ransu ɓaci ya yi. Mahaifinta har ya kusa dukanta ya yi ummanta ta ce masa ya ƙyale ta, tun da ba ita kaɗai ba ce tana da juna biyu.
A ranar Baba ya kira Hafiz ya ce yama son ganinsa da daddare, cikin girmamawa ya amsawa Baba. Hakan ne ya sa daga Kasuwa Hafiz ya wuce gidansu Amina. Cike da karramawa mahaifinta ya sa aka kai shi falon saukar baƙinsa, Amina ya sa aka kira masa tana shiga ta takure a gefe tana jifansa da harara.
Baba ne ya fara jin ta bakin Hafiz, ya zayyane masa duk abin da ya sani. Sai dai bai faɗa masa ganin layar ɗakin Bilkisu ba, ita ma Amina cewa ya yi ta faɗi duk abin da yake yi mata. Sai kuwa ta zayyane duk maganganun da ta ji Bilkisu tana faɗa, da duk wasu makirce-makircenta. Baba yana gama jin haka ya saki murmushi, don ya fahimci koma. Hafiz ya dubi Baba ya ce.
"Wallahi Baba ni ban san da duk waɗannan abubuwan da ta faɗa ba. Hasali ma a ranar da ta ce na kai wa su Bilkisu wanki, ita da kanta Bilkisun ta kira ni ta ce ta kai mana wanki maƙota za ta biya."
"Hafiz na fahimci komai ba sai ka ɓata bakinka ba. Ke Amina shiga ki ɗebo kayanki."
Baba Ya furta yana miƙewa, kamar za ta yi kuka ta ce.
"Ni dai ba zan koma ba Baba..."
"Kallon da Baba ya yi mata ne ya sa maganarta ta maƙale, don haka ta tura baki gaba tana hawaye ta shige cikin gida. Suna shiga Baba ya sanarwa da mahaifiyarta duk abin ya faru, sannan ya ɗora da cewa.
"Amina Allah Ya haɗa ki da makirar kishiya ne, wacce ta fi ki wayo, kissa da makirci. Duk waɗannan abubuwaa da kika faɗa, ta yi ne domin ta tunzura ki. Tun wuri ki dawo cikin hankalinka, wallahi koda rana ɗaya ban taɓa jin Hafiz zai zalunce ki ba." Baba da Umma sun jima suna yi wa Amina nasiha, bayan Baba ya fita Umma ta sake nusar da ita yadda ake zama da kishiya. Daga ƙarshe ta ɗauki jakarta ta fito, ƙannenta suka yi mata rakiya har ƙofar gida. Cikin zumuɗi Hafiz ya ɗauki akwatinta ya saka a gaba, ta hau mashin suka wuce gida.
Bilkisu tana gida ba ta san wainar da ake toyawa ba, don a ranar tun bayan isha'i ta yi wa yaran shimfiɗa suka kwanta. Ta sheƙa wanka cikin tsukakkun ƙananan kaya, wandon da ta saka da kaɗan ya sauka daga cinya. Sai rigar da ta saka mai yankakken hannu, ta yi haka ne don ta ja hankalin Hafiz saboda wani turaren humra da zumar mallaka da ta saya take son gwada amfaninsu. A lokacin da Hafiz ya shiga tana kicin, jin sallamarsa sa ta fito da sauri cikin kwarkwasa tana faɗin.
"Oyoyo baby."
Turus ta yi, ganin hannunsa ɗaya riƙe da akwati, ɗayan kuma yana riƙe da na Amina.
GIDAN ALHAJI UMAR
A sanyaye Alhaji Gambo ya dubi Hajiya Karima ya ce.
"Ki yi haƙuri Hajiya, ni ina ganin abin da ya fi ki fitar da su ɗin. Saboda a matakin da ake kai daga ɓangarensa wallahi komai zai iya faruwa, saboda ki duba ki ga duk yadda nake da shi bai ji nauyin furta mini baƙaƙen maganganu ba." Cikin kuka Mommy ta ce.
"Alhaji kada ka manta, tun muna tsohon gidan can fa nake kiwon nan! Yanzu duk haƙuri da kawar da kan da na yi lokacin aurensa, da sakayyar da Daddyn Mami zai yi mini kenan?" Ta yi maganar cikin kuka mai cin zuciya, ajiyar zuciya ya sauke ya ce.
"Fiye da haka ma zai iya yi Hajiya. Ni da ke mun san da Umaru ba haka yake ba, jikina yana ba ni har da aikin sihiri a jikinsa. Amma idan aka yi haƙuri komai zai zama labari, yanzu idan na fita zan kira wasu abokaina da suke da suya sporta. In Shaa Allahu cikin su biyun za a samu wanda zai saye, idan aka sayar ba shi kenan ba tun da wannan ce matsalar." Hajiya Karima ta share hawaye sannan ta gyaɗa masa kai. Har ya miƙe sai kuma yace.
"Don Allah ku ƙara haƙuri ke da yara, na san abin da ciwo sai an daure. Amma muna nan watarana za ki yi mamaki kamar ba a yi ba." Amsa masa ta yi sannan suka yi sallama.
Koda Mommy ta koma cikin gida yaran ta samu duk sun yi carko-carko, faɗaɗa fara'a ta yi ta ce.
"Mun gama magana da Alhaji Gambo ya ce zai haɗa ni da masu sayen kajin." Cikin takaici Ruƙayya ta ce.
"Wato Daddy ya kafe dai sai kin sayar? Ai shi kenan, idan ma adalci ya yi Allah Yana kallo. Kuja sai Allah Ya saka..."
Bige mata baki Mommy ta yi, rai a ɓace ta ce.
"Idan na sake jin makamanciyar wannan maganar daga bakinki, wallahi sai ya yi jini. Shashasha sakarai, wani banzan hali za ki koya? Mahaifin naki kike faɗawa haka? Wallahi idan na sake ji zan ba ki mamaki. Tashi ki fice ki ba ni wuri." Mommy ta ƙarasa maganar a tsawace. Kusan lokaci ɗaya duka suka fita, Mommy ta zuba tagumi tana tunanin sabuwar rayuwar da suka faɗa ita da 'ya'yanta.
A wannan ranar Daddy bai dawo gida da wuri ba, kuma ko da ta ba shi abinci kai tsaye ya ce mata ba ya ci. Tana gani ya ɗauki filo ya fice daga ɗakinta, haka Mommy ta kwana cikin takaici da ɓacin rai.
Kwanan Shukura Biyu a gida ta tarkato ta dawo gidan, kuma a cikin kwanakin abokan Alhaji Gambo suka saye kaji da dusar wurin Mommy. Ga mamakinta, sai gani ta yi Daddy ya sa ana farfashe katafaren kejin kajin nata. Kamar za ta yi masa magana, sai kuma ta fasa gudun kada abin ya zame musu fitina.
Tun dawowar Shukura ta lura da take-takenta, duk da dama can sun san da rashin mutumcinta. Amma a wannan lokacin ya ninka na baya, saboda kai tsaye take kiran Haidar ko Ruƙayya ta saka su aiki ko aike cikin gadara. Idan suka yi magana kuma ransu da na mahaifiyarsu ya ɓaci, saboda idan Daddy ya tashi faɗa yake yi mata ya ce ta hurewa yaranta kunne, tana son ɓata tarbiyyar da ya gina su a kai. A cikin lokaci ƙanƙani zaman gidan Daddy ya sauya salo, su Ruƙayya da suka saba zama su yi hira cikin wasa da dariya da mahaifinsu, a wannan lokacin duk tsoronsa suke ji. Da sun ji sallamarsa suke shiga taitayinsu, ita kanta Mommy wani lokacin gabanta har faɗuwa yake yi. Ta sha zuwa ta same shi don ta ji laifinta, amma ƙarshe sai dai ya rufe ta da faɗa. A cikin wannan zaman kai kuka ni tagumin da suke yi ne, Daddy ya karɓe mukullin store daga hannun Mommy ya koma hannun Shukura. Ranar da Mommy ta yi wa Daddy maganar haka ya gama ci mata mutumci, kuma da yake a ɗakinta yake cikin fushi ya tafi ɗakin Shukura ya kwana a can.
A wannan lokacin Hajiya Karima har yayan Daddy ta samu da maganar, amma babban abin da ya ɗaga hankalinsu da kai tsaye ya ce a kan Shukura hatta shi ɗan'uwan nasa da suke ciki ɗaya zai iya rabuwa da shi. Haka Mommy ta cigaba da haƙuri, duk abin da suke so sai Shukura ta ga dama za ta ba su damar su ɗiba, don haka ta saka musu dokar shan shayi a sati sau biyu ragowar kwanaki sai kunu. Hatta abincin dafawa ita ta saka su yin tazarce daga rana zuwa dare, don haka Mommy ta same shi da maganar.
"Daddyn Mami shin ka san abin da yake faruwa a gidan nan? Yanzu saboda Allah a ce kowanne irin abinci tazarce za mu yi masa." Fuska a haɗe Daddy ya ce.
"Ai wallahi ban taɓa sanin ba ki da hankali ba sai yanzu, yanzu ke Karima tsofai-tsofai ba ki san ya kamata ba? Yanzu a ce yarinya ƙarama ita za ta fi ki tattali da sanin ya kamata? Wallahi kin ba ni kunya." Duk yadda ta so shawo kan Daddy fir ya ƙi amincewa. Sai ya zamana idan tana son su sauya abinci, sai dai ta fitar da kuɗi a jikinta ta bayar su sayo abin da suke so, a haka suka cigaba da tafiya har bikin Ruƙayya ya rage saura kwana goma.
Da farko Mommy ido ta kawo masa, saboda ta ga ko zancan kujera bai yi mata ba. Duk wani abu da uwa take yi wa 'ya na kicin babu abin da Mommy ba ta saya wa Ruƙayya ba, sai kayan gado ne kawai ya rage take jira daga gare shi. Ana saura kwana bakwai biki ta je har ɗakinsa ta same shi, fuska a sake ta fara yi masa maganar duk da lura da ɓata ran da yake yi. Sai da ya gama sauraronta sannan ya ce.
"Kayan gado da duk wani abin buƙata kama daga kan abinci, garar amarya da komai da kika sani na buƙata na damƙa wa Shukura, ba sai kin wahalar da kanki ba za ta aiwatar da komai tun da ita kin ga ta zamani ce za ta fi ki sanin abin da ya dace." Hajiya Karima ji ta yi kamar ya watsa mata ruwan zafi, rai a ɓace ta ce.
"Wallahi na gaji Alhaji, yanzu saboda wulaƙanci na haifi 'yar a cikina. Duk wata ragamar ɗawainiyar raino da tarbiyya na yi mata, rana tsaka ka ba wa wata bare kuɗin hidimar bikinta, wallahi ba zai yuwu ba. Ai kuwa wannan karon sai dai duk abin da zai faru ya faru."
"Rashin mutumci za ki yi mini Karima?"
"Wallahi duk abin da za ka faɗa sai dai ka faɗa, amma babu ƙatuwar da za ta yi mini wannan cin kashin." Ita ma Mommy ta katse shi a zafafe, Daddy ya miƙe a fusace ya ce.
"Ba ni ne ubanta ba, wallahi idan kika saka tsiya auren ma sai na fasa shi." Cak Hajiya Karima ta tsaya, ta dube shi rai a ɓace ta ce.
"Saboda mace za ka zubarwa da kanka mutumci, to wallahi bari ka ji idan har ka yi wannan abin kunyar. Wallahi zamana da kai ya zo ƙarshe, sai dai ka zauna da Shukura ba ni ba." Daddy ya matsa gabanta ya ce.
"A yanzu ma kina iya tafiya ai ban riƙe ki ba."
"Wallahi da zaman wulaƙancin da kake yi mini gara ka sawwaƙe mini, amma wallahi ka ji na ratse ba zan yarda ace kayan ɗakina da kuɗin hidimar biki yana hannun matarka ba."
Hajiya Karima tana rufe baki Daddy ya ce.
"Karima ba ki san na jima ina haƙurin zama da ke ba ko? To tun da haka ne ki je na sake ki saki ɗaya. Idan ya so sai ki yi rayuwar jin daɗi, 'ya dai ni na haife ta. Zan ga uban da zai ɗaura mata aure." Yana gama faɗa ya fice a fusace.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA GOMA
ALL NATURAL PRODUCT💃🏻
Tsumi
Tsumin tighten
Tsumin Sanyi
Tsumin basir
Tsumin 3in1
Kazar Amare yan mata.
Kazar Amare zawarawa.
Kazar Masu haihuwa.
Kazar 3in1
Kazar uwargida ko amarya da suke son burge oga.
Gumbar dabino.
Gumbar kwakwa.
Gumbar Madara.
Garin dahuwar kaza.
Garin dahuwar ciccibi.
Garin dahuwar hanta.
Garin dahuwar kwai.
Garin dahuwar kifi.
Garin hakin maye na sha da Madara ko nono.
Ingantaccen tsumin maganin sanyi, wanda aka samo daga masunta masu kamun kifi,bayan maganin infection yana magance sanyin da aka sha a ruwa ko a tiles ko irin sanyin nan mai kumbura jikin mutum.
Bugu da kari ana iya ba yara kanana masu fama da mura ko tari, haka akan dace idan yaro yana fitsarin kwance aka bashi in sha Allah yana dainawa.
Ta tuntuɓe mu a wannan lambar. 09065730652
***
Wani irin sanyi ƙafafuwan Mommy suka yi, kanta ta ji ya sara kamar an buga mata guduma. Da sauri ta tsugunna a ƙasa, saboda yadda ta ji juwa tana barazanar taɗe ƙafafuwanta zuwa ƙasa. Cikin ɗacin zuciya ta fashe da wani irin kuka, jin kukanta ya sa Ruƙayya ta shiga da gudu tana tambayarta. Yadda jikin mahaifiyarta yake rawa ne ya sa ta riƙe ta hankali a tashe ta ce.
"Mommy lafiya me yake faruwa?" Har lokacin ba ta daina kuka ba, don haka ita ma Ruƙayya hawayen ya fara zubo mata. Sai da Mommy ta yi kuka mai isarta sannan ta ce.
"Daddynku ne ya sake ni Ruƙayya."
Da wani irin kallo Ruƙayya ta bi mahaifiyarsu, sai kuma ta zabura kamar zararriya ta miƙe tana ja da baya.
"What are you trying to said Mommy? Don Allah kada ki maimaita mini wannan maganar, saki like how? Kina nufin Daddy ya sake ki, babu aurensa a kanki or what?"
Cikin kuka Mommy ta ce, "Haka nake nufi Mami, tun farkon aurena da mahaifinku ko yaji ban taɓa yi ba. Amma because of that yarinyar har yau ni mahaifinku ya saka, Mami har yanzu ina ganin kamar mafarki nake yi."
Ruƙayya tana shirin yin magana suka ji ƙarar taunar cingam ƙas ƙas ƙas, da sauri suka ɗago sai suka ci karo da Shukura a tsaye tana bin su da wulaƙantaccan kallo tana taunar cingma.
"Ke! Zo ki karɓi takardar sakin uwarki ki kai mata, sai ku yi hanzarin tattare kayanku ku bar gidan nan. Don ba zan iya ganin wannan abar tana giftawa a gaban mijina ba, kin san zuciya ba ta da ƙashi. Kada shaiɗan ya gifta su fara wani irin zama da ita." Shukura ta furta cikin isa da izgilanci. Ran Mommy sake ɓaci ya yi, za ta yi magana Ruƙayya ta ƙarasa zuciyarta tana zafi. Cike da tsanar Shukura ta karɓi takardar ta fara kantawa. Babu ko tantama rubutun mahaifinsu ta gani, sai dai a wannan lokacin ta fi ganin laifin Daddy fiye da na Shukura, saboda da bai ba ta ba; ba za ta samu ƙwarin gwiwar zuwa wurinsu tana rashin mutumci ba. Shukura ta sake yamutsa fuska ta ce.
"Yawwa, a gaggauta fita tun da ba gidan..."
Marin da Ruƙayya ta zabga mata ne ya katse kalaman da take yi, cikin jin azaba ta dafe kumatunta. Kafin ta ɗago Ruƙayya ta sake ɗauke fuskarta da mari har sai da kanta ya bugu da bango. A razane Shukura ta ja da baya, ta saka hannuwa biyu ta dafe kumatunta cikin tsoro ta ce.
"Ni kika mara Mami?"
Cikin zafin zuciya Ruƙayya ta sake yin kanta gadan-gadan ta ce, "Na mare ki, wallahi idan kika sake furta kalma mara daɗi a kan mahaifiyata sai na yi ƙasa-ƙasa da ke. Annoba makira, In Shaa Allahu da sannu za ki girbi abin da kika shuka."
Shukura ta sauke hannunta, ta nuna Ruƙayya da yatsa ta ce.
"Wallahi za ki san kin kai hannunki saman kumatuna, na rantse da Allah sai na rama a kan wannan tsohuwar kilakin." Tana ganin Ruƙayya ta yo kanta, ta fita da gudu haɗe da fashewa da kuka. Lokacin da Shukura ta fita harabar gidan, Alhaji Umar ya shiga mota kenan zai fita. Tana zuwa jikin motar ta sake rushewa da kuka tana riƙe cikinta, da sauri Daddy ya fito jikinsa har rawa yake yi ya ce.
"Me ya faru Shukura? Mene ne ya samu cikin naki?"
Durƙushewa Shukura ta yi cikin kuka ta ce. "Kawai daga kai wa Hajiya takarda, shi kenan ita da Mami suka rufe ni da duka. Hajiya har tana dukan cikina, wai gara na rasa cikin kowa ya huta. Ni gaskiya ba zan cigaba da zaman gidan nan ba, wallahi ko dai su fice su bar ni ko kuma ni na fita bar su, don wallahi ba zan zauna su kashe ni ba."
Cikin kumfar baki Daddy ya ce.
"Ita Hajiyan saboda ba ta da hankali ta dake ki a ciki? Wato saboda na sake ta sai ita da Mami su huce a kanki ko? Bari na shiga gidan." Yana gama faɗar haka ya shige da sauri, har babbar rigarsa tana shirin kayar da shi. Shukura miƙewa ta yi tana sakin murmushin ƙeta, sannan ta rifa masa baya. Maigadi shiru ya yi cike da jimami, don duk da 'yan gidan ba shiga huruminsa suke yi ba amma ya fahimci zuwan Shukura bai kawo komai a gidan ba sai sharri.
Lokacin da Shukura ta fita da faɗa Mommy ta tari Ruƙayya tana faɗin, "Ruƙayya kanki ɗaya kuwa? Kin san me kika aikata? So kike ki janyo wa kanki masifa kina zaune ƙalau?" Hawaye yana zuba daga idonta ta ce.
"Mommy ba ki ji abin da take faɗa ba? Duk wannan maganganun sai na yi mata shiru, yanzu saboda Allah ban da Daddy ya ba ta fuska ta isa ta faɗa miki haka?"
"Tun da mahaifiyarku ta ɗaure muku ai dole ku yi rashin mutumcin da kuka ga dama." Daddy ya furta a zafafe, cikin sauri Ruƙayya ta waiga ta ce.
"Daddy ka ga..."
Tas! Daddy ya ɗauke fuskarta da mari, kafin Ruƙayya ta yi motsi ya sake sauke mata wani. Rai a ɓace ya ce.
"Don ba ki da mutumci matar tawa uwarki za ta saka ki daka? Ni za ku wulaƙanta saboda rashin tarbiyya."
"Ai ba ita ba ce har da Hajiyan, kuma wallahi sai ka rama mini ko ni na rama." Shukura ta faɗa a shagwaɓe. Daga Mommy har Ruƙayya ɗagowa suka yi suna kallon Shukura, ta fakaici idon Daddy ta sakar musu gwalo sai kuma ta sake fashewa da kuka.
"Ni ba zan rama miki ba, sai dai ki rama da kanki."
Daddy ya faɗa yana matsawa gefe. Babu ko kunya Shukura ta matso da niyyar yi wa Mommy mari a fuska. Ruƙayya ce ta sha gaban Mommy, fuska a haɗe tana wurgawa Shukura mugun kallo.
"Za ki matsa ta rama marin da uwarki ta yi mata ko sai ranki ya ɓaci?" Daddy ya buga wa Mami tsawa. Zuciya a ƙeƙashe ta ce.
"Duk wani hukunci da za ta yi ta sauke shi a kaina, amma idan ta sake ta ɗora hannu a jikin mahaifiyata wallahi za ta gane kurenta." Cikin zafin zuciya Daddy ya sake marin Ruayya ya ce.
"Haka Karima ta gurɓata tarbiyyarku ban sani ba? Ba za ki matsa ba sai na sumar da ke."
"Ko za ka kashe ni Daddy ba zan bari wannan matsiyarciyar ta mari mahaifiyata ba." Ruƙayya ta faɗa zuciyarta a dake, don a yadda take ji a ranta komai za ta iya aikatawa a kan mahaifiyarta. Tana nan tsaye Daddy ya rufe ta da duka, amma taurin kai irin na Ruƙayya ya sa ta ƙi motsawa daga wurin. Kuka Mommy ta saka, ta janye Ruƙayya ta ce.
"Ba sai ka illata mini yarinya ba, za mu tattara mu bar maka gidanka." Fisge Ruƙayya Daddy ya yi, a zuciye ya dubi Mommy kamar zai kai mata duka ya ce.
"Kada ki sake shiga tsakanina da 'yata idan ina hukuntata. Idan ba haka ba wallahi ranki zai yi mummunan ɓaci." A daidai lokacin Haidar ya shiga, jin abin da ake tattaunawa ya sa ransa ɓaci. Shukura ta sake fasa wani sabon kukan ta ce.
"Yanzu shi kenan sun daki banza da wofi ko? Wallahi ba zan sake kwana a gidan nan ba, kuma wallahi idan ban rama ba sai ka sake ni" Da sauri Daddy ya janyo Shukura jikinsa ya ce, "Babu inda za ki je, kuma mari kamar kin rama kin gama." Shukura da ke gaban Mommy ta ɗaga hannu ta zabga mata mari a fuska, ko sauke hannu ba ta yi ba Haidar ya ɗauke fuskarta da mari. A zafafe Daddy shi ma ya sauke wa Haidar mari sannan ya ce.
"Ni za ka wulaƙanta ka tozarta Haidar? Ashe kai ma ba ka da mutumci?" Rai a ɓace Haidar ya ce, "Daddy ba ka ga abin da ta yi ba ne? Ni fa dama na jima ina tara yarinyar nan. Wallahi tuntuni darajarka take ci, da tuni na ɓarar da ita." A zafafe Daddy ya ce.
"Za ka gane ba ka da hankali kuwa, idan hauka ne a kanka zan sa a sauke maka shi." Yana gama faɗa ya zaro waya ya nemo wata lamba, yana jin an ɗauka ya ce.
"Hello officer, ina son ganinka yanzu. Please ka taho da yaranka." Daga haka ya katse wayar, da mamaki Mommy take kallonsa kamar za ta tanka masa sai kuma ta haƙura. Suna nan tsaye suka ga ya ja hannun Shukura yana lallashi suka fita. Daga Haidar har Ruƙayya rungume Mommy suka yi, Mommy da Mami sai kuka suke yi. Haidar ne ma yake iya lallashinsu, ba su ɗauki lokaci ba suka haɗa kaya a cikin akwatunansu. Gabaɗaya kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci suna cikin matsananciyar damuwa. Suna gab da fitowa suka ji ƙarar motar 'yan sanda, babu jimawa suka ji muryar Daddy yana cewa.
"Ku shigo ga yaron nan, ku zo ku tafi da shi. Ba shi tarbiyya ko kaɗan yaron nan, duk wanda ya zo belinsa kada a bada shi sai saka hannuna. Ku hora shi yadda ya kamata." Mommy da su Haidar suna tsaye, suka ga 'yansanda biyu sun shiga falon Mommy. Nan take suka saka masa hangoff a hannu, Daddy ya ba su umarnin su tafi da shi. Mommy tana kuka tana riƙe shi haka suka tasa ƙeyarsa suka tafi da shi, da ƙyar Ruƙayya ta lallashi Mami ta tsagaita da hawaye. Sannan suka ɗauki jakunkunansu suka fito harabar gidan.
GIDAN HAFIZ
Wani dogon tsaki Bilkisu ta saki cikin jin haushi ta ce.
"Da ka san ba kai kaɗai ba ne ai da sai ka sanar da ni." Ajiye akwatin Amina ya yi ya rungumo ta jikinsa ya ce.
"Kafin a fara faɗan ya kamata a yi mini oyoyo ɗin tukunna." Ajiyar zuciya Bilkisu take saukewa akai-akai, saboda yadda ta ji zuciyarta tana harbawa kamar ta faɗo daga ƙirjinta. Amina ta taɓe baki ta ce.
"Sannu da gida Aunty."
A sheke Bilkisu ta dube ta, ta ce. "Ke zan yi wa sannu, ni da nake gidan mijna sannun me za ki yi mini." Amina ta fahimci maganarta, don haka ta ce.
"Ai da yake tare muke da Habibi, na san kuma kin sha aikin gida shi ya sa na miki sannu. Ga shi sai da na ce ya kira ki kafin mu ƙaraso amma ya ƙi."
Bilkisu ji ta yi kamar an zuba mata borkon, Hafiz da ke tsaye mamaki ya kama shi, don shi dai ya san bai yi haka da Amina ba. Yana shirin yin magana Amina ta yi gaba tana faɗin.
"Baby ka shigo mini da akwatin, kuma ni yau kwana za ka yi kana matsa mini ƙafa don ciwo take yi mini."
Bilkisu jin haka ya sake hargitsa ta, rai a ɓace ta saki hannun Hafiz ta wuce ɗaki fuuuu kamar za ta tashi sama. Amina tana ganin haka ta saki murmushi, a ranta ta ayyana.
'Ashe dama matar nan sakarya ta mayar da ni, shi ne take kunna ni ban sani ba. Ai kuwa da ni take zancen.'
Tana shiga ɗaki Hafiz ya shigar mata da akwatin, sannan ya fito ya nufi ɗakin Bilkisu. A kan kujera ya same
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 35