Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya kai kunnsa. Sai da ya ji ta ɗauka sannan ya ce. "Aunty Nana da fatan ban katse miki bacci ba." Daga can ɓangaren Aunty Nana ta ce. "Ban kwanta ba Hafiz, an wuni lafiya ya iyali?" "AlhamduLillah, ya su Usaina?" "Duk lafiyarsu ƙalau, ina Amina da jiki?" Aunty Nana ta tambaya, sai da Hafiz ya amsa mata sannan ya ce. "Don girman Allah wata tambaya gare ni Aunty Nana." Jiki a sanyaye ta ce. "Wani abu ne ya faru Hafiz?" Hafiz ya ce, "Ba wani abu ba ne kawai tambaya ce da ni Aunty Nana." "Ina jinka Hafiza." Ta ba shi amsa. "Don Allah na taɓa zuwa na ba ki kuɗi, na ce ki yi wa Amina farfesun naman kai?" Hafiz ya furta yana kallon Amina. Ajiyar zuciyar Aunty Nana ya yi sannan ta ce. "Gaskiya ba ka taɓa ba, kwanaki dai Amina ta turo mini kuɗi ta ce a yi mata farfesu a kai mata..." Aunty Nana ta kwashe duk yadda suka yi ta faɗa masa. Godiya ya yi mata sannan ya katse wayar. Fuska a haɗe ya dube su ɗaya bayan ɗaya, ya nuna su da yatsa a haukace ya ce. "Wallahi duk wacce ta sake yi mini irin wannan makircin daga ranar zamana da ita ya ƙare, so kuka ku mayar da ni mahaukaci? Kun mayar da ni wani ɗan iska da za ku dinga raina mini hankali?" Ya furta a tsawace har sai da kowacce ta shiga taitayinta, don ba su taɓa ganin ya haukace musu haka ba. Ya miƙe tsaye jikinsa har rawa yake yi ya ce. "Duk faɗi-tashi da wahalar neman da nake yi ba a kanku nake yi ba? Amma za ku dinga caza mini kai, so kuke ku kashe ni da damuwa ku huta ko? Wallahi kun ji na rantse duk wacce na kuma samun ta yi irin wannan makircin sai ranta ya yi bala'in ɓaci. Makiran banza da wofi, an gaya muku yanzu ana irin wannam haukan kishin ne? Me kuka nema kuka rasa a wurina da za ku dinga raina mini hankali? Dama na yi wannan wayar ne domin na ƙure kowacce a cikinku, idan kun ga dama kada ku fasa. Na rantse da Allah daidaita nake da ku, sakarkarin banza da wofi." Hafiz yana gama maganar ya fice daga ɗakin rai a ɓace, daga Amina har Bilkisu kowacce shiru ta yi suka kasa magana. Jiki a sanyaye Amina ta miƙe ta koma ɗaki, tana zuwa ta ga kiran Aunty Nana ya shigo wayarta, sai da ta ɗauka sannan ta ji ta ce. "Amina lafiya mijinki ya kira ni yanzu yake tambayata? Kin san fa tun wancan lokacin na ce kada ki aikata abin da kika yi, wannan ba hanya ce mai ɓillewa ba kika dinga yi mini magiya." Cikin kuka Amina ta ce. "Wallahi Aunty ba halina ba ne, yau da gobe ta sa na ce bari na fara gwada abin da Maman Sayyid take yi. Amma In Shaa Allahu ba zan ƙara ba. Wallahi yau ba ki ga baƙaƙen maganganun da Hafiz ya faɗa mana ba." A ƙufule Aunty Nana ta ce, "Da kuka samu bai zazzage ku ba, wai me ya faru." Nan take Amina ta kwashe komai ta faɗa mata, cikin takaici ta ce. "Wa ya gaya miki idan kare yana haushi ana tanka masa? Ai Amina tun da kika gane halin kishiyarki sai ki ci maganin zama da ita. Ina hankali da tunani tare da tarbiyyar da kika samu? Wallahi da ace tana yi kina share ta yau da gobe dole ta gaji ta watsar, wallahi ki shiga hankalinki. Idan kila bari su Baba suka ji labarin makamancin abin da kika yi kin san sauran." Aunty Nana ta jima ta yi mata faɗa sannan suka yi sallama. Amina tana nan zaune tana jiran Hafiz ya shigo ta ba shi haƙuri, har bacci ya yi awon gaba da ita. Koda ta farka cikin dare ba ta gan shi ba, hankali a tashe ta ɗauko waya ta latsa lambarsa. Sai da ya ɗauka a ɗan rikice ta ce. "Habibi kana ina?" "Ina ruwanki da inda na je?" Ya bata amsa a takaice. "Don Allah kana ina?" "Ina ɗakin yara." Yana ba ta amsa ya katse wayar, hijabi ta saka ta fito ta shiga ɗakin su Sayyid. A can gefen yara ta hango shi a zaune ya rafka tagumi, cikin kwantar da murya ta ce. "Don Allah ka zo mu tafi ɗaki." Kamar ba zai tanka mata ba, sai kuma ya ɗago ya ce. "Kada ki wahalar da kanki Amina, ki bar ni a nan har sai na huce don kaina zan dawo. Idan kuma kika takura mini, wallahi idan na fice daga gidan nan ba za ku sake ganina ba." Duk yadda Amina ta kaɗa ta raya da Hafiz fir ya ƙi amincewa, haka ta haƙura ta koma ɗaki. Tun daga wannan ranar Hafiz ya koma ɗakin su Sayyid da kwana, a haka sai da ya shafe sati uku ba tare da ya koma ɗakin kowacce a cikinsu ba. Sai dai kowacce idan ranar girkinta ta zagayo, ta yi girki ta ajiye masa ya ci ya fita. Tun suna ganin abin Hafiz kamar wasa, har Amina ta samu Bilkisu ta ce su je su same shi su ba shi haƙuri. A lokacin Bilkisu taɓe baki ta yi ta ce. "Wallahi bai kai wannan matsayin ba, ke da za ki iya ba shi haƙuri kina iya zuwa don ni ba zan juri wulaƙanci ba. Duk haƙurin da muka ba shi a ranar da abin ya faru bai haƙura ba, tun da ba haifata ya yi ba ai sai dai mu dawwama a haka. Ba fa mu kaɗai muke da buƙata ba, shi ma ai taimakon kansa ne. Uwa-uba ma mace ai da jan aji aka santa, amma idan za ki je ga hanya nan." Ajiyar zuciya Amina ta yi ta ce. "To shi kenan, ai wai da gani na yi kamar ya dace mu je mu ba shi hauƙurin, amma bari mu gani a kwana biyu." Murmushin ƙeta Bilkisu ta yi a ranta, musamman da ta tuna ranar ita ce da girki. Daddare tun bayan Isha'i Bilkisu ta sheƙa wanka, ta yi gayunta cikin doguwar rigar atamfa. Ɗinkin ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, tun da Hafiz ya zauna cin abinci ta lura da satar kallonta da yake yi. Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, sai da ta tabbatar da Amina ta yi bacci kusan sha ɗayan dare sannan ta sauya kayanta cikin wata figigiyar rigar bacci. Ɗakin su Sayyid ta shiga, ta hango Hafiz kwance a kan carpet yana kwance da kayan shan iska. A gefensa ta kwanta, cikin kissa mai jan hankali ta shige jikinsa. Ta kai bakinta saitin kunnensa ta ce. "Don Allah ka yafe mini Habibi, sonka zai kashe ni idan ka cigaba da azabtar da zuciyata. Ni kaɗai na san irin kewar da na yi duk tsawon waɗannan kwanakin." Ta ƙarasa maganar tana hura masa iska a kunne. Sannu a hankali yake jin saƙonta yana ratsa gaɓɓan jikinsa, don shi kansa ya san ba ƙaramin kewar matansa ya yi ba. Janye jikinsa ya shiga yi, don ba ya son nuna mata shi ma yana buƙace da su. Da sauri ta sake shigewa jikinsa cikin kukan kissa ta ce. "Ko za ka hukunta ni don Allah kada ka azabtar da ni ta wannan sigar, na saba da jikinka ba na son kana yin nesa da ni." Salonta ba ƙaramin rikita shi ya yi ba, a hankali ta fara yawo da hannunta a jikinsa. Tun yana jurewa har ya shiga mayar mata da martani, bakinta ta sake kai wa kunnensa ta ce. "Mu je ɗaki saboda yara." Bai musa mata ba, ya saƙalo ta suka wuce ɗaki sannan suka cigaba da farantawa juna rai. Bilkisu ta yi mamakin irin zafafan salon da Hafiz ya dinga yi mata, a nan ta fahimci ba ƙaramin kewarsu ya yi ba. Cikin dare suka wuce banɗaki suna riƙe da juna suka tsarkake jikinsu, a maƙale da juna suka koma bacci. Wurin gabannin asuba ta ji Hafiz ya sake kai hannunsa jikinta, cikin so da ƙauna suka sake farantawa junansu. A wannan karon ma tare suka shiga wanka, suna cikin banɗaki Amina ta fito za ta yi alwalar sallar asuba. Jin ana wanka ya sa ta dakata, don har cikin zuciyarta ba ta kawo komai ba. Tana nan tsaye Hafiz da Bilkisu suka fito suna riƙe da juna, Hafiz ya maƙale Bilkisu kamar wani zai ƙwace masa ita suka wuce ɗakin Bilkisu. Mun kusa kammala book 1 fa💃🏻 don haka masu son karanta book 2 su fara aiko da kuɗinsu, duk da masu himma tuni sun fara biya.💃🏻 Book 2 dai 500 ne idan ya zama document 800, za turo ta Acc. Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam🌚 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA SHA UKU Har suka shige ɗaki Amina ba ta daina bin su da kallon mamaki ba, jiki a sanyaye ta shige banɗaki tana sake jinjina girman makirci irin na Bilkisu. A haka ta ɗaura alwala, ta wuce ɗaki ta gabatar da sallar asuba. Lokacin da ta idar da sallah ta jima a zauna tana saƙa da warwara, don gabaɗaya kanta ya cushe. Sannan ba ta son ta yi abin da Bilkisu za ta ce ta kwaikwaye ta, tana nan zaune sai kawai ta dafe ciki da baya ta ƙwalla ƙara tana faɗin. "Wayyo Allah cikina." Hafiz yana daga ɗakin Bilkisu, da dawowarsa daga masallaci babu jimawa ya ƙaraso da sauri yana faɗin. "Amina! Lafiya, ko jikin ne?" "Wash cikina, wallahi ji nake kamar zan mutu." Ta furta tana satar kallonsa ta gefen ido, a hargitse ya sake tallafo ta ya ce. "Mutuwa Amina? Don Allah ba na so, ba na son ki dinga furta kalmar mutuwa hankalina tashi yake yi." Amina ta ja numfashi ta fesar tana yarfe hannu ta ce. "Wash! Hasbunallahu wa ni'imalwakil." A daidai lokacin Bilkisu ta ƙaraso ɗakin a yatsine ta ce. "Wai wanne irin ciwo ne da za a ce bai tashi ba sai yanzu da asuba." Ta yi maganar, saboda ta fahimci Amina ƙarya take yi. Don ta tabbata ganinsu tare da Hafiz ne ya sa ta yi yunƙurin yin ciwon ƙarya. A fusace Hafiz ya ɗago ya ce. "Haba Bilkisu, kina da imani kuwa? Ba ki ga halin da yarinyar nan take ciki ba?" Amina tana jin haka ta karyar da kai gefe ta ce, "Don Allah ka kai ni asibiti, ji nake ɗan cikina kamar zai birtso waje." A hargitse Hafiz ya ce, "Bari na yi wa maƙocina Habu magana, sai ya kai mu a adaidaita sahunsa." Yana gama maganar ya fice da sauri. Bilkisu ce ta riƙe ƙugu cikin tijara ta ce, "To munafuka algunguma, wallahi tun wuri gara ki ware. Don na san makircinki ne da munafurci ya sa kika yi ƙaryar ciwo." Amina ta dube ta tun daga sama har ƙasa sheƙeƙe, sannan ta miƙe tsaya ta yi taki biyu ta ce. "Ashe makiran suna da yawa, wai Bilkisu yaushe za ki sauya hali ne? Wallahi-wallahi zuciya ɗaya nake tare da ke, amma ƙarfi da yaji kin koya mini makirci da munafurci. Ƙiri-ƙiri na ce mu je mu ba wa Habibi haƙuri kika ce mini ba haka ba, ashe ni kika mayar 'yar iska. Tun da dai duk nasihar da ya yi mana ba za ki ɗauke ta ba, ni da ke mu zuba mu gani." "Ni kike cewa Bilkisu kai tsaye?" Bilkisu ta furta a ƙufule, Amina ta watsa mata harara ta ce. "Haifata kika yi da ba zan faɗi sunanki ba? Tun asali ina ba ki girma shi ya sa nake sakaya sunanki, amma tun da na lura ba zaman lafiyarmu kike so ba. Wallahi zan tafiyar da ke a yadda kika zo mini." Rai a ɓace Bikisu ta ce. "Sannu macijiya da ba ta ramin kanta, aikin kenan. Sai kun yi kwantai a gidajen iyayenku ku dinga aure mazajen wasu, ai wallahi na rantse da Allah sai kin yi nadamar auren mijina da kika yi. Saboda Hafiz nawa ne ni kaɗai, ƙaddarar da ta saka kika aure shi ita za ta sa na gasa miki aya a hannu." "Ai kuwa ni da ke sai dai mu gasawa juna, kuma dama can Hafiz ba mijinki ba ne ke kaɗai. Saboda Allah Ya ƙaddara masa auren mata har huɗu, ke ko yau zai kawo biyu ba zan ɗaga hankalina ba saboda na san kowacce mace da ƙaddararta. Kuma ki bar cika baki, saboda kema kina da 'ya'ya mata, idan Allah Ya ƙaddara musu auren masu mata za mu ga yadda za ki yi." Amina ta furta a fusace, Bilkisu ta yi saurin shan gabanta ta ce. "Mugun bakinki ya faɗa kanki, kin ɗauka yadda kika yi kwantai ta ƙare miki kika kasa samun mijinki sai na wata. Kin yi zaton kowa haka yake? Ai indai auren mijin wata ne baƙinciki da ƙuncin gidan miji yanzu kika fara gani." "Yanzu muka fara gani dai ni da ke, don babu abin da kika fi ni da shi wallahi. Duk tunƙahonki matsayinmu ɗaya, ke matarsa ce ni ma haka." Amina tun ba ta rufe bakiba Bilkisu ta ce. "Ƙarya kike wallahi, matsayina da na ki har abada ba zai zama ɗaya ba. Domin ni ce matarsa ta farko, ni na ɓare abina sabo kar a leda. Mahaifinsa da mahaifina aminaine, na san duk rintsi babu rabuwar aure tsakanina da shi. Ke kuwa gayyar tsiya arna a Idi, haka aka yayimo ki daga duniya aka kawo mana annoba gida. Ko yanzu zai iya rabuwa da ke, kuma ya zauna lafiya. Don ni da kika gani, na zama ƙadangaren bakin tulu ban fito ba sai da na shirya, na zama ƙasar saman kabari duk taƙamar mamaci sai na raɓe shi. Na zama kujerar zaman gida, ko an ƙi ko an so dole a zauna da ni." Bilkisu tana rufe baki Amina ta saki dariyar rainin hankali sannan ta ce, "Ai duk na banza ne, tun da kika kasa riƙe shi har ya fita waje ya nemo ni domin ya samu kwanciyar hankali. Da kin isa da isarki ai da kin dakatar da shi daga aurena, ba ki san sakaci na rashin gamsarwa da kulawarki ne ya sa shi auro ni..." A zuciye Bilkisu ta kai wa Amina mari, a daidai lokacin Hafiz ya kawo kai ganin haka ya sa shi shiga ɗakin da sauri ya ce. "Ke Bilkisu ba ki da hankali ne? Mace da ciki a jikinta kike marinta." "Na mara ɗin, ko za ka rama mata? Ni ka san irin magamganun da ta furta mini..." Tas! Ita ma Hafiz ya ɗauke fuskarta da mari. Amina da ke kwance a ƙasa ta saci kallon Bilkisu ta sakar mata gwalo, sai kawai ta fashe da kuka ta ce. "Wayyo Allah cikina za ta kashe ni." A hargitse Hafiz ya ɗago ta ya ce, "Sannu Amina, za ki iya tashi mu tafi ko na ɗauke ki." Kamar tana jira ta ce. "Jiri nake ji ba zan iya tashi ba, ga shi dukan da ta yi mini cikina ciwo yake mini." Hafiz ne ya ɗauki Amina cak zai fita cikin sauri Bilkisu ta tare ƙofar ta ce. "Wallahi babu inda za ka kai munafukar nan, kuma wallahi tun da ka mare ni sai na nuna muku ɗanyan kai." "Ki matsa na wuce Bilkisu kada ki ɓata mini rai." "Ba zan matsa ba." Bilkisu ta ba shi amsa kai tsaye, rai a ɓace ya sake cewa. "Ki matsa na wuce Bilkisu, wallahi idan kika bari raina ya ɓaci ba za ki ji da daɗi ba." "Wallahi sai dai ka yi duk abin da za ka yi amma ba za ku fita ba, saboda yau ranar girkina ce babu karuwancin da za ta nuna mini..." Bilkisu ba ta rife baki ba Hafiz ya hankaɗe ta ya wuce, daga can baya ta faɗi ƙasa warwasa don ba ƙaramij buguwa ta yi ba. Hafiz ya wuce da Amina ƙofar gida ya saka ta a Adaidaita sahu, sai da ya koma ya ɗauko katin asibitinta ya rufe ƙofar ɗakinta sannan ya fita suka wuce asibiti. Bilkisu ta jima a wurin tana kuka, sai da ƙyar ta yunƙura ta shiga ɗaki. Ta sauya kayan jikinta, sannan ta shirya yaranta ta tasa ƙeyarsu gidansu Hafiz. ALHAJI UMAR Da mamaki Daddy ya dubi Baba malam ya ce. "Yaya ina da Karima bayan wacce ka sani?" Fuska a tamke babu alamun wasa Baba Malam ya ce. "A da dai na sanka da Karima, amma a yanzu Karimar da na sani ba ka da hurimi da ita." "Don Allah Yaya idan wasa kake yi mini ka daina, wallahi tallahi hankalina a tashe yake. Ina son na ganta, saboda mummunan mafarkin da na yi a kansu." Daddy ya furta a hargitse. Kallon da Baba malam ya yi masa ne ya sa shi shiga hankalinsa. Ya nuna shi da yatsa ya ce. "Ni na yi kala da sa'anka ko wanda zai zauna yin wasa da kai? Kai Umaru! Kada ka raina mini hankali, Karima ba matarka ba ce. Ka koma can gidanka ka cigaba da zama da matarka, a yanzu haka tana gab da ɗaura aure. Idan kuma 'ya'yanka za ka karɓa, a yanzu zan shiga na taso maka su ka tasa ƙeyarsu a gaba ka tafi da su." Kafin Baba Malam ya gama magana tuni gumi ya wanke fuskar Daddy, hankali a tashe ya zube a gabansa ya ce. "Don girman Allah kada ka yi mini haka Yaya, wallahi ni ban saki Karima ba. Yaya ka yi mini rai, wallahi ji nake ba zan iya rayuwa idan babu ita ba." "Idan ka mutu kwananka ne ya ƙare Umaru, kada ka manta; a yanzu ba ni da uwa ba ni da uba. Don haka babu numfashin wani da zan rasa a yanzu, har ya ɗaga mini hankali. Ruwanka ne ka cigaba da rayuwa, ruwanka ne kuma ka zaɓi mutuwa. Amma ina me tabbatar maka, idan ka sake zuwa da maganar Karima gidan nan wallahi zan ba wa securities umarnin kada su bari ka sake shigowa." Baba malam yana gama magana ya shige ciki, da sauri Daddy ya bi bayansa sai dai kafin ya ƙarasa ya datse ƙofar. Daɓar! Daddy ya zauna a wurin yana jin duniyar gabaɗaya ta yi masa zafi. A nan barandar da Daddy ya zauna, yana nan zaune har aka kira sallar asuba, Daddy yana nan zaune Baba Malam ya fito zai tafi masallaci. A sanyaye Daddy ya ɗaura alwala ya bi shi suka wuce masallaci, sai dai kallon fuskar Baba malam da ya yi ya ji fargaba ta sake mamaye shi. A haka suka yi sallah suka dawo cikin gida, Baba malam yana gab da shiga cikin gida Daddy ya ce. "Don Allah yaya, don zatin Ubangiji ka..." "Umaru ba na son damuwa don Allah, yanzu haka kaina ciwo yake tun tashin da ka yi mini ina bacci. Ka je wurin matarka idan na yi nazari zan neme ka." Daga haka Baba malam ya wuce ya bar shi a tsaye. Kamar zai ɗora hannu a ka, haka Daddy ya wuce ya shiga mota ta nufi gida zuciyarsa a dagule. Lokacin da ya je gida gari har ya yi haske, a lokacin da ya shiga Shukura tana zaune a takure cikin damuwa. Tana ganinsa ta miƙe zumbur kamar marar gaskiya ta ce. "Baby ina fatan ka dawo lafiya?" "Eh." Kawai ya furta a taƙaice ya wuce ɗakinsa. Da sauri Shukura ta bi bayansa har ta shiga rai a ɓace ya ce. "Get out please, ba na buƙatar hayaniya." "Wai me kake nufi ne Alhaji? Ya za a yi a kan tsohuwar matarka ka dinga wulaƙanta ni. Wallahi ba zan ɗauka ba, idan ba za ka iya ba ka sallame ni sai ka dawo da ita." Shukura ta yi maganar cikin tsiwa, saboda sabon da ta yi. A fusace Daddy ya ɗago ya ce. "Idan haka kika zaɓa ki wuce gidanku, amma ki sani idan har bakinki ya sake furta magana marar daɗi a kan matata wallahi a bakin aurenki." A razane Shukura ta dube shi, jiki yana rawa ta ja ƙafa ta koma ɗaki. Sai da ta saka sakata sannan ta faɗa kan gado ta fashe da kuka, a hankali ta janyo wayarta ta latsa lambar mahaifiyarta. Tana jin ta ɗauka cikin kuka ta ce. "Inna don Allah ki yi wani abu, wallahi da matsala." Daga can ɓangaren Inna ta ce. "Tun tasowa ta ban taɓa cin karo da matsala ba, don haka a yanzu ma ba zan ganta ba. Tun bayan sallar asuba na fito zuwa wurin malam, yanzu haka zan haɗa ki da shi a waya ki masa cikakken bayani." Bakin Shukura har rawa yake ta ce. "Ba shi Inna, maza ba shi don Allah." Tana faɗar haka ta miƙe ta shige banɗaki, don kada Daddy ya jiyo wayar da suke yi. Littafin kuɗi ne 500 idan ya kammala 800 ne. Za a turo a acc Aisha Adam 3090957579 First bank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624. Ummou Aslam Bint Adam🌚 [17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. SHAFI NA SHA HUƊU Daga can ɓangaren Inna ce ta ba wa Malam waya, yana karɓa ya ce. "Yarinya faɗi buƙatarki." Kamar Shukura tana jira ta ce. "Malam duka aikin da ka yi mini a wancan karon ne ya lalace." "Yarinya aikinmu ba ya buƙatar garaje, ki yi mana bayani dalla-dalla ta yadda za mu san yadda aka haihu a ragaya." Malam ya faɗa a ɗan tsawace. Ta cikin wayar ta ji Inna tana faɗin. "Ke Shukura ki shiga nutsuwarki mana, ki yi masa bayani dalla-dalla yadda zai fahimta." Tsawa ta ji Malam ya buga wa Inna ya ce. "Tun kafin ki zo, muka san abin da yake tafe da ke. Kada ki sake cewa za a fahimtar da mu, domin mu masu sani ne. Kawai dai muna son ji daga gare ta ne, kin san waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi." Baki yana rawa ta ji Inna ta ce. "Tuba nake malam, a yi mini aikin gafara." Amsa mata ya yi, sannan ya sake yi wa Shukura magana. Tiryan-tiryan Shukura ta yi masa bayanin abin da ya faru, tun daga tashin Daddy daga bacci har zuwa dawowarsa. Sai da ya gama sauraronta sannan ya ce. "Haƙiƙa kishiyarki ta tashi tsaye ba da wasa ba, kuma wannan birkicewar da kika ga

Chapter 11 of 35