Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da wata damuwar ne? Turon lambar asusunki sai na turo miki dubu ashirin ko kati ki saka." Da sauri Maimuna ta ce, "Dubu ashirin fa?" Jafar ya yi murmushi ganin kamar tarkonsa ya kama ta ya ce, "My moon, na rantse da Allah, zan iya ɓatar da ko nawa ne a kan samun farincikinki. Idan ba za su ishe ki ba, ki faɗa mini sai na ƙara miki." Bugun ƙofar da Maimuna ta ji ana yi mata ya sa ta ce, "Ana buga ƙofa, zan turo maka account number." Daga haka ta katse, tana zuwa gate da ta buɗe ta ga Maman Nana ta shigo da alama ranta a ɓace yake. Kabir yana idar da sallar magriba, bai tsayana ko ina ba sai ƙofar gidansu Sury. Waya ya zaro ya kira ta, tana ɗauka ya ji muryarta a can ƙasa taha faɗin. "Mu gaɗu a bayan layinmu ta ɓangaren hannunka na dama, idan ka zagaya ka same ni a bakin layin ƙarshe." Kabir yana jin haka ya amsa mata sannan ya katse wayar, kwatancan da ta yi masa ya bi. Yana zuwa ya daidai wurin ya shiga waige-waige, daga bayansa ya ji ta ce. "Bai gane matarsa ba." Da sauri ya waigo, cikin mamaki yake bin sa da kallo. "Wai baby ke ce?" Sury ta saki murmushi ta ce, "To ya za a yi, ai idah hagu ra ƙi sai a koma dama. Ƙarya na yi zan je dubiya, shi ya sa na ɓoye niƙab ina zuwa bayan layi na saka. Yanzu dai mu yi sauri kada a ga na daɗe." Kabir ya kanne mata ido ɗaya ya ce, "To shi kenan amaryar Kb, amma daga jiya zuwa yau na yi kewarki." Bakin titi suka ƙarasa ya tsayar musu adaidaita sahu, shi kansa ya ji daɗin yadda Surayya ta ɓatar da kamanni. Domin har a cikin ransa yaja fargabar wani ya gan shi, kuma a yanzu kowayw ya gansu yana iya ce masa ƙanwarsa ce. Tafiyar kusan minti ashirin suka yi, da yake sabuwar unguwa ce gidajen tsilli-tsilli haka suke. Tun daga farkon layin Kabir ya ce mata. "Ki jira a nan zan je na buɗe ƙofa na shiga, bayaj wani lokaci zan taɓo ki a waya sai ki biyo bayana. Kin san mutane da munafinci, ba za a rasa 'yan tsurku ba. Kina miƙe layin nan da zan bi idan kika yi kwana gida na farko za ki ga ba fulasta ƙofarsa ta langa-langa ce." Sury ta amsa masa shi kuma ya yi gaba. Lokacin da Kabir ya shiga layin gidan babu kowa a waje, don haka jikinsa har rawa yake ya latsa lambar Surayya ya ce mata ta ƙaraso. Yana nan tsaye ta ƙarasa ciki, kunna fitilar wayarta ta yi saboda duhu ta shiga haske cikin gidan. Ciki da falo ne guda ɗaya, sai fallan ɗaki da banɗaki a ciki. A gefe banɗaki ne da kitchen sai ɗan ƙaramin tsakar gida. Kusan an gama komai, sai daɓe, fulasta, fenti, ƙofafi da winduna su suka yi saura. Farinciki ya sa Sury ta rungume shi tsam, tana faɗin. "Gaskiya gida ya yi masoyina, amma kana ganin wannan ƙarashen zai iya kai wata nawa baba gama ba?" Tun da ta rungume shi ya ji duk yanayin jikinsa ya canza, jikinsa a mace ya shiga yawo da hannunsa a jiki sa. Da wata irin murya ya ce, "Kin san samun namu lokaci-lokaci ne, amma dai ina fatan har aurenmy ba zai haure shekara ba." Ganin saƙon da take aika masa ya fara tasiri a jikinsa ya sa Sury ta cigaba shi ma yana mayar mata da martani. Dogon hijabin jikinta ya zame mata, dama Surayya kafin ta fito sai da ta faki idon mahaifiyarta ta zuro dogon wando da ƙaramar riga a ciki sannan ta zura zumbulelen hijabinta har ƙasa. Duk zuwan da Kabir yake yi wurin Sury wani abu bai taɓa shiga tsakaninsu ba, bayan rungume-rungume da shafe-shafen da suke yi wa juna. Don haka da ya ji Sury za ta zo ganin gidansa ya ci alwashin saninta a wannan ranar, yana tsaka da yawo da hannunta ya ci karo da abin da bai yi tsammani ba. "Mene ne wannan?" Kabir ya faɗa ransa a ɗan ɓace. "Gabannin magriba period ɗina ya zo!" Ta furta masa, don dama ta ƙi faɗa masa ne saboda kada ya fasa kawo ta. Domin ta san matuƙar suka zo gidan ta san sai ya nemi koda taɓa wannan ɓangaren ne. Cikin wata irin murya ya raɗa mata a kunne, "Yanzu ya za ki yi da ni?" Murmushi ta sakar masa ta ce, "Dabarun mu na mata mana, ko ba ka san idan macen aure tana wannan halin akwai dabarin da take yi ba." Ya sani sarai, domin Fauziya duk a halin da take ciki tana ƙoƙarin faranta masa. Amma shi sam ba haka ya so ba, ita ma Sury ta fahimci haka amma ta basar. Babu kunya Surayya ta shiga sarrafa shi, tamkar yadda macen aure take yi wa mijinta. Suna cikin wannan yanayin kiran Fauziya ya shigo cikin wayarsa, kamar ba zai ɗauka ba tuna matsalar da aka samu a daren jiya da ta je shagonsu aka ce ya fita da wuri ya sa ya ɗauka don ya ji abin da ya faru. "Hello!" Daga can ɓangaren Fauziya ta ce, "Abi barka da yamma!" Ya ɗan yi gyaran murya don ka da ta fahimci sauyinsa ya ce, "Barka dai Ummu Banat, ya jikin?" Ta amsa masa tana wurga masa tambaya. "Amma ba ka shago ko? Na ji ban ji ƙarar ɗinki ba?" Duk da ya san zai yi wuya Fauziya ta gane a inda yake, amma sai da ya ji gabansa ya faɗi. Ya janye jikinsa daga jikin Surayya yana faɗin, "Na'am eh na je karɓo wa oga kayan ɗinki ne, ina zuwa an zo kaina." Daga haka ya katse, tun da ya fara waya Surayya take wurga masa harara tana shirin yin magana ya ce. "Ayi mini afuwa." Juyar da kai gefe ta yi cikin fushi, ya shiga lallashinta sannan Surayya ta cigaba da sarrafa shi. Sai da suka ɗauki lokaci a haka sannan Kabir ya samu nutsuwa, da yake gidan akwai rijiya sai kawai ya ja ruwa da gugura ya yi wanka da ita sannan suka fito daga gida. A yi haƙuri da error ban yi editing ba🫠 Ummou Aslam Bint Adam🌚 +2347062062624 [09/02, 20:22] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA HUƊU Fauziya tana gama waya da Kabir ta tashi da sauri ta faɗa banɗaki ta sheƙa wanka, bayan ta fito ta ciro wata doguwar riga ta saka. Jikin rigar roba ce, ba ta da tsayi har ƙasa. Daga iya gwiwarta ta tsaya, ta ɗauko kum ta fara gyara gashinta. Fauziya irin dogayen matan nan ne, sai dai tana da ɗan kauri. Tana da ƙira sosai sai dai ba fara bace tas, tana dai da haske da kuma yalwar gashi. Faka gashinta ta yi jelar ta sauka har gadon bayanta, ta ɗebi turarruka masu ɗaɗin ƙamshi ta feshe jikinta da su. A gaban mudubi ta tsaya tana ƙarewa kanta kallo, su Na'ima sai zagaye ta suke yi suna cewa ta yi kyau. Ita kanta ta san ta yi kyau, don haka take ta ɗokin Kabir ya dawo ya ga kwalliyarta. Dafa tsohon cikin jikinta ta yi ta saki murmushi, domin ta san Kabir mutum ne mai san ƙananan kaya. Jin kiran sallar Isha'i ya sa ta saka zumbulelen hijabinta har ƙasa, ta tasa su Na'ima suka gudanar da sallar Isha'i. Bayan sun idar sai da ta yi wa yaran tilawar Alƙur'ani, sannan ta zuba musu abinci suka ci. Da suka gama suka ɗan yi wasa sannan ta yi musu shimfiɗa a tsakar ɗaki, don ta ci alwashin duk zafi ta daina fitar da su waje. Kabir da Sury tare suka tafi har unguwar su Surayya. Ita ta sauka ta wuce gida, shi kuma ya wuce shagonsu. A lokacin da ya koma Ogansu ba ya nan, don haka shi ma bai zauna ba ya fice daga shagon. A madadin ya wuce gida yana fitowa sai kiran abokinsa Abbati ya shigo masa. "Ya Abbati kana iya?" Kabir ya furta bayan ya ɗauki wayar, daga can ɓangaren cikin muryar maye Abbati ya ce, "Ga mu a majalisa, kai fa muke jira kwana biyu nan ba ma gane maka sai wani eh yane kake yi wa mutane." "Don Allah mijina ka daina wannan shaye-shayen, a yanzu matsayinka na uba ne. Idan za ka yi sara, ka dinga lura da bakin gatari kana wasa shi. A yanzu da muke rayuwa, kamata ya yi ka duƙufa a neman ciyar da mu halali ba shaye-shaye ba. Allah Ya yi mana arzikin 'ya'ya mata, ina gudun kada watarana idan suka girma a dinga goranta musu. Ka yi mini alƙawarin ba za ka sake shan komai ba Kbna." Kabir ya tuna kalaman da Fauziya ta yi masa, bayan ya dawo hayyacinsa a ranar da ya faɗa ɗakin A'ilo yana cikin maye. Murya a can ƙasa ya ce. "Ku sha kawai Abbati, Fauziya ba ta san shaye-shayen da nake yi." "Ɗan abin rage zafin shi ne za ka ce Fauziya ba ta so? Kai yanzu kana namiji mace ce za ta zauna tana yi maka ƙabali da ba'adi? Haba bros kada ka bayar da maza mana, don Allah ka taho muna jiranka." Daga haka Abbati ya kashe, har zuciya ta ce masa ya yi tafiyarsa gida, sai kuma wata ta ce ya je ya sha ko kaɗan ce. Saboda shi kansa kwana biyun da ya yi bai sha ba, har jin sa yake yi wani iri. Don haka daga nan bakin ƙofar shagon ɗinkinsu ya wuce bayan wata makarantar firamare, wacce iren-irensa suka laɓewa a lungunta suke shaye-shaye. Kabir yana zama T-boy ya miƙa masa wata 'yar roba haɗe da da wata baƙar leda, nan take Kabir ya fara shaƙa yana ɗaɗɗakar ruwan robar kafin wani lokaci tuni ya yi wa kansa caji. Jin shiru har ƙarfe goma da rabi Kabir bai shigo ya sa Fauziya ta ɗauki wayarta ta latsa lambarsa. Sai dai wayar ta ƙari ringing har ta katse bai ɗauka ba, haka kawai ta ji gabanta ya faɗi. Zuciya ta shiga raya mata ko dai Kabir yana wurin shaye-shayen da ta hana shi, girgiza kanta ta yi cike da ƙwarin gwiwa ta ce. "In Shaa Allah a wannan karon ba zai sake ba..." Maganarta ce ta katse sakamakon jin mummunan bugun ƙofar da ake yi, wanda ya gigitata saboda tsoro, firgici da tashin hankali. "Fauziyataaaaaa! Fauzeeeee, zooo ga ni na zo." Kalaman Kabir cikin maye suka doka sallama cikin dodon kunnenta, ba yau ta saba jin haka daga gare shi ba. Amma a wannan ranar sai ta ji wani irin ɗaci, ɓacin rai da baƙinciki ya mamaye ta. Ta kalli su Na'ima da ke kwance a ƙasa, haka kawai ta ji tausayinsu a ya kamata. Hawaye ne bibbiyu suka fara zuba daga kwarmin idonta, tana nan zaune ta sake jin ya buga ƙofar da ƙarfi yana cewa. "Don Allah... kar ki min faɗa... ni babu abin da na shaaaa..." Sanin halin mutanen gidansu ya sa ta yunƙura da ƙyar ta fita, inuwa ta gani a bakin ƙofar Maman Sabir da alama a tsaye take tana leƙen ganin abin da zai faru. "Ni fa... ba na shan... komai, Fauziyaaaaaa ko kin sha kin bugu ne... kika yi bacci... ki zo ki buɗeeee." Ta sake jin muryarsa a daidai lokacin da ta tura ƙofar gidan, tana buɗewa ya faɗo jikinta da yake ya saki jikinsa a kan ƙofar. Hannu ta saka ta kare cikinta, tana shaƙar ƙamshinsa ta ji yana wani irin warin hayaƙi. "Fauzinaaaa." Ya furta yana shafa fuskarta, takaici ne ya gama maƙure ta. Ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta dube shi tana jin kamar ta rufe shi da duka, a wannan ranar ji ta yi da ace su kaɗai ne a gidan tana buɗe masa za ta bar shi a wurin. Idan ya ga dama ya shiga ko ya kwana a nan, amma gudun kada ya shiga ɗakin matan aure ya sa ta kamo shi. Suna tafe yana layi tana dafa bango, tana shiga tsakar gida ta hangi A'ilo da Maman Sabir suna magana ƙasa-ƙasa. Duk da ba ta ji me suka faɗa ba, amma jikinta ya ba ta maganarta da Kabir suke yi. Ta girgiza kanta cike da tausayin irin rayuwar da take ciki, sannan suka shiga ɗaki. Suna ganin Fauziya ta shiga ɗaki suka saki shewa haɗe da tafi A'ilo ta ce. "Ke dai Maman Sabir a kullum maraɗinki ba ya kunya, wato yau kuma da haka kika shigo. Sabon salo kiran salla da usur, ai gara haka da ki faɗa ɗakin da ba na ki ba." Maman Sabir da tuni ta fahimci zancan ta ce, "Ke kuwa ai dukan da kuka yi mini ban ji da daɗi ba. Abin dariyar ma, baban Sabir tunkur yake zama bai yi bacci ba yana jirana." Sai kuwa suka sake kwashewa da dariya. Lawisa da take ɗaki take jin su kamar ba za ta tamka musu ba, sai kuma ta yi zaraf ta leƙo ya ce. "Sai ki yi takatsantsan kuwa, domin babu ruwan Ubangiji. Ba abin mamaki ba ne ki ga Sabir ya gado ki. Ni ina fata da roƙon Ubangiji, tun da har fatan da kike yi wa kanki kenan Ubangiji Ya sa Sabir ya gaji abin da kike yi wa izigili." Tana faɗar haka ta koma ɗaki. "Wallahi sai dai ki gani a kanki, aniyarki ta biki mai mugun baki." Maman Sabir ta furta cike da tsoro. Fauziya suna shiga ɗaki, bayan ta saka shi ya tsallake su Na'ima da ke kwance sai kuwa ta sake shi rai a ɓaci. Daga gefen gadon ya faɗi, kansa ya bugu da katakon gado. Cikin azaba ya runtse ido yana shafa wurin, takaici ya sa Fauziya ta zauna a gefen gadon sai kawai ta fashe da kuka. Sai da Maimuna ta tura ƙofar ta rufe sannan ta waigo tana bin bayan Maman Nana da harara, ganin za ta waigo ya sa ta saki fuska cikin wayancewa ta ce. "Uwar gida kuma amarya a gidan Baban Nana, ke kaɗai ki sha kurumki daga ke babu ƙari." Maman Nana ta saki guntun tsaki ta zauna a kan kujera, sai kuma Maimuna ta sha jinin jikinta duk da Jafar ya tabbatar mata da ba ta gane da wacce yake wayar ba. Amma sai ta ce, "Uwar Nana ko dai kin samo wa Abdul abokin wasa ne? Na gan ki duk a sanyaye." Maman Nana ta zaunar da Abdul da bai wuce shekara ɗaya ba ta ce, "Ni da wannan ne ai da sauƙi, sai na saka shi ya ɗauko mini mai aiki ta dinga komai kamar lokacin da na yi cikinsa." Cikin bugar ciki Maimuna ta ce, "To! Me yake damunki?" "Wallahi ban tabbatar namiji munafiki maci amana ba ne ba sai yau, wai har ni Abban Nana zai munfurta?" A razane Maimuna ta dube ta, tana shirin yin magana ta cigaba. "Wai har ni zai dinga yin waya da budurwa a ɗaki? Tsabar wulaƙanci ya saka ni aiki, ina can ina haƙilo ko yaro ya ƙi riƙe mini ashe soyayya zai sha. Wallahi ta ci sa'a ban same ta a waya ba, da sai na ƙare wa kaf danginta zagin rashin mutumci. Sai da na raini mijina yanzu kuma 'yan'iskan mata za su fara kawo mini hari, wallahi duk yarinyar da ta yi gangancin auren mijina sai na lahantata." Ras! Ƙirjin Maimuna ya buga, don ta san halin Maman Nana akwai ta da baƙin kishi. Amma duk baƙin kishinta ba ta ji ko ɗar ɗin za ta iya rabuwa da Jafar ba. Dalilin haka ya sa ta dafa ta ta ce. "Gaskiya ni Abban Nana ma ya ba ni mamaki, saboda Allah duka shekararku nawa da zai dinga wani kule-kulen 'yan'mata?" Maman Nana ta wara hannu tana taɓe baki alamun kema dai taya ni gani, don Maminuna ta sake zuga ta sai ta ce. "To ai ko ni me shekara goma da aure Nazir ba shi da budurwa, ina laifin ma ya bari ku shekara ko sha biyar ne kin ga lokacin ke da yaranki kun samu jindadin da kuka samu bakin gwargwado. Amma kina zaman zamanki a kwaso miki gayyar tsiya, gara dai tun wuri ki san abin yi." Ai kuwa nan take Maman Nana ta sake cika, rai a ɓace ta ce. "Ai wallahi bari ya dawo, dama ai na faɗa masa sai ya kira mini budurwar idan ba haka ba zai ga ɓacin raina." Wani irin farinciki ya mamaye zuciyar Maimuna, saboda a yanzu babu abin da yake damunta sama da ta ji Maman Nana ta ce suna cikin daɗi ita da Jafar. Ta sake taɓe baki ta ce, "To ni ban da ma abin namiji, mace har mace kamar ki me zai yi da wata kuma. Dirin nan bakin gwargwado kina da shi, gashin nan kina da na zaman falo. Ke dai a fuska ba za ce miki mummuna ba, to don Allah me namiji yake so da ba ki da shi." Maman Nana ta yi caraf ta ce, "Jaraba fa irin ta namiji, ki duba ki ga irin magungunan da ke ɗurawa cikina Maman Dija, ke kanki shaida ce saboda Abban Nana na fara shafe-shafen man bilicin, tun da na lura yana leƙe-leƙen fararen 'yanmata." 'Ba dai leƙe ba, sai da faɗawa. Jafar ai ya yi nisan kiwo a kan alkyabbar mata.' Maimuna ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce. "A toh ga shi kina ƙoƙari a turaka ma na ji kin ce ba kya sanya, to wai da ba kin ce har zauce miki yake ba?" Maman Nana ta yi ƙwafa ta ce, "Yaushe rabo? Ni yanzu rabona ma da shi ai mun kusa sati, Abban Nana da yake da jaraba wai shi ne har yake sha mini ƙamshi jiya. Ƙiri-ƙiri mutumin nan ya ce mini ba shi da lafiya..." "Sati fa Maman Nana? Ke kuwa kina me? A gaskiya ki dawo nutsuwarki, ni fa ba don kar na faɗa ki ji haushi ba da na ce wani abu." A zabure Maman Nana ta dafa Maimuna ta ce, "Faɗi mana, ni da ke ai kin san ba ma haka." "Astagafirullah ba wai zargi nake ba, sai na ga ko dai budurwar tashi ce ta ɗauke masa hankali? Kin san fa 'yan'matan yanzu wallahi idonsu a buɗe yake, ba abin da ba sa yi wa sauraye ke kina can yashe a baki suna harkarsu." "Bantan uba! Ai kuwa sai yanzu kika kamo mini bakin zaren." Maman Nana ta furta jikinta yana karkarwa, sannan ta cigaba. "Ai kuwa zan saka ido a kansa, wallahi idan na gano wani abu a tsakaninsu sai an maimaita yaƙin dunuya na biyu." Maimuna ta cigaba da zuga ta, sai ta gama yi mata famfo sannan ta yi mata sallama ta tafi. Tana fita Maimuna ta saki shewa, cike da ƙeta ta ce. "Sakarya wawiya marar lissafi, in dai ni ce wallahi baƙinciki yanzu kika fara ƙunsa. Sai na raba ki da jin daɗin, da kike hura wa 'yan unguwa hanci kina faɗar ke mowar miji ce." Ummou Aslam Bint Adam +2347062062624 [11/02, 14:13] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA BIYAR Maman Nana ta fita babu jimawa yaran Maimuna suka dawo daga makaranta, hankalinta yana kan wayarta saboda so take Jafar yaa turo mata kuɗin ta goge alert ɗin. Sai da su Asiya suka ci abinci suka wuce Islamiya sannan Maimuna ta sake lalubar wayarta. Kamar ya san wayar tana hannunta nan take ta ga alert na dubu ashirin, wani irin tsalle ta buga tana riƙe baki. Jikinta har rawa yake ta shiga ɗaki ta ɗauko ƙaramar wayarta ta saka batirin ta kunnata, a gaggauce ta shiga kiransa sai dai bai ɗauka ba don dama ta san ba lallai ya ɗauka ba sai dai ya kira ta. "Baby yanzu na ga kulin ya shigo." Maimuna ta furta muryarta har rawa take yi, jin sautin murmushin da yake yi har cikin zuciyarta ta yi. Ta ya ce, "Yanzu saboda dubu ashirin kika kira? Haba my Moon, don Allah kada ki sake yi mini haka." Maimuna ta saki murmushi, tana shirin magana ta ji ya shagwaɓe murya ya ce. "Ni fa na gagar haƙuri gaskiya, na biya ta kasuwar waya na saya miki sabuwar babbar waya wacce za mu dinga ganin hotuna da bidiyon juna." Maimuna ta ji daɗi sosai, amma tana tsoron kada asirinta ya tonu Nazir ya gano ta. "To ya za a yi ta zo hannuna? Kuma ni ina jin tsoron kada Nazir..." "Idan muna magana ba na son ki dinga ce mini kina tsoron Naziru, wai wanne irin zama yake yi da ke da kike mugun jin tsoronsa." Jafar katse ta cikin sauri, shiru Maimuna ta yi sai ya cigaba da cewa. "A gaskiya alamu sun nuna ba kya jin daɗin zama da shi, a haka ka gan shi kamat na gari yana sunkuyar da kai ƙasa. Amma ya zo a jiye kyakkyawar mace, yana azabtar da ita." Sai kuma Jafar ya ɗan kwantar da murya ya ce. "Haba my Moon, ki duba irin kulle da takunkumin da yake yi miki? Wai a haka kika iya zama da shi har tsawon shekara goma? A gaskiya an ci amanar kyau wallahi." Jin maganganun Jafar sai suka soso mata mikin da yake ɗamfare cikin zuciyarta, kalamasa suka yamutsa zuciyarta tana jin ɗacin yaudarar da Naziri ya yi mata a shakarun baya. "Hmmm ai Nazir ya dasa mini mikin da zai jima a zuciyata bai goge ba, lokaci kawai nake jira my baby." "Kada ki jira lokaci Moon, kamata ya yi lokaci ya jira ki. Saboda yara uku rak ba za su hana ki rawar gaban hantsi ba. Wai ma kina kallon kanki a mudubi kuwa?" Tambayar da Jafar ya yi mata ya sa Maimuna ta yi saurin matsawa gaban mudubinta tana ƙarewa kanta kallo. "Ni fa tun ranar da na fara ganinki na san Allah Ya zuba halitta, kuma wallahi duk wanda ya ganki ba zai cw kin taɓa haihuwa ba. Ba kamar waccan kasaran da ta yi shaɓar da jiki ba, dubi ƙirjinta ba kyan gani duk ya saki ya tamushe kamar an tsoma leda a ruwa." Dariya Maimuna ta shiga ƙyaƙyatawa har da riƙe ciki, sai da ta yi mai isarta ta ce. "An ya ba faɗa kake ba Baby, ka san fa babu laifi ƙawar tawa tana mayar da hankali wurin gyara." Jafar Ya saki tsaki ya ce, "Hmm ke dai a yi sha'ani kawai, yanzu dai wayarki zan ba

Chapter 16 of 35