Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Xanje ai, so nake in sauke wannan nauyin ko ni,a na kama dahir. Yayi dan murmushi yana kllonta, mama kenan, to a dawo lfya, nasan sakon bai wuce na Danliti ba. Tayi 'yar dariya. Shi ysa nake sonka Yayana, bari dai in dawo amaryarka ka xan fara xuwa na in gani. Ta wuce tana cigaba da dariya, ganin yadda yayi tsaye duk jikinsa ya mutu. Ya bita da kallo, sannan ya kada kai, yace, ni ma ina mutuwar sonki Mama. Ina ma ace hankalinki xai dawo gareni? Ya sauke numfashi ya shige wajen amaryarsa. Bakinta har kunne take sallama kofar shagon, ayuba ta gani xaune ckin shagon ya amsa mata cike da fara'a amaryarmu kenan, ya gajiyar tfya? Tace tabi lfya, ina mutumin? Ya amsa yana ciki tun azahar yake barci saboda ragwanci. Ta fara dariya, lallai kuwa ragwanci, barin inshiga dole ya tashi ya bani goron albshiri. Ta wuce ciki, ayuba na fadin, ya dai kamata ya tashi ko salla ya samuyi. Kan tsaye bisa katifar ta fada, ta dada masa duka cinya, don Allah tashi rago! Ka wani baje kana gugar barci, ni ina can ina tunaninka. Ya bude ido firgigi yana kallon ta jim, sannan yayi dan gajeran tsaki. Yace kash! Wlh ba don ke bace, marin Mutum zanyi. Kin ji dadin barcin kuwa? Tayi far da ido, tace ko? To ka tashi, na tabbata dadin barcin bai kai albishir din baki na ba. Ya xuba mata ido yace fadi ina jinki. Idan kuma bai fi ba, kinsan Allah sai na sanya ki kuka, ai kin san gamuwar mu babu tausayi. Tayi 'yar dariya, tace, haba duk wannan kukan wasa nakeyi, kama daina hura hanci. Yayi murmushi, haka kikace? To shiknen, fadi ina jinki. Ta gyara xama albishirnka? Yamasa goro. Xaka bani Ah! Me xai hana? Ke dai gaya min inji. Abba yace in fada maka ka turo, ranar auren mu za a sanya. Ya xuba mata ido, ya kasa ko motsi, kayi shiru? Ya sa hannu 2 ya mutsutsuke idanuwansa yace, dan Allah karki xalayeni! Ta ware ido, kana nufin baka yarda ba? Gaskiyya ban yarda ba, yaushe Abba xai yarda ya bani ke, bayan ya san bani da kowa a garin nan? Sannan suna min kallon dan... Tayi wuf ta rufe bakinsa, sau nawa xan gaya maka ka daina dorawa kanka maraici? Ina sonka Danliti..... su abba kuma sun amince ka turo asa mana rana da gaske na ke gaya maka maganar nan ba wasa ba da sauri ya figo ta jikinsa yayi wani irin ihu wai shi murna ayuba ya kwaso a guje ya fado dakin ya same si kankame da juna dan haka. Bai tsaya tambayar komai ba ya juya ya fita yana kada kai cikin ransa yana fadin "Danliti akwai dan iska"ya jima bai kyale mama taci gaba dayi masa bayani ba yanzu yaushe. Zaka turo? Ya yunkura ya tashi zaune yace bashine matsalar ba wadanda zan turar sune matsalar ta dan bata fuska tace ai ba za ka rasaba "Danliti ko yan dattijan daku ke gaisawa sun isa su wakilce ka ko kuwa? Ya zura mata ido duk sun juye, yace haka ne sai ki baru in gan su mudaidaita tukunna sannan in gaya miki ranar daza su zo ko" tace shi ke nan bari in kwashe sauran kayana in koma gida ya kara matsarta haba tun yanzu ?" Umma ta ce kar na dade kuma tunda sun amince da kai ai zaka rinka zuwa ne kan ka tsaye,"ya kankameta ya na fadin haka ne amma ban so ki tafi yanzu sonki kawai ke azabtar da ni ina kewarki da yawa jiya da kyar nayi barci kinji yadda ki ke tashin kamshi?gaya min dame dame ki ka shafa in karo miki irinsu?"Bata iya bashi amsa ba don tun tafiyar su yake koya mata irin wannan renon ya gama da rayuwar ta gaba daya kai ALLAH ka raba mu da sharrin masu sharri,magariba ta wuce wadan da sukaje masallaci ma sun koma gida yayin da mama ta fito daga shagon Danliti jaye da katuwar jakar kayanta. -yar tafiya kadan ya taka mata ya dawo abinsa bata sami dan dakon da zai daukar mata kayanba ba don haka da kanta tayi ta ja har gida abba da umma na zaune a falo dauke da bakin ciki maras misaltuwa mama ta turo kofa ta shigo sa sallamar ta dauke da uwar jakar kaya babu wanda ya amsa mata ta wuce ta gabansu ta tsugunna tace sannu abba, wani irin kallo yayi mata mai isar da sakon haushi da takaici kafin yace daa ina kike?ta dan sunkuyar da kai tace naje gaya wa Danliti sakon ka ne ai na gayawa umma kafin na fita ko um..."Ya daka mata tsawa rufe min baki don ALLaH shine zakije ki zauna har bayan magariba kiji tsoran ALLAH mama ki sani cewar mutuncinki ki ke zubarwa wannan uwar jakar da kika shigo da ita tawace tukuna? idanuwanta suka kawo kwalla ta fara rawar murya na...nawa ne.. Kayan da...Danliti ya siya min ne yace to ba a gidan nan ba idan yazo ki maida masa kayansa ya baki can gidan sa,ai kinji ni ko,?ta amsa da kai umma ta cire tagumi ta kare mata kallo sannan tace Alhaji ya kamata a tuhumi yarinyar nan idan idan tabada kanta gareshi kasan istibira'i ya kamata, kafin a daura auransu domin ni banyarda da mama ba a yadda suke tare da yaron nan,ya numfasa ciki da bacin rai yace ki na da gaskiya don ni ma wallhy ina wasi wasi cikin raina ke mama ki gaya min tsakaninki da ALLAH ki fi jin tsoran sa akan komai na duniya ki gaya min gasjiyar abinda ke tsakanin ki da Daliti kar kisa muyi kuskure da gangan idan kin san da wani abu to ki gaya mana mubi tsarin da ALLAH ya shimfida. -sosai ta goce da kuka murya na rawa tace ALLAH abba babu abinda ya shiga tsakanina da shi duk sukayi shiru suna dubanta kamar sun gaskanta ta kamar basu yarda ba amma dolensu yarda tunda basu da wata hujjar kama ta don haka abba ya daka mata tsawa ya isa don ALLAH tana wani bare baki kamar mummuna tashi kiba mu wuri kuma na gaya miki yana zuwa ki maida masa jakar kayansa,ta goge hawaye ta dan sunkuyar da kai tace yace ya gode insha ALLAH zai turo din suka yi banza da ita shiyasa da dago ido ta dube su uwar hararar da ta yi arba da ita tilas tasa tayi saurin maida kanta kasa jim sun kikara cewa komai yasa ta mike simi simi ta janye jakar ta, ta wuce daki bakin nan tamkar na agwagwa kai tsaye bayi tashige tayi wanka ta dauro alwala ta fito ana ta kiran issha'i,don haka tana yin magariba ta dora issha'i bayan ta kammala ta fito neman abinci nan falo sukayi kicibis da yaya ali wai me ki ke nufi baza kizo kiga amarya ba?ta kama kugu hannu biyu tace wannan amarya an damu nazo na ganta hala tafini kyau ne ya kama dariya kafin yace soosai kuwa tafi ki kyau muje ki ganta tace haka yake amma duk kyanta dai ni aka fara so kifin ita saboda haka a daga min kafa inci abinci tukuna"kalamanta sun ruruta wutar zuciyarsa ba kadan ba koda ganin yadda jikinsa ya saki kasan ya fada wani yanayi ya zura mata ido hannayensa rungume a kirjinsa murya sanyaye ace zancan ki dutse yar uwata,. [12/01 21:52] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 2***13 hasalima rashinki yasa na aure ta koda yaushe ki kace da ni kule da sauri xan ce cas mama don son ki ya zauna a raina, tayi yar dariya tace yaya ali ke nan kar kasa amaryar ka ta tsane. Ni daga wasa sai ka hau jera zance!ba haks nake nufi ba yaya ali muje kawai naga amarya in na dawo na ci abincin bata jira yace wani abuba ta yi gaba abinta tilas ya biyo bayanta yana kada kai!Amare kam masha ALLAH suna dauke da tasu baiwar da ALLAH yayi masu musamman aminar yaya ali har mama na masa tsiya wai ya kamata ya maida sunan sa aminu dan su kara dacewa da juna kallon ta kawai yake yi cikin ransa shi yasan babu wacce tafi dacewa dashi face ita kanta maman,bata wani dade ba ta dawo sasan su ta dauko leda cike da kayan garar amare bayan ta gama cin abinci ta zauna gaban madubi tayi wa fuskar ta kwaskwarima tayi zaman jiran Danliti har barci ya fara dibarta bataji aiken yaro ba,ta kwana zullumi da juyayin abinda ya hana Danliti zuwa alhalin ya sami izinin yin hakan ko har yanzu bai amince wa ransa bane?ya gudun kar yazo ya fuskanci wulakanci!wannan tambayar taso ta hana ta barci domin ta kai sama da karfe dayan dare bata sami barci ba,Da sassafe ta tashi da ciwon kai wanda ya haddasa mata jiri akai akai duk da haka ko karyawa bata yiba karfe bakwai da rabi tasa kai ta fice babu wanda ya sani ta nufi wajen Danliti dauke da ledar kayan garar amaren da aka bata jiya ita ta tashe shi barci ya tashi a gigice yana tambaya lafiya kika bugo sammako haka?tace nayi zaton zaka zo jiya hira me ya hana ka zuwa. ya ja dogon tsaki ya kauda kai jim sannan ya juyo ya dubeta wai me ke damun kine?ba kinzo nan ba sai bayan magariba kika tafiba?to kuma me zanje in yi maki saboda ALLAH ta zura masa ido ya kare mata kwakwazo nan take idanuwanta suka tara kwalla murya na rawa ta ba haba Danliti laifi ne don ban gan kaba na biyo in duba ko lafiya?ya bita da kallo tana ta gugar kwalla ya kece da dariya kamar mahaukaci hakan yasa ta daina hawaye ta zuba masa ido yayi dariya mai isar sa sannan ya natsu shima ya bita da kallo to meye abin kuka ni ina can ina ta billayin neman mana waliyai ai banga ta zaman fira ba sakeena"nan da nan ta hadiye tashin hankalinta ta fara murmushi duk kin wani daga hankalinki don baki ganni ba jiya kawai " kawai ne? In gaya maka dai dai da sakwan daya bana son zama babu kai,yayi wata budurwar dariya yace ko to na kara baki tukuicin kaina ta kwanto masa tana dariya kasan ALLAH da ciwon kai na tashi ga wani jiri na diba na amma na kasa daurewa na fito ko karyawa banyi ba, yace ai ya bebi na sannu ko ya kamata mu karya ki sha magani bari inzo. Ya fice ya bar ta kwance bisa katifar wucewar minti ashirin ya dawo da soyayyun kwai da naman kaza da doya itama hade da kwai ta hada masu shayi suka batse cikinsu harda ayuba anan ta yada kafada daga fira barci ya kwasheta Danliti ya dawo shago ya zauna tare da ayuba ya zura masa ido yace don ALLAH ka tasheta ta koma gidan su yayi banza dashi ya fito yana zuba fito kamar katon arne. -Ayuba ya kada kai yace karshen alewa kasa Danliti idan an ciza a rinka hurawa ya ballo masa harara ya ce ba ruwanka malam ka kyale ni in ci lokacina ya tabe baki yace na barka zaifi kyau suka yi shiru kowa na harkan gabansa, a gida kuwa tunda suka shafa babu mama a dakin ta suke ta kwasar BAKIN CIKI don sun tabbata tana can shagon Danliti karfe tara uban dawaki ya gama shirin sa zai fita ko karyawa bai yi ba saboda tsabar takaici yasa umma ta fito masa da jakar kayan da mama ta shigo dasu ya sunkuta yayi waje da ita kalla ya tarbe shi da sauri ya amsa ya bude but ya saka Abba yace minna zasu tafi amma zasu tsaya shagon Danliti, kalla yaja mota suka wuce yayi fakin kofar shagon abba ya umarci daya fito masa da jakar nan kai tsaye ya wuce shagon lokacin da su Danliti ke ta harkokinsu yayi tsaye babu sallama har hankulansu suka juyo gareshi Danliti ya matso yana fadin sannu alhaji ina kwana yace nasan mama na nan tare da kai ina take baki sake yace tazo amma ta tafi yayi jim yana kallonsa kafin yace ba shi ya dame ni ba wannan ya rage kuda ubangiji ina fatan. Ta gaya maka yace ta gaya min kokarin da nakeyi ke nan na samu na turo yace kar ka bata lokaci domin na kosa na kauda kazantar da nake gani ya dan sunkuyar da kai yana murmushin izgilanci naji abba in ALLAH ya yarda zuwa anjima ko gobe zan turo yace shike nan ina sauraronka amma ga kayan ka nan ka aje idan ta tare gidanka sai ka bata ba na bukatar komai daga gareka sai sadakin da ALLAH ya wajabta ga jakar nan bai saurari wani abu ba yasa kai ya bar shagon ya fada motarsa kalla ya ja suka dauki hanya Ayuba ya matso gare shi yace, Allah na tabaka dama, don ka gyara kuskuran ka Danliti, kar ka bari ta subuce maka, ka dawo kana cizo yatsa. Ya watsa masa harara yace bana bukatar wa'azinka alaramma karfa ka manta da ni da kai duk daya ne. Na ma dai san abinyi, ayuba ya xuba masa ido ya rasa ta cewa babu abinda ya sami Danliti, yasa hannu ya dauki jaka ya shige da ita. Hannu 2 ya rike kugu, yana kallon mama xucyarsa na masa sake-sake. Kusan 5mins yana tsaye, sannan ta tsugunna ya bubbugata. Ta farka tana yamutsa fuska, menene? Tashi kiji? Ta yunkura ta tashi xaune, yasa hannu ya kara janyo jakarta, don ta ganta sosai. Cike da mamaki tace waya kawo ta? Yace, abbanki mana! Wannan kadai ya tabbatar min baya sona, baya kaunta. Bai dameni ba, amma me yasa zai uzzura min dole sai na turo magabata na yanxu-yanxu? Hankalinta ya tashi, ta matso a hankali ta dafa kafadarsa. Don girman Allah kar hankalinka yatashi Danliti.... Cikin sababi. Yace ki daina gaya min wannan maganar! Kora da hali abba ke min, saboda haka ki hkr, kije su baki wanda suke so! Tashi ki bar dakin nan, kar kuma ki sake xuwa, ni babu ruwana! Ta narke da kuka, murya na rawa tace, karka yi min haka Danliti, ina mai tabbatar maka xan kashe kaina idan ka juya min baya. (Kuji banza mtsw ). Ya cire hannunta daga jikinsa yace, ni ban aikeki ba ya kamata ki gane ki gane ba dole bane na aureki. Don me xa a daga min hankali akan magabata? Banda su, uban wa xanje na tura idan ban nema ba? Kinga ki tshi kije ki gaya musu na fasa. Ta marairaice kamar ranta xai fita ni ina sonka Danliti ba xan iya rabuwa da kai ba, ai dai ni xa'a daurawa aurenko? Xan gaya musu su kyaleka, sai ka shirya. Shikenan? Ya kara murtue fuska, yana kallonta bai tanka ba. Takara matsarsa sosai taci gaba da fadin, muddin suka ki yarda da uxurinka wlh na yi rantsuwa xasu sha mamaki dan wlh nan xan dawo na tare..... Ok, ki sa a daureni kenan? Tace wa xai daureka? Don Allah ki kyaleni ni bana son surutu, tashi ki tafi kawai, sai na nemeki! Dan..... Ya daga mata hannu, idan baki so raina ya baci to ki tashi kawai ki bar dakin nan! Ta cigaba da share hawaye, ta xura takalmi ta dauki mayafi ta mike xata wuce, amma ta kasa, tayi tsaye tana kallonsa, don Allah kayi hkr Danliti. Ya dago ido ya dubeta, hawaye keta ambaliya, yayi dan jim, kafin yace nayi hkr, amma kije tukunna xan nemeki. Xaka xo gidanmu? Eh xan xo ki share hawayen, ba wani abu. Ta share da sauri ta duro bayansa, Nagode Danliti na! To kayi dan murmushi mana ko naji dadi mana. (mayya ) Ya banbare hannayen ta ya mike tsaye, karki damu da murmushina, muje in rakaki, kafin tace wani abu, ya fice, dole ta biyo bayansa, bakin shagon kawai ya tsaya, yace sai nazo ko? Tace, daga nan xaka tsaya? Xan wuce neman wadanda xan turo din ne. Nan da nan sanyi ya ratsa mata xuciya, baki har kunne. Tace, Allah sarki nawan, to sai mun hadu anjima. Ya daga gira yana fadin, sai mun hadun, yana sakin tsaki. Tana shigowa dakinta, ta shige, motsinta kawai Umma ta jiyo ta biyo ta dakin, tana kokarin cire kaya, don shiga wanka. Umma ta kare mata kallo, ta kada kai, tace don girman Allah mama ki rinka xama a gida. Tunda Danliti na sonki kuma abbanki ya bashi dama ai shi xai biyoki. Kullum inaga ya miki babu mutunci ga 'ya mace ta rinka bin saurayi har makwancinsa. Ko bai aikata miki komai ba jama'a ba za su dube ki da mutunci ba. Me yasa Danlit ya sauya miki tarbiya.? Tayi shiru tana ciccika tana batsewa, Umma tacigaba ni rokonki nakeyi, ki taimakemu ki taimaki kanki, don mu tsira da 'yar martabar da tareg mana a idon jama'a. Kinji? Ta amsa da ka, kafin tace, Umma idan abba ya dawo ki fada masa ya daina matsawa Danliti akan turo magabatansa...... Ta katseta kamar ya? To umma tunda an gayama sa kuma ya amsa xai turo din, ba sai asa masa ido ba? Ta mako mata harara, bangane asa masa ido ba? Shi daman can bai shirya auran ba, ya hanaki sauraron wandan ya shirya? To baku isa ba, mu ba wasa mukeyi ba, tunda ya hure miki kunne dole ya gaugauta turowa, ya raba da mu da bakin ciki da muke gani, kinji nagaya miki. Tayi ta tashi tana fadin, to shikenan ai matsa masa ba shine xaisa ya turo din ba. Me kikace? Ta shige bayi da sauri ta rufe kofa. Mama ni kike wa rashin kunya? Lallai kin rika, kina gab da tsinka min mari akan Danliti. Sallamar da jiyo, shi yasa tayi shiru. Ta mike ta fito tana amsawa. Inna saude ce da Baraka, saude sannunku da xuwa. Duk suka amsa, yayin da Baraka ta tsugunna ta cigaba da gaisawa. Bayan sun nutsa a falon, inna saude tace, tun jiya naso fitowa, wani axababben ciwon kai ya addabeni. Tace ayya ina fatan yayi sauki. A'a da sauki, ina maman? Tana ciki ta shiga wanka.... Wai dama saboda ita kika zo? Ai da kin yi kwanciyar ki kin huta, domin al'amarin Mama ya zama jiki. Tace, ya xama dole in taso yaya. BAKIN CIKI kuwa baya taba zama jiki sai dai imani. Allah dai ya bamu ikon cinye jarabawar, ta nisa tace amin. Tace, yanxun me kuke ciki? Ta fada mata yadda al-amarin yake, ta cire tagumi. Tace haka shi yafi dacewa, in ma banda sakarci ba ita xata taimaka mana ya turo da wurin a huta ba. Tace ina fa, ai ina mai tabbatar miki tafi son shi akan mu. Allah dai shi kyauta. Ta amsa da amin. Suka ci gaba da hira har suka ji motsin fitowar Baraka ta tashi ta shige dakin. Ba suyi wata hirar kirki ba, domin ra'ayinsu yasha bambam yanxun. Duk mai zagin Danliti Mama bata ganinsa da kima haka ta fada ma baraka, shiyasa ta shiga taitayinta, tafito daga dakin tace xata ganin amare. Mama dataga shirinta can ta sameta dakin amaryar Ya Ali, nan suka shantake, sama da 2hrs sai da Inna saude ta shiryo tafiya tasameta can, ita ma bata yi ma Mama maganar komai ba akan abinda ta aikata. Domin a tunaninta babu wata bakuwar kalmar da xa agaya mata wacce bata sani ba. A wannan daren mama tasa ido taga xuwan Danliti shiru kakeji yasa ta jin haushin rashin dawowar abba. Al- amarin nata cizon ta taga ba xata daure ba, karfe goma harta goa, ta fito ta bude kofar ta fice abinta. Ko kafin Umma ta fito taga wanda ya bude kofar mama har ta kai kofar gidan, ganin bata a dakin ya tabbatarma da Umma ita ta fita. Ta nemi kujera ta xauna hannunta a kunci BAKIN CIKI ykamar ya kasheta. Take nan taji xuciyarta na ciwo, wani abu dum! Cikin kanta kamar xai makantar da ita, tasbihi ta shiga jerawa ko ta samu saukin kan. Ita kuwa mama Tunda ta kwashi sauri bata sausauta ba sai da taje shagon mutumin nata ta ja birki. Ayuba na xaune daga ciki, taga kanta ta shiga tare da sallama. Ya amsa mata ta wuce tana fadin sweetyna naciki ne? Da sauri ya amsa mata ai bayana nan bai gaya miki bane? Ta tsaya cak dauke mamaki, ina yaje? Ya amsa gaskiya bai gaya min ba, cewa yayi xaiyi tafiya kawai. Na xaci ya gaya miki daxun. Ta kada kai, bai gaya min ba wlh, amma xai dawo gobe ko? Yace watakila, ta danyi shiru sannan tace to shikenan sai goben. Allah ya kaimu. Taga kanta ta fice, ya bita da kallo. Duk tasuayinta ya lullbe shi, aransa yace Allah ya kubutar dake daga sharrin Danliti. To nima nace AMEEN! Da babbar murya. Tana tafe tana sakar xuci, wai duk fushin ne yasa Danliti yatfi ba sallama? Ina xansa kaina idan kalaman Abba suka korar min Danliti? Bata samo amsa ba taji ann fige mayafinta, 'yammata ji mana! Firgigi ta waigo hankalinta ta dubi gungun samarin da suka kai kusan shida, kowanne su dauke yake da tabar wiwi. Ta dora hannu bisa kai wayyo nashiga uku, duk suka fashe da dariya, ina kika nufa mu rakaki? Ta durkusa kuyi hkr dan Allah, dariya kwai suke kyakyatawa, 2 daga cikinsu suka kawo mata cafka. Ta xabura ta mike, Allah ya taimaketa ta kutsa ta cikinsu ta xura aguje, dawa Allah ya hada su ba da ita ba, ta watsar da takalma, ko daman gyalen yana hannunsu, taci gudun fitar rai, ta rufta cikin gida, yayin da alh. Adamu, ke kokarin rufe gidan, bakara min figita yayi ba, amma yayi axama ya maida kofar ya jefa sakata. Mama kuwa tuni tana sassansu, ta fadi warwas! Tana maida numfashi tamkar xata mutu, Alh. Adamu ya biyota, ya isketa daidai kasa, ya xura mata ido kafin yace, wai daman mama ce kartin Maxan nan suka biyota? Me kike a waje har 11pm? Umma tayo waje tana sallami, ganin mama a kasa yasa ta dafe kirji lfy? Ya dubeta ido waje, yace, yanxun saboda Allah me yarinyar nan take a waje cikn duhu? Kinga kartin da suka biyo sunyi su 10, wannan ai diban albarka ne da iskanci. Jiri ya soma dibar Umma tana fadin me? Innalillahi Wainna ilaihir raju'un kasan Allah, Alh. Adamu har na rufe kofa naji motsin fitarta, xaune nake kawai narasa inda xansa kaina dan BAKIN CIKI! Ban san yadda mama ta maida rayuwarta ba......... Tana rufe baki, tayi kasa da dafe kirji, saboda ciwon da yake tsananin yi mata. A hankali hawayenta ke fita tana fadin, BAKIN CIKIN ki zai kashe ni Mama.... Alh. Adamu ya daga murya yana masifa, kin shiga 3 mama! Kin maida kanki 'yar iska da karfi da yaji, to ki bi a hankali, muddin kika bari BAKIN CIKI ya kashe mahaifanki, kin buga babbar asara, tashi ki ba mutane wuri, kafin in taka ruwan cikinki. Ta yunkura ta tashi da kyar, amma ta kasa mikewa tsaye, a duddauke ta shige falo a tym din har mutanen gidan sun fara taruwa, don ji me ya faru, Alh Adamu ke daga murya cikin dare? Nan take ya maida yadda akayi har ya dora karya, wai kartin har sun turmusheta, tsawat da yayi masu, yasa suka gudu. Kowa tafa hannu yakeyi yana salati, kusan 12am suna xuba magana. Sannan kowa ya koma sasansu, aka bar Umma kwance da ciwon abubuwa barkatai. Ya ali ne kadai bai tanka ba, don BAKIN CIKIN sa na gaske ne, tamkar yadda UMMa takeji cikin xuciyarta. Dakin amaryarsa ya koma yana kuka da hawayensa. Amina tayi rarrashinsa tana nuna masa addu'a Mama tafi bukata ba kuka ba. Mts!.... Amina ba zata gane ba, BAKIN CIKIN dake cin angonta ba xai iya jurewa ba, tilas sai ya matse shi. Hasalima ba zai iya zama yana kallon irin wadannan abubuwan ba, gara ya koma bakin aiki ko ya kauracewa idanuwansa ganin abinda ya fi komai daga masa ciwon xuciya. Saboda haka yacewa amina ta shirya kayansu gobe zasu koma birnin gwari da yardar Allah. Al'amarin ya daure mata kai, kuma tayi tambayoyin da bata sami amsarsu ba. Washe gari da suke shirin tafiya, taji fashin baki na bakin Haj. Hajjo. Eh lallai biri yayi kama da mutum. Nan take kumallon mata ya taso mata, ya dasa mata kyamar Mama cikin ranta har tafi Ya ali kosawa su bar garin. 12pm kuwa ya samo shatan mota suka damki hanya. Mama bata ma san anayi ba, tana can tana murkususun ciwon ciki ita kadai a daki. Don ko daya shigo yin sallama da umma bai shiga wajenta ba. Sai wajen azahar barci mai nauyi gaske ya dauke ta. Haka ita ma Umma ke ta gyangyadin takaici bisa kujera. Rabonta da abincin kirki tun jiya da daddare motsi taji a falo ana shigowa da kaya, ta taso da sauri ta leko falon. Kalla ta gani da tsirin kwalaye ya aje gefe yana gaisheta. Ta amsa da fara'a ta karfin hali. Bai karasa ficewa ba, abba ya kawo ka falon tilas ya rabe gefe ya bashi wuri ya shigo, sannan ya fice. Alhajin yana fadin, agaida Iyali, yace xasu ji. Kallo daya yayi wa Umma gabansa ya fadi, ya amsa sannu da xuwan da tayi masa. Ya xauna falo. Yayi da ta shiga kitchen dauko masa ruwa ta kawo masa ta xauna gefe tana kara masa sannu da xuwa. Bayan yasha ruwa ya numfasa. Tace an dawo lfy? Ya amsa lfya lau, duk suna gaisheki, ni ne har abuja, daga can na xarce kd yau da safe. Tace, wai kunsha hanya, ina fatan duk lfya ka baro su? Yace kalau, amma sai naga kamar kin rame, ina fatan ba ciwo ne ya tashi ba? Ta kada kai. Kai dai bari Alhaji, ciwo na ba zai taba warkewa ba, idan ban ga yarinyar nan dakin miji ba. Kaci abinci tukunna, kaji abinda ya faru jiya. Yayi dan shiru har ta mike xata dauko abinci kafi, yace ki gaya min kawai Halima, nasan babu bacin ran da xanji wanda ya wuce na baya. Ta dawo ta xauna ta fede masa abinda ya faru. Ya kada kai. Yace ya rage nata, ba burinta ta fita duk tym da ta ga dama ba? Jikinta xai gaya mata, xata gane akwai wadanda suka fita iskannci. Yanxun tana ina? Tana daki, ni yau ko kalarta ban gani ba. Bata xo ta gaisheki ba ke nan? Tace ni a suwa? Bana ma bukatar gaisuwarta, amma tun jiyan na gaya mata idan na mutu, ta sani BAKIN CIKIN tane ya kasheni. Yace, ba xaki mutu ba Halima da Yarda Allah mama ba zata salwantar min da rayuwarki ba. Karki manta, su hudu kika haifa, kuma Allah ya albarkace su dubi tsibin kwalayen nan, duk sakonki ne, kowa na da sa nau'in tsarabar, zabi kalar abubuwan da kika fiso. Bayan haka, jibi asabar duk zasu hadu anan, don su share mana hawayen kukan da Mama ta samu. Don kuwa zau tsaya tsayin daka dole Danliti ya turo wakilnsa a daura masu aure a

Chapter 17 of 28