da gudu suna haske-haske, Mai Yasin ya yi tsumu-tsumu a ɗaki yana saka kayansa, ya yi lakur a kan katifa yana mayar da numfashi. Sai da suka yi binciken duniya amma ba su gan shi ba, suna cikin haka Mai Yasin ya fito yana tambayarsu kamar bai san abin da ya faruba. Labaran ne ya yi masa bayani, bayan ya gama Yaya Inu ya ce.
"Ai na yi mai wuyar tun da na samu tufafinsa, zan sa Mai gobe da nisa ya yi mini aiki mai zafi a kansa. Dama abin da yake buƙata takalmi ko wani abu da aka samu daga jikin ɓarawo ko kwarto, wallahi daga wannan karon ba zai sake haurewa gidan wani ba."
Jin haka ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 35