An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
MABUƊI
Idan aka ambaci kalmar 'Fuska' abin da yake fara zuwa zuciyoyi da dama, ita ce fuskar ɗan'adam da Allah Subhanahu Wata'ala Ya hallita masa. Wacce a cikinta Ya samar da rassa mabambamta, don a mafi yawancin lokuta ta hanyar ganin fuskar ne ake gane ɗan yanki kaza da kuma al'umma kaza.
Idan muka dubi aure ta fuskar addinin Musulumci, za mu fahimci abu ne mai kyau. Domin koyi ne, ga sunnar Annabinmu Annabi Muhammad (S.A.W). Wanda hawa doron sunnar yana iya kai miliyoyin Al'umma zuwa ga turbar tudin tsira, wato Aljannar da kowanne cikakken ɗan'adam musulmi yake fatan rabauta da ita. Kuskurewa haka; ko wofantar da ƙa'idojin bin sunnar, suna iya kwasar al'umma zuwa ga wutar Jahannama. Wacce duk musulumin ƙwarai yake bakin ƙoƙari, wurin yin katangar ƙarfe/ tsari da ita.
Kamar yadda muka sani, zamani rikiɗa yake tamkar hawainiya/wahainiya. Haka kowanne zamani da suffar da yake tafiya, tare da al'ummar da suke rayuwa a cikinsa. A wannan zamanin da ake tafiyar biri a yashi, mata da dama suna kallon aure da ta fuskoki daban-daban. Haka kuma wasu sukan kalli ƙarin aure, ko kawo abokiyar zama ta munanan fuskoki mabambamta. Musamman yadda iyayen gida suke ganin wayo ko dabararsu ce, ta sa aka auro su a matsayinsu na iyayen gida. Har wasu daga cikinsu suke cin duniyarsu da tsinken tsire, ta hanyar gasa wa amare gyaɗa a hannu. Ko kuma ɗanɗana wa maza kuɗarsu, domin hana su rawar gaban hantsi da amarensu. Saboda suna ganin sun zama tamkar ruwa a cikin gida ko kuma kujerun zama, da ko an ƙi ko an so dole a zauna da su. Ba tare da sun hangi me gobensu za ta haifar musu ba.
To amma duk da yadda ake ganin iyayen gida suna wasan juyin waina da amare, lamarin bai sauya zani ba. Domin a ɓagaren amaren da suke ta cin alwashin mijin wata ne zaɓinsu, a guntun tunanin wasu daga ciki. Sukan yi tsammanin gazawa, gajiyawa da rashin so ne yake sa miji yake nemansu har ya aura a matsayin mata ta biyu, uku ko huɗu. Musamman da ya kasance maza da dama, sukan kwayewa iyayen gida baya tun a neman auren. Silar haka ne yake sa amare suke hangen kansu a bigiren cusguna uwargida, duk don su nuna musu miji ya daina yayinsu. Ko kuma sun daina ganinsu, a matsayin mata masu ƙirar da Allah (S.W.A) Ya hallata musu, domin su kasance sanyin idaniya a wurinsu. Ba tare da amaren suna tsalle ko yin ɗage ba, don su hangi yankan kunkurin Balan da suke yi wa rayuwarsu.
SHAFI NA ƊAYA
Gidan Yaya Salis cike yake da mata har da ƙananan yara, saboda yinin dannar ƙirjin da ake yi wa Aunty Murja. Tun da yamma ta ƙarato gabanta yake ta faɗuwa, don haka ta koma cikin 'yan uwanta da ke ɗakin gadonta. Musamman da giftawa ɗaya-biyu idan ta yi, daga tsakar gida zuwa falonta sai ta ji maganar da za ta sosa mata rai.
Bilkisu zaune take a falon gidan ita da ragowar 'yan'uwanta, don yawanci cikin falon cike yake da su dangin miji. Kallon Hafsa ta yi ta ce.
"Miƙo kuɗin na ki ankon, dama ai kin ce idan muka haɗu yau za ki ba ni. Kin san yanzu an daina kasuwanci da bashi, maza ki ba ni na ɗora lissafi." Murmushi Hafsa ta yi ta ce.
"Aunty Bilkisu duk cinikin da kika yi ina laifi ma ki bar mini a ribar da kika samu." Harararta Bilkisu ta yi, za ta yi magana suka ga Aunty Murja ta fito ta shiga kicin. Salma ce ta ɗan zunguro Bilkisu, ta yi ƙasa-ƙasa da murya ta ce.
"Ni fa wallahi Aunty Murja tausayi take ba ni, duk da tana danne kishinta amma kin ga duk ta rame, ji fuskarta duk ta sauya kamar kuka ma ta yi."
Taɓe baki Bilkisu ta yi ta ce, "Ni babu wani tausayi da ta ba ni, ai wallahi ba ƙaramin daɗi na ji ba. Ki duba fa ki ga yadda ta samu wuri a gidan nan, duk girman ɗakunan nan a ce daga ita sai 'yan 'ya'yanta uku. Duk ta bi ta kanainaye shi kullum sai uwar ƙiba yake yi, yanzu idan aka kawo amarya ai dole ta lanƙwashe ƙafafuwanta." Lokaci ɗaya suka saki shewa haɗe da tafawa.
Hadiza da ke gefe, abokiyar wasan su Bilkisu ce ta ce.
"Magana ta domin Allah fa babu macen da ba ta san sakewa a gidanta, sai dai idan ba ta samu yadda take so ba. Kishiya kuwa ai babu daɗi, ni wallahi Aunty Murja ma ba ƙaramin birge ni ta yi ba. Saboda ko babu koma ta kama kanta, babu abu ɗaya da za a ce ta yi a lokacin bikin nan."
"Allah ko sakaran neman wurin zaman? To ni dai ina shafin amarya. Don jiya da na je lalle na biyo ta nan, danginta sun zo jere har taya su buga ƙusar labule na yi. Ke zanin gado ma ni na shinfiɗa, yoo hauka ake zan bi bayan matar wa ga wurin da ɗan'uwana zai ɓarje amarci."
Bilkisu ta faɗa cikin isgilanci, sai kuma ta sake taɓe baki ta ce.
"Wai kun ga yadda jiya ya tasa ta a gaba yake aikin lallashi, kai na sake yarda wallahi an shanye Yaya Salis har ƙafafuwansa. Wai duk yadda yake bautawa matar nan jiya har ji na yi yana yi mata alƙawarin sayen mota. Wallahi wannan auren da ya yi na san har da addu'arsu Baba, don yadda ta wanke hannu a kansa idan an ce zai kalli mace ma zan yi mamaki."
Sadiya ta saki dariya ta ce, "Ni duk ba wannan ba, wallahi idonta kawai nake son gani idan an kawo amaryar. Yen yen yen yen abu kaɗan Abban Sajida, Allah Ya sa ya yi mata halin mazan ta gani ba dai ya yi auren..." Maganar Sadiya ce ta maƙale sakamakon ganin Aunty Murja ta fito daha kicin za ta wuce, duk da ta ji wasu daga cikin kalaman da suke tattaunawa sai ta yi kamar ba ta ji ba. Da za ta wuce ta sakar musu murmushi ta ce, "Sannunku da hutawa."
Bilkisu ta yi zaraf ta ce, "Aunty Murja ai ke ce da sannu, kishiya ai ba sauƙi ba ce. Ni wallahi idan aka ce akwai ranar da Yaya zai yi miki kishiya ƙaryatawa zan yi, hmmm namiji rumbun ƙaya mai abin mamaki." Kafin Aunty Murja ta yi magana suka ji tsaiwar motocin 'yan kawo amarya a ƙofar gida. Guɗa aka fara saki ta ko'ina hakan ya tsananta bugawar zuciyar Aunty Murja. Idanunta suka ciko da ƙwalla, ba ta yi aune ba sai ji ta yi hawaye yana zuba. Bilkisu ce ta yi saurin sunne kai ƙasa tana dariyar ƙeta, da sauri Aunty Murja ta wuce ɗakinta jin kukan da take dannewa zai ƙwace mata. Su Sadiya ne suka miƙe da sauri suka nufi hanyar waje don tarbar amarya. Yadda Bilkisu ta zaƙe a lokacin za ka ɗauka ciki ɗaya suka fito da amaryar, don har wasu daga cikin dangin amaryar sun gane ta musamman waɗanda suka je jere.
Yadda su Bilkisu suke haba-haba da amarya da danginta ya sa daɗi ya mamaye su, har suke ganin kamar sun fi sonta a kan Aunty Murja. Wasu daga ciki har suke tsegumin ko Aunty Murja ba ta da hali mai kyau, shi ya sa suke yin nan-nan da ita.
Kusan duka 'yan uwan Yaya Salis sun watse tun bayan da aka kawo amarya, haka daga ɓangaren 'yan uwan uwargida Aunty Murja. Sai Bilkisu ce kawai ta rage, da yake ta ce mijinta Hafiz ne zai biyo ya ɗauke ta su tafi.
Aunty Murja ba ƙaramin mamakin Bilkisu ta yi ba, a tsammaninta koda ya kasance yayanta ne zai yi auren, amma za ta iya yi mata kara ko don kada ta ji haushi. Amma abin da ya tsaye mata a rai Bilkisu ce har da fitar da atamfar anko, domin har wunin bikin Aunty Murja ta ce ba za ta yi ba, Bilki ta ce su za su yi idan ita ba za ta iya ba. Ganin irin rawar jikin da suke yi a kan amaryar ya sa ta sake janye jikinta da su.
A lokacin da Hafiz ya zo ɗaukar Bilkisu a daidai lokacin Yaya Salisu ya shiga gidan, da gayya Bilksu ta raka shi sashen Murja don ta ga abin da zai faru. Tana tsaye a bakin ƙofa ta ga ya rungume Aunty Murja, daga shi har ita aka rasa wanda ya riga wani fara zubar da hawaye.
"Ki yi hauri Ummu Sajida, kin san wane ne mijinki. Na san duk abin da zan faɗa a yanzu ba za ki yarda da ni ba, but trust me wallahi ban yi auren nan don na wulaƙanta ki ba. Har abada ke ta dabance a cikin raina, ke ta musamman ce 'yar Aljannata." Yaya Salis ya furta yana sakar mata fake a goshi, saboda Aunty Murja mace ce mai haƙurin gaske. Kuma har cikin zuciyarsa yake faɗar kalaman bakinsa, guntun tsaki Bilkisu ta saki ta nufi sashen amarya. Tana shiga ta ga ƙawayenta sun yi carko-carko, ta ji ɗaya daga ciki tana cewa.
"Na'ima mu kam za mu wuce tun da angon har yanzu bai shigo ba, wai ba kin ce ya ce miki ya kusa ƙarasowa gidan ba?"
Bilkisu ta taɓe baki ta ce.
"Ina za ku gan shi yanzu? Yana can waccan uwar kusasun ta saka shi a ɗaki sai lailaye ta yake yana lallashinta. To Aunty Na'ima ni zan wuce, don na ga abin na yaya ba me ƙarewa ba ne, sai ya kawo ki gidana bayan kwana biyu." A ɗan kunyace Na'ima ta amsa, Bilkisu ta fita ta haye mashin ɗin Hafiz suka wuce gida.
WASHEGARI
Tun da gari ya waye Bilkisu ta lura da sauyin Hafiz, sai wani nannan yake yana haba-haba da ita. Sai da yaran suka tafi makaranta gabaɗaya sannan ya cewa Bilkisu.
"Ummu Sayyid, don Allah magana nake so mu yi da ke ta fahimta. Kuma ki kwantar da hankalinki wannan ba wani abu ba ne, ni dai kin san ina sonki kuma ina matuƙar ƙaunarki Bilkisu." Gabanta ne ya faɗi, da sauri ta haɗe fuska ta ce.
"Ka ga ni ba na son wannan kewaye-kewayen, duk me ya kawo waɗannan maganganun?" Murmushi ya yi ya ce.
"Haka ne, to kin san komai da kika sani a rayuwa muƙaddari ne daga Ubangiji. Kuma kin san akwai abin da yake ƙaddara a cikin rayuwar mutum, ko ba ya so babu yadda zai yi da shi."
Hafiz ya ɗan yi jim sai ya cigaba da cewa.
"Dama tun kwanaki nake son sanar da ke, akwai wata yarinya da na yaba da hankalinta. Ko kaɗan ba ta da hayaniya, shi ya sa nake son aurenta. Don ba zan kawo wacce za ta tarwatsa mini gida ba..."
"Dakata don Allah Hafiz, wannan wacce irin maganar banza kake faɗa mini? Yanzu dama akwai ranar da za ka munafurce ni? Ni za ka ƙara wa kishiya Hafiz?"
Bilkisu ta furta cikin fusata. Hafiz ya sake kwantar da murya ya ce.
"Wallahi na so sanar da ke tun rannan, sai kuma na ga za ku shiga bikin Yaya Salis don haka na bari sai an gama. To jiya bayan kin fita su Baba Ƙarami suka je kai kuɗin aurena wurin iyayen Amina."
A wannan karon ma ɗagowa Hafiz ya yi yana satar kallonta sannan ya ce.
"Wallahi ana zuwa, mahaifinta ya ce a ɗaura aure idan har da gaske nake yi. Idan ya so ko daga ba ya a yi duk bidi'o'in da ake yi na al'ada, wai saboda wasu samarin suna amfani da kai kuɗin aure don su ɓata ya..."
"Kutumar..."
Uban ashar ɗin da Bilkisu ta lailayo ta maka ya katse maganar Hafiza, nan take jikinta ya ɗauki karkarwa cikin tsananin zafin kishi ta cikumo wuyansa ta ce.
"Wallahi duk shegiyar da ka aura sai ka sake ta, ni za ka wulaƙanta ka tozarta? Wallahi ko ka sake ta ko na kashe ka, kuma na kashe kaina yanzun nan." Bilkisu ta ƙarasa maganar tana fisgo sharɓeɓiyar wuƙa a kwandon wanke-wanke.
GIDAN ALHAJI UMAR
Hajiya Karima wayarta ta ɗauko ta latsa layin lambar mai gidanta, ba a ɗauki lokaci ba ta ji ya ɗauka. Don haka cike da ƙosawa ta ce, "Alhaji ko na wuce ɗaki ne? Tsawon minti goma sha biyar fa kenan da ka ce na fito kuma na ji ku shiru."
"A'a ga mu nan zuwa." Daga can ɓangaren Alhaji Umar ya ba ta amsa. Tana nan zaune babu jimawa ta ji ya shigo falon baki ɗauke da sallama. Ɗago da kai ta yi ta amsa masa, ta hangi hannunsa a maƙale da na Shukura da take biye da shi. Zama ya yi a kujerar da ke kallonta, Shukura ta matsa jikinsa tana lafe kanta a gefen kafaɗarsa. A ɗan duburburce Alhaji Umar ya ce.
"Wallahi... kin san akwai gajiyar biki. Duk ta gaji ne."
Murmushi Hajiya Karima ta yi, duk da tana jin zafi a ranta amma sai ta danne ta ce, "Ai dama gajiya sai a hankali za ta warware."
A hankali Shukra ta gyara mayafinta cikin dabara ta fara ƙarewa Hajiya Karima kallo.
Hajiya Karima babbar mace ce da za ta kai shekara talatin da bakwai zuwa arba'in, ita da Alhaji Umar aure suka yi tun na saurayi da budurwa. Alhaji Umar zai yi shekara arba'in da bakwai zuwa hamsin, tun da suke tare da Hajiya Karima bai taɓa ƙara aure ba, sai a wannan lokacin da ya auro Shukura mai shekara goma sha takwas a duniya.
Ta cikin mayafi Shukura ta yamutsa fuska a cikin ranta ta ce.
'Gaskiya baby ya yi haƙurin zama da wannan abar, don Allah dubi yadda duk naman fuskarta ya saki. Aba ta yi shirim da uwar ƙiɓa babu fasali.'
Gyran muryar da Alhaji Umar ya yi ne ya katse gajeren tunanin da Shukura ta faɗa.
"AlhamduLillah! Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangiji (S.W.A), Hajiya ke da Shukura na haɗa ku a nan ne domin na yi muku 'yar nasiha. Gabaɗayanku matana ne, ke Hajiya ke ce babba. Idan kika kama girmanki za ku zauna lafiya babu rashin kunya ko tashin hankali, haka kema Shukura. Wannan uwargidana ce, ba ta da matsala da kowa tun zamana da ita. Ban auro ki don ki raina ta ba, haka ita ma daga ɓangarenta."
Alhaji Umar ya furta cikin tausasan lafuza. Ya jima yana yi musu nasiha sannan kowa ya wuce ɗakinsa.
Tun da Hajiya Karima ta shiga ɗaki ta ji zuciyarta duk babu daɗi, duk yadda ta kai ga danne kishinta sai da ta ji ƙwalla ta zubo mata. Saboda rana ta farko kenan, da suka raba makwamci da Alhaji tun tsawon shekara ashirin da biyar da aurensu. Alwala ta ɗauro ya fara gabatar da sallolin nafila, ta shiga kwararo addu'o'i sannan ta ji zuciyarta ta yi mata sanyi.
WASHEGARI
Asubar fari ta ji ana buga mata ƙofa, a hankali ta yunƙura ta zage sakatar ɗakin. Alhaji ta gani sanye ta doguwar rigar, ta ɗan murza idanunta ta ce.
"An kira sallar Asuba ko?"
Murmushi Alhaji ya yi yana ɗan sosa kai ya ce, "A'a tukunna dai."
Shiru ta yi tana jiran abin da ya kawo shi a lokacin, Alhaji ya sunne kai ƙasa ya ce.
"Wallahi dama ashe gas ɗinta ne ba a haɗa mata ba. Shi ne na ce za ki ɗan ɗora mana ruwa."
Ƙirjinta ne ya yi wani irin bugu da ƙarfi, nan take ta ji zuciyarta ta ɗauki tururi. Da wani irin kallon mamaki ta kalle shi, don ta yi tsammanin ko babu komai zai ji nauyin yi mata wannan maganar. Tun da kawaici mai sunan kawaici ta yi a lokacin shirye-shiryen aurensa.
"Amm... dama... saboda ta ce ba za ta iya amfani da ruwan sanyi ba ne..."
Alhaji Umar ya furta a rarrabe cikin jin nauyi, musamman da ya lura da irin kallon da take jefa masa.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA BIYU
Haɗiye yawu mai ɗaci Hajiya Karima ta yi, ta shanye abin da yake ƙunshe a saman ƙirjinta ta ce.
"Babu damuwa."
Fitowa ta yi ta za ta nufi ƙofar kicin ɗinta jiki a sanyaye Alhaji Umar ya ce.
"Na ce ko na zo na ɗora, na ga kamar na katse miki bacci."
Kallon tsaf ta yi masa, kamar za ta yi shiru sai kuma ta ce.
"Da ka san za ka iya ɗorawa kuma ka taso ni?"
Shiru ya yi mata baice komai ba, Hajiya Karima ta ɗauki tukunya ta ɗora musu ruwan. Kan kujerar falo ta ga ya je ya zauna, har ta juya za ta shiga ɗaki daga can ɗakin Shukura ta ji an ce.
"Babyyyyy!"
A zabure ta ga Alhaji ya miƙe ya nufi ɗakin ta girgiza kai ta shige ɗakinta, tana tuna yadda ta ji ana cewa zama da kishiya sai an daure. Ashe dama haka matan da aka yi wa kishiya suke ji a cikin zuciyoyinsu? Ashe dama duk tsawon shekarun da ka ɗauka da miji idan ya yi aure sai ka ji zafi a ranka? Ashe gaskiya ne da ake cewa ba a tsufa da kishi haka ne? Ayarin tambayoyin da ta dinga jefa wa zuciyarta kenan, bayan ta shiga ɗaki. Sai da ta tabbatar da ruwan ya yi zafi sannan ta fito ta kashe gas ɗin ta koma ɗakinta, don ba ta son duk wani abu da zai kai kunnenta har ya ɓata mata rai. Alwala ta ɗauro saboda lokacin an fara kiran sallar Asuba, jin za a shiga masallaci ya sa ta nufi ɗakunan yaran gidan ta tashe su yin sallah.
Da gari ya waye kamar kullum ita da Ruƙayya suka haɗa abin karyawa, bayan sun kammala ta zuba na su Shukura a cooler ta ajiye musu. Ita da yara kuma, suka baje a babban falo kamar yadda suka saba idan babu makaranta. Suna nan zaune suka ga Alhaji da Shukura sun ƙaraso ɗakin sai yatsina take yi, a ɗan kunyace yake son zame hannunsa daga cikin naya saboda ganin yaransa a wurin. Sake riƙe hannunsa ta yi gam, sai kawai ya wayance da cewa.
"Mamana yau ko tayi babu? Amma dai ke kika yi girki don na ji gidan sai ƙamshi yake yi."
"Ummm!"
Ruƙayya ta furta a daƙile, saboda har lokacin ba ta daina fushin auren mahaifinsu ba.
"Hajiya barka da safiya." Alhaji ya furta yana ƙoƙarin kawar da idonsa daga cikin nata, don haka kawai yake jin nauyinta.
"Barka dai Daddyn yara ya kwanan amarya?"
Alhaji ya washe baki ya ce, "AlhamduLillah."
"Daddy ina kwana." Yaran suka haɗa baki suka gaida shi, amsa musu ya yi sai ya ce.
"Ba ku gaida Auntynku ba."
"Mazan ne kawai suka gaishe ta, amma Ruƙayya ko ƙurarta ba ta kalla ba." Zama Alhaji ya yi a ƙasa, ita ma Shukra ta zauna a kusa da shi tana ta yarfe hannu alamun ba ta jin daɗin jikinta.
"Ina kwana."
Shukra ta furta wa Hajiya tana sake yamutsa fuska, Hajiya ta luwa sarai da yanayin Shukra sai ta yi kamar ba ta gane ba ta ce.
"Lafiya ƙalau, ya kwanan baƙunta."
"AlhamduLillah." Shukra ta furta tana lafewa a jikin Alhaji. Miƙewa Ruƙayya ta yi za ta bar falon, mahaifiyarta ta ce.
"Mami ɗauko abincin Auntynku a kicin." Wani baƙinciki ne ya mamaye ta, ta wurga mata harara karaf idonta ya haɗu wuri ɗaya da na Shukura. Wani siririn murmushi Shukura ta yi a cikin zuciyarta ta ce.
'Da alama yarinyar nan kin fi uwarki zafin kai, ai kuwa zan sauke miki shi don ni ba sa'ar yinki ba ce. Ubanki ne daidai da ni, da ni kike zancan.'
Kamar mai ciwon haƙori haka Ruƙayya ta amsa da to, sannan ta wuce kicin ta ɗauko ta dire a gaban Shukura.
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 35