Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Tsugunnawa Bilkisu ta yi ta share ta saka a shara, sannan ta wuce ɗaki tana murmushin mugunta. Wunin ranar haka Amina ta yi shi cikin damuwa, zuciya ta raya mata munafurcin da Hafiz zai tsiro mata. Har take ji a ranta da ya san ba zai yi musu adalci ba, da ba ta aure shi ba. A yammacin ranar sai da ta yi wanka sannan ta ɗora girki, bayan ta gama ta ɗebi nata ita da Hafiz sannan ta ba wa Bilkisu da yaranta. Kuma a wannan ranar lafiya ƙalau suka ci abinci, har Hafiz yana janta da hira saboda girkin da ta yi ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba. Hakan ne ya sanyaya zuciyar Amina har ta sauko daga fushin da take yi, ta so ta yi masa magana a kan rashin adalcin da ya fara yi amma sai ta ƙyale shi don kada ya ga kamar ta cika ƙorafi. Sannu a hankali rayuwar gidan Hafiz ta cigaba da tafiya, da daɗi babu daɗi haka suke rayuwa. Saboda kusan kullum da abin da Bilkisu take tsiro da shi, musamman idan Hafiz yana ɗakin Amina. Sautari idan yana ɗakin Amina sai dare ya yi za ta buga masa ƙofa ta ce ɗaya daga cikin yaran babu lafiya, ko kuma ta ce ya fito ya duba mata ɗakinta ta ji motsin wani abin. Tun Hafiz bai fahimta ba, yana biye mata. Har ya fahimci kamar da makirci a cikin lamarinta, saboda idan yana ɗakinta lafiya ƙalau suke kwanciya su yi bacci. Ana cikin haka sai Bilkisu ta tsiri idan Hafiz yana ɗakinta sai ta fice ta koma cikin yaran ta kwanta, a ranar farko da ta yi da ya tambaye ta sai ta ce ita ta fi jin daɗin kwanciya a cikinsu. Da ya nemi kasancewa da ita nan ma sai ta ce ba ta buƙata, daga haka sai ta koma idan ya dawo ɗakinta sai dai ta zauna ta yi ta rusa kuka ko ta ce ya sake ta. Hakan ba ƙaramin ɗaga hankalinsa ya yi ba, da ya tambaye ta sai ta ce masa idan yana ɗakinta ji take kamar ta kashe shi. Kuma sai jikinta ya ɗauki zafi kamar ana dafa namanta ko ana tsira mata allura. Wannan lamarin ne ya ɗaga hankalin Hafiz, ya shiga nema mata maganin aljanu a tsammaninsa ko su suka fara shafarta. Watarana da safe Hafiz yana shan shayi, ta fara shara, da gayya Bilkisu ta sharo ƙarƙashin kujera sai ga wata ƙatuwar laya ta fito. Da mamaki ta ɗauki layar ta ce. "Abban Sayyid kai ne ka ajiye ta." Yamutsa fuska ya yi ya ce "Ni kuwa me zai haɗa ni da laya Bilkisu? Miƙo mini na gani." Ƙin ɗauka ta yi ta janye gannu gefe ta ce. "Cab wallahi ba zan taɓa ba, haka kawai ban san ta mece ce ba zan taɓa ina zaune ƙalau." Miƙewa ya yi ya ƙarasa wurin ya yi bismillah ya ɗauka. Ya shiga warwarewa yana buɗewa sai ga wani busasshen ɗanyan nama, da ƙananan allurai a ciki. Wata takarda ya gani ya buɗe ta, a ciki ya ga an rubuta sunansa da na Bilkisu na farraƙu. Daga ƙasa kuma an saka sunansa da na Amina an yi rubutun mallaka." A firgice ya ɗago yana bin Bilkisu da kallon tausayi, sai a lokacin ya fahimci irin abin da ta ce masa tana ji a cikin jikinta. Kamar Bilkisu ba ta san da komai ba, ta matsa kusa da shi ta ce. "Me aka rubuta a ciki, ba ni mu gani." Naɗe takardar ya yi, don ba ya son ta gani ya cusa a aljihu ya ce. "Ƙarasa shararki babu damuwa." Haɗe fuska Bilkisu ta yi ta ce. "Kamar ya babu damuwa Abban Sayyid? Ya za a yi a ga laya a ɗakina kuma a ce ba zan gani ba, salon haka kawai a ce asiri na yi tun da dama yanzu ni ce mai lefi." Rasa abin da zai faɗa mata zai yi, sai kawai ya fice daga ɗakin ya shiga ɗakin Amina. A lokacin da ya shiga tana kwance, saboda a kwana biyun gabaɗaya ba ta jin daɗin jikinta. Kullum cikin tashin zuciya da kasala take, tana ganinsa ta tashi zaune a hankali. Cikin zafin rai Hafiz ya miƙa mata ya ce. "Mene ne wannan? Me kika aikata haka Amina?" Ita warin busasshen naman ma tayar mata da zuciya ya yi, ta ɗan yamutsa fuska ta ce. "Kamar ya ya? Mene ne wannan kuma" Takaici ne ya kama shi, rai a matuƙar ɓace ya shaƙo wuyanta yana jin kamar ya zabga mata mari ya ce. "Ina tambayarki mene ne wannan kina tambayata? Baƙar munafuka algunguma, ashe dama haka kike ban sani ba?" Hankali Amina ba ƙaramin tashi ya yi ba, duk sai ta birkice jikinta ya fara rawa saboda Hafiz bai taɓa birkice mata irin haka ba. GIDAN ALHAJI UMAR Alhaji yana fita Shukura ta yi shiru, don ba ƙaramin mamaki ya ba ta ba. Bata taɓa tsammanin har kawo wannan shekarun yana son Hajiya Karima haka ba, ta shi ta yi ta buɗe drowerta ta kwaso kayanta da duk wani abu da za ta buƙata ta saka a akwati. Tana shirin saka mayafi ya dawo ɗakin. Da mamaki yake bin ta da kallo, har lokacin fuska babu walwala ya ce. "Ina za ki?" Kuka Shukara ta saka, ta ce. "Wurin mahaifiyata zan tafi, gara na je can tun kai da matarka ba ku kashe ni ba. Idan na haife maka ɗanka sai ka je ka ɗauka ka kawo mata." Hankalin Alhaji ne ya tashi, cikin sauri ya riƙo hannunta ya ce. "Haba Sjukura, kawai saboda wannan maganar za ki yi fushi ki tafi gida? Tun da haka ne to zan kai ki ɗaya daga cikin gidajena na bayan gidan nan ki zauna. Haka ya yi miki?" Girgiza kai Shukura ta yi ta ce. "Salon idan ba ka gidana wani ya haura mini kafin ka zo duk abin da za a yi an gama ko? Wallahi ba zan iya zama a wani gidan ba. Ni kawai ka bar ni na tafi, idan ta fitar da kajin na dawo." Duk yadda Daddy ya so Shukura kar ta tafi fir ta ƙi amincewa, don haka ya ce zai kai ta ta yi kwana biyu idan ta ji daɗin jikinta sai ya dawo da ita. Hajiya Karima tana gani Shukura ta shirya ta fita, aka ɗauki ƙatuwar akwatinta aka fita da ita. Sai daga baya Alhaji yake ce mata ta je gida ta kwana biyu saboda ba ta jin daɗin jikinta. Bayan da Daddy ya tafi, Shukura tana shiga gida ta wassafa wa mahaifiyarta abin da ya faru. Bayan ta gama sauraronta ta ce. "Shukura abin da na fahimta ko za ki yi kissa fa dole sai mun haɗa da neman taimako. Don gaskiya na lura ba za mu cimma manufarmu ba, har sai mun kawar da hankalin mutumin nan. Saboda na lura ba ƙaramin so da shakkar tsohuwar guzumar nan yake yi ba, kin ga kuwa zama bai kama ni ba. Yadda ubanki ya mutu ya bar ni a talauci, na sha wahalar kula da ku tun kuna ƙanana ke da ƙannenki. Dole yanzu mu tara dukiya mu huta, tun da lokacin hutun ne ya zo." Shukura ta yi zaraf ta ce. "Ai Inna shi ya sa na kafe kai da fata na ce sai na zo gida, wallahi na tsani matar nan da 'ya'yanta. Komai za ki ji ya ce Hajiya, komai Mamana yadda kika san na shaƙe shigiyar yarinyar nan haka nake ji." Taɓe baki Innar Shukura ta yi ta ce. "Wannan ƙaramar alhaki ce, ki bari mu gama da ubanta na ta mai sauƙi ne." Ajiyar zuciya Shukura ta sauke ta ce. "Ai ita mun ma kusa rabuwa tun da aurenta bai fi wata guda ba yanzu, don ma saurayin ne ya ce a ƙara masa sati biyu saboda uzurin gabansa. Yanzu ya za a yi Inna?" Miƙa hannu Innarta ta yi ta ce. "Kawo kuɗi, ni kuma yanzu na bazama sha yanzu magani yanzu." Jaka Shukura ta zuge ta ɗebo kuɗi masu kauri ta miƙa mata. Nan take Innarta ta ɗauki mayafi ta fice ba ita ta dawo ba sai dare, don su Shukura har sun yi bacci suka ji motsinta. Sai da safe Inna ta fara yi wa Shukura bayani. "Wannan baƙar ledar da kika gani, a yadda ya ba ni a haka ya ce mu binne ta. Mai binnewar yana yi yana ambatar sunan Alhaji Umar, sai kuma wannan ruwan rubutu ne da za ki sha ki yi wanka da shi." Murmushi Shukura take yi tana gyaɗa kai, Inna ta sake ɗauko wata ledar ta ce. "Wannan kuma, sai a cikin gidansa za ki binne shi. Ki tabbatar wani bai gani ba, sai wannan ƙarshen zance sunansa." Inna ta ƙarasa maganar tana ɗauko wata ƙaramar ƙwalba mai ɗauke da wani baƙin abu a ciki ta ce. "Amma fa duk waɗannan abubuwan ba za su yi tasiri ba, har sai kin yi amfani da wannan. Za ki matsa shi a jikinki, ki tabbatar Alhaji ya yi amfani da ke yana jikinki. Idan kika yi shi sai ki yi sauran, daga nan magana ta ƙare." Murmushi Shukura ta yi ta ce. "Allah Ya bar mini ke Inna, gaskiya na ji daɗi. Ai wannan ma yau zan yi amfani da shi." Shukura ta furta tana adana su a jakarta. Hanif ƙanin Shukura ne ya zauna a gefenta ya ce. "Aunty tun kwanaki kika yi mini alƙwarin keke don Allah ki saya mini." Dafe kanta ta yi ta ce. "Na manta Hanif, amma zuwa an jima Siyama ta raka ka shagon Harisu sai ku tambayo mu ji nawa ne. Ita da Inna kuma dama alƙawarin waya na yi musu." Cikin jin daɗi Inna ta ce. "Ai haka nake ta son harkar arziki, yo ta ina zan zauna ganin kallon ruwa ƙwaɗo ya yi mini ƙafa." Lokaci ɗaya suka saka dariya. Sai da aka yi sallar magriba Shukura ta saka abin da Inna ta ba ta, da yake tun safe ta cewa Alhaji tana son ganinsa da daddare. Ana sallar Isha'i motarsa ta faka a ƙofar gidansu. Abaya ce a jikin Shukura, ta ciki kuma sai wasu figaggun kaya. Tana shiga ta zame abayar jikinta, kallonta ya yi yana murmushi ya ce. "Ki tausaya wa bawan Allah kada ki birki ta shi." Cikin shagwaɓa Shukura ta ce. "To ai idan na birkita shi sai na saita abina, tun da dama a lissafi yau kwana ne. Ni kuma kewarka na yi shi ya sa na kira ka dama, tun da babu mai kawar da damuwar sai kai." Ta ƙarasa maganar tana shiga jikinsa, cikin wani irin yanayi ya ce. To mu wuce gida kenan? Tun farko dama shi ya sa ban so kika taho ba. Kuma ni kaina a yau cike nake da kewarki, musamman da na tuna ba kya gidan." "Ka kama mana hotel don ni ba zan koma ba sai an kwana biyu." Ta ba shi amsa, da sauri Alhaji ya ce. "Hotel? Haba Shukura, da girmana da komai sai a ganmu ni da ke a hotel? Wasu fa mummunar fassara za su yi mana." Hawayen ƙarya ta fara yi ta ce. "To shi kenan, ai dama ba ka damu da ni ba. Tun da kana da wacce za ka nema a gida, ni kuma ko oho." Janyo ta ya yi jikinsa ya ce. "Ba haka ba ne Shukura, yanzu mu wuce kenan?" Gyaɗa masa kai ta yi, Alhaji ya saka wa motar key suka bar ƙofar gidan. Ummou Aslma Bint Adam🌚 07062062624 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA TAKWAS AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_ _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ *08089965176* *07084653262* *** Tafiya mai ɗan nisa suka yi daga unguwa uku, zuwa Arrayan hotel da ke titin Karkasara. Zuciyar Shukura ƙal saboda farinciki, a reception Daddy ya tsaya ya kama musu ɗaki. Suna shiga ɗakin Shukura ta faɗa jikinsa, cikin kissa ta ce. "Allah ka ga yadda nake ƙaunar wannan ruhin, Allah kada ka nuna mini ranar da zai juyawa soyayyata baya. Domin idan haka ta kasance, mutuwa zan yi." Riƙo hannunta ya yi suka zauna a bakin gado, ya zagayo da ita ta gabansa ya ce. "Ba na son na sake jin harshenki yana furta mini kalmar mutuwa, ina ƙaunarki Shukura ba zan iya jure rashinki ba." Murmushin gefen baki ta yi ta ce, "Amma ai ka fi ƙaunar matarka a kaina, kodayake duka-duka yaushe na shigo rayuwarka..." "Shiii! Idan ina tare da ke ba na ganin kowa a gabana, ke ce sarauniyata. Koda wasa, kada ki sa a ranki wannan fadar ba ta ki ba ce." Kiss ta sakar masa a baki, cikin salonsa ya shiga mayar mata da martani. Sai daga baya ya miƙe ya kira waya ya musu oder abinci, ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba aka kawo musu. Sai da suka ci suka ƙoshi, sannan Alhaji ya ce ta raka shi su yi wanka. Har ta fara rage kayan jikinta, sai ta tuna da maganin da yake jikinta. Cike da kissa ta nuna masa ba sai sun yi ba, ta shiga ribatarsa har ta yi galaba a kansa. Tsoro ne ya kama Shukura ganin Alhaji ya ɓingire da bacci mai nauyi, girgiza shi ta fara yi a ɗan ruɗe amma ta ji shi shiru kamar gawa. A hargitse Shukura ta ɗauki wayarta ta shiga banɗaki, ƙasa ta yi da murya ta kira lambar Inna bayan ta ɗauka ta ce. "Inna da matsala fa." "Ba na fatanta kowacce iri ce, me yake faruwa?" Inna ta furta da sauri. A ƙagauce Shukura ta ce, "Inna bayan mun gama fa na ga jikinsa ya saki yana bacci, yanzu na yi masa tashin duniya ya ƙi."Murmushi Inna ta yi ta ce. "Kada wannan ya dame ki, ƙa'idar maganin ce haka. Yanzu ko zai farka zai kai ɗaya zuwa biyun dare, kada ki nuna masa damuwa ko tsoro idan ya nuna miki mamakin yin baccinsa." Sai a lokacin hankali Shukura ya kwanta don haka ta ce. "A nan za mu kwana kenan Inna?" "Ke ba na son sakarci, ba mijinki ba ne idan kun kwana sai me?" Wani tunani ne ya faɗo wa Shukura, cikin sauri ta ce. "Shi kenan sai goben Inna." Suna gama waya Shukura ta fice ta koma ta samu Alhaji yadda yake a kwance, zagayawa ta yi ta ɗauki wayoyinsa duka ta kashe. Sannan ta koma banɗaki ta gyara jikinta. Kamar yadda Inna ta faɗa Alhaji bai farka ba sai kusan ɗaya da rabi na dare, ita ma a lokacin Shukura ta yi bacci. Motsin da ta ji na Alhaji ne ya tashe ta, jikinsa ya ji duk ya yi masa tsami kamar an yi masa duka. Suna haɗa ido ya ji ƙaunar Shukura tana sake fisgarsa, banɗaki ya shiga bai jima ba ya fito ya sake janyo ta jikinsa. Sai bayan wani lokaci suka sake komawa banɗaki suka tsaftace jikinsu, sannan suka koma bacci. Washegari sai da gari ya yi haske suka tashi saboda makarar da suka yi, sai da suka yo sallah sannan suka sake kwanciya. Kunna wayarsa ya yi, yana kunnawa ko minti biyar bai yi ba ya ga kiran Hajiya Karima ya shigo. Guntun tsaki ya saki kamar zai ɗauka sai kuma ya saci kallon Shukura, wata irin shakkarta ya ji don haka ya sake kashe wayar gabaɗaya. Bacci suka koma, ba su suka tashi ba sai kusan sha biyu. Oder abinci ya fara yi musu, suna fitowa daga wanka aka kawo musu abinci. Cikin tsantsar soyayya Alhaji yake ciyar da su, yana jin kamar ya mayar da Shukura cikinsa. Don yadda yake jin soyayyarta tana fisgarsa ko lokacin farkon aurensu bai ji haka ba. Su Shukura ba su suka bar hotel ɗin ba sai kusan bayan la'asar, sai da suka biya ta Mubeen Store ya sayawa Inna kayan shayi da na abinci dangin, shinkafa, taliya makaroni, mai, maggi da sauransu. Sannan ya haɗa mata da kayan ƙwalam da maƙwalashe ya kai ta gida, da ƙyar Shukura ta bar shi ya tafi saboda yadda take narke masa tana zuba masa kissa. Daddy bai ƙarasa gida ba sai kusan sallar Magriba, a lokacin da ya shiga gidan sai ya samu Hajiya da yara duk sun yi jigum-jigum. Suna ganinsa daga ita har yaran suka ƙarasa wurinsa, cikin kuka Mami ta ce. "Daddy ina ka shiga tun jiya muna kiranka a kashe." A madadin ya amsa musu sai kawai ya janye Ruƙayya daga jikinsa, fuska a haɗe ya ce. "Ai gani na dawo yanzu." Sororo suka yi gabaɗaya suna bin sa da kallon mamaki, Hajiya Karima ta sakar musu murmushin yaƙe ta ce. "Ta yiwu akwai abin da yake damun Daddynku, bari na je na same shi a ɗaki." A sanyaye suka amsa mata, ta nufi ɗaki ita kanta tana jin zuciyarta babu daɗi. Lokacin da ta shiga ɗakin waya ta samu yana yi da Shukura, ya saki murmushi ya ce. "I miss too my baby." Yana sauke wayar Hajiya ta riƙo hannunsa ta ce, "Barka da zuwa ranka shi daɗe." "Barka!" Daddy ya amsa a daƙile, Mommy ta sake kawar da damuwar zuciyarta ta ce. "Daddyn yara tun jiya muke cikin tashin hankalin rashin ganinka, na kira waya ba adadi ba a ɗauka ba. Daga baya kuma da na kira na ji an yi rejecting, wallahi ka ganmu yau ko abincin kirki ba mu ci ba. Don har na kira Alhaji Gambo, muna shirin kai report." Cikin halin ko in kula Alhaji ya ce. "Kawai don ba a samu wayata ba sai a fara kira Alhaji Gambo ana jajena, a hotel na kwana tare da Shukura kuma ba na son hayaniya shi ya sa na kashe wayar." Wani abu ne ya daki zuciyar Hajiya Karima, amma sai ta danne ta ce. "To ai irin haka da sai ka faɗa mini, ka ga atleast mun san wurin da kake." A zafafe Alhaji ya waigo ya ce. "Don zan kwana da matata a wani wuri sai na faɗa miki? Haifata kika yi ko rainona kika yi?" A sanyaye Hajiya ta ce. "A'a." "To ki saurara mini haka, kin hana yarinya zama a gidan nan saboda baƙin kishinki, kenan babu dama na ɗauke ta mu keɓe a wani wurin idan ina da buƙatarta? Wai yaushe kika sauya ne Karima? Girmai-girmai da ke ki zauna kina kishi da 'yar cikinki? Me Shukura ta tsare miki ne a gidan nan? Wallahi idan ma baƙinciki kike yi da cikin jikinta, to In Shaa Allahu za ta haife shi lafiya." Alhaji Ya furta kalamansa rai a ɓace, kasa daurewa Hajiya ta yi ta ce. "Wai Alhaji me kake nufi ne? Saboda kawai na tambayi a inda ka kwana? To Allah Ya ba ka haƙuri, amma ka sani wallahi ko kaɗan ba na baƙinciki da abin da Shukura za ta haifa." "Idan ma kina yi sai dai mugun halinki ya faɗa kanki, sannan magana ta gaba da zan faɗa miki a kan wancan kiwon kajin da kike yi ne. Na gaji da ganin ana ɓa ta mini gida, kuma ba zan juri ɗaukar matar aurena ina yawon hotel da ita ba. Na ba ki daga yau zuwa gobe ki kwashe mini duk wani abu da ya danganci kiwon kaji, ko buhun dusa ɗaya ba na son sake gani." A hargitse Mommy ta dube shi ta ce. "Au ta nan kuma ka ɓullo, ai sai ya yanzu na gano inda maganarka ta dosa. Kaji ba yau na fara kiwo ba, kuma wata ba ta isa a saka na fitar da su ba. Idan ba haka ba sai na bar maka gidanka." Kamar Alhaji yana jira ya ce, "To ki tafi mana, idan haka kika zaɓa ai ƙofa a buɗe take ban riƙe ki ba." A razane Hajiya Karima ta zaro ido ta ce. "Ni kake cewa na tafi Alhaji?" "Ƙwarai kuwa, idan har haka kika zaɓa kina iya kwashe 'ya'yanki ku tafi." Yana gama maganar ya fita daga ɗakin. A sanyaye ta zauna a bakin gado, kawai sai ta fashe da kuka. Tana cikin wannan yanayin su Ruƙayya suka yi sallama cikin ɗakin hankali a tashe. Cikin damuwa Haidar ya ce. "Mommy wai lafiyar Daddy kuwa? Muna yi masa magana kin ga yadda ya hankaɗe Mami har ta faɗi ƙasa kuwa? Kuma bai tsaya ba ya fice daga gidan..." Maganarsa ce ta maƙale ganin mahaifiyarsu tana zubar da hawaye, da sauri suka ƙarasa cikin damuwa suka ce. "Mommy mai ya faru kike kuka? Ko Daddy ne?" Sai da Hajiya Karima ta share hawayenta sannan ta ce. "Daddynku yana buƙatar addu'arku Haidar, saboda jikina yana ba ni kamar ba ya cikin hayyacinsa. Yanzu haka kaji can ya ce a fita da su, ba ya buƙatar abin kiwo ɗaya a gidan nan." "A fita da su?" Suka tambaya kusan lokaci ɗaya, gyaɗa musu kai ta yi. Ruƙayya ta yi murmushin takaici ta ce. "Wallahi ba kowa ba ce sai annamimiyar yarinyar nan, hmmm amma a wannan karon ta yi ƙarya don uwarta. Wallahi ba za a fita da su ba." Waya Hajiya ta ɗauko ta ce, "Ku fita zan kira Alhaji Gambo." Damuwa lulluɓe a fuskarsu suka tashi suka

Chapter 6 of 35