mijinku ya yi asiri ne ta yi masa." Shukura ta yi zaraf ta ce.
"Ai wallahi na zargi matsiyaciyar nan."
"To wannan ba damuwa ba ne, tun da kayanki suka tsinke a gindin kaba. Za a yi miki aiki iya aiki, amma fa sai kin zubar da kuɗi. Saboda aikin za mu yi da baƙaƙen aljanu, kuma su kansu za mu zubar musu da jini. Ragowar kayan aikin ma idan muka faɗa miki su, idan za ki shekara ɗari ba za ki same su ba." Ta ji malamin ya yi mata bayani. Cikin sauri ta ce.
"A'a Malam, gara dai ka sayo da kanka. Ni kuɗi ba matsalata ba ne, nawa kake ganin za a bayar?"
"Zan sanar da mahaifiyarki, domin ita ya kamata ta damƙa mini hannu da hannu." Amsa masa ta yi sannan suka yi sallama, sai bayan ta gama sannan ta fito ta koma kan gado ta kwanata. Tana jin damuwar da take ciki kusan kaso casa'in ta tafi, don haka ta samu bacci ya yi awon gaba da ita.
ALHAJI UMAR
Abin duniya ne ya haɗe wa Daddy, gabaɗaya komai ya fita daga rayuwarsa. Har ji yake yi, a kan Mommy matuƙar bai same ta ba zai iya rasa rayuwarsa. Babban abin da ya ɗaga masa hankali, har kawo wani lokaci mai tsayi Baba malam bai sake bi ta kansa ba. Idan kuma ya kira shi a waya ba ya ɗauka, haka ita ma layin Hajiya Karima ya kira babu adadi ta ƙi a ɗauka. Daga ƙarshe ma sai ya ji wayar ta daina shiga, da Momny ta ga ya ƙara sauya layuka yana kiranta da su, sai ta saka wayar a DND sannan ta samu lafiya da shi.
Da Daddy ya ga ya bi duk wata kafa da zai samu Mommy bai samu ba, sai ya koma kiran ragowar 'yan'uwansa yana kai kukansa wurinsa. A ranar da ya kira yayansa Baba Yunusa ya gama zayyane masa damuwarsa, ba ƙaramin tausayinsa ya yi ba. Saboda ya san duk abin da ya yi a baya ba yin kansa ba ne. Cike da tausayin ɗan uwansa ya ce.
"Umar wannan matsalar taka tana hannun Baba malam, saboda ni da 'yan'uwana ka san ba mu da hurumi a kan wannan maganar. Yanzu dai ka yi haƙuri, In Shaa Allahu zan gwada sa'ata na kira shi na ga ko zai saurare ni." Jiki a sanyaye Daddy ya taso daga gidan, bayan kwana biyu a tsakani Baba Yunusa ya kira shi ya ce Baba malam bai saurare shi ba.
Tun Daddy yana ganin abin kamar wasa har aka sake shafe watanni a haka, duk wanda ya kira ya je wa da ƙorafin maganar Mommy sai dai ace masa ya bi ta wurin Baba malam. Wannan yanayin ya sake birkita shi, har zamansa da Shukura ya koma irin zaman doya da manja. Kwata-kwata ba ta ganinsa a gida idan ba dare ne ya yi ba, idan gari ya waye zai fice. Idan kuma ta matsa sai ya zauna a gida, ba shi da magana sai ta Mommy da iyalanta. Ga kaɗaici da ya dame ta, saboda gidan ya yi mata girma wani lokacin har tsorata kanta take yi. Musamman idan zuciya ta fara yi mata ayyane-ayyane, ga shi duk kuɗaɗen da suke kashewa a wurin malamai babu aikin da yake ci. A kan haka har faɗa suka taɓa yi da mahaifiyarta, saboda Shukura gani take kamar cinye mata kuɗi Inna take yi. Ita kuma Inna ganin bakin ƙoƙarinta take faɗi-tashi wurin bin malamai sai ya abin ya ɓata mata rai. Sai daga baya suka daidaita, ta cigaba da bata miyagin shawarwari amma babu wacce take mata amfani.
Bayan kwana biyu da faruwar al'amuran, watarana da safe ciwon hawan jinin Daddy ya tashi. Hankali a tashe Shukura ta fita wurin mai gadi cikin kururuwa ta sanar da shi, da sauri ya shiga ɗakinta ya riƙo Daddy da ya fara fita daga hayyacinsa ya saka shi a mota. Da sauri Shukura ta shiga mazaunin direba ta tuƙa shi ta nufi asibiti da shi, cikin kulawa likitoci suka karɓi Daddy suka shiga ba shi agajin gaggawa. Sai da ta ga ya ɗan dawo hayyacinsa, sannan ta zame jiki ta fice daga ɗakin, ta latsa lambar Inna ta kira ta sanar da ita. Sai da ta gama sauraronta ta ce.
"Wai Shukura me ya sa ba ki da wayo ne wani lokacin? Dama kin san haka jikinsa ya yi zafi shi ne ba ki sanar da ni ba? So kike mu gama ƙarar da gishirinmu a dahuwar ƙaho, ba tare da ya amfane mu da komai ba? Ko so kike mu yi wahalar hura wuta, zafin hayaƙi ya gama kashe mana idanuwa ba tare da mun sharɓi romon ƙahon da muke dafawa ba?"
"To Inna ya kike so na yi? Ba fa ni na ɗora masa ciwon nan ba, duk ta sanadin tsohuwar matar nan yake neman kassara rayuwarsa. Wallahi ba na son na rasa Alhaji, saboda ba ƙaramin so nake yi masa ba." Shukura ta furta muryarta tana rawa.
Dogon tsaki Inna ta ja sannan ta ce.
"Wallahi kin ba ni mamaki Shukura, au ke da soyayyar gaskiya ce ta kai ki gidan? To ki buɗe kunnenki da kyau ki saurare ni."
Murya a sanyaye Shukura ta ce, "Ina jin ki Inna."
"Har yanzu ba ki ci adadin kwanakin da na ɗebar miki a gidan Alhaji ba, duka-duka yaushe aka yi abin da mutuwa take ƙoƙarin hana mu rawar gaban hantsi? Ko fa haihuwar fari ba ki yi ba, idan ya mutu yanzu ribar me muka ci?" Inna ta furta cike da damuwa, kamar Shukura za ta yi kuka ta ce.
"A'a Inna don Allah ki daina zancan mutuwa, ni dai tsakani da Allah nake son shi wallahi. Ina laifin abin da muke samu yanzu ma."
"Shashasha! Ana nuna miki gabas kina cewa kudu ce. Yanzu dai abin da nake so da ke, ki shirya ki tafi gidan yayansa Baba malam ɗin, ki sanar da su rashin lafiyarsa. Sannan ki fashe da kuka ki nemi yafiyar Hajiyan da 'yan'uwansa, ni kuma duk abin da na zo asibitin na aikata a kanki kada ki tuhume ni. Duk a cikin plan ne, ke ko dawo da itan ne ki tsaya tsayin daka a dawo ita ai ribarmu ce."
"Haba Inna, me kike faɗa haka? Gidan Baba malam fa? Kin san yadda suka tsane ni kuwa?"
Murmushin manya Inna ta yi ta ce, "Yaro man kaza, kin san dai ba na ƙwaina ai sai da zakara. Kuma banza ba ta kai romo kasuwa. Tun da kika ji na faɗi haka ki bar ni mu tafi a haka, idan hagu ta ƙi ai sai mu koma dama. Tun da asirin ya ƙi ci, sai mu gwada kissa mu gani."
Cikin damuwa Shukura ta ce, "Gaskiya Inna hankalina bai kwanta da wannan shirin ba, yanzu sai mu bari ya dawo da Hajiya ana zaune..."
"Shukura kin san dai ba zan saka ki a hanyar da ba za ta ɓille mana ba. So nake mu dafa ta da ruwan jikinta, ta yadda za ta gwammace zamanta a waje saɓanin cikin gidan." Inna ta furta cike da kwantar da hankali. Murmushi mai sauti Shukura ta yi, sannan ta ce.
"Allah Ya bar mini ke Innata." Inna ta amsa sannan suka yi sallama.
Shukura tana shiga ta tarar har lokacin Daddy bacci yake, da yake allurar da suka yi masa mai ƙarfi ce. Kuma a wannan asibitin Daddy yake ganin likita, nurses ɗin ta samu ta ce musu za ta je gida ta dawo. Amsa mata suka yi, sai da suka kira wasu daga cikin ma'aikatansu suka zauna a wurin Daddy sannan ta wuce gidan Baba Malam.
Shukura tana zuwa gidan Baba malam ta yi horn a bakin gate, mai gadi ne ya tambaye ta wurin wanda ta zo. Bayan ta sanar da shi, sai da ya ɗaga waya ya kira Baba malam ya sanar da shi sannan ya buɗe mata ta shiga.
Duk da Baba malam ya ji ɗacin zuwan Shukura, amma ya bar ta ta shigo ne albarkacin tana auren ɗan'uwansa. Uwa-uba kuma ya sa an buɗe mata ne, don ya ji abin da yake tafe da ita. Shukura ta yi mamakin yadda mutanen gidan suke ta karrama ta, duk sai ta ji ta tsargu. Tana nan zaune Haidar ya shiga falon, wani mugun kallo ya wurga mata. Da sauri ta kawar da kanta gabanta yana faɗuwa, buɗe firji ya yi ya ɗauki ruwa ya yi gaba. Fitarsa babu jimawa Mommy ta shiga da niyyar cire wayarta a caji, kallon-kallo suka shiga yi wa junansu. Mama ba ta taɓa tsammanin Mommy za ta kula Shukura ba, amma sai ta ga ta saki murmushi ta ce.
"Aunty yau baƙi ne a gidan namu?"
Mama ta ce, "Eh wallahi, Shukura ce ta zo wurin Daddyn yara. Wai Daddyn Mami ne a asibitu ba shi da lafiya." Ɗan taɓe baki Mommy ta yi ta ce.
"Oh dama fa haka ake ta fama, Allah Ya sawaƙe." Daga haka ta ɗauki waya ta nufi ɗakinta.
Baba malam ne ya shiga cikin falon, Shukura tana ganinsa ta cigaba da share hawaye cikin shasshekar kuka.
HAFIZ
Su Hafiz suna zuwa asibiti likitoci suka shiga yi wa Amina tambayoyi tana ba su amsa, gwaje-gwaje suka yi mata suka tabbatar da cikinta lafiya ƙalau yake ba su ga wani abu da yake damunta ba. Sai kuma jininta da ya ɗan yi ƙasa kaɗan, abin da suka ce sun gani a jikin Amina kenan. Gudun kada Hafiz ya gano Amina, sai ta ce musu tana ɗan yawan ciwon kai. A nan suka sake ba su shawarwari a kan ta dinga samun bacci wadatacce, ta kuma dage da cin abubuwa da ke gina jiki. Suna fitowa daga asibitin ya ga kiran mahaifinsa, sai da suka shiga adaidaita sahu sannan ya ɗauka cikin girmamawa. Bayan sun gaisa Baba ya ce.
"Hafiz kana ina ne?"
Hafiz ya ce. "Baba yanzu na fito daga asibiti."
"To idan ka gama ina son ganinka kai da Amina."
Baba ya furta a gajarce, sannan ya katse wayar.
Gaban Hafiz ne ya faɗi, don tun da ya ji haka ya san ba ya wuce Bilkisu ce ta kira ta faɗa masa wani abin. Ita kanta Amina sai da ta ji gabanta ya faɗi, da yake ba ta saba irin waɗannan ƙarairayin ba har gani take kamar idan suka je za a iya gano ciwon ƙarya take yi.
Lokacin da suka ƙarasa gidansu Hafiz, su Sayyid suna tsakar gida suna wasa. Oyoyo suka yi masa, bayan da suka gaisa da mutanen gidan sannan suka wuce ɗakin Mahaifinsa. Tun da ya ga su Sayyada jikinsa ya ba shi Bilkisu tana gidan, sai da suka gaisa sannan Baba ya sa aka kira Bilkisu. Fuska a haɗe ta shiga ta nemi wuri ta zauna, Baba ya dubi Bilkisu ya ce.
"Bilkisu maimaita mini abin da kika ce ya haɗa ku."
Kamar tana jira, Bilkisu ta shiga wassafa jawabin abin da ya faru. Baba ya dubi Hafiz ya ce.
"Shin abin da matarka ta faɗa haka ne?" Gyaɗa kai ya yi sannan ya cigaba da cewa.
"Baba ni ban hankaɗe Bilkisu, saboda wata manufa ko don na wulaƙantata ba. Yanzu Baba saboda kwananta ne, sai ta ce ba zan kai Amina asibiti ba don ba ta da lafiya? Ita Bilkisun sau nawa idan kwanan Amina ne, za ta kira ni ta ce yaro ko ita ba lafiya amma haka nake fita na ba su kulawa."
Ajiyar zuciya Baba ya yi ya ce.
"A gaskiya Bilkisu ba ki kyauta ba, ko Hafiz ba ya nan ai ke mai kai 'yar'uwarki asibiti ne." Baba ya nuna Amina, sannan da sake kallon Bilkisu ya ce.
"Ke Amina da Bilkisu na dawo gare ku, ku ji tsoron Allah a zamantakewarku. Ku sani duk wacce kuka cutar Allah ba zai bar ku ba, zan yabi Hafiz ba don yana ɗana ba. Amma ku sani yana ba kin ƙoƙarinsa a kanku, ku haɗa kanku ku rungumi mijinku ku zauna lafiya." Baba ya jima yana yi musu nasiha, har jikin Amina ya yi sanyi ta ji za ta watsar da duk wani zaman ƙarya da makirci da ta tsira. Ta saka wa ranta duk rintsi za ta cigaba da zaman haƙuri, da kyautatawa mijinta. Musamman da Baba ya nuna musu muhimmanci haƙuri da ladan da mace take samu ya yin ibadar aure.
A kwanaki biyun da suka biyo baya, gidan Hafiz suna zaune lafiya ƙalau. Saboda Amina gabaɗaya ta zubar da makamanta, ta cigaba da zama da Bilkisu da zuciyarta ɗaya tsakaninta da Allah kamar yadda ta zo tun farko. Ita ma Bilkisu a haka nunawa ta yi kamar komai ya wuce, don haka ta dinga kwantar da kai har Hafiz ya gama sakin jiki gidansa ya zauna lafiya.
Ana cikin haka kuma sai Bilkisu ta tsiro da wani sabon makircin, don har lokacin da cikin Amina ya tsufa ba ta cire rai da fitar da ita daga cikin gidan ba. Sabon layi Bilkisu ta saya ta saka a wayarta, idan Amina da Hafiz suna zaune sai ta tura mata saƙon soyayya. Idan ka ga irin saƙon za ka yi tsammanin saurayi ne ya turawa budurwrsa da yake tsananin so. Tun abin bai fara damun Amina ba, har watarana ta taɓa yin replay da cewar wrong number ne. Tun ana tura mata text har ta kai wani lokacin ana kiranta a waya, amma idan ta ɗauka sai ta ji an yi shiru. Tafi-tafi sai ya zamana idan ta ɗauka sai dai ta ji an ce ana sonta, ko an yi kewarta. Wani zubin har cewa ake yi an yi kewar ni'imarta. Tun da ta ji ire-iren miyagun kalaman, ba ta sake ɗauka ba. Kuma ba ta taɓa tunanin faɗa wa Hafiz ba. Ita kaɗai ta bar abin a cikin ranta, don ba ta ɗauka lamarin zai yi tsamari ba.
Watarana da daddare Hafiz yana ɗakin Bilkisu yana cin abinci, sai ji ya yi ana ƙwanƙwasa ƙofa. Miƙewa ya yi ya fita ya buɗe ƙofar, wani almajiri ya yi gani da wata leda a hannu. Almajirin bayan ya gaishe shi ya ce.
"Ai ko ni aka yi."
"Kawo saƙon, waye ya turo ka?" Hafiz ya furta yana kai hannu zai karɓa, da sauri almajirin ya janye ya ce.
"Mutumin ya ce kada na ba wa kowa sai Amina."
Da mamaki Hafiz ya ce.
"Wani ne ya turo ka? Wane ne shi?"
Almajirin ya ce, "Eh wani ne a mota, ya ce na kawo mata."
Zuciyar Hafiz ce ta fara tafasa, sai ya daure ya ƙwala wa Amina kira. Da ƙyar ta yunƙura ta taso, saboda yadda cikinta ya tsufa. Tana zuwa rai a ɓace Hafiz ya ce.
"Ga aikenki nan sai ki karɓa."
Da mamki Amina ta dubi Aljamirin ta ce, "Kai waye ya aiko? Daga ina kuma?" Almajirin ya waiga ya ce.
"Wani ne a mota ya ce na kawo miki, ya ce a ce miki wanda ya ɗauko ki daga asibiti ne rannan. Wai ki kira shi idan kin ga wannan saƙon." Cikin mamaki Amina ta sake cewa.
"Ni kuma? An ya nan aka ce ka kawo kuwa? Gaskiya ba nan ba ne."
"Ni dai nan ya ce na shigo na kawo wa Amina."
Almajirin ya faɗa, Amina za ta sake magana Hafiz ya ce.
"Yana ina mutumin?"
Almajirin ya ce, "Ai yana ba ni da ya ga na shigo ya tafi." Zuciyar Hafiz har ɗaci take yi ya kai hannu ya karɓi ledar ya ce.
"Jeka kawai." Yaron ya juya ya fita, Hafiz ya buɗe ledar yana leƙawa. Farin hanki ya gani da turare, sai zoben azurfa da aka ƙawata mai ɗauke da alamun gift daha masoyi. Sai ya ga wani ɗan memo mai kyau, yana buɗe ciki ya ga an rubuta.
' _Ga ɗayar numberta nan, idan kin nemi waccan layin ba ki samu ba. Daga masoyinki da ke burin kasancewa da ke koda bayan kin haihu ne._'
Nan take idanun Hafiz suka kaɗa jajir saboda tsananin kishi, kallon da ya wurga wa Amina ne ya sa cikinta ya karta.
"Ina wayarki take?"
Hafiz ya furta da wata irin murya, jikinta har rawa yake ta ce.
"Ta...tat... tana ɗaki."
Bai amsa mata ba ya wuce ɗakinta rai a ɓace.
In Shaa Allahu gobe za mu gama book 1💃🏻👌🏻
Masu son karanta book 2 za su biya 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa document 800 ne.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA SHA BIYAR
BABA MALAM
Da mamaki Baba malam ya dubi Shukura ya ce.
"Lafiya dai na ga kina hawaye? Hajiya ko wani abin ne ya faru?" Ya tambaya yana kallon Mama da ke zaune a gefe, girgiza kai ta yi ta ce.
"Babu abin da ya faru Alhaji, na ji dai ta ce Daddyn Mami yana asibiti babu lafiya. Ban sani ba ko jikin nasa ne, amma dai tun da ta shigo take hawaye."
Baba malam zai yi magana Shukura cikin kuka ta ce.
"Don Allah Yaya ku gafarce ni, ku yafe mini ku yafe wa Daddyn Mami. Wallahi yanzu haka yana can a asibiti rai a hannun Allah. Don Allah ka yafe mini Yaya, na san gabaɗaya kowa ya tsane ni saboda abin da ya faru."
Jin rashin lafiyar Daddy ya sa gaban Baba malam ya faɗi, amma gudun kada ya nuna wa Shukura damuwarsa sai ya ce.
"Tun daga haihuwar mutum dama ai ransa yana hannun Allah Shukura, Allah Ya ba shi lafiya. Batun tsana kuma da kika yi, duk cikinmu babu wanda ya tsane ki. Ƙarƙari dai abin da muka yi, mun dai tsani halinki ne."
Shukura a cikin ranta ta ce, 'Ko ni ɗin kuka tsana kun yi ta banza, yanzu ma so nake na yi amfani da ku kafin buƙatata ta biya.' Amma a fili sai ta ce.
"Dama na zo ne na nemi yafiyar Hajiyan Mami, wallahi na yi nadamar duk abubuwna da na aikata a baya. Don Allah Yaya ku yafe mana, wallahi sharrin shaiɗan da ruɗin ƙawaye ne." Shiru Baba malam ya yi ya ce, "Allah Ya yafe mana gabaɗaya, amma wannan ba magana ce da za a yi ta a taƙaitaccan lokaci ba. Muna buƙatar isasshen lokaci tukunna, idan ya so sai a tattauna abin da ya dace." Kamar mutuniyar kirki haka Shukura ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce.
"Na gode Yaya, Allah Ya ƙara girma." Ganin ya yi shiru ta sake cewa.
"Yaya don Allah ku taimaka ku leƙa a sibitin nan, Dadyn Mami yana jin jiki sosai." Karɓar adireshin asibitin ya yi, sannan ya ce ta wuce zai taho.
Bayan tafiyar Shukura Mama ta dubi Baba malam ta ce, "Alhaji wallahi ban yarda da makirar yarinyar nan ba. Haka kawai nake ji a jikina ba da zuciya ɗaya ta yi wannan zuwan ba." Miƙewa tsaye Baba malam ya yi ya ce.
"To ai kowa ya yi na gari kansa, idan ma da wata manufa ta zo Allah ya mayar mata da mugun nufinta kanta. Ki cewa su Mu'alim su shirya za mu je duba shi yanzu."
Mama ta amsa masa sannan Baba malam ya wuce ciki don ya shirya. Sai da ya kira 'yan uwansa ya sanar da su, sannan ya fito shi da su Haidar da 'ya'yansa suka wuce asibiti. Kusan lokaci ɗaya motar Shukura da ta su Baba malam ta shiga harabar asibitin, saboda Shukura ta biya ta store ta yi musu sayayyar abubuwan da za a buƙata. Ganin ta taho hannuwanta ɗauke da manyan ledoji, ya sa Baba malam ya ce su Haidar da Mu'allim su karɓa, babu yadda Haidar zai yi don dai ya san ba shi da damar musawa. Amma da babu yadda za a yi ya karɓi kayan hannun Shukura, suna shiga reception suka hango Inna tana zaune jigum. Shukura tana ganinta har za ta mata magana, cikin zafin nama Inna ta tsinke da mari. Ɗgowar da za ta yi ta sake tsinke ta da mari, da sauri Baba malam ya matsa ya ce.
"Subhanallah! Haba Hajiya ya da haka? Ba ki ga a yanayin da take ciki ba ne?" Inna ta fashe da kuka ta ce.
"Alhaji ka bar ni na kashe yarinyar nan na huta da ta kaicin da ta ƙunsa mini, ashe dama kishiyarta Hajiya ba ta gidan? Sai ɗazu da ta kira ni take sanar da ni abin da ya faru. Wallahi Shukura ke dai ba ki da mutumci, albasa ba ta yi halin ruwa ba." Inna ta ƙarasa maganar tana sake kai wa Shukura duka, da sauri Shukura ta yi bayan Baba malama tana kuka saboda marin da Inna ta yi mata ba ƙaramin shigarta ya yi ba. Baba malam ne ya kare ta cikin lallashi ya ce.
"Don Allah ki yi haƙuri hajiya, idan ka ce za ka biye ta halin yara sai ka nakasa su a banza."
Inna ta fyace majiya haɗe da rushewa da kuka sannan ta ce.
"Alhaji yarinyar nan so take ta ɓata mini suna? Me ta aikata haka? Wallahi kin ci sa'a da Alhaji Ya ƙwace ki, amma wallahi idan ba ki saka Alhaji ya mayar da matarsa ba babu ni babu ke. Mara mutumci ina zaman-zamana za ki ja wa zuri'ata zagi, ke dai ba ki ji daɗin halinki ba." Inna ta furta tana sake kai wa Shukura duka.
Da ƙyar Baba malam ya samu ya shawo kan Inna ta daina barazanar kai wa Shukura duka, haka a gaban kowa ta dinga jaddada idan Shukura ba tayi bakin ƙoƙari, ta saka Daddy ya mayar da Hajiya Karima ba za ta tsine mata. Wannan abin da ta yi ya sa mutane suka dinga yabonta, a ɓangare ɗaya suka dinga kallon Shukura a matsayin wacce take da uwa tagari amma ba ta yi koyi da ita ba.
Lokacin da suka shiga ɗakin Daddy yana kwance ya ƙurawa saman silin ido, har suka ƙarasa wurin bai sani ba. Baba malam ne ya dafa hannunsa ya ce.
"Sannu Umaru."
A hargitse Daddy ya ɗago ya ce, "Yaya kai ne? Don Allah tare kuke da Karima?" Shukura da ke gefe ta ji wani abu ya daki zuciyarta, don ko mai irin sunan Mommy ba ta son ta ji an ambata.
Baba malam ya ce, "Umaru ka nutsu don Allah, ba mu kaɗai ba ne a wurin nan. Ga yara ma sun zo duba ka." Sai a lokacin ya ɗago ya dubi su Haidar cike sa so. Su kansu ba ƙaramin kewar mahaifinsu suka yi ba, ganin ya rame sosai ya sa Haidar ya matsa kusa da shi jiki a sanyaye ya ce.
"Sannu Daddy ya jikin?"
Daddy da idonsa ya fara zubar da ƙwalla ya ce.
"Haidar! Haidar ina Mommynku ko ba ta zo duba ni ba?" Gyaɗa masa kai Haidar ya yi ya ce.
"Ta ce a duba ka, Mami ma ta ce gobe za ta zo duba ka."
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 35