"Shukura za ki ci ta zuba miki ne?"
Alhaji Umar ya tambayi Shukura, girgiza masa kai ta yi cikin sangartacciyar murya ta ce.
"Baby ta kai mana ɗaki, ni fa ko magana ba na so komai ciwo yake yi mini."
Kunya ce ta kama Alhaji Umar, duk sai ya ji ya tsargu yana ganin kamar yaran duka sun fahimci abin da ya shiga tsakaninsa da ita. Haidar ne ya miƙe ya fita daga falon, sai ragowar 'yan'uwansa suka rufa masa baya. A zuciye Ruƙayya ta ɗauki cooler tana jin kamar ta kifa a kan Shukura, ta shiga ɗakinta ta dire mata ta fito. Tana dawowa ko zama ba ta yi ba ta wuce ɗakinta. Hajiya Karima sakato ta yi da baki tana kallon ikon Allah, saboda tashi ma da Shukura za ta yi sai da Alhaji ya taimaka mata. Tana ganin sun tafi ɗakin ta jinjina kai cikin mamaki ta ce.
"Tirƙashi! Lallai akwai aiki." Ƙarasa cin abincin ta yi, ta ɗauki sauran na yaran da suka tashi ta rufe. Saboda ta san sun tashi ne ba don saun ƙoshi ba, sai don jin nauyin ganin mahaifinku da Shukura.
Tun daga wannan ranar kullum Hajiya Karima ce take girki, idan kuma babu makaranta Ruƙayya ta taya ta. Tun a washegarin tariyar Shukura da dare ta cewa Alhaji za ta dinga girki ya dinga kai musu ɗaki suna ci a can, ya ji daɗi sosai sai ya sake jin Hajiya Karima ta mamaye zuciyarsa. Saboda tun da ya ɗauko maganar aure, har kawo lokacin babu wani abu da ta yi masa na hatsaniya ko ɓacin rai. Tsakaninta da Shukra sai gaisuwa, don tun washegari ta lura da wani irin kallon raini da take yi mata. Ita kuwa ta san ko Haidar da yake bin Ruƙayya ya girme ta, a ganinta abin kunya ne ta ce za ta nuna mata ta fahimci abin da take yi.
A cikin waɗannan kwanakin na amarcin Daddyn su Ruƙayya da Shukura, kullum da kalar naman da ake sarrafawa a cikin gidan. Duk da dama can Daddy mutum ne mai ƙoƙari wurin farantawa iyalansa rai, sai dai kuma yadda yake ɓarin kuɗi wurin sayo kayan ƙwalam da maƙwalashe abin har mamaki yake ba wa Mommyn Ruƙayya.
Ranar da Shukura ta cika kwana biyar da tarewa, a ranar Hajiya Karima ta fara fuskantar sauyin fuska daga wurinsa. Da farko sai ta yi tsammanin ko daga cikin abokan kasuwancinsa ne, suka yi waya wani ya ɓata masa rai. Saboda shiga ɗaya-biyu idan ya yi sai ta ji ya saki tsaki, ko kuma da ya ga abu sai ya fara faɗa. Ana gobe zai cika kwana bakwai a ɗakin Shukura bayan sallar Magriba, ya dawo daga masallaci ta ji yana ƙwala mata kira. A gaggauce ta shafa addu'ar da take yi ta fito ta ce.
"Ga ni Alhaji."
Cikin faɗa ya ce, "Wato kuɗin banza gare ni ko Karima? Saboda wulaƙanci na kawo dankalin nan ba za a shiga da shi store ba?" Da mamaki Hajiya Karima take kallonsa, don rabonta da jin ya kira ta da Karima har ta manta. Murya a sanyaye ta ce.
"Ruƙayya ce ta ce a bari da safe za ta wanke store ɗin, saboda ya yi datti. Amma ka yi haƙuri Alhaji." Ƙwafa Daddy ya yi ya nufi ɗakin Shukura yana faɗin.
"Ban da rashin sanin darajar abu, wasu matan ma nema suka amma ke an kawo kina wulaƙantawa." Sam ba ta ji daɗi ba, amma sai kawai ta haɗiye dumuwarta ta bar wurin. Ruƙayta tana dawowa, kallo ɗaya ta yi wa mahaifiyarta ta fahimci tana cikin ɓacin rai. Tambayar duniya ta yi mata a kan ta faɗa mata sai ta ƙi, don ta san Ruƙayya tana da riƙo. Kuma ta san dama ba ƙaunar Shukura take ba, sai kawai ta saka ta gyaran store ɗin a daren.
Ranar Asabar ce ta kama ranar da Daddy zai koma ɗakin Hajiya Karima, tun da gari ya waye har zuwa dare Shukura take cika tana batsewa. Ganin yanayin da take ciki duk sai ya sake birkita shi, rungumo ta ya yi yana shaƙar ƙamshinta ya ce.
"Yanayinki duk ya wargaza mini ƙwarin gwiwata Baby. Me yake damunki?"
Kukan kissa ta fashe da shi tana sake shigewa jikinsa ta ce.
"Habibi ina cike da fargabar kewarka, yanzu haka za ka bar ni cike da kewarka? Dama duk irin ƙaunar da ka ce kana yi mini kenan? Ni gaskiya ban gaji da jin ɗuminka ba, saboda kusancina da kai ya fi mini komai da kowa a duniyar nan."
Ta ƙarasa maganar hawaye yana bin gefen idonta, sake matse ta ya yi a jikinsa tsam kamar wani zai ƙwace masa ita. Ya saka bakinsa a daidai kunnenta kamar mai raɗa ya ce.
"Ni kaina zan bar ki ne ba don kin gundure ni ba, zan yi kewarki babyna. Amma ai ba wasu kwanaki ne masu yawa ba, kwana biyu ne kawai." Kamar ƙaramar yarinya sai ta hau shure-shure tana maƙe kafaɗa ta ce.
"Ni dai wallahi ka nemo mana mafita, gaskiya ban gaji da kai ba."
Ire-iren shagwaɓar da take yi masa ba ƙaramin narke zuciyarsa take yi ba, cikin so da ƙauna ya shafo fuskarta zai yi magana sai kawai ta haɗe bakinsu wuri ɗaya. A wannan lokacin haka Shukura ta dinga yaudararsa cikin kissa da kisisina, har ta birkita shi gabaɗaya. Sai da Daddy ya nemi tarawa da ita ta maƙale kafaɗa cikin shagwaɓa ta ce.
"Kai da za ka tafi ka bar ni."
A ɗan birkice Daddy ya ce, "Please ki bari, daga baya za mu yi maganar." Girgiza kai ta yi tana sake narkewa ta ce. "Ni a'a, sai dai idan za ka ƙara mini sati ɗaya."
Ɗan jim Alhaji ya yi ya ce, "Idan na yi haka Mommyn Mami ba za ta ji daɗi ba."
Da sauri cike da kishi Shukura ta ɗan ture shi ta ce, "Shi kenan, sai ka je can wurin nata ai." Marairaice murya Daddy ya yi saboda yadda ya yi nisan kiwo a buƙace da ita ya ce.
"Haba baby don Allah kada ki yi mini haka."
Turo baki gaba ta yi ta ce, "Kai ne da wani zance ai, kyauta za ka nema a wurinta? Ba sai ka sayo mana kwanan ba." Cikin sauri ya ce.
"Yadda kika ce haka za a yi." Murmushi Shukura ta yi, ta janyo Alhaji ta sakar masa kiss sannan ta ce.
"To ni dai ka je wurin nata sai ka dawo." Kamar mai jira sai kawai Daddy ya yi zaraf ya miƙe, ya zura doguwar rigarsa. Sai da ya ɗan daidaita kansa sannan ya fice ya nufi wurin Hajiya Karima. Shukura tana ganin ya fita ta saki dariyar ƙeta har da buga ƙafa, cike da isgilanci ta ce.
"Tsoho ya ji haza saura hazihi." Sai kawai ta sake tuntsirewa da dariya.
Kiran waya ne ya shigo wayarta, tana dubawa ta ga lambar ƙawarta Zuby ce. Da sauri ta ɗauka ta ce.
"Wai haka kawai an san mutum amarci yake ci a dame shi da kira." Daga can ɓangaren Zubby ta saki shewa ta ce, "Ka ji shegiya ko har yaushe kika san daɗin mijin? Yarinyar nan kina lokaci fa. Tun rannan kike tashin kanmu da hotuna a status, idan mun yi comment kuma ba replay."
Cike da shaƙiyanci Shukura ta ce, " Ku zauna kuna fama da ƙananan samari, ai wallahi auren mijin wata duniya ne. Zo ki ga mijin wata kuma uban wasu yadda yake ta biyayya tun da na zo, ke yanzu haka ma na aika shi ya sayo mini kwana a wurin waccan guzumar."
Ihu Zubby ta saki ta ce, "Ke fa 'yar iska ce ba ki iya samun wuri ba." Shukura ta yi dariya ta ce, "To ina dalili, shekara da shekaru yana fama da tsohon... ke dai kin gane ba sai na faɗa ba. Yanzu kuma rana tsaka daga yin sati zai koma, ni wallahi na tsani matar nan don kwana biyun nan da na yi na fahimci yana sonta."
Tsaki Zubby ta yi ta ce, "Ni fa daɗina da ke rashin hankali, to dama matarsa uwargidansa da suke tare sama da shekara ashirin zai daina sonta ne? Wallahi ki bi dai a hankali kada ki yi abin da za ta sa 'ya'yanta su ɓarar da ke."
"Kutt ai kuwa da na ɓarar da ubansu ni ma, don wallahi da sai sun gwammace kiɗa da karatu." Shukara ta furta tana dariya, sannan suka yi sallama da Zubby ta kwanta tana jiran dawowar Alhaji.
GIDAN HAFIZ
Wani irin kukan kura Bilkisu ta yi ta nufi Hafiz da wuƙar gadan-gadan, da sauri ya yi baya amma tsautsayi ya sa ta same shi a tsintsiyar hannunsa. Wata irin azaba ya ji tana ratsa shi, nan take jini ya fara zuba. Ga mamakinsa sai gani ya yi ta sake ɗaga wuƙar za ta sauke masa, da sauri ya saka ɗayan hannunsa ya murɗe hannunta har sai da ya yi ƙara. Ta cakumi wuyansa tana kuka ta fara jijjiga shi tana faɗin.
"Wallahi ba ka isa ka yi mini kishiya ba, tun da babu abu ɗaya da na rage ka da shi a cikin gidan nan." Bai kula ta ba, sai ma yarfe hannu da yake yi saboda azbabar da yake yi masa. Da gudu ya ga ta fita tsakar gida, haka kawai ya ji hankalinsa bai kwanta ba. Yana fita ya ga ta ɗauki galan ɗin man fetir ɗin da yake sayo man mashin ɗinsa. Cikin zafin nama ya hankaɗe galan ɗin, fetir ɗin ya zube a ƙasa. Za ta sake ɗauka ya tsinke ta da mari, rai a matuƙar ɓace ya nuna ta ya ce.
"Idan ba ki da hankali wallahi zan nuna miki na fiki ɗanyan kai, saboda na ce miki na yi aure har kike neman illata ni ki illata kanki. Ke wacce irin mahaukaciya ce Bilkisu? Yanzu da ace da tsautsayi ya sa kin hallaka ni fa?"
"Ni kake kira da mahaukaciya? Wallahi kuwa sai na nuna maka asalin haukana. Ba don saboda ka samu wata ne za ka yi mini haka ba? Wallahi sai na nuna maka asalin haukan da kake faɗa." Cikin kicin ta faɗa ta ɗauki ashana, tana zuwa ta ƙyasta a kan fetir ɗin da ya zube a ƙasa. Nan take wuta ta tashi, a tsorace yake bin Bilkisu da kallo saboda gani yake kamar wata aka canza masa ba ita ba. Ganin wutar tana ƙoƙarin laso wurin da mashin ɗinsa yake, ya sa shi ɗebo ruwa a bokiti ya kwara. Wayarsa ya ciro da sauri ya kira layin mahaifin Bilkisu ya sanar da shi abin da ya faru. Wayar Baba ya ce a bawa Bilkisu tana karɓa ta doka ta da ƙasa, da yake a ƙaramar wayarsa ya yi kiran kwaso batirin ya yi ya sake kunnawa. Layin mahaifin nata ya sake kira, yana ɗauka ya sanar da shi abin da ta aikata, a fusace mahaifinta ya ce ga shi nan zuwa ya katse wayar.
Can gefe Hafiz ya koma ya zuba mata ido ganin yadda duk ta birkice, ta fita hayyacinta kamar sabuwar mahaukaciya saboda ko ɗankwali babu a kanta. Mamakinta yake yi sosai, musamman da ya tuna yadda ta yi uwa da makarɓiya wurin auren yayanta Yaya Salis. Don idan bai manta ba shi ya ba ta rancan kuɗi, ta saro atamfar ankon bikin da ta fitar take sayarwa tana ɗora ribarta. Yana nan tsaye ya tuna wata tattaunawa da suka yi shi da ita.
"Abban Sayyid wallahi sai yanzu ne Yaya Salis zai yi aure, ka ga matar da zai auro kuwa? Yarinya doguwa ga gashi har baya, wallahi ba ka ga hanci ba har baka. Amma da kullum ya ƙare a kan Aunty Murja, ni a wata majiyar ma na ji an ce hatta kayan sallah shi yake yi wa ƙannenta."
Murmushi Hafiz ya yi ya ce.
"Shi dama ƙarin aure ai kamawa take yi, amma kuma ai na ji kina yabonta." Bilkisu ta taɓe baki ta ce.
"A da kenan kafin Yaya ya faso gari, tun da ya yi kuɗi ba ka ga duk ta tattare komai ba. Makira ai wallahi gara ya ƙara auren ko ta shiga hankalinta."
Jin jinin hannunsa yana cigaba da zuba, shi ya dawo da shi daga duniyar tunani. Wani ƙyalle ya janyo ya ɗaure hannunsa, ya cigaba da tsayiwa a wurin yana kallon kallo shi da Bilkisu. Bayan wani lokaci sallama ya ji a ƙofar gida, yana fita ya ga mahaifin Bilkisu ne da Yaya Salis. Iso ya yi musu cikin gida, tun daga tsakar gida suka tabbatar da abin da Hafiz ya faɗa musu. Suna zaune a falo Bilkisu ta shiga ɗakin tana sunkuyar da kai ƙasa kamar sabuwar maunafuka. Tana ƙoƙarin zama mahafinta ya tsinka mata mari, da sauri Hafiz ya matso gaba ya ce.
"Don Allah Baba a yi haƙuri, abi a sannu don Allah."
A zafafe Baba ya dubi Hafiz ya ce.
"Ba na son sakarcin banza da wofi Hafizu, ita mahaukafiyar ina ce da za ta aikata ɗanyan aikin nan haka. Dubi yadda ta ji maka rauni a hannu." Shiru Hafiz ya yi, Baba ya shiga yi mata faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Daga ƙarshe ya ɗora da cewa.
"Kuma ki buɗe kunnenki da kyau ki saurare ni, wallahi koda wasa na kuma jin kin aikata makamancin wannan haukar ni da ke ne. Idan kuma kika kuskura kika ƙure yaron nan har ya sake ki, wallahi sai kin fi jin daɗin zaman gidan yari a kan gidana. Allah Ya gafartawa mahaifiyarki, ke dai albasa ba ta yi halin ruwa ba. Lokacin da zan ƙara aure mahafiyarku ce ta tara mini kayan lefe, kuma har ta rasu ba ta taɓa aikata mini wani abin ɓacin rai saboda kishi ba. Shashasha sakarai marar tunani." Baba yana gama faɗa Yaya Salis ya ɗora, haka Bilkisu ta dinga share hawaye har suka gama suka tafi.
Tun daga wannan ranar Bilkisu ba ta sake yinƙurin cutar da Hafiz ba, sai dai kala-kalan ruwan rashin mutumcin da take zabga masa. Don kusan a wannan lokacin ta daina girki da shi, tsakaninsa da ita sai ɓacin rai da baƙar magana. Idan ya zo neman haƙƙinsa wurinta haka za ta gasa masa maganganu ta juya masa baya. Ire-iren abubuwan da Bilkisu take yi bai tsaya iya kansa ba, har sai da ya shafi danginsa. Domin duk wanda ya je gidanta, matuƙar daga ɓangarensa ne ko karɓar kirki ba ta yi musu, ko ruwa ba ta ba su haka suke karkaɗe ƙafafuwansu su tafi. Gabaɗaya Bilkisu kallon munafukai take yi wa dangin Hafiz, don haka su ma suka janye jikinsu daga wurinta.
Duk wani shige da fice da Bilkisu za ta yi don ta san yarinyar da Hafiz ya aura ta yi, sai dai har lokacin ba ta samu ba. Watarana da daddare, kimanin biyun dare. Ta jango wayar Hafiz, ganin password a jiki ya sa jikinta ya yi sanyi, wani tunani ne ya faɗo mata. Da sauri ta shiga gwada sunayen yaranta bai yi ba, sai ta gwada sunansa ta samu wayar ya buɗe. Whatsapp ɗinsa ta shiga, a nan ta fara cin karo da lambar Amina da irin zafafan kalaman soyayyar da suke yi wa junansu.
Da farko ɗaukar lambar ta yi za ta kira ta zagi Amina, sai kuma wani tunani ya faɗo mata. Cikin sauri hannunta yana rawa ta rubuta.
_Ni Hafiz Adam, na saki Amina saki ɗaya, na sake ta saki biyu na sake ta har saki uku. Sakamakon saɓanin da nake samu da matata saboda na aure ki, domin ba zan iya ɓata wa matata rai ba._
Bayan saƙon ya tafi sai ta goge saƙon daga kan wayar, sannan ta ajiye masa wayar a gefensa ta koma ta kwanta tana jin zuciyarta fes.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
https://chat.whatsapp.com/IAZVt2Pz4LvIcklCxSTHwo
SHAFI NA UKU
Lokacin da Hafiz ya tashi zai yi sallar asuba misscall ɗin Amina ya gani rubutu, yake ya ji masallaci sun shiga da sauri ya zura wayar a aljihu ya nufi masallacin saboda tuni ya yi alwala. Ana idar da sallah ya fito daga masallacin, ya ciro wayar a nan ya sake cin karo da wani kiran nata. Ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi, hannu yana rawa ya ɗauki wayar yana faɗin.
"Salamu alaikum, Amina."
Kuka ya ji ta fashe da shi, hakan ya sake ɗaga hankalinsa. Jikinsa yana rawa ya sake cewa, "Amina me yake faruwa a gidan ne? Lafiya kike kuka?" Daga can ɓangaren Amina ta sauke ajiyar zuciya murya a dashe saboda kukan da ta sha ta ce.
"Tambayata ma kake yi Hafiz? Tambaya kake yi me ya faru? Dama ka so cin mutumcina ne shi ya sa ka zo gidanmu neman aurena?" Da mamaki ya ɗago wayar yana bin lambar da kallo don sake tabbatar da wacce take magana, cikin rashin fahimtar zancanta ya ce.
"Amina wai me kike faɗa ne? Kin san wa kika kira kuwa?"
"Kana nufin na fara hauka ne Hafiz? Ko ka ɗauka ina shaye-shaye ne?" Ita ma ta faɗa a ɗan fusace. Shiru ya yi yana nazari, don ya san Amina sarai mace ce mai haƙuri. Tun da suke tare ba ta taɓa faɗa masa makamantan irin maganganun nan ba. Gwaron numfashi ya sauke cikin tausasa murya ya ce, "Don Allah Amina ki yi mini bayani ban san me yake faruwa ba."
Wani takaicin ne ya sake rufe Amina, cikin gatse ta ce.
"Kana nufin har ka manta sakin wulaƙancin da ka yi mini, saboda matarka ta fi ni a wurinka don kuna samun saɓani shi ne za ka sake ni? AlhamduLillah tun da har na fahimci matarka ta fi ƙarfinka, na gode ka aiko gidanmu a karɓar maka sadakinka." Daga haka Amina ta katse wayar.
Wani irin gumi ne ya lulluɓe Hafiz, da sauri ya jingina da bango sakamakon jin da ya yi juwa tana yunƙurin taɗe ƙafafuwansa.
"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un." Ya furta a fili, sannan ya zura wayarsa a aljihu. Da sauri ya nufi gida, ya shiga kiciniyar fito da mashin ɗinsa waje. Yana rufe gidan ya hau mashin ɗinsa, kai tsaye ya wuce unguwarsu Amina.
Yana zuwa ƙofar gidan ya ciro wayarsa ya yi mata kiran duniya ta ƙi ɗauka, ƙwanƙwasa ƙofar gidan ya fara yi a rikice. Don kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci yana cikin damuwa. Mahaifinta ne ya buɗe ƙofar ya fito, cikin girmamawa Hafiz ya tsugunna ya gaida shi sai kuma ya yi shiru ya ma rasa ta ina zai fara yin magana.
"Hafiz dama na so kiranka da kaina zuwa an jima. Amma na ji daɗi da Allah Ya kawo ka yanzu."
Da sauri Hafiz ya ɗago ya ce. "Baba lafiya kuwa? Dama... dama na ji Amina tana ta wasu maganganu." Mamaki ne ya kama Baba, sai ya ce.
"Shigo ɗakina, wannan ba maganar tsaiwa ba ce."
Baba ya furta yana shiga ciki, kamar zakaran da ya bi ta mahauta haka Hafiz ya bi bayan Baba jiki a sanyaye. Yana nan zaune a ɗaki Amina da Baba suka yi sallama suka shiga, wayar Amina ya karɓa ya nuna masa ya ce.
"Da asubar nan Amina ta nuna mini saƙon da ka turo mata cikin dare." Hafiz yana gama karanta saƙon ya ce.
"Wallahi Baba ban san yadda aka yi ba, wallahi ba ni na rubuto mata wannan saƙon ba. Tun da ko a daren jiya lafiya ƙalau muka gama waya da ita." Hafiz ya yi jim, ya ɗago da sauri ya ce.
"Sai dai idan matata ce, babu tantama wallahi sai dai idan ita ce Baba." Shiru Baba ya yi yana nazari, ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"To a gaskiya idan har haka ne sai ka tashi tsaye Hafiz, don ba na son duk wani abu da zai sa a dinga tashin hankali. Haka kuma wannan maganar ba za mu bar ta daga mu sai kai ba, dole ne ka kirawo manyanka a yi magana. Ita ma ya zama wajibi ka tsawatar mata, ka kuma kiyaye haƙoƙinta. Don za ka yi aure ba shi zai sa ka wulaƙanta matarka ba, ko ka dinga cin fuskarta kana cin zarafinta. Ka ji tsoron Allah Hafiz, wallahi idan ka cuci 'yar mutane Allah ba zai bar ka ba." Cikin girmamawa Hafiz ya russuna ya ce.
"In Shaa Allahu Baba."
Miƙewa Baba ya yi ya fita, har Amina za ta fita cikin sauri Hafiz ya ƙarasa ya riƙo ta. Rungumo ta ya yi jikinsa ya haɗa ta da bango ya ce.
"Kina tunanin akwai ranar da zan iya rabuwa da ke ne?"
A ɗan shagwaɓe Amina ta ce, "Na sani tun da tsoron matarka kake ji." Sunkuyawa ya yi ya sakarwa bakinta kiss ya ce, "Haka kike gani Meena, amma babu wani tsoro. Kin san duk macen da za a ƙara wa abokiyar zama dole a lallaɓa ta, musamman Bilkisu da take da kishi." Janye jikinta za ta yi ya sake matse ta ya ce.
"Me ya sa kike guduna ne?"
"To ni kada wani ya ganmu a haka." Ta ba shi amsa a sanyaye, zuba mata ido ya yi yana jin sonta na fisgarsa. Cikin wani irin yanayi ya ce, "Ai ba wamda zai shigo tun da kowa ya san ke matata ce, ba ki ga ma Baba ya ba mu wuri ba."
Zaro ido ta yi tana rufe baki ta ce, "To wallahi ni tafiya zan yi, wato duk kallon haka suke yi mini?"
Gyaɗa mata kai ya yi ya tallafo fuskarsa da hannu biyu ya ce, "Ina ƙaunarki Meena, na yi mamaki da har kika yarda zan iya rabuwa da ke." Tura baki gaba ya ta yi cikin jin nauyinsa, Hafiz lumshe ido ya ce.
"In Shaa Allah nan da sati biyu za a kawo kaya, sai a yi wunin biki a wuce wurin don haƙurina ya fara ƙarewa." Sunkuyar da kai ƙasa ta yi cikin jin kunya, ya sunkuya saitin kunnenta ya yi mata raɗa a kunne. Da sauri ta ɗago tana rufe ido cikin jin kunya ta ce.
"Allah Ya shirye ka, ni wallahi ba haka nake ba. Don Allah babu abin da ya dame ni."
"Ai shi ya sa na ga ba kya hana ni idan ina..."
Da sauri Amina ta saka hannu ta rufe masa baki, sai kuma ta ce.
"Ka zo ka tafi ka bar Madam tun da farar safiya." Cikin kwaikwayon muryarta ya ce.
"To duk ba ita ta ja komai ba."
Dariya Amina ta yi ta ce, "Allah Ya shirya ka Hubby."
Har ƙofar gida Amina ta raka shi tana jin soyayyar Hafiz a cikin ranta. Duk da ta ji zafin abin da Bilkisu ta yi, ta wani ɓangaren tana yi mata uzuri, saboda ba kowacce mace ce take danne zuciyarta ba idan za a yi mata kishiya.
Hafiz yana zuwa gida ya samu Bilkisu tana yi wa yara shirin makaranta, kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kanta. Haka shi ma bai kula ta ba ya zauna har yara suka gama cin abinci, ya ɗauke su ya kai su makaranta. Lokacin da ya koma tana kwance a kan gado, a gefenta ya zauna ya ce.
"Bilkisu ki tashi za mu yi magana da ke."
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 35