Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zauna da shi ba? Wahalar tace tunda tasan halinsa. Tace sai shi. Wai kuma mu ake ganin laifin mu, don fin karfi! Mts.... Ya ja tsaki yayi waje abin sa. Alh. Basiru ya mike yana kada kai, shi ma ya fice. Zaman doya da maja yaci gaba da yaduwa cikin gidan, duk da ba gaba daya sukeyi ba, amma babu wata kyakkaywar fahimta atsakninsu. Shi uban dawaki yana ganin ya kamata su ba shi hkr a matsayinsa na babban su, sannan yana gani sun yi masa laifi, don sun bada labarin yadda akayi mama ta gudu, tunda ba su suka xuga ta ba, komai ya kwana gidan sauki saboda haka basu ga dalilin da xai sa Uban dawaki Ya dauki dalan laifi ya dora masu ba har ya rinka jiran kalaman tubansu. Su ma fah yanxun ba yara bane, girman 'ya'yan su ya kai, ya gane shekarun su sun cika daidai matsayin masu 'yanci. Zuwan Ali da Ya saed don duba jikin Umma da kuma jin labarin Mama ko ta bayyana, Al-amarin bai yi musu dadi ba, ganin Yadda iyayen su suka ware ubandawaki suna masa yankar baya. Musamman Ya ali, hankalinsa yayi mummunan tashi, babu bata tym ya gurfana gaban abba yana bashi hkr. Daga bisani Ya saeed ya shigo falon. Ya ali Yayi rantsuwa da ace mama zata dawo ta amince da auransa, maimakon Danliti, a shirye yake a daura masu aure. Ko a gaban iyayen sa haka ya maida zancansa. Haj. Hajjo ta rufe shi da bala'i Allah wadarn wannan so kuwa, tunda yake hana ka kishin kanka. To idan ma mafarki kake yi, ka wanke idon ka, ka saurareni, idan har ni na haifeka, ba xaka auri ragowar Danliti ba. Wannan kalma tayi masa ciwo, bai san tym daya tasshi ya tabbatar wa su Haj. Hajo cewa kashe miciji sukeyi basa sare kansa. Domin ko banza sun kwana da mamakin Ya ali da yayi tafiyarsa, daga magana, shima ya gudun kenan? Ko mene nufinsa? Muna iya cewa matsalarsu ce, ko dama abba ya fadi kaddara na kan kowa....... Inna saude ke xaune gefen gadon tana mata fifita. Kallo daya zakayi mata, ka gane cewa ta jima tana fama da ciwon tsananin damuwa, domin dai ta fyade ta fita kamanninta. Amma hakan bai hana ragargazar shagalin bikin da akeyi cikin gidan ba. Nasan xakuyi mamaki, idan na gaya musu cewar bikin yaya Ali da Ya Sa'ed akeyi. Iyayeyn sun hur masu wuta, tun tym din da suka lura da take taken shi Ya alin, sam hankalinsa ba shi akan abinda zai fishshe shi. Shi yasa suka matsa kwarai da gaske akn ya fiddo matar aure ko su su fidda masa, ya kuwa tabbatar da mahaifiya sa xata ita. Gudun kar ta manna masa alakakai ya sa ya fito da yarinyar da ta dade tana sonsa a birnin gwari. Amina sunanta, kuma makwabtansa ne a gidan daya ke xaune. Sa'ed tuni yake tare da Hassana a kd. A yau ne maza suka daura auran 11am. Daga can suka wuce kd, inda xa'a daura na sa'ed bayan azahar. 8pm wannan rana motocin amare ke shigowa layin gidan angwayensu, haka daidai wannan tym motar Danliti parkn a kofar shagon sa dauke da tasa amaryar. Cike da mamki ayuba ya taso, ya bude kofar yana fadin, wa nake gani kamar amafarki? Wai dama kuna tunanin gida? Dan liti ya fito yayi doguwar miki, yana dariya, yace ah gamu kuma mun dawo, ya juya cikin mota ya cigaba da fadin, ya Gimbiya anan zaki sauko ko na karasa dae gida? Ta kada kai, tace, naji tsoro ya kamani Danliti, bansan yadda xanyi ba? Yayi 'yar dariya. Yace tsoro kuma? To me xa suyi miki? Ta kada kai bari dai na sauka nan, canm ajima na karasa gidan. Ya kace da dariya. Amma ke shirmen ki yayi yawa, to fito ki shiga ciki. Ta ballo murfin ta fito, kai! Anya kuwa Mama ce? Tayi wata shegiyar kiba ta kara ja, ina ganin shi yasa Ayuba ya xura mata ido, tym din da take mika masa gaisuwa. Danliti ya bude but suka ciro manyan jakunkuna guda 2 da kit, sai manya ledoji guda 3. Ayuba ya taimaka suke shige da su cikin shago. Kai tsaye dakinta shige ta xube a katifa. Duk suka biyo bayanta. Danliti ya xauna kusa da ita. Yace kin gaji ko? Tace kai dai bari, kamar in kwanta inyi ta barci wlh. To ki kwanta mana, ai ba kya jin yunwa ko kinaji? Ta kada kai, banji, to ki kwnta ki huta ne, xuwa karfe goma sai in tashe ki, ki koma gida. Haka za'ayi, ta jawo filo ta yada kai, suna kallon juna suna musayar murmushi. Ya lukuce mata hanci, yace baby na kenan. Ta juya gefe tana 'ya dariya. Ya mike ya dubi ayuba yace, to muje dogari. Ya juya yana murmushi, ina tsarabata? Yace yauwa ka tuna min, ya suri jakar leda suka fice da ita. Ya xauna bisa kujera ayuba na kan tabarma, ya zazzzage kayan kedar a gabansa. Gaba daya kayan sawa ne. Na gayu ya siyo masa, ya dube shi suka hada ido, yace ga tsarabar legos nan. Baki sake yace babu wai, har ma ga tsaraba nan duka naka ne. Ya washe baki m amma na gode, watau shi ya sana kunyi jajur abinku, ashe kuna bakin teku. Yace, hutu ba karya bane ayuba, ga kuma lafiyayyar bebi na, nake gaya ma. Yayi shiru yana kallon sa, fuskarsa gaba daya tabayyana babu abinda bai faru ba. Ya numfas duk jikinsa ya mutu yace, bakaji Danliti. Me nayi ma tukunna? Ko kaji surutu ne a gari? Ya gyara zama yace ba'a tonawa Danliti, abinda nake son ka da shi, ku sasanta ka aureta kawai, ka ba masu surutu kunya, donn sunce ba auranta zakayi ba, tayi saki reshe ne, ta kama ganye, ya shafa habarasa yace, ko? To ai ba suyi karya ba, shagali kuma basu ga komai ba daga nan ma illa masha Allah ba za mu daina ba. Ya kada kai yace, meye nawa a ciki? Idan ka huta ko xuwa gobe mayi lissafi. Yace ina fatan akwai kudi sosai, don wanda na tafi da su naci uabansu, ya amsa ciniki na na ba laifi, sati biyu ma da suka wuce na je kno na karo kaya da cinikin yafi haka. Da kyau mutumina, shi yasa nke sonka wlh. Yayi 'yar dariya yana daga kayan da aka kawo masa, ni kuma ina sonka da nutsuwa ba amma kakiji. Ya mike ya nufi daki yana cewa, kai ka fiye surutu, bari in baka wuri. Ya shige dakin ya bar ayuba da kallonsa. Ya kada kai yace aransa, Allah ka shiryemu. Shi kuwa Danliti komawa yayi ya hana mama barcin. Karfe 10 ta dan gota, dan liti ya umarci Mama da ta koma gidan iyayenta, su san ta dawo, dan su san matakin karshe da zau dauka. Watakila hakan su ta cimma ruwa. Watau su amince da auransu cewarsa madugu uban tafiyar. Ya hado mata kayanta taf! Da katuwar jaka, tana xaune tana kallonsa, kafin tace gaskiyya ba xan dauki jakar nan ba, guda uku kawai dauka cikin kit, in tafi dasu. Ido waje ya tambaya, sabda me? Ka sani ko su koroni? Ka bari tukunna mu gani, idan suka kyale ni, sai in dawo in kwashe sauran. Idan basu kyaleki ba fah? Sai na dawo nan ka yanke hukunci duk da zaka yanke. Ya xura mata do, ai iyayenki na san ba su ki karbarki ba, hasalima ai laifin su ne, na tabbata yanxun sun gane kuskurensu, dole su lallabaki. Ta doke kafadarsa tana dariya, har ma kasan dole su lallabani? Kai dai ka yi fatan su amince da auranmu. Yace shikenan, yanxun ki dauki abinda xaki dauka na rakaki, dare nakara yi. Ta bude kit ta xuba kaya kala 3, yasa hannu ya dauko wata 'yar karamar doguwar riga yace..... Yace ba xaki dauki wannan rigar ba? Tace wannan shegiyar rigar? Shegiya? Lallai ba ki san yadda take mi ki kyau bane, a'a ka dai barta anan, sanin kanka ne, su Abba bna za su barni na sanya taba cikin gidansu. An wuce wurin, ki barta kyasa a gidana. Ta yada kai kan kafadarsa tace ashe ka gane. Ya tsikare ta, ta mike xumbur! Ban fa so Danliti banso! Ta figi kit dinta, tayi waje baki a ture. Ya kwaso mata gyale da takalmi ya biyota yana fadin sorry 'yar bebi na! Taja ta tsya tana haraarsa, ya yafa mata gyalen, ya aje takalmin gabanta ya jawo kafufuwanta, sa abinki mu tafi. Ta xura kafar tace wa Ayuba, sai da safe. Yake yayi ya amsa, Allah ya kaimu. Suka fice, Danliti na cewa, har kin tabbatar da xamanki a gidan ne kike ce masa sai da safe? Tace gane min hanya wai, makaho ya so gulma. Ya ci gaba da dariya, suna tafe suna hira. Gab da gidan, ya tsaya sukayi sallama, idan kuma ya gan ta ta dawo shikenan. Y koma ita kuma taci gaba da tafiya hankalinta kwance yake, don bata saka komai illa in su koroto, ta koma inda ta fito. Daga bisani ma wata dabara ta fado mata. Tana dosowa kofar gidan, ta hangi kamar ana hada hadar jama'a, duk da dare ya fara yi, kana iya gane wa ana sha'ani a gidan. Bata yi wa kowa magana ba,a haka suma babu wanda ya shaidata. Sai da ta shige xauran karshe ta aje kit dinta, ta xauna akai ta hade kai da guiwa ta kirkiro kukan dole ta shiga yinsa har da shesheka, sannan hankulan masu wucewa ya fara xuwa gunta kuma, Ya ali shine mutum na farko daya fara dosar ta da tambaya, wai wacece xaune? Gida kike son komawa? A zata son cikin 'yan kawo amare ne, yayi dan murmushi, don ta bashi dariya. Da girmanki da komai kike kauyanci? Dan Allah tashi ki koma cikin gida tun kafain yara su fara miki dariya. Ko an yi miki wani abu ne? Daga ji ta gane mai magana, shi yasa ta dago sosai ta dube shi, kawai batare da tayi magana ba. Gabansa ya tsinke ya fadi xuciyarsa ke ambato sunan, mama? Sannan ya tsugunna gabanta ya furta a hankali, mama! Hawayenta suka kara tsunkewa, ta sadda kai, tana gogewa da bayan hannu. Innalillahi wa Inna illaihir raju'un! Ya waiwaiga babu mai kallonsa yayi sauri ya ja mayafinta ya rufe fuskarta, yace, taso muje, kar ki bari kowa ya ganki. Ya ja hannunta suka sulale dakinsy Danlami. Babu kowa cikinsa, duk suna can wajen fatin da sukeyi da abokansa. Ya xaunar da ita gefen gado ya tsugguna. Yace, yaushe kika dawo mama? Baki na rawa ta amsa, yanxun, idanuwansa suka kawo kwalla a raunane. Yace abinda kikayi kin kyauta kenan mama? Da mtuncin ki da komai? Iyayen mu masu girma da daraja a gurin jama'a, kika tozarta su? Haba mama, kamar baki sami tarbiya ba? Ta goge kwalla. Tace, ba haka bane, Ya ali me yasa zaku rinka ganin laifi na ni kadai? Nace ga wanda nake so, ba sai a ba ni shi ba. Ina ruwan kowa da rashin asalinsa? Ai dai ba daga sama ya fado ba, da uwarsa da ubansa. Yace, Maganar banza ce wannan mama, don na tabbata Daliti bai fi miki iyayenki ba. Kin kuwa san halin da umma ke ciki tun ranar da kika sa kafa kika bar gidan nan? Kin daure min kai, ban taba xataon zaki aikata irin wanan mummuna aiki ba. Tace hakan kadai xai memin mafita kuma akan bakana na dawo ko Danliti, ko su rasa ni baki daya. Ya xura mata ido, yana kada kai. Afuwa ya kamata ki nema ku sulhunta da iyayenki, su sa miki albarka, ko kin ga rayuwa mai kyau da anfani nan gaba. Saboda haka ki xauna anan ki jirani, xan shiga wajensu in kwantar musu da hankali tukina, gaskiyya bana so ayi miki taratsi cikin jama'a, kuma gidan cike yake da baki. Baki? Me akeyi a gidan? Ya amsa, biki na akeyi dana seed. Kana nufin kunyi aure? To Ya xanyi, tunda kinki ni Mama? Akan dole na yi auaran nan, su Baba sun matsa min. Ina muku murna, nima Allah yasa ni a danshinku. Ya xura mata ido gwanin tausayi. Yace, nasan ba xaki ji komai a ranki ba, tunda ba so na kike ba, amma ni har kwanan gobe ina sonki, shi ya sa abinda ke faruwa da ke ya xame min ciwon cikin raina, ki yiwa girman Allah mama ki sanya tunanin ki dawo sak! Yadda kowa ya sanki. Karka damu dani Ya Ali, ko da yaushe ina gaya ma kai dan uwana ne, kauanar mu ta jini ce mai asali. Kwanciyar hnakalina kuwa Danliti ya zama mijina. Ina fatan iyayen Al-ameen sunyi xuciya su fasa? Ko baka ji komai akai ba? Ya xuba mata ido yana mamakinta, ya jima bai amsa ba, kafin yace, Al-ameen ya koma Rasha da ciwon xuciya Mama..... Ta katse shi ido rufe ta dafe kirji. Tace, nagode Allah! Har naji sanyi cikin raina. Ya kada kai yana kallonta. Yace, baki masa adalci ba, baki tsoron amanarsa ta ciki? Akan me? Bafa dole bane na aure shi, ina son kowa ya gane wannan, kawai kaje ka gaya masu na dawo din, kaji me xasu ce? Yace ni ne nayi niyyar yin hakan, ba sai kin bani umarni ba. Yi hkr Yaya, bai tanka ba, ya tashi ya five, ta bi bayansa da kallo tana fadin cikin ranta, je ka dawo, duk na kosa in san babin da nake. Cikin dakin yayi sallama, abba ya amsa masa yana kokarin hadawa Umma shayi ta samu ta dan sha, ya akayi Ali? Ya xauna gefe kusa da shi, yace babu komai abba, wata alfarma naxo nema wajenku. Hankalin abba ya dawo gare shi, yace ina jinka. Allah ya sa batafi karfi na ba. Ya kada kai ya amsa, bata fi ba Abba, duk mai laifi idan ya nemi afuwa, me yakamata ayi masa? Ya dube shi da kyau da mamaki yace, ayi masa afuwar, domin Allah yana son masu yafiya ga bayinsa. Su kuma masu laifin su yi alakwarin ba xasu sake komawa ga wancanm laifin ba. Laifin me kayi? Ya amsa, laifin mai girma ne Abba, a misali Mama ta dawo ta nemi gafara, abba xa ka karbi tubanta? Ba abba kadai ba harda Umma dake kwance ta xubo masa ido, abba ya jima kafin ya numfasa. Yace Bansan dalilin da yasa ka min tambayar nan ba, amma ina so ka sani, mama ta aikata laifi mafi muni a shafin tarihin gidan nan, da mu karbeta da kar mu karbeta, bakin fentin da ta shafa mana yana nan baxai goge ba, ina so ka sani Ali, xaiyi wuya a fadin gari na Mama ta sami wani mijin, face katon daya dauke ta ya boye wani wuri tsowon watanni 3. Abu na karshe da nake so ka snai, shine bai kai kadai ka rokeni ba. Al-ameen ma ya rokar mata gafara kuma nayi masa tare da alakwarin ba xanki karbarta ba. Saboda haka ka kwantar da hankalinka, muddin Mamma ta dawo gidan nan, ba xan ce ta koma ba, haka xalika idan bata sauya ra'ayinta ba, ba xan ce mata a'a ba, Allah na kallo, nayi kokarin na, don nuna mata hanyar kwarai da samun abokin zama na kirki mai kyan asali. Ko duniya ta zageni, alhakin Na suka duka kuma zamuyi shari'a da su gobe kiyama. Kawai ji yayi kwallah na xubo masa, saboda tausayin Abba, yasa hannu ya goge, abba ya riga shi sake magana, ka daina kuka Ali, kaddara ce, tashin hankalina daya, mahaifiyarta da ta kasa samun nutsuwa. Ina jin tsoron kar ciwon xuciya ya kamata kamar yadda likitocin da ke duba ta suke gargadin ta kullum. Dalilin da yasa kenan nake fatan Allah ya sa mama ta dawo, watakila ya zama waraka ga mahaifiyarta. Na tabbata hankalinta xaifi kwanciya idan tana ganin ta koda a dakin auran Danliti ne. Ya Ali ya gyara xama yace, gaskiyya ne abba, kuma naji dadin bayanan ka. Saboda haka ina mai farin cikin shaida maku cewar mama na nan ta dawo. Abba ya xura masa ido. Umma kuwa ciccibawa tayi ta tashi xaune. Ba fahimce ka ba Ali? Inji Abba, yace Mama na nan a cikin gidan nan, idan kun ban izini, zan shigo da ita ta roki gafararku. Suka dubi juna shi da Umma baki sake, tuni hawaye suka tsinke mata, tana kada kai tare da salatin Manzo. Abba ya dube shi yace, je ka ashigo da ita Ali. Har ya mike ya sake komawa ya xauana, yace Abba ina fatan ba xaku daga mata murya ba, kasan gidan na cike yake da baki. Yace Insha Allahu, ba xan daga mata ba. Yace nagde abba. Ya mike ya wuce, abba ya bishi da kallon, sannan ya dubi Umma, ashe haka Ali ke da hankali? Nayi kuskuran hana masa auran Mama tunda farko. Umma ta goge hwaye tace, hakika mama tayi asara masoya 2. Haka Allah ya so, ba mu da abinyi, dai yi masa godiya, abba ya sauke numfashi, sukayi xugum suna sauraron ta yadda mama xata bayyana garesu. Jimawa kadan suka tsinkayi muryar Ya Ali yana fadin ki shigo mana! Na gaya miki komai ya wuce, ki shigo kawai. Make-maken munafurci takeyi ba wai ainihin tsoron bane cikin ranta, da su abba xa suyi kuskuran cewa ta juya, fes! Zata juya babu waiwaye sukayi sallama dakin. Ya ali na dauke da kit dinta. Ta toge bakin kofa, yasa hannun ya janyo ta har gabansu abba dake sake da baki suna kallon abin al-ajabi. Gata abba, umma ga Mama, ku mance da abinda ya faru, ku amince da xabanta, ku sa musu albarka, sai kuka ga Allah ya basu zuri'a abin alfahari. Mama ki durkusa ki roke su gafara. Ko dama a durkushen take kuma tuni hawayen suka tsunke mata, murya na rawa, tace.. [12/01 19:16] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 2***12 Abba kuyi hrk, Umma ki yafe min. Abba ya numfasa yana kada kai. Ya ce a rayuwata gaba daya Mama ba tba xataon xaki min irin wannan mugun butulcin ba. Na dauke ki 'yar da na dauki burin duniya na dora a kanki. Kece kika bambamta da kowa cikin xuciyata, kuma na nuna miki dukkan gata amma dare daya, kika numa mana akwai wanda ya fi mu muhimmaci a rayuwarki. Tabbas na yarda da hakan, don a tunani na xan ga kin dawo kin bushe a lalace saboda tunanin kin barmu cin BAKIN CIKI sai gaki Fes! Kinyi kiba. Ban miki baki ba, ba kuma xan miki ba, amma ina mai tabbatar miki in rasa masoyi, kin rasa mai tsanin kaunar ki tsakani da Allah, kuma a yau na kara nadamar hana Ali auaranki tun farko. Maganata karshe itace, tunda kin nace sai Danliti to ki gaya masa ya turo magabatansa, muyi magana, sannan kiyi wa Yayanki Ali godiya, domin yayi miki dukkan taimako. Zaciyarta fara sol! Jin Abba ya ambato Danliti ya turo. Ta kara dukawa tana goge kwalla. Tace, ngde abba, kuma ina kara baku hkr, don Allah ku yafe min. Ta rarrafa gun Umma ta cusa kanta jikinta, umma kiyi hkr! Ta share hwaye tace ai ya wuce Mama, kinci albarkacin al-ameen da ali. Amma gyara kayanka, ai baya zama sauke mu raba ba. Ki bi duniya a sannu, domin ita duniya budurwa ce mai kyale-kyale da yawa, da zarar ka biye mata, to ka bace ka kuma shiga uku ka lalace. Ban da abin kari a gareki, don nasiha anyi miki, amma kin rushe saboda batan basira. Allah ya ganar da ke, ya sa ki a hanya madaidaiciya. Ya ali ya amsa da amin, yayin da mama ke ci gaba da gugar hawaye. Alin ne ya cigaba da cewa, don Allah abba karku nuna kowa ta dawo har tym din bakin nan xasu koma. Ko su Baba a kyale su tukuna. Ke mama ina son ki cigaba da xama cikin dakinku dan Allah, na san xuwa gobe da yamma kowa xai watse, sai a kam magana ta gaba, kinji? Ta amsa da kai, Abba yace shikenan Ali, kana son ka rufawa 'yar uwarka asiri, asirin kuwa da ya riga ya tonu. Yace kayi hkr dai abba, yace babu komai, ta tashi ta koma dakinta, idan tana jin yunwa, akwai abinci, yace xaki ci abinci ne? Ta kada kai, to taso na raka ki dakinki. Umma mun gode, tace Allah yayi albarka, ya amsa da amin. Tare suka mike suka bar dakin. Umma ta tafa hannu tana salati, sannan ta buga tagumi. Yanxun alh. Danliti xata aura? Yace, t ya xamuyi, wa kike ganin xai fito neman auranta, bayan ya san wannan kwamacala? Haka nan xamu hkr da abinda Allah ya kaddaro, yanxun dai bana ce ya turo ba? Sai mu sa ido mu ga wadanda xai turo din. Ta numfasa, tace Allah shi kyauta yace amin. Ke dai ki kwantar da hankalinki, ki daina xa damuwa a ranki don Allah. Tace naji alh. Ya ciga ba hada mata shayin suna tattaunawa. Kamar yadda ake tattaunaea da mama da Ya Ali. Shawarwari kawai yake bata, tana sauraronsa kamar gaske. Har kusan sha daya da rabi suna tare. Dagab bisani yayi mata sallama ya barya cike da farin ciki da baya misaltuwa. Nan da nan ta fada bayi tayi wanka, ta kintsa jikinta ta kwanta. Kewar Danliti ta lullube ta, fadi take cikin ranta, ba dan dare yayi ba da naje yiwa sweety Na albishir. Da kyar barci ya sace ta saboda murna. Washe gari hidima taci gaba, mama na cikin dakin na kulle babu wanda ya san ta dawo, daga Ya Ali sai su Umma. Kuma anyi sa'a taji maganar Ya Ali batayi marmarin fitowa ba, sai shi ne ma ya kan saci jiki ya shiga wajenta, ya ganta yaji dan ji sanyi aransa. Allah sarki! Garin dadi na newa, iska na ta wahalar da mai kayan kara, bayan sallahr la'asar baki suka koma muhallin su aka bar amare da angwayensu. Shi kuwa Ubandawaki 'yan uwansa ya tara falon baki yace, naki ku ne a matsayin ku na kannena na in shaida muku cewar Mama ta dawo daren jiya, kuma har na yanke hukuncin ta gayawa Danlitin ya turo magabatansa, muyi maganar aure. Ban san yadda zaku karbi abin ba, ko da mahimmanci ko ya zama abin dariya a gareku, duk daya ne, ni dai na fita hakkinku. Suka dubi juna cikin sigar tsarguwa, sannan Alh.basir yace, ai shikenan yaya, amma banji dadin yadda kayi mana fassara ba, ya kamata kayi mana uxuri tunda mun ce maganar nan bada wata manufa muka fadeta ba. Amma ace mama ta dawo tun jiya, sai yanxun mukeji? Ba komai. Alh. Adam ya cage, tabbas naga Danliti a shagonsa, sai dain banyi tunani tare suka dawo ba, tunda banji labarin ba a cikin gida. Sai dai Yaya a gaskiyya muna so mu ganar da kai cewa ba farinciki mukeyi da abinda ya sami mama ba, mutuncin gidan nan, ai duk namune, me zai sa muyi murna da rugujewarsa? Abba yace duk naji, magana ta gaskiyya, Allah kadai yasanta, don shine masanin sirrin xukata. Abinda ya sa bau san Mama ta dawo ba, sai yanxun. Ali ne ya fara ganinta kuma ya xo ya sameni guiwa 2 ya roke ni da kyale mama kar in daga murya, saboda baki fa ke cikin gidan nan. Idan sun tafi ayi su wacce xa ayi. To maga ma ta kare, nacewa Danliti ya fito a daura musu auran, su karata. Allah dai ya gani ba da son raina bane. Fuska Ya mutse Alh. Basir ke cewa, Dan liti xata aura? Yace bamu da abinyi, haka Allah ya so, sai dai muyi mata fatan alkhairi. Saboda haka bana son abin yayi tsawo, yana turo sai aure. Ya turowa za'a sa rana kuma ba zata wuce sati 3-4 ba duk abinda Allah ya hore min shi xa'a kai mata. Ita kenan maganara, kowa na iya tafiya harkokinsa, mu saurari xuwan magabatan nasa shikenan, Allah ya nuna mana. Haka suka fadi baki dayansu. Abba ya amsa da amin, suka bar falon ba yabo ba fallasa, cikin xukatansu, ma'ana intayi ruwa rijiya in ba tai ba masai. Suna shuga sasan su, suka bajewa iyalensu babu bata tym suka fara xuba sharhi. Haj. Gake kuwa har da guda. Daga bisani suka baxama sassan Uban dawaki, don gain Mama tare da yiwa Umma murna dawowar Mama fida, amma a zahiri a cikin xukantasu yanayin Maman suke son gani. Suka kwarara sallama, umma ta amsa, sai mukaji daddadan labari! Ina maman? Inji Haj. Hajjo, tana dakinta, gaba daya sukace Allah shi kyauta na gaba. Yanxun da Danliti xa'ayi auran? Tace, nufi ne Allah, duk abinda ya rubuta bamu isa mu goge Ba. Haj. Hajjo tace gaskiyya ba haka muka so ba. Sai dai hkr kwai. Haj. Gaje ta tabe baki tace, ya xama dole, amma a hakikanin gaskiyya mama ta bamu kunya. Ajin ai ba daya bane in banda batan basira. Koda yake ance so mako ne. Allah ya sanya alkhairi. Sukayi dan shiru, kafin suka nufi dakin Mama, ina kike? Kina jin mu amma ba xaki fito ki gaishemu ba? Tana xaune gefen gado, ta fesa ado kyanta ya kara bayanna, banda haka da ibar da ta kara suka kalli juna sabe da haba, kafin Haj. Gaje ta soma xuba, lallai Mama, watau hankalinki a kwnace kika je, ki ka dawo! Wannan kiba haka? To Allah yasa ki sami irin wannan a gidansa. Haj. Hajjo ta amshe amin dai, kin dai riga kinsan halinsa, komai yayi miki sai ki hadiyewa cikinki, kar ki doshi kowa, tunda kin nace shi kike so! Ko kuwa gaje? Tace haka yake yaya, ai kowa ya sayi rariya yasan zata xubda ruwa. Mayafinta dake bisa filo ta figo ta mike tsaye ta xura takalmanta tayo waje tana yafa gyelenta, ta barsu anan sake da baki, suna kallon juna. Ko kinga dibar albarka? Inji Haj. Hajjo, Haj. Gaje tace, mamaki kikeyi Yaya? Karfa ki manta watanni 3 ta shafe a bariki, an kuwa ce xama da madaukin kanwa, shike kawo farin kai. Mu meye namu? Ta malam ai bata wuce amin. Can suka sameta dakin Umma tana neman izinin zuwa wajen Danliti, don ta shaida masa sakon abba, suna isowa, umm ana fadin bance kije ki xauna ba, mutunciki shine ya biyo ki nan kofar gidanku. Saboda haka daga yau kar na sake jin kin koma shagonsa. Tace, to Umma, insha Allah yanxun xan dawo. Ta sa kai ta fice, ba tare da Umma ta kara wani abu ba. Nan su Haj. Hajjo suka xauna suka cigaba da kwasar tsegumi, ita kuwa tana fitowa xauran farko, angwaye ta ci karo dasu, saeed Ya maka mata harara, ya wuce abinsa cikin gida. Ta dubi ya Ali, tace me nayi masa? Yace kin fi kowa sani. Taja dogon tsaki, aikin banxa, to shinme me? Don ya ki min magana? Yace, kin baci da Rashin K mama, me yasa? Da ba haka kike ba. Ta dan tabne baki tace, ni ina da wurin xauwa, ba na fito magana da Ya Saeed bane. Yace amma ba kije kinga amare ba.

Chapter 16 of 28