Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta tashi biyu za ta raba shi, ta sha rabin roba yau gobe ta sha rabi. Shi kuma wannan man zafi ne, na ciwon bayan da ta ce tana yi ne. Za ta dinga shafa shi a bayanta safe, rana da dare. Amfaninsa iya baya ne. Kar ta ji ƙafa ko gwiwa tana yi mata ciwo ta shafa, ba zai yi mata aiki ba. Duka dai bayanan maganin suna jiki, na san kin fahimta abin da ba ta gane ba sai a bari na dawo, saboda ba na son na ba wa mutum magani ya sha ba daidai ba a samu matsala." Duk bayanin da Baba Sale yake yi Fadil yana cikin mota yana jin sa, ba ƙaramin birge shi ya yi ba. Don haka ya fito ya ƙarasa wurinsa cike murmushi ya ce. "Am Baba Sale na ji duk bayanin da kake yi mata, kuma AlhamduLillah ka birge ni matuƙa. Saboda yadda na ji kana bayanin magungunanka daki-daki cikin ƙa'ida, ta yanda ba zai haifar wa mutane matsala ba." A sheƙe Baba Sale ya dubi Fadil ya ce. "Kai yaro da me ka ɗauki masu magungunan gargajiya? Jahilai ka ɗauke mu ko yaya? Ka ɗebo tsila-tsilan ƙafafuwanka kamar ƙwailayen lawashi za ka yi mini iyayi." Kunnuwansa Fadil ya riƙe ya ce, "Allah Ya huci zuciyarka ba haka nake nufi ba, ka yi abin da ya dace ne shi ya sa na yabe ka. Saɓanin wasu masu magungunan da suke sayar da magani babu dosage, mutum ya sha yadda ransa ya so babu ƙa'ida." Baba Sale ya taɓe baki ya ce, "Da ka ɗauka maganin asibiti ne kaɗai yake da galihu? Masu magungunan ai wasu suna suka tara, kamar yadda a cikin likitocin akwai muna likita. Kai dube ni nan. Sana'ata ba irin ta sauran masu magani ba ce. A yanzu ma idan na samun jari, babban wuri zan buɗe na huta da gararanba a titi. Sai na sake inganta su, don ina da burin har jami'an lafiya zan zuba tun da ni dai ka san summun bukumin ne, zo na kashe ka da turanci ban sani ba ballantana na san harkar gwaje-gwaje." Fadil ya saki murmushi, ya yaba masa sosai da sabon tsarin inganta maganin da ya ɗauko, har zai tafi ya waigo ya ce. "Na ji Daddy ya ce an yi wa yaron nan shayi ya jikinsa?" Jin tambayar Fadil ta sa hawaye ya zubo masa, ya saka hannun rigarsa ya share. Mamaki ne ya kama Fadil yana shirin magana Baba Sale ya ce. "Ɗan Bishir dai ga shi can rai a hannun Allah, daga kaciya jikin yaro sai fitar da ruwa yake duk ya jagalgale abin ba kyan gani. Na saka masa magani a banza, haka wanzan da ya yi masa kaciyar ya aiko masa da magani amma sai ta fara kamewa sai ta koma 'yar gidan jiya." Ya ƙarasa maganar yana fashewa da kuka. "Subhanalla, kuma ka kai shi asibiti?" Kamar Baba Sale yana jira ya ce, "Kaciyar zan kai asibiti don lalacewa? Wai me ya sa a kullum, sai ka nemi wulaƙanta mana sana'ar wanzanci ne?" Fadil ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Ni fa ba da wata manufa na faɗa ba, yanzu mu je na ga yanayin jikin na sa." Babu musu Baba Sale ya yi gaba Uwale da Fadil suna biye da shi. Suna zuwa suka samu Ɗan Bishir a yashe a ƙasa, kudaje sun yi yamama a kan jikinsa. Da sauri Fadil ya ƙarasa ya fara karkaɗe masa, ya ɗago a ɗan zafafe ya ce. "Garin yaya kuka bari jikin yaron nan ya yi haka? Saboda Allah dubi yadda ƙudaje suka bin sa ko su ba su isa su saka masa wata cuta a jiki ba." Mai shirin kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, jin kalaman Fadil ya sa Baba Sale ya saki wani wawan kuka har sa da ya tsorata Uwale da Fadil. Ya riƙo hannun Fadil jikinsa yana rawa ya ce. "Boka wallahi ban san yadda aka yi ba, don Allah yanzu mene ne abin yi?" Jim Fadil ya yi sannan ya ce, "Mafita kawai a ɗauke shi zuwa asibiti shi ya fi fa'ida. Don haka a yanzu muke bayar da shawara idan za a yi kaciya a san wuraren da ya dace a kai yara, ba zan kushe ta wanzamai ba. Domin tun daga shekarun baya zuwa kusan ɗan shekara ashirin da yake a yanzu, kusan yawancin duka kaciyar gida aka yi musu. Amma a inda gizo yake saƙar, rashin kula da tsaftace kayan aikin yin ta zuwa kula da ita bayan an yi wa yara, sune manyan ƙalubalen." "Wai boka da kake ta ƙafafa a kan shayin, asibiti shin tana da bambamci da ta gida ne? Duk dai ba abu ɗaya ake yi ba?" Uwale ta tambaya, don ta fara jin haushin yadda Fadil yake fifita aikinsa a kan sana'ar mijinta. Fadil ya cigaba da karkaɗe wa Ɗan Bishir ƙuda ya ce. "Gaskiya akwai bambamce-bambamce da dama. Kamar yadda muka sani shayi wacce a kimiyance ake kira (Circumcision) wata ƙaramar tiyata ce da ake cire fatar loba (Foreskin) wacce take zazzagowa ta rufe kan al'aurar namiji(Glans). Kaciya tana da dalilin da ya sa ake yin ta, daga ɓangaren addini zuwa al'ada. Mafi yawancin ƙasashen da suka ci gaba, suna yin shayi ne a rana ta farko da aka haifi jariri. Wasu ƙabilun kuma suna yi bayan suna ko idan an yaye yaro. To amma kin ga a irin yankin ƙabilunmu, yawanci ana yi wa yara daga shekara uku zuwa bakwai. Sannan rashin yin ta babbar barazana ga lafiya ne. Kamar yadda shayi ke da dalili akwai amafanin da take da shi, musamman a ɓangaren lafiya. Domin yin ta yana bayar da kariya daga saurin ɗaukar cutar infection, saboda cututtuka suna iya ɓoyewa a ciki idan ba a cire fatar ba. Tana bayar da kariya daga kamuwa da penile cancer, a ɓangaren mata kuma zai rage musu kamuwa da cervical cencer, har ma da matsalar saurin kamuwa da ciwon (Balanitis) kumburin saman al'aurar namiji. Da ma sauran cututtukan da ban lissafa ba." Jikin Uwale ba ƙaramin sanyi ya yi ba, Baba Sale ya zube a ƙasa kamar wanda aka zare wa laka ya ce. "Yanzu boka duk wannan bayanan a kimiyance ka karance shi? Shi Ɗan Bishir wannan ruwan da take yi na me ne ne?" Ganin yadda Baba Sale ya ɗaga hankalinsa, ya sa Fadil ya tsugunna a gabansa ya ce. "Ka kwantar da hankalinka Baba Sale, wannan ba komai ba ne In Shaa Allah za a kamo bakin zaren matuƙar aka je asibiti. Rashin kula da tsaftar wurin ya sa infection ya shiga, har ya haifar da zubar wannan ruwan da kake gani. Idan har aka je asibiti za su duba shi, su yi abin da ya dace su ba shi magunguna. Ni ma don dai ina da uzuri, da zan iya yi masa treatment. Amma ba zai yuwu, a bar yaro haka har tsawon lokacin da zan dawo ba. Sannan yana da kyau a kula da tsaftar raunin, kada a bari ƙudaje da wasu ƙwarin su dinga hawa jikinsa; saboda za su iya fesa masa ƙwayoyin cutar da ido ba zai iya gani ba. Rashin kulawa da tsafta, haɗe da takatsantsan zai iya haifar da kamuwar cutuka, har ya haifar da fiye da wannan da muke gani wanda ba ma fatan hakan." "Uwale maza ɗauki Ɗan Bishir mu tafi asibiti, wallahi ni babban tashin hankalina kada ma abin ya guntule ya faɗo ƙasa." Baba Sale ya faɗa cikin hawaye. Fadil ya jima yana ba su shawarwari da ƙwarin gwiwa sosai, sannan suka fito suka shiga mota ya sauke su a asibiti shi kuma ya tafi uzurinsa. Motar Fadil ta fita babu jimawa Mai adaidaita sahu ya sauke Baba Ɗanladi, hannunsa ɗaya riƙe da matarsa ɗayan hannun kuma riƙe da akwati. Sai da ta sauka sannan ya ɗauko musu akwatinan su ya ajiye a gefe. Kuɗi ya zaro ya biya mai adaidaita sahun, ya kamo hannunta yana shirin shiga gida Uzee gaye ya ƙarasa wurin bakinsa a washe kamar gonar auduga ya ce. "Oyoyo jirgin ceto, Oga murfi namu na gargajiya, uban gidan kowanne mai cin mushe. Duk wanda kwaɓarsa ta yi ruwa ya zo a ɗaure masa, ka suturta kuma ka rufa asirin gayu. Ina wanda ya samu 'yar shila ya bige aka samu matsala? In wanda bargon suturarsa yake son yayewa? Ya zo ga mai lulluɓe masa har ya yi bacci. Oga murfi wannan 'yar shilar ita ma zuwa ta yi a kifar da madafun ikonta ne?" Tun da Uzee guye ya fara maganar kan Baba Ɗanladi ya ƙara girma, ya faɗaɗa fara'arsa ya ce. "A dai dinga iya baki Uzee saboda tsaro ba don tsoro ba. Wannan da kake gani ba costomer ba ce, matar da na auro ce." Murmushi ta yi tana jifan Uzee da wani karuwan kallo, wanda kallo ɗaya kawai ya yi mata ya fahimci ita ma 'yar hannu ce. Uzee ya yi ƙasa da murya ya ce. "Wallahi Oga murfi ka zo a daidai, domin yanzu haka akwai wata yarinya da rana ta ƙwace mini. A taƙaice dai cikinta wata biyu kenan, don Allah ka rufa mini asiri kamar yadda ka saba ka ɓarar da shi." Baba Ɗanladi da irin su Uzee suke kira da Oga murfi ya ce. "Ka ga zuwana kenan, ko cikin gida ban shiga ba. Koda zan dawo bakin aiki sai zuwa nan da sati guda, domin shi kansa chemist ɗin yana buƙatar gyara." Uzee gaye ya yi masa godiya, sannan Baba Ɗanladi ya shige cikin gida hannunsa maƙale da na matarsa da yake jin ta kamar tsoka ɗaya a miya. Tun daga harbar gidan mutanen cikin gidan suka shiga yi masa barka da zuwa, sai dai kusan kowa bakinsa ƙunshe yake da magana kasancewar ganin Baba Ɗanladi rungume da wata mace mai zubin 'yan duniya. Amma da yake ba su ga fuska ba, sai kowa ya tsuke bakinsa. "Lale marhabun wa nake gani haka da hantsin nan?" Inno ta faɗa tana washe fuska, turus ta yi ganin Ɗanladi sarƙafe da mace a gefe. Inno ta ƙanƙance ido tana ƙare mata kallo ganin gashin doki ya yi mata yaro-yaro a fuska. "Ɗanladi daga ina ka samo wannan abin?" Inno ta tambaya tana miƙe wa tsaye rai a ɓace. Ɗanladi ya saki murmushin soyayya, ya shafo fuskar matarsa cikin so ya ce. "Inno wannan ita ce matar da na auro ai, so nake sai mun zauna na gabatar miki da ita." Inno ta fara bin ta da kallo, tun daga ƙafa har zuwa tsakiyar kanta. "Baby ina buƙatar hutu ka san na gaji. Mu je ɗaki ka yi mini tausa." Ta furta tana shafa jikin Ɗanladi. Inno salati ta saki tana tafa hannu ta ce. "Yanzu Ɗanladi, ƙaddarar da ka kwaso mana kenan wannan mai zubin alakwankwan ɗin?" Ɗanladi ya sunkuya ya sumbaci matarsa ya ɗago ya cewa Inno, "Wallahi Inno kamar kin sani wannan ita ce ƙaddarata. Jin ta nake har birnin zuciyata. Beb wannan ita ce Mom ɗina, you know i told you Dad ɗina ya jima da mutuwa." Ta ɗago tana taunar cingam ta ce, "Am so sorry Mom, ya kike?" Inno ta saki baki da hanci tana kallon ikon Allah. Jin maganganu a tsakar gida ya sa Mai yasin ya leƙo yana faɗin. "Inno ke da waye ha..." Maganarsa ce ta maƙale, sakamakon haɗa ido da suka yi, lokaci ɗaya wani irin tari ya turnuƙe shi. Daga can ɓangarenta ita ma ido ta zaro, amma sai ta daidaita nutsuwarta ta basar kamar ba ta san Mai yasin don kada su gano su. 'Me ne ne alaƙar wannan yaron da 'yar gwal? Ko dai aurensa ta yi ban sani ba, lallai kuwa dara ta ci gida idan har haka ne.' Mai Yasin ya raya a ransa. Ɗanladi ya zaro mukulli a aljihu, ya buɗe ɗakinsa ya fara jan akwatinansu ya shigar musu da su ciki. 'Yar gwal a wurin ta fara rage kayan jikinta, ta zame mayafinta ta wurga a kan igiya. Ta zamo hular gashin dokin kanta za ta wurga igiya a daidai lokacin Yaya Inu ya shigo cikin gidan, a bisa tsautsayi ta jefa masa a fuska. Warin gashin ya daki hancinsa, a tsantsance ya wurgar da shi gefe rai a ɓace yake kallonta, cikin tsawa ya ce. "Ke! Wace ce ke?" Daga cikin ɗaki Ɗanladi ya ce, "A'a Yaya Inu, kada ka sake ka sake yi wa 'yar gwal tsawa don ba zan lamunta ba." Da mamaki Yaya Inu yake ƙare mata kallo ya furta. "Za ki fice daga gidan nan ko sai na sumar da ke? Kai Ɗanladi, a gidan uwar wa ka samo wannan abar mai zubin surar Fir'auna?" 'Yar gwal ta bi Yaya Inu da kallo a ranta ta raya. 'Ni za ka yi wa barazana? Ai kuwa za ka ga aikin 'yan bariki. Sai na nuna maka sheɗan ne uban gidana ba Fir'auna ba.'' Yaya Inu yana shirin sake magana, 'Yar gwal ta yi wata wawar sufa ya ɗane shi. Na kusa kammala free page In Shaa Allah, ma su son cigaba za su fara payment daga yanzu. 500 Aisha Adam 3090957579 Firstbank evidance ta wannan no ba 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [04/01, 13:36] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITERS ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. *MARUBUCIYAR:* MARWAN JARIRI ASEELA BAƘAR DAULA AN YA BAIWA CE? ƊAN BA ƘARA... SHU'UMAR MASARAUTA DUBU JIKAR MAI CARBI UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA YAWON SALLAR HAJIYA IYA ZAUJATU JINNUL-ASHIQ SANADIN RAGON LAYYA https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻 SHAFI NA SHA ƊAYA "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Ke! Wane irin iskanci kike yi haka? Ba za ki cika ni ba, sai na saɓa miki." Yaya Inu ya yi kalamansa yana kokawa da 'Yar gwal amma fir ta ƙi sakinsa, ta ƙadandane shi sosai kamar mayen ƙarfe. "Ke yarinya, ba ki da mutumci ashe ban sani ba, ba za ki sakar mini yaro ba." Inno ma ta yi maganar tana ƙarasawa wurinsu. Mai Yasin ya gimtse dariyar ƙetarsa, saboda dama a ciki yake da Yaya Inu. Kuma ya san fiye da haka ma 'Yar gwal za ta iya aikatawa. Ganin da gaske 'Yar gwal ba za ta sake shi ba, ya sa ya tattare iya ƙarfinsa da niyyar ya warɓo ta ƙasa, sai ta maƙale shi ƙam a madadin 'Yar gwal ta faɗo sai wata wawiyar tusa ce ta ƙwacewa Yaya Inu. "Subhanallahi! Inusa mene ne haka da sakin tusa?" Mai Yasin ya furta, sannan ya ce. "Ke yarinya kanki ɗaya kuwa? Kamar muna ƙasar kafirai za ki ƙadandane mutumin da ba muharraminki ba." 'Yar gwal ta ɗago tana bin sa da wani irin kallo, sai kawai suka ji ta saki jiki ta faɗi yaraf a ƙasa. Sai a lokacin Yaya Inu ya ja gefe yana kaɗe riga, ya cigaba da wurga mata kallon tsana kamar zai mata duka. "Sannu babyna, ko jikin ne ya dawo?" Furucin Baba Ɗanladi kenan. 'Yar gwal ta fara jera atishawa, Ɗanladi ya ɗago ya dubi Yaya Inu ya ce. "Shi ya sa tun farko na ce babu ruwanka da ita, saboda ni na san aljanun jikinta ba sa nisa da ita. Ina zaman zamana za ka rikita mini mata babu gaira babu dalili." Ɗanladi ya ƙarasa maganar yana ɗaukar 'Yar gwal ya shige ɗaki da ita. Inno ta shiga share hawaye ta ce. "Inusa yaushe ɗan'uwanka ya yi lalacewar haka? Wai Inusa saboda ya mayar da mu ba komai ba a wurinsa, har shi zai je wani wuri ya aurar da kan shi. Inusa ba za ku yi wani abu a kai ba?" Yaya Inu da ya gama cika da mamaki ganin ƙiri-ƙiri 'Yar gwal ta raina musu hankali ya ce. "Inno kin fi kowa sanin wane ne Ɗanladi, tun da rayuwar da ya ga ta fiye masa ba sai ya yi ba." Daga cikin ɗakin Ɗanladi ya ce. "Inno yanzu auren da na yi ne ba za ki saka mini albarka ba? A da kuna yi mini ƙage, kuna cewa ina lalubar yaran mutane a chemist ɗina. Amma yanzu kuma na yi auren ma ba za ku sarara mini ba? Sunnar Annabin ce kuke ƙyashi na raya?" 'Haƙiƙa na lura duk balaja'un Inusa ashe shi shafar mai ne a kan wannan. Tirƙashi, wannan Ɗanladin ai ya gama tashin kaina.' Mai Yasin ya raya a ransa. Yaya Inu ya kamo hannun Inno ya furta. "Mu je Inno, idan kika biye ta wannan yaron ranki ne zai yi ta ɓaci a banza. Yanzu mu je ciki ni ba wannan ce damuwata ba, wani tashin hankali ne yake tafe da ni da na garara samun nutsuwa." Inno ba ta musa ba, ta bi bayan Yaya Inu suka shiga ɗaki. "Inno ɗazu Abu ta zo, ta kawo mini jaririyar da ta haifa..." "Amma dai wannan yarinya an yi marar mutumci, yanzu ita saboda rashin hankali daga haihuwar yarinyar za ta ɗauko ta kawo maka? A kanta aka fara mutuwar aure?" Inno ta katse shi tun bai ƙarasa magana ba. "Don Allah Inno ki bari na dire maganata." Inno ta yi fakare tana jiran ya gama magana ta ɗora daga inda ta tsaya. "An samu matsala domin yarinyar zabiya ce. Ni kuma gaskiya ina zargin ba 'yata ba ce, saboda kowa shaida ne ban taɓa haihuwar zabiya ba." A razane Inno ta ja da ba ya tun bai gama magana ba, ta fara dubansa da wani kallo sannan ta ce. "Kada ka raina mana hankali Inusa, batun ka ce 'ya ba ta ka bace ai bai taso ba. Saboda kowa ya san ta yadda ake samun zabiya, sai da ka je ka gama saɓon Allah sannan za ka same ni kana yi mini 'yar murya? Me zan iya yi maka a yanzu? Bayan Allah ya yi ikonsa, ai sai dai ka ɗauki na Annabawa. Ka je can kai da Zainabun ku yi ta istigifari kuna tuba ga Allah." Inno ta yi maganar tana miƙewa, har za ta shige uwar ɗakinta ta waigo ta ce. "Yawwa dama daga yanzu kada ka sake ka shigo mini. Saboda kada zunubin da kuka kwaso Allah Ya jarabce ni da shi." Tana gama maganar ta shige ciki. Kamar Yaya Inu zai ɗora hannu a ka, haka ya fice daga sashen Inno abin duniya ya haɗe masa. Yamma ce sakaliya, sanyin la'asar tuni ya riga da ya sauko. Fadar Mai gari cike take da mutane ana zaune ana zaman fada. Mafi yawan mutanen da suke zaune gulma ce ta kawo su, a kan abin da ya faru da Mai gari. Shi ma da yake ya fahimci haka sai ya tsuke fuska, ya dubi su Mahmud da suke takure kamar zakarun da aka tsamo daga ruwa ya ce. "A madadinmu da na talakawan yankinmu muna yi muku barka da zuwa. Muna buƙatar ɗayan bayan ɗaya, ku gabatar da kanku a gaban mutane. Mudassir ne ya ɗan muskuta zai yi magana, Mai gari ya yi wa Mahmud ƙuri da ido ya ce. "Kai yaro, kamar na san fuskar nan taka?" Cikin Mahmud ya karta, amma sai ya yi ta maza ya ce. "A'a ranka shi daɗe, sai dai idan mai kama da ni ka sani. " Jin Mai gari ya yi shiru ya sa Mudassir ya furta, "Ni dai sunana Mudassir Najib, ɗaya daga cikin ɗaliban da aka turo daga babbar Jami'a yin bautar ƙasa (NYSC)." A fili Mai gari ya faɗaɗa fara'arsa yana jinjina kai, saboda ya ji ya ce bautar ƙasa suka zo don haka sai ya ci banza. Har ya fara lissafa kansa, a sahun mahajjatan da za su sauke farali a bana. Duba da irin aikin gonar da ya ayyana zai jibga wa su Mudassir. Shi ma Mahmud ya gabatar da kansa, sannan Mai gari ya fara baza babbar yana haɗe rai ya ce. "Tun da har Gwamnati ta aiko ku garin nan, na tabbata babbar Masarauta ƙasar nan ta san irin gudunmawar da nake bayarwa a ƙasata. A don haka, ya zame muku wajibi ku zage damtse ku yi mini noma yadda ya kamata." Mai gari ya zaro ido waje cike sa barazana ya sake dubansu ya ce. "Ku dube ni nan, bautar ƙasa ba wasa ba ce yara ina fatan kun gane. Domin shinkafar da kuke miƙe ƙafa kuke ci, ita ma sai da aka gama bauta mata sannan ta bauta muku a cikinku. "Ammm amma ina ganin kamar ba ka fahimce mu ranka shi daɗe. Service muka zo fa, ga wannan takardar za ka iya karantawa." Mahmud ya ƙarasa maganar yana miƙa masa takardar. Gaban Mai gari ya faɗi, da ya ga ya miƙa masa wata zungureriyar takarda mai cike da rubutun turanci. Sai da ya fakaice su ya sharce gumin fuskarsa, sannan ya riƙe takardar yana ɗan matse idanu ya fara karantawa. "Assalamu Alaikum. Ni Mai girma gwamna, na aiko waɗannan jajirtattu kuma haziƙan ɗaliban nan, domin su zo garin nan su taya Mai gari aikin gona wanda muke kira da bautar ƙasa. Kuma a don haka, muke jan kunnensu domin su jajirce wurin yin aiki tuƙuru. Idan ba haka ba, za mu zartar musu da mummunan hukunci." Mai gari ya ɗago yana muzurai, daga can ƙasa ya ga wani rubutu da lambar waya har da saka hannu, sai ya ce. "Ga lambar wayata nan ni mai girma gwamna, duk wani ƙorafi da kuke da shi kai tsaye za ku iya tuntuɓa ta. Kuma duk wanda ya yi ba daidai ba a cikinsu, muna bayar da umarnin Mai gari ya saɓa masa. Idan da hali ma ya ci tararsa." Tun da ya fara jawabin Mahmud da Mudassir, suka yi zuru suna kallonsa cike da mamaki. Mutanen da ke wurin suka ɗauki sowa cikin kambaba Mai gari suka ce. "Allah Ya ja zamaninka mai martaba. Haƙiƙa gado ba karanbani ba, duk wanda ya san gidanku ya san mane ne mulki." Mai gari ya fara zuba doro yana kalle-kalle cikin izza. Hambali da yake gefe cikin tsananin jin kunya ya ce. "Allah Ya taimake ka, idan na fahimce su fa kamar ba haka suke nufi ba. Duk da dai ni ma ba karatu na yi mai zurfi ba, iya ka ta diploma. Idan aka ce an tura ɗalibi NYSC wato bautar ƙasa, ana nufin ya hidimtawa ƙasa ta hanyar bunƙasata da ciyar da ita gaba. Kuma kamar wani ƙarin horo ne, da ɗalibai suke sake gogewa; domin su zama shugabanni ko al'ummar da za a yi alfahari da su a gobe. Amma a gafarce ni ranka shi daɗe, idan na faɗi ba daidai ba." Tun bai gama magana ba Mai gari ya fusata. Rai a ɓace ya nuna Shazali ya ce. "A kanannaɗe shi a hukunta shi, mu zai kawowa raini a gaban fada? Shazali, yaron nan yana nufin fada ba ta san me take yi ba

Chapter 32 of 35