kallo kamar tana som gano wani ɓoyayyan abu daga jikinsa. Shafa jikinta take yi don ta tabbatar ba mafarki take yi ba, ta saka hannu ta mintsini cinyarta jin zafin ya ratsa wurin ya sa ta tabbatar da zahiri ne. Tana kallo Kabir ya kashe wayar gabaɗaya, jikinsa gar rawa yake ya ɗebo kayan shimfiɗa ya yi wa yaran. Yana gama shimfiɗar ta ga ya ɗauki wayarsa ya fice daga ɗakin alamar fita ma zai yi daga gidan gabaɗaya.
Tun da ya fice Fauziya take saƙa da warwarar hukuncin da za ta yanke, ban da kai wa da kawowa babu agim da take yi. Hat yanzu zuciyarta rawa take yi a kan ko dai idanu da kunnuwanta ba su jiyo mata daidai ba. Babban abin da ya sake ɓata mata rai, yadda ta ga ya ɗauki wayar ya fice daga gidan wato duk ma abin da za ta yi ta je ta ƙarata. Ta jima tana ƙoƙarin dakatar da hawayen idonta, amma ta kowanne ɓangare ya gagara ba ta haɗin kai.
Shinshina jikinta ta fara yi tana son gano ta inda ta gaza, ta ɗaga rigarta tana kallon mamanta ko za ta ga hango aibun na jikinta. Domin Allah ya yi mata baiwa duk da haihuwarta uku ga ta huɗu za ta yi amma mamanta bai lalace, ballantana ta ce ko nata ne suka zube har yake hangen na wasu. Kuma idan ma lalacewa suka yi a tsawom shekaru bakwai da aurensu bai ci ace ya ɓoye mata ba. Har gara ya faɗa mata domin ta san matakin gyaran da za ta ɗauka. Ta matsa gaban madubi tana bin kanta da kallo, sai dai har ta gaji da tsaiwa ba ta gano makusar da za ta sa Kabir ya dinga musayar munanan kalamau da hotuna da 'yanmata.
Gajiya ta yi da tsaiwar ta zauna a gefen gado, sai ta shiga tausayin kanta da 'ya'ya matan da ta haifa.
"Wannan wacce irin rayuwa, aai yaushe zan sanu kwanciyar hankali? Sai yaushe zan samu nutsuwa kamar kowa? Sai yaushe..."
Wani sabon kukan ya sake ƙwace mata, a wannan ranar da take jin kamar zuciyarta za ta yi fiffike ta ɓullo daga ƙirjinta, ba ta shayi ko kunyar bayyana kukanta a sarari domin gurin ɗabi'u da halayen Kabir ba a ranar suka fara yi mata ba. Kamar kuwa Fauziya ta sani, su Ai'lo da ke ɗaki duk sun kasa kunne suna son gano dalilin kukan nata. Don sun san fa wuri ya dawo gida ba a buge ba, ballantana su ce takaicin rashin dawowarsa ne ya saka ta kuka.
Lawisa da ke ɗaki har sun kwanta ita da mijinta ta gagara haƙuri, ta fito zuwa ƙofar ɗakin Fauziya.
"Maman Na'ima! Maman Na'ima ke jaɗai ce zan iya shigowa?"
Fauziya da muryarta ta gana dacewa ta ce, "Shigo ni ɗaya ce."
Tana shiga ɗakin ta ɗan ƙasa fa murya ta ce, "Me yake faruwa MamAn Na'ima? Tun ɗazu nake jiyo kukanki lafita kuwa?"
Ta san Lawisa tana ƙaunarta tana ba ta kulawa, amma wannan wani gingimemen sirrin mijinta ne da ba za ta iya furta mata ba.
"Mahaifiyata na tuna Lawisa, mahaifiyata cw ta faɗo mini. Akwai abubuwa da dama da nake ganin iyaye mata suna yi wa 'ya'yansu Lawisa na rasa wannan gatan. Ban san wa zan raɓa na ji danshi da sanyin mahaifiyata."
Jikin Lawisa ya yi sanyi, da jin kalaman Fauziya. Domin ta taɓa ba ta tsakure kaɗan daga cikin labarinta, da irin baƙar wahalar da ta sha a hannun matan babanta. Sai ta yi tsammanin ko wani abin suka yi mata bayan ta je gidan, don haka ta dafa kafaɗarta ta ce.
"Ba kuka za ki yi mata ba Mamam Na'ima, addu'a ya dace ki yi mata. Ki yi haƙuri watarana sai labaru."Fauziya ta gyaɗa kai sannan ta yi mata godiya Lawisa ta koma ɗakinta. Tana nan zaune kimanin sha biyu da rabi na dare Kabir ya shiga gidan, a ɗarare ya zauna ya san Fauziya sarai da zafin kishi. Duk sai ya ji haushin kansa da tun yana gama gani bai goge ba. A tsammaninsa Fauziya za ta kula shi amma ga mamakinsa sai ga ko ƙurarsa ba ta kalla ba.
"Fauziya don Allah..."
"Ba na buƙatar jin komai daga gare ka." Ta furta a kausashe tana ɗaga masa hannu. Shiru ya yi ya kasa cewa uffan, Fauziya ta miƙa ta koma gefen yaranta ta kwanta ta shiga nazari da lissafin takaicin da mummunan ganin da ta yi.
Bayan Maman Nana ta koma gida haka ta sake cika fam, don tana aiki amma zuciya tana raya mata abubuwa da dama har aka yi sallar Magriba Jafar ya dawo. Yana zura ƙafarsa cikin gidan ya bi ta da wani kallon cike da ƙyama, ya saki guntun tsaki sannan ya wuce ɗaki. Yanayin fuskar Maman Nana ce ta sa ya tuna abin da ya faru kafin ya fita, don haka shi ma ya yi watsi da ita. Kaskon turaren wuta ta ɗauka har za ta fita Jafar ya ƙwala mata kira, fuska a haɗe ta ƙarasa ƙofar ɗakin ta ce.
"Ga ni."
Sabuwar wayar ya ɗauko gal a cikin kqalinta ko buɗewa ba a yi ba, ya miƙa matasa sai kuwa ta saki fukarta ta hau washw baki don ta yi tsammanin ita ya sayo wa sabuwar waya.
"Idan kin fita ki miƙa wa Maman Asiya, idan Naziru ya dawo ta ba shi saƙon sa da ya ce a taho masa da shi."
Murnar Maman Nana ta koma ciki, nan take ta haɗe rai don kusan sati uku kenan ba ta da waya tun da Abdul ya jefa mata wayarta a ruwa. Ta yi nacin Ya sayo mata waya kullun da zancan da zai ɓullo mata.
Gidan Maimuna ta ƙwanƙwasa da yake Maimunan ta san da maganar wayar da sauri ta je ta buɗe ƙofar, tana ganin Maman Nana ta ji wani farimciki ya lulluɓe ta. Wayar hannunta ta miƙe mata, sannan ta ce.
" A ɗan sammun gawayi zan yi turaren wuta."
Maimuna ta ce, "Wannan wayar kuma fa?"
"Baban Nana ne ya ce ki ajiye wa Abban Asiya."
Kamar Maimuna ba ta san kwanan zancen ba, ta saki fuska cikin murna ta ce.
"Allah Ya sa Abban Asiya suprise zai yi mini, don bai yi mini zancen za a taho masa da waya ba."
Maimuna ta saka cokali tana ɗiba gawayi ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Wai har yanzu ba ki gama girki ba Maman Asiya? Kai gaskiya masu girkin gawayi kuna ƙoƙari ina zan iya wannan jidalin?"
Wani takaici ya maƙaure zuciyar Maimuna, ta bi bayan Maman Nana da harara a ranta ta ce.
'Ni za ki yi wa iskanci kenan? To wallahi daga wannan karon kema kin daina aiki da gas ɗin, ba dai ni za ki yi wa iskanci ba? Za ki ga muna ƙoƙari ganin idonki.'
Maman Nana tana gama ɗiban wutar ta yi wa Maimuna sallama ta fice, a ta cikin riga Maimuna ta sakaya ledar wayar ta shige uwar ɗaki ta ita. Kayan sakawarta ta ɗaga daga can ƙasa ta tura wayar, ta ciro ƙaramar har za ta saka layi ta kira shi sai ta mayar saboda ta fi son sai zuwa jimawa idan ta sallami yaranta sun yi bacci ta kira shi su sha hira kamar yadda suka saba daddare kafin Nazir ya dawo. Tun da dama can shi Nazirba mutum ne mai dawowa gida da wuri ba, idan ma ya dawo ɗin mafi yawa lokaci hankalinsa yana kan wayarsa bai cika ba ta lokacinsa ba.
Hatta su Asiya sai da suka lura da farincikin da take ciki, amma sai ta nuna musu ba komai. Da yake a ƙage take da ta ji muryarsa, ana idar da sallar Isha'i ta yi musu shimfiɗa. Sai da ta tabbatar da bacci ya kwashe su sannan ta shige ɗakinta ta ciro ƙaramar wayar da suke waya ta kira shi.
A ɓangaren Jafar kuwa tun bayan da ya lura da haɗe ran da Maman Nana take yi, shi ma sai ya yi watsin iska da ita. Hakan kuwa ya sake ɓata mata rai, don haka ta ci alwashin za ta gasa masa a ya a hannun ta cikin ruwan sanyi. Yana gama cin abinci ya fice daa gidan, ya tafi can nesa da layinsu wurim da ya saba waya da Maimuna ya zauna. Ya jima yana dakon flashing ɗinta har sai da ya fara cire rai, sai ransa ya ɓaci da ya ayyana ko dai Naziru ne ya dawo shi ya sa ba ta smau damar kiransa ba.
Yana nan zaune ya ji flashing ɗinta, a fili ya saki ajiyar zuciya. Hannunsa har rawa yake ya latsa layin nata, tana ɗaga wa ya ji ta fashe masa da wani irin kukan kissa. Wani abu ya ji yana zarga masa wanda ya kashe masa ilahirin jijiyoyin jikinsa. Sai da ya yi ƙarfim hali sannan ya iya fisgar maganar bakinsa.
"Wannan shagwaɓar taba gigita ni my Moon, idan ba kya son hana ni bacci a ɗan daga ta da kukan nan haka."
Daga can ɓangaren Maimuna ta sake yin wata shasshekw wace ta sake birkita shi, murya can ƙasa kamar wacce take waya da mijinta ta ce, "Ina kukan farinciki ne my J. Haƙiƙa ka faranta mini rai domɗn wannam wayar ba ƙaramin tsada gare ta ba."
Murmushi ya yi mata ya ce, "Ko nawa zan iya ɓatar mini Moon, fata da burina kawai ki mallaka mini kanki."
"Idan hat ni ce kamar ka samu J, kada ma ka sake wasu-wasi a kan soyayya ta."
Har Jafar zai yi magana Maimuna ta katae shi a shagwaɓe.
"Ɗazu matarka ta ci mutumcina bayan ta zo ɗiban gawayi, a gaskiya raina ya ɓaci domin an daɗe ba a ci zarafi kamar na yau ba. Duk da ba cikin faɗa ta yi mini magaanar ba, amma a wasan dare ta ƙare mini cin mutumci. Har takw yi mini ƙafafa a kan ita amfani take yi da gas."
Sai kuwa Maimuna ta rushe da kuka, kukanta yake ji har cikin ransa. Don ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, cikin rarrashi ya ce, "Ya isa haka baby Moon. Wallahi tun ranar da na fara ganinki ba ki kalar amfani da gawayi ba. In Shaa Allaha na san yadda za a yi na saya muki gas ki daina amfani da gawayi. Ita kuma ki bar ni da ita na rantse miki da Allah daga gobe ta daina amfani da gas gabaɗaya. A yanzu ma don dai dare ya yi, da a daren nan zan siyo masa kurfoti da buhun gawayi."
Ummou Aslam Bint Adam
+2347062062624
[13/02, 21:16] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.
SHAFI NA BAKWAI
UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳
Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi 😍shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😍 akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya
Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731
***
Wani irin farinciki ne ya lulluɓe zuciyar Maimuna, saboda dama ba a ranar Maman Nana ta saba zuwa tana yi mata fariya, tana baje mata jin daɗin da Jafar yake yi mata ba. Wani abin ma sai ta lura kamar da gayya Maman Nanan take yi, saboda mijinta duk ya fi ragowar mazajen layin rufin asiri. Wannan ne dalilin da ya sa Maimuna ta ci alwashin sai ta tarwatsa farincikinta, tun da ita ba ta samu kwatankwacin abin da Maman Nana take samu a wurin miji ba.
"Na ji kin yi shiru ko hukuncin da na ɗauka bai yi miki ba?"
Jafar ya furta jin Maimuna ta yi shiru, Maimuna ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Hakan ya yi Baby J, to amma ta ya ya zan mallaki gas ɗin? Ni dai ba sana'a nake yi ba ballantana na cewa mutumin nan saya na yi."
"Wannan mai sauƙi ne Moon, zan san yadda zan ɓullowa lamarin."
Hirar soyayya suka cigaba da yi tamkar ma'auratan da suke nesa da juna, kowanne yana cike da kewa da begen ɗan uwansa. Suna gab da yin sallama Jafar ya ce, "Wayar nan da na aiko ba ta buƙatar caji, na saka mata caji ɗazu. Abin da ya rage kawai don Allah ki ɗaukar mini hotunanki."
Maimuna ta ce, "Sai zuwa gobe idan Nazir ya fita, amma ka ɓoye su ta yadda matarka ko wani ba zai gani ba."
Murmushi Jafar ya yi ya ce, "Kada ki damu akwai folder da nake ɓoye hotuna, a nan zan ɓoye naki."
Yana faɗin haka daga gefensa ya ji Nazir ya yi masa sallama yana daga kan mashin, duk da ya san Nazir ba zai taɓa fahimtar da wacce yake magana ba. Amma sai da gabansa ya faɗi, ya cire wayar daga kunnensa ya ce.
"Ale Nazir barka da shigowa."
Nazir ya ɗan rage gudun mashin ɗinsa ya ce, "Barka dai Alhaji Jafar, ka na nan a bayan fage kana waya ko? Ai sai na aika na faɗa mata." Nazir ya yi furucin cikin barkwanci.
"Tuba nake kada ka sa a rufe mini ƙofa." Jafar ya furta yana kama kunnensa, dariya Nazir ya yi ya wuce gida. Ganin ya tafi ya sa Jafar ya ja dogon tsaki yana mayar da wayar kunne ya ce, "Ina tsaka da farinciki wannan mutumin zai datse mini, don Allah Moon ki rage ba shi kula a turaka. Wallahi haka kawai kishinsa yake nuƙurƙusata."
Maimuna da ita kanta haushin Nazir ya kama ta ce, "Ai yau duk bala'insa babu ma abin da zai haɗa mu, dama na kwana biyu ina juya masa baya."
Kamar ba za su rabu ba haka suka yi sallama.
Maimuna tana gama wayar ta yi saurin mayar da ita wurin da take, ta yi sauri ta haye gado ta kwanta ta rufe ido. A kan kunnenta Nazir ya shiga gidan, ya ɗan jima a falo sannan ya tashi ya shiga ɗakin.
"Maimuna! Maimuna!"
Ya furta yana bubbuga filonta, yamutsa fuska ta fara yi tana miƙa kamar wacce ta jima tana bacci.
"Sannu da zuwa."
Ta furta masa tana sakin hammar ƙarya.
"Yawwa sannu ya gida?".
A hankali ta zuro ƙafafuwan ƙasa, ta jinginta kanta da fuskar gadon ta ce. "Lafiya ƙalau."
Ya yi mamakin a 'yan kwanakin nan da Maimuna ba ta yi masa ƙorafi, domin kusan kullum idan ya dawo gida sai ta yi masa ƙorafi a kan kai wa daren da yake yi a waje. Miƙewa ta yi ta fito falo, Nazir ya rufa mata baya. Kayan abincinsa ta ɗebo ta ajiye masa har ta miƙe za ta koma ɗaki ya riƙo hannunta.
"Maimuna kwana biyu na ga duk kin sauya, me yake damunki ne?"
Fuska babu walwala ta ce, "Me ka gani?"
"Na ga kwana biyu kamar ba ki damu da ni ba, kuma ni dai na san ba wani abu na yi miki ba."
Nazir ya furta a sanyaye.
"A'a babu abin da yake damuna kawai dai baccin da na tashi ne!"
"Ba haka ba ne Maimuna, a 'yan kwanakin nan ko ƙarfe nawa na dare zan kai ba za ki kira ni ba, idan na dawo kuma ba za ki tambaye ni dalilin kai wa daren da na yi ba. A yanzu ko zan kwana ina chatting uffan ba za ki ce mini ba, ni sai na ga kamar haushina kike ji."
"A'a ni babu wani haushinka da nake ji, ai kowa rayuwar da ya ga dama ita yake yi. Tun da na lura kulawar da nake ba ka ce ta sa kake yi mini wasu abubuwan, don haka na bar wahalar da kaina."
Maimuna ta sake yin maganar tana shirin tafiya.
"Zauna mana, yau fa hira nake son mu yi. To yanzu dai ki yi haƙuri, ga biskit da chocolate nan na taho muku da shi ke da yara."
Ta fahimci sarai hirar da yake nufi, domin dama ba ta cika amfani a wurin Nazir ba sai yana buƙatarta. Sau tari idan hakan ta taso babu wata kulawa da nuna soyayya haka kawai zai afka mata, ta kawar da kai gefe ta ce.
"Ai kuwa sai dai ka yi haƙuri zuwa gobe kaina matsanancin ciwo yake, shi ya sa ma na sha magani na kwanta ɗazu." Tana gama maganar ta janye hannunta ta wuce ɗaki, kamar sakarai haka yake bin Maimuna da kallon mamaki. Ya san dai Maimuna ba shiga gidan kowa take ba, ballanta ya ce maƙota ne suke zuga ta. Kuma ya santa da ƙorafi matuƙar ya ɓata mata rai ko bai san laifin ba za ta fito ta sanar da shi. Da sauri ya tashi ya bi ta ɗakin a lokacin har ta ja bargo ta rufa, ransa ya sake ɓaci amma sai ya saita nutsuwarsa ya ce.
"Magana nake yi miki fa Maimuna kika shigo ɗaki."
Tana daga kwance ta ɗago ta ce, "Ni ma ai amsa na ba ka Abban Asiya."
Ƙwafa ya yi ya juya ya fita, ya zauna ya cigaba da cin abincinsa. Sai da ya gama uzurinsa sannan ya shiga ɗakin ya kwanta a gefenta, juyi yake shi kaɗai yana mamakin sauyin halinta. Don haka ya so danne buƙatarsa amma sai ya gagara, hannu ya kai ta janyo ta kamar tana jira ta ture shi tana faɗin.
"Haba Abban Asiya, wai me kake yi haka na ce maka ban da lafiya fa."
"Kin sauya Maimuna, Me ya sa kike son horar da ni ne? Yau rabona da ke kwana nawa, rannan kin ce mini zazzaɓi kike. Shekaran jiya kin ce ciwon baya, yanzu kuma kin ce mini kanki yana ciwo. Idan kina ganin ba za ki iya ba ni haƙƙina ba sai na ƙara aure." Nazir ya furta cike da barazana saboda ya san Maimuna tana da kishi, amma cikin halin ko in kula ya ji Maimuna ta ɗago ta ce.
"Sai me don ka yi aure Naziru? A kaina za ta zauna? Ko ni zan ciyar da ita, ruwanka ne ka ƙara aure kuma ruwnaka ne ka bari na samu lafiya. Idan kuma ƙarin auren ka ga shi ya fi maka mafita wallahi ni ko a gefen takalmina."
Tsoro ne ya kama shi saboda ya ji an ce idan mace ba ta ba ka kulawa, ba ta nuna kishi a kanka kawai zama take yi da kai ba don soyayya ba. Da a ce a shekarun ba ya ne ba zai yi mamakin jin haka daga gare ta ba, amma yanzu da shekarun aurensu suka tura ya lura duk ta zubar da makamanta.
"Au haka kika ce?"
Nazir ya faɗa a zafafe.
"Eh haka na faɗa, tun da kishiya ba a kaina aka fara ba." Tana gama faɗa ta sake gyara kwanciyarta.
Cike da kewar Maimuna Jafar ya nufi gida, a lokacin da ya shiga ƙarfe goma sha ɗaya da rabi. A zaune tunkur ya samu Maman Nana da alama jiransa take yi, ya shiga ɗakin kamar bai ganta ya fara rage kayan jikinsa.
"Abban Nana wato fitar da ka yi gidan su budurwarka ka tafi ko?"
Bai waiwayo wurinta ba ya ce, "In ji wa?"
"Sai an faɗa mini?"
"To tunaninki bai harsaso miki daidai ba." Shi ma ya faɗa fuska a haɗe. Hakan kuwa ya sake harzuƙa ta, rai a ɓace ta ce.
"Wai Abban Nana me kake nufi ne? Ka bi ka sauya mini lokaci ɗaya na rasa gane kanka, da idan ka shigo gidan bayan sallar Isha'i ba ka sake fita sai washegari. Amma yanzu kana gama cin abinci sai ka fice ba za ka dawo ba sai dare, na gaji fa wallahi na gaji da irin cin kashin da kake yi mini."
"To idan ba za ki iya ba sai ki nemawar kanki mafita."
Ta riski miyagun kalamansa a cikin kunnuwanta, ƙirjinta ya buga da ƙarfi. Cike da tsoro ta dube shi amma sai ta nuna masa ba ta fahimci abin da yake nufi ba ta ce.
"Me kake nufi?"
"Ina nufin idan ba za ki iya zama da ni da ki kama gabanki."
Wani irin dum! Ta ji kamar an kwaɗa mata guduma, da sauri ta runtse idonta ta buɗe su a kansa. Ta taka gabansa muryarta tana rawa ta ce, "Abin da za ka ce mini kenan Abban Nana? Dama ka gaji da ni ban sani ba?"
"Ko ban gaji da ke ba wulaƙancin da kika tarko ne ba zan ɗauka ba, na lura samu ma yana saka mace ta yi iskancin abin da take so. Amma babu damuwa tun da irin zaman da kike so mu yi shi kenan."
Shiru ta yi kamar ruwa ya cinye ta, ta shiga nazari daga safiyar ranar zuwa dawowarsa ko za ta iya tuna laifin da ta yi masa amma ba ta iya tunawa ba.
"Don Allah ka faɗa mini laifin da na yi maka Abban Nana?"
Bai tanka mata ba ya saki tsaki ya ɗauki fulo ya koma kan kujera ya kwanta. Abin duniya ne ya haɗe wa Maman Nana, sai ta ji ya fara ba ta tsoro domin lamarin nasa ƙara yin gaba yake yi. Don haka ta shiga alla-alla gari ya waye ta leƙa gidan Maimuna ko ta ba ta shawarwarin abin da za ta yi.
Washegari
Tun da Jafar ya yi sallar Asuba bai koma ba, gari yana yin haske ya shiga cikin kitchen ya ɗauke tukunyar cilinder gas ya fice da ita. Da yake Maman Nana ba ta tashi da wuri ba, saboda a daren bacci bai ɗauke ta da wuri ba ko kaɗan ba ta san wainar da ake toyawa ba. Sai da ta ji alamun buɗe gate ta tashi ta fito, a tsammaninta Jafar fita ya yi kasuwa.
Banɗaki ta shiga bayan ta fito ta shiga kitchen za ta shirya wa su Nana abin breakfast da na makatanta. Amma sai ta ga wayam babu clinder, ba ta kawo komai a kanta ba; sai ta yi tsammanin ko ƙaro musu gas zai yi saboda idan ya ga ya kusa ƙarewa yana ɗauka ya ƙaro mata.
Tana daga ƙofar kitchen ta hango shi yana kokawar shigowa da ƙaton buhun gawayi, sai da ya ƙarasa ya jingine shi sannan ya sake fita gate ya sauke mirgino buhu na biyu. Maman Nana tana tsaye ya gama dire buhunnan gawayin har guda biyar, sannan ya ɗauko kurfoti ya dire a gabanta. Fuska a haɗe ya ce, "Daga yau ga abin da za ki dinga girki da shi, gas ya sake tsada ba zan iya sayensa ba. Cilnder ma na sayar wa mai shagon da nake sako mana gas, sai a ci gaba da malejin rayuwa tun da komai tsada yake sake yi." Jafar yana gama faɗar haka ya shige ɗaki.
Kabir kwance ya yi a kan gado, yana jin haushin kansa a kan abin da ya aikata. Fushin Fauziya ya fi komai ɗaga masa hankali, don Fauziya mace ce
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 35