kuma wanda ita kanta Sadiyan take faɗa mata, wani tunani ne ya faɗo mata don haka ta yi saurin janyo wayarta ta latsa layin Kabir. Sai fa ta kusa katse wa ya ɗauka yana faɗin.
"Ina hanya."
Tana jin yana shirin kashewa ta ce, "Magana nake son mu yi Abban Na'ima." Kamar ba zai amsa mata ba, sai kuma a daƙile ya ce.
"Ina jin ki."
Gaban Fauziya ya shiga faɗuwa, tana fargabar irin fassarar da zai yi wa kalamanta. Jin shiru ya sa Kabir ya ce, "Kin san ba ki da abin faɗa kika kira ni?"
Maganar da ya yi ba ƙaramin bugun zuciya ta saka ta ba, ta yi ƙarfin halin faɗin.
"Abban Na'ima don Allah ka kama mini haya!"
"Saboda me?"
Ya wurga mata tambaya a gaggauce.
"Haka kawai, ina ganin kamar za mu fi sakewa. Na ga gidan Inna kamar babu ɗaki, ga kuma yara."
Guntun tsaki ya yi ya ce, "Duk ɗakunan gidan Innar ne za ki ce babu? Ko dai zama da mahaifiyar tawa ne ba kya so?"
Kamar Fauziya za ta yi kuka ta ce, "A'a na ga ɗakin da ya rage ba kowa shirgi suke ajiyewa."
Ajiyar zuciya Kabir ya sauke ya ce, "Na sa yara sun gyara ɗazu, idan Allah Ya kai mu da sassafe akwai mai motar da na yi wa magana zai zo ɗaukar kaya."
Murya tana rawa ta ce, "Ko na kira dillaliya ta sayi keken ɗinkin nan nawa? Idan ya so kafin jibi sai mu nemi ɗaki."
A hassale Kabir ya ce, "Wai me kike nufi Fauziya? Mahaifiyar tawa ce ba kya ƙaunar zama da ita? Ko kin manta ita ta ɗauki cikina wata tara ta haife? Saboda raini har ni kike cewa za ki kamawa haya, a kan ki zauna da mahaifiyata?"
Nan take ta rikice, don ta san dama ba lalle ya fahimci irin abin da take gudu ba. Tuni hawaye ya wanke fuskarta, tana shirin magana ta ji Kabir ya katse a fusace. Kuka Fauziya take yi wanda take jin ɗacinsa yana fitowa daga ƙasan maƙoshinta, tsakar gidansu ta ƙura wa ido tana hangen ɗakin Lawisa. Tana ji a ranta yadda zuciyarta take zafi, da ace Lawisa tana nan ita ce mutum ta farko da za ta fara faɗawa halin da take ciki ko ta ji sanyi. Duk da wannan ba ɗabi'arta ba ce, amma tana jin idan ba ta sanar da wani ba zuciyarta za ta iya bugawa. Tashi ta yi ta fara kai wa da kawowa domin neman mafita, amma gabaɗaya kanta ya cushe. Tunanin tafiya gidan mahaifinta ta yi, a nan ma ta ga sam ba mafita ba ce domin mahaifinta ba zai taɓa goya mata baya ba.
Da wannan tunanin Fauziya ta wuni har sai da zazzaɓi ya rufe ta, haka daren ranar ya zo mata cikin ƙunci. Da Kabir ya dawo ta ga yana fushi ba ta tanka masa ba, da ta miƙa masa abinci kuma ya ce ba ya ci. Ita ma da yake a cike take da haushinsa, ba ta sake bi ta kansa ba ta kwanta. A daren ranar kwana ta yi tana miyagun mafarkai a kan zamanta da Inna har gari ya waye.
Tun da farar safiya mai motar da Kabir ya yi wa magana suka yi sallama, ya fara fitar musu da kaya. Fauziya tana haɗa kaya tana hawaye, Na'ima da Fatima tun da suka ji mahaifiyarsu ta ce gidan Inna za su koma duka walwalarsu ta dusashe, amma da yake Hidaya ba ta san dawan garin ba haka ta dinga tsalle tana murna.
Sai da aka gama kwashe kayan tsaf sannan ta leƙa ta yi wa Maman Sabir sallama, da neman yafiyar juna.
Tun da suka doshi layin ƙirjinta yake bugawa, tana fargaba irin zaman da za su gudanar a cikin gidan. Tsayuwarsu a ƙofar gidan, ya yi daidai da tsala ihun da Salim yake yi. Jiki a sanyaye Fauziya ta tsoma ƙafarta cikin gidan, bakinta ɗauke da sallama. Inna ta hango a zaune ta maƙure Salim a ƙasan ƙafafuwanta tana tsala masa dorina yana sakin ihu, sai da ta gaji don kanta sannan ta ce.
"Don ƙaniyarka gobe ma ka sake zubar mini da kuɗin tsintsiya, wallahi dukan da zan yi maka sai ya ninka wannan."
Sai a lokacin ta ɗago ta dubi Fauziya ta ce, "Baƙin safe ashe kun ƙaraso, ga ɗaki can sai ku fara jera kaya."
A ɗarare Fauziya ta gaishe ta, su Na'ima da dukan Salim ya tsorata su ya sa duka suka riƙe zanin mahaifiyarsu a tsorace suna leƙen Inna.
"Ku kuma leƙen me kuke yi mini kamar ba ku sanni ba? Ku dama uwarku ba ta koya muku gaida mutane ba ko? Kai shi ya sa 'ya'yan Mudam suke birge ni, uwar su Zaliha akwai tarbiyyar. Ai kuwa ga yaranta nan gwanin birgewa, duka tarbiyyarta suka gado." Ita dai Fauziya ba ta kula ta ba, ta wuce ɗakin da aka nuna mata. A bakin ƙofa ta tsaya tana ƙarewa ɗakin kallo, ɗan ƙanƙani ne ko gadonta ta haɗa ba zai zauna a ciki ba. Ballantana a kai ga saka keken ɗinki, kwanuka, manyan robobi da akwatunan kayan yara.
Sadiya ce ta ƙarasa wurin fuskarta cike da jimami ta ce, "Fauziya kun ƙaraso?" A madadin Fauziya ta amsa mata sai kawai ta fara zubar da ƙwalla, a tsorace Sadiya take waigen wurin Inna tana girgiza mata kai. Ita ma girgiza kan ta fara yi cike da tausayin kanta da 'ya'yanta. Da ƙyar ta ja ƙafa ta faɗa cikin ɗakin. Sadiya ce ta rufa mata baya ta yi ƙasa da murya ta ce, "Fauziya ba ta son tun daga zuwanki Inna ta fahimci ba kya son zaman gidan nan. Don Allah ki yi haƙuri ki mayar da komai ba komai ba, ni ban ma san yadda aka yi kuka gagara tarewa a gidanku ba. Allah na tuba indai aka yi rufi ko a ya yake ai gidanka ne, sannu a hankali sai a ƙarasa." Fauziya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce.
"Sadiya!"
Ɗagowa Sadiya ta yi jin yadda Fauziya ta kira sunanta, Fauziya ta share hawaye mai ɗaci ta cigaba da cewa.
"Kabir ɗin da na sani a baya kamar ba shi ba ne yanzu ba, Kabir ya sauya mini Sadiya. Ina tsoron kada wani abu ya biyo bayan tariyarmu, domin a yanzu ban cika gane gabansa da bayansa ba."
A fili Sadiya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, "Tabɗijam! Lallai da alama tura ta kai bango Fauziya, tun da har yau ke kika fito kika faɗi aibun Kabir, tabbas an kusa zuwa daidai gaɓar da nake son a zo." Sadiya ta kamo hannun Fauziya ta ce, "Shi ya sa ba tun yau ba, nake nuna miki ba a ɗaukar yarda ɗari bisa ɗari a damƙa wa ɗa namiji. Ki zauna da shi saffa-saffa, ta yadda idan ya yi watsin iska da ke abin ba zai ɗaɗa ki da ƙasa ba. A duk lokacin da na ga kin nuna wauta, sau tari ina son na ankarar da ke amma ina gudun ki ga kamar ina son haɗa ki da mijinki. Ko kuma ki ga ina kushe shi, don haka na kawo na mujiya na zuba miki."
Fauziya ta share ƙwallar idonta ta ce, "Haka ne Sadiya, amma don Allah kada ki ga laifina. Idan kika cire mahaifina Kabir shi ne mutum na farko da na shaƙu da shi, na kuma damƙa wa ragamar rayuwata."
Sadiya za ta yi magana daga can waje suka ji Inna ta ce, "Ke Sadiya me kike yi a ɗakin Fauziya tun ɗazu ne? Ko munafurcina za ki kai mata, ga tuwo can kin bar shi yana kamawa sai ki je ki kwashe mana." Jiki yana rawa Sadiya ta amsa mata, sannan ta kalli Fauziya ta ce, "Sai na sake shigowa bari na je kada na ja miki karantsana a wurinta." Daga haka ta fice.
Shiru Fauziya ta yi tana ayyana ita ma kenan irin wannan rayuwar za ta fara. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fara jan kayan tana lodewa a gefe, sai ta ɗauko katifata ta shifiɗa. Ragowar wurin da ya rage bai fi kwanciyar babba mutum ɗaya ba, keken ɗinkinta, mangal ɗin girki da abin zuba ruwanta ba su samu wuri ba sai a ƙofar ɗaki ta ajiye su. Sannan ta ɗora musu abinci, bayan ta gama ta zuba wa yaranta sannan ta zuba kaɗan a roba. Ita kuma Inna ta saka mata a plate ta rufe, Sadiya ta miƙa wa na robar sai kuma ta ba wa Inna nata.
A yatsine Inna ta dubi farantin har Fauziya za ta miƙe Inna ta ce, "Au ashe fa ke ba ki san tsarin gidan nan ba ko?" Fauziya ta gyaɗa kai.
Inna ta saki murfin ya faɗi ƙasa a wulaƙance ta ce, "Abincin rana a gidan nan haɗa shi ake a yi girka gabaɗaya, girkin safe da na dare ne kowa yake yin nasa. Sannan daga yau kada ki sake zuba mini abinci a ciki shatalallan faranti, saboda mu a lokacinmu kwanon uwar miji daban ake yi mata don haka ki kiyaye wannan ma ai wulaƙanci ne." A sanyaye Fauziya ta amsa mata, ta koma ɗakinta. Tana shiga ta ga Zainabu, 'yar wurin Sadiya ta cika hannu da ƙatuwar lomar abincin su Na'ima ta tura a baki, tana ganin Fauziya ta sake kwasar ƙatuwar loma ta fita a guje tana dariya. Hidaya da Fatima suka saka kuka suna faɗin, "Ta cinye mana abinci, Mami tun ɗazu take kwashe mana abinci." Shiru Fauziya ta yi sai ta ji duk zuciyarta babu daɗi, buɗe tukunya ta yi ta ɗebo daga cikin wacca ta rage za ta ci ta zuba musu. Ta zauna gefen katifa ta janyo tukunyar ta fara ci a ciki, tana nan zaune ta ga Zainbu da ƙaninta Faisal ɗan shekara ɗaya da rabi suka dinga leƙensu sai su tafi da gudu.
Tun daga wannan ranar, zaman Maman Nana da Jafar ya koma irin zaman doya da manja. Sakamakon rashin kyakkayawar alaƙar da take shiga tsakaninsu. Kuma har kullum zaman nasu ƙara tsamari yake, don Jafar ya jima da ƙaurace mata. Idan dare ya yi sai dai ya ɗauki filo ya tafi falo ya kwanta, gari yana wayewa kuma ko breakfast ba ya yi yake fita. Idan ta ce abu ya ƙare sai dai ya ba ta kuɗi ta sayo kaɗan, saɓanin a baya da komai idan ya tashi dire mata yake yi mai yawa. Wani abu da Jafar ya tsiro mata da shi sai suna zaune ya ɗauki waya ya yi ta latsawa yana sakin murmushi, ita kuma da ta yi magana kamar jira yake sai ya rufe ta da faɗa. Watarana tana suna zaune da safe, da yake ranar ba ta ga alamar zai fita da wuri ba. Waya ta ga ya latsa yana kai wa kunnensa, tsam ya tashi ya wuce uwar ɗaki sai ta ji ya kashe murya yana faɗin.
"Barka da hutawa My Moon."
Ƙirjin Maman Nana ya buga da ƙarfi, don a yanayin maganar da ta ga yanayi ta fahimci da mace yake waya. Ta jinjina kai tana sauke ajiyar zuciya ta ce.
"Wato duk wannan cin kashin da yake yi mini saboda mace ya yi mini fana? Ai kuwa ba zan lamunci ya dinga yi mini waya a ɗaki ba." Tuni zuciya ta ɗebe ta, ita ma ta faɗa cikin ɗakin a daidai lokacin ta ji ya ce.
"Wallahi tallahi Moon babu wata 'ya mace nake jin kewa da muradinta a yanzu, ganin hotunanki kaɗai suna iya hargitsa ni har na gagara gane kaina."
Tsaye Maman Nana ta yi hawaye ya gama wanke idonta, baki yana rawa ta ce.
"Abban... Nana... ashe a kan wata 'yar iskar kake wulaƙanta ni?" Ɗago kansa ya yi ya kalle ta, ga mamakinta sai ta ga ya ɗauke kansa gefe ya cigaba da cewa.
"Na rasa abin da zan yi miki don ki yarda da abin da nake faɗa, kin san Allah ke ta daban ce a cikin mata..."
Shiru Maman Nana ta yi tana ƙura masa ido cike da hawaye, har gani take kamar ba Jafar ɗinta ba. Domin a baya Jafar ba ƙaramin shakkarta yake yi ba, amma a yau wai shi yake yabon wata a gabanta. A haukace ta fisge wayar ta yi wurgi da ita, cikin matsanancin kishi haɗe da ƙaraji ta ce.
"Jafar ni za ka mayar mahaukaciya? Da wacce 'yar iskar kake waya a ɗakina..."
Maganarta ce ta katse sakamakon wani gigitaccan mari da ya sakar mata, idanunsa sun kaɗa jawur saboda ɓacin rai. Ya dube ta a hargitse ya ce, "Kada ki sake ce mata 'yar iska, idan kuma ba haka ba wallahi sai na ɗauki mummunan mataki a kanki." Wani irin sanyi jikin Maman Nana ya yi, sai kuma tsoro ya kama ta. Har take ganin kamar Jafar ba a hayyacinsa yake ba, ta sake matsawa gabansa ta riƙo rigarsa tana jijjiga shi, a ganinta ko hakan zai sa ya dawo hayyacinsa. Hawaye yana zuba ta ce, "Kana cikin hayyacinka kuwa Jafar? Ni kake mari saboda na cewa wata 'yar iska?"
Kamar yana jira ya yi saurin faɗin, "Na mare ki Sumayya, wallahi idan kika kuma faɗar mummunar kalma a kanta sai na yi miki abin da ya fi haka." Maman Nana ta ji kamar ya watsa mata ruwan zafi, zuciya a ƙeƙashe ta ce.
"Na faɗa 'yar iska karuwa don Allah ka kashe ni a wurin nan."
Kamar wancan karon haka ya sake tsinke ta da mari, sai dai a wannan karon tagwayen mari Maman Nana ta samu. Wayarsa ya ɗauka, da yake dama ya yi wanka sai kawai ya shiga ɗaki ya saka kayansa ya fice daga gidan.
A wurin Maman Nana ta durƙushe tana kuka kamar ranta zai fita, sai da ta yi mai isarta sannan ta sauya kaya. Ta ɗauki Abdul da yake bacci ta goya shi ta fito daga gidan, duk wanda ya ganta kallo ɗaya zai yi mata ya fahimci ba ta cikin nutsuwarta. Gidan Maimuna ta shiga ta same ta zaune a falo, Maimuna tana jin shigarta ta saki murmushin ƙeta saboda duk abin da suka yi a kan kunnenta, tunda wayar ba mutuwa ta yi ba a lokacin da ta yi wurgi da wayar Jafar. Amma a fili tana ganin Maman Nana ta dafe ƙirji ta ce, "Lafiya kuwa Maman Nana? Me ya samu fuskarki ta kumbure haka?" Da yake har lokacin da ɗacin abin a ranta, sai Maman Nana ta rushe da kuka mai cin zuciya.
'Na rantse da Allah kuka ma yanzu kika fara, mu je zuwa wai mahaukaci ya hau kura." Maimuna ta faɗa a ranta, amma a fili cikin ruɗewa ta ce.
"Maman Nana ki yi magana don Allah, kin ɗaga mini hankali. Daga gida ne aka kira ki wani abu ya faru, ko Abban Nana ne?"
Maman Nana ta girgiza kai, Sai Maimuna ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"To mene ne? Don Allah ki yi mini magana, wannan kukan da gani dai ba na lafiya ba ne."
"Wai yau ni Jafar ya mara saboda wata maman Asiya, Jafar ya zama wani iri wallahi asiri aka yi masa, don Jafar ɗina ba ya cikin hayyacinsa."
Maman Nana ta yi maganar cikin kuka.
"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Kada ki ce mini tun yarinyar da muka yi magana da ke kwanaki? Ai kin ga sakacinki Maman Nana, tun wancan karon na ce ki ɗauki mataki amma kika tsaya sanya. Yanzu ai ga shi kina gani ƙarfi da yaji yarinya ƙarama ta shanye shi."
Cikin ƙaguwa da neman mafita ta ce, "Yanzu mene ne abin yi Maman Asiya?"
Shiru Maimuna ta yi kamar mai yin nazari, sai ta ɗago da sauri ta ce.
"Gidanku sun san abin da ya faru?" Girgiza kai Maman Nana ta yi, sai Maimuna ta ce.
"Yanzu abin da za ki yi kai tsaye ki wuce gida, ki sanar da iyayenki a san halin da ake ciki. Saboda wallahi matuƙar ba a ɗauki mataki ba abin ƙara gaba zai yi, kin san aka ce idan namiji ya ji daɗin dukanka ya samu wuri kenan. Kar ma ki faɗa masa za ki tafi, ki bari sai dai ya dawo kawai ya ga ba kya nan. Idan aka yi muku sulhu daga baya sai ku daidaita ki dawo, amma ina mai tabbatar miki da sai kin tashi tsaye." Shawarar Maimuna ba ƙaramin kwanciya ta yi a zuciyar Maman Nana ba, haka ta dinga ba ta shawarwari daga ƙarshe suka yi sallama ta fita. Da yake makarantar su Nana a bakin titi take, sai ta da ɗebi kayansu sannan ta wuce ta makarantar ta ɗauke su suka wuce gidansu da ke unguwa uku.
Tun bayan da Maman Nana ta yi wa Maimuna sallama da ta ji fitarta daga gida, ta kira Jafar ta kwashe ƙarya da makirci ta faɗa masa. Don har cewa ta yi Maman Nana tana ta zaginsa kuma ta ce ta tafi gidansu kenan, domin ta gama zaman aure da shi. Maganar da ta fi tsaye masa a rai da Maimuna ta ce wai Maman Nana tana kuka tana cewa, ta yi dana sanin haɗa zuri'a da shi, domin shi ba miji kuma uba nagari ba ne. Da irin waɗannan miyagun huɗubar, Maimuna ta samu yin galaba a kan Jafar. Har shi ma ya hau dokin zuciya da cewar ba zai taɓa nemanta ba, kuma ba zai je biko ba tun da ba shi ya ce ta tafi ba. Ya kuma ci alwashin ko a ranar ta nemi takardar saki, a shirye yake da ya miƙa mata kayarta. A ranar tun yamma ya dawo gida saboda ya san Maman Nana ba ta nan, kuma har cikin zuciyarsa da zai samu yadda yake so kuma da babu 'yan gulma tsaf zai ce Maimuna ta zagayo su sha soyayya. Amma da yake ya san akwai matan maƙota da suke kai kawo, sai ya haƙura da buƙatarsa. Ya shiga ɗaki ya rage kayan jikinsa sannan ya jira Maimuna a waya, ya ce ta kunna data za su yi magana. Ita ma da yake ta gama girki ta kuma sheƙa wankan ƙananan kaya, sai wayar ta shi ta zo mata a daidai. Ta whatsapp ya kira ta video call, ta ɗauka a kunyace tana sunne kai ƙasa.
"Wai wai wai, wannan wankan duk ni aka yi wa? A gaskiya baby za ki hargitsa ni." Sai kuma Jafar ya shagwaɓe murya ya ce, "Don Allah idan babu damuwa ki zagayo mana Moon. Wallahi babu wanda zai gane, domin a cike nake da ƙishirwarki."Maimuna ta yi shiru tana nazari, domin ita kanta wannan lokacin ta jima tana buri da fata.
Tun da dare ya yi bayan ta kwantar da yaran ta yi shiru tana ƙare musu kallo, Na'ima da Fatima ne ta yi musu shimfiɗa daga ƙasan katifa. Hidaya da Humaira kuma ta yi musu shimfiɗa a kan katifa, tana nan zaune Kabir ya shiga ɗakin bakinsa ɗauke da sallama. Amsa masa ta yi ta mayar da kanta gefe, saboda haka kawai haushin Kabir take ji. Shi kansa shiru ya yi ganin yanayin kwanciyar da suka yi, sai kuma jikinsa ya yi sanyi tausayinsu ya kama shi. Kayan abincinsa ta ajiye a gabansa, ba tare da ta ce masa uffan ba. Shi kansa ya fahimci fushi take da shi, sai ya ɗan saki fuska ya ce.
"Haba Fauzina yanzu wannan fuskar da kika haɗe duk saboda za ki zauna da mahaifiyata ne, zaman nan fa ba na dindindin ba ne. Don Allah ki daina ɓata ranki ba na so." Fauziya da dama ciki take da shi ta ce.
"Ni ba ina fushi da zaman da zan yi tare da mahaifiyarka ba ne Abban Na'ima, domin Inna tamkar mahaifiyata haka na ɗauke ta. Kawai yanayin zaman ne bai yi mini ba, dubi a inda yaran nan suka kwanta. A gaskiya sam babu tsari wallahi, don girman Allah ka bari mu koma gidannmu idan ya so ko a hankali sai ka ƙarasa."
Kabir ya ɗan yi jim ya ce, "Ummu banat kin san dai muna da maƙiya, waɗanda suke son ganin cigabanmu, wallahi ba na son na koma a ga gidana ko fulasta babu. Kin san idan aka ce shago ba naka ba ne sai haƙuri, Oga ba wata kyakkaywar sallama yake mana ba. Kin ga Allah Ya taimaki Sani da yake shi kekensa ya kai shagon, shi yake cin gashin kansa. Sai dai ɗan kuɗin da yake bayarwa duk shekara, wanda Oga yake cikawa ya biya kuɗin shago. Ni ma kin ga da ina da keken kaina rufin asirin da zan samu sai ya fi haka."
Shiru Fauziya ta yi, ta kallo keken ɗinkinta da ke waje. Ta tuna ba wani ɗinki take samu ba, mafi yawa sai ɗan gyare-gyare da mata suke kawo mata. A yadda take jinta kamar kwance cikin ƙaya, babban burinta bai wuce ta ga sun tashi daga wannan gidan ba. Don haka ba ta yi dogon tunani da nazari ba ta ce. "Indai hakan zai sa ka yi ka ƙarasa mana, ga kekena nan ka ɗauka Abban Nana. Babban fatana Ubangiji ya rufa mana asiri." Tana gama magana Kabir ya rungumo ta jikinsa, sai ya shiga sakar mata kiss a duk ilahirin jikinta. Cikin wata irin murya ya ce, "I love you my Fauzee."
Fauziya ta saki murmushi ta ce, "I love you too Abi." Gani ta yi Kabir yana yunƙurin wuce gona da iri, don haka ta janye shi daga jikinta ta ce, "Ga abincinka fa." Kafaɗa ya maƙale mata yana bin ta da wani irin kallo ya ce. "Idan da ke abinci da komai ba ne." Tana shirin sake yin magana Kabir ya janyo ta jikinsa, ya shiga yawo da hannuwansa a cikin jikinta.
"Wallahi kunya nake ji, magana ta Allah ba zan iya wani abu a cikin ɗakin nan ba. Don gani nake kamar Inna tana jin duk abin da muke yi, tun da kaga ɗakinmu a jikin ɗakinta yake. Kuma ka dubi kusancin kwaniya da muka yi da yaran nan."
Kabir ya zame hannun rigarta ƙasa, ya ɗora kanta a saman cinyarsa cikin wata irin murya ya ce.
"Babu abin da za ta ji, don haka kada ma ki..."
"Kabiru! Kai Kabiru ashe kana ciki?"
Maganar Inna da bakaɗa labulen ɗakin da ta yi ne ya sa maganar da Kabir yake yi ta maƙale, cikin tsananin jin kunya Fauziya ta tashi tana jan rigarta sama. Inna ta saki baki haɗe da riƙe baki ta ce.
"Dole na ji ku shiru a ɗaki mana, ku dai wallahi an yi jarababbun yara. Don masifa tun a farkon dare? Ko tara fa ba ta yi ba, shi ne za ki saka yaro a ɗaki ki ƙadandane kamar alkaki."
Shi kansa kunya Kabir ya ji, ya ɗan sosa kai ya ce.
"Amma Inna ai da kin yi sallama kafin ki shigo."
"Ba zan yi ba, na ce ba zan yi shashashan banza da wofi. Ina ganin jarabar su Sadiya da duk asuba za ka ji su suna karafniya da ruwa kamar kifaye, ashe nasu shafar mai ne tun da ga ku; ku tun garin bai nausa ba. To idan ka gama shinshine-shinshinen sai ka zo ka same ni a ɗaki." Inna ta ƙarasa maganar tana sakin tsaki sannan ta wuce ɗakinta.
Bayin Allah na kusa kammala free pages, masu son littafin za su biya kuɗin karatu 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[19/02, 17:43] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 35