Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ne?" "Allah Ya taimake ka, abin da bawan Allahn nan ya faɗa fa haka ne. Ba aikin gona muka zo ba, kamar yadda ka faɗa..." Da sauri Mai gari ya katse Mahmud. "Kai yaro ka iya bakinka. Shin ya bari mun gama fesar da maganganun bakinmu ne? Ko numfashinmu ya tara? Abin da muke shirin faɗa kenan ya yi mana katsalandan, don haka dole a hukunta shi." Kallon tsaf Mahmud ya yi masa, yana jinjina ƙarfinsa. Bayan Mai gari ya sallame su, suna tafe a hanya ya ce. "Na lura da Mai garin nan tsaf, ashe duk burgagin banza yake yi. Ba abin da ya sani wallahi, kawai su yake naɗewa." Mudassir ya yi murmushi ya ce, "Ai kuwa sai dai su ya naɗe su, don idan ya shiga tawa gonar sai na yi masa naɗin da ya fi na huhun goro." Gabaɗaya suka saka dariya. Baba Sale shi da Uwale ba su suka dawo daga asibiti ba sai yamma liƙis, saboda bayan likita ya gwada Ɗan Bishir sai da aka ba shi gwaje-gwaje. Bayan sakamakon ya fito aka yi masa dressing, sannan aka rubuta musu magungunan. Duk soyayyar da Baba Sale yake yi masa haka ya danne shi da ana wanke masa, saboda likita ya tabbatar masa da matuƙar bai samu kyakkyawar kulawa ba komai zai iya faruwa, tun da har wurin ya fara ruwa yana ɗan wari. Likitan ya gargaɗe su sosai, wurin kula da tsaftar sabon gyambo koda ba na kaciya ba ne, sannan ya ce bayan kwana uku su koma a sake duba jikin nasa. Bayan sun koma gida, ko zama bai yi ba ya nufi gidan Bala wanzan. A ƙofar gida ya tsaya ya ce a yi masa sallama da shi, yana nan tsaye yaron ya dawo tare da wani ɗan matashin saurayi. "Kai Tasi'u, ina mahaifinka yake?" Baba Sale ya furta fuska babu walwala. Matashin da ba zai wuce shekara goma sha uku ba, ya rausayar da murya cike da neman tausasawa ya ce. "An tafi da Baba ofishin 'yan sanda ɗazu." Da sauri Baba Sale ya ce, "Ofishin 'yansanda fa? Me ya yi aka kai shi can?" "Ban san takamaiman abin da ya yi ba, amma an ce wai Idi Naira ya yi wa aska, kuma wai ana zargin yana da cutar ƙanjamau!" "La'ilaha'illa'illahu Muhammadur Rasulillahi, Sallallahu alaihi wasallam. Ɗan Tasi me kunnuwana suke zuƙo mini? Kada ka ce mini Ɗan Bishiriri ya kamu, wayyo Allah Tasi riƙe ni da ƙarfi duhu nake gani." Baba Sale ya yi maganar yana jin wata irin hajijiya tana yin ɗiban karan mahaukaciya da shi. Da sauri Tasi'u ya riƙe shi yana kiran sunansa da ƙarfi, "Baban Ɗan Bishir lafiya." A hankali Baba Sale ya ɗago duk da ba ya gane abin da Tasi'u yake faɗa sosai ya ce, "Tasi'u maza kai ni ofishin 'yansandan." Kamar sabon ɗan maye haka suka tafi Tasi'u yana riƙe da shi, don har suka ƙarasa wani irin layi yake yi idanunsa suna yi masa gizo. Su Baba Sale suna zuwa, suka samu Bala Wanzan a tsaye yana bayani. "Wallahi tallahi yallaɓai ban taɓa sanin Idi Naira yana da cutar abar nan ba, ni ko sunanta ba na son faɗa. Kuma babban tashin hankalina yaran da na yi wa shayi, a ranar da wannan tsautsayin ya afku. Domin su ne masu tasowa ba su mori ƙuruciya ba..." Wata irin ƙara suka ji gijiiiiiif Baba Sale ya faɗa ta saman kanta, saboda tun a bayanin farko da ya ji Bala wanzan yana yi, ya ji ƙafafuwansa ba za su iya ɗaukarsa ba. Kalaman Bala na ƙarshe suka sa ya ga wani baƙin duhu ta lulluɓe idonsa, numfashinsa ya ɗauke. "Subhnallah! Waye wannan? Lafiya?" Wani kurtun ɗansanda ya ƙarasa kansa yana tambaya. Tasi'u ne ya yi musu bayanin abin da ya faru tsakaninsa da Baba Sale, har zuwansu cikin station ɗin. Ruwa aka ɗebo aka zuba masa, a hankali ya farfaɗo yana daga kwance yake kallon mutane ɗaiɗai. Ya yunƙura a hankali ya zauna sai a lokacin komai ya shiga dawo masa. "Yallaɓai Ɗan Bishir, kun bincika mini Ɗan Bishiriri." Wani Sergent da ya fahimci Baba Sale, ya dubi Bala Wanzan ya ce, "Kai Wanzan ka yi wa yaron wannan mutumin kaciya ne?" Da yake a lokacin an mayar da Bala cikin cell, yana daga ciki ya ce. "Eh na yi masa yallaɓ..." Tun Bala bai gama magana ba Baba Sale ya sake sumewa a wurin, haka suka sake zuba masa ruwa ya sake farfaɗowa. Sai dai su kansu abin da ya fi ɗaga hankalinsu, yadda Baba Sale yana farfaɗowa zai sake suma. Har sun lura ko ya farfaɗo ba ya zama cikin hayyacinsa. Don haka suka tattarashi hankali a tashe suka yi asibiti da shi, sai bayan sun je suka saka Tasi'u ya yi musu rakiya har gida aka sanar da Uwale da su Baba Ibrahim halin da ake ciki. Tun da suka fito daga asibitin yake zabga sauri, cikin sassarfa ta rufa masa baya ganin ya fara yi mata nisa ya sa ta fara ƙwala masa kira. "Masoyi! Masoyi don Allah ka jira ni saurin me kake yi kamar za ka tashi sama." "Ya muke da jirgin sama? Na ce ya muke da shi?" Baba Labaran ya furta a zafafe. Sororo ta yi tana kallonsa don har tsoro-tsoro ta ji, ganin yana yi mata faɗan da ba ta saba gani a tattare da shi ba. Hasali ma ba ta ga abin faɗa a maganarta ba. "Asibiti na uku kenan a yau muna zuwa suna yi miki gwaji, amma duk maganarsu ɗaya kamar haɗin baki. To magana ta gaskiya na fi son mace a haihuwar fari, saboda magaji nake nema. Haka kawai duka asibitocin sun ce mace suka gani. Wallahi da sake an ba wa mai kaza kai." Da mamaki ta dube shi ta ce. "Da sake fa ka ce Masoyi? Shin butulci za ka yi wa uabangiji ne? Mutane nawa ne suke neman haihuwar ba su samu ba, mace ko namiji mai albarka ya kamata ka roƙa." Maimakon ya ba ta amsa sai kawai ya saki tsaki ya yi gaba yana faɗin. "Kanki ake ji, ni na gama faɗar ra'ayina." Daskarewa Rahinatu ta yi, ta ɗora hannunta a kan ƙaramin cikin jikinta da bai fi wata uku da satika ba. Cikin sanyin murya ta ce. "Dama duk soyayyar da mutumin nan yake yi mini ta fatar baki ce? Haƙiƙa Labaran ya cika butulu." Daga haka ta fara takawa a hankali, ta rufa masa baya tana jin zuciyarta na suya. Damuwa haɗe da tarin ayarin tunaninnika ne suka cunkushe masa kwanya, saboda Indo da su Hansatu sun nemi mayar da shi kamar mahaukaci. Don da sun kalle shi sai kowacce ta gimtse fuska, yana bada baya sai su kwashe da dariya. Rumfar Tsalha mai kayan miya nufa, yana zuwa ya yi sallama amma babu wanda ya amsa masa. Kamar haɗin baki, lokaci ɗaya mutanen cikin rumfar suka watse . Turus Yaya Inu ya yi, yana shirin magana ya ji Tsalha ya ce, "A gaskiya malam Inusa ka dakata da zuwa cikin rumfata, saboda ka da ka kawashe mini albarkar cinikayyata. Ba zan ɓoye maka Inusa ka san dai ni abokinka ne, maganar haihuwar zabiyar nan fa ya karaɗe ciki da wajen garin nan don haka ka yi hattara." Daga haka Malam Tsalha ya koma kujera ya zauna yana haɗe rai, don kada Yaya Inu ya samu fuskar zama. Kamar zakaran da aka tsamo daga cikin ruwa haka Yaya Inu ya fito ya nufi hanyar gida, tunanin Zuly matashin kai ce ta faɗo masa. Ya saki murmushi ya nufi ƙofar gidansu. Ƙaramar wayarsa ya ciro ya kira ta, ba a ɗauki lokaci ba ta fito tana taunar cingam. "Haskena ashe kaine da yamma haka?" Yaya Inu ya saki murmushi ya ce, "Takanas na shiryo na zo na ganki domin na huce takaicin zuciyata, saboda ke kaɗai ce hasken da ke yaye duhun da ke ɗanfare a ciki." Sai da ta hura kwai da cingam ta ce, "Wani zance nake ji yana tashi, wai an haifar maka zabiya 'yan gidanmu har sun fara bala'i. Ni kuwa na ce duk bala'insu ba zabiya ba, ko rabi mutum rabi aljan aka haifa maka babu wanda ya isa ya han ni aurenka." Farinciki ya sa ta Yaya Inu ya zaro rafa kuɗi har dubu goma ya miƙa mata. "Ki sha lemo da wannan, masoyiyata kuma hasken zuciyar Inusa." Alewa ta buɗe ta wurga a baki ta tsotsa, sannan ta zaro ta miƙa masa cike da kissa. Cikin so da ƙauna Yaya Inu ya karɓi alewar, ya jefa a baki ya yi mata sallama. Yana gab da shiga gida ya hango wani mai magani, yana tafe da wata ƙatuwar Mp3 da wani faffaɗan kwando mai ɗauke da magungunan maza a ciki. "Ina mai matsalar kuzari? Ina namijin da ya rako maza? To ya hanzarta ya zo ga adamalmala. Maganina rabo ne, maganina sa'a ce. Alhaji sai mai tsananin rabo ne zai dace na ba shi, ina mazan da basir ya jima da yi musu illa? Alhaji ba ka nisan zango wurin tuƙa sitiyarin mota? Don Allah ka zo, ga mai adamalmala ya dawo. Idan na bar garin nan ba zan dawo ba, maza kaɗai nake ba wa magungunana domin na fi kishinsu a kan mata. Alhaji ko Malam kada ka ji kunyar karɓa, indai matsalarka a ɓangare iyali ne ta kau. Sabon aure za ka yi ne? Ko kuwa ka rasa gane kan matanka ne? To maza gangaro ka karɓa sadakar ƙalilance, ni dai ba na rowa domin burina na kankaro mutumci a wurin maigida." Yaya Inu ya tsaya a jikin bishiya ya yafito shi da hannu, Mai maganin ya ƙarasa wurinsa adaidai lokacin Na Balaraba ya ƙarasa ta wurin zai wuce. "Kai wa nake gani kamar Gambo, ko idanuna ne?" Cewar Gambo. Mai maganin ya ɗago yana kallon Na Balaraba da sauri ya ce, "Kai! Wa nake gani kamar Na Balaraba? Dama rai kan ga rai?" Yaya Inu ya washe baki, "Na Balaraba ka san shi ne?" Na Balaraba ya furta, "Na san shi farin sani, yanzu ne dai zumunci ya zama yanda ya zama, shekara biyar zuwa shida rabona da shi." Yaya Inu ya washe baki ya ce, "Ka ce faɗuwa ta yi daidai da zama, dama kiransa na yi zan sayi magani." Mutumin tun da ya yi tsaye yake ƙarewa Yaya Inu kallo, har sai da gabansa ya faɗi. Amma jin Na Balaraba ya ce ya san shi ya sa ya saki jikinsa. "Haba ba ka da damuwa Inusa, ka sayi maganinka wannan da kake gani ba na shakku a kansa." Yaya Inu ya nuna wani magani ya ce yana son saya, Mai maganin ya yi zaraf ya ce. "A'a mai gida bari na ba ka wannan, ai wannan shi ne gagara-badau an buga da kai an barka." Ya ƙarasa maganar yana miƙa masa wata roba ƙarama ya ɗora da cewa. "Yanzu kana komawa gida tun da magariba ta ƙarato ka shafa shi, sai bayan minti talatin ka wanke da ruwan ɗumi. Ka zuba wa sarautar Allah ido za ka ba ni labari idan na sake dawowa." Jiki yana rawa Yaya Inu ya zaro kuɗi ya biya. Bayan Mai maganin ya tafi Baba Ado da yake gefe ya ce masa. "Yanzu Allah Yaya, ba za ka raba kanka da gabzawa kanka waɗannan magungunan barkatai ba? Haka kawai maganin kare da doki kowa na ka ne, ba ka duba inganci ko ka je wurin masu magungunan gargajiya waɗanda suka san kansu ka saya..." A sheƙe Yaya Inu ya katse shi. "Kai dakata kada ka yi mini rashin kunya, tuzurun banza da wofi. Wai har da su kaza a cin danƙo? Kai da ko arzikin auren ba ka samu ba, shi ne har za ka zauna kana yi mini fi'ili? Tun da kai 'yan mata aljanu sun gama tsuƙe jijiyoyin jikinka, ai sai ka bar masu raya sunnar Annabi su yi. Da uwar kuɗina nake saya babu wani ƙato da yake saya mini, don haka kada ka sake shiga hurumina." Yaya Inu yana gama magana ya shige gida a fusace. Yana zuwa ɗakinsa bayan ya huta ya shafa man kamar yadda Mai maganin ya faɗa masa, bayan kamar minti biyar da shafa man ya ji wani irin zafi yana ratsa shi. A ɓangare ɗaya kuma ya fara jin kamar ana tsoma wurin a ruwan zafi, ba shiri ya tashi ya rage dogon wandon jikinsa. Ya ɗauki muhuci yake firfita, jin azabar ta yi yawa ya sa yaYaya Inu ya faɗa banɗaki a guje har yana ɓari da kwanuka. Ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi, bayan ya shafo jikinsa ya ji tamkar ba na shi ba. Yaya Inu yana kai kallonsa, ganin sauyin hallitarsa ya sa wani wawan kuka ya kwace masa. Saura na ji wani ya yi wa Yaya Inu dariya.😂 Littafin kuɗi ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [05/01, 19:31] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻 SHAFI NA SHA BIYU Indo tana daga bakin murhu ta fara jiyo numfarfashin Yaya Inu da shasshekar kukansa, da farko ba ta yi tsammanin shi ba ne. Saboda hayaniyar yaran da ke kai-kawo a cikin gidan, sai da ta kasa kunne sosai sannan ta fahimci kukan babba ne. Mamaki ne ya kama ta, don su Hansatu gabaɗaya suna nan ballantana ta ce wata daga cikinsu ce. Miƙewa ta yi ta nufi hanyar banɗakin tana zuwa ta ji yana faɗin. "Kaico wannan wanne irin tsinanna magani da mai maganin ne? Ai kuwa ni da magani irin wannan har abada." Sai ya sake ɓarkewa da kuka. Ƙirjin Indo ya buga da ƙarfi, ta ɗan buga ƙofar banɗakin ta ce. "Mai gida lafiya kuwa? Me yake faruwa?" Daga can cikin banɗakin Yaya Inu ya ja majina ya ce, "Shigo ciki Indo." "Cikin banɗaki fa Mai gida?" Ta tambaya da mamaki. Yaya Inu bai sake tanka mata ba saboda yadda abin duniya ya dame shi, tambayar Indo ma haushi ta ba shi, don haka ya ja baki ya tsuke. Jin Yaya Inu ya yi mata shiru, ya sa Indo ta faɗa banɗakin gabanta yana faɗuwa musamman da ta tuna bai taɓa yin haka ba, kada ko wani abin ne ya same shi a ɓanɗakin ba ta sani ba. "Mai gida lafiya kake kuka a banɗaki?" Indo ta yi maganar bayan ta samu Yaya Inu har lokacin a tsugunne. "Indo na haɗu da wani iftila'i, wallahi ina cikin tashin hankali komai ya canza mini, al'amarin ya munana." Muryar Yaya Inu kaɗai da ta ji ce ta tabbatar mata da tabbas babu lafiya, ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Me ya faru dai yanzu?" Yaya Inu ya zauna a kan wani ɗan dandamali da suke zama su yi wanka, ya dubi Indo da shanyayyun idanunsa da suka yi mitsi-mitsi saboda kukan da ya sha ya ce. "Ku je ku kori yara ɗaki, ki kira mini su Hansatu ku mayar da ni ɗakina. Saboda su kansu jijiyoyin ƙafafuwana sun yi sanyi, ji nake kamar da na wani aka zuba mini ba nawa ba." Jin haka ya sake ɗaga hankalin Indo, ta ja ƙafafuwa jiki a sanyaye ta samu Hansatu da ke ɗinkin mahuci ta furta. "Mai gida fa babu lafiya Hansatu." Da yake har lokacin Hansatu cike take da haushin Yaya Inu, kai tsaye ta ce. "Allah Ya sawaƙe, kowa ma fama yaka da rashin lafiya." "Wannan fa ba irin rashin lafiyar yau da gobe ba ce, don ya ce a tura yara ɗaki mu je mu ɗauke shi mu mayar da shi ɗakinsa." Furucin Indo ya sa Hansatu zaro ido, a razane ta ce. "Shi Mai gidan za mu ɗauka mu kai ɗaki? Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!" Da sauri Hansatu ta miƙe, kowacce ta shiga ƙoƙarin tura yaranta ɗaki. Kafin wani lokaci tuni yaran sun shige ciki, Hansatu ce a kan gaba sauran suna biye da ita. A inda Indo ta bar Yaya Inu, a can suka koma suka same shi. Yana zaune ya haɗa kai da gwiwa. Abin da ya sake ɗaga hankalin matan nasa, ganin hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarsa yana ambaliya. "Mai gida! Wai me yake faruwa haka?" Hansatu ta jefa masa tambaya a rikice, Yaya Inu da muryarsa ta shaƙe can ciki ya ce. "Ku yi tara-tara ku kai ni ɗaki. " Da yake Yaya Inu ba mutum ne mai ƙiba ba, ya sa su ukun suka haɗu suka ɗaga shii suka yi ɗaki da shi suka kwantar a katifa. Zani suka janyo suka rufe masa jikinsa, suka yi carko-carko kowacce tana saƙa da warwara a cikin ranta. "Ɗazu gabanin zan shigo gida na haɗu da wani matsiyacin mai magani, bayan na saya ya ce mini na shafawa ne. Ina shafawa kun ga abin da ya faru!" Yaya Inu ya ƙarasa maganar yana bankaɗe zanin rufar da suka rufa masa, wannan karon hankalinsa ya fi tashi don ya lura da ci bayan da yake ta samu a jikinsa. "Innalillahi! Malam mene ne haka a tsotse kamar hanjin ligidi? Wannan wane irin magani ne haka ka shafa?" Hansatu ta faɗa a ruɗe. Indo ta jinjina kai ta ce, "Gaskiya wannan abin akwai ayar tambaya, amma babu lambar waya a jiki da sai ka kira shi." Yaya Inu ya yi zaraf ya ciro robar maganin, cikin sa'a ya ci karo da lambar mai maganin. Yana kira bugu biyu ta yi ya ɗauka, nan take ya zayyane masa duk abin da ya faru. Daga can ɓangaren ya ce. "Allah sarki Mai gida, na manta ai tun farko ban yi maka wannan bayanin ba. Amma kada ka damu wannan ba komai ba ne, dama a rana ta farko dole za ka fuskanci haka. Amma zuwa gobe war haka komai zai dawo daidai." Yaya Inu da kamar zai yi kuka ya ce. "Yanzu har sai na kai gobe war haka? Yanzu fa ƙarfe takwas na dare, haka zan yi ta zama a zuƙe?" "Wannan ba wani abu ba ne, idan har maganin ya game duk jikinka, muna nan da kai sai ka nemo ni ka kawo mini kwastoma saboda kyawunsa." Kalaman mai maganin kenan da suka ɗan ƙara wa Yaya Inu ƙwarin giwa. Larai da ke riƙe da haɓa ta jinjina kai ta ce, "Magana ta gaskiya Mai gida lamarin nan fa ya ba ni mamaki, ba yau ka fara amfani da irin wannan maganin ba fa. Wallahi akwai dai magana, ka tuhumi tsakaninka da Ubangiji gaskiya." Yaya Inu ya zaburo ya ce, "Ke Larai me kike nufi?" Larai ta murguɗe baki gefe ta yi ƙasa da murya ta ce, "A'a toh, ga dai abu ya bayyana nan tun da har ka haifo zabiya. Ƙila fushin da Allah Yake yi da kai ne ya jarabce ka ta wurin, ba sai a ga ta saɓon Allah ba. Tun da Ubangiji da kansa Ya yi hani da kusantar mace tana cikin jini..." "Na rantse da Allah zancanki yana hanya Larai, kai duniya jama'a akwai darussa a rayuwar nan fa." Indo ta furta tana jinjina buwayar Ubangiji. Kalaman su Larai ba ƙaramin ɗaga hankalin Yaya Inu ya yi ba, yana daga kwance ya tashi zaune ƙirjinsa yana bugawa ya ce. "Na rantse da girman Allah ban taɓa aikatawa ba, Allah ne shaidata. Na shiga uku Hansatu ku taimaka mini, wallahi ina cikin wani yanayi." Larai ta yi hanyar waje ta ce, "Wallahi Mai gida ni kam a yanzu ma tsoron taɓa ka nake yi, kada na je ni ma wata hallitar tawa ta tsotse." Daga haka ta yi ficewarta. Kuka Yaya Inu yake iya ƙarfinsa, ya janyo zanin Hansatu yana ɗago mata hannu. Ba ƙaramin tausayi ya ba ta ba, saboda duk abin da zai saka Yaya Inu kuka ba ƙaramin tashin hankali ba ne. A sanyaye Hansatu ta zauna ta ce, "Mai gida! Yanzu mene ne abin yi?" Yaya Inu ya wara mata hannu alamar ba shi da mafita ya furta, "Sai abin da kika ce Hansatu." Indo ta gimtse dariya ta yi ficewarta, don ita ma a wani ɓangaren ya fara ba ta tsoro. "A'a kai ne mai faɗa aji ai, tun da kai rana ta ƙwacewa. Laifi dai ka riga da ka aikata, kawai dai ka yi ta isgifari. Sannan sai mu zuba wa sarautar Allah ido, zuwa washegari kamar yadda Mai maganin ya faɗa." Wata sabuwar soyayyar Hansatu ta mamaye shi, ya riƙo hannunta ya ce. "Hansatu dama haka kike sona, ke kaɗai ce ba ki guje ni ba a cikinsu." Hansatu ta yi wa Yaya Inu ƙuri da ido, tana tuna soyayyarsu tun ta saurayi da budurwa. Sannan ta tuna irin cin kashin da yake yi musu, musamman na ranar ta ce. "Ai wannan kalaman da kake faɗa na fatar baki ne ranka shi daɗe, mu da ka ce fuskokinmu kamar na sumammun birarrika? A'a za ka yi aure ai, ni ma abin da ya sa ka ga na tsaya a kanka, ina duba darajar da ka ba ni a cikin matanka da ba ka taɓa sakina ba. Tun da ni ma ka mutumta ni a matsayina na uwar gida." Shiru Yaya Inu ya yi kunya ta lulluɓe shi, Hansatu ta cigaba ɗebe masa kewa sai da ta fara jin bacci sannan ta wuce ɗakinta. Dai-dai da abincin dare Yaya Inu da ƙyar ya iya ci, haka ya kwana cikin tunani da bacci mara daɗi yana miyagun mafarkai kala-kala. Lokacin da su Uwale suka samu labarin abin da ya faru ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, abin sai ya haɗe mata goma da ashirin ga halin da Ɗan Bishir yake ciki, da zargin da ake yi ya kwashi cuta mai karya garkuwar jiki ga kuma halin da mijinta yake ciki. Da yake dawowar Baba Ibrahim kenan daga wurin aiki, ko gidan bai shiga ba ya ce wa Uwale ta koma shi zai je ya ji abin da yake faruwa. Kai tsaye ƙaramin asibitin gwamnati ƙauyen nasu ya wuce, a can ya samu Baba Sale ana yi masa ƙarin ruwa . Da yake an yi masa allurar bacci sai ya zauna a gefensa yana jiran tashinsa. Kusan zaman awa guda Baba Ibrahim ya yi, sannan Baba Sale ya buɗe idonsa. "Sannu Sale, ya jikin naka?" Baba Sale ya tashi zaune yana dafe kansa da ya yi masa nauyi, ya dubi Baba Ibrahim murya tana rawa ya ce. "Yaya ka ji abin da ya faru ko?" Ya gyaɗa masa kai ya ce, "Sale ina son ka saurare ni da kyau don Allah. Na farko dai kai musulmi ne, ka yarda da ƙaddara mai kyau da

Chapter 33 of 35