Ɗagowa ta yi ta kalle shi a sheƙe ta ce.
"Faɗi maganarka ai kunne ne yake ji."
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "Bilkisu kin san ina sonki ina ƙaunarki, kuma kin san babu macen da zan kawo na bari ta raina ki, ko ta ci mutumcinki. Kin san ba zan ɗauki haka ba, duk abin da kike wa 'yan uwana ina sane, amma duk da haka ban bari ɗaya daga cikin ƙannena sun raina ki..."
"Don Allah idan ba wata magana mai muhimmanci za ka faɗa mini ba ka ƙyale ni." Bilkisu ta faɗa rai a ɓace. Girgiza kai ya yi yana danne ɓacin ransa ya ce.
"Muhimmancinta ne ya sa na same ki da maganar. Bilkisu yanzu ba ki ji kunyar saƙon da kika turawa Amina a matsayin ni ba ne? Ko kin ɗauka aure wasan yara ne da za ki yi wannan shirmen? Don Allah ki kama girmanki Bilkisu, ina respecting ɗinki a wurin Amina. Don haka ita ma ko da wasa, ba ta taɓa kawo maganar wargi a kanki ba, ina girmamaki fiye da yadda kike tsammani. Ki girmama kanki ta yadda ba za ki bada ƙofar da yarinyar nan za ta raina ki ba, ni idan kin yi mini zan iya shanyewa. Amma kin san ba lalle ne ita idan kin yi mata wani abin ta ɗaga miki ƙafa ba..."
"To duk abin da za ka saka ta yi mana, wallahi duk shegiyar da ta kawo mini raini sai na yi mata dakan sakwara." Bilkisu ta faɗa tana tashi zaune. A ɗan zafafe Hafiz ya ce, "Kada ki sake zagar mini mata."
Bilkisu ji ta yi kamar ya watsa mata ruwan zafi, don haka a zafefe ta ce.
"Na zaga idan ka ga dama ka rama mata, 'yan iskan 'yan mata ba za su nemi mijinsu su aura ba sai mace ta raini mijinta su zo su aure suna tunƙahon mijinsu ne." Jin ba zai iya ɗaukar maganganun da Bilkisu take faɗa ba, ya sa shi ficewa daga ɗakin ya nufi ɗakin yaran ya kwanta a can.
Kamar yadda Hafiz ya faɗa cikin ƙasa da sati biyu ya ƙarasa haɗa duk wani abu da ake buƙata na lefe, juma'a tana zuwa aka kai kaya gidansu Amina. A nan su kuma iyayenta suka tsayar da ranar juma'a mai zuwa, a matsayin ranar da za a yi wuni da kai amarya. Hafiz ya yi ƙoƙari sosai, akwati biyar ya yi mata daidai rufin asirinsa. Ya ba ta kuɗin kamu da gyaran jiki don shi ba shi da ra'ayin zuwa wurin kamu. Haka ita ma Bilkisu akwati guda ya cika mata da kaya, dangin atamfofi da lesuna da kayan shafe-shafe har da kayan bacci. Yaran kuma ya saya musu sababbin ƙananan kaya kala ɗaiɗai da shadda kala bibbiyu.
A cikin satin Hafiz ya sa aka fitar da kujerun Bilkisu aka kai wurin kafinta ya gyara mata su, aka saka sababbin sosuna da sababbin yadi suka dawo kamar sababbi. Sai labulaye da ya saya mata masu yanayi da kujerunta duk don ya faranta mata. Sannan ya ba ta dubu hamsim ya ce ta yi duk wani gyara da za ta yi dangin kitso da ƙunshi. Ana saura kwana biyu Amina za ta tare ya kira masu fenti suka yi wa gidan fenti, sai dai jere ne ya hana 'yan uwan Amina su yi a ranar saboda yana tsoron kada Bilkisu ta aikata abin da za ta kunya shi a wurinsu.
Ranar juma'a tun da sassafe 'yan uwan Amina suka je gidan Hafiz yin jere, kallo ɗaya suka yi wa Bilkisu suka fahimci zai yi wuya a yi zaman lafiya da ita a cikin gida. Don haka suka dinga kaffa-kaffa, gudun kada ta ce sun yi mata wani abin. Saboda sun ji sai faɗa take yi wa yara da habaici, kuma abu kaɗan yaro zai yi mata sai su ji ta rufe shi da duka. Kusan azahar suna ta aiki sai ga Fadila ƙanwar Hafiz, ta yi sallama cikin gidan hannunta ɗauke da ƙatuwar cooler. A ƙofar ɗakin Amina ta tsaya suka gaisa da masu jere, ta miƙa musu abincin ta yi musu bayanin kanta. Ta sake fita ta shigo da ruwa da manyan lemuka ta ajiye musu, sannan ta nufi ɗakin Bilkisu.
Tun da Fadila ta shigo Bilkisu ta hango ta, ta cikin labule. Ta dubi ƙanwarta Hafsa ta ce.
"Hmmm dangin miji ko baƙaƙen munafukai, dubi Fadila can ki ga. Wai ita aka aiko ta kawo musu abinci, saboda neman wurin zama. Wai yanzu duk yadda nake da su Fadila, haka za su yi mini su koma ɓangaren amarya." Bilkisu ta ƙarasa maganar cikin ƙwafa.
Ajiyar zuciya Hafsa ta sauke ta ce, "To ya za ki yi ai sai haƙuri, kin san mijinki ne fa ɗan'uwansu. Kuma duk abin da yake so shi za su so, tun da ke dai bare ce a cikinsu." Shiru Bilkisu ta yi ta cigaba da girgiza ƙafa, suna nan zaune Fadila ta shiga ɗakin da murmushi bakinta ɗauke ta sallama.
"Ina wuni Aunty Bilkisu." Fadila ta faɗa cikin girmamawa, tun daga ƙasa Bilkisu ta ɗebo Fadila da harara ta watsar a gwasale ta ce.
"Lafiya."
Shiru Fadila ta yi tana tsaye, don ba ta ga fuskar da za ta zauna ba. Bilkisu ta ce, "To ai sai ki koma can tun da wurinsu kika zo."
"A'a abinci ne kawai na kawo musu." Fadila ta faɗa a sanyaye. Kamar Bilkisu tana jira ta ce.
"Ai shi ne na ce ki koma can, tun da ni matar yayanki ce waccan ɗinma da za ki wurin matarsa ce." Fadila ba ta tanka wa Bilkisu ba ta fice daga ɗaki ta yi wa 'yan'uwan Amina sallama ta tafi.
"Haba Aunty Bilkisu, ki dinga rage wani abin mana. Wai ba ki ga yadda Aunty Murja ta yi ba ne, kowacce mace fa tana jin kishi kawai iya taku ne." Hafsa ta furta, don ta lura idon yayarta ba ƙaramin rufewa ya yi ba. Cikin masifa ta ce .
"Ita daban ni daban, malama kema idan ɓata mini rai za ki yi ki fice ki ba ni wuri." Hafsa ta yi shiru tana mamakin zafin ran 'yar uwarta.
Koda 'yan uwan Amina suka gama jere ba duka suka tafi ba, sai aka bar mutum biyu a ɗakin da yayarta da kuma ƙanwar babanta. Suna gani Bilkisu shiga ɗaya-biyu idan ta yi sai ta yi musu habaici, ko ta saki tsaki tana harararsu. Sai da aka idar da sallar Magriba, sannan Hafiz ya aika aka ɗauko Amina zuwa gidansa.
GIDAN ALHAJI UMAR
Tun ranar da Shukura ta cika kwana shida a gidan Hajiya Karima ta yi ɗan jiƙe-jiƙenta, dangin abin da ya shafi tsimi da sauransu. Dama tun asali Hajiya Karima mace ce mai gyara sosai, tana da tsafta uwa-uba ba ta wasa wurin gyaran jikinta. Ta yi wannan haɗe-haɗen na musamman ne, saboda yadda ta lura da rawar jikin da Daddy yake yi a kan Shukura. Ba ta son ko kaɗan ya ga gazawarta, ko ta fuskaci wulaƙanci a wannan ɓangaren daga wurinsa. Saboda ta san duk son da namiji yake wa mace dole tana buƙatar gyara, kuma ko namiji bai fito ya bayyana ba idan bai samu yadda yake so ba za ta ga alama.
Ko lokacin da Alhaji ya shiga ɗakinta, ta gama shan tsumin gumbar nonon raƙumi da ta sassaƙen ɓaure. Yana shiga ɗakin ta ƙare masa kallo duk sai ta gan shi a firgice, ƙarasawa ya yi gefen kujerar da take zaune ya sakar mata murmushi. Martanin murmushin ta mayar masa, ya riƙo hannunta ya ce.
"Mommyn Mami kin ga yadda kika yi kyau kuwa?"
Murmushi ta yi ta ce , "Wanne irin kyau kuma, kai da kake da amarya." Ta faɗi haka don ta ji me zai ce.
"Kowa ai da irin nata kyawun."Ya furta mata yana murmushi. Shiru ta yi tana jin daɗi har a ranta, saboda ta ji an ce maza idan suka yi aure haushin iyayen gidansu suke ji. Amma ita sai ta ji yana yabonta, tana cikin tunani ta ji ya ce.
"Dama zuwa na yi na nemi alfarma a wurinki." Ba ta kawo komai a kanta ba ce.
"Alfarma kuma Daddyn Mami? Wacce iri kenan?"
Gabansa yana faɗuwa, ya zaro kuɗi daga aljihunsa ya dire a gabanta. Muryarsa tana rawa ya ce.
"Amm... dama... so nake ki sayar mini da kwanaki bakwai."
Dum! Ta ji kanta a saman kanta kamar an buga mata guduma, wani abu ne ya turniƙe mata ƙirji. Murya a ɗan sarƙe ta ce.
"Ban... ban gane ba." Kunya ce ta kama shi, amma har cikin zuciyarsa yake jin ba zai iya ɓata wa Shukura rai ba, uwa-uba ba ya son yin nesa da gangar jikinta. A tattaro mayafin jarumta ya yafa wa kansa sannan ya ce.
"Ina nufin ki sayar mini da kwana bakwai na ƙara a wurin Shukura." Ya ƙarasa maganar yana satar kallonta. Haɗe fuska ta yi tamau, rai a ɓace ta ce.
"Ban amince ba Alhaji."
Ransa ne ya fara ɓaci, don haka ya ɗauki kuɗin ya ɗora mata a cinya ya ce.
"Shi ya sa na kawo miki dubu hamsin ga shi nan, kwana bakwai fa kawai zan ƙara haba Hajiya." Ya ƙarasa maganar a ɗan tsawace. Da mamaki take kallonsa ita ma, don ta sake ɓata masa rai sai ta ce.
"Ka ɗauki kuɗinka ba na so, kuma kwana ban lamunce ba."
Da sauri Alhaji ya ce, "Au haka kika ce? Ke wacce irin mace ce ne wai? Shekara nawa muna tare da ke kawai don na ce ki ƙara mini kwanaki za ki ɗaga wa kanki hankali? Yarinyar nan fa 'yar cikinki ce, don Allah ban da abin mata kishin me za ki zauna kina yi da ita?"
Shiru Hajiya Karima ta yi har lokacin ba ta daina bin sa da kallo ba, zuciyarta ta fara wassafa mata abubuwa da dama.
'Kada ki yarda, idan kika amince masa wallahi daga ranar yarinyar nan za ta raina ki.'
'Ki yi haƙuri ki kyale shi ya yi kwanakin da yake so, 'ya'ya gare ki idan kika biye wa namiji ba kunya gare shi ba. Zai iya aikata abin da zai shafi tarbiyyar yaranki ko kuma ya sa su fahimci rashin jituwa a tsakaninku.'
Shawarar ƙarshe da zuciyarta ta ba ta, ta ɗauka don haka ta ce.
"Shi kenan babu damuwa, kwana bakwai ai kamar yau ne." Washe baki ta ga ya yi, ya matsa kusa da ita ya rungumo ta ya ce.
"Yawwa ko ke fa Hajiya, idan kika kwantar da hankalinki Shukura ba baƙuwar zafi ba ce. Yanzu akwai abin da kika buƙata ne?" Girgiza masa kai ta yi a sanyaye ta ce.
"Babu abin da muke buƙata."
Miƙewa ya yi ya fice daga ɗakin, ya nufi ɗakin Shukura. A kwance ya same ta, ya rungumo ta ya ce.
"Baby ta amince."
Da sauri Shukura ta riƙe shi ta ce.
"I love you Babyna." Fake ya sakar mata a goshi ya ce.
"I love you too my baby."
Ɗan lumshe ido ta yi ta ce, "To amma idan mun gama yau ina son shaƙatawa, almost six days kenan fa ina gida Baby." Shiru ya yi ya ce.
"Don't worry baby, idan wannan ne an gama."
Farr Shukura ta yi da ido sannn suka cigaba da hirar soyayya.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
https://chat.whatsapp.com/IAZVt2Pz4LvIcklCxSTHwo
SHAFI NA HUƊU
A daren ranar sai da Alhaji ya fita da Shukura, ba su suka dawo ba sai da dare ya tsala. Don gabaɗaya yaran gidan sun yi bacci sai Hajiya Karima ce ta ji motsin shigowarsu, shiru ta yi tana mamakin wai ita ce yau Alhaji ya sayi kwana a wurinta. Murmushin takaici ta yi tana jin hawaye mai ciwo yana zubo mata, ganin tunani zai yi mata yawa ya sa ta ɗauki carbi ta kwanta da shi tana lazumi har bacci ya yi awon gaba da ita.
A washegarin ranar ma da yake Ruƙayya ba ta da lecture ta safe ita da Mommynta suka shiga kicin suka sarrafa abin karyawa. Kuma a ranar ne Hajiya ta ci alwashin yi wa Alhaji magana dangane da girki, tun da ta yi mata na kara wato girkin sati ɗaya. Tana son ta ji idan raba girki za su yi, ko kuma haɗewa za su yi. Su Shukura ba su fito ba sai kusan sha biyun rana, a lokacin yaran gidan duka sun tafi makaranta. Hajiya Karima tana zaune a falo tana kallo suka shiga, gaisawa suka yi da Alhaji sai washe baki yake yana haba-haba da ita. Shukura ba ta gaida ta ba, sai ita ce ta gaishe ta. A yatsine Shukura ta amsa mata, Hajiya ta yi kamar ba ta ga irin kallon rainin da take yi mata.
Kwanciya Shukura ta yi a jikin Alhaji ta ce, "Baby yunwa nake ji." Jin haka ya sa a birkice Alhaji Ya ce.
"Hajiya ina abincin ne?"
Sauke ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Yana kicin." Miƙewa ya yi da kansa ya shiga kicin ya ɗauko musu ya ajiye, har zai zuba musu Shukura ta maƙale kafaɗa ta ce.
"Mu je can mana baby sai na fi sakewa."
Kamar wanda ake ba wa umarni haka ya yi zumbur ya miƙe zai fita, cikin sauri Hajiya Karima ta ce.
"Alhaji ina son magana da kai." Ɗan satar kallon Shukura ya yi sai ya koma ya zauna. Hajiya Karima ta ce.
"Dama game da girki ne, na ce za a haɗa girki ne ko kowa zai yi nasa? Saboda ina son sani ne don Shukura ta karɓi girkint." Shiru ya yi yana son jin abin da Shukura za ta faɗa, don yana gudin ya ɗauki wani zaɓin ta ce bai yi mata ba, Hajiya kuma ta ga kamar zaɓin Shukura yake bi.
"Tabɗi, gaskiya ba zan iya girkin haɗaka ba. Duka yaushe na zo da zan fara girka uwar tukunya, kowa dai ya yi nasa kawai shi ne magana." Shukura ta furta cike da tsiwa, jinjina kai Hajiya Karima ta yi tana jin zuciyarta na zafi. Kasa daurewa ta yi ta ce.
"To ai kin san yana da tawagar kika aure shi haka." Kamar Shukura tana jira ta ce.
"Eh saboda shi mijin mace huɗu ne, kuma don na aure shi ba shi zai sa na yi wa 'ya'ya bauta ba."
Hajiya Karima za ta yi magana Alhaji ya ce.
"Yanzu dai duk ba wannan ba, shi kenan kowacce ta yi girkinta ina ganin haka zai fi." Amsawa Hajiya Karima ta yi ta miƙe ta shiga ɗaki, taɓe baki Shukura ta yi ganin Alhaji zai bi Hajiya Karima ya sa ta riƙe hannunsa suka nufi ɗakinta.
Alhaji Umar mai leda shi ne cikakken sunan Daddy, asalinsa mutumin Jigawa ne. Neman kuɗi ne ya kawo shi Kano, shi da Hajiya Karima auren saurayi da budurwa aka yi musu, mahaifinta da mahafinsa duka abokai ne. Don haka aka haɗa su aure a wancan lokacin, lokacin da aka yi aurensu Alhaji dako yake yi a kasuwar singa da ke Kano. Rashin wadataccan ƙarfi ya sa bai kawo Mommy a lokacin ba, har sai da ya ta haifi Ruƙayya (Mami). Da yake a lokacin ya ƙara samun cigaba ya zama yaron shago. Daddy mutum ne mai zuciyar nema, kuma a tsaye yake a kan iyalinsa daidai gwargwado. Ba za ka saka shi a cikin sahun hamshaƙan masu kuɗi ba, kuma ba zai shiga sahun talakawa ba. Shi mutum ne mai rufin asiri daidai misali, yana da dukiya mai yawa da kadarori.
Hajiya Karima macece mai haƙuri da zurfin ciki, tun asali ba ta da hatsaniya. Zamanta da Alhaji ne ya sa a haka ake ganin ta yi baki, duk da wanda bai santa a baya ba zai dinga yi mata kallon marar son magana.
Haihuwarta takwas da Alhaji Umar biyu sun rasu, sai guda shida da suke raye. Ruƙayya ita ce babba tana shekara shirin da huɗu, sai Haidar yake bin ta. Shi kuma tsiran shekara ɗaya ne tsakaninsu da yake kwanikar haihuwarsu ta yi. Sai Nabil, Nazir, Sadik da kuma Sulaiman ɗan autanta mai shekara goma. Lokacin da Alhaji ya yi aure bikin Ruƙayya saura wata biyu, don haka take ta Allah-Allah ta bar gidan ko ta rage ganin kayan takaici. Ita da Haidar gabaɗaya suna level 400 a makarantar Maitama Sule University da ke Kano, Nabil da Nazir kuma sun yi candy neman Admission suke yi. Sai Sadik da yake ƙaramar sakandire, shi kuma Sulaiman yana ajin ƙarshe na firamare ba.
Tun da Alhaji ya raba girki kowa ya koma yin nasa, don haka wani lokacin sai a shafe wuni guda wani bai ga wani ba a cikinsu. A haka kwanaki suka dinga shuɗewa har Alhaji ya dawo ɗakin Mommy, yanayinsa babu yabo babu fallasa. Sai dai ta lura wuni Shukura ta yi tana shige da fice a gidan tana ɓace-ɓacen rai. Ita Hajiya abin har mamaki ya bata, saboda gani ta yi har idan kishi ne ai ita ya kamata ta nuna kishinta. Tun da ita ta shafe shekara da shekaru da shi suna tare. A daren ranar da Alhaji ya dawo ɗakin Mommy cikin dare suna kwance suka ji ihun Shukura, daga Daddy har Mommy rige-rigen fita suka yi don ganin abin da ya faru. A tsaye suka same ta daga ita sai wata yaloluwar rigar bacci, samarin gidan da su Ruƙayya ne su ma duk suka firfito. Ganin yanayin da take ciki ya sa su Haidar suka koma ɗaki, kallo ɗaya Ruƙayya ta yi mata ta saki tsaki har sai da Shukuran ta waigo suka haɗa ido, sannan Ruƙayya ta yi tafiyarya ɗaki.
"Me ya faru kike ihu Shukura?" Daddy ya furta cikin kulawa. Kuka ta rushe da shi ta ce.
"Ina kwance kawai na ji an shigo mini ɗaki, ban yi aune ba na ji an fara jan zanin jikina ƙasa." Cikin sauri Daddy ya ce.
"Shigowa? Ɗakin naki aka shigo?" Gyaɗa kai ta yi tana cigaba da kuka, haskawa ya fara yi ya ga ko ina a rufe kamar yadda yake. Ya haske saman doguwar katangarsu bai ga alamar za a iya hawa ba, haka daga ƙofar da za ta sada ka da babban gate a datse take. Cikin mamaki Dadday ya ce.
"Ko dai mafarki kika yi Shukura?"
"Ni babu wani mafarki, bayan ana ji na yi ihu na ji an fito da gudu kuma ba fita aka yi ba a cikin gidan nan ne."
Wani irin ɓacin rai ne ya dira a zuciyar Hajiya Karima, don ta fahimci sarai makirci ne da tuggu za ta yi wa yaranta. Rai a matuƙar ɓace ta ce, "Ke yarinya ki shiga hankalinki, wallahi kada ki kuskura ki saka yarana a cikin makircinki."
"To ni me nace? Na ce 'ya'yanki ne suka shigo? To ko dama can haka yaran na ki suke?"
Shukura ta yi maganar tana narkewa, a zafafe Hajiya Karima ɗago za ta yi magana Alhaji ya ce.
"A'a Hajiya ki dai bari a gama jin bayaninta, da kike musawa Shukura yarinya ce da za ta yi ƙarya ne?" Jikin Hajiya Karima wani irin sanyi ya yi, ta zuba wa Alhaji ido cike da mamaki.
GIDAN HAFIZ
Sai da 'yan kawo amarya suka watse sannan Hafiz ya shiga gidan cikin shigar angoncinsa ta babbar riga. Ɗakin Bilkisu ya fara shiga, ya same ta a kwance a kan gado idanunta duk sun kumbura alamun ta ci kuka ta more. Duk sai ya ji tausayinta ya kama shi, zama ya yi a bakin gadon ya ce.
"Ummu Sayyid." Ɗagowa ta yi ta dube shi, sai ta ga ya yi mata wani irin kyau. Nan take kishi ya mamaye ta, hawaye ya fara zuba daga idonta. Hannu ya saka ya goge mata, tana jin hannunsa ba ta hana shi ba. Cikin tausasawa ya ce, "Zo mu je falo." Girgiza masa kai ta yi ta ce.
"Ba zan iya ba Abban Sayyid."
"Don Allah ki daina kukan yana damuna." Ɗagowa ta yi ta zuba masa ido ta ce.
"Yanzu fa wurin wata za ka tafi ko? Dama Hafiz za ka iya mu'amala da wata macen bayan ni..."
"Don Allah ki daina wannan maganar Bilkisu, ki taso mu je please." A sanyaye ta zuro ƙafafuwanta ƙasa, ta ɗauki hijabi ta saka tana goge fuskarta. Ɗakin Amina ya shiga ita ma ta kira ta, Bilkisu tana ganinta gabanta ya shiga faɗuwa. Nasiha Hafz ya fara yi musu, jin ba za ta iya danne abin da yake cikin zuciyarta ba ya sa ta miƙe fuuuu ta shige ɗaki. Girgiza kai Hafiz ya yi, ya ce Amina ta koma ɗakinta, sannan ya shiga ɗaki wurin Bilkisu. Yana shiga ya hango ta ta cusa kanta cikin ƙafafuwanta, ƙarasawa ya yi gabanta sai kawai ta ɗago ta rumgume shi ta saki sabon kuka. Riƙe ta ya yi sosai, musamman yadda ya ji jikinta yana rawa. Murya a dashe ta ce.
"Mutuwa zan yi."
"Ki daina faɗin haka Bilkisu, ke fa musulma ce don Allah ki ɗauki wannan auren a matsayin ƙaddara."Hafiz ya furta cikin lallashi, sannan ya ajiye mata ledar kazarta da lemuka. Sallama ya yi mata har ya juya zai tafi ta ce.
"Au da gaske wurinta za ka je?"
Shi maganar ma dariya ta so ba shi, don ya lura wani abin da Bilkisu take yi kamar ba ta cikin hayyacinta. Ya waigo ya ce.
"Eh." Sai hawaye ya cigaba da zuba daga idonta cikin kuka ta ce.
"To ka je duk abin da ka yi mini, Allah ya yi maka Hafiz kuma ka zo ka ɗauki tsinanniyar kazarka ba na ci." Ta ƙarasa maganar tana yin jifa da ledar da ya ajiye. Hafiz bai kula ta ba ya wuce ɗakin Amina, sai da ya ba ta haƙurin jimawar da ya yi sannan suka shiga gabatar da abin da yake gabansu.
Kamar wata wacce aljanu suka kama haka Bilkisu ta dinga ɓurumtu tana shige da fice a tsakar gida, kusan yadda ta ga rana haka ta ƙarasa ganin darenta. Da asubar fari ta ji Hafiz ya haɗa musu ruwan wanka ya kai banɗaki, jin haka ya sake ɗaga hankalin Bikisu. Da ƙyar ta lallashi kanta, ta samu ta gabatar sallar asuba.
Tun asuba ta shiga ɗakin yaran ta dinga jibgarsu tana tashinsu sallah, abu kaɗan za su yi za ta fara zaginsu tana duka. Tsakar gida ta fita, ta cigaba da kwaramniya da kwanuka tana fafutukar ɗora abinci. Su dai yaran shiru suka yi, duk suka takure wuri ɗaya. Tsoron mahaifiyarsu duk ya kama su, sun san dai ranar asabar babu makaranta. Kuma sun ga sai shiri take yi tana musu masifar su yi su ci abinci kada su makara, tsoron kada ta dake su ya sa suka gagara faɗa mata. Don haka a ranar tun bakwai da rabi ta gama shirya su, ta ƙarasa ƙofar ɗakin Amina ta shiga bugawa da wani irin ƙarfi.
Tun da Hafiz ya yi sallar asuba bayan ya leƙa Bilkisu da yara, ya koma ɗakin Amina ya kwanta suka koma bacci. Suna tsaka da bacci suka ji bugun ƙofa a tsakar kansu, a hargitse ya fito daga shi sai gajeren wando yana faɗin.
"Lafiya Bilkisu me ya faru ne?" Kallon yanayin da yake ciki ya sake turnuƙe ta, a fusace ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 35