Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wa Maman Nana ta kawo miki gobe..." Tun bai gama magana ba ta katse shi, "Maman Nana fa? Ka san me kake faɗa kuwa Jafar?" Dariya ya yi a fili ya ce, "Saboda zan ba wa maman Nana waya ta kawo miki har shi ne ya sa kike kiran sunanan gatsal? Zan ba ta ta kawo miki kamar yadda na faɗa, zan ce mata mijinki ne ya ba hi sautin waya daga kasuwa. Sai na ce ya miƙo miki, amma sai na kintaci lokacin da Naziru ba ya gida don kada a samu matsala. Idan kuma na samu wata mafitar shi kenan, ko kina da wata shawarar?" Kamar Jafar yana ganinta ta girgiza kai ta ce, "A'a babu." Sun ɗan ɗauki lokaci suna waya sannan sula yi sallama cile da kewar juna. Fauziya tana nan zaune a gefen gado tana hawaye ta fara jin sautin munaharinsa, wanda hakan ne yake tabbatar mata da tuni bacci ya yi awon gaba da shi. Haska shi ta yi da wayar hannunta, tana ƙare masa kallo. Ta kawar da kai gefe cikin sanyin murya ta ce. "Ya Allah Ya Ubangiji ba don ni ba, ba don halina ba. Allah ka shirya mini mijina." A inda yake ta bar shi, ita kuma ta haye gado ta kwanta zuciyarta a cunkushe ɓacin rai, a haka bacci ya yi awon gaba da ita. Sai da asuba ta yi cikin bacci ta ji Kabir yana tashinta, a hankali ta yunƙura ta tashi zaune. Sai ta ga ya yi mata kalar tausayi ya zauna a gefenta, ya saka hannunsa ta bayanta ya riƙo ƙugunta. "Don Allah ki yi haƙuru Fauzina!" Kabir ya furzo kalamansa ƙasa-ƙasa. "Zuwa yanzu ya ci avw na haddace waɗannan kalaman naka, ka sake ni Abban Na'ima zan yi sallah. Ta ba shi amsa rai a ɓace, Kabir ya riƙo ta a jikinsa tsam ya ce. "Wallahi ba laifina ba ne, su Abbati ne suka ingiza ni amma In Shaa Allahu wannan ne ƙarshe." "Ashe idan su Abbati suka ce ka shiga wuta sai ka bi su ko? A yanzu babu wata magana da za ka faɗa mini na yarda da kai a kan shaye-shaye. Su Abbati sun isa su yi maka dole idan kai ma ba ka so ba." Kabir ya yi shiru har sai da Fauziya ta gama sannan ya shiga lallaahinta. Alwala ya fita ya yi, ya wuce masallaci. Bayan ya dawo cike da daɗin baki ya ce. "Ni kuwa ya maganar Dillaliya? Allah Ya sa ta taya kayan da mutumci." Da yake a lokacin Fauziya ta ɗan sauko ta ce, "Ta taya shi dubu saba'in har ta bada rabin kuɗin." Fauziya ta miƙe ta buɗe drower kayanta, jakar ratayarwa ta ɗauko ta zura hannu ta zaro kuɗin ciki ta miƙa masa. "Ragowar ta ce sai bayan kwana uku, an jima idan gari ya waye ta ce za ta zo da wanda zai ɗauka." Kabir ya janye hannunsa daga kuɗin ya ce, "A'a ki ajiye a wurinki ko jari sai ki ja da su" Girgiza kanta ta yi ta ce, "A'a ka cika ka sayi wani abin na aikin gidan can, ka an rage. Idan ta kawo cikon kuɗin, kafin nan kai ma ka samu wasu sai ka haɗa da na wurinka kafin dai ranar tashinmu an rage abin da za a rage." Fauziya ta ɗan kalli ɗakinsu da shinfiɗar su Na'ima cikin damuwa ta ce. "Na gaji da zaman da muke yi ɗaki ɗaya Abban Na'ima. Yaranmu sun fara wayo kwana da su a ɗaki ɗaya zai iya haifarwa tarbiyyarsu da matsala." Kabir ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Haba ne Fauzina, amma kuɗaɗen da kike ba ni a ginin nan ina gudun wani abu a nan gaba." Yanayin yadda ya yi mata maganar cikin sanyin murya ya sa jikinta ya yi sanyi, ta dube shi a sanyaye ta ce. "Me kake gudu Abban Na'ima?" "Ina gudun kada watarana abin abu ya haɗo mu ki yi mini gori, sannan tarin kuɗaɗen da kika ba ni lissafinsu nake yi. Idan Allah Ya buɗa mana nan gaba zan biya ki kuɗinki." Maganar Kabir ba ƙaramin ɓa ta ranta ya yi ba, domin duk abin da take yi wa Kabir tana yin sa tsakani da Allah ne domin a ganinta rufin asirinsa tamkar rufin asirinta ne. A irin kalubalen rayuwar da ta fuskanta a kaf faɗin duniya gifa biyu ne ya zame mata gata kuma madogararta. Daga gidan mahaifinta sai gidan mijinta, gidan mijin da take fatan sai dai mutuwa ta ɓamɓare ta daga ginin turɓayarsa. Gidan mahaifinta kuwa a yanzu ba ta fata ko burun kawo wata ƙaddara da za ta kwashe ta daga gidan mijinta kuma aljannar duniyarta zuwa ƙangin bauta wato gidan mahaifinta. Amma sai ta ji Kabir yana faɗar kamalan da take jin tamkar bai ba ta matsayin da ta ba shi a cikin zuciyarta ba. Don haka a ɗan ƙufule ta ce. "Shi kenan tun da kai abin da ka ɗauka kenan sai ka lissafa abin da nake bin ka, tun da ai da na ba ka cewa na yi na ba ka aro." Murmushi ya yi don ya fahimci ta ji haushi, sai ya gyara zama ya ce. "Tuba na ke uwargida kuma amarya a gidan Kb babban tela. Haba Fauzin Kb fushin na mene ne?" Fauziya ta ɗan kwaɓe murya a shagwaɓe ta ce, "To ai kai ne da wata irin magana." Hira suka yi ɓarke da ita har gari ya ƙaraaa wayewa, gabanin Kabir zai fita ta ce masa za ta je gida ta gaida mahaifinsa. Amma sai ta fara biyawa ta wurin Inna ta gaida. Fita ya yi ya sayo mata ɗan omo, sabulu da magi ƙulli bibbiyu. Ƙulli ɗaya ya ce ta miƙa wa mahaifiyarsa, ƙulli ɗaya kuma ta kai wa mahaifinta. Godiya ta zuba masa sosai, ta sake ba wa Kabir wani matsayi a zuciyarta. Domin kusan duk ranar fa za ta je gaida mahaifinta sai ya sayo wani abim ya ce ta kai masa, har turare sayo mata yake ya ce ta kai masa. Kyautatawar da yake wa mahaifinta ya sa Kabir ya sake samun fada a zuciyarta da zuciyar mahaifinta har ma da matan babanta. Don ba ta taɓa zuwa gida haka, idan ya saya wa mahaifinta abu. Ita kuma da ɗan canjin hannunta na kuɗin kitso ko gyaran tsumma da take yi sai da saya wa matan babanta ɗan magi ko tsintsiya. Wani lokacin kuma ƙannenta take sayawa alewa ta tafi musu da shi, haka idan za ta leƙa gidan mahaifiyarsa Inna ko bai ba ta komai ba da kuɗinta take ɗan saya mata omo da ɗan abin da ba a rasa ba. Shirya su Na'ima ta yi tsaf cikin ankon atamfa dogayen riguna, sannan ita ma ta shirya cikin doguwar rigar abaya ta ɗora babban mayafi ta yane kanta. Lokacin da za ta fita Lawisa kawai ta yi wa sallama, saboda magana bai daɗi ba ta taɓa haɗa ta da su A'ilo. Koda ita ta yi musu mai daɗi, sai sun san yadda suka yi suka mayar mata da martanin baƙar magana. Duk wanda ya ga Fauziya da 'yan'matanta uku sai sun birge shi, saboda kusan gabaɗaya tazararsu babu yawa. Daga gidan su Fauziya zuwa gidan Inna babu nisa sosai, don a adaidaita sahu bai fi naira ɗari ba. Idan mutun bai sa ƙyuya ba ma zai iya zuwa da ƙafa. A lokacin da Fauziya ta yi sallama a gidan Inna Sadiya tana tsakar gida tana wanki, Inna kuma tana zaune tana ɗaurin tsintsiya. Sadiya ce ta faɗaɗa fara'arta ta ce, "Yanzu uwar biyu ba ki rufe fita ba sai kin haife mana ɗa a titi?" Murmushi Fauziya ta yi mata, ta ƙarasa gaban ta tsugunna ta ce. "Barka da hutawa Inna." Inna ta ɗan taɓe baki ta ce, "Wane hutu Fauziya ana fama da rayuwa." Fauziya ta sake yin murmushi saboda idan da sabo ta saba da halin Inna domin irin matan nan ne da ba su da godiyar Allah. Saboda bakin ƙoƙari 'ya'yanta suna kyautata mata, amma duk lokacin da suka haɗu sai ta yi jajen tana cikin wani hali. A cikin yaran Inna mijin Sadiya da Kabir ne marasa ƙarfi sosai, don haka ta fi ji da matan 'yan uwan Kabir. Kuma a haka ma tana nannan da Fauziya saboda kyautatawa da take yi mata, amma Sadiya da yaranta da suke zaune a gida ɗaya kullum cikin tsangwama da kyara suke. Su Na'ima suka zube ƙasa suka gaida Inna, Inna ta ɗan taɓe baki ta ce. "Ai dama ku ba na ganinku sai idan uwarku za ta zo, ko ban isa a turo mini ku ba ne oho." Sadiya da Fauziya suka haɗa ido suka saki murmushi, Inna ta sake leƙen hannun Fauziya ta ga ba ta ga komai ba sai kuwa ta sake cewa. "Kabirun ma kusan sati guda kenan ban gan shi ba, tun ranar da ya kawo mini garin tuwo da taliya. To dai nan ɗin da ba kwa son zuwa, nan ne dai gidanku tun da ubanku ma a nan ya tashi. Kuma ni na haifi Kabiru babu yadda kuka isa ku yi da ni." Shiru su Na'ima suka yi, saboda dama babban dalilim da ya sa ba sa son zuwa wurin Inna yawan faɗanta. Sau tari Fauziya za ta shirya su musamman ranar Juma'a ta cw su zo su gaida Inna amma suna zuwa ko zaman minti talatain ba sa yi suke tafiya. Wani lokacin ne ma suke zama su yi wasa da yaran Sadiya. "Ke Salim ku zo ku ɗauki tsintsiyoyin nan, ke kuma Zainabu ga mafitai ki ɗauka. Yau idan kika sake ki yar munnda kuɗi wallahi sai ubanki ya biya ni kuɗina." Inna ta furta wa 'ya'yan Sadiya tana tura musu farantan da aka jera tsintsiya da mahutan. Sadiya ko kaɗan ba ta jin daɗin tallan da Inna take ɗora mu, don dai babu yadda za ta yi ne amma ba ta son tallar musamman ga Zainab da ta kasance 'ya mace. "Inna ga wannan a yi wanki da shi babu yawa." Fauziya ta zaro ledar daga kan cinyarta. Ina sai da ta ɗora wa su Salim farantin tsintsiya sannan ta waiga wurin Fauziya riƙe da baki ta ce, "Oh ke dai Fauziya ba kya gajiya, to an gode madalla. Ai kuwa kin ce na sha wanki, dama kayan sawata duka sun ƙare sai masu datti. Ai ka ga masu abin kirki, amma wasu kuya ko ƙullin gishiri ba su san su ba ni ba. Ke dai Allah Ya yi miki albarka, wannan ciki da kike ɗauke da shi Allah ya sauke ki lafiya ya sa ki haifo wa Kabiru magaji." Fauziya ba ta amsa ba, suna nan zaune suka ɗan taɓa hira. Fauziya tana son su keɓe da Sadiya amma tana tsoron fassarar da Inna za ta yi musu. Sun ɗan jima suna hira Inna ta ce, "To yanzu ni dai ragowar Taliya ɗaya gare ni ballantana na dafa mana abinci, ko da wuri za ku wuce ne Fauziya." Girgiza kai Fauziya ta yi tana mamakin rayuwar Inna, Fauziya ta miƙe ta ce. "Yanzu za mu wuce Inna, dana zan je gaida Baba ne na ce bari na zo na gaishe ki." Nan take kuwa Inna ta hau washe baki ta ce, "To shi kenan ku gaida gida, shi kuma Kabiru ki ce masa ina son ganinsa." Fauziya ta amsa sannan ta nufi hanyar fita, da sauri Sadiya ta bi ta tana faɗin. "Wai har za ku tafi, bari mu fita tare dama zan miƙa wa Mariya kayan wankin da na yi mata." Da biyu Sadiya ta bi Fauziya suka fita, suna fita Fauziya ta ce. "Wai dama har yanzu su Salim ba su daina tallar muhucin nan ba?" Sadiya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce, "Ai na kusa barin gidan nan Fauziya, wallahi na gaji haƙurina ya kusa ƙarewa." "Idan kin tafi yaran kuma fa Sadiya?" Cikin halin ko'inkula ta ce, "Allah zai raya su, wasu ma suna tasowa babu iyayen kuma su yi rayuwa kamar kowa." Fauziya ta tsaya tana bin Sadiya da kallo, duk ta lalace saboda rashin kwanciyar hankali. "Don Allah ki daina wannan maganar, addu'a za ki cigaba da yi har Allah Ya hore muku ku bar wa Inna gidanta. Kin san zama wuri ɗaya dama yana kawo haka, ki cigaba da addu'a sai ki ga watarana sai labari." "Hmmm ba za ki gane ba Fauziya, ni na san takaici da baƙincikin da nake ci a gidan." Cikin ƙarfafa gwiwa Fauziya ta ce, "Babu abim da ya fi ƙarfin addu'a." Fauziya da Sadiya sun jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama, Fauziya ta wuce ta tari adaidaita sahu suka wuce gidan mahaifinta.A tsakar gida ta samu mahaifinta yana ta bambamin faɗa a kan 'yan nefa sun zo karɓar kuɗin wuta. Har ƙasa ta tsugunna ta gaida shi, sannan ta miƙa masa saƙonsa, nan take Baba ya shiga washe baki yana saka mata albarka. Ɗakin Inna Sakina ta shiga da yake a nan ɗakin aka raini Fauziya, bayan sun gaisa ta fara bin ƙannenta da alawoyi tana danƙa musu. Su Nai'ima kuwa dana tun a tsakar gida suka fara wasa da ƙannen mahaifiyarsu. Kabir yana fita daga gida kai tsaye wurin masu sayar da ƙofa ya nufa, ƙofofin ba ƙaramin tsada ya ji sun yi masa ba. Ya cika da ragowar kuɗin wurinsa ya sayi guda ƙofofin guda uku, ƙofar farko ta ƙofar gida. Sai ɗakin da yake a tsakar gida, da kuma ƙofar falon gidan. Daga nan wurin can gidan nasa ya nufa, ya kira masu saka ƙofofi suka fara aiki. Ba su suka gama ba sai yamma liƙi, gabanin zai fito daga gidan kiran Hafsa ya shigo masa, zama ya yi a bakim dandamalin rijiyar sannan ya ɗauka. "Gimbiyar mata!" Ya furta cike da kashe murya, daga can ɓangaren Hafsa ta ce. "An ya kana jin abin da nake ji kuwa?" Kabir ya sake kwantar da murya ya ce, "Haba Hafsyna, don Allah ki daina faɗin haka." Hafsa ta ce, "Ka duba whatsapp ɗinka na turo maka da hotuna." Jikin Kabir har rawa yake ya katse wayar, sannan ya yi saurin buɗe datarsa. Yana shiga whatsapp ya fara cin karo da saƙonninta, buɗe hotunan ya yi ya ga ta ɗauko masa hoton ƙirjinta da ƙasanta kamar yadda ya buƙata. Cikin wani irin yanayi ya sake kiranta, a kunyace Hafsa ta ɗauka sai ta ji duk muryarsa ta sauya. "Baby kin yi kyau sosai, amma don Allah ki yo mini bidiyo mana." Hafsa da duk ta ji nauyinsa ua kama ta ta ce, "Baby gaskiya ka yi haƙuri, wallahi wannan ma da ƙyar na iya turo maka." "Guda ɗai-ɗai fa kawai za ki yi mini, kuma kin san ai aurenki zan yi ko ba ki yarda ba?" Shiru ya ji Hafsa ta yi, ya ɗora da cewa. "Akwai kuɗin da nake saka ran za su shigo mini nan da kwana uku. In Shaa Allah a satin naa za a kawo kuɗin aurenmu." Daɗi ya lulluɓe Hafsa, jikin yana rawa ta ce. "Zan turo maka amma don Allah kana gani ka goge." Cikin sauri Kabir ya ce, "Wallahi ina gani zan goge." Kashe wayar Hafsa ta yi ta shige ɗakinta ta yi masa bidiyo ta tura masa. Kabir yana ganin bidiyon a ruɗe ya shiga yi mata replay da kalaman batsa, tun tana jin nauyinsa har ta fara biye shi. Yamma liƙis Fauziya ta koma gida ta ɗora musu girki, a wannan karom ma ana yin magrina ta kira Kabir ta sake tuna masa maganar da suka yi game da alƙawarin da ya ɗaukar mata ba zai sake shan komai ba. Sannan ya ce ta yi tsala masa kwalliyar domin a cike yake da kewarta. Zuciyar Fauziya fes ta tsala wanka cikin wata doguwar riga marar nauyu, ta raba gashinta gida biyu kamar wata 'yar baby ba ƙaramin kyau ta yi ba. Suna nan zaune ita da yara kimanin ƙarfe tara suka ji sallamarsa. Kusan lokaci ɗaya ita da yaran suka rungume shi har ita suna faɗin. "Abi oyoyo." Rungume su ya yi gabaɗaya, sai Fauziya ta saci kallon yadda suke nishaɗi ita da yaran saboda dawowarsa da wuri kuma a cikin nutsuwarsa, sai ta ji ƙwalla tana shirin zubo mata. Ɗaya bayan ɗaya ya tsugunna yana sumbatar yaran a goshi, sai ya ɗago ya dube ta suka haɗa ido. Rungumo ta ya yi jikinsa yana kashe mata ido ɗaya, irin kallon da take bin sa da shi ya sa shi hura mata iska a fuska. "Wannan kwalliyar zan biya tukwicinta an jima." Ya furta matana hankali, ta sakar masa murmushi ta ce. "Na fa tsufa da yawa." Kafaɗa ya maƙale mata cikin kwaikwayon muryarta ya ce, "Ni ban yarda ba." Duk da yaran ba su fahimci me suka tattaunawa ba, jin yadda mahaifinsu ya maƙale murya ya sa suka fata ɗariya. Hula, agogo da wayarsa ya ajiye a gefen gado ya ɗauki bokiti ua zuba ruwa ya tayi yin wanka. Kabir ya manya shaf da abin da Hafsa ta turo masa bai goge ba har ya iya ajiye wayarsa, kuma ya bar hotunan ne saboda udan ya keɓe ya dinga kalla yana jindaɗi. Fatima ce ta ɗauki wayar ta shi, da yake wani lokacin idan yana gida ya kan kunna musu game ko cartoon su kalla. Shige-shige suka fara yi masa har suka shiga cikin gallery ɗinsa, Na'ima tana ta zura kanta ta danna ɗaya daga cikin bidiyon da Hafsa ta tura masa. Fauziya da ke tsugunne tana jera masa kayan abin ci ta ji muryar mace raɗau a kunnenta tana faɗin. "Baby kana gani, wannan bidiyon..." A giguice Fauziya ta fisge wayar daga hannunsu jikinta yana karkarwa, sakamakon ji irin bayanin batsar da buduwar take yi. Domin a bidiyon hafsa tana yi masa tana bayanin komai dalla-dalla. "Lah Mami mene ne wannan?" Na'ima da ta fi su wayo ta tambaya, sai da Fauziya ta saita nutsuwarta ta ce, "Bidiyin wata marar lafiya ne da take neman taimako, za a haɗa mata kuɗi a yi mata magani. Na sha faɗa muku idan mutum ya ajiye abu sai an tambaye shi ake taɓawa ko?" Gabaɗaya suka gyaɗa mata kai, Fauziya fa take jin wani abu yana taso mata a ƙirji ta yi ƙarfin halin faɗin. "To daga yau, ko da wasa ka da na sake na ƙara ganin ku taɓa wa mutum wayarsa. Idan ba haka ba ranku zai ɓaci." Su Fatima suka amsa mata. Ear pices ta ɗauko ta saka a kunne, ta shiga bidiyan ta kunna shi. Jikinta ya ɗauki karkarwa gabanta yana wani irin bugu da ƙarfi, lokaci ɗaya hawaye ya wanke fuskarta domin bidiyon ya matuƙar ƙazanta. Da sauri ta shiga whatsapp ɗinsa, ta ga yawanci masu saƙon duk maza ne don haka take mamaki a inda Kabir ya samu wannan bidiyom. Har za ta fita ta ga an saka costomer Hafsa lace bubu, tana shiga ta karo da emojin heart ta turowa Kabir. Can sama ta haura ta fara cin karo da saƴonnin batsar da suka tattauna, a nan ta gado wannan bidiyon na Hafsa ne tun da ga muryar ta nan ta kunna voice ɗinta ta ji." Jikinta yana rawa ta kifa wayar, sai ta jingina da bango tana jim wata irin tsanar Kabir ta mamaye ta. Ummou Aslam Bint Adam +2347062062624 [11/02, 19:29] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA SHIDA Tun tana zubar da hawayen zuci don kada yaranta da ke zaune su fahimci halin da take ciki har ta gagara sarrafa zuciyarta saboda wani irin zafi da ɗacin da take yi mata. Hawaye taka sosai tana shassheka tamkar za ta shiɗe, saboda wani irin kakkarwa da jikinta yake yi ƙirjinta ya shiga bugawa da sauri-sauri. Ganin halin da mahaifiyarsu take ciki ya sa suka ƙarasa wurinta suna tambayarsu, ba ta iya tanka musu ba sai ma wani irin kallo da ta dinga bin su da shi kamar ta ga sababbin hallita. A ranta ta ayyana ƙila yarinyar da suke musayar munanan kalamai da Kabir ko kaɗan iyayenta ba su san abin da take aikatawa ba. Sai kawai ta rungumo su jikinta ta sake fashewa da wani irin kuka mai cin zuciya, ganin haka ya sa su Fatima su ma suka rairai kukan su ma. Duk da ya san ba hali ko ɗabi'ar Fauziya ba ne binciken wayarsa, haka kawai yana wanka da ya tuna ya bar wayar a kan gado ya ji gabansa ya faɗi. Nan take ya yi sauri ya kwakkwara ruwa ya fito, don ba ya so Fauziya ta fahimci irin alaƙar da ke tsakaninsa da su Hafsee. Kamar wanda aka kifa haka Kabir ya faɗa cikin ɗakin har yana tuntume, Fauziya ta ɗago tana kallonsa ta ƙura masa ido. Ganin yanayin da ya same ta ita da yaran da kuma mummunan kallon da take wurga masa, ya sa ƙirjinsa ya buga da wani irin ƙarfi. Da gudu yaran suka tafi wurinsa cikin haɗin baki suka ce, "Abi Mami ce take kuka." Yanayin yadda ya ga hankalin yaran ya tashi ya sa ya kalli wurin da ya ajiye wayarsa, rashin ganinta a wurin ya sa shi tabbatar da tabbas mai afkuwa ta riga da ta afku. Ya san duk irin saɓanin da za sh samu da Fauziya ba ta iya zubar da hawayenta a gaban yaran, duk abin da za su yi ko wata tattaunawa ce sai ta bari sun tafi makaranta ko kuma idan sun yi bacci amma gudun kada ya bada kai bori ya hau sai ya yi kamar bai san dalilin ɓacin ranta ba ya ce. "Ummu banat lafiya kike hawaye a gaban yara?" Tamabayar da ya wurga mata ta ji ta yi tamkar ya zuba mata ruwan dalma, ta dube shi cike da mamakin wai ita Kabir zai raina wa hankali. Murmushin takaici ta saki sannan ta miƙa masa wayar ta ce, "Ungo wayarka, cikina ne yake ciwo." Ya san ta faɗi haka ne saboda gudun yaran su fahimci shi ya yi mata wani abin, Na'ima ta ɗauko kwalmar maganin tarinsu ta miƙa mata ta ce. "Ammi riƙe ki sha magani ba na son na ga kika kuka!" Ƙuri ta yi wa yarinyar tana kallo, murya a dashe ta ce. "Wannan maganin yara ne Na'ima, cikin nawa ya sarara idan na tashi zan ɗauko maganina a cikin jaka." "Amma za ki daina kuka?" Na'ima ta sake wurga mata tambaya, gyaɗa mata kai Fauziya ta yi. Dai kuma ta ƙarasa gaban Kabir ta ce, "Abu ni dai ka kai Ammi asibiti, ba na son ta dinga kuka ni ma zan yi." Ta ƙarasa maganar tana janyo hannunsa. Tamkar wanda aka liƙewa ƙafa da super glue, haka ya ji ƙafarsa ta manne ta ƙasa wata irin shakkar Fauziya ta kama shi. "Ko... ko... za mu... wuce asibiti..." Ya furta bakinsa yana rawa, sai dai tun bai fire kalamansa ba Fauziya ta wurga masa mugun kallon fa ya sa shi haɗiye kalamansa. "Ai jikin mamanku da sauƙi Na'ima, ba sai mun je asibiti ba. Yanzu dai bari na yi muku shinfiɗa kun ga gobe kuna da school." Tana gee har lokacin idonta yana kan Kabir, da take yi masa

Chapter 17 of 35