Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
lamari..bai zaunaba yajuya yana kokarin fitatace ya maganar abinci?zan girka ne ko za'a na kawomin na sayarwa? Ya kalleta sama da kasa yace,wai ke me kikadaukeni?baki ganin kudin dana kashe a asibiti? Koshagon kikeso ya rushe na tsugunna? baga saurankayan tea a nanba?ki hada mana kisha! Kedamaba'aso ki nannagi abu mai nauyi.mtsssss..... Yajatsaki yayi waje,,,ta koma gefen katifa tana tabe baki...a ranta tana fadin Allah ya huci zuciyarka.tadangyara waje tamaida kai ta kwanta ba'a jima ba bacciya dauketa... Bayan sallar la'asar kukan yaro yatasheta.ta tashi da sauri tabashi nono da ruwa..nandanan yasake komawa barci.tafito tsakar gida tanahamma tareda mikar yunwa..tayi dan shawaginta a tsakar gida takoma daki..tajanyo ledar kayan tea tazuba a kofi tajanyo fulas zata tsoyayi ruwa taji baburuwan..tasaki tsaki ta nufi kichen babu itace ko dayabare ta daura.haka tadawo tasha tea da ruwansanyi..tasake kwanciya dan babu abunda zatayi harqarfe taran dare bataga danliti ba,,bare tasa ran wani abun sanyawa a baka. Ga yunwa tana sha'awar tacimai dan gishiri...nan take tayafa gyale ta zura silifastadauki jariri taja kofa tayi waje ta lallaba a hankalitayi wajen danliti.....yana ganinta ya daurefuska,,,yayinda ayuba ya taso ya karbi maikudi,,meya kawoki?inji danliti tace naji shiru ne ga yunwa inaji.....ba akwai kayan tea ba?we me kedamunki ne? Murya raunane tace nasha wlh..dama ruwan sanyinasha babu sauran ruwan zafi kuma babu itace...maidan gishiri nake sha'awan ci kodan yayane! Ya gyarazama nifa ba ubanki bane,bakuma mijinkiba bare kinadauramin wannan nauyin,,kingane koh?daga taimakosai ya zama tsiya?ki dauki duk nauyinki ki dauramin? to bafa zai yiyuwa kinjiko?karkisake biyoni shago kicenabaki wani abu...abun da nasamu nabaki basai kinmatsamin ba..karki sake dauko danki kizominnan...idan kunne yaji..... Tace yi haquri,,,yacewaayuba bata danta ta koma.ta karbeshi tajuya zatawuce taji yana fadin bata taliya daya taje tadafa karta cinyeni....ta karba tana murna ya wurga mata nairaashirin tasaya itacen..jikinta na rawa ta dauka hardagodiya ta sabo yaronta takoma gida..sai yanxu matake tunanin a ina zata samo icen dare yayi?ta sauqenumfashi numfashi takoma takwanta dayunwarta.dasafe da kanta taje ta nemo itace,ta tafasa ruwa ta dura a filas,tayi wa danta wanka itamatayi..tahada tea tasha da ragowar biredi. Tayi wanka tayi wanki duka ita kadai,,anjima kumadole ta bararraka taliyan da zataci.ko ta ci gaba dashan shayi...aikin yamata yawa ita daya shisa dakwantawarta zazzabi ya rufeta. Maganar haihuwartakuwa naci gaba da yaduwa a gari,wasu emmata masukarambani haar suna zuwa mata barka.haka tci gaba da manejin rayuwa sai abunda danliti yaga dama yakekawo mata taci,a lokacin da kuma yagadama! .......kwana 7 suka cika tayi masa maganarkomawarsu asibiti,,,kai tsaye yace bai zuwa,Allah daikonsa jikinta ya hade kamar yana samun kyakkyawarkulawa.haka mai kudi yayi bulele dashi alamun ruwan nonon dayake sha yanada kyau...batadai zuwa koina,,,saboda danliti yahana.komaisa oho?shi kadaiyasan dalillin yin hakan. wannan satin shine ake bikin baraka da muhddinta,mama na gida mai kudi goye a bayanta.tunsafebatasa komai a cikintaba,,,har zuwa yanxu da akaidar da sallan la'asar.tagumi hannu bibbiyu tayi tunanitake lafiya meyafaru da danliti baizoba?bata samuamsarba taji tsayuwar motarsa. Farin ciki ya lullubeta ta taso ta tarbesa.babu walwala ya wuceta yashigedaki...t abiyo sa abaya tazauna kusa dashi tanatambaya,,,waya tabamin cweethrt dina?ko fushin netunna jiya? Ya ballo mata harara yace kinason wanimarinko?to kici gaba da tadamin wannanzancen,,tadan kada kai tana murmushi tace sha kuruminka,indai maganar aure ne bazan sakeyimakaba duk lokacin dakaga ya dace saimuyi,,shiyasa bangankaba tunsafe?.......ido zuruyana kallonta bansaniba! tace yi haquri shalele mezanci yau?yace babu,ki tashi kishirya kije gidan bikikici..tace bikinwa? yace ke saboda sakarci ma bakisan ana bikin yar uwarkiba?bikin yarinyar nanakeyi baraka...ta ware ido ta washe baki,bikin barakaakeyi?to ina zan sani ka hanani fita? Yayi matabanzan kallo ai dama ni kike gani na hanaki fita?toubanwa zakiyi a waje?kina samun ci kina samunsha...kinfiso kirinqa yawo kwaroro kwaroro da goyo ana nunaki?to shikenan tunda kinfison hakan gahanya nan,,,,amma kisani kwayar dawa bazan kawomiki gidan nan ba..da sauri ta rungumeshi,Allah sarkidan litina,ba haka bane ,nima bana sha'awarfitan,tunda baka so.yanzu bari in shirya ka saukeni agidan bikin...a razane ya kalleta,wai ke meyasa jaka ce?kawai sai in daukeki a mota in kaiki gidan biki anakallonmu? idan ke mahaukaciya ne nida hankalinanasan abun da nakeyi.... BAKIN CIKI 3***2 Yaja dogon tsaki ya tashi .da sauri yatashi yafitayana fadin sakaryar yarinya kullum sai ta bata wamutum rai!ta taso ta biyo shi tana bashi haquri,baisauraretaba yafada mota abinsa,,,,tadawo tanahawaye tana shirya mai kudi.ta goyashi ta rufa gyaleta kulle gidan...bata zame ko inaba sai gidansu baraka.ana tsaka da biki kallo yadawo kanta....dukyan uwa na kallonta a wulaqance,tana gaishesu sunabasarwa.kai tsaye inda inna saude take ta dosa,takuma zuba mata ido harta qaraso gunta,,,sannu inna!Ta bita da kallo daga ina?tace daga gida,yanxu danlitiyake gayamin ashe auren baraka ake,nace ina nasani! inna saude tace dama ya za'ayi ki sani?ke kokunya bakijiba?kika ratso jama'ar nan da goyo kikashigo?dubeki kamar ankoraki babu mamaki ma bakiciabinciba. Duk baki ya wani bushewa anya kuwamama...baza kiji magana bako?wannan duniyarkagama da iyayenka lafiya ma ya ka qare?belle ke kina kallo mahafiyarki tafadi ta mutu saboda BAKINCIKi,,mahaifinki nacan bisa keken nakasassu.ammaduk wannan baisa kinyi nadama ba mama?ke kuwawata irin iskar duniya ke kwasarki????? A marairaicetake magana inna bai kamata ku ringa ganin laifina bani kadai....ta katseta da sauri rufemin baki sakarya! Da yana son aurenki da tuntuni baizo yayi maganaba?tun yaushe kika haihu?ina lissafi watanki biyarkenan! ya ajiyeki kawai kin biye masa kunawatsewa..wa llahi ki guji makomarki,,ki kuma gujiwalaqancin da namiji.gashinan ai kinfara gani da hakakike?to wlh ki kuka da kanki karma kice kin sanni,,saboda haka juya ki koma inda kika fito! Tace aidama shima dan liti yace inya shirya zaizo yasameku a daura mana aure,ta watso mata harara tajadogon tsaki zata wuce mama tace banga amaryarbainna,ina take?ta juyo tace,suna makwafta itadaqawayenta..tayi tafiyarta sabgoginta.mama ta shigazabga loma,rabonta da abinci da naman kaza harta manta.tayi ta zabga tana zare ido gwanin tausayi.kankace kwabo,ta tada shinkafar nan cikin kwanotatas,ta kora ruwa da kunun aya tayi gyatsa tayihamdala,sannan tajita aduniya.. Tananan tsuru kamarmujiya baraka tashigo cikin gidan,inna ke gayamatamama tazo,,ta zagaya bayan kicin din tasameta zaune tana bawa mai kudi nono,,bakin ciki yaturnuketa kamar ta hadiyi zuciya ta mutu.haka nan tacije ta qarasa gunta fuska daure....amare!injimama,tace mama kenan,ya kike?tace kuma dankowa ya gujeni shine hardake koh baraka?zancenbikinma a bakin danliti nakeji,,,banci arzikin da zakizo kisameni ki gayaminba.ai kinsan inda nake.ta kalletasama da qasa ni bansan inda kikeba,,koda ma nasaniwannan ba gidan zuwana bane..hasalima namantadake.bandan kinxo inna tace kinanan ba wlh bazantaba tunawa dakeba.! mama tace ba laifinkibane,,,,,,,ta rausayar dakai tace thank god da kika gane ba laifina bane.bari inkoma frnds dina na jirana.tajuya dasauri tawuce ko kallon yaron batayiba.mama ta tabebaki tace agayas mai qawaye,zakaran da Allah yasoda cara,ko ana muzuru ga shaho sai yayi.danliti nedai ba a kauna,nikuwa inason kayana,bazan rabudashiba! yawwa! Ta mike ta jefa mai kudi a baya ta goyeshi ta tafi neman inna tasameta tace innazantafi,ta juyo ta dubeta,bangane zaki tafi ba?bakijiabunda nace bane?ko a zatonki wasa nake?nandanan ta kumbura fuska.samu wuri ki zauna kafin nabata miki rai!ta zauna gefen gado tana kunkuni,kowana kallonta,masu taya inna fada nayi........ana sallar magaruba gida ya gwaraye da duhu sai inda aka ajiyefitulun kwai keda haske.mama ta fakaici ido ta sulaleabunta ta kullin wainar ta da miya,duk ta juye su cikinleda.abincin dare ne da aka rabawa kowa tajuye nataa leda,,ta cika wa zaninta iska ta harba gida abinta.Hankalin inna bai dawo garetaba,,sai da za'a wuce da amarya.ta nemi mama sama ko kasa ta rasa.ta dokatagumi tana sanar da Allah da manxonsa kafintace,kai jama'a!wannan yarinyar tayi nisa batajin kira! Allah ka shirya mana ni saude..sauran mutane sukace amin!haka aka wuce da baraka tana kukan BAKINCIKI!da takaicin yar uwarta.ita kuwa mama tana can hankalinta kwance,ta juye wainarta a kwano miyarkuwa taji tantakwashi masu taunuwa,zatafara cikenan danliti yashigo gidan ,ya tokare bakin kofayana kallonta,,,tace saboda me?yace saboda naxokafin magruba naga baki dawoba. Tayi dan murmushidanliti kenan,bikinma badan kaikace najeba maizai kaini?kaga maganar inki dawowa ma baitasoba.yaqaraso yana fadin Allah yasoki,dama bell dina nadawo induba,idan baki dawoba inbiki hargidan indawodake,,sannan inmiki shegen duka! kinganshi ko?, Tace Allah sarki danliti bai kamata kanadukanaba,,,iyakar biyayya inamaka,amma dankuskure kadan sai ka hassala..!ya zauna kan tabarmayace,ke dai kiyi shiru tunda Allah ya kwaceki yau,aiku mata sai da haka,domin kwakwalwar kifi Allah yayimuku. Ta sosa kai tana kallonsa,batace komai.danki yayi barci ne?tace eh! Meye wannan kike ci? tacewaina ce inna ta bani.yajanyo kwanon gabansa yacedama kuwa yunwa nakeji..tace to muci tare mana aitana da dan yawa.yace ni bazanci dakeba miko filet inzuba miki.ta jawo filet din roba ta miqa masa,ya jefamata guda daya..tace guda daya nagani?......a fusace yace wannan wani tambayar banza ce?don kinxo dawaina zanci? shine kike min kurilla?watau nawa nebanza!ga tsiyarki cinye dani kike zancen,,,,ya turamata kwanon.da sauri ta maida masa ta tarairayo shikamar na goye,tayi ta rarrashinsa,sannan ya aminceda cin wainar. Tarinqa bashi a baki,,ya taune qashin ya batse.ita kuwa ko guda dayar bata ciba,bata ma kokwatanta ci ba,don karya ransa ya baci.sai dayagyatse,sannan ya gaya mata bibikon da yake nanemanta...babu musu tabada kai bori ya hau Haka rayuwar mama ta kasance tamkar tadabbobi,,duk inda danliti ya kadata can zatadosa.tsakaninta da Allah kafin maikudi ya shekarabiyu ya zubda mata ciki sau uku kuma kowanne babuwanda batasha wahalar zubansaba.,,duk ta jeme tayiduhu fatar jikinta yafara yaushi saboda wahala da ukuba.(Allah zai i sarmata) ......tabbas hakane,tundamasu ganin rashin jinta ne yajawo mata halin da takeciki sunayi mata addu'a, mussamman abba kullum yadaga hannu samu bashi da abun nema wajen ubangijiface Allah ya dafa masa akan qaddarar data sauqaaka sakeena,wanda hakan shi ke hana yan uwanta zuwa fandogari...amma kannen abba sukanxo abujasu dubashi.haka ya ali musamman yake zuwa damatarsa su duba abba su koma. Shekarunta qarashudewa suke tare da qara dumulmulewar rayuwarmama cikin kunci da talaucin dole...duk yansuturunsu sun mutu,ko da yaushe busu busu zaka gansu,musamman lokacin sanyi.babu manshafawa ,babu sabulun wanka,balle na wanki,sau ukutana zuwa neman taimako wajen inna tanahanata.tace muddin bazata dawo cikin yan uwantatazaunaba,ko kwandala bazata bataba......mama tagammace hakan shiyasa ma tadaina zuwa.wani lokacin tsirara zakaga mai kudi yana yawo sabodarashin sutura.sai makwafta sunga Allah sunga annabizasu kamashi su sanya masa kaya sadaka,anya?kaicon wadanda imani yayi musu karanci! BAYAN SHEKARU GOMA SHA BIYu. Nasan maitausayi da imani zai daura hannu akai yanakururuwa,idan yadubi halin da mama take ciki dayaronta kai duniya!ina zaki damu? shekarunta nahaihuwa talatin da biyu cif cif.amma idan ka dubetazaka rantse da Allah ta zarce hamsin.tsufa ya bayyana kuru kuru a jikinta,badan takai shekaruntsufanba sai don wahala. Sau da yawa tanayin rashinlafea babu kulawar data dace,saboda zata kwantaciwo sai ta kusa sati akwance kafin danliti yakaitaasibiti. koya sayo mata magunguna.muddin kuwahakan ya kasance to tabbaci idan ta warke sai ya kirkiro mata laifin da bai taka kara ya karyaba,don yajibgi kudinsa...a wasu lokuta idan taje rokonsa ayubake tausaya mata ya dauka cikin shagon yabata aranar kuwa zai bita gidan ya narketa yandayaso,dataga hakan ba riba sai ta fara neman wankaua makwafta tana samun abincin da zasuci itada danta. A wannan hali mai kudi yatashi yagamahaifiyarsa cikin ukuba da azabar duka wajenbabansa,wanda shikansa yagane randa yazogidan,sai yaga mahaifiyarsa na kuka.tunyana matamaganar makaranta har yadaina.ya fahimci cewabashida gatan xuwa makaranta kamar sauran yara!!... Daka dubeshi,kaga yaro mai kyau amma babugata.sai dai abun mamaki a game dashi yana danitsuwa kuma a koda yaushe yana taredamahaifiya rsa.,musamman inyaga tana kuka,daya farakawo qarfi sai yafara fita nema,shine yankan ciyawaya siyar,shine neman kwalabe da fasassun robobi da tsofaffun karafuna a bola,yana kaiwa inda akesayarwa,ya siyar ya kawo mata kudin. A haka tasamu da kudin datake wankau tahada,tajajarin AWARa,tana rabin tiya tana sayarwa a zaurengida.a haka take dan saya musu kayan gwanjo masuarha.duk wannan halin da mama take ciki gaba dayajama'a namata kallon rashin biyayyar iyayece ta jawomata hakan.shiyasa kalilan ke tausaya mata.itada gidansu sai gani sai hange,,ko a hanya ba dukkansuke magana da itaba,rayuwa tayiwa mama tsauri dayawa,tsawon shekaru ashe dole tayi tsufan qarfi dayaji........yamma tayi sosai lokacin da mama kezaune gaban kaskon suyar waranta a cikin zaure.yaranata shigowa suna saye naira biyar biyar,goma ashirin,duk yanda takama.muna iya cewa tanaciniki,don bata tabayin kwantaiba.maikudi ya shigosabe da buhun tarkacensa a kafada.kayan jikinsaduku duku,kafa babu takalmi,ta cire kai cike da fara'ata kallesa,yaro dan umma andawo?ya zagaya gefentaya zauna.nadawo umma.tace angaisheka.to kaje kayi wanka kayi sallah,akwai dumamenka yananan atukunya,ka zubo kaci.yace to ya mike ya sungumibuhun kayansa yashige gida.yayi duk abunda taumurcesa.ya zubo tuwunsa yadawo zauren gefentaya zauna. Ta dubesa sai kaki ci saboda riba?kai nalura kafini son kudi,,,,yayi yar dariya yace umma kenan yanxu saboda Allah gabadaya ribar nawakikesamu?tace mungode wa Allah ko nawa ne,ammaai dole aci,dauki guda biyu to,yace barin gama cintuwon tace gama idan kuma ta qare ka huta. Ya sa hannu ya dauki guda biyu ya ajiye a gefe,yaceban nuna miki ciwona ba,wani tsohon kwano ya yankemin gefen kafa!ta kamo qafar cikin sauri da tausayitace wayyo dan umma,sannu,shiyasa na kosaingama tara maka kudin takalma ka sayo,gamacintuwon inbaka naira goma kasayo ja da yalo in rinqa barbada maka yana saurin warkar da ciwosannu.....yace to umma!sukayi shiru yanata cintuwonsa yana gutsurar awaransa,jim kadan yaceumma wai ni bani da wani suna ne sai mai kudi?tayidan murmushi tace kana da shi mana...yace aibantaba jin kin kirani bane,zura masa ido tayi tace sunan kakanka gareka shisa bana kira shima yabitada kallo yace kigayamin inji,gobe idan munhadu daabokina in gayamasa,tace sunanka adamu,ya sakibaki yana murmushi,yace lalle ai sunan tsofi neamma inason sunan.tayi yar dariya tace amma karkabari babanka yaji yasan nafada maka dan baya so,yace saboda me?bashi ya radamin ba?tace shineamma saboda sunan babansa ne baiso ana kira.yatabe baki yayi tsaki,yace bani kudin ja da yalon,tamika masa naira goma yafita yana sude hannu,tabishida kallo ta kada kai,domin ta fahimci bayasonmaganar babansa,,,bai taba yabonsa ba kuma bai damu da al'amuransaba.bai dade ba yadawo damaganin,ya zauna ya kakkabe kasar jikin ciwon,yamika mata kafar tasanya masa garin maganin.nansuka zauna sunata hirrasu har wara ta qare,ya kwasomata kayayyakin yadawo mata dasu gida,yayin da itake zaune tana qirga kudin,gaba daya dari uku tayi ta ware uwar kudi Ta ware uwar kudi,tasamu ribar naira tamanin,ta cirenaira goma tabawa mai kudi tace jeka wurga a cikinasusun takalminka,kayi sauri kayo mana cefane danaira saba'in din,sannan ka auno min wakensuya,rabin tiya mai gwangwani biyu....yace to ya karbikudi yafice,itama ta mike ta ddebi ruwa a bokiti ta dauki sabulunta yankan qusa,da soso tayo wankatafito.injin oil dinta a yar roba,,ta dauko ta shafa tacanxa tsumman zaninta da wankakke, ta hada dawata kodaddiyar t shirt,ta fito tashiga kicin ta doraruwan tuwo. Sallamar mai kudi ta amsa ta leqo dagakofar kicin din jirgi dan umma,shiyasa nake sonka saboda babu wasa,,yana murmushi ya zube matacefane,ta duba komai dai dai yasayo ya laluba aljihuya ciro naira biyar ya miko mata ta me ce ce?yacemai waken suyane yamin ragin naira biyar,ta dafakansa,tace Allah sarki mungode,amma kaima kajekasha minti,,,ya kada kai,umma me zanyi da minti kamar qaramin yaro......ta kece da dariya!iye lalle maikudi angirma ko?to je kasha rake..yace umma ki ajiyeko farin maggi kya saya ko kuma a xuba a asusu...tazura masa ido tadan kada kai jeka tura a asusun,,,yawuce taraka shi da kallo harya fito tana tsaye batamotsaba mezan tayaki umma? tace kaga ka zauna ka huta ai ka sha gararanba dan umma,,,ya kamata kahuta,kaga rauni a qafarka.yace to. Ya jawo tsohuwartabarma ya kakkaba ya shimfida a kofar kicin din,yakwanta.it a kuma tana ta hidimar mada miyar kukakamar yadda yayo mata cefane,. Bayan ta kammala,ta fito da robar gari tanatankadewa tana fadin daga yau ma garin tuwunmu yaqare,,,ya yunqura yatashi,yace ai gara daya qare maumma.nagaji da cin tuwon nan,ta dubeshi da kyautace yaro kenan!har ka mance wata rana ma nemantuwon mike ido rufe? bama samu?kadaina fadar haka komai Allah yabaka kayi masa godiya sai ya qaramaka kaji ko?yace naji umma amma kinsan waniabu?sai ka fadi...yace in Allah yasa natara kudi dayawa zanbaki mamaki.tana dariya tace aidamakasaba bani mamaki yarona.....yace amma baki tabaganin wannanba....kedai kiyimin addu'a Allah yasa intara kaya da yawa,,,tace to Allah yasa dan ummayace ameen..ya koma ya kwanta yayi matashi dahannunsa.yana bata labari tanashan dariya.ta qaregirkinta ana kiran magrub..ta kwashe ta aje gefe gabadayansu sukayi alwala sukayi salla,shiya dauko musuabincin sukaci tare kamar yadda suka saba. Bayan sallar isha'i ta koya masa karatun alqurani kamaryadda suka saba haryakai amma,mai kudi nason yinkrtu amma basu da kudi shiyasa take koya masa dakanta.kullum kafin su kwanta,,,musamman ranakunda babansa bai xoba,,,shiyasa bayason zuwansa.donyasan zuwansa baya haifar da komai sai BAKIN CIKI .A Garesu Kwana uku mama na ririta kudin da ke hannunta dankar dan jarin da take taqama dashi ya qarye,,,gashidan gogan yaqi waiwayarsu balle ya wurga masu nairadarin datake samu tayi awo akai niqa,su sami garintuwo....shikuma mai kudi yana can kasuwa wajen yankyadi da tulin kayansa.. Daya tara buhu buhu,,,kuma Allah da ikonsa wannan karon yasamu manyan kayamusamman karafa,aka auna kayansa sai gashi dakudi naira dari bakwai da hamsin...kai farinciki kamarya kasheshi,,,,nan da nan yafada kasuwa.dafarkoshinkafa yasaya rabin tiya.......ya wuce teburin mainama yasayi na dari da hamsin,ya koma bangaren kayan miya aka hada masa na naira dari,yabadamarkade,,,aka juye masa aleda,,mai gwangwani biyuda maggi mai tauraro dda fari,ya koma ya nemi wajeya nutsu ya qirga ragowar kudinsa naira dari dasaba'in yanade abinsa yamaida aljihu ya kwasocefanensa ya dawo gida. Mama tasaki baki tana kallonsa da ledodi,,,ina kasamo kaya haka? yacedama nagaya miki zanbaki mamaki,kayan da na tarane...ta bude ledodi tana fadin iye! yanxu kayan nanharsun kai haka?yace naira dari bakwai dahamsinfa...kinga harda canjin dari da saba'in nakawomiki ki qara jari,,,,ta saki baki tana kallonsa ya miko mata kudin,,,ta amsa kina ta kallona umma ko bankyautabane?ta janyo shi jikinta da sauri tace a'a danumma..gani nayi ka kwashe kudinka ka kashe,bakasayo wa kanka komaiba,,,,ai da kasayo kodatakalmine,kaga wancan asusun sai kaci gaba da zubamasa abunda yasamu kawai.........yace babu komai umma,nima so nake muci dadi yau,,rabonmu fa dashinkafa tun na sunan maman fati kullum tuwo mukeci,,aiya kamata mu canza,tunda nayi dabara nasamukudin. Tayi dariya tana mamakin mai kudi,,,,sannan tanumfasa,,gaskiyane,Allah yayi maka albarka.ammaduk da haka kadauki saba'in da biyr kasayosilifas,inyaso daga baya sai kasayo dan dari biyu dahamsin din,,,yace umma kibar maganan takalminnan,yanxu kawo talatin nasayo itace,tace to tamiqa masa to maza kaje ka dawo kayi wanka ko?yace toumma.ya fice tana fadin haba ni inacan inata tunaninbanga dan ummaba ashe yanacan yana kashe managara.Allah sarki mai kudina!ta kwashe kaya ta nufikicin ta hura wuta ta daura shinkafa da sauranitacen,,,,yana kawo mata itacen tahadi wani murhun,,,ta kama hidimar miya.shikuma mai kudi yayiwanka ya sauya kaya ya fito ya shimfida tabarma yazauna .ta miqa masa warar data aje masa gudabiyu,ya karba yanaci suna hira abinsu. Kafin kiranmagruba ,gida ya hautsine da qamshin dage dage gashinkafa a gefe,,,,,tuni ta sauketa gwangwani uku ta dafa ta wadace su sosai .kawai tsayuwar mota sukajia qofar gida,mai kudi yayi wuf yatashizaune,,,gabansa ya yanke ya fadi,mama da sauri taleko tace kamar tsayuwar motar babanka?ya qaradaure fuska,,shine man..to menene na bata rai?yayiwuf ya mike ya dauki buta yafada bayi. Ku sakani a addua zan fara exam, tnx. BAKIN CIKI 3****3 Ta bishi da kallo tana kada kai,,,,babu sallama yashigo.bakinta har kunne..sannu da zuwa!ya kalletasama da qasa hannaye cikin aljihu,yace tundagazaure nakejin qamshi,na makwafta ne?ko a nangidan???ta matso shi sosai ganin ba fara'a a fuskarsatace wlh mai kudi ne yasayar da kayansa yayi mana cefane harda nama,shiga ciki barin zubo maka....yawatso mata idanuwa mai kudi?karki mai dani wanisakarai mana.kinfara iskanci kina samo kudi ko?dasauri ta katse shi,,iskanci dan liti?ya daka matatsawa,rufe min baki ko in farfasa miki kai,,,banxakawai ina magana kina so ki qaryatani..ya wuce kicin din a fusace yaje ya duba,,banda ke yar rainin hankalice mai kudi ne zai samo miki kudin uban wannancefane?ina mai kudin?ta durkusa gabansa ido tafhawaye tace na rantse da Allah danliti bangaya makaqaryaba,,anan yayi ta tara kayansa buhu buhu ya fitadasu ya....ya isa haka don Allah! mtss yaja tsaki ya wuceta tsugune. Tsakar gida yatsaya yana dagamurya ina mai kudin?cikin sanda yafito daga bayin,daganinsa dama can kuka yakeyi,,,zonan danuwarka.ya matso gabansa yana kokarin tsugunawayasa hannu ya murde masa kunne miqe tsaye daniska!gidan ubanwa kasamu kudin wannan cefanen? yayi banxa dashi BAKIN CIKI ya hanasa badaamsa...... Kafara sata ko?to saurareni dakyau,,,duk ranarda aka kamakakayi sata daga kai har uwartakamai goya maka baya karku kuskurakuce kunsanni! kajiko?bai tankaba.illa hawayensa da suka qaratsinkewa bace min dagani shegebarawo yaruga bayan kicin yatsuguna yana kuka,mama na tsayeta rasa nayi itama hawayentakeyi,,,,yaja dogon tsaki ya wucedaki.dole ta biyoshi badan rantayasoba sai dan sanin batada yancinrarrashin danta agabandanliti...........yana zaune gefenkatifa tazauna a hankali tace kabanmamaki danliti daka mancezamanka nakeyi a cikin gidannan,,,,ya daga mata hannu bansonjin komai dan Allah.tace to nazubomaka abincin?yace kema kinsan baabincinku naxo ciba..tadannumf asa kanta sunkuye gwanin bantausayi..... ...ankusa idar da sallarmagruba taje kicin ta debo masaabinci cikin langa da nama yakaiyanka hudu,,,,,,ta hado masa dakofin ruwa ta ajiye agabansa.yanaci yana danqara matamaganganu! bai kammala ba maikudi yashigo gidan,,,waye yakemana sanda?ya amsa da kyarnine,,to miye kakeyi wa mutanesanda? yace ba sanda nakeyibamasallaci nadawo!yace sannu dazuwa liman,ya koma can jikin kicinyayi zamansa.ya qare cin abincinsannan ya dubeta baki buqatarkomai tunda danki nakawo miki. Kafin tace wani abu,ya miqe yanashirin barin dakin,ta biyoshi tanahaba danliti!kwana nawa rabondaka waiwayomu?kuma wannan yarshinkafa kwana nawa zata mana?idocikin ido yace bafa dolenabane,,,,ni ba mijinkiba ni baubankibane,ko ban fadaba?.........tayi shiru dan bataso ta qara waniabu dazai jawo mata duka,,,sabodahaka ta kyaleshi,,,yasa kai ya ficebai ko kalli inda mai kudiyakeba.....ta jima tsaye tsakar dakisannan ta fito ta tsugunna gabanmaikudi tadafa kansa kayi haquridan umma!yace wai umma meyasakika auri wannan mutumin?cikinfada take masa magana karka sakemin wannan tambayar idan kanasomu shirya dakai cikin gidan nan.yagoge kwalla da bayan hannu kiyihaquri umma,dole nagayaa mikigaskia natsani wannan mutuminnatsane sa.shiyasa danayi sallahyanxu na roqi Allah ya kasheni danbanaso na girma dashi. Ta xuramasa ido na tsawon lokaci habadan umma karka daga min hankalimana meyayi zafi?yace umma dukabunda baba yake miki ina kallokuma inajin zafi,mesa zaice minbarawo?bayan ni banasata...umma da baba yayi minbaki inzama barawo gara na mutuAllah! tace bazaka mutu ba danumma kuma da yardar Allahbazaka zamo barawo ba.kai yarone shisa kake gani babanka ya cikafada.amma idanka girma zaka ganesauqin kai gareshi.baka ganin harabinci na xuba masa yaci?to aialbarka yasa maka.saboda haka kakwantar da hankalinka komai zaiwuce da yardar Allah kajiko?bariinyi salla inxo muci abincinmu. Ta share masa hawaye ta tashitayo wanka tadauro alwala tayisalla,lokacin ana kiran isha'i,,,,donhaka tadaura gaba daya,,,,shikuwamai kudi yanajin kiran masallaciyatafi bayan ya dawo suka zaunacin abincinsu.tanata lallashinsakafin tasamu hankalinsa ya kwantatadaura masa karatu sukakwanta......yau kwanansa hudu cifdayin rauni a qafarsa yana tafeyana yawon neman robobi dakwalabe amma bayajin dadinjikinsa....wani irin sanyi yakeji gazazzabi na neman kamashi hakayaketa yawo bashi wannan bolabashi wancan,,,,,,har aka kiraazahar,ya nufi wani masallaci danyin sallah.ana idarwa yafito yadaukibuhun kayansa yaci gaba,,,la'asart ayi,,,yanajin qira bai bata lokaciba ya nufi masallaci,,yabada faraliAllah kenan yaro qarami sai kaifinhankali shiyasa yake bawa mutanemamaki harba mai iya daga kaiyayi masa gori. Yana fitowamasallaci gida yadawo sabodazazzabin qaruwa yakeyi,,,mamanata yanka wara tana sawa a cikinruwan gishiri.....yayi sallamayashigo tana amsawa yau da wurihaka dan umma?ya jingina buhunkayansa yadawo kusa da ita yazauna.yace zazzabi nakejiumma..da sauri tajawo shi jikintata cusa hannunta kasan wuyansataji zafi rau..wai wai aikuwa gajikinka yayi zafi maikudi meyasatuntuni baka dawoba? yace inatunanin dan abunda zan samomana ne umma,,,kinga bamudaabinci Ta rungumeshi,sosai ya kwantajikinta,tace Allah sarki yaronakomai ai sai da lafiya.bari inyisauri inje chemist insamo makaparacetamol kasha....kwanta nan kajirani.ta miqe tadauki naira ashirinta yafa mayafi ta wuce.........ka fintadawo ya qarasa yanka mata wararyazuba cikin ruwan gishiri,,,,tazura masa ido maimakon kakwanta mai kudi kaji zafin jikinkakuwa?yace natayaki ne umma kobaki so?tace inaso Allah yamakaalbartka ungo maganin barin debomaka ruwa kasha guda biyu. Tadebo masa ruwa yasha maganin tamatsa masa ya kwanta adaki,,,,amma dayaso yafitar matada kayan suya zaure ya hura matawuta....ai kuwa yana kwanciyabacci ya kwasheshi.harta gama baifarka ba,tazo ta taba jikinsa zafirau.hankalinta ya tashi kwarai dagaske ta zura masa ido sannan taqirga kudin dake gabanta,,,,kawaiabinda yazo ranta shine takaishichemist a hada masa maganinmaleriya .haka kuwa akayi baifarkaba sai da aka kira magrub.kaitsaye alwala yayi yakama hanyazaifice,ina zaka mai kudi?yacemasallaci mana umma!tace kayi agida tunda bakajin dadi.....yacenafiso inje masallaci umma taceadawo lafiya,yawuce yanaamin.yana dawowa tariqehannunsa har chemist aka hadamasa maganin maleriya takashedari uku suka dawo,,,takawo masasauran tuwon datayi da ranasukaci,,,,tabashi magugunayasha,,,yana sallar isha'i wanibaccin yasake kamasa. Cikin dare taji yana ta rawansanyi,,ko ina jikinsa rawayake,takwaso duk tsummanzannuwanta ta rufa masa.amma abanxa haka suka kwana zaunekamar bazaiyi raiba...hankalinmama yatashi kwarai ganin yaumaikudi ko sallah yakasa tashiyayi.don haka tana sallame sallahta figi gyale sai shagon danliti.Ayuba ke alwala kofar shagon bisabenci..ya dubeta afujajan kwalla tafidanta yace lafea sakeena?tacemaikudi baida lafiya ayuba jiyabamuyi bacci ba.danliti yananan? yace yananan baima tashiba.......tawuce ciki tuni hawayenta sukafara zuba tausayi yakama ayubadomin ya hango matawalakanci,,,,danliti na bacci zatatashe shi? haka kawai ma ya akaqare? ya kada kai yarasanayi,,,,yana kwance dai dai akankatifa ta tsugunna ta tanbubbugashi.ya bude ido yamutseya zuba mata ido baitankaba....hakan yabata damarfadin abunda ke tafe da ita. Maikudi babu lafiya kamar zai mutudanliti don Allah kazo ka taimakaakaishi asibiti.....nakaishi kemisanbashi magunguna amma baiyibako barci......ke ya isheni haka!haba!ke sakaryar inace wai?tukunama banhanaki zuwa shagon nanba?kin raina ni koh?har ina bacci kizokitashen...nina samasa ciwon?iye?ina tambayarki? Da gudu hawayenta ke kwarara! takada kai murya na rawa tacebakaga halin dayake ciki banedanliti.don girman Allah kataimakaka kaishi asibiti..wallahi sukenankudadena duk na tattara na kaishichemist Idanuwa sunkafe,,,,,ta yada mayafita doka salati ta tarairayoshi...tanakira amma ya gagaretadagawa,,saboda duk gabobinsa sunmimmike ta koma kicin takandamo ruwa tazo tana shafamasa bakinta na fadin nashiga ukuyau me zangani me kudi? Hawayenta yaci gabada kwararatsawon lokaci batare datasanadadinsaba kawai hango rana tayiyafito ba danliti ba alamansa.tafitokofar daki idanuwanta duk sunkumbure tarasa yanda zatayi taceto rayuar danta mai tsananintausayi nta....batasan lokacin datafada gidan maman fati ba. afiya maman maikudi?ta durqusaa gabanta baki na rawa kitaimakenimaman fati,,,,mai kudi zai mutu!maikudi zaimutu maman fati!meyasameshi? daga zazzabi sai sumayakeyi....kitaimakeni da kudiinkaishi asibiti inmundawo zantayimiki wanki har kudinki yaqare....dan Allah kitaimakenimama n fati. Naje nagayawa babansa yaqizuwa....tausayi yakamata tanumfasa tace nima maigidan bayagari ne maman maikudi.ammabarin dubo miki abundayasamu.tashiga daki tafito mata dakudi yan dari bibbiyu. Ta mikamata ungo nan dubu daya cekawai!nasan bazasu ishekiba ammakiyi kudin mota xuwa kagara sai kinemi taimako.idan kuma babannasa yaga dama yajeshikenan.Allah ya sauwaka. Takoma dakin tasameshi yanananyanda tabarshi...ta sake baxamatasha neman mota suka tsadanceakan dari takwas dan sun tausayamata....tadauko mai motar harkofar gida....sannan tace yashigoyataimaka mata da maralafiyar...yayi sallama yashigodakin.me direba zaigani?dafara ngangara gefen bakin maikudi dasauri ya tabashi ya jujjuya ya dubimama dake tsaye idanu waje. Yace uwargida,ai ina ganin yaronnan babushi!ta qara zaro ido tanafadin a'a malam babu ruwankadashi...kasanya minshi a motakawai tunda nace biyankazanyi....yace uwargida haquri fazakiyi ko kinje asibiti wahalar kawaizakisha dole kidawo dashi,,,dominbabu abunda zasu iya masa...kiyihaquri kawai Allah yajikiansa.yasakai yafice cikin alhiniyaja motansa yakoma tasha. Mama ta zubawa mai kudiido..ahankali ta zube gabansa takamo hannayensa taci gabadakallonsa hawaye na zuba kamarfamfo..shikenan anyi angama?dagazazzabi kwana daya?haka zuciyartataketa wasi wasi.haqiqanin gaskiyakuwa ciwon maikudi tun ranardayaji rauni a bola tetanus yashigeshi.rashin kulawa kuma yakaishi garasa ransa..kokuma mucekwanansa ya qare ya huta dagwagwarmaya. Tamkar a mafarki mama ke ganinabun,,,shiyasa take zaune bataredatasan meya dace tayiba.kawaimurya taji bisa kanta.kitaso mutafiasibitin in ajiyeku sauri nakeyiinada wurin zuwa.!taciree kai tadubeshi ido yayi jawur wasuhawayen suka qara tsunkowa bakina rawa tace yamutu...yacebangane ya mutuba? Mama ta zubawa mai kudi ido..ahankali ta zubegabansa ta kamo hannayensa taci gabada kallonsahawaye na zuba kamar famfo..shikenan anyiangama?daga zazzabi kwana daya?haka zuciyartataketa wasi wasi.haqiqanin gaskiya kuwa ciwonmaikudi tun ranarda yaji rauni a bola tetanus yashige shi.rashin kulawa kuma yakaishi ga rasaransa..kokuma muce kwanansa ya qare ya huta dagwagwarmaya.Kan dole ta tsagaita da kukanta...amma hawayentayaqi yanke.jimawa kadan ayuba yazo tare da abokandanliti mutum hudu,,,,daya daga cikinsune ma yatahoda likkafani.ayuba yayi masa wanka...ya kintsa shisuka nadoshi a tabarma sika fito dashi.kowannensuyayi alwala suka sallaceshi tare da tsirarun mutane masu wucewa, Sannan suka tafi kaishi suna bada baya maman fatita shigo tasami mama tana ta kuka.tazauna tayitararrashinta harta sami yar nutsuwa.ta dauko kudinmaman fati tabata tace nabarmiki mama.nidai fatanakokuma ince roqona gareki shine Allah yasa kiganewannan zama bayida wata fa'ida ga dan musulmi. Tausayi rayuwarki kebani,,,saboda duk wanda yahaihu baikamata yazauna yana aibanta waniba.donyaganshi a wani hali marar kyau.don Allah kirinqa yinaddu'a kina rokon Allah ya kore miki wannanshaidanin daya dabai bayeki miki ziciyarki.saifa kindage kin yaqi zuciyarki sannan Allah zai taimakeki kinji? kiyi haquri ni zankoma Allah yajikansa.....tashare kwalla tace ameen ngd maman fati kumaazanyi addu'a kamar yadda kikace..tace toshikenan.ta taso tabaro gidan cike da tausayinta Suna dawowa maqabarta shago kawai ya wucedasu.yan rakiya kowa ya kama gabansa..ayubayazauna yanata juyayin mutuwan maikudi.shikuwagogan cikin shago yashige ya kwanta.baza ace gaabinda yake tinani ba.domin zuciyar danliti sai Allahkawai.ita kuwa mama zaune take idanuwanta na kallon sama,,,hawaye nata sauqa bisakuncinta.maganganun mai kudi ke yawo cikinranta.kiyi hauri umma"!yazama dole ingayamikigaskia!natsani mutumin nan na tsanesa umma!shiyasa danayi salla yanxu na roqi Allah ya kashenidan banso na girma tare dashi.Tayada kai bisa filo tagoce da kuka,,meyasa ka rokimutuwa maikudi?tayi kukan daya isheta babu mairarrashinta har akayi kiran azhar.sannan ta fito kantasosai yake ciwo haka kuma batajin yunwarcikinta.dukda cewar rabonta da abinci tunjiya.ta zubaruwaa abuta tashiga bayi tadawo tazauna tana alwala.karaf! idanunta suka sauqa akan buhuntarkacen maikudi.buhun yananan inda ya jingineshi.tazubawa wajen ido tana kallon shigowansa da dukkanabunda yamata jiyan kafin yakwanta.nantake kukantayadawo sabo tana alwala tanayi.tashiga sallahhawaye na zuba harta qare.karo na farko da Allah yafara bata ikon daga hannu tayi addu'a.Allah kajiqanadamu!Allah kasanyamin haquri da dangana!Allah kakoremin sheidanin daya dabaibaye zuciyata!Allah kataimakeni!tasauqe hannu tana goge kwalla takomagefen katifa ta zauna BAKIN CIKI 3***4 Kun jini shuru ko wlh sub dina ne yayi expired da kuma exam da nakeyi kuyi hakuri Zamanta keda wuya almajirin maman fatee yayisallama...yashigo dauke da kwano

Chapter 21 of 28