Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zura mata ido dauke da murmushi mai isar da sako barkatai. A nutse ta bude fuskarta ta dubeshi "sannu da zuwa" taushin muryarta yasa jinin jikinsa ya tsinke yaji son Mama ya kara malale kowane lungu cikin zuciyarsa tamkar ya hadiyeta yakeji kai bai tabajin azababben so irin wanda ya kama hsi ba, ya numfasa yace gimbiya ta kenan. An fito lfy? Tace kalau ya hanya? Yasu Baba sukaje gida? Ya amsa duka lfy lau, tace mungide Allah. Yanzu ka ban minti daya zan bude maka inda zaka zauna, yace ni kadai? Gsky ban yarda ba! Tayi dan murmushi to inda zamu zauna. Yauwa yanzu naji batu gara da kika gyara. Ta wuce tana 'yar drya. Shi kuma yayi wawan ajiyar zcya, ya dawo jkn motrsa ya harde. Jimawa kadan ta budo babban kofar get da ke can wani bangare na katangar gidan, ta fito tace dashi, "bismillah!". Bai yarda ta tsere masa ba, jerawa suka yi suna tafe yana fadin, "ga Amarya ga Ango!". Ta ballo masa harara, fuskarta kunshe da kyakkawan murmushi, har suka shige falon. Ta nuna masa kujera ya zauna, ita ma ta koma gefen damarsa ta zauna, suka sake gaisawa. Yace, "to Alhamdu lillah, godiya ta tabbata ga Allah wnda ya nufi al'ameen ya zama angon sakeena. Ko kinsan cewa jiya banyi barcin kirki ba?". Ta kada kai, "me yasa?" "ban taba zaton abba zai saurari kukana ba, shi yasa na kasance tamkar maraya, ni kadai cikn daki, bana aikn komai sai na addu'a, idanuwan nan sun fidda hawaye gaban Ubangiji don neman biyan bukata. Beliete me ma jinina ya hau kfn dady ya dawo......." ta katse shi, "amma da ya dawo fa?" yace, "albishir din da ya dawo min dashi ya hana min barci sbd tsabar murna da farin ciki, cnt explain sakeena" tace, "ka mamayi abba, kuma ni kaina nayi mamakin amincewarsa, koda yake abba mai saukn kai ne, kuma bai cika jayayya ckn al'amarn rayuwa ba" "na yarda da ke. allah ya sakawa abba da alkhairi, domin ya ceci rayuwata. Ko har da taki?" Ta dube shi suka hada ido, ta dan kauda kai. Tayi 'yar drya. Yace, "ban damu ba, tnda ni nayi nasara". Tace, "ni kuma bazan yarda da kai ba, sai naga alkawari na". Ya zuro mata ido, "a tunaninki zan manta ne? No sakeena, kece komai nawa, bazan taba mantawa da wani abu wnda ke alaka da ke ba, balle kuma ace alkawari ne......," Ya tura hannu aljihu ya dauko wani dan karamin mazubi ya bude, ya nuno mata wani gangariyan zoben zinari yace, "ina jin wannan shine alkawarin ko?" Baknta yaki rufuwa, ya matso gabnta ya tsugunna ya miko mata, tasa hannu ta dauka ta zurawa yatsanta. Wayyo! Al'ameen zuru kawai yayi yana kalln zara-zaran yatsnta, zoben nan ya zauna kamar da shi aka halicce ta. "tsarki ya tabbata ga Ubangijn da ya halicce ki sakeena". Ya dago ido ya dubeta, "kiyi min alkawari har abada ba zaki daina sona ba". Tace, "insha Allahu zaka sameni mai cika alkawari komai wuya, komai tsanani zan jure akan alkawarinka. Har abada kai kadai ne, ba wani sai kai" Idanuwnsa suka kawo kwalla, murya sanyaye yace, "na gode sakeena" tace, "kar ka damu". Ya mika mata gidan zoben ta karba. Ya koma mazauninsa ya zauna, abba ya gaya wa dadyna kema irin karatu zaki yi, kinga ta kwana gidan sauki, wai matar likita ta haifi panadol" Ta fara drya, "oh, drya na baki ko? To shikenan, ai ba ke matar likitan zaki haifi panadol din ba........" tace, "au son kai ne abin?" "eh mana. Nawa bouncing baby ne, baby boy ko girl? Zabar min". Ta mako masa harara, ya hau drya. "well, daga nan idan na tashi zariya zan wuce, sai kuma nxt week zan dawo in sake ganin gimbiyata" tace, "Allah ya kaimu lfya, nima anjiman zan wuce minna wajn yayana zanyi hutu" Ya bude ido, "owk, kuma shine tnda nazo baki gaya min ba, ai sai in juya in kaiki, daga can in wuce". Ta kada kai, "bana son ka wahala, ka wuce wurin aiki abinka. Babu komai". Yace, "uhm...... To na gode, amma ina fatan akwai phon number a can, kin ga sai mu rika gaisawa ko?" tace, "eh akwai land- line zan baka" Yayi ajiyar zuciya, sannan yace, "yanzu ki bani labari, ku nawa ne a daknku?" tace, "mu hudu, yaya abdul-kadeer soja, shine babba, sai yaya abdul-kareem yana CBN Minna, shine zani hutu gunsa, then yaya Abdul- rahman yana kadna, lst year ya fara aiki da ma'aikatar kimiyya da fasaha ta jiha, shi kadai ne bai yi aure ba......" "sai kuma ke ko?". Tayi 'yar dryar nan da yake so. Yace, "kun burgeni, Abdul 3, ni kuwa tilo ne ckn gdnmu, bani da yaya balle kani. Kadaicn yayi min yawa sakeena". Tace, "kamar ynda gata yayi maka yawa ba" "haka kike gani? No ba zaki gane ba, naso ace akwai wasu, musamman kanne, na rika yi musu 'yan mazurai ina cewa, kai ku bari mana! You knw, smthn like that dai. Amma ka zauna shiru babu mai maka fada, babu wnda zaka yi wa? Babu dadi abin". Ckn tausayi tace, "ai shirin na Allah ne" yace, "yes haka ne, na yarda. Amma very soon zan samu many babies, su zagayeni, dady kalla! Dady bani wannan! Dady sa min riga! Kin gane? Ina son hayaniyar yara sosai" Tana drya tace, "kana da aiki" "come on, muna da aiki dai. Ai mu biyu ne muna tsakhya, sun zagaye mu, na 6 can 6. Wuu! Confusion! Wa zai gane min ke?" Hannunta tallafe da kunci, ta zuba masa ido tana kallnsa yana ta zuba bayani, idanuwanta suna nuna mata yaran zagaye da shi. Shi yasa yana sa aya ta fashe da drya. Yace, "drya ma na baki ko? Yarnya gudu zanyi in kyaleki dasu" Ta dan tabe baki, ta tashi tsam! Zata bar falon, yace "ina za ki? Har kinji tsoro ne?" tace, "tsorn me? Ruwa zan kawo maka, kaji dadin santin". Sosai yayi drya, har ta bar falon. Ya koma a hnkali ya jingina bayansa da kujera, ya rufe ido tamkar mai barci. Wani kasaitaccen taro yake hangowa, wnda cikarsa baya misaltuwa. Jimawa kadan ya keto taron rike da hannun sakeenarsa, da ka dube su kaga amarya da ango. Jama'a na musu tafi, su kuwa baki yaki rufuwa. Bisa wasu kasaitattun kujeru suka zauna, ta tsiyaya lemu a kofi ta mika masa a baki, ya dauka zai fara sha...... "Assalamu alaikum!". Ya bude ido a hnkali, tana tsugunne gabansa rike da kofin ruwa. "barci kayi? Lallai na dade da yawa, ayi min afuwa". Ya saki wani wawan numfashi, ya girgiza kai, "dogon tunani ne ya dauke ni. A duniya bani da wani burin da ya wuce aurenki sakeena.....". Yayi dan shiru jim! Yana kallnta, ya kada kai, sannan ya karbi kofin hannunta, "na gode". Ya shanye ruwan, ta zuba masa lemu, ta koma ta zauna, ilahirin jiknta ya mutu. Wane irn so al'ameen ke mata? Ta tambayi kanta. Tana ganin ita ma irnsa take yi masa, domin itama burinta ta zama mata a gareshi. Ko don ita kunya na maida ita kurma, shi yasa yake ganin shi kadai ke da buri a kanta? Zurun da tayi masa a rashn sani, shi ya jawo hnkalnsa ya daina kurbar lemun. Ya matso gabnta yasa mata kofn a baknta, ta sha kadan ta dube shi, "ba kai kadai ke da buri ba Dr., sanin kanka ne mu duka muna da bukatar kasncewa tare. Idan baka sani, ynzu na gaya maka ka sani, don ka daina damuwa". Ya numfasa yace, "Allah ya tabbatar mana da wannan buri" tace, "amin". A natse suka zauna suka ci gaba da faranta wa junansu rai da dad'ad'an kalamai. A nan yayi sallar azahar, ya ci abnci, sannan yayi shirn wucewa zrya. Ita ta jagorance shi ya shiga ya gaida umma, don ya matsa kwarai yana son kai mata gaisuwa. Ta kuwa ji dadi, ta kuma yaba da tarbiyyar sa, yanaynsa da alkunyar sa.! Suna tsaye jikin motarsa sallama taki karewa Ya Ali ya danno kofar gidan da jakarsa akafada, bakinta har kunne ta tarbeshi Ya Ali! Sannu da zuwa, ya kalleta ya kalli wanda take tsaye dashi kafin ya amsa. Ya mikawa bako hannu tare da sallama (Allah Sarki ubana akwai jarumta!). Ita kuma tana fadin Ya Aliyu kenan cosin dina ne, Allah sarki inji Al-Ameen an dawo lfy? Yace lfy lau! To madalla. Aliyu yace dauke da matsanancin kishi da mamaki a ransa. Al-Ameen kuwa fadi yake kuna satar kama da juna da an ganshi an ga dan'uwanki, tace ko? To ai da Baban shi da Abba duk dakinsu daya. A Birnin gwari yake aiki. That's gud' ina ganin ya kamata in lallaba in barki ku wuce ko? Kar dare yayi. Tace hakane, kai din ma bana son dare yayi maka. To shikenan karfe tara ISA zakiji wayata. Allah ya yarda a sauka lfy. Ameen. Ya shiga mota ta rufe masa tana kara fadin kayi tuki a hankali, yace thank U. Ta juya zata wuce yayai kiranta Skaeena! Ta juyo tare da murmushi yace "I love you!" Ta kara fadada murmushinta ta rausaya kai ta juya zata wuce Sakeena! Ta sake juyowa. I love u! Tayi jim kafin tace I love U too! Ta ruga cikin gida ya rakata da kallo bakinsa kamar gonar auduga kasala ta rufe ya kasa tada motar. Ta sake lekowa tayi masa bye-bye shima ya daga mata hannu sannan ya sami karfin tada motar yayi ribas yai kwana ya fada hanya ya kara dago mata hannu ya wuce cike da begenta tamkar yadda takeji a ranta. Tana shiga cikin gida muryar Ya Ali kawai ke tashi yana bambamin fada "ai dama haka rayuwa take kiri'kiri jininka saiya wulakantaka don baka da kudi! Muma muna kan hanya indai arzikine abuna Allah! (Kana da gsky Baffaba!) Mama tayi tsaye jikin kofar sassansu tana saurare haj Hajjo tace nace dai kayi shiru haka ko? To kaci gaba idan hakan shi zai sa a baka ita. Mama dai ba saurana mata tafi ba ga yanmata nan bila adadin duk wacce ka zaba sonka zatayi idan ita ma ba kwadayi tasa wa ranta ba. Sbd haka kar in sake jin wata magana ta fito daga bakinka akan wata Mama! [11/01 12:51] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 1****5 H. Gaje ta cafe, "ki kyale shi ya amayar da bacin ransa, kar ya zame masa ciwo! Da wanne zai ji?" yace, "ai inna ba zata gane ba mama gaje, wannan rainin arziki ne a ckn gida. Uwa daya uba daya? Haba! Ya kamata a duba!". H. Hajo tace, "wa zai duba? Lallai ranka zai fita idan har zaka kwallafa wa kanka wannan maganar!" Tana sa aya daidai da sallamar uban dawaki, yayi tsaye yana kalln mama na zubda kwalla, yaynda yaji muryar h. Gaje na fadin, "babu wnda zai duba wannan al'amari, tnda dai shi da kansa alh. Babban ya ya yamutsa al'amarin!". Kalaman da suka fada kunnuwan uban dawaki tare da bugun zcy, ya zurawa mama ido tamkar ynda take kallnsa, "me ke faruwa?". Bai gama rufe baki ba yaga Ali ya fito a fusace, idanuwnsa na tsatso kwalla. Shi kansa gabnsa yayi mugun faduwa, kasala ta kama shi, ya rage sauri, "kai ali lfy?". Ya gnge fuska, ya dan rankwafa yace, "sannu abba!" "nace me ya faru?" "babu komai" "ina wasa da kai ne? Kake gaya min babu komai!". Mama tace, "abba tun jiya gidan nan a yamutse yake, ana ta habaici tare da yada magana akan zancen al'ameen. Umma taki gaya maka ne sbd gudun fitina. Amma kowa gani yake yi sbd kudi ne yasa ka amince inyi aure, bayn ka hana kowa kace karatu zanyi. Me yasa za'ayi mana mugun zato?" Nan da nan ransa ya baci, yayi fushi sosai, ya kwalawa umma kira. Ta fito ta samesu ransa bace. Ckn fushi yace, "kira min matan gidan nan!" "lfya alh?" yace, "ban son jin wata magana". Tace, "alh ka kwntar da hnkalnka kayi hakuri har zuwa lokcn da mazajnsu zasu dawo. Zai fi kyau duk abnda zaka fadi ka fada a gabnsu. Ina rokn wannan alfarmar don girmn Allah!". Alh. yayi jim! Shiru yana kalln umma, kafn ya dubi mama yace, "kin shirya kayanki?" tace, "eh" "to kwaso ki zuba a mota maza mu tafi". Ya wuce da sauri daknsa, kowa ya kama gabnsa, har da ali ba tare da wani ya kara cewa komai ba. Kayn jiknsa kawai uban dawaki ya canza, yayi rawani kamar ynda ya saba, ya fito lokacn mama na tsakar gida da jakar kaynta tare da tsarabar da umma ta bayar a kaiwa yara. "Baki kai kayan motar ba?" inji abba. Tace, "ai basu da yawa, su kenan" "wuce muje". Umma tace, "Allah ya tsare, a sauka lfya". Ya amsa da amin, yayi waje. Mama ta biyo baynsa. Ali na zaune bisa dakali tmkar yayi bindiga sbd tsabar fushi da kishi, domin sosai yake son mama. Kuma yayi wa ransa alkawari zai ci gaba da farautarta, sai yaga abnda ya turewa buzu nad'i. Shi yasa ya aje wa ransa zai iya jiran ta gama karatnta. Shi kuma zai ci gaba da gina kansa da duk wani tanadi wnda zaizo daidai da jin dadin rayuwr aurnsu. Ina zai sa ransa yau yaji dadi? Yana ganin mama ta shige mota idanuwnsa suka yo tam! da hawaye. Musamman wannan zuwan ita yazo gani, sanin cewa sunyi hutu. Kamar ya kwarma ihu. Ya mike ya sake fadawa ckn gida. Alh. Ya bude mota, kalla ya matso, "ranka ya dade tfya za kuyi?" yace, "ai tare zamu tafi da kai, taso ka shiga mota. Minna zan kai mama na" yace, "to shi kenan". Ya mika masa makulli, "ka tuka motar kalla, bana jin dadin jiki na". Ya amsa yana fadin, "assha! Allah ya sauwake" "amin". Ya bude gidan baya inda mama take, shima ya shiga. Jikn mama ya kara sanyi, tasan abbanta ya kanso suyi tfya su 2 kacal! Suna tafe yana bata labarin duniya. Ta tabbata bacin rai ne yasa ya gayyato kalla ya tuka su, gudun afkuwar wani abu. Sun mika tfya shi babu mai magana, shirun sam baya mata dadi, sbd haka tace, "Abbana kayi hakuri don girman Allah, kar hnkalnka ya tashi akan wannan maganar". Ya dubeta sosai yace, "dole raina ya baci, sbd an zarge ni akan abnda ba shine a ckn zcyata ba. 'Yan uwana basu yi min adalci ba, na tabbatar da saninsu mataynsu ke yada habaici da kananan maganganu. Amma zanyi wa tufkar hanci. Tnda babu wnda ya haifa min ke". "kara kayi fada dasu abba....." yace, "ya za'ayi in tsaya ina fada da kannina? Umarni kawai zan bayar, kuma dole kowa yabi idan ana son zaman lfya. A iya sanina na basu hakknsu, na zauna da su na gaya musu uzuri na. Amma duk da haka basu gane cewar komai na Allah bane. Ke dai abnda nake soki dashi, ki rike yarn nan amana, sannan ki kara kula da kanki, don tsare martabar gidan nan" tace, "Allah ya taimaki mai martaba. Mamanka na tare da albarkar umma da abbanta, da yardar Allah ba zata basu kunya ba". Yayi dan murmushi yace, "Allah ya kara yi miki albarka". Tare da kalla suka amsa, "Amin abba Sun iso minna la'asar sakaliya, shi yasa ruwan alwala kawai alh. Ya fara tambaya. Yayi sallah a babban falon gidan, yaynda jerin kayan abincnsa ke jiransa. 'yan jikoknsa kuwa sai safa da marwa suke yi. Ya idar da sallar, suna jiran su tumurmushe shi. Ilai kuwa yana idarwa suka zube a jiknsa, yana drya ya soma tsokanarsu" "ameera tsohuwa mai majina" tace, "Allah ameer ne mai majina" ameer yace, "karya ne abba, kullum wa ake ba tishu in zamu skul?". Abba yace, "kyaleta Uwair, waye bai san halima tsohuwa bace? Mai majina kawai". Ai nan da nan tayi fushi ta tashi fuu.... Zata fice,suna mata drya. Sai ga sallamar anti Rabi. "momy kin gansu ko? Wai nice mai majina". Ita ma dryar tayi ta wuce ta zube gabn abba ta kwashi gaisuwa, sannan ta tambayi mutan gida. Yace, "duk lfyrsu kalau" Kuka ameera ke yi, yaynda mama ta shigo da ita falon, "ynzu don Allah wa ya taba min umma na?" yace, "kyale ta mai majina ce, ni bana auranta!". Ta kara kware baki, mama ta rungume ta, "kiyi shiru ki kyale shi, ke ma baki auran. Me zaki yi da shi tsoho?" ameer sai drya yake mata. Da yaga kukan da gaske take ynsa sai ya jawota jiknsa, "wanene ya taba min madam dita? Manta da ameer, tsoho ne shima. Ina dady bai dawo bane?" ta amsa da kai tana murzar ido. Anti rabi tace, "bai shigo gida ba tukuna, amma yana bisa hnya". Yace, "To Allah ya dawo dashi lfya" suka ce amin..anti rabi da mama suka bashi wuri yaci abinci tare da jikoknsa. Yan minticoci bayan kammalawarsa motar Ya Abdulkareem tayi fakin a harabar gidan, ganin motar Abbansu yasa ya fito da sauri kalla ya tarbe shi ya karbi jakarsa yayi masa sannu da zuwa suka gaisa, tare suka shigo falon ya zube gaban Alh yana fadin oyoyo abbanmu! Yace Abdulkareem dan Abba sadauki! Ya kara fadada dariyarsa domin yana jin dadin kirarin da Abba yake masa tun yana yaro sbd tsananin kokarinsa wajen neman duk abnd yake so musamman ilimi. A yaran gidan kaf! Babu wanda ya fara sauke Qur'ani da karancin shekaru sai shi, yana 14yrs yayi sauka kuma yasan littattafai dayawa. Daka dubeshi kaga Mama illa dara daran idanuwanta ne kadai suka banbantasu. Kazo lfy Abba? Yasu Umma? Yace lfy lau Mamana na kawo maka hutu.....Mama? Yanzu haka tana ciki? Sai gata ta shigo falon ta karaso gunsa da gudu ta zube jikinsa Yayana!. Ya kamo kunnenta ba wani yayankitashi zakiyi ki koma inda kika fito! Tace Allah sarki yayana dan Abba sadauki! Ya dada mata duka suna ta dariya "maras kunya ba Abj kika fiso ba? Ai dama nace duk randa kikazo yan kafafuwan zan karya.. Tace, "tuba nake yayana, daga yau duk hutu anan zan yi shi" yace, "naji amma ban yarda ba, ke da soja ai sai Allah, watakila kema sojan zaki aura". Ta kada kai ckn shagwaba, "a'a!" Abba yace, "ai baka ma sani ba? To karkade kunnenka kasha labari". "ko abba? To bani insha". Abba na bashi labari, ita kuma mama na boye a bayn yayn nata. Tas! Ya zayyane masa abnda ke faruwa. Abdul-kareem ya cika da mamaki, "to menene abn tashn hnkali a nan?" yace, "nima shi na gani, har ga Allah zcya ta bata da wani nufi akan wannan al'amari, amma tnda haka suka dauko zamu tafi a hakan, kuma mama zata auri wnda take so". Ya dan kada kai yace, "kayi hakuri abba, kasan shi mutm a kullm yakan fi son kansa maimakn neman zabn Allah. Abu kankani sai a ruruta shi yayi girman da zai rarraba kan zumunci. Abba ka dauki girma kamar ynda ka saba, ka dauke kai ga tsegunguman mata". Ya zura masa ido yana murmushi, "dan abba sadauki! Duk abnda ka fadi gskiya ne, shi yasa ma bazan gaya wa yaynku ba, don nasan halnsa, daga ali har mutn gidan babu wnda zai kyale idan hauknsa ta tashi". Yace, "haka ne, kuma nasan ali yana son mama, dole yaji zafi a rnsa, amma su a matsaynsu na manya ai bai kamata su rika tnzira shi ba. Abnda ya dace shine su nuna masa komai na Allah ne. Amma muna musu fatan Allah ya ganas da su. Ke kuma mama ki rike amana, domin duk garin nan babu wnda bai san familn marafan lafai ba. Babban gida ne masu mutnci. So u hv 2 b very carefl, ke ma ki nuna wa duniya kin fito daga babban gida mai cike da tarbiyya, OK?" Tace, "insha Allahu yaya zanyi iya kokari na". Yace, "to da kyau likita matar likita. Abba kasan wani abu? Ai mu juma munyi bye-bye da rashn lfya". Suna ta drya, anti rabi ta shigo itama. Sun jima suna hira, sannan uban dawaki ya bar garin minna tare da yarnsa kalla.! Anyi sallar magriba lokacn da suka shigo Fandogari, don haka a guje uban dawaki ya nemi bada farali. Bai wani ci abnci sosai ba, sbd abncn da ya ci da yammacin dazu a minna. Umma ya aika ta tattaro masa kaf kannensa da 'ya'yan gidan tare da ali. Duk suka hallara a falnsa, ya dubesu ya fara magana ckn rashn jin dadi, "abnda yasa nace a kira min ku, a gskya abnda ya biyo baya sakamakn maganar da muka yi da ku jiya, sam banji dadnsa ba. Basiru da amamu kar ku manta gaba daynmu ciki daya muka fito, babu bare. Kar ku bari tsegunguman mata su raba kawunan mu, domin da halima da hajo da gaje tare suka same mu. Bai kamata in gaya muku uzuri na ba, ku kuma ku koma kuna min yankn baya wajn mataynku, har su sami damar yada maganganu marasa dadi akai ba. Ko ban haifi daya daga cknku ba, ina zatn ni uba ne a gareku, kuma daidai gwargwado ban shiga hakkn kowa ba. Ali da sa'eed a wancn lokaci sun yunkuro, kowannensu yana son auren mama, a gabnku yaran nan suka rika rigima a junansu, gaba ta kullu, babu mai kalln dan uwnsa. Sbd Allah idan ban ynke wancan hukunci ba me ya kamata inyi? Shi za'a tsaga mama gida 2 ne, ali ya auri rabi sa'eed ya auri rabi? A gani na idn aka hana kowa zai fi mana alkhairi. Ko da bani da ra'ayn mama tayi zurfn karatu, ballantana ina da shi. Wlh bani da wani buri akan mama da ya wuce tayi zurfn karatu ta zama likita gabana. Amma da Allah ya sauya al'amarinsa, ba zan iya jayayya ba. Sai dai a cknku laf din nan na bar muku zabi, idn akwai mai iya yin wani abu bayn wnda Allah ya zartar bismilla, ina saurarnsa. Ni kam na yarda nayi gmanin al'ameen Allah ne ya turo shi, ban isa in koreshi ba. Kuna iya kirana kuda sbd kwadayi, ba zai sauya komai a jikina ba, don nasan har ga Allah bana bukatar sisin kwabo daga al'ameen ko mahaifnsa. Na kare maganata, idan akwai mai abin cewa yana da damar fadi". Gaba daya ka rasa mai yin koda motsi, sbd dogn jawabn uban dawaki ya tattaro musu kunya ckn idanuwnsu, musamman matan. Jin sunyi shiru, uban dawaki ya kara da cewa, "idan babu mai magana kuna iya tfya, shikenan magana ta kare" Har matan sun mike, alh. Basiru yace, "ku zauna. A gskya munyi kuskure, amma ynzu mun gane bamu kyauta ba ko kadan. Kayi hakuri alh. Da yardar Allah wata magana ba zata sake bullowa akan mama ba. Ku kuma hajo da gaje ku ba alh. hakuri, har ma da h. Halima" Da ganin fuskoknsu kowacce ba akan son ranta take magana ba. Sun dai bada hakurin, kuma abba da umma sun yafe, sun maida komai ba komai ba, a matsaynsu na manyan gida, sun nada gammo sun dauki girman kamar ynda hausawa ke fadin Babba juji ne. Aik. Adamu ma yayi nasa dan guntun jawabin na neman afuwa. Kowa ya tashi aka bar Ali a zaune, ba tare da yace wani abu ba. Abba ya dube shi yace, "akwai magana ne ali?" ya karkada kansa da ke sunkuye, sai hawaye shar-shar! Suka hau zuba. Uban dawaki ya sauke numfashi, gaba daya jiknsa ya mutu. Harga Allah bai taba tunanin soyayyar mama tayi zurfi ckn zcyar ali haka ba, wa ke ganin hawayn ali? Da yarntarsa ma ba karamar azaba ke sanyashi kuka ba, shi yasa yaci sunansa Gadanga! Domin kaf tsaransa babu mai nuna masa yatsa. "zo nan ali!" yayi kirnsa yana nuna masa waje bisa kujera kusa da shi, "zauna kaji". Ya zauna yana goge kwalla. "abnda nake sonka dashi ali kayi wa girman Allah ka dauki imani ckn ranka. Wlh a zatona tuni kun share maganar mama a zuktnku, ganin na jima da soke maganar. Amma kayi hakuri, ka dauki dangana kasa wa ranka, duk abnda Allah ya hukunta daidai ne" Ya dan gnge kwalla ya dube shi, "abba sa'eed ne ya hakura, amma ni burina inyi ta jiran mama har zuwa lokacn da zata gama karatnta. Kullum addu'a nake yi Allah yasa a tsayn shekarun nan zcyr mama ta aminta da ni". Ya numfasa ya kada kai, sannan ya ci gaba, "bansan yanda zanyi ba abba". Abba ya rungumo kafadarsa, "hakuri magani ne ali, ban son ka tashi hnkalnka. Mama 'yar uwarka ce, ka taimaka ka bata goyn baya tare da addu'ar fatan alkhairi, kaji? Ka kwntar da hnkalnka, nayi rantsuwa da mama tana da kanwa da na baka ita. Amma tnda babu, ina son kasa natsuwa ckn ranka, ka ji ni?" Yace, "naji abba, kuma na gode". Umma tace, "nima dai hakurn nan shi zan baka ali, gaba daya hawaynka sun kashe min jiki. Amma babu abnda zamu iya yi, sai dai ince Allah ya musnya maka da alkhairi" yace, "amin umma". Abba yace, "to tashi kaje ka kwnta, ka ci gaba da addu'a, komai zai wuce". Ya mike babu kuzari ya bar falon. Shiru su umma suka yi tsawn lokaci, kafn abba yace, "Allah ya kyauta!". Ta cire tagumi tace, "amin. Da gaske ali yake yi" "mtsw!" yayi dan tsaki ya tashi ya shige daknsa dauke da tausayn ali, ya bar umma zugum! Tana tunanin iska. Gidan yayi tsit! Ko da tasa damuwar. Washe gari da wuri ali ya koma birnin gwari don kara samun natsuwa. Idan bakwa comments sai inga kamar littafin ne baiyi muku dadi ba, na kuma sai inji bana son turowa din. [11/01 12:54] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 1***6 Karfe bakwai da rabi na safiya wayar tebur ke ta bugawa a babban faln. Dawowar anti rabi kenan daga rakiyar mai gidan da yara da zai aje makrnta, kfn ya wuce wajn aiki. Can gefn wayar ta nufa ta dauka tare da sallama. Bai mance muryar da ya fara ji jiya tawaya ba, don haka ya zarce da fadn, "ina kwana anti?" tace, "lfya kalau, wa ke magana?" "al'ameen ne'. Take ta fara fara'a, "au Allah sarki, ya aiki?" "Alhamdu lillahi" "madalla, bari in kira ta" "to na gode". Ta aje kan wayar gefe ta wuce da sauri tana kira, "mama! Mama ki aje girkn nan kizo, mutumin naki ya bugo!". Ta fito daga kicn da sauri, suka hade a kofa. "wannan likita naki da naci yake" "kai anti!" ta fadi cike da fara'a. "ke dai jeki da sauri". Ta wuce tana drya, ta dauki wayar, daddadar muryarta a sanyaye tace, "hello!". Ya runtse ido yace, "hello 'yan mata ya aka yi?" tace, "kalau, an kwana lfya?" "sosai ma, har da miyan barci". Tayi 'yar drya, "kaji dadnka" yace, "har na kai ki? Nasan barci kike yi aka taso ki". "haba, kamar wata raguwa?" "ita ce mana. Kowa ya ganki ai yaga kalalatu" "kai kuma kalala ba" Yayi drya yace, "tun asuba nake tsaye ina shirn ofis. Na rataya neck tie, shine nace bari in kira madam ta daura min" Ta dan rufe fuska da hannu daya tana murmushi. Yace, "baki ce komai ba" tace, "to me zance?" "au ba zaki daura min ba?" tace, "na daura!" yace, "ga abu a wuyana yana lilo kice kin daura, don Allah ki daura min" Ya fada a shagwabe. Tace, "yau na bani! To rufe idnka". Ya kuwa runtse yace "na rufe" "me ka gani?". Ya danne kan wayar a gefn wuynsa ckn tunaninsa yake magana ido ruee, hannaynsa na aikin daura neck tie din. Yace, "ga ki nan kin fito daga dakn barci, kin zuba kwalliya da wani farin less, kin yi kyau bebyna. Sai murmushi kike min, kin kama neck tie din kina daura min........ "Wash!" ya bude ido firgigi, jin ya shake wuyansa. "menene?" Ta tambaya ido waje, ji tayi ya shagwabe, "Gaskiya ba haka ake yi ba, ba haka ake yi ba sakeena. Ai dai ba'a shake wuya". Drya sosai ta kubce mata, "ni na shake ka?". Yana sassauta daurn wuyn yana fadin, "da kyar fa nake numfashi, so kike in suma?" tace, "kaga zaka makara wlh, idan suka ma bulala babu ruwana". Yace, "ya zaki ce in tafi? Kin bani brkfst ne? Ga kofn tea nan a gabana, yi sauri ki ban insha in wuce". Tace, "oya, dauki kofi kayi bismilla". Ya dauka ya rufe ido yana kurba, yana ganinta ckn idanuwnsa, itace ke bashi. "ka shnye?" "minti daya, na kusa saura kadan". Ya kwalkwale ya aje kofn, "yauwa, na koshi". Tace, "good boy. To sai ka dawo ko?" "to me zan cewa zobenki?" "ina gaishe shi". Ya zura wa zoben ido, sannan ya sumbace shi yace, "wai yana amsawa". Tayi murmushi, "shikenan, tek care, ok?". Murya sanyaye ya amsa, "i will......." yayi dan jim, tace, "ina jinka!" ya rada mata, "I love u!". Ta dan numfasa tace, "me too!". Tayi saurn kife kan wayar. Da baya da baya ta tafi har ta jingina da kujera,

Chapter 3 of 28