Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA SHA ƊAYA GIDAN INNA Wani irin ɓacin rai ne ya lulluɓe zuciyar Fauziya, rai a ɓace ta miƙe tsaye tana ɓalle maɓallin rigarta. Shi kansa Kabir bai ji daɗi ba, cikin tausasa harshe ya ce. "Don Allah ki yi haƙuri Fauziya." Fuska babu walwala ta ce, "Babu damuwa." Ya ɗan leƙa fuskarta ya ga har lokacin babu alamar fara'a, duk sai ya ji babu baɗi. "Kin san iyaye wani abin sai ana haƙuri da su." Ya furta a sanyaye. "To ni me na ce Kabir? Ka je idan ka gama sai ka ci abincin." Fauziya ta furta bayan ta zura doguwar rigar bacci, can gefen katifa ta koma ta kwanta. Kamar Kabir zai yi mata magaba sai kuma ya fasa ya nufi ɗakin Inna. A bakin gado ya samu Inna da alama ta gama cika, ya zauna a ƙasa ya ce. "Gani Inna." "Kai ma ashe sakarai ne Kabiru ban sani ba? Don Allah kai ba ka ji kunyar kanka ba, a ce tun farkon dare ka naniƙe 'yar mutane a ɗaki? Kai Allah dai ya sawaƙe da wannan jaraba ta 'yan zamani." Shiru Kabir ya yi, sai ya ji kunya duk ta kama shi. Inna ta taɓe baki ta ce, "To dama kuɗinka na wurina nake son na ranta, idan ba amfani za ka yi da su ba. Na ji an ce barkono ya sauko a ƙauye zan saro na dinga ƙulla wa yaran nan." Da sauri Kabir ya ɗago ya ce, "A'a Inna, dama na ce ki adana mini su ne saboda ban samu ciko ba. Amma zaman da muka yi da Fauziya, yanzu ta ba ni keken ɗinkinta, idan na sayar da shi sai na haɗa kuɗin suka cike dubu ɗari. Idan ya so sai a tura su Yaya su kai kuɗin, don Allah Inna kada ki taɓa ko sisi, wallahi yayan yarinyar nan ne ya ba ni sati biyu. Idan ban tura ba zai iya aura mata wani." Inna ta wara hannu ta ce, "Ai ka ga matar rufin asiri, wallahi da Sadiya ce sisi ba za ta ba shi ba. To idan an kai kuɗin auren wai a ina za ka saka ta, ban da abin ka ai da bari ka yi ka kammala gidanka tukunna. Ka ga lokacin hidima ta yi maka sauki, don ma kai Allah Ya haɗa ƙashin arzikinka da na matarka" Tagumi Kabir ya zuba da hannuwa biyu ya ce, "Wallahi ni ma haka na so Inna, to yayanta ya matsa ne. Haka ta kira ni tana kuka wai zai aura mata wani ɗan uwansu idan ba ta fitar da miji ba." A gwasale Inna ta ce, "To dama mene ne ribar yawan zancen idan ba aure za a yi ba? Ai gara a yi wacce za a yi a wuce wurin." Kabir ya tashi daga wurin da yake zaune, ya hau kan gado gefen Inna ya riƙo hannunta, sannan ya yi ƙasa da murya ya ce. "Amma wata alfarma nake nema a wurinki Inna, don girman Allah ki cewa su Yaya kada su faɗa wa matansu. Don ina gudun kada Fauziya ta ji labari, da so samu ne ma har sai bikin ya matso tukunna." "Idan ta ji uwarka ce da za ta hana ka aure? Ko kuma ƙanwar uwarka ce ita?" Kabir ya miƙe tsaye cikin tsoron kada Fauziya ta ji ya ce, "Don Allah Inna ki yi shiru kada ta ji, kin san fa yadda aka yi wurin sayen filin gidan can da kuma ginin. Wallahi idan ta sani tana iya cewa Surayya ba za ta zauna a gidan ba, tun da haɗa su nake son yi.." "Mtsswww." Inna ta ja dogon tsaki ta cigaba da cewa, "Amma dai wallahi an yi lusarin namiji, shashasha da bai san ciwon kansa ba. Saboda ta sayar da firjinta ta ba ka ka sayi ƙofofi, sai ta hana ka yin aure? Wai me ya sa kake son zama sakarai hotiho ne Kabiru? Kai ne fa miji ba ita ba, wai dama haka ka lalace a wurin yarinyar nan ban sani ba?" Kabir ya saka hannu yana kare bakinsa alamar Inna ta yi shiru, ya sake kwantar da murya ya ce. "Ba fa kuɗin firji nake nufi ba, wannan ai na ƙarshe-ƙarshe ne da ta ba ni. Kin manta na ce miki kuɗin gadon wurin mahaifiyarta ne, ta ba ni muka haɗa da kuɗin wurina muka sayi filin, to a ginin ma akwai kuɗaɗen da ta ara mini sai daga baya ne ta ba ni na firji." Jin kalaman Kabir ya sa Inna ta taɓe baki ta ce, "To sai me? Kai dai an riga da an shanye ka wallahi." Kabir da ya lura Inna ta ɗauki zafi kuma tana iya tsula wa kwaɓarsa ruwa, sai ya shiga rarrashinta. Sannan ya nuna mata da ta gargaɗi 'yan'uwansa a kan maganar auren, har ya samu ya shawo kanta. A lokacin da ya koma ɗaki Fauziya tuni ta yi bacci saboda gajiyar aikin da ta sha, cikin sanɗa ya sake jan ƙafa ya fice daga ɗakin sai ya nufi hanyar fita. A bayan layinsu ya tsaya ya zaro wayarsa ya latsa lambar Surayya, bugu ɗaya wayar ta yi ya ji ta ɗauka muryarta da alamun bacci. "Baaabyyy." Jin yanayin muryarta ya sa jin wani irin yanayi, ya kwantar da murya yana raɓewa a jikin bango ya ce. "Baby wannan muryar tana azabtar da ni." Surry ta saki murmushin ƙeta ta ce, "Kamar yadda taka take hargitsa ni ba." "Albishirinki zumata." Cikin sauri Suryy ta ce, "Goro My." "In Shaa Allahu a satin nan su Yaya za su kawo kuɗin aurena gidanku." Farinciki kwance a saman harshenta ta ce, "Don Allah da gaske?" "Zan yi miki wasa ne?" Kamar tana gabansa ta girgiza masa kai, Kabir ya cigaba da cewa. "Ina tunanin har da rana za a saka, kafin nan da shekara guda In Shaa Allahu na gama haɗa lefe." Surry ta sake kanne murya ta ce, "Na ji daɗi sosai sadaukina, ina ƙaunarka masoyi." Shi ma Kabir ya kwantar da murya ya ce, "Na yi kewar komai naki." "Surayya da komai mallakinka ce Kbna." Wata sabuwar soyayyarta ce ta sake mamaye shi, ya gyara tsayuwarsa haɗe da sakarwa wayar kiss kamar yana tare da Surayyan. Sun jima suna musayar daɗaɗan kalamai, sai da dare yayi sosai sannan suka yi sallama Kabir ya koma gida. Yanayin da Surayya ta jefa shi a ciki ne ya sa bayan ya gama cin abinci, ya lallaɓe jikin Fauziya domin ya rage zafi. Duk da ya so a ce Surayya ce a maƙale a gefensa, amma a haka ya samu da ƙyar Fauziya ta ba shi haɗin kai. Domin gani take ko yaya suka yi motsi Inna za ta iya gane halin da suke ciki. Washegari tun da farar safiya ta fara jiyo hayaniyar Sadiya da mijinta, tun suna yin faɗan da cacar baki a cikin ɗaki har suka fito tsakar gida. Kamar Fauziya ta danne kada ta fita, sai ta ji kamar dukanta Sadiya Yaya Nura yake yi. "Wallahi ba zan taɓa yafe maka ba, Allah sai ya saka mana." "Kada ki yafe mana, ai wallahi na yi nadamar aurenki." Cikin kuka ta ji Sadiya ta ce, "Ni zan faɗi haka don wallahi na gama zama da kai har abada." Da sauri ta fita tsakar gidan tana faɗin, "Subhanallah me yake faruwa haka?" Wurin Sadiya ta ƙarasa da ke yashe a ƙasa tana kuka, a daidai lokacin Yaya Nura ya fito yana faɗin. "Ki tarkata komatsanki ki koma can baƙin garinku, na ƙarashe ragowar igiyar aurenki a kaina. Na saki, yau zan yi bacci da saleɓa." Sadiya ta fisge hannunta daga jikin Fauziya ta ce, "Sai me? Ai wallahi da wannan ƙaddararran auren na ka gara na ƙarasa rayuwata a haka." A wannan lokacin Kabir ya fito daga banɗaki ya ce, "Haba Yaya, a gaskiya abin da ka yi sam bai dace ba. Aunty Sadiya ba ta cancanci haka daga wurinka ba, ga duka ga saki abin ya yi yawa." "Ɓarauniyar za ka ce na cigaba da zama da ita? Me ake da mace ɓarauniya ana zaune ƙalau, ni wallahi da na san haka zuri'arsu take ta ɓarayi; wallahi da ban auro ta ba. Haka kawai ta zo ta gurɓata mini zuri'a da mugun hali." Inna da tun farko take ɗaki tana sauraronsu, sai a lokacin ta leƙo ta ce. "Ai wallahi ya yi mini daidai, saboda Allah Sadiya duk ta raina yaron nan. Miji wasa ne? Abin ya kai har da sata, yara gasu nan su uku ne Allah ya raya su." Mamaki ne ƙarara ya lulluɓe Fauziya, don son zuciyar Inna a bayyane yake ƙarara. Duk wanda ya ga Sadiya ya ga halin da take ciki ya san ba ta jin daɗin gidan aure. Cikin tsantsar tsana Sadiya ta miƙe ta isa gaban Inna zuciya tana suya ta ce, "Ai dama 'ya'yanki ba sa laifi, amma ki sani ki bar ganin 'ya'ya maza duk gare ki. In Shaa Allahu sai kin ga sakayyar son zuciyar da kika nuna mini, shi kuma yadda ya azabtar da ni da yunwa haƙƙinmu ba zai bar shi ba. Sata kuma da ake iƙirari ko gaban malamai na je hukuncin sata ba zai hau kaina ba. Saboda abinci ya hana mu, ni kuma na shiga rumbunsa na ɗiba zan girka mana shi ne ya rufe ni da duka. Allah Ya ba ni wanda ya fi ka, domin kai ba mijin aure ba ne." Yaya Nura ya saki dariyar izgilanci ya ce, "Kina fama da gajartar ne za ki samu wanda ya fi ni, ai ni ma tsautsayi ne ya taɗe ƙafafuwana har na faɗo kanki. Ki tashi ki fice mana daga gida, kuma kada ki sake ki ɗaukar mini 'ya'ya." Tuni hawaye ya wanke Fuskar Fauziya ta ce, "Sadiya wai mene ne haka kuke yi a gaban yara ne?" Ta kalli yaran Sadiya da su Na'ima da suka yi carko-carko, wasu daga cikinsu suna hawaye. "Waɗannan mutanen da kika gani ƙarshen butulaye ne, ba su san karamci da hallaci ba Fauziya. Hakan shi ya fi mini alheri In Shaa Allahu." Sadiya tana gama magana ta miƙe ta shiga ɗaki, kayan jikinta ta sauya. Ta ɗauko wata ƙatuwar jakarta ta loda kayanta a ciki, hijabinta ta saka ta fice daga gidan. Maƙota ta dinga bi tana karɓar kuɗaɗen waukau da take bi, sannan ta ƙarasa titi ta taro Mai adaidaita sahu har ƙofar gida. Kusan a inda ta bar Fauziya a nan ta koma ta same ta, suna ganinta gabaɗaya suka yi kanta cikin sanyin jiki. Ɗaki ta shiga ta jango ƙatuwar jakartata, Salim da Zainabu suka ƙarasa suka rungume ta suna kuka. "Don Allah kada ki tafi Umma." "Umma idan kika tafi Inna dukanmu za ta yi." Suka furta cikin kuka, hawayen da Fauziya take riƙewa ne ya fara zuba. Ta saka hannu ta toshe bakinta tana kuka, Sadiya ta haɗiyi yawu mai ɗaci hawaye masu zafi suka shiga tsiyaya daga idanunta. Cikin tausasa lafazi ta riƙo hannunsu ta ce, "Zan dinga zuwa ina ganinku lokaci-lokaci, Allah Ya yi muku albarka Zainabu." "A'a mu dai ki tafi da mu." Zainabu ta faɗa tana hawaye. Da sauri Yaya Nura ya ƙarasa a fusace ya fisge hannunsu yana faɗin, "Duk wanda na ƙara jin muryarsa sai na taka wuyan yaro." Fauziya ta ƙarasa cikin kuka ta ce, "Don Allah ka bari ta yi sallama da 'ya'yanta cikin salama, wannan hawayen da ka ga suna fitarwa har abada ba za su manta da shi ba." "Da ta san tana ƙaunar yaran take ƙin yin haƙurin zaman gidan ubansu." Sadiya ta dube shi cike da tsana ta ce, "Kada ki damu Fauziya, ni uwa ce na tabbata duk daren daɗewa za su nemo ni. Hakan da ya yi ba shi zai sa su kankare ni a matsayina na mahaifiyarsu ba, ba don na san halin mugun halin gidan nan ba. Da sai na damƙa miki amanar 'ya'yana, amma na san wacece ke Fauziya da kyakkyawar zuciyarki. Ina fatan Allah ya sada mu da alheri. Fauziya ta rungume Sadiya tana hawaye, a hankali ta janye jikinta tana jan jaka har ƙofar gida. Ganin haka ya sa su Salim suka saki matsanancin kuka suna ƙwala mata kira. Sadiya ba ta waigo ba sai ma hawaye da take zubarwa, jakar ta saka a cikin adaidaita sahun. Har ta zauna a ciki tana jin ihun Zainabu da take ƙwala mata kira tana ihu, sai kawai ta kifa kanta a kan cinyoyinta ta saki gunjin kuka mai cin zuciya. GIDANSU MAIMUNA Shirun da Maimuna ta yi ya sa Jafar ya ce, "Kin yi shiru My Moon." Maimuna ta ce, "Gaskiya tsoro nake ji, kada tsautsayi ya sa Nazir ya dawo bai same ni a gida ba. Ka san akwai matsala tun da ba barina fita yake ba, ni dai ina ganin mu cigaba da yin video call hakan zai fi." Ba don ya so ba ya narke mata ya ce. "To ya na iya baby? Amma dai gaskiya ki rage mini kayan jikinki, na fi son na ganki sosai bari ni ma ki ga." Jafar yana gama maganar ya jingine wayar a gefe, ya zame ragowar ƙananan kayansa. Ita ma Maimuna babu kunya, ta zame rigar jikinta. Ya rage daga ita sai rigar mama, can saman gadonta ta haye sannan ta ɗauki wayar ta ce. "Baby ka gama kuwa." Ido suka haɗa ta cikin wayar, Jafar ya ji wani irin abu ya tsarga masa. Bakinsa yana rawa saboda shauƙi ya ce, "Mooooonnn." Yanayin yadda ya kira sunanta ya sa ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe ido, sai ta buɗe su tana ƙura wa faffaɗan ƙirjinsa mai cike da yalwataccan gashi da kallo. 'Haƙiƙa dole Maman Nana ta dinga ɓarin zancan a kanka, tabbas! Jafar ba irin ragowar sauran mazaje ba ne.' Maimuna ta raya a ranta, tana shirin yin magana Jafar ya ce. "Baby wai dama haka Allah ya zuba miki sura? A gaskiya Nazir ba ƙaramin dace ya yi ba." Maimuna ta shagwaɓe murya ta ce, "Nazir ne ya yi dace ko Maman Nana? Allah Ya sani ba zan ɓoye maka ba Baby J. Wallahi za a daɗe ba a samu ingarman namiji kamarka ba." Kalaman Maimuna suka sake kashe masa jiki, ya kwantar da murya cikin shauƙi ya ce. "Ina ma yanzu haka a tare muke, da na shayar da ke romon soyayyar da ba ki taɓa sharɓa ba. Ina kewarki Moon, ina ƙaunarki komai ina ji a kanki Habibtee." Maimuna ta saki murmushin jan hankali, suna cikin haka Jafar ya nemi Maimuna da ta cire rigar da ta rage mata, kamar ba za ta iya ba sai sheɗan ya sake ingiza ta. A hankali ta cire komai na jikinta, suka shiga musayar munanan kalaman batsa. Suna nuna wa junansu duka sassan jikinsu, Daga Jafar har Maimuna ba ƙaramin gigicewa suka yi da ganin surar junan ba. A haka har Jafar ya yi galaba a kanta, ta amsa masa gayyatar da ya dinga yi mata magiya. Maimuna ta amsa masa da cewar za ta shiga wurinsa washegari idan Nazir ya tafi kasuwa, tun da yaranta suna makaranta. Ya so ta shiga a ranar amma ta nuna masa yamma ta yi, yaranta za su iya dawowa daga makaranta. Daga ƙarshe suka yi sallama cike da kewar juna. MAMAN NANA Tun bayan da ta fita daga gida take tafe tana hawayen baƙinciki, ta biya ta makarantar su Nana ta ɗauke su suka wuce gidansu, yaran sai tambayarta suke yi ta ce musu ba ta da lafiya. Lokacin da ta je gida mahaifinta ya fita kasuwa, ta sanar wa mahafiyarta duk abin da ya faru. Ko kaɗan ba su ji daɗin abin da Jafar ya yi ba, amma ita ma sun yi mata faɗa sosai kuma suka ba ta rashin gaskiya. Daddare bayan mahaifinta ya dawo, mahaifiyarta take sanar da shi abinda ya faru. Kiran Maman Nana ya yi, ta tunkari ɗakin gabanta yana faɗuwa. "Amma ban taɓa sanin ba ki da hankali ba sai yau Sumayya, an faɗa miki miji wasa ne da za ki cakumi wuyansa a kan yana waya da budurwa." Mahaifinta ya rufe ta da faɗa bayan ta zauna. "Baba marina ya yi fa a kan na ce mata 'yar iska, kuma don wulaƙanci a ɗakina yake waya da ita." Mahaifinta ya girgiza kai ya ce, "Idan ya yi waya a ɗakinki Sumayya, tambarin wayar ne zai fito a goshinki? Tun da kin faɗa da baki bai ji ba me ya sa ba za ki bar masa ɗakin ba? Kin san maza kowa da irin halinsa ai, wani har ya gama neman aurensa mace ba za ta sani ba. Wani kuma a gabanta zai yi komai, to yanzu da kika yi hakan me ya rage shi?" Maman Nana ta saka kuka, Baba ta nuna ta da yatsa ya ce. "Daga yau kada na sake jin kin aikata wannan ɗanyan aikin Summaya, idan kin ji yana wayarsa ki bar masa ɗakin ko ki kama aikin gabanki. Kuma ko da wasa kada na sake jin ki kira budurwarsa da 'yar iska, ke ba a auren aka aure ki? Namiji ai mijin mace huɗu ne, bayan ita ma yana ikon neman guda biyu ya aura." Cikin shasshekar kuka ta ce, "Baba ba za ka gane ba, Jafar duk ya canza mini kamar ba shi ba. Yanzu fa ko abinci bai cika ci ba, ga shi gas ɗin da nake aiki ya ɗauke sai buhun gawayi ya dire mini. Da na yi masa magana har gori ya yi mini, wai su Umma ma da itace suke amfani." "Ƙarya ya yi? Ai ba ƙarya ba ne, ko ɗazu ma da shi kika ga na yi girki ai. Yaran yanzu ba ku ajiye komai ba sai baƙin kishin tsiya." Mahaifiyarta ta yi maganar cikin faɗa. "Tun da har yana ciyar da ke yana tufatar da ke, duk abin da ya kawo miki matuƙar ba guba ba ne sai ki karɓa, da hannu bibbiyu ki yi godiya ki sarrafa shi. Haba Sumayyan Baba ina ganin ki kamar mai wayo ashe ba haka ba ne, don Allah ki kiyaye gaba. Shi kuma zan kira shi ya zo na yi masa faɗa don a sharuɗɗan aure babu dukan mace a ciki." Baba ya ƙarasa maganar cikin tattausan lafazi, sai ya ciro wayarsa ya latsa lambar Jafar ya ji ta a kashe. Ya mayar da kallonsa wurin Sumayya ya ce. "Na kira mijinki wayarsa a kashe, yanzu dai dare ya yi babu damar ki tafi. Amma idan Allah Ya kai mu gobe da safe, ki shirya yaranki ki koma ɗakinki za mu yi magana da Jafarun." Maman Nana ta gyaɗa masa kai, Mahaifi da mahaifiyarta sun jima suna yi mata nasiha sannan ta tashi ta koma ɗaki. In Shaa Allah gobe za mu gama free pages, masu son littafin za su biya kuɗin karatu 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 Idan kun ba ni haɗin kai zan yi ƙoƙari na kammala shi kafin Azumi🥹 idan kuma na ga kun wankacalar da ni, sai na bari zuwa bayan Sallah idan muna da yawancin kwana.🥸 Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [20/02, 19:45] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA SHA BIYU GIDANSU MAIMUNA Ganin irin miyagun ɗabi'un da Maimuna ta ɓullo wa Nazir, ya sa shi tattara ta gabaɗaya ya yi watsi da ita. Dama can ba ya dawowa gida da wuri, don haka ko da ya kai dare idan ya ci abinci hakan ba ya hana shi ya sake fita. Har mamakin Maimuna yake, saboda gabaɗaya halayenta sun sauya. Maimunan da ya sani a baya ko kara ya ajiye ba ta isa ta ƙetare ba, duk da taurin zuciya irin nata sai da ta kai ta kawo ya sa ta yi laushi, ta yadda ko musu ba ta isa ta yi masa ba. Amma a yanzu Maimuna ta yi masa rainin da ko ƙannensa ba su yi masa ba, ya hana ta shiga mutane ya hana ta hulɗa da maƙota. Ya hana ta riƙe babbar waya, ya hana ta shige cikin danginta sosai. Ya hana ta cigaba da karatu duk don kada ta saba da shiga jama mata su zuga masa ita. Amma sai ga shi a rana tsaka tana shuka masa rashin mutumci son ranta, don a yanzu ba ta shakkun idan ya faɗi magana ta mayar masa. Dalilin haka ne ya sa ya tsiri zuwa majalisar gaban gidansa, da yake wasu maƙonsu suna zama shi ma ya bi sahunsu. A ɓangaren Maimuna kuwa hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba, saboda tana jin fitarsa take yin zaraf ta ɗauko wayarta ta kunna data su fara shan soyayya ita da Jafar. Maimuna bayan whatsapp har sabon Acc na facebook ta buɗe, amma ba da sunanta na ainahi ba sai kawai ta rubuta 'Matar Mai Rabo' ta cigaba da fantamawa tana harkokin gabanta. Zaman Nazir a majalisar kenan, ya samu maƙocinsa Adam yana nuna wa ɗayan maƙocin wani rubutu da ya ga an yi posting ya ce. "Ni ban san me matan aure suka ɗauki aure ba, bini-bini za ka ga rubutu ace wai a bata shawara ga halin da take ciki. Don Allah dubi wannan, wai mijinta ya hana ta cigaba da karatu bayan an yi yarjejeniya a ba ta shawara." Lawan ya saki tsaki ya ce, "Sakarcin fa, ai mata wasu a cikinsu mahaukata ne. Na tabbata a nan wasu za su zuge ta har ta kashe auren." Haruna ya ce, "A'a ba lalle ba, ka san wasu matan suna jin nauyin tambayar 'yan'uwansu neman mafita. Sai suka zaɓi a ɓoye sunansu tun da ba wani ne zai gane su ba." "Kai wannan fa ba magana ba ce, shi ya sa tun matata tana budurwa na ce mata ban yarda da wannan hawa soshiyal midiyar ba." Adam ya faɗa cikin ɓacin rai. Jin haka ya sa Nazir ya yi zaraf ya ce, "Ai wallahi tun farko shi ya sa na datse duk wata alaƙa da za ta sa a hurewa iyalina kunne, ba sai ta fita ko tana hawa soshiyal midiyar kanta zai sake wayewa ba? Don lalacewa kwanaki haka na ji ana maganar wata matar aure tana soyayya da wani matashi. Shi ma kuma a onlayin ɗin suka haɗu." Haruna ya yi dariya ya ce, "Wallahi ina faɗa muku mace fa kariyar Ubangiji ce, wallahi duk kaffa-kaffarka

Chapter 22 of 35