ce.
"Ta ina za ka san abin da ya faru? Tun da ka saka mace a ɗaki kamar a kanta ka fara sanin mace." Ko kaɗan bai ji daɗin furucinta ba, saboda ko babu komai yaransa suna tsaye suna kallonsu.
Rai a ɓace ya ce, "Wai me yake damunki ne Bilkisu? Wacce irin maganar banza kike yi haka a gaban yara ne?"
"Ƙarya na yi? Ba macen ka saka a gaba ba? To duk jarabarka sai ka fito ka kai yara makaranta."
Bilkisu ta faɗa cike da kishi. Waigawa ya yi ya hangi yaran duk sun yi zuru-zuru, kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci a tsorace suke. Ga su sanye da uniform da kulolin abinci, girgiza kai ya yi a ransa ya ayyana tabbas Bilkisu ba ta cikin nutsuwarta.
"Dama suna zuwa makaranta ranar asabar ne? Ko kin manta yau asabar?" Shiru Bilkisu ta yi cike da kunya, jin hayaniya ta yi yawa ya sa Amina ta ɗan turo ƙofar ta leƙo. Kanta babu ɗan kwali ta sha ƙananan kitso mai kyau, ta yafa zanin rufa a jikinta.
"Ina kwana Aunty."
Ta furta a sanyaye, wani mugun kallo Bilkisu ta wurga mata kamar tana jira ta ce.
"Kada ki sake ce mini Aunty, ni ba yayarki ba ce. Me na haɗa da ke? Ai ƙanwata ba za ta taɓa auren mijina ba." Waigawa Hafiz ya yi ya ce.
"Koma ciki."
Babu musu Amina ta koma ciki, ya riƙe hannun Bilkisu ya kai ta ɗaki ya zaunar a kan kujera. Ƙasa ya yi da murya ya ce.
"Haba Bilkisu, me ya sa duk maganar da nake yi miki ba kya ji ne? Don Allah ki kama girmanki, ba na son ki dinga abin da yarinyar nan za ta zo ta raina ki. Yanzu don Allah me kika yi haka? Kin fa san yau weekend, yaran nan ba sa zuwa makaranta."
Idon Bilkisu ne ya ciko da ƙwalla ta ce, "To ai mantawa na yi." Hannu ya saka ya goge mata hawayen, zai miƙe ta sake cewa.
"Yanzu shi kenan kuma ka daina sona." Shiru ya yi cike da damuwa, ya girgiza mata kai ya ce.
"Idan ana mata ɗari ko fi, duk wacce zan auro ba zan daina sonki ba Bilkisu. Don Allah kada ki sa wannan a ranki, kin taɓa ganin namiji ya zauna da macen da ba ya sonta?" Girgiza masa kai ta yi ta ce.
"To amma ai ga shi nan ka je ka kwanta da wata, shi kenan ta gama gane mini sirrinka."
Murmushi ya yi don ya san kishi ne duk yake damunta, ya matsa kusa da ita ya ce.
"Ke ce fa uwargida, ko kin manta ni da ke auren saurayi da budurwa muka yi? Duk wacce zan yi mu'amala da ita fa a bayanki ne, kuma da kike faɗin haka ita ma fa matata ce. Ba wurin macen banza na je ba, ko kin fi son na fara biye-biye a waje da na yi auren?" Girgiza kai ta yi, ya zauna ya cigaba da lallashin Bilkisu har sai da ya ga hankalinta ya ɗan kwanta sannan ya tafi ɗakin Amina.
A wannan ranar Hafiz ya ɗauka Bilkisu za ta yi abincin safe da su, bayan da suka yi wanka ya fito ya tambaye ta kai tsaye ta ce ba ta girka da su ba, tun da ba ita ce da miji ba. Gudun tashin tarzoma ya sa shi fita ya sayo musu shayi a waje, saboda ba a haɗa gas ɗin Amina ba. Sai da suka karya sannan ya ɗauki silindarta ya tafi da ita ya ciko mata, a lokacin da ya dawo 'yan'uwan Amina sun zo da wasu tsirarin danginsa. Bilkisu kuwa tana ɗaki ko ƙurarsu ba ta bi ba, don gabaɗaya dangin Hafiz ya shafa musu kashin kaji.
Yamma liƙis Hafiz ya kawo kayan miya ya ce Bilkisu ta gyara, a nan ma ta kafe kai da fata ta ce ba za ta yi girki ba. Idan kuwa ta sarrafa ba za ta ba shi da amaryarsa ba, babu yadda ya iya haka ya kai wa Amina. A lokacin da ya shiga ɗakin, zafi ya ji a jikinta na zazzaɓi saboda rashin ƙwarin jiki, tausayi ta ba shi sosai. Don haka ya rage kayan jikinsa ya gyara kayan miyar ya ba wa yara suka kai markaɗe, da kansa ya ɗora miyar ganin haka ya sa Amina ta miƙe cike da rashin ƙwarin jiki za ta taya shi ya ce ta je ta kwanta. Cikin lokaci ƙanƙani ya ƙarasa miyar, ya ce Bilkisu ta dafa taliya sai da ƙyar ya samu ta dafa ta miƙa musu.
Tun daga wannan ranar Amina ta karɓi girkin rana da na dare, na safe ne kawai kowa yake yin na sa. Abin da Bilkisu ta tsira a cikin kwanakin amarcin Amina sai gari ya waye sai ta yi wa yaranta wanka da sassafe ta saka su, su shiga ɗaki wurin mahaifinsu. Wani lokacin ma idan suka shiga suna kwance a kan gado, haka Amina za ta sako hijabi ta janyo su falo. Babu wata dama da suke samu ta kulawa da juna da safe ko da rana, matuƙar yaran suna gida. Idan kuma yaran ba sa nan Bilkisu ta dinga yi musu habaici ta cewa Hafiz ya cika jaraba, ko ta ce ya auro makira mai karuwancin cikin gida. A haka suka cigaba da tafiya tun abin ba ya damun Amina har abin ya fara damunta, saboda akwai lokacin da rana Hafiz ya dawo suna ɗaki duk da sun tura ƙofa sai ji suka yi yara sun shigo ɗakin da suke kwance.
"Lah Abba."
Sayya mai kimanin shekara uku ta faɗa ganin mahaifinta yana mu'amala da Auntynsu.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buɗe a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!😍
‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah!
MG’s Beauty Lounge ya buɗe da kwalliya, tsafta da ƙamshi irin na sarauniyar zamani!
Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:
Gyaran gashi da kitson zamani
Kwalliyar Sallah mai ɗaukar ido
Wanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya rai
Kayan gyaran fata na gaske
Lalle mai kyau da salo na zamani
Tura-turai, humra, incense da ƙamshi masu daɗi
Shirin amare da na musamman
Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya.
Zo ki ji daɗin wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai kyau.
Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.
Tambaya/Booking:
WhatsApp: 08062991549
Kira: 09016108092 / 08064532391
Ki zo ki gani da idonki – ki ji daɗin sauyin MG’s Beauty Lounge.
Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge
SHAFI NA BIYAR
A razane Amina ta ja bargo ta rufe jikinta, haka shi ma Hafiz cikin sauri ya janye jikinsa daga jikin Amina haɗe da rufe jiki. Ya haɗe fuska tamau cikin tsawa ya ce.
"Fita daga nan."
Ganin yadda mahaifinta ya birkice lokaci ɗaya ya sa ta fita da gudu tana kuka, miƙewa Hafiz ya yi yana suturce jikinsa. Bai yi aune ba sai ji ya yi Bilkisu ta banko ƙofar ta shigo cikin masifa tana faɗin.
"Uwar me Sayyada ta yi miki kika dakar mini ita take kuka, baƙar munafuka kin san ba kya ƙaunarsu kika maƙale saboda kwantan da kika yi kika auri mahaifinsu." Ganin Amina ba ta falo ya sa Bilkisu ta faɗa ɗakin za ta yi magana ta ci karo da su suna gyara jikinsu, wani baƙinciki ne ya maƙure ta. Cikin zafin kishi ta ce.
"Wannan wacce irin jaraba ce da rana tsaka salon ku ɓa ta mini tarbiyyar..."
"Fita ki ba ni wuri ba na son rashin hankali."
Hafiz ya katse ta a zafafe, yadda ya hautsine mata ya sa ta ja ƙafa ta fita don ta lura ransa a matuƙar ɓace yake.
Amina da ke zaune a gefen gado kifa kanta ta yi ta fashe da kukan takaici, jiki a sanyaye ya ƙarasa ya rungumo ta ya ce.
"Don Allah ki yi haƙuri Amina."
"Habibi na gaji, wallahi na gaji da abin da matarka take yi mini. Yanzu wanne irin abu ne a ce ni da ɗakina ba ni da sirri, ina kwance da mijina dubi yadda 'yarka ta zo ta same mu? Wanne irin kishi matarka take da shi, da har ta gwammace gara ta ɓata tarbiyyar yaranta? Wallahi matuƙar ba za ka ɗauki mataki ba ba zan cigaba da zama a haka ba." Amina ta ƙarasa maganar tana zubar da hawaye. Ya sani sarai Amina tana da haƙuri, don akwai abubuwa da dama da idan ya ga Bilkisu ta yi mata ya san idan ita ce ba za ta yarda ba. Cikin lallashi ya ce.
"In Shaa Allahu haka ba zai sake faruwa ba, don Allah ki yi haƙuri babyna." Hawayenta ta share tana gyaɗa masa kai, bakinta ya sumbata. Ya janyo ta yana yi mata raɗa a kunne, turo baki gaba ta yi a shagwaɓe ta ce.
"Ni a'a, ba yanzu ba." Marairaicewa ya yi kamar zai yi kuka ya ce.
"Please, ai ba laifina ba ne da za a hukunta ni. Kuma kin san dai ba zan iya..." Sai kawai ya kashe mata ido ɗaya, ɗauke kai ta yi ta alamar fushin wasa ta ce.
"Kuma hakan za ka haƙura ka bar wa dare, wai dama haka idonka yake a buɗe amma kafin aurenmu kullum sai ka yi ta sunne kai ƙasa." Dariya ya yi sosai ya ce.
"To wancan lokacin da yanzu akwai bambamci ai, ni dai gaskiya ki san yadda za ki yi da ni." Hararar wasa ta yi masa, sannan suka cigaba da ba wa juna kulawa.
A tsammanin Bilkisu tun da ta katse musu yanayin da suke ciki ta wargaza musu na wannan lokacin, ta ɗauka Hafiz zai fito ya same ta da maganar ta yadda za ta ja shi da faɗa har ya ɓata lokacin a wurinta. Jin shirunsu a ɗaki ya sake ɓata mata rai, don haka ta koma ɗaki ta cika fam da ɓacin rai. Tana nan zaune ta hangi Amina ta fito ta shiga banɗaki, tana wuce babu jimawa shi ma Hafiz ya rufa mata baya. Cikin suɓutar baki ta ce.
"Kan babban bala'i, wato ni za a gwadawa bariki ido biyu da rana. Hafiz saboda ya wulaƙanta ni har wankan ma tare za su shiga?" Tana rufe baki sai hawaye ya fara zuba, don rabonta da shiga banɗaki tare da Hafiz tun Sayyid yana ƙarami. Tana nan zaune ta ga Amina ta fito, bayan wani lokaci shi ma Hafiz ya wuce ɗakin Amina. Sai da ya shirya cikin ƙananan kaya sannan ya fito hannunsa riƙe da wayar caza, ya ƙarasa ɗakin yaran da suke wasa. Hannun Sayyada ya kama duka biyun ya riƙe wuri ɗaya, ya shiga zabga mata wayar cajar a ƙafa da sauran jikinta. Nan take 'yan'uwanta duk suka takure wuri ɗaya cikin jin tsoro, don sun ɗauka yana gamawa zai koma kansu. Jin kukan Sayyada ya sa Bilkisu ta fito fuuu a fuskace ta kai hannu za ta janye ta. Da wata irin muryar ɓacin rai ya ce.
"Idan kika taɓa mini 'ya ina dukanta wallahi sai kin tafi gidanku a yau." Janye hannunta Bilkisu ta yi, saboda duk abin ta tana matuƙar son Hafiz, koda wasa ba ta son wani abu da zai raba ta da shi. Kiran sauran yaran ya yi ya haɗa su wuri ɗaya, fuska a haɗe ya fara magana.
"Daga yau sai yau duk wanda ya kuma shiga ɗakin mamanku ko ɗakin Aunty amarya, ba tare ya yi sallama ba sai na farfasawa mutum jiki. Sannan zan haɗa ku gabaɗaya, na kai can bolar bayan gari na watsar. Idan ya so nan gaba sai mamanku da Aunty amarya su haifo mini wasu yaran." A tsorace duk suka gyaɗa masa kai, cikin tsoratarwa ya buga musu tsawa da cewar.
"Kun ji me nace ko? Kuma idan kuka yi sallama sai kun ji an amsa an ce ku shigo, idan ba haka ba wallahi dukan da zan yi wa mutum sai ya fi wannan." Baki yana rawa yaran suka amsa, ya ɗauko alawa ya damƙa wa kowa a hannu sannan ya lallashe su cikin nasiha ya tashi ya fita.
Ɗakin Bilkisu ya shiga, saboda tun da ya yi mata magana ta yi zuciya ta fice ta tafi ɗaki. A zaune ya same ta ta haɗe fuska, shi ma fuskar ya sake haɗewa ya ce.
"Bilikisu!"
Shiru ta yi masa ba ta amsa ba, ya dube ta ya cigaba da cewa.
"Ba zan zura ido ki lalata mini tarbiyyar yara ba, saboda kishin rashin hankalin da kike yi, daga yau sai yau idan kika kuma tura mini yara ina ɗakin Amina ba tare da ƙwaƙƙwaran dalili ba sai ranki ya ɓaci. Ni ba hana su shiga ɗakinta zan yi ba, amma ke ma ki san lokacin da za ki dinga tura su. Wai duk wannan abin da kike yi na mene ne? Ba dai don kana da na yi mu'amala da ita ba ne? To me ya yi saura yanzu? Na fahimci duk karar da nake yi miki da mutumtawar da nake yi miki ba kya gani. Bari ki ji, yadda kike matata haka Amina take a wurina duk matsayinku ɗaya, yadda kika san ni a matsayina na mijinki haka ita ma ta san ni. An faɗa miki kishi hauka ne? Ke wanne irin abu ne ba ki yi ba a lokacin da yayanki zai ƙara aure, ba ke ce amara ba har da ɗauko auko? Amma a kaf dangina wa ya taɓa zuwa gidan nan ya nuna miki yana farinciki da auren da zan yi, duk suna yi ne don su yi miki kara ba wai don ba sa so ba ne.
Wallahi tun wuri ki dawo hayyacinki, ina faɗa miki haka ne tun ba ki ƙure yarinyar nan ba. Idan kika buɗe mata ido nan gaba ba za ki ji daɗin zama da ita ba."Hafiz yana gama magana ya fice daga ɗakin rai a ɓace.
Wannan faɗan da Hafiz ya yi wa Bilkisu da yaransa su Sayyada, shi ya sa Amina ta samu 'yanci sakata ta wala a ɗakinta. Don idan Hafiz yana nan, tana samun damar saka ƙananan kayanta masu jan hankali da rigunan bacci. Saɓanin a baya da take saka manyan kaya, gudun kada yaran su shiga su ga shigar da ba ta dace a jikinta ba.
A ranar da Hafiz zai koma ɗakin Bilkisu tun safe take cikin annshuwa tana walwala. Hatta Amina da ba wata hirar suke yi ba, ta fahimci walwlarta. Tana zaune bayan la'asar ta ji sallamar Aunty Murja da Na'ima, duk da Amina ba ta sansu ba amma fuska a sake ta amsa sallamarsu tana yi musu sannu da zuwa. Fuska a sake su Aunty Murja suka amsa mata, suna cikin gaisawa Bilkisu ta leƙo a fusace ta ce.
"To tsaiwar me kuke yi Aunty Murja ku shigo mana." Ƙarasawa suka yi ɗakinta, sai da suka gaisa Aunty Murja ta ce.
"Oh ashe kuma haka abu ya faru Bilkisu, ni ai ina zaune rannan katsam Abban Sajida yake faɗa mini wai Hafiz zai yi aure. To daga baya kuma na ji an ce ba za ki yi wuni ba, don dama cewa na yi zan zo ƙafa da ƙafa. Da muka ji ba wuni sai kawai na cewa Auntyn yara ta bari ma zo daga baya." Taɓe baki Bilkisu ta yi ta ce.
"Tsinanniya gata can ai, an kawo ta baƙar daga. Sai ta zo ta ci uwar da nake ci." Aunty Murja murmushi ta yi, ta tuna irin habaici da cin kashin da suka dinga yi mata. Sai kawai ta ce.
"Allah Ya haɗa kanku, ya sa zuwanta alheri ne."
"Haba Aunty Murja, kin taɓa ganin zuwan kishiya ya zama alheri?" Bilkisu ta faɗa cikin sauri, sunkuyar da kai Na'ima ta yi. Aunty Murja ko kaɗan ba ta ji daɗi ba saboda Na'ima tana wurin, don haka ta miƙe ta ce.
"Mu bari mu wuce yawon namu da yawa, za mu leƙa barka matar yayan Auntyn yara ce ta haihu."
Mamaki ne ya kama Bilkisu ganin yadda Aunty Murja ta ɗauki kishiya kamar wata ƙanwarta. Har soro ta raka su, Na'ima ce ta fara fita. Cikin sauri Bilkisu ta kamo hannun Aunty Murja ta ce.
"Aunty Murja wai kishiya kike yi wa wannan haba-habar? Salon kina zaune ta zo ta raba ki da mijin? Ai wallahi ni da kishiya sai dai kallon banza." Murmushi Aunty Murja ta yi ta ce.
"Ya danganta da irin kishiyar da kike da ita Bilkisu, ita kishiya kana karantar yanayin yadda ta zo ne. Idan ta zo da arziki ku yi shi, idan kuma da tsiya ne sai ki kama kanki. Ni ba abin da zan cewa Na'ima, saboda zuciya ɗaya take tare da ni da yarana. Yanzu haka zancan da nake yi miki Nimrah ta koma hannunta, kema ki karanci taki kada ki cuce ta. Ki zauna ke da ita zuciya ɗaya, sai ki ga zamanku ya yi daɗi."
Ajiyar zuciya Bilkisu ta sauke, tana jin magnar Aunty Murja kamar busar sarewa. Daga ɗan waje Na'ima ce ta leƙo ta ce.
"Aunty kin san dai halin Abban Sajida, wallahi idan muka yi dare ke zan ɗorawa laifi. Ko kuma na kama hanya na yi gaba sai kin taho." A gaggauce Aunty Murja ta yi wa Bilkisu sallama tana dariya ta ce, "Wallahi ki ɗora mini laifi, ni ma sai na faɗa masa laifin jiya da na rufa miki asiri." Na'ima ta yi dariya suka tafi.
Kwana biyu gidan Hafiz lafiya ƙalau ake zaune, saboda a ɗakin Bilkisu yake. Koda Hafiz ya koma ɗakinta, babu wani canji da ya nuna mata. Hasali ma duk don ya faranta mata, haka ya dinga santin girkinta da duk wani abu da ta yi masa. Shi kansa ya ji daɗi sosai ganin yadda ta watsar da komai, duk da ba wata doguwar mu'amala suke yi da Amina ba. Amma babu wani abin faɗa ko baƙar maganar da take haɗa su, haka daga ɓangaren Amina ta ji kewar Hafiz da zai bar ɗakinta. Amma hakan bai sa ta yi wata muguwar kissa ko ɓacin rai ba, hasali ma ta rungumi su Sayyada hannu bibbiyu. Don haka take jan su ɗaki su yi ta wasansu a cen.
Tun a safiyar ranar da Hafiz zai koma ɗakin Amina Bilkisu take haɗe rai, da Magariba ta yi Amina tana gama girki bayan ta shiga wanka Bilkisu ta saci jiki ta shiga ɗakin Amina. Cikin sauri ta buɗe galan ɗin fetir ɗin da Hafiz yake sayan mai da shi, ta ɗebi kaɗan ta yaryaɗa a cikin kular abincin. Da sauri ta fito ta koma ɗaki zuciyarta fes, bayan wani lokaci ta ji ƙarar mashin ɗin Hafiz ya shigo cikin gidan. Dariya ta fara ƙyaƙyatawa har riƙe ciki, ta jikin labule ta hango Amina ta fito cikin tsaleliyar atamfa. Ta ƙafa ɗaurin ɗankwali ba ƙaramin kyau ya yi mata ba. Yana saukowa daga kan mashin Amina ta rungume shi, fake ta sakarwa kumtunsa. Ya saka hannu ya riƙo ƙungunta ya ce.
"Wannan wankan zai sumar da ni."
Murmushi ta yi tana fari da ido ta ce, "To ni kuma na yi yaya kenan?"
"Sai ki farfaɗo da ni." Ya faɗa yana murmushi, ledar hannunsa ta riƙe suka shiga ɗaki. Yana shiga ɗakin, ya cire hula ya ajiye sannan ya fito ya shiga ɗakin Bilkisu.
Gaisawa suka yi ya tambayi yaran, babu yabo babi fallasa ta ba shi amsa sannan ya fita. Yana fita ta sake sakin dariyar ƙeta, tana jiran sakamakon abin da ta aikata.
GIDAN ALHAJI UMAR
Jin abin da Ahaji ya faɗa ya sa Shukura ta sake kwaɓe baki ta ce.
"Gaskiya ni dai tsoro nake ji baby, wallahi ba zan iya kwana a ɗakin nan ba kada a sake shigowa."
Shiru Daddy ya yi, sai ya nufi ɗakin su Haidar ya ce.
"Kai Haidar a cikinku akwai wanda ya fito waje ne?" Sun fahimci sarai inda maganarsa ta dosa, amma gudun ɓacin ransa ya sa suka ce masa a'a. Komawa ya yi wurin da ya bar su Shukura, ya dubi Hajiya Karima ya ce.
"Ke ki je ɗaki Hajiya, zan zauna da ita zuwa nan da sallar asuba." Da ido Hajiya Karima ta bi shi, saboda ɓacin rai ko tanka masa ba ta yi ba ta nufi ɗaki zuciyarta tana suya. Cikin ɗaki Shukura ta shiga, Daddy ya rufe mata baya. Suna shiga ta shige jikinsa, tana runtse ido alamun tsoro take ji. Sannu a hankali yanayin salon zaman da suke yi ya sauya. Shukura ta shiga aika masa da saƙonni masu birkitarwa, ko kaɗan Daddy bai yi niyyar biye mata ba. Amma yanayin saƙon da take aika masa ya sa shi yi wa zuciyarsa biyayya, ya shiga mayar mata da martani. Jin Shukura tana ƙoƙarin kai shi matsayar da bai yi niyya ba, ya sa shi ɗagowa cikin wani irin yanayi ya ce.
"Baby mu bari sai na dawo nan ko?" Cikin kissa Shukura ta fashe masa da kuka tana narkewa a jikinsa ta ce.
"Amma ai ni ba haramun ba ce a wurinka, wai dama haka za ka dinga wulaƙanta ni ban sani ba." Yadda ta ƙarasa maganar tana haɗe jikinsa da nata ya sa jin wani abu yana fisgarsa a kanta, ya sunkuya ya laso hawayenta cike da so ya ce.
"Ba na son kukanki baby."
"To ni idan ba ka so ka daina hana ni." Ta furta tana sake aika hannunta cikin jikinsa. Cikin kissa da kisisina Shukura ta cigaba da sarrafa Alhaji har sai da suka biyawa juna buƙata, sai daga baya duk ya ji bai ji daɗi ba. Ko babu komai ya san wannan lokacin na Mommyn Mami ne. Shukura da gayya ta fita ta ɗora ruwa a tukunya, tamkar rana haka ta dinga buga tukunyar lokacin da za ta ɗebi ruwa. Sai da ta ɗora musu sannan ta koma ɗaki ta narke a jikin Daddy.
Hajiya Karima tana shiga ɗaki ta haɗa kai da bango saboda damuwa, ba ta yi tsammani ba sai ji ta yi hawaye yana bin idonta. Babban abin da ya fi ɓata mata rai, yadda ake ƙoƙarin yi wa 'ya'yanta sharri amma ƙiri-ƙiri Alhaji ya turbuɗawa idanunsa toka ya bi bayan matarsa.
"Dama akwai ranar da Daddyn Mami zai fifita mace a kan 'ya'yan da na haifa? Innalillahi wa inna'ilahir raji'un." Ta furta domin ta samu zuciyarta ta yi sanyi. Kwanyarta ce ta tushe, zuciyarta duk babu daɗi. Don haka ta miƙe ta fita domin ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar nafila ko ta ji daɗi a ranta, tana fita ta nufi banɗaki don ta kama ruwa a nan ta ji motsin ruwa alamun ana wanka. Tana shirin komawa ɗaki ta ga Shukura ta fito, hannunta riƙe da na Daddy daga shi sai towel a ɗaure a ƙugunsa. Wani abu ne ta ji ya daki zuciyarta, sai ta yi kamar ba ta gansu ba. Ta shiga banɗaki ta kama ruwa sannan ta ɗauro alwala, ta nufi ɗakinta tana jin wani irin ɗaci a ranta.
Shukura daɗi ta ji a zuciyarta, duk da ta ga Daddy duk ya birkice. Doguwar riga ya zura ya nufi ɗakin Mommy cike da sanyin jiki, a
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 35