Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
lokacin da ya je ta idar da raka'a ta biyu. Cike da borin kunya ya riƙo hannunta ya ce. "Ai ɗazu da kika ganmu ruwa na watsa saboda zafi, kin san garin kwana biyu..." "Ban tambaye ka ba Daddyn Mami. Ko wuta ka watsa wannan ba damuwata ba ce tun da kai da iyalinka ne, wannan sirrinku ne ba sai ka tona ba." Hajiya Karima ta katse shi cikin ɓacin rai, ganin yanayin da take ciki ya sa shi kama kansa. Ta sake tayar da sallah yana nan zaune duk jikinsa a sanyaye. Har gari ya waye Hajiya Karima ba ta ba wa Daddy fuska ba, shi ma ganin haka ya sa ya fara nan-nan da ita, bini-bini sai ya tambaye ta ko tana son wani abu. A kwana na biyun Hajiya Karima Shukura ba ta yi komai ba, lafiya ƙalau suka kwanta har Daddy ya koma ɗakinta. Sannu a hankali zamansu ya cigaba da tafiya, sai dai kusan kullum Mommy danne zuciyarta take yi. A ɓangare ɗaya kuma tana ƙara dannar Ruƙayya, don sautari ta sha cewa za ta tare da a kan wasu abubuwan da take yi a gidan ta mata magana. Amma sanin Shukura irin matan nan masu sharri ne ya sa take haƙurƙurtar da ita. Duk da an raba girki, amma wani lokacin Shukura tana sani sai ta ce wa Daddy ba ta yi girki ba na Hajiya Karima za ta ci. Haka zai je har ɗaki ya saka Ruƙayya ta zuba mata, kuma duk wannan abin da take yi Mommy ba ta taɓa tanka mata ba. Da ta lura da hakan ba zai kawo fitin ba, sai ta tsiri duk ranar girkinta za ta kira Daddy ta ce masa ba ta da lafiya, ko kuma ta ƙirƙiro wani abin da ba za ta yi girki ba. Idan ya ce zai taho mata da abinci sai ta ce masa ya kira Ruƙayya ya saka ta girka mata, tun Ruƙayya tana yin kara har haƙurinta ya fara ƙarewa. Ana cikin haka watarana Shukura ta yi wa Daddy waya, ta ce za ta yi baƙi kuma a ƙaryarta ta ce masa ba ta jin daɗi. Ruƙayya tana tsaka da typing ɗin assignment a laptop ɗinta, Daddy ya kira ta ya ce ya ta je ta karɓi ATM ɗin Shukura za ta yo cefane ta mata girkin baƙi. A ranar cike da ƙosawa ta ce. "Yanzu Daddy saboda Allah matar nan kullum lafiyarta ƙalau sai ta dinga ce maka ba ta lafiya, gaskiya Daddy ni na gaji." Daga can ɓangaren Daddy ya ce. "Mamana kina son na saɓa miki ko? Idan mahaifiyarki ce ta saka ki za ki faɗi haka? Daga yau idan na sake jin ta saka ki abu kin yi mata musu wallahi ranki zai ɓaci." Tana jin Daddy yana mata faɗa ta fara hawaye, ba don ta so ba ta je ta karɓa cike da raini Shukura ta faɗa mata duk abin da za a saya. Ana cikin wannan yanayin Shukura ta fara laulayi, sai ta fara tsiro musu da tsirfa kala-kala. Watana rana Daddy yana dawowa da yake a ɗakinta yake, sai kawai ta fashe da kuka. A rikice ya riƙo ta ya ce. "Me aka yi miki Shukura?" Shukura ta share hawayen idonta ta ce, "Waɗancan kajin da Hajiya ta zuba wallahi cutata suke yi, kullum sai na yi amai ya fi sau biyar saboda warin kashinsu har nan yake zuwa. Kuma idan ina aman ji nake kamar ɗan cikina zai zube, gaskiya ni dai ka saka ta fita da su wallahi." Hankalin Daddy ne ya tashi da jin furucinta, sai kuma ya yi shiru yana nazari saboda Mommyn Mami ta kusa shekara goma tana sana'ar kiwon kaji, kusan duk shekara sai ta zuba na sallah ƙarama, sallah babba da na maulidi. Kwantar da kai Daddy ya yi ya ce. "Ai na ga a bayan gida suke Shukura, kuma duka kajin yanzu ko wata ɗaya ba su yi ba. Ga shi kin ga da yawa ta zuba su, a ƙalla za su kai guda ɗari ko fi ma. Zan sayo miki turarurruka..." "Ka san dai ba na son ƙamshin turare tun da na samu ciki, wallahi ni dai idan ba za ta fita da su ba sai dai na bar maka gidanka ka sake ni. Dama ai ka fi sonta da ni, tun da ita ce uwar 'ya'yanka. Wa ya sani ma ko dama cikin jikin nawa ne ba ka so." A rikice Daddy ya ce. "Ba zan iya rabuwa da ke ba Shukura, bari na je na same ta." Daddy ya furta yana fita da sauri, Shukura ta faɗa kan gado tana sakin dariyar ƙeta. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. *ADVERT* Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buɗe a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!😍 ‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah! MG’s Beauty Lounge ya buɗe da kwalliya, tsafta da ƙamshi irin na sarauniyar zamani! Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu: Gyaran gashi da kitson zamani Kwalliyar Sallah mai ɗaukar ido Wanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya rai Kayan gyaran fata na gaske Lalle mai kyau da salo na zamani Tura-turai, humra, incense da ƙamshi masu daɗi Shirin amare da na musamman Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya. Zo ki ji daɗin wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai kyau. Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna. Tambaya/Booking: WhatsApp: 08062991549 Kira: 09016108092 / 08064532391 Ki zo ki gani da idonki – ki ji daɗin sauyin MG’s Beauty Lounge. Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge SHAFI NA SHIDA A lokacin da Alhaji ya shiga ɗakin Mommy tana zaune tana waya, gani ya yi ta yi rubutu a cikin littafin da take lissafi da shi. "Eh rannan an kawo mini buhun dusa ashirin, wancan lissafin ai mun gama da shi. So nake a ƙaro mini buhu biyar, yanzu nawa zan ciko kuma?" Amsa aka ba ta daga can ɓangaren sannan ta ce. "To shi kenan, zan turo da kuɗin." Mommy ta ƙarasa maganar ta kashe wayar, jikin Alhaji ne ya yi sanyi. Duk sai ya ji fargaba ta cika shi, Hajiya tana ɗagowa ta sakar masa murmushi ta ce. "Daddyn Mami ka shigo ina waya, wallahi lissafi muke da Halliru mai kaji. Ina tunanin ma zan ƙaro guda ashirin fa, saboda Ɗan Fulani suya sport ya ce yana kamun guda tamanin." Murmushin yaƙe ya yi ya ce, "Eh haka ne, dama zuwa na yi mu yi wata magana a kansu." Amsa masa ta yi Alhaji ya zauna ya yi shiru, kallonsa ta yi ta ce. "Ina jinka Alhaji." Shiru ya sake yi gabansa yana faɗuwa ya ce, "To dama... game da kiwon kajin nan ne... to kin san Shukura ciki gare ta, shi ne..." "Shi ne me?" Mommy ta katse shi da sauri, saboda ta fahimci akwai abin da yake tafe da shi. Abba ya ce. "Wai warinsu yana damunta, har tana jin kamar za ta yi ɓari idan tana amai." Wani kallo Mommy ta yi masa, wanda hakan ne ya sa shi yin shiru da bakinsa. A ƙufule ta ce. "To yanzu me ta aiko ka a yi?" "Nake ganin tun da sun kwana biyu, me zai hana ki fitar da su ai za a samu masu saye. Ko ni ina da mutanen da za su saya, saboda kin san me laulayi. Idan ya so bayan ta haihu..." "Alhaji!" Hajiya ta kira shi sunansa cikin ɓacin rai, a sanyaye ya ɗago ya ce. "Ina jin ki." Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Tun da nake da kai, ba na ja'inja a kan maganar da ka faɗa. Amma ka sani a wannan karon ba zan amince da maganarka ba. Ka sani na kai shekara goma ina sana'ar kiwon kaji, tun ina kiwo da kaji biyar har Allah ya sa na ci gaba. Amma yanzu rana tsaka ka zo ka ce wai matarka ba ta son warin ka ji, kajin da suke can bayan gida sune warinsu har..." "Kina nufin ban isa da gidana ba kenan? Ko kina nufin kin fi ni iko da gidana?" Alhaji ya katse ta. Girgiza kai ta yi ta ce. "Ba haka nake nufi ba, amma wallahi a wannan karon sai dai ka yi haƙuri." Cikin zafin rai Alhaji ya ce. "To na dakatar da kiwon na ki ma gabaɗaya, saboda kawai na ce ki bari har zuwa lokacin da za ta haihu shi ne za ki faɗa mini magana." Baki sake Mommy take kallon Alhaji, ya miƙe ya nufi hanyar fita sannan ya waigo ya ce. "Zuwa nan da gobe akwai mutanen da za su yi miki maganar kajin, idan kuma ba haka ba ni da kaina zan sa a fitar da su." Har ya saka ƙafa zai fita Hajiya ta bi bayansa da sauri ta ce. "Ina mai tabbatar maka idan ka fitar mini da kaji wallahi-wallahi sai dai ka zauna da Shukura a gidah nan ba ni ba." Cak! Daddy ya tsaya, rai a ɓace ya waigo ya ce. "Wato kaji sun fi maganata kenan? Me kike nufi?" "Ina nufin zan bar gidanka?" Ita ma ta ba shi amsa kai tsaye. "Saboda kina baƙinciki da abin da za ta haifa? Yanzu dama akwai ranar da za ki ƙi jinina Karima? Saboda kawai na ce ki yi haƙuri zuwa wani lokaci za ki faɗi haka? Wato kin fi son ta yi ɓarin cikin kenan?" Ahaji Ya furta, Mommy da ranta ya gama ɓaci ta ce. "Idan duniya Shukura za ta haifa maka wallahi ba na baƙinciki ko ƙyashi, saboda na san na wuce ta har abada ni da 'ya'yana ne a gaba. Amma wallahi ba zan ɗauki kowanne irin cin kashi da yarinyar nan za ta yi mini ba." Kamar Alhaji zai yi magana sai kuma ya fice daga cikin ɗakin zuciyarsa tana suya. Can ɗakin Shukura ya shiga, tana ganinsa ta tashi zaune ta ce. "Ya ake ciki ne?" Dafe kansa ya yi ya ce, "Wallahi ta ƙi amincewa, ni na rasa yaushe Hajiya ta fara musu da ni." Shukura tana jin haka ta fashe da kuka, cikin tashin hankali ya riƙo ta ya ce. "Don Allah kada ki ɗaga hankalinki, wannan ba abin damuwa ba ne. Wallahi na yi bakin ƙoƙari don ta amince amma fir ta ƙi amincewa. Har tana ce mini za ta bar gidan nan idan aka fitar mata da kaji." Da sauri Shukura ta ɗago ta ce. "To sai me? Ba sai ka sake ta ba tun da ba za ta bi umarninka ba. Daɗin abin ai ba ita kaɗai ce matarka ba." Da wani irin sauri Alhaji ya fisge jikinsa daga jikin na Shukura, har sai da ta tsora ta. Rai a ɓace ya nuna ta ya ce. "Ko a mafarki kada ki sake tunanin zan iya rabuwa da Hajiya Karima, wannan matar da kike gani ita ce komai nawa. Kuma ban auro ki saboda na daina sonta ba, ina son matata domin ita ce rufin asirina. Duk wani mataki da kika ga na kai, wallahi ta silarta ce." Alhaji ya gama faɗa ya fita daga ɗakin a zuciye. GIDAN HAFIZ Bayan Hafiz ya watsa ruwa, zama ya yi daga shi sai kayan shan iska.A gefen Amina ya zauna, ya fara bin ta da wani irin kallo. Murmushi ta sakar masa, ya shafo fuskarta ya ce. "Na yi kewarki Meena." Cikin zolaya ta ce, "Ba wani nan ni ban ga alama ba." Matse ta yi a jikinsa tsam, ta saki 'yar ƙara kaɗan lokaci ɗaya suka saki dariya. Janye jikinta ta yi ta ce. "Akwai tea akwai drink wanne za ka fara sha?" Lumshe ido Hafiz ya yi ya ce. "Da ke zan fara mana." A ɗan shagwaɓe Amina ta ce. "Habibi ka fiye wasa fa." Sauka ya yi ƙasa, Amina ta zuba masa ruwan shayi a kofi, ta buɗe fulas za ta zuba masa abinci, daga bakin ƙofa suka ji Bilkisu ta zuro kwano cike da abinci ta ce. "Idan har kin yi haka don ki kashe ni ko ki kashe 'ya'yana, In Shaa Allahu sai dai ki gani a kanki. Saboda kin ɗebi naki abincin da na Abban Sayyid shi ne mu za ki hala ka mu, ai shi kenan Allah Yana kallo." Daga haka Bilkisu ta bar wurin. Kallon juna Hafiz da Amina suka yi, a sanyaye ta miƙa hannu ta ɗauko kwanon tana kallonsa, sai dai ko kaɗan ba ta ga komai ba. Abu ɗaya ta ji shi ne wari-warin fetir, Hafiz ya ɗauki abincin ya shinshina ya ce. "Me kuma ya kawo warin fetir a abinci?" A sanyaye Amina ta ce. "Wallahi ban san yadda aka yi ba. Lafiya ƙalau na yi girki na gama." Ajiye kwanon ta yi, ta fara zubawa Hafiz shi ma. Yana matso da plate ɗin gabansa ya ji warin fetir ya doki hancinsa, da sauri ya ɗago ya ce. "Amina wai me yake faruwa ne? Wannan wanne irin wulaƙanci ne za ki saka mana fetir a cikin abinci? Ina ce galan ɗin fetir daban na mai ma daban?" Idanun Amina suka ciko da ƙwalla, ta saka hannu ta share hawaye murya tana rawa ta ce. "Wallahi ban san komai ba, lafiya ƙalau na gama girki." "Ƙafa gare shi man ko hannu da zai zuba kansa? Shi kenan sai ki san yadda za ki yi da shi." Hafiz ya furta cikin fushi sannan ya zura doguwar rigarsa ya fice. Bilkisu da ke ɗaki murmushin ƙeta ta saki, ta ɗauko waya ta kira shi tana ji ya ɗauka ta ce. "Abban Sayyid yanzu ya zan yi da yara? Ga shi suna kukan yunwa." "Ki dafa musu taliya mana." Hafiz ya faɗa a ɗan faɗace. Kwantar da murya Bilkisu ta yi ta ce, "Ai ina tsoron ko man ne yake da fetir kada na sake saka musu a koma 'yar gidan jiya." Shiru Hafiz ya yi sannan ya ce. "Ki fara dubawa kafin ki zuba, idan kin dafa kuma ki zuba mini ni ma a cooler ina dawowa." Daɗi ne ya cika Bilkisu, ta amsa masa sannan ta kashe wayar. Ummou Aslam Bint Adam🌚 07062062624 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA BAKWAI AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_ _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ *08089965176* *07084653262* *** Bilkisu drower kayanta ta buɗe, ta jima a tsaye tana nazarin waɗanda za ta ɗauka. Wata doguwar riga shara-shara ta ɗauko ta zura, ta shiga ɗakin yaran ta same su har sun fara bacci da yake an yi sallar Isha'i. Shimfiɗa ta yi musu ta ɗauko net ta saka musu, ta koma ɗaki sannan ta ɗauki ragowar taliyar da suka ci ita da yaran wacce ta zuba a cooler ta ajiye. Motsin Amina ta ji, don haka ta yi zaraf ta fito ta ɗauki buta ta yi kamar banɗaki za ta shiga. Amina ta gani ta fito da abincin ta saka a kicin, murmushin ƙeta Bilkisu ta yi ta shiga banɗaki bayan wani lokaci ta fito har za ta shiga ɗaki ta ja tsaki ta ce. "Aikin banza, haka kawai a jaza wa mutum ɗora girkin dare. Ai shi ma Abban Sayyid ɗin maganinsa kenan, kana tare da matarka cikin rufin asiri ka ci ba ka ci ba babu wanda ya sani. Amma haka kawai rana tsaka a ɗauko maka baƙar ƙaddara ta addabe ka, tun da nake a gidan nan 'ya'yana ba su taɓa kwanciya ba su ci abinci ba sai yanzu."Ta gama faɗar haka ta faɗa ɗaki. Amina da ke durƙushe tana juye abinci a tukunya ta share hawayen idonta, saboda ta yi tunanin duniya ba ta tuna a lokacin da ta zuba fetir a madadin mai a abinci ba. Kuma ko da ta gama girki ba ta ji warin komai ba, a sanyaye cikin damuwa ta koma ɗaki ta zauna. Waya ta ɗauka ta kira layin Hafiz ta ji bai ɗauka ba, abin duniya duk ya dame ta don bai taɓa yin fushi da ita irin haka ba. Bilkisu tana daga ɗaki wani tunani ne ya faɗo mata, da sauri ta ɗauki waya ta je bakin ƙofa yadda Amina za ta ji ta ce. "Hello Abban Sayyid, na ce ka haɗo mini da tsiren jiya da ka sayo mini. Amma dai yau kada a cika albasa, sai kuma su Sayyada yogot ɗin nan za ka taho musu da shi." Sai Bilkisu ta yi shiru kamar ana ba ta amsa sannan ta sake cewa. "A'a ba sai ka sayo mini kifi ba, kai dai ka sayo wanda za ka ci taliyar da shi." Ta sake yin shiru sai daga ƙarshe ta ce. "A'a ai abin da Amina ta yi maka bai kai ka ce za ka ƙauracewa kwanan ɗakinta ba. Ba a yi haka ba, gaskiya kada kasa ta ƙulla ce ni. Sai dai ka shigo kawai." Bilkisu ta lallaɓa ta koma kan kujera tana ƙunshe dariyar ƙeta, saboda ta san babu tantama Hafiz ba zai shigo ba sai da kifi. Ɗabi'arsa ce indai ta yi shinkafa ko taliya fara da mai to ba ya taɓa ci sai ya sayo kifi ya ci da shi, ita da yara kuma sai ya sayo musu balangu ko tsire. Amina tana daga ɗaki wani irin takaici ya lulluɓe ta, musamman da ta ji wai Hafiz yana faɗa wa Bilkis zai ƙauracewa kwanan ɗakinta. Kiransa ta gani, saboda haushi kawar da kai gefe ta yi ba ta ɗauka ba. Miƙewa ta yi ta shiga uwar ɗaki ta cire kwalliyar atamfar da ta yi, ta ɗauki wasu riga da wando marasa nauyi na bacci ta saka, sannan ta fita ta ɗauro alwalar Isha'i ta gabatar da sallah. Tana nan zaune ta ji sallamar Hafiz, mamaki bai gama kashe ta ba sai da ta ga Hafiz ya nufi ɗakin Bilkisu. Bai wani jima ba, ta ga ya ɗawo ɗakinta ya zauna, sai dai har lokacin fuskarsa a haɗe take. Kifin da ta ga ya fito da shi ya sake tabbatar mata da wayar da ta ji Bilkisu tana yi, Hafiz bai kalli ɓangaren da take ba ya ce. "Idan za ki ci ki sauko." Haushi ya kama ta da jin abin da ya faɗa, zuciya ce ta ciwo ta ta ce. "Na ƙoshi." Sai a lokacin ya ɗago ya kalle ta, bai tanka mata ba ya cigaba da cin abincinsa. Sai da ya gama ya tura mata ledar wani ƙunshin kifi gabanta ya ce. "Ga shi nan ki tashi ki ci." "Na ƙoshi ka cinye." Amina ta faɗa a karo na biyu, ransa ne ya ɓaci don ya san ba ta ci abinci ba. Cikin faɗa ya ce. "Wai saboda na yi miki faɗa shi ne za ki hau ɓata rai? Wani sabon hali za ki tsiro mini Amina? Kin san asarar yawan abincin da kika yi mini?" A ɗan zafafe ita ma ta ce. "To yanzu me nace maka? Kawai don na ce na ƙoshi sai ya zama abin faɗa? Idan ba da son ranka ka dawo za ka kwana a nan ba, ba sai ka koma can." "Me kike nufi Amina?" Ya jefa mata tambaya rai a ɓace. Shiru Amina ta yi, cikin hawaye ta miƙe ta shiga ɗaki tana kuka. Kukan da Amina ta yi shi ya sake harzuƙa Hafiz, don gani ya yi bai ga abin fushi da kuka ba saboda kawai ya nuna mata kuskurenta. Hafiz yana gama cin abinci kallo ya kunna, don ba ya son ya sabarwa kansa da zaman majalisa. Yana nan zaune har ya ji bacci don haka ya kashe ya shiga ɗaki, a lokacin da ya shiga Amina ta yi bacci. Rage kayan jikinsa ya yi sannan ya haye gado ya kwanta. Duk abin da ya faru tsakanin Amina da Hafiz, Bilkisu tana laɓe tana jin su. Daɗi ne ya cika ta, cikin farinciki ta koma ɗaki ta buɗe ledar kifin da Hafiz ya ajiya mata. Sai da ta cinye shi tas, sannan ta ɗauki ruwa ta sha ta haye gado ta kwanta hankali kwance. WASHEGARI Washegari koda Amina ta tashi yanayinta babu yabo babi fallasa, haka shi ma daga wurin Hafiz. Sai da ta zo yin wanke-wanke ta juye shinkafar a leda, saboda ko akuyoyi ba za su iya ci ba. Bilkisu ce ta sharo ɗakinta a lokacin tuni Hafiz ya jima da fita, da gayya ta sharo wata ƙatuwar takardar tsire wacce take sharkaf da mai, ƙuli da albasa. A yatsine ta sharo takardar da ta yi fakaka a saman makwashin shara ta ce. "Shi ma Abban Sayyada na faɗa masa ya cewa mai tsiren nan ya rage zabga mana albasa, amma kullum sai ya manta." Ta gefen ido Bilkisu ta kalli Amina da ke wanke-wanke, sai da ta je wucewa ta gabanta sannan ta saki takardar ta faɗi ƙasa da gayya don ta gani.

Chapter 5 of 35