A'ilo ya faɗa."
Fauziya ta yi shiru ta rasa bakin magana, Lawisa ta ɗaga labule tana faɗin.
"Haba ku kuwa kamar ba ku san faɗan yara ba har za ku shiga? Wallahi indai yara ne kuna zaune za su ba ku kunya..."
A zafafe Abu ta katse ta. "Sai ki bari idan an ciji naki 'ya'yan sai ki faɗi haka, za ki fito ki yi wa mutane gwalangwaso. Don sun ce ubansu ɗan maye ne shi ne za ta cije su. Shekaran jiya waccan, ina ce butata ya ɗauka ya yi mini wurgi da ita ta fashe." Lawisa za ta sake magana Fauziya ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta girgiza mata kai sannan ta ce.
"Don Allah ku yi haƙuri, In Shaa Allahu ba za su sake cizonsu ba."
Kusan lokaci ɗaya suka taɓe baki, Fauziya ta yi wa su Na'ima magana suka wuce ɗaki. Jiki a sanyaye ita ma ta wuce ɗaki, tana jin su A'ilo suna ci gaba da yadda mata magana da habaici haɗe da yin dariya.
"Mami wai mene ne shaye-shaye? Me ya sa kullum su Sabir suke ce mana Abi yana shaye-shaye?"
Tambayar Na'ima ta katse dogon tunanin da Fauziya ta faɗa. Ras! Ta ji gabanta ya faɗi, da sauri ta kamo hannunta fuska ɗauke da alamun tsoro ta ce.
"Kul Na'ima yara ba sa faɗan irin wannan maganar kin ji! Babu kyau kada na sake jin kun faɗi haka."
Lokaci ɗaya suka gyaɗa mata kai, sai Hidaya ta ce. "Mami to ki faɗa wa su Hafsa su daina faɗa kada Allah Ya ƙona su a wuta."
Fazuiya ta yi murmushi ta ce, "Su ma mamansu za ta faɗa mu, sannan don Allah Hidaya ku daina zuwa cikinsu kuna wasa. Ba ga kayan wasanku nan ba, ku dinga zama a ɗaki kuna yi kun ji."
Lokaci ɗaya suka amsa mata, tana nan zaune ta ji sallamar Sadiya facalarta.
Daga wurin da take zaune ta amsa mata, Sadiya ta shiga tana faɗin.
"Uwar huɗu, wai har yanzu ba za ki kotse ba ne?"
Fauziya ta miƙa mata fulo ta ce, "Zauna uwar 'yan sa ido, ni kaina kullum jiranta nake yi."
Sai da suka gaisa Fauziya ta ce, "Ina zuwa haka da tsakar rana?"
Sadiya ta yi dogon tsaki tana kallon su Na'ima da ke wasa ta ce, "Ai tun da akwai radiyo mai jini dole na gyara zancan. Wallahi Fauziya komai ya yi mini zafi, kin san dai halin wancananka. Yau haka ya ƙare mini zagin cin mutumci, saboda kawai na ce ya biya ni kuɗaɗen da nake bin sa bashi. Ke dai shaida ce kin san ba yau ya fara zagin iyayena ba, ni ma yau na gaji na rama. Ke faɗa har sai da ya kaimu tsakara gida, shi ne fa o'o (Inna) ta shigarwa ɗanta suka yi mini zagin ƙare dangi. Abin da ya sake ɓata mini rai kwanana uku kenan ina zazzaɓi, kullum nace ya ban kuɗin magani sai ya ce mini yake ba shi da kuɗi. Amma ina duba wayarsa a chart ɗin da suke da budurwarsa, na ga ya tura mata dubu shida kuɗin ɗinki wai bikin yayarta ake yi."
Sadiya ta furzar da iska mai zafi, tana tuna ɗacin abin da mijinta ya yi mata ta cigaba.
"Kin san fa shi indai a kan 'yanmata ne duk arzikinsa a nan yake tafiya, ni kuwa ina gida ko oho wani lokacin na omon wanki ma gagarata yake yi."
Fauziya ta girgiza kai cikin damuwa ta ce, "Ke ma Sadiya tun tuni kin san halinsa, da kin sani ba ki biye masa ba kun yi ba daɗi a gaban yara ba. Ita kuwa dama kin san yaranta ba sa laifi, kwanaki fa a gabanta ya mare ki amma sai cewa ta yi ai ɓata masa rai kika yi."
Kamar Sadiya za ta yi kuka ta ce, "Idan ban biye masa ba Fauziya ya zan yi? Kina ga fa haka zai tsallake ya bar mu indai akwai tsaba babu ruwansa da kuɗin kayan mahaɗi, duk ni nake fafutukarsu. Ga shegen kule-kulen mata har da na hauka, don wallahi da kuɗin da yake kashe musu ba gara mu ya kashe mana ba."
"Eh to haka ne, lamarin ne sai haƙuri kawai. Ni dai ta nan fanin sai dai na ɗaga hannu na gode wa Allah, domin gaskiya babu macen da ta sha gaban Kb da har zai tsaya ɓa ta lokaci a kanta..."
Murmushin da Sadiya ta yi ya katse furucin Fauziya.
"Ban ga laifinki ba, da kika faɗi haka. Domin ruwan da ya dake ka shi ne ruwa. Amma ni dai a wannan gaɓar da zamantakewata da Ali, ta koma irin da zaman cin kunamar ƙadangare. Na rantse da Allah ko me aka ce mini ya yi ba zan musa ba, ki bar cin alwashin namiji saboda ko yaya basa rasa 'yanmatansu ke dai ki ga rijalu kawai."
Fauziya ta yi dariya ta ce, "A'a Sadiya, dole na bigi ƙirji wallahi ko a gaban mutanen duniya Kb ɗaya a cikin dubu, ya zamo mini tamkar zara a cikin taurari. Ni shaida ce wallahi-wallahi tun daga ranar da ya muka fara soyayya, har kawo yanzu babu macen da yake kulawa."
Sadiya ta miƙe tana gyara hijabinta ta ce, "To ni bari na zo na wuce, ko ba komai mun ɗan tattauna na rage zafin da nake ciki. Kada na daɗe uwar masu gida ta fahimci na fita, na ƙara wani laifin."
Har soro Fauziya ta raka ta, Sadiya ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Wai mutanen gidanku har yanzu zaman naku sai a hankali ne? Na ga da na yi sallama A'ilo ba ta amsa mini ba."
Fauziya ta furta, "Hmmm ke dai bari, wallahi shi ya sa zaman gidan duk ya gundure ni."
Fauziya da Sadiya sun jima suna hira sannan suka yi sallama.
Sai da ta tabbatar da yaran sun tafi makaranta, shi ma Nazir ya tafi kasuwa. Sannan ta shige uwar ɗaki, ta buɗe drower kayanta. Daga can ƙasa ta zura hannu ta ciro 'yar ƙarama wayarta, ta koma gefen gado ta zauna sannan ta kunna ta. Ba a ɗauki lokaci ba wayar ta kunnu, nan take ta latsa wata lamba ta kira, daga can ɓangara aka ɗauka.
"Barka da safiya sarauniyata!"
Maimuna ta saki murmushi cike da kissa ta ce, "Barka dai jarumin jarumai."
"Wai sai yanzu ya matsa ya ba mu wuri ne? Wallahi tun safe nake jin ƙishirwar muryarki."
Jafar ya furta cike da sha'awa.
"Hmmm to ya za a yi? Ka san abin ka da mai iyali ko ya fita ai dole sai na sallami yara."
Jafar ya yi murmushi ya ce, "Me zan samu? Don wallahi yau kwana biyu kenan, na kasa kataɓus da waccan sakaryar." Dariya sosai Maimuna ta yi ta ce, "Wallahi babu ruwana, kai da Maman Nana."
Jafar ya sake kwantar da murya cikin wani irin yanayi ya ce. "Moon!"
Yadda ta ji ya ambaci sunanta ya sa har sai da ta ji tsikar jikinta tana tashi, ta janyo filo ta rungume cikin wata irin murya ta amsa.
"Na'am Abban Nana!"
Ajiyar zuciyarsa ta ji har a fili, ya sake narke murya ya ce.
"Ba na son ki dinga kirana da wannan sunan, tun da ita ma waccen haka take faɗa. Don Allah ki saka mini sunan da zai dinga faranta mini rai."
Maimuna ta lumshe ido, ta ɗan shagwaɓe murya ta ce.
"Baby ya yi?"
Shi ma sai ya yi irin muryarta ya ce, "To ya zan yi? A dinga faɗa mini hakan, amma dai har yanzu kin ƙi ki ba ni dama na nuna miki zallar soyayyar da nake yi miki a cikin zuciyata."
Jafar ya sake kwantar da murya cike da shauƙi, kamar wanda yake waya da matarsa ya ce.
"Moon! A gaskiya Naziru ba ƙaramin dace da sa'a ya yi ba. Wallahi da ace ke na fara gani kafin Sumayya, da babu abin da zai hana ban aure ki ba. Don Allah ki ba ni dama koda sau ɗaya na nuna miki salon tawa kulawar."
Wani farinciki ne ya lulluɓe Maimuna, tabbas ko bai faɗa mata ba. Ta sha ji a bakin Maman Nana, cewar Jafar gwani ne a fagen kulawa da soyayya. Don da bakinta take ba ta labarin Jafar irin maza nan ne masu buɗaɗɗan ido, don cewa ta yi wani lokacin wayewarsa har tsoro take ba ta. A duk lokacin da Maman Nana take ba wa Maimuna labarin mijinta, sai dai ta yi ta sha'awa tana jin ina ma ita ce ta yi dacen samun miji wayayye mai rifin asiri kamar ita. Kafin daga baya kuma su tsunduma kogin soyayyar da suka yi nisan kiwo ba tare da sun ankare ba.
"Moon! Ba ki ce komai ba."
Jafar ya katse mata tunani, Maimuna ta yi murmushi sannan ta ce.
"Ina tsoron kada Maman Nana ta gano mu, ka ga a cikin unguwa ɗaya muka."
"Haba My Moon, ai dama ko don magulmata ba za mu haɗu a unguwa ba. Wallahi ko hotel zan iya kama mana..."
Cikin razani Maimuna ta ce, "Hotel!"
Kafin Jafar ya yi magana daga can falo ta ji motsi, da sauri ta katse wayar ta zare batirinta. Jikinta har karkarwa yake, ta tura wayar cikin drowerta.
Tana waigowa ta ga Naziru yana tsaye a bakin ƙofa ya harɗe hannuwa a ƙirjinsa.
"Maimuna da wa kike magana?"
Ƙirjinta ya buga da wani irin ƙarfi, cikin firgici bakinta yana rawa ta ce.
"Ni... ni... kuma?"
Fuska ta ga ya ƙara haɗewa, bai tanka mata ba sai gyaɗa mata kai da ya yi.
Kabir yana fita daga gida tun bai ƙarasa titi ba, ya kira Sury. Cikin muryarta mai fisgar hankalinsa ta ce, "Matsoracina! Wato sai yanzu ka samu damar fita daga gida?" Kabir ya saki murmushi ya ce, "Kin gan ki ko?"
Sury ta ɗan haɗe fuska kamar tana gabansa ta ce, "Kb ni fa jiya abin da ya faru ka sa na fara jin tsoron ko yadarata kake yi. Ka duba fa ka gani tambaya ɗaya matarka ta yi maka amma duk ka birkice, yanzu a haka za mu yi auren har ka kai ni gidan da kake gini?"
Kabir ya kwantar da murya ya ce, "Haba baby, me ya sa kike kawo wasu-wasi a cikin soyayyarmu ne? Kin san dai ina sonki ina ƙaunarki. Ko soyayyar da na nuna miki jiya ya ci ki fahimci irin soyayyar da nake yi miki. Ki ajiye maganar aure, wannan wani lissafi nake yi a kansa kin san ke ba kalar zaman gidan haya ba ce."
Sury ji ta yi kanta ya sake girma, ta lumshe ido cike da jin soyayyar Kabir tana sake nuƙurƙusarta. Domin Kabir irin mazan nan da suka iya nuna zallar soyayya, duk cikin samarin da ta yi babu wanda take yi wa mutuwar so kamar Kabir.
Sun jima suna hira sannan suka yi sallama, suka tsayar da magana a zuwa bayan la'asar zai kai Sury gidan da yake gini ta gani.
Har zai saka wayar a aljihu sai ya ha wata lambar ta shigo, guntun tsaki ya saki kamar ba zai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka. Yana ɗauka ya ji ta fashe masa da kuka, shiru ya yi yana jin kukanta har cikin jikinsa.
"Kukan na mene ne?"
Kabir ya furta cikin tattausan lafazi.
"Na gagara jure rashinka ne, na gagara jure horon da ke raunatar da zuciyata. Kabir! Ka san na saba da hutawa a lambun ƙaunarka, sai da ka bari zuciyata ta yi nisan kiwo a ƙaunarka sannan kake ƙoƙarin fincike ta da ƙarfin tsiya. Me ya sa kake azabtar da ni Kabir?"
Kabir ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Hafsa kenan! A kullum haka kike faɗa a fatar baki, amma kin gagara nuna mini zallar soyayyar da kike faɗa. Hotuna biyu kawai na ce ki ɗauka ki turo mini, amma kin ƙi yarda ko ba ki yarda da ni ba ne?"
Jim Hafsat ta yi tana nazari zuwa can ta ce, "Shi kenan, zuwa dare zan turo maka matuƙar za ka sauka daga dokin zuciyar da ka hau."
Kabir ya cije baki yana murmushin samun nasara ya ce, "Haba ko ke fa Hafsyna, da sai nake ganin kamar ni nake wahalar da kaina a kanki."
Hafsa ta ce, "Hmmm ba za ka gane halin da nake ciki ba, yanzu dai yaushe za ka zo."
Shiru ya yi yana nazari, don Sury ta kwaɗaitar da shi irin salon tata soyayyar. Kuma ko babu komai ya san idan ya kai ta kangon da yake gini, zai iya samun fiye da abin da ta yi masa a soron gidansu a daren jiya. Don haka ya ce, "Ammm yau dai gaskiya ɗinki ya yi mini yawa, saboda akwai kayan amaren da ban kammala ba. Bayan haka ma, Oga yana raba mana ɗinki saboda gobe za a tafi da su Abuja. Ina jin sai zuwa gobe za ki gan ni."
Hafsa ta narke murya ta ce, "Wallahi na yi kewarka, kwana ukun da ka daina ɗaukar wayata ji nake kamar mun shekara ɗari uku."
Kabir ya yi murmushi sannan suka cigaba da hira, bayan sun gama ya wuce shago.
Bayin Allah wasa farin girki kenan, me kuka fahimta a game da rayuwar Kabir?
Kabir yana da 'yanmata amma ya aka yi Fauziya ba ta sani ba? Kuma me kuke tunanin ya sa ta ba shi yarda 100% a kan babu budurwar da yake kulawa. Ga dai Maimuna tana soyayya da mijin maƙociyarta, shin wacce amsa za ta ba wa mijinta Naziru? Sai na ji daga gare ku.😄
Ummou Aslam Bint Adam
+2347062062624
[07/02, 20:00] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.
SHAFI NA UKU
Tun da yamma ta kawo kai Sury ta fara doka wa Kabir kira, saboda zumuɗi tun bayan azahar ta gama shiryawa. Kasancewar akwai ɗinkunan da Ogansu ya tara na 'yan wunin biki ya sa shi tsayar da ragowar yaran shagon ya raba musu ɗinkunan domin su yi saurin gamawa. Wannan dalilin ne ya sa da Sury ta kira shi ya sanar da ita, ta ɗaga mata ƙafa ko zuwa gobe ne. Ko kaɗan ba ta ji daɗi ba don haka ta nuna masa ɓacin ranta.
"Kb shi ya sa nake tsoron soyayyarmu, wallahi sai na ga kamar yaudarata kake yi. Na kai kwana nawa ina son ka kai ni na gano ginin nan, amma yanzu ka zo kana tsara ni."
Kabir ya miƙe ya fita zuwa ƙofar shagon ya ce, "Kin gane Sury, wallahi da gaske nake yi miki. Amma tun da haka ne ki ba ni zuwa nan da bayan sallar magriba, duk yadda zan yi na san yadda zan ɓullowa Oga koda ban gama aikina ba."
Sury ta ɗan yi jim sannan ta ce, "Amma ka san bayan magriba Yaya Umar ba ya barinmu fita, sai dai na san dabarar da zan yi masa."
Kabir ya yi saurin faɗin, "Yawwa Suryna, kamar ba mace ba. Don Allah ki shawo mana kansa ba za ku daɗe ba, muna gama gani za mu wuce."
Sai a lokacin Sury ta ji daɗi, ganin ya lallaɓa ta ya sa shi yim sallama da ita ya koma cikin shagon. Ɗinkin kusan mutum uku ne a gabansa, don haka ya ci gaba da ɗinkin cikin sauri don ba ya son abin da zai sake ɓata ranta.
Girgiza kai Maimuna ta yi, don har cikin ranta gani take kamar Nazir ya ji kalaman da suke tattaunawa. Amma gudun ta yi saurin bada kai bori ya hau, ya sa ta ce.
"Gaskiya sai dai idan kunnenka ne."
Shiru ya yi yana kallonta kamar mai nazari, har sai da ta sake tsarguwa. Domin a lokacin da ya shiga ji ya yi kamar waya take duk da bai ji abin da take faɗa ba, amma da yake ya ga wayarta tun a falo sai ya basar. Yana shirin yin magana ta ce, "Ko dai waƙar da ka ji ina yi ce?" Cikin halin ko inkula ya ce, "Wataƙila! Ina wayarki take?"
Ya tambaye ta don Nazir mutum ne mai bin diddigi da tsanani a kan iyalinsa.
"Tana falo!"
Ta ba shi amsa a taƙaice.
Falo ya koma ya ɗauki wayarta, sai da ya yi shige-shige sannan ya saki muryarsa ya ce.
"Wallahi mantuwa na yi, na manta hulunan mutane ɗauko mini suna drowerta."
Sai a lokacin hankalin Maimuna ya kwanta, ta shiga ciki ta buɗe drowersa ta ɗebo masa hulunan ta ba shi sannan ya sake fice. Ajiyar zuciya ta sauke a fili, sannan ta furta.
"Dole na sauya taku, tun da mutumin nan yana key da yake buɗe ƙofa. Ya zama dole na yi takatsantsan, idan ba haka ba a samu matsala."
Gate ɗin ta sake komawa ta saka sakata a gidan, sannan ta koma ta zaro ɓoyayyiyar wayarta. Mayar da batirin ta yi bayan ta kunnata ta sake kiran Jafar.
"Hello!"
Ta furta cikin kashe murya. Daga can ɓangaren Jafar ya ɗauka murya can ƙasa, sai kuma ta ji muryar Abdul yana kuka.
"Wai kana nufin ba ja fita kasuwa ba? Na ji kamar muryar Abdul ko?"
Murmushi Jafar ya yi ya sake jan bargo ya ƙudundune, wani shauƙi yana fisgarsa a kan Maimuna ya ce.
"Ya za a yi na iya fita? Bayan ina lulluɓe da bargon bege da kewarki. Don Allah Moon ki nemar mana mafita mana, ki tausaya mini wallahi muryarki ba ƙaramin gigita nutsuwata take yi ba."
Shiru Maimuna ta yi, tana nazarin hanyar da za ta ɓullo musu domin ita kanta ta kwaɗaitu da ta ga irin soyayya da Maman Nana take faɗa mata.
"Ka san dai halin Nazir mutum ne mai shegen kishi, ga shi da zargi da bin diddigin duk abin da nake yi. Kana ga hatta unguwa ba ya iya barina na je, shi yake kai ni duk inda za ni. Wallahi kaina ya kulle ban san ya zan yi ba."
Nazir ya kwaɓe murya ya ce, "Wallahi ni sai na ga kamar ma ba kya jin irin soyayyar da nake yi miki. An ya kin san yadda zuciyata ta kamu da mutuwar sonki kuwa..."
Salatin da Maman Nana ta saki ya sa Jafar ya yi sauri ɗagowa, nan take gabansa ya faɗi. Maman Nana da kishi ya gama tirniƙe ta ta ce, "Na gode Abban Nana, yanzu wulaƙanci da tozarcin naka ya kai har ka haye mini kan gado ka kira wata shegiya kuna waya da ita? Yanzu ka yi mini adalci kenan? Ashe duk alƙawarurrukan da kake ɗaukar mini na ƙarya ne." Sai kuwa ta fashe da kuka. Hamdala ya yi a ransa da ya fahimci Sumayya ba ta gane da wacce yake waya ba.
"Don Allah ki yi haƙuri My love, wallahi duk wani abu da kika ji na faɗa wa yarinyar nan a fatar ba ki ce. Wata yarinya ce ta nace mini, ni kuma ba na son yi mata rashin mutumci kin san wulaƙanci babu kyau shi ya sa nake soj mu rabu lafiya."
Wani irin mugun kallo tajw jifansa da shi, rai a ɓace ta ce. "Idan kai ba za ka iya yi mata rashinn mutumci ba hi zan iya, ka kira mini ita in zazzage ta ko wacece."
Kamar gaske Jafar ya ɗago wayar ya kira ta amma sai suka ji a kashe, ya saki murmushi a cikin ransa. Ya rungumo Maman Nana ya ce, "Kin ji wayar a kashe take, amma riƙe ki yi blocking ɗinta da kanki. Dama ni ban taɓa kiranta ba, ita take kirana amma tun da an yi haka babu ni babu ita. Munafuka haka kawai za ta haɗa ni faɗa da iyalina ian zaman lafiya da ita."
Har a ranta ta ji daɗi, don haka ma ta ɗan saki fuskarta. Ta karɓi wayar ta saka ta a blacklist, sannan ta ce.
"Abban Nana wallahi wannan ita ce ta farko ta ƙarshe, kada ka mata kwanaki ma haka na yi yaƙi da kai a kan Fati wacce ka ce wai ƙanwar abokinka ce. Wa ya sani ba ko ita ce wannan, wai yanzu duk irin kulawar da nake ba ka amma sai ka kula 'yanmata."
Maman Nana ta ƙarasa maganar cikin ɗacin rai.
"Don Allah ki daina dawo da bara bana, waccan ta wuce kuma wannan ma In Shaa Allahu ta wuce ba zan sake ba." Ruwan wanka ta juye masa ta dawo ta ce, "Lokacin fitarka yana tafiya ga ruwan wanka can na juye maka."
Yanayin da yake ciki na tunanin Maimuna ya sa shi janyo hannunta ya ce, "Wai kwana biyu ba ki da lafiya na ga ko gayyatata ba kya yi!"
Murmushi ta yi masa ta ce, "Ai na ga ba ka dawowa da wuri ga gajiya shi ya sa." Da yake ta kwantar da Abdul ya yi bacci, sai bayan da komai ya gifta a tsakaninsu sannan suka faɗa toilet lokaci ɗaya. A gurguje ya shirya ya tafi kasuwa ganin har sha biyu saura, Maman Nana ta cigaba da aiki cikin sauri tana alla-alla ta gana ta leƙa gidan Maimuna.
Tun lokacin da Maman Nana ta fara magana, Maimuna ta yi shiru tana sauraronsu. Lokacin da ta ji Jafar ya ce zai kira layin Maman Nana ta zage ta, sai ta yi sauri ta kashe wayar gabaɗaya. Haka kawai ta ji wani irin kishi ya rufe, ta shiga hango irin rarrashin da Jafar zai mata. Domin Maman Nana ta sha ba wa Maimuna labarin idan Jafar ya yi mata laifi matuƙar shi nw ba shi da gaskiya har kusan tsugunna mata yake yi.
Sai da Jafar ya shiga mota yana driving sannan ya kira Maimuna amma sai ya ji ta a kashe, guntun tsaki ya saki ya ajiyw wayar sannan ya cigaba da driving. Sai da ya cikin shagonsu sannan yana duba wayarsa ya ga misscall ɗinta. Hannunsa har rawa yake ya kira ta ya ce, "Wallahi Sumayya ta yi bala'in ba ni haushi, ina tsaka da jin muryarki ta zo ta yi mini tsaye a ka." Ya yi maganar yana sakin tsaki.
"Hmmm bayan da ka gama ba ta haƙuri kenan, ai na san yadda kalw bala'in jin tsoronta."
Jafar ya saki dariya ya ce, "Kamar wani matsoraci, idan muka haɗu ai za ki gane ni jarumin gaske ne "
Maimuna ta yi murmushi za ta yi magana ya katse ta.
"Yanzu dai ba wannan ba, na lura haɗuwa za ta yi mana wahala. Amma me zai hana na saya miki babbar waya sai mu dinga chatting da ita, na fito na dinga ganinki ina jin daɗi ko na samu nutsuwa."
Shiru Maimuna ta yi ta ce, "Kana ganin ba za a samu matsala ba?"
"Matsalar me Moon? Ai kin ga wannan layin da muke waya babu wanda ya sanki da shi, kuma ke ba kowa za ki yi wa magana ba sai ni. Ba sai mu dinga magana ba."
'Maimuna me kike shirin aikatawa ne? Wai ko kin manta kina da aure?'
Wata zuciyar ta raya mata a rai, sai ta ji sam zuciyarta ta mata babu daɗi.
"A gaskiya sai na yi nazari, sai an jima zan dafa wa yara abinci."
Jin sauyin muryarta ya sa shi saurin faɗin, "Lafiya My Moon, ko kina
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 35