"An gode Yaya, Allah Ya ƙara girma da jinkiri mai amfani." Baba Malam ya yi murmushi ya ce.
"Amin Ya Rabbi."
Hajiya Karima tashi ta yi ta nufi ɗakin da aka ba ta, ɗakin akwai banɗaki da katuwar katifa a ciki. Ruƙayya kuma da ƙannenta Baba Malam ya ce su shiga cikin yaran gida su cigaba da mu'amalarsu. Da yake Baba Malam tsayayyan mutum ne, duka matansa biyun da yaransu kansu a haɗe yake. Hakan ne ya sa ko kaɗan Mommy ba ta fuskanci wani abu marar daɗi a gidan ba.
Kamar yadda ya yi mata alƙawari, a ranar ya je ta taho da Haidar. Fuskarsa ta ɗan kumbura, saboda ya ce sun ɗan daddake shi. Sai da ya yi wanka da ruwan ɗumi sannan Baba malam ya kira family Doctor ɗinsu ya duba shi ya ba shi magani.
Haka suka cigaba da rayuwa a gidan tun su Mommy suna ɗari-ɗari, har suka saki jikinsu ake komai da su. Sannu a hankali kwanaki suka dinga gangarawa har lokacin bikin Ruƙayya ya matso. Duk wata ɗawainiyar kayan abincin biki, gara da kayan ɗaki Baba Malam ne ya yi mata. Kuma da yake amaryarsa tana sana'ar gyaran jiki ita ta dinga yi wa Ruƙayya gyaran amare. Sai dai babban abin da yake damun Ruƙayya da Mommy, rashin bibiyarsu da Daddy bai yi ba duk tsawon kwananin da kusa kwashe. Lokacin da uwargidan Baba malam ta fahimci damuwarsu, zama ta yi da Mommy a ɗaki ta taushe ta.
"Maman Mami, tabbas duk macen da take cikin irin yanayin da kike ciki dole za ta ji babu daɗi. Ace mijin da kake tare da shi sama da shekara ashirin, rana tsaka ya juya maka baya a kan wata ƙanƙanuwar yarinya. Amma abin da nake son ki sani komai ya yi zafi maganinsa Allah, idan Alhaji ya fahimci damuwarki zai ga kamar ba ya kyautata muku yadda ya dace. Don Allah ki cire komai a ranki Karima, ba na son ranar taron yarinyar nan da ya kasance miki ranar farinciki na tsinci damuwa a fuskarki. Kin ga ita kanta yarinyar idan tana ganin yanayinki ba za ta sake ba. In Shaa Allahu za a cigaba da roƙon Allah, idan ma wani abin ta yi masa ƙadarinta zai karye ki koma ɗakinki."
Mama tana gama faɗa Mommy ta saki murmushin takaici ta ce.
"Yaya duk maganganunki haka ne, kuma In Shaa Allahu zan kiyaye. Sai dai ba na jin zan sake zaman aure da abban su Mami."
Shiru Mama ta yi ta ce, "Babu mai tilasta ki Karima, Allah Ya zaɓa mafi alheri. Mommy ta amsa da Amin.
Ruƙayya ba wani event ta yi mai yawa ba, saboda dama can ba ta cika hayaniya ba. Henna day ta yi, sai kamu. Kuma duka a cikin harabar gidan Baba Malam aka yi decoration, aka kawo masu kiɗan ƙwarya suka sha biki. Ranar ɗaurin aure tun asuba Mommy da mutanen gidan suka shiga hidimar girke-girken abincin 'yan ɗaurin aure. Kallo ɗaya za ka yi wa Mommy ka fahimci tana cikin farinciki, danginta gabaɗaya a nan gidan suka sauka saboda ta sanar da su a gidan Baba Malam za a yi bikin. Sai dai babu wanda ta sanarwa da dalilin yin haka sai 'yan uwanta da suke ciki ɗaya, saboda kunyar faɗa take ji.
A masallacin jikin gidan Baba malam da ke hotoro, yan'uwa da abokan arzikin da ya gayyata duka suka taru. Haka dangin saurayin Ruƙayya da abokansa suka yo zuga, mafi yawa sanye suke cikin fararen kaya. Baba malam da waliyin saurayin Ruƙayya ne a zaune har sun fara gabatar da ɗaurin aure, kamar wanda aka jefo daga sama haka Daddy ya faɗo cikin masallacin rai a ɓace ya ce.
"Ban lamunce kowanne mutum ya ɗaura mini auren 'ya ba. Idan ba haka ba kuwa wallahi kowaye hukuma ce za ta raba mu."
PROMO🔥🥳
PROMO🔥🥳
PROMO 🔥🥳
Mun kawo muku garaɓasa ne domin taya ku murnar bikin sallah💃🏻🥳 kowanne littafi mun zabge muku farashinsa.
Shu'umar Masarauta 1&2 600
Baƙar Daula 300
Zaujatu Jinnul-Ashiq 300
An ya baiwa ce 200
Dubu Jikar Mai Carbi 200
Uwani 'YarƘashin Gwiwa 400
Gidan Likitoci cmplt 400
Naushin Wuta cmpt 400
Za ku tura ta wannan asusun na ƙasa.
Aisha Adam
3090957579
Firstbank
Sai shaidar biya ta wannan lambar.
07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA SHA BIYU
KU ZO KU SAYI MUSULMAN KAYANMU💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Assalamu Alaikum
Ina manyan mata yan gayu masu ji da kwalisa ...
Ina masoyan jakankuna da mayafai da kuma sarƙoƙi?
Ummee's Collection ta tanadar muku su kala kala acikin farashi mai sauki, lallai ku hanzarta kada a barku a baya.
Domin mallakar naku sai ku tuntube mu anan
What'sapp or call :- 08082350419
***
Ilahirin mutanen da ke cikin masallacin waigowa suka yi, suna kallon Daddy da babu ɗigon rahama a fuskarsa. Baba malam ji ya yi kamar ya tsaga ƙasa ya shige ciki saboda tsabar kunya, wani ƙanin mahaifin saurayin Ruƙayya ya dubi Baba Malam ya ce.
"Alhaji lafiya? Me yake faruwa ne?" Daddy ya yi farat ce.
"Ni mahaifinta ya kamata ku tambaya ba shi ba."
Girgiza kai Baba Malam ya yi, ya dubi wasu securites ɗinsa ya yi musu magana, sai da ya matsa kusa da su ta yadda mutanen gefe ba za su ji ba ya ce.
"Ku fita da shi, a kai shi ɗakin saukar baƙina."
Babu ɓata lokaci suka tasa ƙeyar Daddy da ke masifa yana zage-zage. Baba malam ya dubi mutanen da ke zaune ya ce.
"Don Allah ku yi haƙuri da ɓata lokacin da aka yi muku, wannan bawan Allahn da kuke gani ƙanina ne kuma mahaifin yarinyar nan. Sai dai kuma a kwanakin baya ne ya samu matsalar ƙwaƙwalwa. Ina mai sake ba ku haƙuri a karo na biyu." Cike da tausayawa mutanen cikin masallacin suka fara cewa.
"Subhanallah, Allah Ya ba shi lafiya ai kuwa ga shi nan biri ya yi kama da mutum."
Daga haka aka cigaba da ɗaurin aure, haka Baba malam da ragowar 'yan uwansa suka fara gaisawa ana ta yi musu Allah sanya alheri.
Mommy tana cikin gida da 'yan biki, labari ya isar musu a kan abin da Daddy ya yi. Saboda takaici Mommy har da kukanta, sai da ta ji an ɗaura aure sannan hankalinta ya kwanta.
Baba malam Allah-Allah ya dinga yi ya sallami mutane ya shiga cikin gida, kai tsaye ɗakin saukar baƙinsa ya shiga. Yana shiga 'yan'uwansa suka rufa masa baya, Baba Sani cikin damuwa ya ce.
"Yaya don Allah ka yi haƙuri, kada wannan abin da ya faru ya sa ka saka shi a ranka ga shekaru sun ja."
Girgiza kai Baba malam ya yi ya ce.
"Kada ka damu Sani, yanzu haka Umaru yana cikin nan. Zan yi magana da shi, na ji mene ne matsalarsa." Yana gama faɗa ya saka mukulli ya buɗe ƙofar ya shiga, a zaune ya samu Daddy fuskarsa ta yi murtuk saboda ɓacin rai. Daddy yana ganinsa ya taso da sauri ya ce.
"Yanzu abin da ka yi yaya ka kyauta mini kenan..."
Bai rufe baki da Baba Malam ya ɗauke fuskarsa da mari, ya saka hannu ya sake taro fuskarsa da mari a karo na biyu. Can baya Daddy ya matsa yana bin Baba malam da kallo, cikin zafin zuciya ya zauna a kujera yana bin sa da mugun kallo.
"Zo nan Umaru."
Baba malam ya furta fuska a haɗe, babu musu Daddy ya zauna a ƙasa yana cin magani. Baba malam ya dubi ƙannensa da ke tsaitsaye ya ce duk su zauna, zama suka yi kowanne jiki a sanyaye sannan ya fara cewa.
"Umaru me kake so ko kuma na ce me kake nufi game da mamana?"
Shiru Daddy ya yi bai tanka ba, Baba malam ya cigaba da cewa.
"Ban san shaiɗanin da yake kanka ba, amma ina mai tabbatar maka da duk wani abin da yake kanka sai na sauke maka shi. Ba ka da hankali da kake son biye wa mace don ka tozarta kanka, kuma ku wukaƙanta 'yarka da zuri'armu a idon duniya?"
"Amma ai ba tun yau ba na ce na fasa auren."
Cewar Daddy, Baba malam ya ce.
"Saboda me?"
Daddy cike da rashin jin nauyi ya ce, "Saboda cin mutumcin da ta yi wa Shukura ita da uwarta." Takaici ne ya rufe su gabaɗaya jin abin da ya faɗa. Baba malam ya ce.
"Amma ka san wulaƙanci da cin zarfi ne ka ɗauki takardar saki ka ba wa Shukura ta kai wa Karima? Ko ka binciki abin da ta yi bayan ta kai mata takardar? Umaru wallahi ka tafka babban kuskuren da za ka yi nadamarsa nan ba da jimawa ba. Ka sani, wallahi har ka mutu ba za ka samu mace kamar Karimatu ba. Kuma aure ne na riga da na ɗaurawa mamana, idan ka ga dama ka kai ƙara ta har majalisar ɗinkin duniya. A shirye nake na fuskanci shari'a da kai." Motsa baki Daddy yake ƙasa-ƙasa yana ƙunƙuni kamar mai zagi ko magana, 'yan'uwansa da ke wurin su ma mamakinsa suke yi. Kamar zai tanka, sai kuma kawai ya miƙe ya fice daga ɗakin, har Baba Alasan zai yi masa magana Baba malam ya dakatar da shi. Sun jima suna tattaunawa sannan suka tsayar da matsayar sake miƙewa tsaye, domin su nemawa ɗan'uwansu magani a kan baƙon halin da yake ciki.
Bayan sun gama tattaunawa da kansa ya sa aka kira Mommy har ɗaki, ya faɗa mata kalaman kwantar da hankali. Ya kuma ba ta haƙuri a kan abin da ya faru, sannan Mommy ta kwantar da hankalinta aka cigaba da hidimar biki. Yamma liƙis motar 'yan kai amarya suka yi fakin a ƙofar gidan Baba Malam, saboda ganin wannan farinciki Mommy har da kukanta a lokacin da za a tafi da Mami. Lokacin da suka rungume juna suna kuka cikin shasssheka Mami ta ce.
"Mommy yanzu haka zan tafi ban yi sallama da Daddy ba? Mommy duk yadda Daddy ya ci alwashin kai ni ɗakin mijina Shukura ta rusa mana." Mommy ta share hawaye, ta riƙe ta tsam a jikinta ta ce.
"Kada wannan ya rusa farincikinki Ruƙayya, mahaifinku yana buƙatar addu'a, domin hatta 'yan'uwansa ba su tsira daga sababbin halayen da ya tsinci kansa a ciki ba." Jinjina kai ta yi sannan suka yi sallama, yaya Mommy da Mama uwar gidan Baba malam ne suka riƙe ta har aka shigar da ita mota sannan suka tafi.
Gidan Mami ya yi kyau sosai, haka mutane suka dinga yabawa. Ana jinjina yadda aka narka dukiya mai yawa a ciki, tun daga kan kayan kicin har zuwa kayan alatun more rayuwa.
Tun ranar da Daddy ya bar gidan Baba Malam, bai sake waiwayowa ko ya kira shi a waya ba. Haka su ma suka duƙufa dai yin addu'a suna kai kuɗin sadaka masallatai, da makarantun islamiyyu da wuraren malamai a kan Allah ya warware matsalolin da suke tattare da Daddy. Cikin hukuncin Ubangiji watarana da daddare Daddy yana kwance, sai ji ya yi kamar an kwara masa ruwan ƙanƙara a kansa. Zumbur ya tashi zaune yana salati, Shukura da ke kwance ta ce. "Baby lafiya?"
Cikin damuwa ya dafe kansa ya ce.
"Wani mummunan mafarki na yi a kan Karima da yaran nan, wallahi na gansu a cikin mummunan yanayi."
Gaban Shukura ne ya faɗi, amma sai ta dake ta ce.
"To yanzu mene ne mahaɗinka da su da har za ka ɗaga wa kanka hankali." Da mamaki ya dubi Shukura ya ce.
"Matar tawa kike faɗa mini haka a kanta da 'ya'yana, kin san me kike faɗa kuwa Shukura?"
A wannan karon tsoron Shukura a fili ya bayyana, ta yi ƙarfin halin cewa.
"Wace matar taka? Hajiya da ka daɗe da rabuwa ita, ai yanzu idan idda ce ma ta jima da gamawa yau wata nawa." A haukace ya dube ta ya ce.
"Kin san me kike faɗa kuwa? Hajiya Kariman na saka?"
"Ƙwarai kuwa, sai dai idan kai ne ba ka cikin hayyacinka, ko ka manta kai da bakinka ka ce mini ita da yaranta suna gidan Baba malam." Shukura ta yi maganar cikin gadara. Zumur ya miƙe ya zura doguwar rigarsa, sai kuma ya ɗauko wayar ya duba agogo ƙarfe biyu da rabi na dare. Lambar Baba malam ya lalubo ya latsa, har ta gama shiga ta yanke ba a ɗauka ba. A gaggauce ya sake kira, sai a wannan karon ya ji an ɗauka. Hankali a tashe ya ce.
"Baba malam don Allah su Karima suna gidanka?"
Cikin muryar bacci Baba malam ya ce, "Eh suna nan ya aka yi?" Ƙit Daddy ya kashe wayar, ya ɗauko mukullin motarsa da ke kan mudubi da sauri Shukura ta sha gabansa ta ce.
"Wai ina za ka je da tsohon daren nan?"
"Zan je na ɗauko iyalina." Daddy ya ba ta amsa.
"Kutumar...! Saboda waccan tsohuwar kilakin za ka fita a tsohon daren nan? Ko ka manta yanzu babu aurenka a kanta? To ko kuma zaman dandi za ku fara..."
Tass! Daddy ya wanke fuskarta da mari, cikin ɓacin rai ya ce.
"Idan kika sake cewa matata tsohuwar kilaki wallahi sai ranki ya yi mummunan ɓaci." Daga haka Daddy ya fice, ya nufi harabar gidan ya ɗauki mota ya fita.
Hankali a tashe Shukura ta ɗauko waya ta latsa lambar Inna ta kira, daga can ɓangaren ta ji muryar mahaifiyarta cikin bacci ta ɗauka. Kuka da fashe da shi, hankali a tashe Inna ta ce.
"Ke Shukura lafiya, ko jikin ne? Ina Alhajin yake?"
"Inna aikin nan fa ina zargin ya karye."
Shukura ta furta cikin kuka, Inna da ba ta fahimci komai ba ta ce.
"Aikin me kuma?"
"Asirin da muka yi wa Baby da Hajiya Karima mana, yanzu haka ya fice wai zai tafi dawo da ita gidan nan. Da na yi magana fa har da marina." Shukura ta ƙarasa maganar cikin kuka, nan take Inna ta wartsake ta ce.
"Shukura an ya ba mafarki kika yi ba? Kin tabbatar da gaske ne?"
"Wallahi ba mafarki ba ne Inna."
"Ai kuwa mun shiga uku, wallahi zama bai ganmu ba. Bari zuwa safiya zan zo gidan." Inna ta faɗa cikin kwantar wa da Shukura hankali.
A wannan lokacin haka ta zauna jigum, ta shiga tunanin nemawar kanta mafita. Don ba ƙaramin tashi hankalinta ya yi ba.
ALHAJI UMAR
Daddy gudu yake yi tun iya ƙarfinsa kamar zai tashi sama, duk hanyar da ya bi idan jami'an tsaro suka tsayar da shi sai dai ya ce musu emergancy ne ya fito da shi ɗansa babu lafiya. Da an duba boot ɗinsa da cikin motar idan aka ga babu komai, sai a bar shi ya wuce.
Yana zuwa ƙofar gidan Baba malam ya fara horn da ƙarfi, securities ne suka leƙo suka gan shi. Sai dai saboda tsaro ya sa ba su buɗe masa ba, ɗaya daga ciki ya nufi cikin gida yana ɗan bubbuga ƙofar. Da yake tun tashin Baba Malam da Daddy ya yi idonsa biyu, sai ya fito ya tambayi masu gadin. Yana jin an ce masa Daddy ne ya ce a buɗe masa gidan ya shiga, kamar wanda yake jira ana buɗewa Daddy ƙofa ya kunno hancin motarsa cikin gidan. Ko ƙarasa fakin bai yi ba ya fito ya nufi hanyar shiga cikin gidan, a bakin baranda ya samu Baba Malam a tsaye. Cikin tashin hankali ya ce.
"Sannu da dare Baba malam, dama zuwa na yi na tafi da Karima."
"Wace ce Karima?"
Baba malam ya wurga masa tambaya fuska a haɗe.
GIDAN HAFIZ
Kamar yadda suka tsara Hafiz yana tashi daga kasuwa gidansu Bilkisu ya ƙarasa, mahaifinta dattijon arziki ne. Tarba mai kyau ya sa aka shirya musu kamar yadda ya saba duk shekara, sai da suka ci suka sha suka yi ƙat wurin sallar Isha'i sannan ya ɗauko Bilkisu suka taho gida.
A lokacin da suka ƙarasa Amina tana zaune da su Sayyada a ɗakinta, yaran suna ta wasansu a junansu amma kallo ɗaya za ka yi wa Amina ka fahimci tana cikin damuwa. Saboda ɓacin rai ko da aka sha ruwa ba ta iya cin abincin kirki ba, ruwa kawai ta sha sai baƙin shayi. Tana zaune ta ji sallamarsu Hafiz, dariyar Bilkisu ta ji tana faɗin.
"Haba kai kuwa Baby, ai dole kowaye ya ji daɗin abin da ka yi wa su Baba, Allah dai ya bar ƙauna a tsakaninmu."
Zuciyar Hafiz ɗaya ya amsa da Amin, saboda shi ya yi tsammanin zuwansa shan ruwa gidan take nufi. Yaran suna jin muryar iyayensu suka fito a kuje suna yi musu oyoyo, rungume su Hafiz da Bilkisu suka yi. Sannan Hafiz ya ce.
"Ina Auntynku ko tana cikin ɗaki."
Sayyid ya gyaɗa kai ya ce.
"Amma Aunty ba ta ci abinci ba, ruwa kawai ta sha." Da sauri Hafiz ya ce.
"Kul, wa ya tambaye ka? Ba na son faɗar abin da ba a tambaye ka ba, koda wasa kada na sake ji."
Daga haka ya ɗaga labulen ɗakin Amina ya shiga. Ita kuma Bilkisu ta ja hannun yaranta suka wuce ɗaki.
"Maman baby barka da hutawa." Hafiz ya faɗa yana zama a gefenta, haɗe da ɗora hanunsa a kan cikinta. Ɗauke kanta gefe ta yi ta ce.
"Barka."
"Ko wani abu ne yake damunki?" Ya sake tambayarta.
Girgiza masa kai ta yi, sai ya saki murmushi ya ce.
"To a kawo mini abinci Gimbiya, kin san cewa na yi ba zan cika cikina ba sai na dawo gida na ci naki."
"Ka kuwa yi wa kanka, don ni ban yi girki da ku ba. Tun da ka je gidan neman suna ai sai ka ci a can, sai dai kuma idan na sahur za ka jira."
Amina ta yi maganar cikin fushi, da mamaki yake kallonta ya ce.
"Ni kike faɗa wa haka Amina? Laifi ne don mahaifin Bilkisu ya gayyace ni shan ruwa? Kada ki manta koda ba Bilkisu nake aure ba, yana iya gayyatata tun da mahaifinta abokin mahaifina ne."
"Ni wani abin na ce maka? Ko ka ji na yi maganar alaƙarka da ta mahaifinsu? Tun da dama ai da manufa a zuwan naka, wallahi duk abin da mutum yake yi Allah yana kallo."
Amina ta ƙarasa maganar tana hawaye. Ransa ne ya fara ɓaci, amma ba ya san abin da zai kai ga ya biye mata don haka ya kwantar da murya ya ce.
"Wai me ya sa kike yin haka Amina, ba fa yau mahaifin Bilkisu ya saba gayyatarmu ba. Don Allah kada wannan ya ɗaga miki hankali." A sheƙe Amina ta dube shi cike da takaici ta ce.
"Wallahi bari ka ji Hafiz, Allah ɗaya za ka ce mini na yarda. Amma wallahi duk abin da kake faɗa sai dai na kalle ka, wai ni za ku yi wa bariki. Ai ita da yake matar so ce, kuma ana mutumta iyayenta ana daraja su ga shi nan ka narka iyayen kuɗi ka yi sayayya ka ba ta; ta kai gidansu. Ni kuwa da ke ba ka ɗauki iyayena da mutumci ba ko biyar ba ka ba ni ba, ai maganina kenan da na tambaye ka. Amma wallahi ka yi da 'yar halak, In Shaa Allahu tsinke na daina tambayarka." Tana gama faɗa ta fashe da kuka tana shigewa ɗaki.
Da mamaki ya bi bayanta da kallo, shi kaɗai ya shiga nazari don gabaɗaya bai gane abin da take nufi ba. Jin kukanta yake har cikin ransa, har ya yi biris da ita sai ya ji ba zai daure ba, don haka ya shiga cikin ɗakin. Janyo ta ya yi jikinta ya ji zafi zau, cikin damuwa ya ce.
"Haba Amina, ya ina yabonki sallah za ki kasa alwala. Don Allah me ya sa kike son ɗaga mini hankali muna zaune lafiya ni da ke." Amina ta goge hawayen idonta ta ce.
"Dole ka ce zan ɗaga maka hankali mana Hafiz saboda ba ka ƙaunata, ai dama ba za ka ga rashin adalcin da kake yi ba. Dubi uban buhun kayan da ka turo wa Bilkisu ɗazu, ka ce ta kai gidansu na shan ruwa wai har da ɗan sahu ka turo a kai ta. Ni kuwa idan zan mutu da ciwo, idan za ni asibiti haka zan tafi na tari adaidaiata sahu a hanya." Tana gama faɗa ta ƙara rushewa da kuka. Shiru ya yi yana nazari, da sauri ya miƙe tsaye har zai fita ya dawo ya ce.
"Ni aka ce na aiko da buhun kayan shan ruwa?"
"Zan yi maka sharri ne? Wai Hafiz ni za ka mayar 'yar iska da ban san me nake yi ba?" Amina ta furta cikin fushi, jinjina kai ya yi ya ce.
"Ta so mu je ina son yin magana da ku." Kamar Amina ba za ta miƙe ba, sai ta yunƙura ta tashi da ƙyar.
Kai tsaye ɗakin Amina suka shiga, a lokacin ta gama yi wa yara shimfiɗa a ɗakinsu ta koma ɗakinta. Tana ganinsu a cikin ranta ta ce, 'Ai na san za a rina wai an saci zanen mahaukaciya.'
Amma a fili sai ta ce. "Abban Sayyid kune?"
"Mune Bilkisu, zo ki zauna."
Zama Bilkisu ta yi, Amina da fuskarta ta kumbura suntum saboda kuka ita ma ta zauna tana wurga musu mugun kallo. Hafiz ya dubi Amina ya ce, "Maimaita abin da kika faɗa mini." Tiryan-tiryan Amina ta sake faɗar abin da ta faɗa masa, ya ɗago ya dubi Bilkisu ya ce.
"Bikisu ni da ke mun yi magana, a kan na aiko miki da kayan shan ruwa?"
Bilkisu ta yamutsa fuska ta ce, "To dama ni na ce kai ka aiko ne, ke Amina hawainiyarki ta kiyayi rama ta. Sharri za ki yi mini ko haɗa ni faɗa za ki yi da mijina?" Kafin Amina ta yi magana Hafiz ya ce.
"Ya isa haka."
Waya ya zaro ya latsa lambar mahaifin Bilkisu, cikin girmamawa suka gaisa ya yi masa ban gajiya. Hafiz ya numfasa ya ce.
"Baba don Allah wata tambaya gare ni, amma ba wani abu ba ne." Baba ya ce. "Yi tambayarka Hafizu."
"Baba don Allah yau Amina ta kawo maka kayan shan ruwa ne?"
Hafiz ya tambaya yana kallon yanayin Bilkisu da ta yi zuru-zuru. Baba ya ce.
"Eh ta kawo mini kaya masu yawa, ta ce mini yayansu ne ya ba su kuɗi da kaya shi ne ta sayo ta kawo mini. Amma wani abu ne ya faru Hafizu?" Cikin girmamwa Hafiz ya ce, "A'a Baba, wata tattaunawa muke yi da ita ne. Na gode sosai Allah Yaa ƙara girma." Baba ya amsa sannan suka yi sallama. Da mamaki Hafiz da Amina suka dubi Bilkisu da ta yi tsumu, kamar an tsoma kaza a ruwa. Cikin gori Amina ta ce.
"Amma dai wallahi kin ji kunya, girma ya faɗi raƙumi ya shanye ruwan 'yan tsaki. An girma dai ba a san an girma ba..."
"Ya isa haka." Hafiz ya katse ta, sannan ta kira lambar Aunty Nana
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 35