Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
har sai an bi mini haƙƙina. Daga nan ma kotu nake son a tura mu." Malam Shehu ya yi fiƙi-fiƙi cike da tsoro ya ce. "Wallahi tallahi ni ma ba ni na faɗa, jita-jita na ji ana yi kuma sai aka yi sara a kan gaɓa. Ni kuma ina ganin kamar Bala wanzan ya sani, amma ya munafurce ni." Bala wanzan ya zaburo yana faɗin, "Amma ai kai ka kawo hukuma har gida suka tafi da ni, ka ce na yi maka aski wai kai ma kana zargin ka kamu." Jin hayaniya tana neman kacamewa wani Sergent ya buga musu tsawa yana faɗin. "Ba ma son hayaniya, kai Bala tun da kai aka fara kawowa ka yi musu bayani." "Ni dai tun da nake ban taɓa yi wa Alhaji Idi Naira aski ba sai wannan karon, ya kira ni har gidansa na yi masa aski da gyaran fuska. To bayan na fito daga gidansa, sai na wuce gidajen iyayen yara da dama na yi wa 'ya'yansu kaciya, wasu ma har aski na yi wa iyayensu. Sai kuma jarirai biyu da na cirewa hakin wuya. Bayan kwana biyu, sai na fara jin surutun wai Alhaji Idi Naira yana ɗauke da cutar ƙanjamu. Kwatsam! Ina zaune sai ga jami'an tsaro su zo da Malam Shehu, su ka tattaro ni suka yi awon gaba da ni." Sergent ɗin ya gama rubuta jawabin Bala wanzan, sannan ya dubi Idi Naira. Idi Naira ya shiga wurga wa Malam Shehu harara ya ce. "Yallaɓai wannan mutumin ya ci mutumcina, ta hanyar yi mini ƙazafin da ban ji ba ban gani ba. Kawai saboda kwanaki na yi fama da rashin lafiyar farankama, shi ne aka fara yawo da ni wai ina da ciwon ƙanjamau. Har wasu suna cewa ƙurajenta sun fito mini." Ƙuri Baba Sale ya yi wa Alhaji Idi Naira yana kallo, saboda irin ramammun mutanen nan. Idi Naira ya ɗora da cewar. "Dr kai ne likita, saboda Allah ina haɗin cutar farankama da ƙanjamau? Ko saboda kullum sun ga ina lalacewa kamar ɗibana ake yi? Ni lafiyata ƙalau, masifar uwar gida da amaryata ne suka saka ni a gaba." Sai a lokacin Baba Ibrahim ya numfasa jin musu da hatsaniya ta fara kacamewa ya ce. "A'a gaskiya babu haɗi ma tsakanin cutar ƙanjamau (HIV) da cutar farankama/ƙarambau (CHIKENPOX). Tun da ita cutar ƙanjamau wato HIV (Human Immunodeficiency virus), cuta ce da take karya garkuwa da kariyar jikin ɗan'adam. Ta yadda za ta ba wa ƙwayoyin cututtuka damar shiga jikin salin-alin, ba tare da wata kariya ba. Alamomin cuta mai karya garkuwar jiki sun haɗa da: Ɓarkewar zawo, yawaitar kaluluwa, matsanancin zazzaɓin da ya ƙi jin magani har zuwa lokaci mai tsawo, ciwon maƙoshi, yawaitar fitowar ƙuraje babu dalili, gumin dare koda lokacin sanyi ne, ramewa da rashin cin abinci, tashin zuciya da amai sai tari mai ɗaukar lokaci ba tare da ya ji magani ba." Cikin Alhaji Idi Naira ya kaɗa sosai, saboda yana jin kusan kaso mai yawa na alamomin da ya ji Baba Ibrahim ya lissafa. "To amma wani hanzari ba gudu ba, koda mutum ya ji irin alamomin da na lissafa ba zai ce kai tsaye yana da cutar ba, har sai ya je asibiti an gwada shi kuma an tabbatar." Jin furucin Baba Ibrahim ya sa Alhaji Idi Naira ya sauke ajiyar zuciya, Bala Ibrahim ya cigaba. "Amma ita cutar farankama/ƙarambau (CHIKENPOX), ƙwayoyin virus na varicella-zoster ce take haifar da ita, cutar tana iya kama yara da manya. Kuma ana iya ɗaukarta ta hanyar shaƙar numfashin mai ɗauke da ita, cin abinci, makwanci ko wasanni tare.Tana saka ciwon ciki, zazzaɓi mai zafi, firgita, jajayen ƙuraje masu ɗurar ruwa, da matsanancin ƙaiƙayi. Mafita ɗaya ce a kiyaye haɗa mai cutar da wanda ba shi da ita, yin gaggawar zuwa asibiti domin bada agajin gaggawa. Killace mai fama da ita, da karɓar rigakafi." Baba Ibrahim ya dubi Idi Naira ya furta, "Ka ga kenan babu alaƙa tsakanin cutar ƙanjamau da farankama Alhaji, amma duk ba wannan ba, yanzu ku tashi sai mu wuce asibiti gabaɗaya a yi muku gwajinta domin kowa ya fita daga zargin." Cikin Alhaji Idi Naira ya ɗuri ruwa saboda shi kansa ba shi da tabbacin rashin cutar, sakamakon idan ya tafi Lagos har ya dawo da matan banza yake mu'amala. Ya haɗe fuska tamau ya ce. "Dakata Dr, babu inda zan je ni lafiyata ƙalau." Ganin borin kunyar da Idi Naira yake yi ya sa kowa ya aminta da tabbas biri ya yi kama da mutum, domin rashin gaskiya ya bayyana ɓaro-ɓaro a fuskar Alhaji Idi Naira. Yaya Inu yana komawa gida daga wurin Zuly matashin kai ya samu Hansatu da Larai sun riƙo Salame ranga-ranga za su tafi da ita asibiti. "Subhanallah! Hansatu lafiya?" Yaya Inu ya furta a razane. "Wallahi Mai gida jikin ne ya rikice ina jin haihuwar ce ta zo." "Allah Ya ba ta lafiya, yanzu ina za ku kai ta?" Kai tsaye hansatu a ce. "Asibiti, saboda jikin ya ba ni tsoro." A gwasale Yaya Inu ya ce, "Yanzu haihuwar ce har sai kun yayime ta zuwa asibiti? A can ɗin rage mata zafin ciwon za su yi?" Haushi ya sa Hansatu ta yi gaba ba tare da ta kula shi ba. Shi ma daɗi ya ji saboda ya san ƙarshen zance a ce ya kawo wani abin. Fadil ne ya ɗauke su a motarsa ya wuce da su asibitin ƙwararru na Malam Aminu Kano (AKTH). Kasancewar a can yake aiki, kai tsaye ɗakin haihuwa aka wuce da ita domin a duba ta. A gwaje-gwajen likitocin ne suka tabbatar da ba ciki ba ne, sai dai ba sa ganin komai a cikin nata. Hankali a tashe Hansatu ta kira Yaya Inu, a lokacin ya ci babbar rigarsa zai tafi ɗaurin aurensa. "Mai gida akwai damuwa ciki dai na jikin Salame ashe ba ɗa ba ne." "Mene ne idan ba ɗa ba? Hansatu kada ku janyo mini masifa a farar safiyar nan. Ni fa ba na son damuwa, yanzu haka ɗaurin aurena da Zuly zan tafi." Baƙin ciki ya sa ƙwalla ta zubo wa Hansatu a ƙufule ta ce, "Yanzu abin da za ka ce mini kenan? Mai gida kana nufin Zuly ta fi 'yarka Salame?" "Hansatu kada ki ɓata mini rai, kin san dai jiya a yadda na kwana. Auran nan da za a ɗaura ne kawai yake ba ni ƙwarin gwiwa, har kika ga ina walwala. Ke bari na wuce kada ki ɓa ta mini lokaci, saboda matashin kai ta ce mini waliyinta wutar ciki gare shi zai iya tafiya idan na makara." Daga haka Yaya Inu ya katse, ya tura waya a aljihu ya rufe ɗakinsa sannan ya fice. Yana kai kansa zai fita a ƙofar gida ya ci karo da Mai gari shi da su Sanƙira, cike da girmamawa mai gari ya russuna ya ce. "Barka da fitowa!" Hannuwa biyu Yaya Inu ya kai ya fara shafa idonsa, a ransa yana ayyana ko dai gizo idonsa ya yi yake nuna masa Mai gari ne yake tsugunna masa. "Ranka ya daɗe ya haka kuma?" Mai gari ya russuna ya ce, "Duk girmanka ne ai, ga wannan a rage da abincin yara." Sanƙira shi da Muzammil, suka shiga kiciniyar sauke buhunhunan kayan abincin daga cikin kura sannan suka tafi. Mai gari har zai juya da sauri Yaya Inu ya tsayar da shi. "Ranka shi daɗe ni fa ka saka ni a duhu, waɗannan ɗin na mene ne?" Mai gari ya shafa kai ya ce, "A da dai ban yi niyyar sanar da kai yanzu ba, amma na ga kana neman ƙarin bayani ne Baba. Magana ta gaskiya Allah Ya jarabce ni da son Laraba, kuma aurenta nake son yi." Yaya Inu ya bayyana mamakinsa a fili, saboda duk cikin yaransa babu mai baƙin jini da samari ba sa kulawa kamar Laraba. Amma ganin irin rawar ƙafar da Mai gari yake yi masa, da tarin arzikin da zai samu ya sa ya ce. "Idan ma yanzu a shirye kake, ka wuce mu je masallaci domin yanzu haka ni ma ɗaura mini aure za a yi!" Cike da shauƙi Mai gari ya ce, "A yi haka kuwa?" Yaya Inu ya washe baki ya ce, "Me ya rage Mai gari? Ni ma ai an sauƙaƙa mini wannan bidi'ar wunin bikin, da mata za su zo su yi ta cinye abinci." Godiya sosai Mai gari ya yi, ya ce zai je ya sauya kayansa sannan ya ƙarasa. Hakan kuwa aka yi, Mai gari yana zuwa masallaci ana gama ɗaurin auren Yaya Inu da Zuly matashin kai. Yana zama ya miƙa wa Malam Liman sadaki ya zama waliyinsa, aka ɗaura aurensa da Laraba a kan sadaki naira dubu ɗari. Fitar Yaya Inu daga gida babu jimawa Goggo ta ƙarasa, almajirai ne suka shiga da ƙullin kayanta. Inno tana hango ta, ta ƙarasa wurinta cikin farinciki ta rungume ta tana faɗin. "Lale marhabun yau ga mutanen Jibiya." Goggo ta saki murmushi ta ce, "Ga mu Allah Ya kawo mu, wai ina Laraba ban ji motsinta ba?" "Idan kika bibiya ta fita ta ɗauko mini magana, yarinya yadda kika san rainon ifiritu." Goggo ta saka dariya cike da zolaya ta ce, "Ni kam wai Inno hala yaron ciki gare ki? Irin wannan ƙyalli da kike yi haka." Inno ta saki guntun tsaki ta furta, "Wuce mu je ku gaisa da Malam, kafin mu shiga ki fara zuba mini labari." Tun shigar Goggo gidan da Mai Yasin ya ji muryarta, ƙirjinsa ne ya yi wata irin bugawa da ƙarfi. Haka kawai ya ji gabansa yana faɗuwa, jin muryar matar da ko a duniyar mafarki ba zai manta da ita ba. Da sallama ɗauke a bakin Inno suka shiga ɗakin, Mai Yasin yana ɗaga ido karaf ya sauka a kan Goggo da ta daskare a wurin. "Malam Jafaru! Dama tsawon shekaru a nan ka laƙe bayan ka halake mini dukiyar marayu? Allah na gode maka, tabbas addu'a ba ta faɗuwa ƙasa banza. Azzalumi maha'inci, ka ci amanata kuma ka tafi ka bar ni da ƙallagaggen aurenka a kaina." Mai gari ya jima bai yi farincikin da yake ciki a wannan ranar ba, saboda mallakar Laraba da ya yi ji yake kamar ya mallaka faraincikin duniyarsa gabaɗaya. Yaya Inu ne ya sanar da shi tariyar Laraba, za ta kama sati mai zuwa saboda 'yan saye-sayen kayan ɗaki da za a yi mata. Bayan sallar Isha'i Zuly matashin kai da wasu fanɗararrun ƙawayenta biyar, suka yi mata rakiya zuwa ɗakin miji. Dama da rana ma tare da ita aka yi jere, don haka da za a kai ta suna tafe suna hira. Zaune take a ɗakin ta, tana jiran shigowar Yaya Inu hayaniyar yaran ta cika mata kunne. Cike da izza ta fita tsakar gidan a gadarance ta ce. "Ku waɗanne irin dabbobi ne, ku da yaranku da za ki dinga tunɓele da dare?" Indo da dama zuciyarta take cike da kishi fal ta ce, "Yadda muka zama dabbobi, sannu a hankali ke ma za ki zama dabbar, har ki haifo balami a ciki gaba da yin tamɓelen da shi." A daidai lokacin Yay inu ya shigo, yana shigowa duka yaran suka nustu suna yi masa sannu da zuwa, ko ƙurarsu bai kalla ba ya wuce wurin Zuly ya kamo hannu ta suka wuce ɗakinsa. Sabuwar hira suka dasa suna ƙyalƙayala dariya, zuciyar Indo kamar za ta buga, tun tana tsakar gida tana jin hirarrakinsu har dare ya yi ta shige ɗaki ta kwanta. Ganin Yaya Inu ya ja filo da abin rufa ya sa Zuly matashin kai ta ce, "Yaya haka ne masoyi? Ban gane ba an yi gabas da kare." Ƙirjin Yaya Inu ya buga amma sai ya basar ya ce, "Na gaji ne kin san fa yau na sha baƙi." Zuly ta ɗan tsuke fuska ta ce, "A'a ai kuwa haka za ka yi haƙuri ka tashi, don ni in saluɓe namiji ba abu ne mai wuya a wurina ba." Tsoro da kunyar Zuly ya mamaye shi, saboda tun da yake aure bai taɓa auro fitsararsiyar mace irinta ba. A ɓangare ɗaya kuma bai san me zai ce mata ba, hasali ma wata irin kunyarta yake ji. Yana cikin nazari, ya ga Zuly ta miƙe tsaye tana warware ɗankwalin kanta ta ce. "Na ka wasa ne Malam Inusa, ai ni ba na sanya. Ba ka ji ma laƙabin sunana ba matashim kai? Bari ma ka gani." Zuly ta ƙarasa maganar tana fisgo siraran ƙafafuwan Yaya Inu. Ya auren Yaya Inu da matashin kai zai kasance? Shin Yaya Inu yana warkewa ko ya tafi kenan? Wacce badaƙalar za a yi a gidan Mai gari da Laraba? Shin za ta so Maigari ko shi yake wahalarsa? Ina matsayin auren Inno da Mai Yasin? Yaya Mai Yasin zai yi tun da asirinsa ya tonu? Zai zauna da Goggo da Inno ko yaya? Mene ne a cikin Salame idan ba ɗa ba? Ya matsayin gwajin da za a yi wa su Ɗan Bishir? Yar gwal da Ɗanladi zaman su zai ɗore? Duka waɗannan tambayoyin da ma waɗansu, amsarsu tana cikin cigaban littafin GIDAN LIKITOCI. AlhamduLillah, a nan na kawo ƙarshen free pages ga me son ci gaba za ta biya ta 500 Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 35 of 35