Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya dandana miki fiye da hakan Da namiji ne fa ki bari ya gama shanye romon da yake hange a jikin ki kisha mamaki daidaiku ke da rikon amana su ajiye ki ke kadai suna girmamaki a matsayin matar sunna mai tsananin kamanta gaskiya shi ne zai ce kik zai kara aur amma sauran shagalinsu suke sha a waje su barki hoto a gida balle wannan Dan'liti daya sami shaidar banza don haka kibi a hankali mama so ba hauka bane tace na ji kin fada amman yarda ba dole bane ko ashe kin gane domin ni duk abinda mutun zai fadi akan Dan'liti ina daukar sa a matsayin hassada ina abin hassadar ga Dan'liti koda ban san shiba labarinsa ya gamsar dani kuma na tsane shi idan kin tsane shi ki daina maganar sa don zai sanima in tsane ki Ta ware ido sosai tana kallon ta ban yi mamakin jin kalamanki ba tunda kika iya shafawa idanuwanki toka ba kya ganin mahaifanki ki balle ki saurari nasihohinsu gareki kin ban kunya mama ban taba zaton wata rana mai kamar wannan zata zoba in sha Allahu zan rarrashin dadin malami ya kyale ki duniya ta koya miki hankali,ido cikin ido ta bata amsa zaifi kyau idan kika yimin wannan kokarin haushi yasa anti amina ta mikie ta fito babban falon asibitin tayi zaune har aka kira asalatu tayi alwala tayi sallah ta je ro addu'o'I tare da rokon Allah ya sanya wa al'ameen dangana idan har ya rasa mama Cikin shigar kakinsa tsaf ya shigo asibitin tare da malami shi ma sanye da kayan makaranta kuratan sojoji biyu na take masa baya dauke da kwandon kayan karin kumallon safe a babban falo ya same ta zaune bisa dardumar sallah,malami ya fara isa gun ta ya gaisheta ta amsa sojojin dake biye suka kwashi gaishuwa yayin da ta miki ta tarbi yallabai amma fuskarta babu walwala sannu da zuwa tace dashi ya amsa yauwa ya dai jikin na ta, tana ciki shiga ka ganta ai ta farfado tun asuba,ko?suka jera zuwa dakin tana gaishe shi jin muryarsa yasa mama ta runtse ido ya tsaya kanta yace ki daina matsr ido nasan kina ji na ina fatan amina ta gaya miki sako na saboda haka ina son ki gane wannan sakarcin bazai firgitani ba abinda na sani kawai al'ameen ya dawo a daura maku aure middin kina numfashi sauran shawara ta rage gare ki, Anti amina dake ta kallon ledar ruwa tasa hannu ta dago igiyar tabbas abinda take zato shine din. Ruwan ba a jikin mama yake ba cirewa kikayi mama, ta juya kan yallabai tayi masa kuri ka gani ko ta cire ruwan yaya ya kawo iya wuya kamar ya nannausheta yake. Ji cikin fushi ya juya ya fita anti amina tace da kanki ki ka kama drip din ki ka tuge,sau dubu aka samin sau dubu zan cire me ruwanku dani tunda baku kauna ta tana rufe baki yayan na shigowa da wasu nosis biyu amma abin karin haushin mama taki yarda su mai da mata ledar ruwan nan basu san lokacin da yayanta ya cire hannu ya tsinka mata mari ba,sai da bakinta ya tsatso jini saboda haushi da takaici kafin ayi haka ya bar dakin anti amina ta biyo bayan sa ta bar nosis na rarrashin mama yana shiga mota ita ma ta fada ciki tace kayi wa girman Allah yallabai karkayi fushi ka tsaya ka saurareni kar ki min magana akan wannan wawayar yarinya," I have finish with her, dama munyi waya da abdul-kareem sun ce za su zo harda abdul-rahman so suna zuwa zasu wuce da ita daga can su bata kudin mota ta wuce fandogari zan iya kashe yarinyar nan idan ina ganinta, tace wallahi ni ma shawarar dana ke son in ba ka ke nan idan kaji maganganun da mama ke fadi zaka tabbatar da tayi nisa bata jin kira sai addu'a kawai zamu zauna ne tana bamu wahala koda yaushe mu ma asibiti a aikin banza?ba zai yuwu ba a irin take taken ta tana gab da fara sufa mana zagi ku kyale ta da dan-litin shi ne zai koya mata hankali,yace ai an gama dokta zuwa kice ya sallame ku kawai zan sake kiran abdul- kareem din in ce su dame mi gida ta numfasa don murna kafin tace,"!58,naji dadi yallabai Allah shi taimake ka ita kuma ya shiryar da ita amin ga break fast can kije kici ki kyale ta bari mu kai malami school gada can zan shiga ofis to a dawo lafiya amin,ta fito sannan sojojin suka taso daga. Inda suke tsaye tare da malami suna jiran su babu bata lokaci suka bar harabar asibitin anti amina ta koma ciki tace wa nosis su kyale ta su tafi abinsu guda tace oga zaiyi fada madam idan ya shigo. ni nace ku tafi kawai abin ku ba mu muka kawota ba,kuma mu zamu biya bill ku wuce kwai ba wani abu"nosis suka wuce da mamaki anti amina ta hada abin kari ta hau ci bata sake komawa ta kan mama ba har likita ya shigo misalin takwas da rabi na safiya anti amina ta maida masa bayanini yallabai likita yace a'a baza ayi haka ba nan ya ja kujera yayi ta rarrashin mama,tayi shiru kamar da gaske sauraronsa takeyi da kansa ya nemo jijiya ya maida mata ruwan amman me yana gamawa bai ko bar dakin ba ta sa hannu ta zare ta aje masa robobin sa haushi ya shake likita ya jima yana kallon ta sannan ya dauki (file)din ta yayi rubutu,ya dubi anti amina yace kuna iya tafiya gida madam da alama ba zamu shirya da sakeena ba tace ai dama na gaya maka kayi hakuri dokta kan ta tayi mawa tace ba wani abu shawa ta kawai ia ce ku kyale ta ta auri wanda ta zaba may be rabon wahala ke kiranta,tace sosai kuwa dokta mun gode ji suka yi mama taja wani shegen tsaki duk suka bita da kallo likita yace I'am sorry for yau,a tunaninki kinyi abu Mai kyau ke-nan? NO,ba hk rayuwa take ba. Ya kamata ki rinka kulaw. Ya sa kai ya fice.Nosis din sa suka take masa baya,kowanne su babu wanda bai shakì taikacin Mama ba. Tana hada kaya direba na shigowa, yaya ya turo shi,idan anyi sallamar ya kaisu gida. Shi ke nan kaya sun tsunke karkashin kaba. Ya kwashe kaya,ta dubi Mama tace, ki na iya tasowa muje gida,idan kin so.Ta yunkura ta tashi,Anti Amina bata saurareta ba ta wuce abin ta. Da kyar ta sauko daga gadon,wani mugun jiri yayi tafiyar ruwa da ita,ta koma dabas! Ta zauna.(maganin mara jin magana,yarinyar nan tana ban haushì! Mts!) Tafi minti uku dafe da kai,sannan ta sake mikewa ta daddafa bango ta fito tana layi. Kowa kallon ta yakeyi,musamman Noisis din da komai ya faru a gaban su,ai nan take aka shiga maida labari. A mota ta same su. Anti Amina na gidan baya,duk ta kulle sakatun kofofin biyu,saboda haka dole Mama ta bude murfin gaba ta zauna tare da direba. Ko a cikin gidan ma,babu mai kula wani,hasalima Anti Amina kwanciyar ta tayi tasha barci,bayan ta yi wanka ta sauya kaya.Ita kuwa Mama taci gaba da sanya tsananin kunci cikin ranta,ji take kamar ana hura wa zuciya ta wuta.Tsananin son ganin Dan-Lati da kewarsa suka hana ta sukuni. A yadda jiri ke dibar ta,sau uku tana fitowa waje ta tsaya wai ko zata ga lakwa-lakwa ta sulale ta gudu.Amma ina,ko fuska babu a wajen kuratan nan,balle ta sami hanyar fita.Don haka ta kifa ciki tsakar falo,tayi ta sharara kuka har azahar,bata san lokacin da barcin wuya ya sace ta ba. Anti Amina ta sauko tayi girki ta gama bata farka ba.Dawowar Malami ya kwarara sallama',shi ya tashe ta,tayi doguwar mika tare da hamma mai kunshi da yunwa da wahalar duniya. Ta tashi zaune taja jikin ta,ta zauna ta jingina da kujera,wucewar 'yan mintoci.sannan idanuwan ta suka kwalli agogo.karfe daya hard a rabi. Da kyar ta yunkura ta tashi ta haye sama a wahale,tana shiga dakin ta zube a kasa,sbd babu karfi a jikinta.Malami da ke cire kayan makaranta,ya zubo mata ido.yana so ya gaisheta yana jin tsoran mari. Ya sauya kaya,ya fice daga dakin,wajen Momin sa ya shiga idanuwan sa cike da damuwa. Ya zauna kusa da ita,tana kallon yadda ran sa ke bace,don hk ta rungumo kafadun sa tace, "Yaya dai,yunwa akeji? Ya kada kai yace, Momi Anti fa zaa mutu,ku maida ta asibiti.Allah bata warke ba. Ta zura masa ido,tace,Ba laifin mu bane Malami,a gaban ka ai kana kallo taki yarda asa mata Drip. To ya take so muyi?" Yace, kawai ku kira mata abba yayi mata fada. Wlh bana son Antí ta mutu. Ina son ta Momì,me yasa take ta wannan ciwon ne? Ta kara rungume shi tace, kowa ma nason Antin ka Malami,kuma babu mai son mutuwar ta,Matsalar taki cin abinci ne,shi yasa ka ganta haka. To sbd me? Tace kaga ka yi shiru da bakin ka,kai yaro ne ba ruwanka da maganar manya.kai daì idan ka yi sallah ka roki Allah ya bata lafiya. Yace, To Momi,tace. Maza kicin ka zuba abincin ka.'ya fice tana kallon sa. Zuwa karfe biyar Mama ta sake fadawa cikin mummunan hali,bata gane kowa. Anti Amina ta rasa inda zata sa ranta,domin ta rasa yadda zata yi da Mama don ta ceto ran ta. Ta sauko falo da nufin kiran wayar ofishin yallabai. Shigowar mota harabar gidan,shi ya dauki hnklnta ta zage labulan taga ta daga.Motar Abdulkareem ke fakin a harabar aje motoci,ta dawo da sauri ta nufi kofa cike da farin ciki da baya misaltuwa. Ta bude kofar tayi waje,farin cikin ta ya karu,ganin har da Abba acikin su. Sannun ku da zuwa! Ta isa wajen tana fadi. Duk suka amsa,sannan suka rankayo cikin gida. Malami ya rugo ya rungume Abba. Bayan gaishe gaishe suka tambayi Mama. Tace,tana daki babu kyan gani,nama fito ne,in kira dadin Malami ko za mu sake komawa asibitin ne,sai gaku. Wlhy Abba taki cin komai tunda suka zo garin. Ban jin tasa ruwa a bakinta,wannan masifa dame tayi kama? Duk suka yi shiru sbd takaici,babu wanda ya tanka har Anti Amina ta mike ta kawo musu abincin da ababen sha. Ruwa kawai suka sha Abba. Ya-ce, muje mu ganta. Duk suka rankaya saman. Yanayin da suka riski Mama,ba karamin daga hankulan su yayi ba. Abba ya zura mata ido,idan da zai hadu da ita a hanya,ba zai shaida ta ba,sbd sauya kamannin da tayi,sbd tsananin son cikawa al-ameen alkawari ko alama bai barì tausayinta ya rinjaye shi ba. Don hk ya dubi sauran yace,wannan ba shi zaisa mutuncin mu ya zube a idon duniya ba.sbd hk zamu koma da ita asibiti,ta farfado.sannan mu wuce da ita fandogari. Farin ciki na Mama ta mutu a dakin nauran al-ameen wanan shne kwanciyar hnkli na. Ku dauko ta mu tafi. [12/01 18:20] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 2***7 .Yayay abdul-kareem yace gaskiya ne abba shi kuwa yaya abdul-rahman abin ne ya zame masa banbarakwai don bai taba zaton labarin da yakeji abin ya kai haka ba duk da yana jin zafin abinda mama tayi ,halin da idanuwansa suka gane masa mama a halin yanzu kwarai tausayinta ya kwanta a zuciyar sa shi ne ya fara kai hannu ya ciccubo ta suka taimaka suka sauko da ita kasa kamat matacciya,da kyar likita ya karbe ta sai da yan uwanta suka yita rarrshinsa sannan ya bata gado yayi mata duk abinda ya dace. Acan yaya abdul- kadeer ya same su bayan sallar magariba kafin ayi issha'I suka rankaya gida akabar anti amina tare da ita,kusan kwana sukayi shawarwari akan al'amarin,kwana daya da wuni mama na kwance magashiyan ledar ruwa goma sha tara ta shanye,ana shirin daura mata na ashirin sannan idanuwanta suka fara washewa ta gane inda take hada ido da abba tare da karkaf yan'uwanta bai haifar mata da wata nadama ba illa kuka da ta fasa wai don su tausaya mata babu wanda ya tanka mata wannan itace shawarar da suka yanke babu wanda zai sake bata bakinsa don yi mata fada amma zata sha mamaki ranar da Allah ya yasa al'ameen ya dawo kasar nan,babu wanda yace cikanki har ta gaji da shashekar kukanta. A zaton ta shirun na su alamma ce ta saduda ma'ana sun rasa yadda zasuyi da ita dole suu sa mata ido anti amina ta fara bata ruwan lipton tana kurba da kyar take iya hadiye shi gaba daya Makogwaronta ya farfashe kafin gari ya sake wayewa mama ta samo kanta misalin goma da rabi kawai ganin su tayi sun shigo suna gaya wa anti amina an sallame ta zasu wuce yanzu bata yi mamakin jin haka ba don haka ta amsa da to,Allah kara lafiya ita kuwa yar gigalar murna ce fal cikin ta jin za a wuce da ita fandogari nan da nan suka kwashe kaya,yaya abdul-kadeer ya dauki matarsa,mama kuma tabi ayarin komawa gida a minna suka yada zango suka ci abinci tare da yin sallolin azahar da la'asr in banda su ameera babu wanda mama tayi magana dashi domin anti rabi ma ta sauya fuska al'ameen dintama bai sami kulawa ba suna idar da la'asar yaya abdul-rahman ya jawo matarsa daga inda ya aje ta aka maida jakar mama ciki ita ma ta fito ta shige gidan baya abba na tare da karamin yaya a gaba Shi ya jasu a hankali xuwa fandagori. tun daga kan kwana hankalin mama ya soma kwantawa, domin dai idanuwan ta sun hango wanda take son gani. yana zaune bisa benci a kofar shagonsa, yayi murmushi itama ta sakar masa nata. har motar ta wuce, ba su daina leken juna ba. sai da ta daina hangensa, sannan ta zauna sosai kirjibta nata bugawa, ji take kamar ta balle murfin motar ta fice taje gunsa. ya mikawa ayuba hannu suka tafa. yace baka da kyau! Yace karya kak don ubanka, kalle ni sama da kasa! ba kyawun sura ba, ina nufin.... ya kai masa naushi a kafada, shi ya katse shi. zan ci..... kai! ka kiyaye ni fa wlh! me na gaya maka? yadda suka dauke ya ahaka za su dawo min da ita. wahalar banza sukeyi sakeena mallaka tace. yace ranar da Allah kuma zai kama. ayuba baya wajen, duk ka gama iskancin ka. ya ballo masa harara yace, to ko ka na wajen me zakyi? kai ma ka ji da naka, don ubanka. Menayi? ni nakai ka iskanci a garin nan? dama wane kai, amma sannu a habkali xzaka biyo ni mujera hanya watakila ma ka xarta ni. ya tabe baki yace Allah ya sawwake, kai din ma so nake na janyo ka baya. ka auri yarinyara nan, ka manta da kudinrinka na wulakantata. ya dafa shi yace ka dan kula da shagon, bari na je nemo gasasshiyar kaza. kasan dole anjima ta zo£ ya xuba masa ido kawai, bai ce masa komai ba. yayi dan saurayin murmushin. ya mike ya fada motar sa yayi birnin gwarin tsinke. kai tsaye mama dakinta ta shige. umma bata gasganta idonta ba, irin yanayin da taga mama saboda haka tatashi tabi bayanta. Kallo daya tayi mata taji kanta ya ci gaba da sarawa, wani kululu ya daure xuciyarta, idanuwanta suka tara kwalla, saboda tsabar BAKIN CIKI. Ta jima kafin tace, Mama kina da hankali da tunani kuwa? Ji tayi an dafata ta biyu, muryar Yaya abdul rahma ke fadin, baki da lfya Umma, karki daga hankalinki, abba yace ki fito ki kyale ta. Ya kamo ta suka fito, jiri na dibarta, shi ya sa tace yawuce da ita dakinta. Abba ya taso ya biyo su, yayin da take kwanciya a gado. Gefen gadon ya xauna yace, bai kamata ki bar ciwon ki ya tashi ba halima, kin ji dai abinda Dr. Ya fada, jininki ne ke hawa saboda damuwar da kika sanya a ranki. Ki hrk kawai. Tace, ba alamun yin nadama a wajen Mama, ni kaina, nasan haka,amma shawarar da mu ka yanke da 'yan uwanta shine mu sanya mata ido tayi shirmen ta, sai ranar da Al-ameen ya dawo xata gane mu ma ba muyi nadama ba. Abdul yace saboda haka ki kwantar da hankalinki, ISA sai dai mama ta mutu a dakin Al-ameen, ba zamu ji kunya ba. Su Yaya babba da Iyalnsu duk sunce gaishe ki, sai sun xo. Tace ina amsawa, Allah ya taimake mu, suka amsa ameen. Abba ya dube shi ya cigaba, kai ma ya kamata ka hanxarta wucewa yamma tayi sosai. Umma ta amshe, ba xai bari xuwa gobe ba? Yace, akwai aiki Umma, yanxun nake so na lallaba. Ta dan kada kai. Tace, to Allah ya Tsare agaida min safiyya da kyau. Zata ji, ki daina damuwa Umma, komai xai wuce da yardar Allah. Ta amsa da kai, tana fadin shikenan abdul, Allah yayi maka albarka. Yace amin. Ya wuce cikin hanzari. A tsakar gida ya hadu da su Haj.Hajjo. Ashe da gaske ne kun dawo? Yara ke fada mana yanxun. Yace eh, nima xan wuce kd kenan. Gaba daya suke to Allah ya tsare! Ya amsa yayi gaba abinda, su kuwa ciki suka kutsa kai dakin mama. Kwakwazon surutun su ya sa Abba ya ta so fito. Sannuku da dawowa Yaya. Yace yauwa, ga haliman can a dakin ta. Haj. Hajjo tace, muna nan mun ganin ikon Allah. Mama ta dawo kashi ba rai? Yace haka take so, ai ku daina bata bakinku, kowa ya sa mata ido. Haj. Gaje tace, lallai kam wannan al'amarin sai ido. Allah ya kyauta. Ameen. Suka fice tare suka koma dakin Umma, suka isheta da surutu. Duk iya kokarin mama na son fita a wannan daren abin ya faskara, domin dai Abba ya kasa ya tsare a falo har goman dare ya garkame kofar ya shige dakinsa barcinsa. Allah da ikon sa, abba bai xare mukulin ba, domin bai taba tunanin Mama xata iya aikata wani abu a wannan tym din ba lallai abba bai san Mama ta wuce tunaninsa ba. Yana bada baya, taji motsin rufe kofarsa ta yi wuf ta mike, takalmanta a hannu tare da mayafinta. Tayo sanda ta fito jim, tsakar falon bata ji mtsin kowa ba, sannan ta karasa kofar ta bude ta cikin nutsuwa ta sulale ta fice. Can ma kofar sassan hka ta bude ta, ta wuce zaurukan gidan, ta zare sakatun ta bude ta fita ta maida kofar ta sakaya. In bakayi bani wuri! Ta callah da gudu bata ko jin rashin karfin jikinta, sai da tayi rabin tafiya, sannan ta tsaya ta sa takalmanta ta yafa gyalen tana ta xuba haki, ta dau hanya babu jama'a sosai. Gata nan ga ta nan har kofar shagon dan gogan. Ya tare da dije a kofar shagon bisa banci, ta cukuikuye shi kamar na goye fadi yake, wai dan Ubanki dole ne? Kin fa matsa min da yawa, xan ci ubanki a daren nan, in ga mai kwatar ki! Kawai ganin mama yayi akan su. Ya banbare dije ya ture gefe, bai bata lokacin ya daga kanta ya shige, shagon yana jan tsaki. Mama ta daga itama ta bishi. Dije kuwa mikewa tayi ta kakkabe jikinta ta wuce tana kwafa. Ya hade rai a kujera, bai ko kalle ta ba. Ta matsa gare shi murya sanyaye tace, fushi kayi danliti? Ni ban yi fushi ba sai kai? Ina can naki ci na ki sha saboda kai. Ashe ka na nan ka tare da wata? Dubi yadda na rame na sauya kamanni, saboda tunanin ka Danliti. Bai kamata ka yi min haka ba. Ya dago idanuwansa farare sol! Sunji kwalli ya dubeta, ko mai nai miki ai kekika jawo, kinbi 'yan uwanki ki manta da ni, ba dole in sami wata ba! Tun yaushe kuka shigo garin nan? Nayi ta xuba ido, amma ban ganki ba, me kike tunanin xan dauka? Kafin tace wani abu ya fizgo hannunta xuwa daki, yana kara fadin, idan karya nake yi, xo muje ki gani! Ayuba dake kwance bisa katifa yayi firgigi ya tashi yana kallon ikon Allah. Ledar kaji ya janyo ya xaxxage su. Yace me kika gani nan? Saboda ke na tafi har birnin gwari na siyo miki gashin xamani kajin turawa. Dubi nan juice ne kala-kala har sanyi su ya fita, baki xo ba. Ba dole in yi fushi ba, in saurari mai so na! Ta sauke numfashi, idanuwan ta taf! Da kwallah, ba laifina bane Danliti, baka san irin bakar wahalar da na sha ba, don kawai su dawo da ni. Sau biyu ina kwanciya a ascibiti, dube ni da kyau, kai kanka kasan ba haka nake ba. Amma kayi hkr, tunda kana ganin kamar da gangan nayi, ka hkr? Ya xura mata ido jim, sannan yayi dan murmushi ya ware hannayensa yace, to oyoyo! Ta sa hannaeyanta ta rufe fuska. Yace kunya? Ashe baki so na, lallai na yarda ni kadai nake haukan sonki. Yana rufe baki ta matso da sauri ta rungunme shi. Ayuba, yayi gyaran murya. Mama tayi wuf ta rabu da jikinsa. Ya dubi Ayuba, yace malam ka fita ka bamu wuri! Yace, ai ku ya kamata ku koma daga waje anan nake so mu xauna, fita ka bamu wuri don Allah, shago fah abude yake, ya yankura ya tashi yana fadin, gaskiyya kuyi sauri ku gamacin kazaraku, barci nakeji. Ba ruwanka wannan. Ya fice yana waigen Danliti yana masa ishara da idanuwansa dauke da gargadu, wanda shi kansa ya gane nufinsa, shi yasa yake wani irin mur0ushin na iya shege. Yana fita ya dubi Mama suka hada ido dukkan su sukayi murmushi, sannan ya kamo kafadunta yace, gashi dare yayi, amma dole ki xauna ki cinye kajin nan, domin saboda ke na siyo su. Ba tace komai bam ya xaunar da ita gefen katifa, ya jawo kayan kwalama, ya baje mata kajin, yana bata abaki, tun tana jin kunya har ta saki jikinta, tana amssa sosai tana ci, suka ci suka sha suna hirar bayan rabuwa. Bayan sun kare. Danliti ya dubi agogonsa ya ce shadaya da kwata yanxu, ya kamata kije gida ko? Sai gobe, ina fatan xaki rika cin abinci don ki gyagije kyanki ya dawo kamar da. Kinji ni? Tace, naji kuma xan kiyaye, amma don Allah ka daina bari 'yan mata na xuwa gunka, watarana xamuyi dambe da su wlh, kaji na rantse. Ya kyalkyale da dariya son ransa kafin yace, xaki kuwa sha duka, don dai nasan sunfi karfinki. Wannan jikin naki rugu-rugu babu kwari. Ya fadi yana mammatsa hannayenta da kafafuwanta. Ta yankura ta tashi tana cewa, haka kake gani, ka maida abin wasa, zaka sha mamaki. Shima ya mike ya kamo yatsunta, yace karki damu, ke kadai nake so, ko da damben ya kama kuyi, xan shigar miki balle ma banda lokacinsu. Ke me xai dameki? Tayi murmushi, tace, to shikenan sai da safe. Ya sumbaceta yace, muje na rakaki. Suka fito yana rike da hannunta, tayi wa ayuba sallama suka wuce. A kofar gida suka fuskanci juna, tallafo kuncinta ya xura mata ido, yace karfa ki damu da ganin Dije tare da ni, wlh ba sonta nake ba, kawai ta matsa min ne dole muyi soyayya, amma xan dauki mataki akanta, tinda ta fara bata miki rai. Tayi murmushi, tace, nayarda da kai, ina fatam Allah ya yarda mana, ya bamu nasara abinda muka sa gaba. Da sauri ya amsa amin sakeena. To sai da safe nagode, wannan karon abin ya cigaba akan labbanta ya sumbace ta. Ta juya da sauri, ta tura gida ta shige ta maida sakatu. Danliti ya runtse ido ya jinjina hannayensa, shege ni! Ya juya yana takawa dda+dai kamar wani kasaitaccen basarake. Mama kuwa sanda takeyi, kamar barauniya ta turo kofar fa'aar dshigo ta mayar d hankali ta kuleta, ta fada gado. Tana jan mayafi, taji a; ttay bude kofa, tayi tsaye jim, sannan ya mayar ya rufe. Muryar umma taji tana fadin, menene alh.? Yace kamar motsin naji ana taba mukulli.. Tace Innalillahi an shi ne? Yace amma ban ga kowa ba. Ya dubi agogo, karfe sha biyu saura kwata, dare ma bai yi ba sosai, to Allah yai mana tsari da sharrin masu sharri. Yace amin, je ki kwanta. Cikin fargaba suka bar falon. Mama ta gyara kwanciya tana gyatsar naman kaxa. Dan kanta tace kwanta naman kaza. Tayi tunani Danliti har barci ya kwashe ta, shi take marfi yana sa mata naman kaza abaki. Da safe tayi wanka, duk 'yan ciwukan da suka rage ba su warke ba, ta goga musu mai, ta shafa hoda ta sa atamfah riga da xani, nan da nan ta dan yi fasali, duk da cewa akwai rama sosai a jikinta. Yau kam tayi dan kyan gani, ta fito falo wajen Umma cikin kicin inda take aikace aikacenta, tace sannu Umma ina kwna? Ta juyo da sauri ta dubeta sama da kasa, tace kalau na kwana. Ta kara matsowa tace, bari in gaida Abba, sai in xo in tayaki aikin. Bata amsa ba ta fice, ta bita da kallo sannan ta kada kai tace, Allah ya shirya. Dakin Abban tayi sallama, ya amsa ya bita da kallo, ta karaso gunsa ta tsugunna, ina kwana Abba? Yace Kalau, ta dan dube shi, amma bata kara komai ba, ta mike tayi waje ta koma kicin: Umma me xan tayaki? Tace ban so, koma dakinki kawai. Saboda me Umma? Ai ban isa na fadi ko saboda mene ba, tunda kin xama shafaffiya da mai. Je ki kawai ki sha xamanki. Kai tsaye kuwa ta wuce daki abinta. Tana fadi cikin ranta, kya gama girkawa, mu zo mu jajja (hmmm mama tayi nisa walle). Kan Umma ya sara ganin yadda mama ta wuce ko ajikinta, bata damu ba. Mamaki bai gama kashe Umma ba sai da ta hange ta kicin din tana diban abinda take son ci. Tana kallo ta koma dakinta ta cinye, ta maida kayan kitchen ta fito. Haushi ya kume Umma bata san tym din da tace, Uban wa kika ajewa kayan ya wanke miki? Tabbatacciya! Ta dan bata rai ta juya ta kwaso kayna ta wanke. Karfe 9 abba ya fita harkokinsa. 9:30 mama figi gyale tayi waje, Umma nace na wanka. Ta sha hirarta wajen Danliti har 12pm sannan ta tsallaka ta gangara wajen Baraka. Sosai taga sauyin fuska wajen Inna saude. Sam abin be dame ta ba. Suna kebewa da Baraka tace. Kawata ban gane ba, sai da nayi miki kallon kurulla. Yanxun saboda Allah dawowa kikayi? Tace ga ni kuma kina ganina. Matsala tace, babu ruwan kowa. Mutane masharanta ne kawai, saboda Allah yayi wa Danliti kyau da farin jini, ga shi ya Rufa masa asiri, shi ya sa ake masa hassada.... Ta katse ta, idan hassada ce, ai kuwa kem kinyi masa da. Menen baki fada ba akansa? Tace, Rashin sani ne, duk surutan da akeyi wai dan Iska ne dan guguwa. Dan wata tsiyace, ni har yanxun Danliti bai taba furta min maganar banxa ba balle ya nemi aikata wani shashanci. Rashin fahimta ne kawai yasa ake masa zargi, kisan mutum mai farin jinin 'yammata (Kuji fa wai bai taba mata komai ba?) baki ganin ko mace ce ta fiye samari sai arinka mata wani irin kallo? Baraka ta sauke fuska, tayi guntun tsaki, baki jin kira Mama. Allah ya shirye ki. Ameen, ni bari

Chapter 12 of 28