Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ƙafa. Saboda shagon su Kabir ana iya zuwa da ƙafa, sai dai akwai 'yar tafiya sosai. Tana tafe tana saƙa da warwara a cikin ranta, ga shi duk lallashin da take yi wa Fatima ta ƙi yin shiru. Wani mai adaidaita sahu ta hango, da sauri shiga ɗaga masa hannu. Har ya wuce ta, ganin goyon da yake bayanta ya sa ya dawo. "Baiwar Allah wannan yarinyar da take kuka daga ina?" Mai ɗan sahun ya tirke ta da tambaya, yana wurga mata kallon tuhuma. "Yata ce, shagon Babanta zan je kunama ce ta harbe ta zan kai ta kemis." Fauziya ta furta a gajiya, kallon da yake yi mata na rashin yarda ya sa ta ɗan waiga ta ce. "Fatima ki faɗa masa me ya samu ƙafarki." Fatima ta sake sakin ihu cikin kuka ta ce, "Cinnaka mai allura ne ya harbe ni, wayyo Mami ƙafata. Don Allah ki cire mini allurar cinnaka." Sai da mutumin ya haska Fatima, sannan ya ga zallar kamar da suke yi da mahaifiyarta. Ya ce Fauziya ta shiga, bayan ta zauna ya wuce da su. Ba su yi wata tafiya mai mugun nisa ba suka ƙarasa, ta miƙa wa mai adaidaita sahu ɗari biyun don ya ɗauki kuɗinsa. Ya ce mata ta je kawai, bayan ta yi masa godiya ta nufi layin da shagon ɗinkin su Kabir yake. Tana gab da ƙarasawa shagon, ta ga wani ya fito daga ciki da mukulli yana shirin rifewa. "Assalamu alaikum." Fauziya ta yi masa sallama, mutumin ya amsa mata yana saka mukullin ƙofar. "Don Allah Kabir fa?" Kallon tsaf ya yi mata, yanayinta ya ga ba ta yi kama da masu karɓar ɗinki ba. Kuma koda ɗinkin za ta karɓa, tana mace har sha biyu saura yana ganin dare ya yi. "Hajiya lafiya?" Fauziya ta dafa bango a gajiye ta ce, "Matarsa ce." Sai a lokacin mutumin ya ɗan faɗaɗa fara'arsa. "Ah Allah sarki, ai ban gane ki ba. Wallahi Kabir ya fita tun bayan sallar isha'i, ni kaɗai na rage a shagon ni ma yanzu zan tashi." Wani abu ya tsaya a zuciyar Fauziya, amma don kar ya fahimci wani abu sai ta saki fuska ta ce, "To shi kenan na gode." Kamar ta karɓi aron kuɗi a wurin mutumin, sai kuma ta haƙura. Don ba ta san duk wani abu da zai taɓa mutumci, da martabar Kabir. Kemis ɗin da ta hango a farkon shigowarta layin ta nufa, ta sake zaro ƙaramar wayarta ta latsa lambar Kabir ko Allah zai sa ta shiga. Bugun farko ta ji an ɗauka, don haka ta yi saurin faɗin. "Hello." Ita ma sai ta ji an ce hello da muryar mace, amma sai ta yi tunanin ko network ne ya maimaita abin da ta faɗa. "Abban Na'ima kana jina?" Daga can ɓangaren ta ji an ja dogon tsaki an kashe. Dam! Gabanta ya yi wani mummunan bugawa, wanda ya sa juya ta fara zabarin ƙafafuwanta har take yunƙurin wurgar da ita. Da sauri ta sake latsa lambar amma sai ta ji ta a kashe, haka kawai ta ji zuciyarta tana yi mata wasu-wasin ko kuskuren lamba ta kira. Kamar wacce take bitar hadda, haka ta fara karanta lambar Kabir a fili tana saka wa a cikin wayarta. Ta sake latsa lambar ta kira saboda ta fita daga kokonton da take yi, amma sai ta ga duk lamba ɗaya ce da wacce ta kira da farko. Wani irin abu ta ji ya tokare mata maƙoshi da ƙirji, ta haɗiyi yawu mai ɗaci har ta ƙarasa shagon mai Kemis ɗin da yake ƙoƙarin rufewa. Da sauri ta ƙarasa ƙofar shagon tana faɗin. "Don Allah ka taimaka ka duba yarinyata kafin ka rufe, wallahi kunama ce ta harbe ta." Tausayinta ne ya kama shi, ya zare kwaɗon ƙofar ya koma ciki. Saboda tsabar gajiya, da ƙyar ta iya sauko Fatima ta miƙa masa. Bayanin abin da ya faru ta yi masa, sannan ya yi wa Fatima allurai. Ya ɗebo magunguna ya yi mata bayanin yadda za a ta dinga ba ta, jiki a sanyaye Fauziya ta ce. "To nawa ne kuɗin?" Sai da ya sake duba magungunan ya ce, "Hajiya gabaɗaya kuɗinki dubu huɗu da ɗari biyar." Kirjin Fauziya ya buga, ta dubi wayarta da ko dubu huɗu ba za a saye ta ba ta ce. "Don girman Allah ka yi mini wata alfarma, don Allah ka yi mini haƙuri zuwa gobe da safe. Yanzu haka shagon mahaifinta na zo ba ya nan, wallahi ɗari biyu ce kawai a hannuna." Cike da takaici yake wurga mata wani kallo, ya furta. "Haba Hajiya, yanzu ni kin yi mini adalci kenan? Tun farko ai da sai ki ce mini ba ki da kuɗi, ni ma fa ba shagona ba ne. Yanzu idan Oga ya zo me zan ce masa? Kin san dai gari ba gaskiya, magana ta Allah ba zan iya ba ki kayan dubu huɗu da wani abu ki tafi da su ba." Wayar hannunta ta miƙa masa ta ce, "Na san ban kyauta ba, amma don Allah ka yi haƙuri. Ga wayata ka riƙe, zuwa gobe In Shaa Allahu zan kawo maka cikon kuɗin..." "A'a gaskiya, ba zan karɓi wayarki ba. Zan dai karɓi magungunan, ki je gobe da safen sai ki kawo kuɗin. Idan ma ba ki dawo ba, ni a aljihuna na biya kuɗin allurar da na yi mata." Mai kemis ɗin ya katse ta yana kwashe magungunansa, sannan ya miƙe mata wayarta ya ƙoƙarin fitowa daga ciki. Duk yadda Fauziya ta kai ga roƙonsa fir ya ƙi amincewa, saboda ya jaddada mata shi ma ba shagonsa ba ne. Idan aka samu matsala a aljihunsa yake ciko. A wannan karon ma haka ta dinga tafiya a ƙafa, sai dai wannan lokacin har ta ƙarasa gida ba ta samu adaidaita sahu ba. Sai tsirarun motocin gida da suke kai kawo a titi. Ta ci sa'a kamar yadda ta janyo ƙofar haka ta same ta, ta yi mamaki sosai da har sha biyu da kusan rabi amma Kabir bai dawo ba. Ba yau Kabir ya saba kai dare da sunan yana shago ba, amma bai taɓa haure sha biyun da rabi na dare a waje ba. Wannan ne ya sake tabbatar mata da zarginta. "An ya Kabir ɗina zai iya zuwa wurin wata mace a tsohon daren nan?" Ta furta tana sake tuna muryar wacce ta ɗauki wayar. "Kabir ɗina babu macen da take gabansa." Fauziya ta faɗa tana girgiza kanta. Da haka ta miƙe ta sake yi wa su Na'ima shimfiɗa a tsakar ɗaki, ta kwantar da su don ta samu Fatima ta tsagaita da kukan. Bugun ƙofarsa ta ji, ta ji wani ɓacin rai ya lulluɓe ta. Kamar ba za ta tashi ba, tuna gidan ba su kaɗai ba ne ya sa ta yunƙura ta fita ta buɗe masa. Saboda haushinsa da take ji, ko kallonsa ba ta yi ba ta wuce ciki. Suna shiga ɗaki ta ɗebo kayan abincinsa ta ajiye ba tare da ta tanka masa ba. "Ummu banat lafiya kuwa? Na ga kamar ba yadda na saba ganinki ba." Kamar tana jira a ƙule ta ce, "Ta ya za ga gan ni dama? Bayan kana can wurin 'yanmatanka, yanzu Abban Na'ima cin mutumcin da wulaƙancin har ya kai ka tafi wurin wata har na kira ka ba ta waya." Idanunta suka ciko da hawaye tana jin wani maƙaƙi a cikin zuciyarta. "Ai duk wulaƙancin da za ka yi mini ban cancanci haka daga gare ka ba, amma babu komai akwai Allah." Ta ƙarasa maganar cikin shasshekar kuka. "Innalillah wa inna'ilaihir raji'un! Yanzu ni kike zargi Fauziya? Ni Kabir ɗinki kike zargi da yawon gidan 'yanmata? Yanzu ko wani ne ya jefe ni da waɗannan kalaman, ashe ba za ki iya wanke ni ta hanyar shaidata ba?" Shiru Fauziya ta yi tana mamakin kalamansa, tana kallon rainin hankalin da yake shirin yi mata. Ita kanta da wani ne ya sanar da ita abin da ta ji a lokacin, ba za ta taɓa yarda ba. "Kana nufin wacce ta yi mini tsaki ɗazu ba ka santa ba? Ko kana nufin ba wayarka ba ce? Don Allah Abban Na'ima kada ka mayar da ni wacce ba ta san me take yi ba." Kabir ya sake marairaice murya ya ce, "Haba Fauziya, mene ne nawa ba ki sani ba? Kina tsammanin akwai wata mace da zan ɓata lokacina a kanta? Wallahi abin da kike faɗa ban san shi ba. Haba Fauzeena, yau fa da farinciki na ƙaraso gida saboda 'yan canjin da na samo." Ya yi maganar yana sakin murmushi ya cigaba da cewa. "Wallahi yau aiki ne ya sha mini kai, mun jima ba mu yi ɗinki irin na yau ba." Girgiza kai Fauziya ta yi tana jin ɗaci a ranta, a ɓangare ɗaya tsoron Kabir ya fara kama ta saboda ita da Kabir ba sa ɓoyewa junansu komai. "Abban Na'ima yaushe ka fara ɓoye mini halin da kake ciki? Yaushe ka fara yi mini ƙarya?" Ƙirjin Kabir ya buga da ƙarfi yana shirin yin magana ta katse shi. "Ko minti talatin ban yi da baro shagonku ba, kuma an tabbatar mini da tun bayan sallar Isha'i ka bar shagon. Ashe kullum ninke ni kake yi? Ina nan yashe da baki ban sani ba." "To ai fitar da na yi daga shagon gidan Alhaji Musa na je, kaya na kai wa iyalinsa kin san duk cikin shagonmu ya fi yarda da ƙwarewa ta. To lokacin da na je ƙofar gidan na kira wayarsa a kashe. Da na ce a yi mini sallama da shi, sai yaran gidan suka ce yana ganawa da wasu abokan kasuwancinsa, sai dai da na jira su kammala. Ganin zaman ya yi yawa ya sa na bayar da wayata aka jona mini caji a gidan, lokacin da Alhaji ya sallame ni har na kusa zuwa gida, na tuna na bar wayata a gidan shi ya sa na koma na karɓo." Kabir ya janyo ledojin da ya shiga da su ya ce. "Ki dubi wannan sayayyar da na yi, duk da kuɗin da Alhaji ya biya ni ne. Wannan shinkafar kwano ɗaya ce, ga taliya da makaroni guda bibbiyu sai wake kwata da na ƙaro mana." Ya sake buɗe ɗayar ledar ya ce. "Wanna kuma fulawa ce kwano ɗaya, ga sabulun wanka da omo dama na ji kin ce za ki yi wanki. Sai biskit da alawar yara." Sai ya sakar mata murmushi ya miƙa mata wata ledar ya ce, "Ga shi har tsire na sayo mana mu da yara, kin ga da safe sai mu sha da shayi tun da har madara na sayo." Har a ranta ta ji daɗi, domin duk halin Kabir mutum ne da ya tsayu a kan ciyar da iyalinsa. Shi ba mai ƙarfi ba ne, amma indai a ɓangaren ciyarwa ne ko wani mai kuɗin ba zai nuna masa komai ba. Amma haka kawai ta ji zuciyarta ba ta aminta da abin da ya faɗa mata ba, duk da ta ji kaso mafi yawa na daga damuwarta ta yaye. "Ina jin a cikin gidan Alhaji ne aka ɗauki wayar da kika kira, amma kin san babu wata mace da zan ɓa ta lokacina a kanta. Haba Fauzeen KB, har kya kawo wani abu ki sa a ranki don Allah?" Jin sunan da ya faɗa mata ya sa ta saki murmushi, nan take ta aminta da shi. Ganin ya shawo kanta sai ya miƙe ya sauya kaya, ya zura jallabiyarsa ya ɗauki ƙatuwar butar da ke cike da ruwa ya ce. "Bari na watsa ruwa wannan zafin ya yi yawa." Har zai fita ta katse shi. "Yau fa kunama ce ta harbi Fatima a ƙafa." Da sauri ya juyo ya ce, "Garin ya ya?" Ya ƙarasa tambayar yana duba ƙafar da Fauziya ta haska masa. A nan ta sanar da shi duk yadda suka yi da mai Kemis, ya ɗan yi jim ya ce. "Wallahi ciki da waje dubu ashirin ne suka rage mini, nake son na adana ta na samu cikon dubu goma sha biyar na haɗa. Domin na sayi ƙofar da za a saka mana a ginin can. Ko ba mu samu ta ɗakuna ba sai mu yi haƙuri zuwa wani lokaci." Sai ya ɗan yi jim ya ce, "Amma daga wurinki babu wani abu da za a samu?" "Wallahi babu Abban Na'ima, sai dai zuwa gobe Dillaliya za ta zo mu ji nawa za ta yi wa firjin nan kuɗi, ni babban tashin hankalina wa'adin kwanakin nan da suke ƙaratowa. Tun da yau saura wata guda cif, kuma na tabbata Alhaji Mudi ba zai taɓa ɗaga mana ƙafa ba. Da ya zo ya yi mana korar kare gara na sayar da firjin, a yi abin da ba ya rage mu koma. Tun da ba wutar nepa muke samu ba, ka ga yafi ajiyar da ake yi da shi." Shiru ya yi yana nazari sannan ya ce, "Allah zai kawo mana ɗauki, amma gaskiya ba na son ki sayar da firjinki Fauziya. Ki bari dai mu ga yadda Allah zai yi da mu, idan muka koma can wataƙila a dinga samun wuta sai ki yi sana'a da shi." Fauziya ta gurgiza kai, "Kai fa ka ce mana ya ce ranar da notice ɗinmu ya ƙare duk wanda bai tashi ba zai fitar masa da kayansa titi, tun da har muna da abin da za a ɗaga a sayar ɗin ya fi zaman wulaƙanci Abban Na'ima. Na gaji da gidan nan, na gaji da zaman takurar da nake yi ni da 'ya'yana a ciki." Fauziya ta ƙarasa maganar tana jin ɗaci a ranta. "To shi kenan Fauzina, amma dai aro zan karɓa idan Allah Ya hore na ba ki kuɗinki ko jari kya ja." Daga haka ya saka kai ya fice, ta bi bayansa da hararar wasa ta ce. "Ko ba aro ba? Lallai Abban Na'ima." Da yake hanyar banɗakin, da hanyar fita duka kusan hanya ɗaya ce. Da sauri Kabir ya yi soron gidan, ya latsa lambar Surry don tun bayan da ya baro wurinta ya saka wayar a blacklist ta yadda ko ta kira shi ba za ta yi ringing ba idan ba shi ya duba ya gani ba. Murya ciki-ciki ya ji ta ɗauka tana faɗin. "Na gode Kb har ni za ka yi blocking saboda ka koma gida, ai na gwada kiranka da wani layin na ji ya shiga." Kabir ya yi ƙasa da murya ya ce, "Kin san bala'in da kika kusa ɓallo mini kuwa? Wai Sury dama bayan kin shiga gida da wayata matata ta kira kin ɗauka? Gaskiya ban ji daɗi ba kada ki sake yi mini haka." Ganin ran Kabir ya ɓaci sai ta kwantar da murya cikin kissa ta shiga ba shi haƙuri, da yake duk ba a nutsuwarsa yake ba sai ta fahimci haka. "My Kb wai lafiya na ji muryarka haka? Kamar a tsorace kake?" Kabir sai da ya ɗan leƙa don kar ataho bai ji ba ya ce, "Ke ina soron gidanmu fa, yanzu haka wankan da kika jaza mini zan yi shi ne na raɓe a soro. Kin ga yanzu dai sai da safe, kada ta ji ni shiru ta biyo bayana." Har zai kashe ta shagwaɓe murya ta ce, "Baby don Allah kada ka fasa zuwa kai ni ganin ginin da kake yi mini, ka san yadda na gama ba wa ƙawayena labarin gidan kuwa? Gaskiya dole na yi bidiyo na nuna musu." Kabir ya saki murmushi ya ce, "Haba love, ai tun da na yi miki alƙawari kin san ba zan saɓa miki ba, yanzu dai ki yi bacci da tunanina..." Motsin da ya ji a bayansa ya sa shi saurin waigawa, ƙirjinsa ya buga da ƙarfi sakamakon tozalin da ya yi da Fauziya. 07062062624 Ummou Aslam Bint Adam [07/02, 10:10] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA* ©®AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* GARGAƊI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye. SADAUKARWA Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin. SHAFI NA BIYU Irin kallon da take wurga masa, ya shi saurin sauke wayar daga kunne gabansa yana faɗuwa. Fauziya ta sauke ajiyar zuciya, tana bin sa da kallon tuhuma. Duk da ba ta ji wayar da yake yi ba, amma tana da tabbacin da mace yake yin wayar. "Abban Na'ima wankan kenan?" Fauziya ta furta murya babu walwala. Kallo ɗaya za ka yi wa Kabir ka fahimci ba shi da gaskiya, a ɗan diririce ya ce. "Wallahi wata amarya ce ta dame ni da kira, wai gobe ɗaurin aure ban gama mata ɗinki ba." A wannan karon ita kanta Fauziya ba ta aminta da shi ba, duk da a cikin duhu ne amma hasken fitilar wayar ta fallasa sirrin zuciyarsa. "Abban Na'ima!" Ta furta kamar za ta yi kuka, saboda sauye-sauyen halayensa a kullum ƙara ba ta tsoro suke yi. "Abban Na'ima, yaushe ka fara ɓoye mini halin da kake ciki?" Kabir da har lokacin ƙirjinsa yake bugawa, ya ɗago wayar da yake har lokacin bai kashe ba ya ce. "Ga ta ai ban kashe ba, kina iya yi mata magana Fauziya." Kamar ba za ta karɓa ba, sai kuma ta karɓi wayar. Saboda ta fahimci kamar akwai abin da yake ɓoye mata. "Hello!" Fauziya ta furta cikin sanyin murya, daga can ɓangaren Sury ta amsa. "Uwar gida sarautar mata!" Kusan lokaci ɗaya zuciyoyin Kabir da na Fauziya suka buga da wani irin ƙarfi. "Ban da abinki uwar gida, Oga ai ba na ki ba ne ke kaɗai." Maganar Sury ta katse su, nan take jikin Kabir ya ɗauki karkarwa saboda ya yi tsammanin Sury za ta rufa masa asiri. Fauziya tana shirin yin magana Sury ta cigaba da magana. "Idan kika riƙe Oga ke kaɗai mu costomers ina muka kama? Kin ga gobe ɗaurin aurena, a haka ma sai magiya nake kada ya jirga ni, shi ya sa na kasa haƙuri na kira yanzu na yi masa tuni." A fili Fauziya ta sauka ajiyar zuciya ta ce, "Shi kenan, Allah Ya sanya alheri." Sury ta amsa da Amin, sannan ta katse wayar. Butar ya ɗauka ya wuce banɗaki, ita kuma Fauziya ta wuce ɗaki duk sai ta ji ba ta ji daɗin abin da ta yi masa ba. Fauziya tana da kishi sosai a kan Kabir, sau tari sai ta yi wani abin sai kuma ta ji ba ta kyauta ba. "Allah ka rage mini raɗaɗi da zafin kishin bawan Allahn nan, ina tsoron kada zuciya ta sa na fara zargin mijina." Ta furta a raunane. Washegari tun da gari ya waye, Fauziya ta fito ƙofar ɗaki ta fara haɗa musu kayan karin safe. Da yake kowacce abin girkinta yana ƙofar ɗakinta, kasancewar babu kitchen a gidan. Gidan da su Fauziya suke zaune, gidan haya ne mai ɗauke da ɗaukunan mata biyar. Kowacce daga mai yara biyu sai zuwa uku, kuma dukkansu ɗakunansu falle ɗai-ɗai ne sai banɗaki ƙwaya ɗaya da suke amfani da shi. Dalilin da ya sa su A'ilo suka kafa wa Fazuiya ƙahon zuƙa saboda, duk cikinsu mijinta ya fi nasu rufin asiri. Domin ta fi su yawan sauyin tukunya, don Kabir idan da 'yan kuɗi a hannunsa haka zai sayo musu nama ko kifi ko ba can mai yawa ba ta sarrafa. Kuma indai Fauziya ta yi sauyin girki duka sai ta zuba a 'yan robobi ta aika masu, saboda fita haƙƙin maƙotaka. Duk cikin gida Lawisa ce kawai ta su ta zo ɗaya, ba ta yi mata irin cin kashin da su A'ilo suke yi mata. Don haka Fauziya da Lawisa suka haɗa kai, su kuma su A'ilo suma su uku suka haɗe kansu. Da yake ita Lawisa ba ta da haƙuri, sai ya zama suna shakkarta don suna yi mata kan kara take yi musu na itace. Saɓanin Fauziya da ta kasance mace ce mai sanyi, tsananin haƙuri da kawaici. Duk abin da za su yi mata ko su yi wa yaranta, sai dai ta yi shiru idan kuma yara aka yi wa sai dai ta zaunar da su a ɗaki. Babu damar yaranta su fita wasa tsakar gida, sai yaran su A'ilo su doke su da yake kusan duk sun girme su. Ita kuma Fauziya ƙiris suke jira ta yi wani kuskuren, ko ta taɓa kayan wani daga cikinsu sai su hau ta da faɗa. Don haka gidan suke zaune kara zube babu haɗin kai, hatta shara kowacce sai dai ta share iya ƙofar ɗakinta. Banɗaki ma kuwa sai dai kowacce idan mijinta zai yi wanka, ta ɗauki buta ta je ta wanke masa. Shara ce kawai idan ta cika suke haɗawa, idan ta cika wannan ce za ta biya idan wani karon ta sake cika sai wata ma ta bayar da kuɗi a kwashe. Maman Sabir tun da ta fito tsakar gida take leƙen abin da Fauziya take dafawa, ana cikin haka Kabir ya fita ya sayo musu ƙwai guda huɗu. Nan take gidan ya cika da ƙamshin suyar ƙwai, baƙinciki da hassada suka ƙara cika zuciyoyin su. Bayan ta gama sai da ta gutsiri kaɗan-kaɗan ta saka a leda kowacce ta miƙa mata, sannan suka shige ɗaki ita da iyalanta suka karya. Da yake ranar Lahadi ce babu makarantar boko ya sa bayan sun gama ta yi wa yaranta wanka. Kabir ya ɗauki Fatima ya mayar da ita kemis, ya karɓo mata magunguna sannan ya wuce shagonsu na ɗinki. Su Fatima ne suka fita tsakar gida wasa, abin ka da yaro duk kyarar da yaran su A'ilo suke yi musu da sun ga suna wasa haka za su je su shiga cikinsu. Zaman su a wurin babu wuya kenan sai Nabila ta fisge abin wasanta a hannun Na'ima ta ce, "Umma ta ce na daina wasa da ku, babanku ɗan shaye-shaye ne." Duk da ba su san me kalmar take nufi ba, amma tun da suka ji suna yawan faɗa musu cikin tsangwama sai suka ƙyamace ta, Na'ima ta ɓa ta fuska ta ce. "Ba dai babanmu ba, sai dai babanku. Abi yana siyo mana alewa da biskit, ba ɗan shaye-shaye ba ne." Duk cikinsu Sabir yayan Nabila ya girme su, don kusan shekararsa goma. Ya fi su wayo don haka ya ce, "Ke mu babanmu ba ya shaye-shaye, Ummanmu ta ce mu daina wasa da ku kada mu zama 'yan'iska. Wai babanku har shiga ɗakin matan aure yake yi."Yaron ya ƙarasa magana yana dariyar tsokana. Abin sai ya yi wa su Na'ima ciwo, don haka suka shiga mayar da martani abin har ya zame musu faɗa. Suna cikin kokawa su Nabila suka tararwa Na'ima da duka, da ta ji zafi ita kuma sai ta ciji Hafsa a hannu. Nan take iyayensu suka fito, dama kamar jira suke yi. Cikin masifa Maman Sabir ta fisge Fatima tana ƙwalawa Fauziya kira, Fauziya da ke ɗaki ta yi saurin fitowa tana shirin yin magana Maman Sabir ta katse ta. "Wallahi wannan shi ne na farko na ƙarshe, ko da wasa idan Fatima ta sake cizar mini 'ya'ya sai na ɗauki hannunta na tura musu a baki sun rama. Ƙarya aka yi uban na su ba mashayi ba ne? Na ga rannan da ya yi mankas ɗakin

Chapter 14 of 35