a garin nan ko?"
Mai maganin ya gyaɗa kai ya ce, "Yanzu ma wucewa na zo yi, duk mai matsalar sanyi ya zo muna bayar da taimako don Allah. Idan ya sake na tafi ba zan sake dawowa ba sai baɗi."
"Miƙo mini wancan maganin na jarka, nawa ne kuɗinsa?"
Baba Inu ya tambaya, yana nuna wata zungureriyar jarka da ke cike da jiƙaƙƙun itatuwa a ciki. Jarka biyu mai maganin ya miƙa masa yana faɗin.
"Wannan da kake gani darr kenan, Mai gida ba kowa nake sayarwa ba sai mai sa'a. Ko kana shan kunya a wurin iyalinka, don Allah ka ɗaga roba ka sha rabi ka shiga wurin uwargida ka dawo ka ba ni bayani."
Baba Inu bai jira cewarsa ba ya ɓalle murfin robar, ya ɗaga ta sama sai da ya ga maganin ya ƙare sannan ya wurgar da jarkar. Mai maganin ya zaro ido waje ya ce, "Master amma ka kwana a wannan layin ko?"
Horn ɗin da Baba Ibrahim ya yi ne ya katse Baba Inu da yake shirin bayar da amsa.
"Abokina ja motarka gefe ga masu iko da gidan sun ƙaraso."
Mai maganin ya ja motarsa gaba, a daidai lokacin Baba Ibrahim ya ƙarasa da ta shi motar ya yi parking sannan ya fito daga ciki. Tun lokacin da mai maganin ya ƙarasa gaban Baba Inu ya shawo kwanar layinsu, a kan idonsa Baba Inu ya ɗaga ya shanye. Da sallama ya ƙarasa wurinsa haɗe da faɗin.
"Yaya barka da hutawa."
Baba Inu ya ɗan kalle shi a sheƙe ya ce. "Bokan turai yau kuma lafiya na ga ka dawo da wuri?"
Baba Ibrahim ya ce, "Lafiya ƙalau Yaya."
Ganin Baba Ibrahim ya tsaya ba tare da ya yi magana ba ya sa Baba Inu ya ce, "Iro ya aka yi? Ka saka ni a gaba ko kai ma a miƙo maka maganin ne?"
Da sauri Baba Ibrahim ya ce, "Allah ya kiyashe ni, ni kam."
Baba Inu ya dube shi a gwasale ya ce, "Yo dama ina abin yake maye ya ci jariri, mai mace ɗaya har ya bugi ƙirji ya saka kansa a sahun mazaje. Ai maza kam suna inda suke."
Baba Ibrahim ya girgiza kai ya ce.
"Yanzu Yaya hanyar da ka ɗauko wa kanka mai ɓillewa ce? Saboda Allah a ce kai kullum cikin shaye-shaye da jiƙe-jiƙen magunguna kake kala-kala. Kullum masu magani sai dai su dinga layi a ƙofar gidan nan, mutanen garin har sun fara gane ka? Magungunan fa yawanci waɗanda kake sha babu wata ƙa'ida kai tsaye kake hankaɗa wa cikinka, kuma mafi yawa masu haɗa magungunan nan da ka suke yi ba su da ilimin abin. Ko mu da muke likitocin asibiti, babu yadda za a yi mu ɗauki magani mu ba ka ba tare da mun duba ka ba."
Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya cikin takaici ya cigaba da cewa.
"Yaya da ace kuɗaɗen nan da kake kashewa a sayen magungunan tara su kake, da ko nauyin karatun yara ka rage da su. Amma ka bar yara haka, hatta makarantar allo ba duka ne suke zuwa ba. Kuma saboda Allah ga shi nan, kullum wasu ƙananan ƙwayayan ake sake ƙyanƙyashe maka."
Baba Inu ya ɗago fuska a haɗe ya ce, "Ka gama ubana? Idan ba ka gama ba na yi shiru ka cigaba."
Baba Ibrahim ya furzar da iska mai zafi ya ce.
"Na gama."
"To shige ciki ka ba ni wuri, ashe shi ya sa ka kwaso fuska kamar akwatin zaɓe ka zo ka tsaya mini a ka. Wallahi Iro ka fara ba ni tsoro, da ace kana da iko na tabbata da sai ka yi duk yadda za ka yi domin ka turmushe mini ƙwaiƙwayen haihuwa. Amma ka don kanka, na lura baƙinciki da hassadar ne fal ranka. Allah bai hore maka irin ƙwaiƙwayen haihuwa masu yawa da albarka kamar ni ba."
Bab Ibrahim a fusace ya ce, "Wallahi gaskiya ka faɗa, yadda kake sakin jiki kai da matan da kake aura kana saki da ina da iko sai na farke ka na ƙone maka su kowa ya huta. Tun da haihuwar kawai ka sani ba ka san jidalinsu ba."
A ɗan tsorace Baba Inu ya dafe ƙirji, yana bin Baba Ibrahim da wani irin kallo ya ce.
"Kai dai Iro an yi mai mugun hali, mugun bakinka ya faɗa kanka. Sai ja je ka yi ta fama da 'ya'ya huɗu, ni kam haihuwa yanzu na fara tun da ban san mai jin ƙaina ba."
Ganin Baba Inu bai ɗauki zugar Baba Ibrahim ba ya sa Mai maganin ya zuro kai ya ce.
"Ai mai gida shi ya sa a kullum idan za mu fito, muke addu'ar neman tsari miyagu irinsu masu hana a yiwa bayin Allah ciniki." Takaici ya sa Baba Ibrahim ya shige cikin gida ba tare da ya tanka musu ba. Saboda halin yayan nasa ba ƙaramin ɓata masa rai yake ba.
Baba Iro yana shirin yin magana daga soron gidan ya ji, gijif! Kwacakwar! Alamar ana jan kaya a buhu. Baba Saleh ne ya fito da ƙaton buhun magungunansa, ganin motar mai magani a ƙofar gidan ya sa ya murtuke fuska yana harare-harare cikin habaici ya fara waƙa.
Komai baƙin cikin tsololon ƙato.
Wallahi sai dai ya yi ƙototo.
Na zama kainuwa a wannan loto.
Ƙaryar mai baƙinciki ya ga bayana, har masu ƙin sayan maganina.
Yana gama faɗar haka ya fizgo ƙaton buhunsa da yake ja da ƙyar, sai ga shi bisa tsautsayi ya fiszo da ƙafar bencin da Baba Inu yake kai. Bencin ya yi gaba shi kuma Baba Inu ya hantsila ta baya ji kake darr ya yi zaman 'yan bori a ƙasa.
Kamar bai san da shi a wurin ba Baba Saleh ya saki buhun hannunsa yana rafka salati sannan ya ce.
"Wai Yaya dama kana nan ƙofar gida? Ikon Allah sannu!"
Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin riƙo hannun Baba Inu, da sauri ya bige hannunsa rai a ɓace ya ce.
"Wallahi duk baƙincikin mutum bai isa ya ga bayana ni Inusa don uban mutum! Haka zan daɗe na yi ƙarko shekaru irin na dabino, sai na ga bayan maƙiyana. Kai mai magani, ungo dubu biyar ka yi mini haɗin komai da ruwanka."
Baba Inu bai yi niyyar sayen maganin dubu biyar ba, amma don ya ɓa ta wa Baba Saleh rai ya yi haka. Baba Saleh ya buga tsaki yana wurgawa mai maganin harara, ya nufi wata tsohuwar motarsa da yake tallan magungunansa, ya buɗe ya tura buhun maganin da ke cike da jarkokin magani sannan ya rufe.
Inna ce ta fito daga gida a fusace hannunta riƙe da Laraba, ta dubi Baba Inu bayan sun yi sallama da mai maganin ta ce.
"Inu na gaji da cin kashin da ake yi mini a cikin garin nan."
Da mamaki Baba Inu ya dube ta ya ce, "Me aka yi miki Inno?"
"Ba ni aka yi ba Laraba aka yi wa, kuma duk wanda ya yi wa Laraba ni ya yi wa. Mai gari ne yake son ganina da ita, wai Laraba ta tare Ɗahe ɗan gidan Sa'a mai ragadada ta cinye masa. Saboda Allah ina Laraba za ta kai ragadada cikin ɗan bokiti ban da son zuciya?"
Jin haka ya sa Laraba ta juya gefe a fakaice ta sake suɗe hannunta da ya yi shanana da miyar ragadada.
Baba Inu ya zuba mata ido ya ce, "Wallahi duk abin da aka ce mini wannan hatsabibiyar yarinyar ta yi ba zan musa ba, shi ya sa tun da satin nan ya kama nake jiran shigowar Uwar marayi garin nan. Wallahi babu abin da zai hana Laraba zuwa birni, ta je can ta yi aikatau ko na huta da takaicinta. Ni duk cikin 'ya'yana babu sai siffar 'ya'yan aljanu irinta."
Wani irin haushin Baba Inu ya kama Inno, sai kawai ta ja hannunta suka wuce wurin mai gari.
Tun daga nesa da aka hango Inno tafe da Laraba ƙananan maganganu suka fara tashi a fadar mai gari. Sanƙira ne ya yi magana sannan kowa ya yi shiru. Da sallama Inno ta zauna a kan tabarmar fuska a haɗe ta ce.
"Allah Ya taimake ka, na ji wai kana nemanmu ni da Laraba!"
Mai gari da tun da Laraba ta zauna yake bin ta da mugun kallo ya ce, "Wai ne ma Inno?"
Ya mayar da kallonsa wurin Laraba ya ce.
"Ke Laraba waye wannan?"
Laraba ta yi kicin-kicin da fuska tana duban Ɗahe kamar ba ta gane shi ba ta ce, "Ban san shi ba, amma na ga yana yi mini kama da 'ya'yan Baraka mai hancin salansa."
Haushi ya sake cika Mai gari ganin irin rainin hankalin da Laraba ta yi masa. Ya sake nuna Huwaila wacce ta kai ƙarar Laraba, a kan ta jefa mata bokiti da guga a cikin rijiya. Laraba ta sake ƙanƙance ido ta ce.
"Wannan kam Lado ƙeya ne!"
Sai kuma Laraba ta washe baki ta ce, "Lado ƙeya dama ka dawo daga Legas?"
Haushi ne ya lulluɓe mai gari, mutanen wurin wasu suka fara dariya yayin da wasu kuma haushin Laraba ya cika su, don kusan duka mutanen garin babu wanda ba shi da tabon ɓacin ranta.
Tsam mai gari ya taso ya zo gaban Laraba, a tunaninta tambayarta zai yi sai ji ta yi ya zabga mata gigitaccan mari, har sai da ta ga waɗansu taurari sun gilma mata. A razane Laraba ta dafe kunci saboda marin ba ƙaramin zafi ya yi mata, amma sai ta basar don ba ta san ta kunyata kanta a gaban mutanen garin. Ta sake basarwa ta sake ba shi irin amsar da ta ba shi da farko. A wannan karon ma haushi ya sa Mai gari ya sake ɗauke fuskarta da mari, abinka da farar fata lokaci ɗaya fuskarta ta yi jajir. Ganin haka ya sa ran Inno ya ɓaci ta dube shi a fusace ta ce.
"Wallahi Sama'ila ka kiyaye ni, jikata fa ba jaka ba ce..."
"Ai dama duk wani iskanci da yarinyar nan take yi ke ce kike ɗaure mata, wallahi mai gari sisina ba zai yi ciwon kai ba sai an biya ni ragadadata. Har kayan miya da mahaɗi kusan dubu biyar na kashe."
Sa'a mai ragadada ta faɗa a ƙufule.
Cikin tsoratarwa da burgagi Mai magari ya miƙe tsaye yana buɗa kafaɗu ya ce, "Inno tun da haka kika ce, bari na aika ku birni wurin hukuma ta yanke mata hukunci. Kin ga idan aiƙali ya ji irin tuhume-tuhumen da ake yi mata ƙila ma ya aikata gidan yari."
Jin haka ya kaɗa hantar cikin Inno, hankali a tashe ta zungoro Laraba ta ce.
"Ke Laraba ki yi magana."
Laraba ta yi wa Mai gari ƙuri tana yi masa kallon ba ka daki banza ba, har sai da cikinsa ya kaɗa amma sai ya basar ya ce.
"Laraba kin tare Ɗahe kin cinye masa ragadada kin tula masa ƙasa a ciki, ita kuma Huwaila kin jefa mata guga da bokita a rijiya yanzu da kin jefa ta ciki me za ki ce?"
Laraba ta wurga wa Huwaila harara ta ce, "Kai Lado ƙeya tun da ka dawo garin nan yaushe muka haɗu da kai!"
Huwaila ta fashe da kuka cike da takaici ta ce, "Mai gari kana ji tana mayar da ni Lado, yanzu Laraba ta rasa da wa za ta haɗa ni sai Lado ƙeya?"
Mai gari ya kalli Sanƙira yace ya tsinko masa itacen dalbejiya ya zuge masa ganyenta. Jikin Sanƙira har rawa yake ya haye bishiyar da ke gefensu, ya fisgo manyan reshe ya zuge ya miƙa wa mai gari. Kafiya da taurin kan Laraba ya sa ko gezau ba ta yi ba, duk da gabanta sai faɗuwa yake yi.
Rai a ɓace Mai gari ya shiga rafta mata ta ko ina, mutanen wurin suka marmatsa don kar a same su. Tun Laraba tana daurewa har dauriyarta ta ƙare ta fashe da kuka tana mutsu-mutsu. Inno ban da kuka da kururwar neman taimako babu abin da take yi.
Yaran da suke zagaye da su ne suka fara tafi suna tsalle da waƙa, saboda tun da suke ba su taɓa ganin abin da ya saka Laraba kuka ba.
Laraba mai kuka ye ye.
Ga majina da yawu ahayye.
Gobe ma ta ƙara ye ye.
Ku zo mu yi mata ɓarɓaɗan tusa a tsakar ka.
Idan suka kai baitin waƙar sai su ƙarasa su dunguro kan Laraba da ke shasshekar kuka.
Mai gari sai da ya gaji don kansa sannan ya koma kujerarsa cike da son nuna birgewa ya ce.
"Duk wanda ya sake aikata makamancin abin da Laraba ta yi, hukuncin da za mu yi masa kenan. Ina Inno take?"
Cike da jin haushi a daƙile Inno ta ce, "Ga ni."
"Za ki biya Huwaila da Sa'a kuɗin ɓarnar da Laraba ta yi musu." Inno ta yi tsagal ta ce.
"Ai kuwa ba za ta saɓu ba, ya za a yi a daki yarinya sannan kuma na biya."
Mai gari zai yi magana suka ga Laraba ta miƙe zumbur! Kamar wacce aka yi wa allurar doki. Don irin zaburar da ta yi ba ƙaramin tsoro ta ba shi ba, ba shi kaɗai ba, hatta ragowar mutanen wurin sai da suka ja da baya.
Idanunta sun yi jawur saboda kuka, ta dube su ɗaya bayan ɗaya abinka da mai manyan idanu sai suka sake fito. Ta fara takawa a hankali wurin saitin fuskokinsu, ta cigaba da kallonsu ɗaya bayan ɗaya kamar wacce take haddace kamanni da sunayensu. Da ta je kan mai gari sai ta matsa dab da shi ta gwalalo masa ido waje har sai da ta ja baya, sannan ta cigaba da kallon mutanen gefensa Tana zuwa ƙarshe, sai kawai suka ga ta ɗiba a guje ta fice daga cikin fili ta nausa daji, hankali a tashe Inno ta rufa mata baya tana faɗin.
"Laraba! Ke Laraba ina za ki je?"
Tun ba a je ko ina ba Laraba ta yi wa Inno nisa, ganin Inno za ta tafi ya sa Mai gari ya ce.
"Inno wai ni za ku yi wa dirama? Ke da Laraba wa ya ba ku ikon tashi daga wurin nan. Wallahi ba don ina duba darajar marigayi Baffa babba ba, da ke da jikarki tuni na kore ku daga garin nan."
Mai gari yana rufe baki, suka hango Laraba ta tunkaro wurinsu a guje, hannuwanta ɗauke da wasu tafka-tafkan reshen bishiya. Ba ta yi wata-wata ba ta shiga tafka musu kan mai uwa da wabi a haukace tana wani irin ƙaraji. Lokaci ɗaya wurin ya hautsine, Mai gari saboda tashin hankali da rarrafe ya dinga tafiya, domin da farko da ya saka gudu sai da ya yi adungure sau uku babbar rigarsa tana taɗe shi.
07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[04/12/2024, 15:03] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
SHAFI NA BIYU
Kamar wata fusatacciyar zakanya, haka Laraba ta cigaba da yin kan mutane tana fatka musu itacen da yake hannunta. Ban da wani irin gurnani babu abin da take yi, Inno da ke raɓe a can gefe jikinta ya shiga karkarwa saboda tsoro da tashin hankali. Don tun da take da Laraba ba ta taɓa ganin ta yi irin haka ba, Sanƙira ta hango maƙale a gefen bishiya. Ta yi wani irin zullo haɗe da ƙaraji ta tunkari wurinsa, kamar sabon marayan da ba shi da mafita. Haka Sanƙiran ya saki wani marayan kuka zai fita da gudu, Laraba ta tuna yadda Sanƙira ya dinga zuge ganyen bishiyar yana wurga mata harara sai kawai ya ɗaga hannu ta tafka masa itace a baya. Sanƙira ya gantsare cikin azaba ya ce, "Wayyo Mai gari bayana wash! Wallahi wannan ba dukan bil'adama ba ne."
Mai gari da babbar riga ta sarkafe shi yana rarrafe yana dungurawa ya ce, "Wallahi na ajiya sarautar na damƙa maka yanzu kai ne mai garin."
Laraba ta saki murmushin ƙeta ta riƙo babbar rigar Sanƙira ta baya, suna gudu tana tafka masa ice a baya. Ganin Larabar tana neman kai shi ƙasa, ya sa Sanƙira ya yi wani ƙaraji ya dara gaban rigarsa gida biyu, da yake dama rigar ta kwana biyu nan take ta rabe biyu. Sanƙira ya zuba a guje ya bar Laraba da babbar riga a hannu, filin wurin ya sake cakamewa da ƙurar ƙasar da take tashi. Mai gari ya hango Laraba tana tunkaro shi, cikin tashin hankali ya zuba kabbara kamar wanda yake filin jihadi. A wannan karon Allah Ya ba shi sa'a ya samu da ya miƙe bai sake faɗuwa ba, gudun kada babbar za ta sake ba shi matsala ya sa ya tuɓe ta ya wurgar. Ya taƙarƙare ya fita da gudu, takalmansa da hularsa sai tsalle suke yi suna tashi sama. Laraba ta so ƙyale shi amma da ta tuna irin marin da ya zazzabga mata sai ita ma ta rufa masa baya da gudu.
A lokacin da Mai gari ya ƙarasa gida, Salame matarsa ta rako Inna mahaifiyarta da ta zo duba ta sakamakon rashin lafiyar da ta yi. Suna nan a soro ya shiga a guje, cikin neman maɓoya ya fisgi hijabin jikin Inna ya yi gaba da ita. Cikin tashin hankali Inna ta fara ihu tana kiciniyar ƙwace kanta, don Mai gari janta yake da gudu ga kanta ya cukwikwiye mata a cikin hijabi.
Ragowar mutanen gidan suna jin ihu daga waje, da suka ga a yadda mai gidansu ya shiga yara da manya sai kowa ya nemi maɓoya. Laraba ce ta yi tsaye tana wani gurnani, ta ga tsakar gidan kowa ya fashe sai wani ɗan ƙaramin yaro da bai fi shekara biyu da rabi zaune a kan fo. Irin kallon da Laraba take yi masa tana gwalo ido, ga zungureren itacen da ya gani ya sa yaron ya miƙe a zabure yana ihu ya shige ɗakin mahaifiyarta.
Tun da Mai gari ya fisgi hijabin Inna, ba shi ya tsaya a ko ina ba sai a uwar ɗakin Salame a can ƙarƙashim gadon ƙarfenta. Ya shiga sauke numfashi da ƙyar yana muzurai, hannunsa ya kai wurin wandonsa ya ji ya yi sharkaf. Jiki yana karkarwa ya zura kansa cikin hijabin Inna ya ce.
"Salame ina jin fa gudawa na yi, wallahi har yanzu ji nake abu yana tsiyaya a jikina kamar an kunna fanfo."
Inna da kunya, haushi da baƙincikin Mai gari suka cika ta murya a dakushe ta ce.
"Ai kana da hannu ko?Sai ka yi ƙoƙari ka kashe fanfon."
A razane Mai gari ya ɗago, sai a lokacin idanunsa suka sauka a kan fuskar sirikarsa. Ya fito daga ƙarƙashin gadon a guje, yana zuro kai ya ga Laraba ta ƙwalla wata irin ƙara ta yanke jiki ta faɗi. Daga Mai gari har ragowar mutanen garin da suke leƙowa tsaye suka yi suna kallonta, aka rasa wanda zai tunkare ta ballantana ya yi yunƙurin tashinta. Laraba ta ɗan jima a haka sai kuma ta fara buɗe idonta a hankali tana salati, tashi ta yi zaune tana kalle-kalle kamar mai neman wani abu ta ce, "Kai, waye ya kawo ni nan?"
Shiru gabaɗaya suka yi mata, ta tunkari wurin mai gari a ɗan razane ta ce.
"Mai gari me nake yi a nan?"
Baki yana rawa Mai gari ya ce, "Ni ma tambayar da nake son yi miki kenan, amma yanzu ki fara zuwa gida tukunna."
Laraba ta saki murmushi a fakaici ganin yadda duk ya birkice, sannan ta fito ta nufi hanyar gida. Kamar sun ga sabuwar hallita haka mutane suka dinga bin Laraba da kallo, ita kuwa ta maze tana tafe tana hura hanci tana buɗa kafaɗa har ta je gida.
Baba Inu yana shiga gida kai tsaye ɓangarensa ya nufa, tun daga bakin ƙofa ya tsaya ya yi gyaran murya yana haɗe fuska, lokaci ɗaya yaran suka fara shiga taitayinsu. Iyayensu kuma suka shiga tsawatarwa 'yan ƙananun da ba su yi wayo ba.
Larai ce da girki ranar, a tsakiyar gida ta ajiye tukunyar abincin rana sai ƙanana da manyan kwanuka birjik a gabanta. Waɗansu ƙananan yara ne kusan su huɗu waɗanda ba su wuce shekara ɗaya zuwa da rabi ba, biyunsu riƙe suke da kwanuka suna kukan yunwa suna kama zanin Larai.
"Gaskiya Indo ba kwa kyauta mini, da wanne zan ji? Da aikin abinci ko da waɗannan yaran. Ke Kulu zo ki janye mini su don ubanki!" Ta ƙarasa maganar a fusace ta fisge kwanukan hannun yaran.
Baba Inu ne ya ƙarewa tukunyar kallo, ya matsa gabanta a kausashe ya ce.
"Ke Larai satar mini abinci kika yi? Kika ƙara a kan wanda na ɗebar muku, da na ga kin rafka wannan rafkekiyar tukunyar?"
Jiki yana rawa Larai ta buɗe tukunyar ta ce.
"Mai gida tukunyar girkin ce ta ɓule shi ya sa na ɗora wannan." Leƙa tukunyar ya yi ya hango abinci a can ƙasan tukunyar sannan ya sauke ajiyar zuciya ya wuce ɗakinsa.
Mukulli ya saka ya buɗe, ya ɗauko wata 'yar madaidaiciyar tukunya ya miƙa mata yana daga tsaye ya ce.
"Maza ɗumama mini miyar nan." Da sauri Larai ta karɓa ta ɗora a kan murhun, Baba Inu ya koma kan benci ya kasa ya tsare yana ganin yadda take rabon abinci. Kowanne kwano idan ta ɗauko bai fi ta yafita ludayi ɗaya da rabi ba, saboda idan da sabo sun saba a kullum abincin ba isarsu yake yi ba.
"Mai gida a zuba maka kana marmarinsa?"
Larai ta tambaya tana gyara goyon Fure da ke bayanta.
"A'a ku ci kawai!"
Baba Inu ya furta a daƙile. Larai ta ɗebi ragowar wanda ta rage masa cikin murna ta shiga ƙara wa kwanonta.
"Ke Larai wallahi son zuciyarki yawa gare shi, ba za ta saɓu ba wallahi sai kin ƙara wa kowa." Hansatu ta yi caraf ta yi maganar ganin abin da Larai take yi. Babu yadda ta iya ganin Baba Inu yana wurin ya sa ta shiga ƙarawa kowanne kwano bai fi cokali ɗaiɗai ba. Bayan ta gama ta ce kowa ya ɗauka, a guje yara da 'yan matasan cikinsu suka ɗauka da sauri, wasu tun a tsaye suka fara zuba loma duk da abincin yana ƙona su.
Ƙamshin ɗumamen miyar ne ya fara dukan hancinsu, Larai ta sauke har za ta kai masa ɗaki Baba Inu ya ce ta kawo gaban bencinsa ta ajiye. Abu da ke da tsohon ciki wani irin ƙwaɗayi ya taso mata. Kwanon abincinta ta ɗauka ya ƙarasa wurinsa cikin marairaicewa ta ce.
"Don Allah mai gida ko man miyar ne, ka taimaka ka yafa mini na ci ko na samu sauƙin abin da nake ji. Wallahi ƙwaɗayi ne ya addabe ni."
Wani banzan kallo Baba Inu ya yi mata ya ce. "Cewa aka yi idan ba ci ba za ki mutu?"
Abu ta yi saurin girgiza masa kai, Baba Inu ya sake haɗe fuska ya ce.
"To yanzu baƙincikin wanda zan ci kike yi? Idan kuma ba na cin mai maiƙon, ta ya ya zan iya samun ƙwarin jikin nemo muku abincin da kuke ci." Abu ta haɗiyi yawu tana kallon farantin da Baba Inu ya zuba miyar da ƙirjin kaza,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 35