Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
"Ai na warke Haidar, Yaya don Allah ka taimaka ka ce Karima ta dawo. Wallahi ban san lokacin da na sake ta ba, wallahi sharr..." Inna ta katse maganar Daddy sakamakon jifan Shukura da ta yi da takalmi ta ce. "Munafuka kin ji abin da mijinki yake faɗa ko? An ya Shukura zuciyar musulunci gare ki, wallahi tun wuri ki je ki nemi yafiyar mijinki, kuma ki bi duk yadda za ki yi ki sa ya dawo da matarsa idan ba haka ba wallahi kada ki sake takowa inda nake." Daddy har cikin ransa ya ji daɗin abin da Inna ta yi, Baba malam ya ce. "Don Allah ki yi haƙuri haka, ba na jin daɗin furucin da kike mata." "Alhaji haushin yarinyar nan da nake ji, wallahi ji nake kamar na maƙure mata wuya ta mutu. Ace ki zo ki samu mace da mijinta sama da shekara ashirin, ki ƙulla makircin da za ki sa mijinta ya sake ta. Alhaji ta kyauta kenan?" Inna ta furta tana kumfar baki. Baba malam ya jinjina kai ya ce, "Ba ta kyauta ba, kin san ɗa ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba. Yanzu dai ki je gida ki huta Hajiya." Inna ta ƙarasa bakin gadon ta duba Daddy sannan ta yi musu sallama ta fita. Su Haidar ne suka fita waje, Shukura ta maƙure a bango ban da hawaye babu abin take yi. Daddy ya sauko daga gadon, ya russuna a gaban Baba malam ya ce. "Don girman Allah yaya ka taimaka ka dawo mini da Karima, wallahi tallahi ban san yadda aka yi na rabu da ita ba. Na yi rashinta a kusa da ni Yaya, don Allah ka tausaya mini." Daddy ya ƙarasa maganar yana hawaye, jikin Baba malam ne ya yi sanyi, zai yi magana Shukura ta matsa ita ma tana sake ƙwaƙulo hawayen munafurci ta ce. "Don Allah yaya ka taimaka mini, hankalina a tashe yake da jin furucin mahaifiyata a kaina. Don Allah yaya ka taimaka ka ba wa Mommyn su Mami haƙuri." Baba malam ne ya ce ta tashi ta zauna a kujera, saboda yanayin da take ciki tun da cikinta ya tsufa. Daga Daddy har Shukura zama suka yi dirshen suna ba shi haƙuri, sai da ya gama sauraronsu sannan ya ce. "Duk na ji maganganunku, to amma ku sani. Ba ni zan zauna da kai ba Umaru, Karima ce mai zama da kai, ita ta san irin zaman da ta yi da ku. Don haka sai da amincewar Karima sannan za a mayar muku da aurenku, idam ta yarda shi kenan idan kuma ba ta amince ba dole ku yi haƙuri." Bakin Daddy har rawa yake ya ce. "Zama ma ta amince In Shaa Allahu." "Allah Ya sa." Baba malam ya furta. A ranar Daddy ya matsa sai an sallame shi, sai da suka gwada shi suka ga jininsa ya ɗan daidaita sannan suka rubuta masa magunguna suka sallame shi. A daren ranar Daddy ya sheƙa wanka ya nufi gidan Baba malam da nufin ya samu ya shawo kanta. Tun da Baba malam ya ji zuwan Daddy ya sa aka aika kiran Mommy, sai da ta shiga wurinsa sannan ya ce. "Karima na san kin san duk abin da yake faruwa, a yanzu haka Umaru yana cikin gidan nan. Ya zo domin ya ba ki haƙuri a game da abin da ya faru, to ni yanzu a tsakiya nake. Ba zan goyi bayan Umaru ba don na tilasta miki ki komai gidansa, haka kuma idan kina son komawa ɗakinki ba zan hana ki ba. Umaru shi ne mijinki tun kuna saurayi da budurwa, ke kika san halinsa da irin zamantakewarku. Kada ki cuci kanki, idan kin ga za ki koma fani'ima, idan ba za ki koma ba shi kenan babu mai yi miki dole." Mommy ta jinjina kai sannan ta ce. "Haka ne Yaya, na gode sosai da wannan shawarar taka. Allah Ya ƙara girma." Baba Malam ya amsa mata sannan ya miƙe ya fita, tana nan zaune Daddy ya shiga bakinsa ɗauke da sallama. A kunyace ya zauna ya sunkuyar da kai ƙasa cike da damuwa ya ce, "Don Allah ki taimaka ki yafe mini Mommyn Mami, ni na san mai laifi ne don Allah ki yi haƙuri ki dawo domin mu rungumi yaranmu." Murmushin takaici Mommy ta yi ta ce. "Ai tuntuni na riga da na gama magana, Shukura ita ce matarka. Don haka ka je ka cigaba da zama da ita, ni kam na faɗa maka har abada na gama zaman aure da kai." Tana gama faɗar haka ta miƙe ta bar ɗakin, kamar ƙaramin yaro haka Daddy ya fashe da kuka. Yana cikin wannan yanayin Baba malam ya shiga, da mamaki yake kallonsa har sai da ya ɗan gimtse dariyarsa ya ce. "Umaru lafiya kuwa?" Daddy ya sharce hawaye ya ce. "Yaya Karima ta guje ni, wai ba za ta dawo gidana ba. Wallahi ba zan jya rayuwa babu ita ba." Sai ya sake fashewa da kuka, Baba malam ya saki murmushi ya ce. "To ai haƙuri za ka yi, yadda ka bi ka cunkusa mata kayan takaici a baya, haka za ka yi haƙuri ka yi ta lallashinta har ta sauko. Idan da rabon zama sai ka ga ta dawo maka, idan babu kuma sai dai ta auri wani." "Wallahi ba za ta auri wani mijin ba bayan ni, hauka ake yi matata Karima ta auri wani ƙaton. Wallahi kowaye sai na yi shari'a da shi." Daddy ya faɗa a ƙufule, Baba malam da ya lura kamar Daddy bai san maganganun da yake faɗa ba sai ya ce. "To shi kenan, yanzu ka je za mu yi magana da kai gobe." Da ƙyar ya lallaɓa Daddy ya tafi, bayan ya tafi Baba malam ya samu matansa ya dinga ba su labarin Daddy suna dariya, don Mommy ba ƙaramin birge shi ta yi ba. So yake ko za ta koma ta gara shi ya ji a jikinsa kafin ta koma. Cikin kwanaki biyu Daddy ya sake birkice musu, yadda ya ɗaga hankalinsa ba ƙaramin tausayi ya ba wa 'yan uwansa ba. Hakan ne ya sa suka same ta suka sake tausarta a kan ta yi haƙuri ta koma, a wani zuwa da Daddy ya yi ne ta ce masa ta amince. A lokaci har zuwa ya yi da sauri zai rungume ta, cikin sauri ta dakatar da shi da cewar. "Me kake shirin yi Daddyn Mami? Ko ka manta a yanzu ni ba matarka ba ce?" A ɗan kunyace Daddy ya sosa kai ya ce. "Ki yi haƙuri, wallahi na manta ne." Murmushi ta sakar masa, sai a lokacin ya sake ganin fara'arta tun barowarta gidansa. A washegarin ranar aka mayar wa Daddy da Mommy aurensu, su kansu su Haidar ba ƙaramin daɗi suka ji ba. Sai dai tariya ce Mama ta ce Mommy ba za ta koma a ranar ba har sai ta yi 'yan gyare-gyare. Satin da ya zagayo da na ɗaurin auren, a ranar Mommy ta koma. Abin da ya ba ta mamaki yadda ta ga Shukura tana ta haba-haba da ita, hatta abincin ranar ita ta girka ta kawo musu a ƙatuwar kula ita da yara. Murmushi Mommy ta yi ta ce. "Shukura kina fama da kanki har da wani girki? Sannu da ƙoƙari Allah Ya raba lafiya." Sunkuyar da kai Shukura ta yi ta ce. "Don Allah ki yi haƙuri da abin da ya faru Mommy, wallahi sharrin shaiɗan ne." Mommy ta girgiza kai sannan ta ce. "Babu komai Shukura, Allah Ya yafe mana gabaɗaya." Daga haka Shukura ta miƙe ta fita, musamman yadda ta ga Daddy yana ta rawar jiki a kan Mommy sai zuciyarta ta hau suya. Tana shiga ɗaki ta datse ƙofa ta kira Inna tana hawaye ta ce. "Inna zuciyata za ta fashe, wallahi ba ki ga yadda yake rawar jiki a kanta ba." Daga can ɓangaren Inna ta yi murmushi ta ce, "Me ya sa wai kin fiye gajen haƙuri ne Shukura? Kada ki manta duk abin da nake yi a lisaafe yake. Ki duba ki ga yadda na sa suka yadda da ni, kowa gani yake ke ce ba ki yo halin kirkina ba. To yanzu ma so nake ki saki jikinki, ki nuna mata ke da ita duk ɗaya ne ta yadda za ki shiga jikinta. Sannan ina fatan duk abubuwan da na ce ki yi duk kin yi su? Kin san fa sune makamanmu na farko da za mu fara dasa bama-bamai a gidan." "Duk na kwaso su Inna, hatta ɗakinsa na shiga na ɗebi duk abin da kika ce. Ai bai san ina da mukullin ɗakin Hajiyan ba, na kai ɗakinta na saka don na san hankalinsu duka ba zai kawo komai a yanzu ba." Dariya Inna ta yi ta ce. "To ki rubuta ki ajiye, na rantse da Allah ba za a rufe sati guda ba, sai tarzoma ta tashi a gidan nan. Kuma ta cikin ruwan sanyi, za mu je har gida mu ci su da yaƙi." Shukura da Inna suka bushe da dariya lokaci ɗaya. GIDAN HAFIZ Jikin Amina yana rawa ta rufa masa baya, tana zuwa ta same shi a tsaye ya ɗauki wayarta yana dubawa. Gabanta ne ya shiga faɗuwa, yadda take jin jiri ya sa ta yi saurin zama a kan kujera. Ɓangaren kira ya duba, bai ga wani baƙon kira da ta yi ba sai wata lamba guda ɗaya. Yana dubawa ya ga a baya an kira ta ita ma ta kira, ɓangaren saƙo ya duba a nan ya ci karo da ire-iren saƙon da ake tura mata. Sai dai kuma bai ga ta mayar da martaninta ba, kansa ya ji ya sara masa. Idanunsa suka kaɗa jajir, jiki a sanyaye ya ajiye wayar. Ya mayar da kallonsa wurin Amina ya ce. "Amina da me na rage ki da shi a cikin gidan nan? Mene ne ba na gamsar da ke da har kika zaɓi cin amanata? Amina kina da aure da cikina kike soyayya da wani?" Jikin Amina ne ya shiga karkarwa, murya tana rawa ta ce. "Wallahi... ban... san komai ba Hafiz, na rantse da Allah ban san shi ba. Wallahi sharri ne..." "Uffan ba na son ji daga gare ki, munafuka maciya amana algunguma." Hafiz yana gama faɗa ya fita daga ɗakin, kai tsaye ya wuce ɗakin Bilkisu. Yana shiga ya zauna a kan kujera, ya zabga uban tagumi. Bai yi aune ba sai ji ya yi hawaye yana zuba, Bilkisu ta saci kallonsa sannan ta ce. "Abban Sayyid lafiya kuwa? Allah sa dai ba daga gida ba ne wani abu ya faru." Girgiza mata kai ya yi, muryarsa tana rawa ya ce. "Bilkisu me na rage ku da shi a cikin gidan nan? Mene ne nake tauye muku wanda ba na wadatar da ku da shi?" Bilkisu ta saki cokalin hannunta ta ce. "Wallahi babu komai Abban Sayyid, na rantse da Allah kafin a samu mijin nunawa kamar kai za a daɗe. Amma wani abu ne ya faru?" Girgiza mata kai ya yi ya ce, "Babu komai, wani abu ne kawai yake damuna." Shiru ta yi tana jin ɗaci a ranta, don ko kaɗan ba wannan hukuncin ta so ba. Suna nan zaune jigum-jigum, Amina ta shiga ɗakin cikin kuka ta ce. "Don Allah ka saurare ni Hafiz wallahi tallahi ban san komai a kai ba." "Amina kada ki sa na yanke hukuncin da ban yi niyya ba a kanki, ki fita ki ba ni wuri tun ranki bai ɓaci ba." Hafiz ya furta rai a ɓace. Ganin ya kuma harzuƙa ya sa ta ja ƙafa a sanyaye ta fita, da sauri Bilkisu ta ba ta ta ce. "Auntyn yara ni fa kun bar ni a cikin ruɗani, don Allah me yake faruwa." Amina ta fashe da kuka, sannan ta zayyane mata duk abin da ya faru. Da sauri Bilkisu ya ta shiga ɗaki wurin Hafiz ta ce, "Abban Sayyid don Allah..." "Bilkisu ba na son hayaniya don Allah." Hafiz ya dakatar da ita a fusace. Tun daga wannan ranar Hafiz da Amina suka shiga wani irin zama marar daɗi, tun yana fushi da Bilkisu a kan maganar da ta so yi masa har ya sauko. Sai dai kuma tsakaninsa da Amina ko gaisuwarta ba ya amsawa, idan ya kwana a ɗakinta ma sai dai ya ɗauki fulo ya fito falo. Idan yana ɗakin Bilkisu kuwa, haka za ta dinga jiyo hira da shewarsu. Kusan kullum Amina a cikin kuka take, sai dai lokaci-lokaci Bikisu tana zama ta yi ta tausarta tana ba ta baki a kan zamanta da Hafiz. Ana cikin haka, har watarana Amina ta tashi da ciwon naƙuɗa, a lokacin da ciwon ya tashi Hafiz ba ya nan. Don haka Bilkisu ce ta yi uwa da makarɓiya ta kai ta asibiti, sai da suka je ta kira Hafiz ta sanar da shi ta kuma kira 'yan'uwan Amina. Duk kusan lokaci ɗaya suka ƙaraso, da zuwansu babu jimawa nurses suka fito suka sanar da ta haifi jaririnta namiji. Har a ransa Hafiz ya ji daɗi, kuma ya nuna farincikinsa. Haka dangin Amina sai farinciki suke yi, ban Bilkisu da take sakin murmushin yaƙe. Don ji ta yi gabaɗaya ranta ya ɓaci, saboda ba ta taɓa tsanmanin Amina za ta haifi namiji ba. Bayan da aka gama gyara Amina da jaririnta ne aka ba su damar shiga, jaririnta ƙato tubarkallah. Kuma kallo ɗaya za ka yi masa ka ga tsananin kamar da yake yi da mahaifinsa, don haka Bilkisu kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kanta tana jin wani abu ya tokare ƙirjinta. Sai washegari aka sallami Amina, kuma a nan danginta suka ce za su tafi da ita gida ta yi wanka a can. Hafiz bai hana ba, don har a ransa dama ba ya jin zai iya cigaba da zama da ita. Ita kanta Bilkisu ba ƙaramin daɗi ta ji ba, don ta ci alwashin cimma manufarta kafin Amina ta yi arba'in. Hafiz ya haɗa mata kayan barka masu yawa gwargwadon ikonsa, bayan ya kai mata ita ma Bilkisu ta sayi atamfa da kayan jarirai kala biyu ta kai mata. Dangin Amina sun saki jiki da Bilkisu sosai, saboda yadda Amina take ba su labarin daddaɗan zaman da suke yi, musamman yadda suka ga ta yi hidima da Amina a lokacin haihuwarta. Ranar suna Hafiz ya raɗa wa jariri suna Muhammad, sai dai har kawo wannan lokacin babu wata kyakkyawar alaƙa a tsakaninsa da Amina. Ita ma kuma sai ta yi kamar ta sanarwa da 'yan uwanta sai ta haƙura, don gani take za su iya shawo kan matsalar daga baya. Tun safe gidan su Amina ya cika maƙil da dangi, 'yan'uwa da abokan arziki. Zuwa azahar aka cigaba da shagalin suna, mutane har maƙota saboda yadda aka cika. Haka Bilkisu ma da maƙotanta suka yi zuga cikin adaidaita sahu biyu suka je suna, daga ɓangaren 'yan uwan Hafiz ma duk sun yi kara sun kuma haɗa sha tara ta arziki. Wata baƙar mata ce a shekaru za ta yi arba'in, sanye da ƙaton hijabi ta shiga cikin gidan sunan. Tun daga soron gidan da fara faram-faram tare da haba-haba da mutane, aka dinga gaisawa da ita cikin karamci da mutumta juna. Har ɗaki ta shiga suka gaisa da Amina, ta shiga yi mata barka tana ta yaba kyawun da Amina ta yi. Amina ba ta san matar ba, sai ta yi tsammanin ko a abokan arzikin da iyaye ko 'yan'uwa suke mu'amala da ita ce. Suna nan zaune ƙawayen mahaifiyarta na makaranta suka shigo su da yawansu, gefe ta matsa suka shigo aka gaisa. Ta miƙa musu jaririn aka cigaba da hira, bayan ɗan wani lokaci Amina ce ta shiga banɗaki don ta gyara jikinta. A nan suka miƙe suka yi sallama suka fito tsakar gida, matar suka miƙawa jaririn. Don a tsammaninsu 'yar'uwar su Amina ce, kafin su gama rurumar saka takalmi cikin sauri matar ta saɓa jaririn abaya. Ta goya shi ta saki jihabin jikinta, tana ganin sun yi hanyar waje ita ma ta zura takalminta ta fice daga gidan. Sai da ta ƙarasa can titi, sannan ta samu mai mashin ɗin da suke tare. Da sauri ta haye suka bar unguwar, sai da suka yi nisa sosai. Sannan ta zaro wayarta ta kira layin Bilkisu ta sanar da ita unguwar da ta dosa. Shin mene ne dalilin Bilkisu da ta sa aka sace ɗan Amina? Kuma ina za a kai shi, me za a yi masa? Ya ya Amina za ta yi? Kuma wa zai wanke ta a wurin Hafiz idan wannan maganar ta fita? Idan Hafiz ya ji an ɗauke ɗansa wanne mataki zai ɗauka? Kada ku manta maza ba su da uzuri a kam yara ko kaɗan. Mene ne harsashenku game da ƙullin da Shukura ta ajiye? Shin za ta yi galaba a kan Mommy ko yaya? Shukura ta kwantar da kanta a wurin Mommy da dangin Alhaji, shin ita da Inna haƙarsu za ta cimma ruwa ko a wannan karon ba za ta yi galaba ba? To jama'a waɗannan amsoshin suna cikin littafi na biyu.🥱 ALHAMDULILLAH a nan na kawo ƙarshen littafi na ɗaya, mai son cigaba zai biya ta wancan asusun. Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa document 800 ne. Ummou Aslam Bint Adam🌚 [04/02, 14:12] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. TSOKACI: Labarin ya faru a gaske, sai kwaskwarima da na yi masa. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA ƊAYA Gumi ne yake keto mata ta ko ina, saboda yanayin tsananin zafin garin da ake busawa. Sai dai zafin da take ji bai kai rabin wanda yake ɗamfare a birnin zuciyarta ba, duba da zafi, zugi da raɗaɗin da ke kwance kane-kane a cikin ranta. Wanda a kullum cigaban da yake samu, shi yake kuma dakusar da ƙwarin gwiwarta. "Fauziya! Ke Fauziya, ki fito ki rufe mana gida. Kin san dai gidan matan aure ne, za ki bar mu a yashe salon wani ƙaton ya faɗo mana." Kiran mafarautar da A'ilo take yi mata, ya katse igiyar tunanin da ta zabarto ta ba tare da ta sani ba. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fita tsakar gida, tana shirin magana A'ilo ta sake katse ta. "Allah dai ya kusan raba yari da ɓarawo, don masifa a ce kullum sai ka kwanta a ishe ka da bige-bigen ƙofa. Haƙƙi dai na zaman maƙotaka, wallahi ana shiga haƙƙinmu. Baban Walid ya shigo tun ɗazu ki je ki rufe mana ƙofa. Idan mijin naki ya dawo, ki riƙe hannunsa ki kai shi har ɗaki. Don wallahi idan ƙaton mashayi ya sake faɗo mini ɗaki sai mun sheme shi." Ko kaɗan ba ta ji zafin maganganun A'ilo ba, domin kusan duk maganganunta a hanya suke. Don haka ta gagara furta koda kalma ɗaya, ta ƙarasa soron mai cike da duhu ta haska da 'yar ƙaramar wayarta ta rufe ƙofar. Sai da ta haska yaranta da ke kwance a ƙofar ɗaki, ta gyara musu kwanciya sannan ta koma ciki. Domin zafin da ake yi ne ya sa ta yi musu shimfiɗa a waje, kamar yadda ragowar matan gidan kowacce take yi wa 'ya'yanta shinfiɗa a ƙofar ɗaki. Idan dare ya tsala gari ya ɗan saki, sai kowacce ta mayar da yaranta ɗaki. A hankali ta zauna, bayan ta kashe fitilar wayarta ta latsa lambar mijinta Kabir. Sai dai tashin farko aka tabbatar mata wayar a kashe take, ta mayar da kallonta wurin agogon wayar ya nuna mata ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na dare. Gyangyaɗi take yi daga zauna, don haka ta kishingiɗa da gefen gadon. Don kada ta kwanta nannauyan bacci ya ɗauke ta, daga baya Kabir ya zo ya yi ta bugun ƙofa da ƙarfi yana ja mata zagi a wurin matan gida. Da yake baccin yana kanta, nan taka ya yi awon gaba da ita. "Wayyo Allah ƙafata! Mami ƙafata cinnaka ya cije ni." Kururwar Fatima ta katse mata daddaɗan baccin da ya yi awon gaba da ita, a gigice ta fita tsakar gidan ta shiga kiciniyar haskewa da hasken fitilar wayarta. Inun Fatima ya cika gidan, saboda azabar harbin kunamar da yake ratsa ta. "Mene ne Fatima? Me ya samu ƙafar ki?" Fauziya ta shiga jera mata tambayoyi tana haska ƙafar tata. Ba ta ga komai ba, sai dai wurin da Fatima ta riƙe ya yi wani irin ja. Da hannu ta janye ta gefe, sai kuwa ta ci karo da wata ƙatuwar baƙar kunama za ta gangara wurin da Na'ima take kwance. Da sauri ta suri wani takalmi da yake gefenta ta buga mata, nan take kunamar ta mutu. Fauziya ta sauke ajiyar zuciya, sai ta rasa taimakon da ake yi na gaggawa idan kunama ta harbi mutum. Ga Fatima da ke sakin kuka kamar za ta shiɗe, duk ta gama gigita ta. Hijabinta ta ɗauko, ta ɗauki Fatima mai kimanin shekara uku ta goya. Wani irin nauyi ta ji, saboda tsohon cikin jikinta da kuma goyon Fatima da ta yi. Kan mudubi ta fara dubawa saboda a nan take ajiyar kuɗi, amma ita kanta ba ta da tabbacin za ta samu kuɗi masu yawa. Naira ɗari biyu taci karo da ita, da sauri ta ɗauka ta fita tsakar gida, ta ƙarasa ƙofar ɗakin Lawisa tana yin sallama. "Salamu alaikum. Lawisa! Lawisa." Cikin bacci Lawisa ta amsa mata, Fauziya ta gyaya goyon Fatima ta ce. "Don Allah ko zan samu aron dubu ɗaya a wurinki? Zan leƙa na miƙa Fatima kemis, kunama ce ta harbe ta." "Subhanallah kunama fa? To bari na dubo miki, amma dai ba za a samu dubu ɗaya ba." Lawisa ta furta tana daga ɗaki. Fauziya tana nan tsaye, Lawisa ta ɗaga labule ta miƙe mata kuɗin hannunta, "Fauziya wallahi ɗari da hamsin kawai aka samu ga ta." Fauziya ta karɓa tana faɗin. "Don Allah zan tura ƙofar gida idan na fita, koda na dawo idan an rufe Lawisa. An ce ba a son barin harbin kunama da sai na bari zuwa safiya." Lawisa ta furta, "Shi kenan sai kin dawo, Allah dai ya tsare mu. Wallahi shi ya sa kullum na kwantar da su Siyama hankalina yana wurinsu, wannan zafi Allah Ya sa mu ga wucewarsa lafiya." Fauziya ta amsa sannan fita. Kemis ɗin da ke bayan layinsu ta zagaya, tun ba ta ƙarasa ba ta hango shagon a rufe. Ta kalli yagulallun canjin hannunta ɗari. 'Bayan kemis ɗin Bala ina zan kai Fatima?'' Fauziya ta raya a ranta, sai wani tunani ya faɗo mata. Da sauri ta sake ɗaga waya ta kira lambar Kabir, amma har lokacin a kashe take. Don haka ta yanke shawarar zuwa shagonsu, don ta fi tunanin ba shi da caji ne ya sa wayarsa take kashe. Bakin titi ta nufa, a lokacin babu mutane sosai sai tsirari da suke kai-komo. Zuciyarta a cunkushe take tafiya, saboda kukan da Fatima take rairawa ga ciwon ƙafafuwa da bayanta suke yi. Ta ɗan jima a bakin titi babu adaidaita sahu, har ta yanke shawarar fara tafiya da

Chapter 13 of 35