Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
idan mace ta so ninke ka a baibai wallahi ba za ka taɓa ganewa ba. Kai tsanani fa ba shi ne ba, ka yi ƙoƙari iya iyawarka a kan kula da iyalinka. Kada ka saki gidanka sakaka, kuma kada ka tsananta. Sauran sai ka bar wa Allah, shi zai tsare maka su." Ya ƙarasa maganar yana miƙewa, sai sauran ma suka miƙe. Nazir ya kaɗe rigarsa ya ce. "Ai wallahi wannan zance ne, kai dai kawai kowa ya ji da gidansa. Amma ka saki mace take walwalawa ai ka riga da ka daɓa wa kanka wuƙa, musamman ma ace ka bar ta tana aiki ko sana'a kuɗi yana juya mata. To kuwa sai abin da ka gani, don matan auren yanzu wallahi mafi yawa sun gama lalacewa." "A'a gaskiya Alhaji Nazir, waɗannan zantukanma bai kamata mu dinga danganta su da iyalanmu ba, Allah Ya nesanta mana su da dukkan wani abin ƙi." Adam ya furta, sannan suka yi wa junansu sallama. Gida Nazir ya nufa sai kuma tunanin Maimuna ya faɗo masa, don haƙurinsa yana gab da ƙarewa. Tun da ta yi watsi da shi, a duk lokacin da ya neme ta sai kawo masa wani uzurin. Maimuna tana kwance ta ji motsin shigowar Nazir, da sauri ta ɗauki wayar ta ɓoye ta koma ta kwanta. Haka kawai ya ji kamar ba bacci take yi ba, don haka ya zauna agefenta yana bubbuga hannunta. "Maimuna! Maimuna." A yatsine ta tashi tana faɗin, "Ya aka yi?" Mamaita kalaman ya yi yana jin ɓacin rai, ya ɗan haɗe fuska ya ce. "Ki tashi mu yi magana." "Ni bacci nake yi sai da safe ma yi maganar." A ɗan tsawace ya ce, "Ki tashi na ce, yanzu nake son mu yi maganar." A hankali ta tashi yana sakin guntun tsaki. "Me ya sa kike ƙaurace mini, me ya sa duka kika canza kin raina niMaimu kada ki bari ki kai ni bango." Murmushi ta saki cikin halin ko inkula ta ce, "Wane kalar ɓacin ranka ne bn sani ba Nazir? Ai sai dai ka faɗa wa wata macen idan ka sake aure." Idanunsa suka kaɗa jawur saboda ɓacin rai, ya matso kusa da ita ya damƙi hannunta yana faɗin. "Uban waye yake zuga ki da yake hure miki kunne har kika raina ni?" Ido cikin ido ta kalle shi ta ce, "Sai ka fara sanar da ni wanda ya zuga ka har ka tauye ni, ka kuma dakushe burikana saboda zalinci ka ƙuntata mini ta hanyar tsauwalawa. Sannan ni kuma na sanar da kai wanda ya zuga ni." Shiru ya yi yana kallonta kamar a ranar ya taɓa ganinta, cikin rashin damuwa ta ce. "Idan kuma ba ka da abin magana sai na yi kwanciyata." "Ni kike faɗa wa haka Maimuna." Nazir ya tambaye ta a zafafe, sai kuwa ta mayar masa da martani cikin sauri kamar tana jira. "Na faɗa maka Nazir, na fa jima ina tara ka a zuciyata. Wlalahi-wallahi daraja ɗaya kake ci a wurin, wato mahaifina. Da ace mahaifina ba ya raye, wallahi da na jima da datse alaƙar auratayyata da kai." Tas! Ta ji ya sauke mata mari a fuska, zuciyarsa tana suya ya nuna ta da yatse. "Duk rashin mutumcin da kike tunƙaho da shi, wallahi daidai nake na sauke miki su. Kin san wane ne ni sarai, ba zan ɗauki wannan iskancin ba." Maimuna ta dafe kumatu tana bin sa da kallon tsana, har zai fita ta ce. "Allah Ya isa ban yafe maka ba, kuma wallahi indai ni ce ba zan taɓa komawa yadda nake a baya ba." Nazir bai kula ta ba ya fita, kai tsaye cikin store ɗin ta ya shiga. Ya ɗauko wani ƙaramin mukulli ya rufe shi, sannan ya ɗauke ƙaramar wayar Maimuna da ke falo ya koma ɗakin. Duk abin da yake yi tana jin sa, don ba sabon abu ba ne idan sun yi faɗa ya rife store ɗinta na kayan abinci. Sai dai kullum idan zai fita ya ɗebo mata wanda za ta dafa. Fulo ta ga ya ɗauka ya tafi falo, ta taɓe baki tana nuna ko a jikinta. Don ta sake ɓa ta masa rai sai ta furta. "Ko a jikina, wai an tsikari kakkaura." Ta gyara kwanciyarta, tana ayyana irin abin da za ta yi wa Nazir don ta huce takaicin marin da ya yi mata. GIDAN INNA Tun bayan fitar Sadiya gidan Inna ya kacame da iface-ifacen kukan yaranta, Inna ban da kyara da hantararsu ba abin da take yi. Fauziya ce ta janyo su ta rarrashe su, da ƙyar Zainabu ta ta yi shiru. Zazzaɓi ne ya rufe Fauziya, saboda duk cikin matan 'yan'uwan Kabiru Sadiya ce ta hannun damanta, suna ba wa junansu shawara musamman da ya kasance Sadiya ba ta da kowa a garin. Sai su rufe su binne ba tare da wani ya ji labari ba, domin dama Kabir da Yaya Nura sune masu ƙaramin ƙarfi. Gudun raini ne ya sa su Fauziya suka kama kansu, don haka ma ya sa matan su Yaya Tasi'u ko gidansu ba sa zuwa. Abincin kari Fauziya ta haɗa gabaɗaya har yaran Sadiya, bayan ta gama ta zuba wa yaran. Suka fara ci, sai dai ta lura har lokacin sun gagara sakin jikinsu. Kabir kafin ya tafi sai da ya kira Mai adaidaita sahu ya fita da keken ɗinkin Fauziya, kai tsaye shagonsu ya wuce da shi. Ya yi sa'a Ogansu yana nan, yana ganinsa ya washe baki ya ce. "Allah Ya taimaki Oga" Oga ya faɗaɗa fara'arsa ya ce, "Kb namu." Janyo keken ɗinki ya fara yi har ya samu ya shigar da shi cikin shagon, sai ya ce, "Oga ya ka ga keken? Ay na faɗa maka sabo ne bai ji jiki ba." Tasowa ya yi daga mazauninsa ya sake leƙa keken ya ce, "Gaskiya ne kuma na ga butterfly ne. A ajiye shi a gefe, zan sa a yi masa service sai ku cigaba da amfani da shi." Kabir ya matsar da keken ciki, sai kuma ya saki murmushi ya ce. "To Oga cittar fa?" "Idan za ka tafi an jima ka yi mini magana, zan ba ka rabin, rabin kuɗin kuma sai zuwa nan da rana ita uku." Ba haka Kabir ya so ba, ya so ace duka kuɗin ya samu. Amma duk da haka ya san idan ya karɓi kuɗin, za su cika a haɗa a kai gidansu Surayya. Tun daga wannan ranar zaman Fauziya da Inna ya fara ɗaukan sabon salo, sai dai Fauziya tana bakin ƙoƙarinta don ganin wani abu bai haɗo su ba. Duk safiya idan ta yi abinci tana bakin ƙoƙarinta, don ta ga ta ba wa su Zainabu abinci ko yaya ne duk da ciyarwarsu ta koma hannun Inna kacokam. Kwana biyu da tafiyar Sadiya, har gida Yaya Tas'u ya zo ya ƙarewa Yaya Nura faɗa a kan sakin da ya yi wa Sadiya. Don wani lokacin idan suka yi faɗa tana zuwa ta kai ƙararsa wurinsa, shi kuma sai ya je ya yi masa faɗa. Idan aka yi haka sai Sadiya ta samu sassaucin rashin mutumcinsa, bayan kwana biyu kuma ya ɗora daga inda ya tsaya. Duk aikin da Sadiya take yi wa Inno sannu a hankali ya dinga dawowa kan Fauziya, lokaci ɗaya ta yi wani irin duhu ga rashin hutu daga wannan sai wannan. Murmurewar jegon da ta yi duk sai ta zuge, a ɓangare ɗaya ga tunanin halin da gininsu yake ciki. Saboda halayen Kabir sun dawo mata sababbi, don tana yi masa magana yake rufe ta da faɗa. Idan Inna ta jiyo sai ta ƙarasa bakin ƙofa ita ma ta cigaba da tofa albarkacin bakinta. Babban abin da ya fi ɗaga mata hankali, bai wuce yadda ta lura da take-taken Inna tana son fara ɗora wa su Na'ima talla ba. Duk da ba ta fito ta faɗa ba, amma ta lura da yanayin shaguɓen da take yi. Hakan ne ya sa ta shiga takura wa Kabir a kan ya saka su a makaranta, amma sai dai ya ce mata ba shi da kuɗi. Kuma ta rasa wurin da yake zuwa, a kullum ya dawo gida da wuri haka zai buga wankan ƙananan kaya ko manya ya fice daga gidan. Wani lokacin ma sai ta yi bacci yake dawowa, saboda gajiya ta sa ana yin sallar Isha'i take yin bacci. Watarana suna zaune bayan magriba yana tsaka da shiri ta ce. "Abban Na'ima!" "Ina jin ki." Ya amsa mata yana saka belt ɗin wandonsa. "Wai kasuwar ɗinkin ce yanzu ba a samu ko yaya? Zaman yaran nan babu makaranta baya zai mayar da su, don Allah ko Islamiya ce ka saka su." Sai da ya ƙarasa komai sannan ya ce, "Islamiyyar ma ai ba kyauta ake zuwa ba, ki bari idan na samu kuɗi zan saka su. Kin san dai yadda abubuwa suke ƙara tsada." Saboda takaici ba ta tanka masa ba, ya gama shiryawa yana fesa turare, a daidai lokacin wayarsa ta kawo haske da yake a silent take. Da sauri ya ɗauke wayar ya saka a aljihu har zai fita Fauziya ta ce, "Abban Na'ima ni fa ban gane wannan shige da ficen nan da kake yi ba. Ina za ka je ne da daren nan?" "Haifata kika yi da za ki tsare ni da tambaya, ina ruwanki da wurin da za ni? Kin san dai yanzu na daina shaye-shaye ballanta ki kafa mini zargi." Sai kawai ya saka kai ya fice daga ɗakin, shiru Fauziya ta yi tana nazari. "Tabbas ruwa ba ya tsami banza, wallahi akwai abin da Abban Na'ima yake ƙullawa." Ta faɗa a sanyaye, tana jin nadamar ba shi kekenta. Saboda ta san da ko da kuɗin gyaran da take yi ne za ta iya samu ta biya musu kuɗin makaranta, a nan take tunani ya faɗo mata a kan ta fara yin wankau tun da yanzu Sadiya ba ta nan. Sai kuma ta ga sam ba za ta iya wankau ba, don wani lokacin ko wankin yaranta ta yi wuni take bayanta yana ciwo. Sai kuma dabara ta faɗo mata a kan ta fara yin kitso, da wannan shawarar ta bar wa zuciyarta a kan idan gari ya waye za ta shiga maƙota duk ta faɗa musu. Kabir yana fita daga gidan ya ciro wayarsa ya latsa lambar Surayya yana faɗin, "Na fito fa baby." Surayya ta akashe murya ta ce, "Tun ɗazu fa nake ciki da muradin son ganinka gwarzona." Amsa mata ya yi sannan ya kashe wayar. Adaidaita sahu ya tara kai tsaye ya wuce unguwarsu Surry, waya ya ciro ya kira ta sannan ta fito. Kamar kullum idan za su yi zance a soron gidan suke yi, hakan ce ta sa yanzu ma ta shimfiɗa musu dadduma a soro. Rungumo Surayya ya yi, ita kuma ta kamo bakinsa ta fara sakar masa kiss. Nan take Kabir ya fara birkice mata, ya shiga kai hannunsa cikin sassan jikinta. Jingina suka yi da bango, ita ma Surry ta fara sarrafa shi da hannunta tamkar ƙwararriyar matar aure. "Baby na gaji fa!" Kabir ya furta cikin wani irin yanayi. "Kamar yau ne fa, ba yanzu saura wata goma ba. Ni fa ba don 'yan gidanmu ba, da ko ba lefe tsaf za a sha biki. Don tun lokacin da aka tsayar da rana na so a saka wata shida." Janye kansa ya yi daga cikin ƙirjinta ya ɗago yana kai hannunsa ciki jikinta sannan ya ce, "Amma kafin lokacin me ya sa ba za ki ɗan dinga rage mini zafi ba dear?" Surry don ta zolaye shi sai ta ce, "Ba kana da mata ba, ya kake abu kamar wanda bai taɓa aure ba." "Mtswww." Ta ji Kabir ya ja dogon tsaki sannan ya ce, "Ana maganar matan da suka cika cikakkun mata, kina sako mini zancan waccan abar. Don Allah ki taimaka mu dinga zuwa gidan can kina yi mini dabaru." Wani irin daɗi Surry ta ji, saboda ta jima da fahimtar matarsa ba komai ba ce a wurinsa. Ta sake maƙale shi ta ce. "Shi kenan my love, zan yi ƙoƙari na dinga yi wa su Yaya dabarar fita, kasan tun da aka saka ranarmu yake saka mini ido sosai." Sake haɗe bakinsu Kabir ya yi sai da suka ji alamar motsin za a fito, da sauri ya sake ta yana sauke numfashi, Surry ta wayance da cewa. "Hasko nan mu ga ko can azurfar taka ta yi." Wayarsa ya zaro ya fara haska mata, kamar masu neman azurfar gaske. Suna cikin haka Yaya Umar ya yi musu sallama ya fita daga gidan. Ya so sake yamutsa Surry ta nuna masa ya yi haƙuri za ta dinga zuwa can gidan, saboda tana tsoron kada yayanta ya sake dawowa ya kama su. Cike da kewar Surry Kabir ya fito daga soron gidan, yana fitowa babu jimawa ya zaro wayarsa. Misscall ɗin Farha ya gani har sau uku, ya latsa layin nata yana karawa a kunne ya ce. "Ina fatan sarauniya ba ta yi fushi da ni da." "Idan na yi ma ai ka saba kanainaye zuciyata har ta yi maka afuwa." Farha ta furta cikin shagwaɓa. Murmushi ya yi yana jinjina baiwar da yake da ita. Kabir irin mazan nan ne masu iya tsara zance da kanainaye zuciyar 'yanmata. Ya ƙwarai sosai wurin iya yaudara da kife mace, kuma yana ɗaya daga cikin maza masu kule-kule da ƙoƙarin dandanlar arzikin jikin budurwa. "To yanzu dai ayi mini afuwa cajina ya ƙare, zan kira ki da asuba. Ina fatan za ki yi bacci da ni a zuciyarki." Kafin su yi sallama sai da suka yi musayar kalaman soyayya sannan ya katse. Lokacin da ya ƙarasa gida tuni Fauziya ta yi bacci, don haka ya ɗauki buta ya faɗa banɗaki ya tsarkake jikinsa sannan ya koma ɗaki. Sannu a hankali haka rayuwa ta cigaba da tafiya watanni suna shuɗewa, Fauziya ta fara kitso babu laifi tana samun ɗan kuɗin kashewa. Da kanta ta saka yaran a wata makaranta da ake yi boko da Islamiyya, sai dai duk da hakan ba su tsira ba sai da Inna ta fara ɗora musu tallar barkono ranar Alhamis da Juma'a. Tun Fauziya tana kara har ta gagara haƙuri ta yi wa Inna magana, a lokacin faɗa ta rife ta da shi amma da shi ma Kabir ya nuna yaransa ba za su yi talla ba sai ta kawo ido ta saka masa. Fauziya da karanbami har magana ta yi a kan su Salim, a nan ne Inna ta ce daga Kabir har ita ba su isa ba matuƙar ba mahaifinsu ne ya hana ba. Wannan dalilin ne ya ja wa Fauziya da yaranta baƙin jini a wurin Inna, ko fita suka yi tsakar gida wasa ta dinga zaginsu tana hantarasu wani lokacin har da duka. Daga ɓangaren Kabir shi ma zamansa da ita tuni ya sauya salo, don babu abin da za ta yi masa haka kawai zai ɗauki fushi da ita. Ko kuma magana kaɗan za ta yi masa sai ya rufe ta da faɗa, daga haka ma sai ya ƙaurace mata. Domin a zaman da suke yi sun tafi kusan wata biyu ba tare da wani abu ya gifta a tsakaninsu ba. Ana cikin haka watarana Kabir ya dawo da daddare a lokacin sha ɗaya saura, a zaune ya samu Fauziya ta yi shiru tana nazari. Tsakin da ya ja ne ya sa ta ɗago tana kallonsa, karaf idonta ya sauka a kan damɓareren jambakin da ke gaban rigarsa har zuwa leɓensa. Ta haɗiyi wani irin yawun takaici, amma ba ta tanka masa. Kamar yadda ta yi tsammani, buta ta ga ya ɗauka ya tafi banɗaki. Ba tun ranar ba, dama ta lura da shi kusan kullum idan ya dawo ya yi wanka ya fita, to bayan ya sake dawowa daga yawonsa sai ta ji ya ɗebi ruwa yana wanka. Ya tafi banɗaki ba jimawa ta ji kira ya shigo wayarsa, a kan windo ta hango wayar jikinta har rawa yake ta saka hannu ta ɗauka. Wannan ce rana ta farko da zuciya ta ingizata a kan ta ɗauki wayarsa, ƙirjinta yana bugu ta ɗauki kiran da ta ga an ributa 'Sec wf' Ɗauka ta yi sai ta yi shiru daga can ɓangaren ta ji an ce. "Baby don Allah idan za ka yi wanka ka turo mini hoton lovely ɗina, ni ma na turo maka ina wanka ka duba whatsapp ɗinka." Da sauri Fauziya ta katse, ta ci sa'a wayar babu key tana duba whtaspp ta ga sakon lambar da aka kira. Ƙazantaccan hotun surorin jikin Surry ne, sai ta yi sama a nan ta ci karo da hotunan al'aurar Kabir ya tura mata hotuna. Sai kuma wasu hotuna da ta gansu rungume da juna hannun Kabir yana saman ƙirjin Surry. A yadda ta gani babu riga a jikinsa, ta ga kuma ita ma Surayyan ko ɗankwali babu a kanta. Amma sai ta lura wurin da suke kamar ba gida ba ne. "Innalilla wa Inna ilahir raji'un." Fauziya ta furta tana jin kanta yana sarawa, idabunta suka fara ganin dishi-dashi. Ɗakin da take ciki ta ga ya fara juya mata. GIDANSU MAIMUNA Saboda fushin da Nazir yake yi da Maimuna ya sa koda gari ya waye bai bi ta kanta ba, wanka kawai ya yi ya ɗebo shinkafa kofi huɗu ya tsiyayo mai wata 'yar roba ya ajiye mata sannan ya fice kasuwa. Maimuna tana kallonsa duk abin da yake yi har ya fita, da yake a lokacin tuni yaranta sun tafi makaranta, wanka ita ma ta shiga ta tsala a banɗaki. Bayan ta fito ta zaro wayarta ta ga misscall ɗin Jafar, goge hannunta ta yi za ta kira ta ga wani kiran ya sake shigowa. Tana ɗauka cikin zumuɗi ya ce. "Baby ke fa nake jira." Murmushi Maimuna ta yi ta ce, "Na gama komai kayana zan saka." Katse kiran ya yi. Maimuna ta jima a gaban drower kayanta, sai ta ɗauko wasu figaggun ƙananan kaya ta saka, ta zaro zumbulelen hijabinta ta zura. Ƙaramar wayarta ta gani Nazir ya mantata a falo, don ta tabbatar da ya yi nisa da gida sai ta kira shi. Har ta kusa katsewa sannan ya ɗauka. "Ina jinki." "Na ga ka ajiye mana shinkafa, har dare ko iya rana." Ta furta tana sauraron yanayin wurin da yake. Daga cikin wayar ta ji alamar yana cikin kasuwa, don ta ji ana tambayarsa hula lamba ashirin (Size 20). "Har dare za ku dafa." Ya ba ta amsa a zafafe yana katse wayar. Tsalle ta buga sannan ta ɗauko mukulli ta rufe gidanta, kamar yadda Jafar ya ce zai bar mata gidan a buɗe haka ta same shi. Duk da ta san Maman Nana ba ta nan, haka kawai ta ji gabanta yana faɗuwa. Tana shiga ciki ta hango shi daga shi sai gajeren wando, da sauri ya ƙarasa ya rungume ta yana zame hijabin jikinta. Wata irin kunyarsa Maimuna ta ji ta sunne kanta ƙasa, shi kuwa ya shiga laluben jikinta kamar waɗanda suka jima da sanin juna. A kan gadon Maman Nana suka yada zango, Jafar ya shiga rage mata kayan jikinta har ya raba ta da su gabaɗaya, ya shiga gwaɗa mata zafaffiyar soyayya. Abin da ya birge ta, ya kuma ba ta mamaki yadda ta ga Jafar ba ƙyamar komai na jikinta. Abin da Nazir bai taɓa yi mata ba, don shi ko kiss bai damu da ya yi wa mace ba. Sai da Maimuna da Jafar suka gigita juna sannan komai ya wakana a tsakaninsu, cike da so ya rungumo ta a jikinsa ya ce. "Don Allah ki cigaba da ni haɗin kai zumata." Gyaɗa masa kai ta yi har lokacin hannun Jafar yana cikin jikinta. Bayan gari ya waye sai da Maman Nana suka ci abinci sannan ta yi musu wanka, ta nufo hanyar gidanta. Mahaifinta ya yi mata nasiha sosai, ya sake tabbatar mata da zai kira Jafar ya yi masa faɗa. Da yake ita ma tana da mukulli a hannunta, tana zuwa bakin gate ta saka key ta buɗe jamlock ɗin. Ta yi mamaki da ta ga motarsa a gida har lokacin, amma sai ta yi tsammanin ko lalacewa ta yi bai fita da ita. Don haka ba ta yi wata-wata ba ta nausa kanta ciki, tun daga tsakar gida ta fara jiyo sautin dariya da wasannin da suke yi a cikin banɗaki da ruwa suna wanka. AlhamduLIllah a nan ƙarshen free pages ya ƙare, ba sai na tsaya bayanin irin cakwakiyar da za a riska a gaba ba. Mai son cigaba zai biya kuɗin karatu 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 In Shaa Allah Jibi Asabar zan cigaba da posting a paid group Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [04/12/2024, 14:28] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA SHAFI NA ƊAYA Jar mota ƙirar golf ce take tafiya a hankali, saboda tsufa da lodin magunguna tare ɗima-ɗiman manyan sifikun da suka yi mata nauyi. Ta baya boot ɗin motar a buɗe yake waɗansu matasan samari ne a zaune, hannuwansu riƙe da jarkokin magunguna suna ɗagawa. Tayoyi da gefen motar duk sun yi butu-butu, saboda ƙura da jar ƙasa. Mai maganin gargajiyar yana daga cikin motar, ya sake ƙara volum ɗin recording ɗin tallan magungun da yake yi. "Alhaji ko Hajiya idan har matsalarku sanyi ne ku zo ga babansa. Ni fa ba na rantsuwa a kan magungunana saboda sadidan ne, amma idan har kuka sha maganina bai yi muku aiki ba ku dawo na ba ku kuɗinku. Ina mai fama da sanyin ƙashi, sanyin mara da ciwon baya ku zo ga waraka ta zo muku har gida. Alhaji kai ne ake ganinka kullum cikin babbar riga, ana yi maka kallon cikakken namiji amma a baɗini kana jin kunya to ka zo mu saka labule don Allah." Mai maganin ya rage volum ɗin recording ɗin, sai ya zuro kansa ta window ganin ya ƙaraso wurin da jama'a suke zirga-zirga ya ce. "Al'ummar Annabi ina magidancin da yake son huce takaicin sanyin nan da muke ciki? Amma ɗan kanoma ya yi masa mugun kamu. Don Allah kada ya ji kunya, ya zo ya samu mai warakar sanyi matsalarsa ta kau da ikon Allah. Cutar rana, kumburin ciki, zafin bayan gida, basir da cutar sanyi duk ni ne likitan da ke magance su." Baba Inu da ke kishingiɗe a kan benci ya tashi zaune, ya ɗan ƙanƙance ido yana ƙarewa motar da mai motar kallo, saboda masu magungunan ba baƙinsa ba ne, don yana iya tantance duka masu magungunan gargajiyar da suke shigowa garinsu. Musamman yadda suke haba-haba da shi, duba da yadda ya zame musu babban costomer. "Kai mai magani, zo nan." Baba Inu ya kira shi yana yafito shi da hannu. Da sauri mai maganin ya gyara paking ɗin motar yana kaikaitata a daidai ƙofar gidan. "Babana da Innata ga ɗan baiwar masu magani ya sauka, mai warkar da matsalar sanyi ya zo kada a yi wasa." Mai maganin ya sake furtawa a loudspeakersa. Ƙuri Baba Inu ya yi masa ya ce. "Abokina amma dai kai baƙo ne

Chapter 23 of 35