Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zan bari ta kwana ba dole in zo in bincika,sai dai alhaji shi yafi dacewa ya sani,tunda nayi sa'a yana nan.Tayi dan tagumi......Subhanalillahi!Bari in yi masa magana.Ta mike jiki a salube ta shiga dakin abba ta iske ya kammala tace,wai magana ce tafe da saude idan ka gama ka taso muje,To muje gani nan".Ta gyara zama ta maida musu abinda baraka ta gaya mata umma ta shiga tafa hannu,abba kuwa sai daya mike."Kar dai ace shi ne yazo jiya da daddare?Lallai biri yayi kama da mutum,ina maman take? Umma ta dube shi ido taf da kwalla,tana daki. Kira min ita!Ta mike ta fita,har suka dawo tare babu wanda ya tanka sbda tsabar mutuwar jinin jikinta,a darare ta karaso dakin tana fadin,inna sannu da zuwa."Ta zuba mata ido,ke ma sannu."Ta gaishe da abba da umma na mata kallon mamaki,ta dube shi suka hada ido,tace abba ga-ni" yace,wanene yazo gun ki jiya?Ta sunkuyar da kai,tayi shiru,ya daka mata tsawa,ko baki ji ne?Nace waya zo gun ki jiya? Tana rawar lebe tace dan-liti?"Kin kuwa san ko waye danliti a garin nan? Tayi shiru,mama ni kike so ki mayar tsohon bnza,ki tozarta?jiya me na gaya miki?To ni ba hayaniya na kira ki mu yi ba domin a iya sani na ke mai hankali ce,kin san abinda ya dace,kin fi kowa sanin cewa saura 'yan watanni suka rage bikin ki.Sannan idan kika nutsu kika yi tunani ba mutuncin mu bane daga ke har mu ace an gan ki,kina karakaina a shagon wani ma,balle danliti sbda haka nake umurtar ki daga rana mai kamar ta yau,bana son in sake jin wani labari makamancin wannan!Ina fatan kin fahimce ni?Ta kara sunkuyar da kai yayin da idanuwanta suka fara tsiyayar ruwan hawaye,umma ta muskuta ta karbe "kin bani mamaki ba kadan ba mama,wai ma in tambaye ki,me kike nufi da bin sa har shagonsa? Shiru babu amasa,umma ta cigaba,wannan katon sakarci da me yayi kama?A zaton ki abin birgewa ne yadda 'yan mata ke tsayuwa kofar shagon samari suna amsar abin hannun su?Ban taba zaton hakan zai fito daga gareki ba mama kuma mun saurara miki ne kawai sbda wannan shine karo na farko da irin haka ta faru!" Inna tace,kin ga gidan nan da dukkan jama'ar gidan dake cikin sa ana ganin girma da mutuncin su musamman mahaifnki,don girman Allah kar ki bari wani ya rusa wannan ginin,ya hure miki kunne ya kai ki ya baro,kin ji mam? Ta goge kwalla bata ce uffan ba,abba yace,to mun ci mun rufe anan bana son ki sake aikata wani abinda zai sa ayi miki zama irin wannan,kin ji ni? Ta amsa da kai tana goge kwalla.umma tace tashi maza muje ki dauko min ledar kayan da aka ce ya baki,a iya sani na dai baki da yunwar su,maza tashi muje!Ta mike da kyar umma ta tasa ta suka je dakin ta dauko ledar.Umma ta fizge cikin zafi tace,Allah yasa in sake gani ko ji sai kin sha mamaki!" Ta fice ta bar dakin,ta bar mama cikin tashin hankalin da bata taba jin irinsa ba,har inna ta gama zamanta ta bar gidan mama na aikin kuka a daki domin dai tamkar sun kara debo soyayyar danliti ne sun kara antayawa cikin zuciyarta.Ita wannan ranar da suke kwakwazon an sanya mata ta jima da manta saurayin ma balle ranar,ba shi a idon ta ko birnin zuciyarta.Al'amarin ya daurewa iyayenta kai,shin wai me mama take nufi da kukan ta? Tambayar zukatan su kawai suke yi amma basu da tabbacin amsa.Karfe takwas da rabi cif! Lokaci ne da motar danliti ke fakin a kofar gidan uban dawaki,kai tsaya ya aiko yaro a kira masa mama,abba na nan a falo yana gadin zuwansa don haka yace da yaron yaje yace tana zuwa. Umma ta fito masa da kullin ledar kayan kwalamar da ya ba mama Abba ya karba ya bi bayan yaro kamar jiya,yau ma yana harde jikin motarsa yana kada mukullai sai dai yau kananan kaya ke jikinsa,gaba daya ya firgita kofar gidan da kamshin turare.Yana hango uban dawaki tilasa ya gyara tsayuwa yana 'yan kame kamen gulma ko kafin ya karaso ya tsugunna yana fadin,sannu alhaji,yace yauwa sannu,ya sake fadin ina wuni? Lafiya kalau,mike abin ka,magana zamu yi,ya mike a hankali yana sunkuyar da kai kamar muminin gaske.Abba yace magana guda daya ce nake so zan gaya maka danliti,'ya ta sakeena na riga nayi mata miji,tuni aka sa musu rana har ma lokacin ya kusan zuwa da yardar Allah sbda haka ina rokon ka da girman Allah kayi hakuri ka nemi wata,daga yau kar ka sake zuwa gun mama don tana da miji,ina fatan ka ji ni? Ya dan yi shiru jim kafin yace naji alhaji amma nima ina roqon arziki ka bar ni in rinka zuwa muna gaisawa,tnda ba'a daura ba.Wlh..."Abba ya katse shi,ba zai yiwu ba danliti domin koda babu alkawarin wani akan mama kai kanka ka sani zai yi wuya ka sami auranta,sanin kanka ne kaf garin nan babu wanda ya san tushenka,kaje kayi tunani mana.Ya saki baki yana kallon abba ran sa a bace,abba ya mika masa keda yace ungo nan,yasa hannu ya karba kafin ya cigaba da fadin,abubuwan daka bata ne dazu tunda ba auranka zata yi ba bai kamata ta amshi kayan ka ba.Don Allah kayi hakuri ka nemi daidai kai,sai da safe.Ya juya ya shige gida abinsa ya bar danliti a tsaye. )Ya kara harde kafafuwansa yana irin murmushin mugunta,sannan yace ko banzo ba ita zata zo wajena,koda kuwa kasheta zaku yi ta dawo.Dama ai zuwan nawa na hure kunne ne ba wai neman nake da gaske ba."Yayi er budurwar dariya ya bude motar sa ya shiga ya sake fadin,sai ni dan gidan buzu mai shayi taba ni kaga tsiya da bala'I!Ya ba mota wuta yaja ya bar harabar gidan hankalinsa kwance.Sabanin mama da take ji kamar ta saci jiki cikin daren nan taje wajen danliti shiyasa tayi ta leken falo,amma kash!Abba da umma sun ki tashi har dare yayi sosai suna tattauna zancenta.Daren nan bata yi barcin kirki ba sbda bakin cikin an hana ta fita ganin danliti.Gari ya waye ko alama umma ta ki sakar mata fuska,sam abin bai dameta ba Allah- Allah take yi kowa ya kama gabansa,itama ta samu ta sulale,ai kuwa abba na fita karfe goma umma ta gama abnda take yi,ta dare gado kamar yadda ta saba barcin safe,mama ta gama caba kwalliyarta ta sadada ta bar gidan.Ta kwarara sallama kofar shagon danliti,ya taso cike da fara'a yana amsawa kafin yace,a zatona ke ma zaki juya min baya ne,har na fara shiga damuwa,jiya sam ban yi barci ba.Ta dube shi cike da tausayi tace nima haka danliti ko gyangyadi ban runtsa ba,me zai sa na juya maka baya alhalin na san cewa nima zan cutu? Ya zura mata ido a marairece yace,abbanki ya nuna baya so na ban san yadda zanyi da rayuwata ba sakeena,kar ki bari ciwon zuciya ya kama ni.Kwalla suka taru cikin idanuwanta tace ka daina fadar wannan maganar don Allah,in ka ga na rabu da kai to sai dai su kashe ni in daina numfashi,zuciya ta kai take so kuma bana ra'ayin auran kowa face kai." Kwalla suka zubo bisa kuncinta.Da sauri ya tauko sabuwar tìshu kware ta ya yago ya miko mata,"share hawayenki, ki daina kuka.Na yarda dake sakeena,amma mece ce mafitar mu? Ta dan kada kai tace, "zanyi tunani,ka ban dan lokaci kadan,zan samo mana mafita.'ya daga kanta ya fito ya gyara zaman benci.Yace zauna kiji Ta zauna gefe shi ma ya zauna ya fuskanceta sosai yace,me zai hana ba zaki gaya musu ni kike so ynzu ba?Ta daga ido ta dube shi,jim,amma ba tace komai ba,yace "kar kiji tsoron komai kai tsaye ki gaya musu ke kin sauya ra'ayi ni kike so,za'a yi miki tilas ne?Dole a baki wanda kike so,don babu wanda zai zauna miki da shi,idan kuma kina son in rasa raina ne shikke nan........Ta kada kai tace,"nace ka daina fadar rasa rai danliti idan ka mutu nima mutuwar zan yi.Ka kwantar da hankalinka insha Allahu a yau zan gaya musu na sami sauyi wanda hankalina yafi kwanciya."Ya dafe kirji,ya lumshe ido yace,kin sa naji sanyi cikin raina sakeena.Ya bude ido ya bi ta da kallo ya cigaba,idan kika yi min haka kin gama min komai sarauniya ta,ba zan cika baki ba sai mun yi aure zaki ga tsantsar son da nake miki,bana jin akwai wata 'ya mace a fadin duniyar nana da zata sami irin gatan da zan nuna miki." Tayi dan murmushi tace,Allah ya nuna mana,yace amin.Ya dan gyara zama ya sake gadin,"wai sakeena kin san cewa kin fi kowa kyau a duniyar nan?Ta saki baki,ido waje tace,duk duniya? Wlh duk duniya babu mace mai kyau irin naki,ta kada kai tana murmushi tace,"ka daina fasa min kai danliti,ni na san ban kai ka ba,ya washe baki ya nuna kansa ya9e "ni kuma? A'a ni dai kike son ki fasawa kan,ina ni ina ke? kin gan ki kuwa?kin ga wannan dan bakin naki dagwas ba karamin kashe min jiki yake ba."Ta sunkuyar da kai tana 'yar dariya ya bita da kallo yana shafo habarsa."Mama!" Muryar kawai taji anyi mata wani gigitaccen kira,gaba dayan su suka kalli mai magana,ta bi shi da kallo babu tsoro ko wata fargaba tace,ah!yaya ali! saukar yaushe?"Ya kara tsuke fusk,yace me kike yi anan?"Tace me kuwa?Ba komai,taso muje gida,kaje ina zuwa,"ina wasa dake ne? nace ki taso mu wuce." "Ta dubi danliti suka hada ido yace,tashi ku tafi sai wani lokaci ko?Ta dan numfasa ta mike ta wuce,yaya alin dake tsaye,ya bi ta da sauri ya sameta,"mama,wai mafarki nake yi ko kuwa gaske ne?Ta yamutsa fuska "da aka yi me?" Zaune na gan ki kofar shago kina hira da wani...." 'Wani? Ba ka ma san danliti ba?"Shut up don Allah!waye danliti kike gaya min magana ba dadin ji?Hauka kika yi?Ina mutunci ga'ya mace tana hira da maza a kofar shago gaban jama'a? Ban san ki da wannan ba,yaushe kika canza mama? Ta ballo masa harara ta ja dogon tsaki ta kwahsi sauri ta wuce shi,shi ma ya biyo ta yana fadin,ban gane nufin ki ba?"Ta juyo ta dube shi tace,wai menene yaya ali?"Shi kike so?" 'Ai kaji,menene na sake tambaya? ya kara cika da mamaki,'Ban fa gane shi ki ke so ba mama.Ina Al-Ameen din?" Ido jajur! Ta dube shi,"kai ka san wannan sunan,don girman Allah ka kyale ni da tambayoyin nan." "Ba zan kyale ki ba Mama,hasali ma sai na gaya wasu Abba.Wannan ai zubar da mutunci ne da cin amana!Me ya tsone miki ido a wajen Dan-Liti?Ke ma kin shiga sahun 'yan matan da yake ruda da kyan sa ne?Kai na ya daure Mama.Allah yasa abinda na ke gani da ji ba gaskiya bane." Da gaske ne yaya Ali! Kuma ko baka gayawa su Abba ba,ni da kaina zan gaya musu."Ta zura da gudu ta bar shi tsaye, shakare da mamakinta.Kafin ya iso gida kansa,ya kusa fashewa sbd tunani da al'ajabi.Rokon Allah kawai yake yi Allah yasa mafarki yake yi. Kai tsaye sasan su Mama ya zarce.Suna tsakar falo umma ta tirke ta da tambaya,"Idan biki gaya min inda kika je ba sai na sumar dake yau a gidan nan!"Yayi sallama.Umma bata iya amsawa ba,sbd bacin ran da take tare dashi.Ya-ce,'yanzu na koro ta daga shagon Dan-Lati suna zaune bisa benci suna hira Umma.Yaushe Mama ta sauya haka? Tuni Umma ke sallallami,ta dafe kirji ta-ce "shagon Dan-Lati ki ka koma Mama?Mu kike so ki zubarwa mutunci a garin nan? Ai kuwa baki isa ba,ba ki isa ba Mama!'Ji ka ke tim! Ta rufe ta da duka ta ko'ina.kafin yaya Ali ya kawo mata dauki,ta sha dan banzan duka.Kukan ta ya watsu cikin sassa,matan gidan da kananan yara suka sheko don ganin meke faruwa?Al'amarin ya daure masu kai,ganin Mama na birgima tsakar falo tana ture hannayen Yaya Ali dake kokarin rarrashinta [11/01 19:21] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 2***2(TRUE LIFE STORY) Wa ya mutu Ali? "suka tambaya,yayin da umma ta fito daga daki dauke da wayar rediyo kafin su yi aune,ta fara tsula mata.Haba gaba daya matan suka cafke hannun Umma, 'Hajiya Halima! Lafiya wannan abu haka?Me ta yi da zafi irin wannan duka?" Umma na haki tace wai yarinyar nan ita ce zata siyar mana da mutunci? Ta rasa wanda zata tsaya da shi, sai Dan-Liti? "Dan-Liti? Waye Dan- Liti?"Dan gidan Buzu mai shayi mana! Yau kwana uku kenan muna fama da ita ta rabu da yaron nan,ta ki! Jiya yazo kofar gidan nan.Alhaji da kansa ya same shi ya gaya masa tana da rana a kanta.shine don dibar albarka ta bi shi shagon sa,yanzu Ali ya ganta ya koro ta! Wace irin tijara ce wannan sbd Allah! Tuni suke kallon juna suna tafa hannu,hajiya hajo tace "danliti kuma?Waye bai san tarihin su ba a garin nan?Yaron da tun tasowar sa garin nan basu da aiki sai bata 'ya'yan mutane koda baki da wayau sosai ai kin yi dan hankalin da zaki gane buzu mai shayi kasurgumin kwarto ne,shi kuwa danliti kananan yara sau nawa ana kama shi dasu?Ko kin mance ranar da dubu ta cika suka ci shegen duka.Danliti ya sha da kyar shi kuwa buzu ya shura barzahi?Me ya dawo da shi kike kwadayi da har idon ki ya rufe kika kasa duban kazantar dake tare dashi?Hajiya Gaje tace "duk ba ma wannan ba kina nufin zaki fasa auran Al-ameen ne?Umma tace,karya take yi sai dai bayan ran mu,bari kuma alhajin ya dawo,yau din nan zai maida ta minna tnda zaman naki anan abinda ya haifar kenan!Ta tashi da gudu ta fada dakinta har da danna sakata ta bar su nan suna maida yadda aka yi. Shi dai yaya ali tunda ya sunkuci jakar sa ya fada dakin mahaifiyarsa bai sake kyakkyawan motsi ba sai tsabar tunani.Muryar mahaifiyarsa yaji a kansa tana fadin,"kai kuma yaushe ka shigo garin?"Firgigi ya dube ta na'am!"Ta zura masa ido,nace yaushe kazo?Ya sauke gwauron numfashi yace,"zuwa na kenan inna".ciwon daya sami mama,ai ya same ni domin jinin mu daya......"Gafara can sakarai kai ka san wannan,da su ma sun san cewa jinin ku daya ba'a hana ka auranta ba ai sbda haka ban ga dalilin dogon tunanin da kake yi ba,don daga ita har iyayenta basu san ka na yi ba!Gara tun wuri ka halkantu ka gane cewar alhakinku ne ya kamasu!Idan ba haka ba,ina mama,ina danliti? Marasa asali da tushe ga tarin abin gori da na kunya a jikin sa?"Ya dafe goshi idanuwansa suka kara kadawa,yayi hucin zafi ya dubeta,"duk wannan maganar bata taso ba inna abinda nake so ki gane shine muddin mutuncin mama ya zube,to martabar gidan nan gaba daya ta fadi,ashe kuwa dole in damu tnda nima dan gidan nan ne,ga shi kuma mama ta dauko hanyar bada mana kasa a ido. Tace can dai zata badawa iyayenta masu kwadayi,ban sa aka ba balle ya dameni wahalar banza kake yi dama ruwa da abinci ka samu ka ci,daya fiye maka wannan sakarcin!Ya sake dafe goshi yana kada kai,me yasa innar sa baza ta gane ba?Takaici ya kara kama shi ya sunkuci jakarsa ya koma dakinsu.Haj Gaje ta shigo saboda gulma ta cigaba,sharri kala kala suka yi ta jifar uban dawaki da su.La'asar sakaliya abba ya dawo gida ya iske idanuwan umma sun jirkita jajur!Ga kumburi sun yi,ko bai tambaya ba ya tabbatar akwai abinda ke damun ta,don haka ya kasa cin abincin data kawo masa,ya zura mata ido yace kamar akwai abinda ke damunki sadiya? Tace akwai matsala alhaji amma ka ci abincin sai mu san abin yi."Fuska ki ta bayyana tashin hankali dake tare da ke ban jin abincin nan zai iya wuce min ba tare da naji damuwae ki ba.Gaya min uwargida,ni kadai gareki wanda zai saurari kukan ki."Ta dan yi murmushi karfin hali tace mama zata siyar da mutuncin mu a garin nan gara ka dauketa ka maida minna ko abj ta zauna can har zuwa lokacin bikinta."Gaban sa ya fadi yace,me tayi?Bata daina zuwa shagon yaron nan ba,yau ali da kan sa ya koro ta tana zaune bisa benci suna hira,benci fa a kofar shagon bakin titi?Kamar mama yadda muke a garin nan take zama tare da danliti?Ta goge kwalla,ina zan sa BAKIN CIKI Alh,anya kuwa mama ce ke aikata wannan abu?Hankalin alh yayi mummunan tashi ya fuskanci umma da kyau ya sanyaya murya yace,ki daina zubda mata hawaye halima ke mahaifyarta ce,sai abin ya kara wargaje mata......" "Ba yin kai na bane alhaji,hawayen ke tilasta wa kansa zubowa."Yace duk da haka ki rinka daurewa kina mata addu'a,insha Allahu gobe zan maidata minna ko ta ki ko ta so dole ta zauna.Ni abinda ban gane ba shine,tana nufin ta fasa auran Al-ameen ne?Idan wani abu yayi mata ai sai tayi bayani,ba wai ta nemi ta maida mutane sakarkaru ba!Ina take ne?"Tace tana daki a kulle tun safe daya koro ta,haushi yasa nayi mata duka har ynzu bata fito ba."Ya mike cikin fushi ya nufi dakin ya buga da karfi yana fadin,"tashi ki bude kofar nan!"Tana budewa ya cafko hannunta ya jawo ta zuwa falonsa,hakan ya sanya mama cigaba da tsiyayar hawaye,ya cillata tsakar dakin ta zube gefen ummanta.Ya zura mata ido yace,"ashe wani lokaci zai zo da zamu ce ki bar abu ki ki bari mama?Kin dai san maganara auren ki da al-ameen ko?To ynzu nake so ki gaya min manufarki ta bin danliti shagonsa.Gaya min inji tun kafin mu tara 'yan kallo!Tayi kasa da kai kukan ta ya karu.Abba ya daka mata tsawa,"kuka na tambaye ki? Ki gaya min dalilin bin sakaran yaron nan nace?Ta cigaba da share kwalla tana mutsu mutsun rashin gaskia,leben ta na makyarkyata tace,"shi....shi na ke......na..na...ke so ab...."Umma ce ra doke ta da bayan hannu tace rufe mana baki mara kunya!"Ta dubi abba dake tsaye sake da baki tace,"ka ji ko?Ni na san take-taken ta kenan!"Ya matso ya cafki kunnenta cikin tsawa yake magana."Idan barci kike yi to ki farka ki bude kunnuwanki da kyau ki saurare ni! Ni ba tsohon banza bane,in har kin ga ki auri yaron nan,tabbaci hakika ni uwaisu na mutu an binne ni cikin kabari na! Ya girgiza kunnen kamar zai tuge shi,kin ji ni! Wannan itace magana ta karshe da zanyi akan danliti kuma gobe ki shirya kayanki zan maida ki minna!"Ya shirga mata dundu tare da fadin,"tashi ki bani wuri!Ai bata iya tashi ba nan ta baje ruf da ciki sbda tsananin zafin dundun da yayi mata abnda bata saba ba,sai ta ji shi har cikin kayan cikinta sun dau zafi ba kadan ba,Ta fasa kara mai shiga zuciya tace wayyo Allah na shiga uku! Na shiga uku!Yaya ali ya mike a firgice,gabansa ya yanke ya fadi ya fito da sauri yana tsinkayar kukan mama,ya nufi sasa.Umman ke fadin,'ba ki shiga uku ba mama sai nan gaba muddin baki dauki nashihar da muke yi miki ba!"Hannu biyu yaya ali yasa ya ciccibe ta ya mikar da ita,zafin duka da tsananin BAKIN CIKI dake dankare cikin ran ta yasa ta kwakume.Yaya ali bakin gado ya zaunar da ita ya dago fuskar ta hannu biyu yake share hawayenta,yayin da nasa kwallan ke neman sauka,yace "haba mama ki yiwa kan ki fada mana!"Murya na rawa tace,me nayi masu yaya ali!Sbda Allah me nayi?"Me kika yi? ynzu a wajen ki wannan ba laifi bane?Haba mama!Ba haka kike ba,kin sauya da yawa kar dadin bakin danliti yasa hankalin ki ya gushe,laifin me al- ameen yayi miki kike so ki yi masa wannan sakayyar?A zato na koda babu Al-ameen nine mutum na farko daya kamata ki fara kawowa ran ki don na dade ina yawo da ciwon son ki mama.Ki tausaya mana me zai sa ki canza kyawawan halayen ki? Ya Girgiza kunnen kamar zai tuge shi. Kin ji ni! Wannan itace maagana ta karshe da xanyi akan Dan-liti, kuma gobe ki shirya kayan ki, zan maida ki bani wuri. Ai bata iya tashi ba, nan ta baje ruf da ciki, saboda tsanannin xafin dundun da yayi mata. Abinda bata saba ba, sai taji shi cikin kayan cikinta sun dau xafi ba kadan ba. Ta fasa kara mai shiga xuciya. Tace wayyo Allah na shiga uku! Na shiga Uku! Yaya Ali ya mike a afirgice, gabansa ya yanke ya fadi, ya fito da sauri yana tsinkayar kukan mama, ya nufi sasan. Umma ke fadin baki shiga uku ba Mama, sai nan gaba muddin baki dauki nasihar da mukeyi ba miki ba! Hannu biyu Ya Ali ya sa ya ciccibeta ya mikar da ita, xafin duka da tsananin BAKIN CIKI da ke dankare cikin ranta ya sa ta kwakume Ya Ali. Bakin gado ya xaunar da ita ya dago fuskar ta hannu biyu yake share hawayen ta, yayin da nasa kwallan ke neman sauka. Yace, haba mama kiyi wa kanki fada mna! Murya na rawa tace, me nayi musu Ya Ali? Saboda Allah me na yi? Me kikayi? Yanxu a wajenki wannan ba laifi bane? Haba mama! Ba haka kike ba, kin sauya da yawa kar dadin bakin Danliti ysa hankalinki ya gushe. Laifin me Al-ameen yayi miki, kike son ki masa wannan sakayyar? A xato na koda babu a alameen, ni ne mutum na farko daya kamata ki fara dawowa ranki, don na dade ina yawo da ciwon sonki Mama, ki tausaya mana, zai sa ki canja halayenki? Ta xuba masa kwala- kwalan idanuwanta da suka kara fitowa waje jajur! Tace, Yaya Ali ina ganin girman ka, ka kyale ni da wadannan surutan, don ba xa suyi tasiri ba. Ni nace ina so Al-ameen, yanxun kuma bana son shi Danlilti nake so. Ra'aryi nane, ba sai a kyale ni ba, ko akwai wanda zai zauna min da shi? Ya bita da kallo, ta sa aya kafin yace, ki daina tunanin wannan ra'ayin na ki mai yuwuwa ne, kin dauko katon aikin da xai rushe martabar gidan nan a idon jama'a. Idan baki son Al- ameen, ki musanya da ni Mama, zai fi miki kyau a bisa shirmen da kie sonyi. Ta runtse ido tace, yaya Ali je ka kawai! Ba ki son gaskiyya? Ta kauda kai kwalla na tsiyaya. Ya sanya murya yace, xan bar ki ki kwanta kiyi tunani sosai, cikin kan ki. Ina rokon ki girma da Allah, ki manta da kudirin da kika dauko. Bata tanka ba, haka bata dube shi ba yace, A bakin tofa ya tsaya ya kare mata kallo kafin ya sake fadin, bana so ana taba jikin ki mama, tamkar ni ake tabawa nakeji. Pls ki sauya tunaninki. Haushi ya kara kuma ta, ta juya masa baya. Ya fice yana kara waigen ta. A daren nan daga ita har Yaya Ali babu wanda ya iya cin abincin balle barci. Tunanin Mama shine xata ga yadda za'ayi a raba ta da garin nan. Cikn xuciyar ta tasha alwashin ko sun maida ta, zata dawo, dole su gaji su kyale ta da wanda take so. Dalilin da yasa ke nan, yau kwata-kwata taki bude kofar ta, kowa yayi bugu, iyayinsa har kawunninta, sai dai kalaman bakin su suka kare. Amma mama taki bude kofarta. Duk wanda ka duba ransa bace yake, musamman Abba, fuska kamar gobara ya dubi Umma yace, dauko min tabarya! Ta mike a salube ta shiga kicin ta dauko masa tabarya, ta mika masa. Alh basiru yayi caraf! Ya karba. Yace karka balle kofar nan yaya, asara biyu xa'ayi..... Yace yarinyar nan dole ta bar garin nan, ba xata xauna tana jawo min xagi ba, ana kallo na tsahon banza, bansan abinda nake yi ba! Buge min kofar nan, ko ka ba ni da kaina, in sauketa! Kowa yayi cirko-cirko. Alh. Basiru ya kai wa kofa duka da tabarya, sai ga sallamar Yaya abdul- kareem. Basu gama amswa ba, yaci gaba da tambaya, lfya? Me ya faru da kofar? Abba yace, nayi farin cikin xuwanka, don ni ma a yau nayi niyyar tafiya gunka. Me ya faru abba? Umma ya naga kamar kina kuka? Yace, mama ce.... Me ya sameta? Ya kwashe kaf halin da suke ciki ya gaya masa. Kai! Bai gaskanta kunnuwansa ba, shi yasa yace, abba ban yarda da wannan maganar ba, ya kamata asake bincikawa. Abba ya xuba masa ido jajur! Yace, wannan maganar ni Uwaisu nake gaya maka ita. Abdul kareem kasan kuwa ba za ayiwa mama kage ba, domin ni na haifeta. Saboda haka gidan ka xata xauna can har xuwa lokacin bikinta! Yace, ya xama wajibi, don ganin nan da kuka yi min xuwa nayi in tafi da ita dama. Al'ameen ya damu kwarai har yana ganin kamar wani abu ne ya faru da ita ake boye masa. Wlh jiya ya turo mahaifiyarsa da yamma wai ta zo ta bincika masa lfiyar mama, shine nace shi kwantar da hankalinsu Insha Allah da kaina xanje in dawo da ita. Wannan al'amari ya daure min kai. Yaushe mama ta canza haka? Kawu Basiru yave xancan banza takeyi, tunda ita ta kawo Al'ameen har aka sanya musu rana, bata isa tace ta canza shi ba! Wannan karya take yi. Haushi ya kara kure yayanta, ya mike ya suer tabarya ya kaiwwa kofar duka sau biyu kofar ta balle, bata a dakin. Ya nufi kofar bayi ya murda can ma garkamen yake, bai tsaya wata-wata ba, ya maka mata tabarya. Bugu daya kofar ta wangem, sai ga mama jikin bango ta fita hayyacinta saboda tsabar kuka. Al'amarin tamakar mafarki yayana yake gani. Ya xura mata ido, yace hauka kikayi mama! Me Al-ameem yayi miki? Iye? Yayi miki laifi ne da ba zaki fada ba! Sannan ki rasa wanda zaki bi, sai dan liti! Kinji abinda nace? Kin yi karya ki xuabar mana da mutunci a garin nan! Zo mu wuce, ban son jin komai daga gareki! Ta sulale kasa hannaye biyu bisa kanta, ta kara fasa kuka mai tsananin gaske. Matan gidan suka kutso kai cikin bayain suka tarairayo ta, suka fito da ita dakin. Yaya yana fadin ko mutuwa zakiyi yau, sai na tafi dake mu je can idan Al-ameen ya kira waya, in tambayehsi a gabanki, muji abinda ya hadaku! Amma yaro na sonki yana tattalinki. Iyayeynsa na ririta ki, tashi guda kice ba kiyi da shi, aikin san wannan karya kikeyi. Ina kayan ta suke umma? Hada mata si don baxan bata lokaci ba! Gaba daya suka yanyame ta da fada kowa na fadin albarkacin bakinsa, su Umma na hada mata kaya. Su Hajiya Hajjo na rarrashi ta suna bata baki tare da gyara mata jiki da fuska. Yaya Ali kuwa yana xaune gefe rayuwa tayi masa bakikkirin! Ana janta, tana togewa suka saka ta gabn motar yayanta. Ya jefa jakar ta gidan baya, daga nan yayi sallama ransa bace, ya ja motar yayi gaba da mama. Dole ne ya saurar daidai shagon Danliti, domin akan mahada shagon yake. Tsayuwar su wajen, ya jawo hankalin Danliti xuwa garesu. Ya xuba wa Mama idanuwan sa suka sha kwalli rangadau! Haka ita take kallonsa kwalla fal! Suna neman sauka. Ya daga kanka ta fito kofar shagon, irin duban da yake mata ya bayyanar da damuwarsa karara bisa fuskarsa. Tausayinsa ya lullubeta, nan da nan hawayen suka fara bulbula. Yayanta bai kula ba, kokarin sa, duk motocin da suka kawo, suka wuce shima ya samu ya haura. Yawanci duk manyan motoci ne, kamar yadda akansan babban titi ne, wanda ya mike ya tafi har lagos. Suna tsagaitawa ya cilla tasa motar ba tare da ya fahimci Danliti da mama sun ruga sun gama magana da idanuwansu ba. Kawai ji yayi ta kara gocewa da kuka mai karfi. Ya dan dubeta, ya kada kai. Yace, Al'amarin ki na bani mamaki, look kina jina? Saurare ni muyi magana ta fahimta. In tambayeki xaki bani amsa? Hankalinta sam ba awajen sa yake ba, balle ta saurare shi. Fuskar Danliti take gani, irin yadda ya shifa damuwa yana neman xubar da hawayensa, shi ya kara dagula mata lissafinta. Yace, saboda Allah zaki gaya min Al- ameen yayi miki da zaki juya masa baya? Tayi shiru, danliti na cigaba da yawo a idonta. Yace, kin kuwa san tun ranar da kika dawo garin nan. Al-ameen ya rasa nutsuwarsa? Ban iya kirga yawon wayoyinsa ba, tunaninsa kina cikin wani matsanancin hali ne aka boye masa. Kar ki saki reshe ki kama ganye Mama, domin kowa yasan Danliti lalata rayuwar ki kawai zai yi, ya kai ki ya baro ki tashar danasani. Ki ga ya min idan Al- ameen yayi miki laifi ne, ni da kaina xan masa magana in ja masa kunne. Kinji? Bai yi aune ba yaga ta balle murfin motar ta dire waje. Ta mulmula cikin ciyayi. Cikn tashin hankali ya take birki.... Allah yasa ba babu mota a bayansa, yayi fakin gefen titi, ya fito. Can ya hange ta tana kokarin tashi, amma ta kasa, kafin ya gangara wajen 'yan tsirarrun jama'ar wajen sunyi caa! Kanta. Suka ciccibota, suna sallalami tare da mamakin yadda aka yi abin ya faru. Gaba daya gwiwowin ta sunyi mugun kurjewa ta xura da gudu amma bata je ko'ina ba mutane suka cafke masa ita. BAKIN CIKI yasa ya dauke da wani mahaukacin mari daya tilasta mata xubewa kasa. Wani dan dattijo cikinsu ya kama shi. Yace, haba malam yaya haka kuma? Baka ganin kaddarar da ta sameta? Da ta mutu fa? Ku rinka kulawa da murafen mota mana don gudun irin hakan! Idanuwan sa ajuye yake magana, kyaleni da yarinyar nan baba! Da kanta ta bude murfin ta fito! Iskanci ne kawai, dama kin mutu, mu huta da wannan BAKIN CIKIN da kike son jefa mu! Saboda haka xan koma in gayawa abba kin bude mota ki diro, ni kuma ba xan tafi dake ba, ki xauna kiyi duk abinda kika ga dama agarin nan, tunda lalacewa kika xaba. Allah ya shirye ki! Ya shura takalmansa ya koma mota ya tayar yayi kwana ya koma gida ya bar Mama anan tana faman kuka, jama'ar dake wajen suna mamakin wannan abu har sun kasa fassara shi. Dan dattijon nan shi ya riko ta hankali suna tafe tana bashi labarin wai

Chapter 9 of 28