Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
auran dole ake son yi mata. Kwarai kansa ya daure jin cewar ita 'yar gidan Uban dawaki ce, don haka ya tasa ta har gidan. Amma me? Suna xuwa kofar shagon Danliti ta xarce can tayi xamanta bisa benci. Dan liti ya fito aguje da ayuba, mamaki ya rufe ayuba, shi kuwa dan gogan munafuncin ne yasa gaba, sai yazo ya narke a gabanta. Yace, saboda me sakina, kinaso ki rasa ranki ne? Tace gara in mutu da su raba ni da kai, ya dubi Ayuba a gigice. Yace, kawo min mukullin mota ayuba! Ya shige shagon da surinsa, shi kuma ya juyo gunta ya marairaice yake fadin, aure na Allah ne sakeena, ina so ki yarda da wannan. Duk iya son da muke juna idan Allah bai nufi auran mu ba, babu yadda xamuyi. Don me xaki nemi halaka kanki? Bata bashi amsa ba. Ayuba ya mika masa mukulan. Bai jira tace wani abu ba, ya kamo hanninta taso muje asibiti asa miki magani. Dattijon nan ya bisu da kallo, duk tausayi ya rufeshi. Rashin sani kenan, ya fi dare duhu, domin shi gani yake irin haka ke jefa yara yawon banza.. [11/01 19:24] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 2***3 (TRUE LIFE STORY) Wasu iyayeyn na da ra'ayin rikau, idan kuma ka bibibya kwadayi ne, wata kila wancan yafi wannan kudi ne? Sai dai kuma ai uban dawaki mutumin kwarai ne, me xai sa ya aikata haka akan yarsa? Duk da cewar dan dattijon nan talaka ne, ya doshi gidan uban dawaki, don ya bashi shawara. Fuskar Umma a sharkaf da hawaye take muryar ta har rawa takeyi, bai kamata ka baro ta can ba abdul... Yaya xanyi umma? Kona cusata cikin, sake fitowa xatayi. Mama ba zata mutu a hannu na ba, umma ta tafi inda take son xuwa, kanta tayi mawa. Fatana kwai Allah ya yaye mata abinda ke damunta. Kuyi hkr ku kyaleta anan domin ina mai tabbatar muku xata xauna can ba dawowa xatayi ba. BAKIN CIKI ya hana abba magana, sai A. Adamu ya iya fadin, gaskiya, gara ta xauna a cigaba da yi mata nasiha watakila a dace. Kuyi hkr Yaya mu dauki wannan a matsayi kaddara. Kai abdul idan ka koma Al-ameen ya kira ka kwantar masa da hankali ka... In ce masa me kawu? Gaskiyya xan gaya masa shi ma ya hkr da ita tunda ba ita kadai bace 'ya mace. Allah xai bashi wata. Ko kuwa? Abba ya dube shi, sai yanxun ya iya cewa, karka gaya masa haka abdul, da yardar Allah sai inda karfina ya kare akan mama. Indai ni na haifeta kuma ni ne xan daura mata aure Insha Allahu shine xai aureta. Kawai ka bashi hkr kayi masa wannan bayanin da naga ya maka yanxun. Ya dafe goshi yayi huci zafi kafin ya dubi Umma. Yace ki share hawayenki, umma ki yi mata addu'a Allah ya shiryata. Ni xan koma sai yadda ta kama. Basu amsa ba, ya mike kawu Basir da Adamu suka yo masa rakiya kuma suna gaya masa kalaman da suka dace ya gayawa Al- ameen. Da dan dattijon nan sukayi kicibis yana sallam cikin xaure suka amsa nan take. Yace baka shaida ni ba ko yaro? Nine wanda yaga lokacin da yarinyar gidan nan ta bude murfin mota ta fito, tayi min bayani ita 'yar mai girma Uban dawaki ce, shine nace ai mai martaba yana da saukin kai xan xo in bashi shawara game da auran dole, yayan ya dube shi da kyau. Yace hakan ta gaya maka? Yace, kwarai hakan ta fada. Yace to tayi maka karya, kawu ka na iya yi masa bayani, don na tabbata abba baxai iya fitowa ba ahalin da yake ciki. Alh. Basiru yace yanxun ina take? Yace tana can ta tsaya wani shago har sun tafi, zai kaita asibiti. Suka dubi juna, yaya yace, kunji ko? Mama ta tafi, bata jin kira saidai addu'ar Allah ya shiryata. Ni na tafi. Ya fice ya barsu nan tsaye. Alh. Basiru ya dubi tsoho yace mun gode baba, amma kayi hkr, bazaka ji komai daga gareni ba, saboda ban sami izinin yin hakan ba. Maganata gaskiyya da nake so ka gane shine karya yarinyar ke maka, tare da shegantaka irin ta yaran yanxun. Mun gode da kulawarka. Tsoho yace, shikenan nima na gode, amma don girman Allah abi a hankali asamu a sulhunta. A. Basiru yace ba komi baba mun gode. Sukayi sallama ya shige gida. Tsho ya kama gabansa cike da wasi-wasi cikin ransa. Falon Uban dawaki A. Basiru ya koma ya xayyane masa labarin da tsho yaxo da shi, da kuma shawarwarin da ya bayar. Abba bai iya cewa komai ba saboda tsabar bacin rai. Sun jima suna tausar xuciyar Abba sannan suka koma sasan su, inda matan suke xaune dirshan suna xuba gulmace gulmace. Suna zagin mama da iyayenta. Basu hanasu ba, hasalima zama sukayi suka dora xancan babu dadin ji, ita kuwa baiwar Allah mama, tana tare da Danliti cikin mota, bayan fitowarsu asibiti, yana ta faman rarrashinta, don ta daina kuka ta kwantar da hankalinta, da kyar ya samu ta nutsu ta daina xubda hawayen. Yayi fakin kofar shagon sa ya juyo ya fuskance ta. Yanxun ya xamuyi mu fuskanci juna abba ya gane cewar idan ba mu auri juna ba, komai zai iya faruwa da mu? Tace, ai ga misali nan na fara nuna masu kuma ba xan fasa ba, ina nan akan baka na. Ya marairaice yace wannan misalin bana son irinsa sakeena, don bana son na rasaki. Gaba ki daya kin fita kamanninki kin kuwa ci abinci yau? Ta kada kai, abinci ba xai iya wuce min ba Dan liti ina cikin wannan masifar meye illar ka? Da abba xai ce samm baka dace dani ba? Ya lumshe ido, ya bude kafin yace, saboda suna ganin ni bako ne, bani da kowa agarin nan..... Ta katse shi, hakan shine xai nuna daga sama ka fado? Wannan ba hujja bace Danliti, son rai ne kawai irin na iyaye ni kuwa ba xan yarda ba, sai dai muyi ta ba juna wahala. Ya ja gwauron numfashi ya sauke, ya lalubo yatsun ta ya runtse su cikin nasa, ya xuba mata ido yace, nasan ki na sona sakeena, amma ki daina damuwa ko sun hana ki xuwa wajena, sannan ki daina wasa da rayuwarki, don tana da muhimmanci aguna. Abu da gaba, ki daina zama da yunwa, ita ma zata iya illata minke. Yaunxu abinda nake so dake, ki zo muje shago in hada miki tea ki sha, sannan kije gida ko sun zage ki, kar ki ce dasu komai, don kar su sami damar dukanki. Kinji bebi na? Ta amsa da ka. Tace, yauwa mai kyau, to dan kalle ni mana, ta dube shi suka yiwa juna xuru, jim kafin ta kauda kai, tana dan murmushi, shima murmushin yayi yana mata kllon kwadayi, ya ja yatsunta xuwa bakinsa ya sumbata. (kuji dan iska). Ta kwace da sauri ta kara sadda kai. Yace, bebi na kenan, sarkin kunya. To muje ko? Zaki iya sauka ko in zo in fito dake? Ta balle murfin batare da tace wani abu ba ta fito, shima yayo waje yana kallon yadda take dingisawa har cikon shagon sa. Ya ba za mata tabarma ta zauna. Ayuba na mata sannu. Akwai wani labule jikin wata kwana a shagon, sai alokacin ta gane daki ne. Cikinsa Dan liti ya shiga ya fito da filas da kofi da cokali ya aje gabanta. Yace ga ruwan zafi, ki daga idonki, ki duba duk irin madarar da kike so, ki zaba na dauko miki. Tana murmushi tace, kai wacce iri kake sha? Yace ai bana shan madara a tea, ganye kawai nake sha. Kinsan buzaye ai? Tayi dariya tace, ba'a raba su da jiko. Yace shayi dai. Ta ciga da dariya tana fadin, to shayi, wai menene sirrin shayin nan ne? Yace xan gaya miki amma da farko wacce madara kika zaba, in dauko miki? Na kowa ki sawa cikinki abinci. Tace, bani peak ta ruwa. Ya mike ya dauko hade da katon bread ya hada mata tea mai kauri, domin duka ya juye peak din. Tana sha, suna hira ya gaya mata ire-iren shayin su. Bayan ta kammala, ya matsa gareta yace, yanxun ya kamata ki koma gida kiyi barci, ki huta kinji? Karki damu ko an hana ki xuwa nan, wane tym zamu hadu. Ke dai kiyi addu'ar fatan samun nasara. Tace, Insha Allahu zanyi. Yana murmushi ya mika baki ya sumbaci kuncinta. Ta sunkuyar da kai tana murza yatsunta. Ya zura mata ido, gaba daya jikinsa yai la'asar, sannan ya dago habarta, suka dubi juna, yace I love U! Tace me too, yace, to ki tashi kije gidan, zaki iya ko? Tace xan iya. Ta yunkura ya taimaka mata mikewa suka fito tare ta sallami Ayuba, ya dan taka mata kadan ya dawo, yana zuwa ya kwashe da dariya, ya mikawa Ayuba hannu suka tafa. Ayuba yace, baka da kyau dan iska. Yace raina kama gayya! Gaskiyya ta gurzu, na tausaya mata wlh. Shegiya akwai taushin fata, baka ji ba kamar auduga, duk ta susuta ni. Ya zura masa ido yace, tunda kuka shiga, na karance ka, shi ya gaba na yayi ta faduwa, kar ka sata labulan nan. Yace, ko na sata ba zata hani ba, nake gaya maka kuma babu abinda zai faru dani. Kawai dai ban yi niyya bane yanxu, ni nasan abinda nake hari. Yace a dai rika tuna Allah Danliti, shagalinka yayi yawa kuma ina ma kwadayin cin ubanta nakeyi, ai har uanxun duniya bata fara zaginta ba. Kaga da sauran mutuncinta. Ya bishi da kallo, bai ce komai ba, yayi tsaki ya tashi ya koma shago abinsa. Tana tafe tana dingishi, ta iso gida, kanta tsaye bata fargabar komai ta fada zaure, kicibus suka yi da Ya Ali sabe da jakar sa zai bar garin. Ko kallon sa batayi ba ta wuce, ya biyota yana kiranta bata waigo ba, balle ta amsa, ta shiga sasan su har falo yana binta. Su abba na kallon ikon Allah, domin dai Mama bata saurara ba, cikin dakinta ta shige. Ya Ali na shigowa ya gansu, ya ja birki amma ransa na son ya shiga wajen mama, yayi magana da ita, abba ya dube shi. Yace, Ali ka daina wahalar da kanka abanza, mama bata bukatar komai sai addu'a. Saboda haka ka kama hanyarka ka koma bakin aikinka. To amma, kayi hkr Abba, don girman Allah karku daketa, kamar yadda kace nayi mata addu'a kuma kuyi mata addu'ar. Yace, na yarda da kai Ali, amma ban yarda auran kowa ba, sai wanda na aminta da shi. Zan gani idan ita zata daura wa kanta aure ko mune? Yace, haka ne Abba don Allah ina rokon 2mins in ishiga in dayi mata nasiha, koda bazata saurere ni. Ya suke numfashi yace, shiga Ali, Allah ya sa taji abinda zaka gaya mata. Ya aje jaka ya wuce cikin dakin. Tana kwance niyyar barci ma takeyi, kamar yadda Danliti ya umarceta. Yana shigowa ta runtse ido ta juya baya, ya tsya kanta yace, komai zakiyi, dole in gaya miki gaskiyya, tunda kunnuwanki naji..... Fadan hakan yasa tai sauri ta toshe kunnuwan nata da yatsunta. Yace aikin banza kike yi Mama, kuma rayuwar ki na cikin hatsari, muddin baki daina jefa su abba cikin BAKIN CIKI ba. Menene anfani abinda kika aikata yanxu? Ki kashe kanki a banza da wofi, ba asarar Danliti bane, don na tabbata duk tsananin son da yake mi, ba zai hallaka kansa ya biki ba. Ki nutsu kiyi tunani. Akwai abinda magabatan mu ke hangowa kan wannan ra'ayin naki. Ni zan koma kuma ina fatan zanji canji daga gareki? Ya juya ya fice bata re da ta daga kai ta dube shi ba. Wani dogon tsaki ta raka shi da shi, wanda ya tilasta masa juyowa ya dubeta ji, sannan ya karasa ficewa. Ya dauki jakarsa ya kara yiwa su Abba sallama, ya bar gidan ciki da Al'ajabin maras misaltuwa a zuciyarsa. Bayan tafiyarsa, su Umma suka shigo gunta ta tana kudundune ta dunkule wuri daya, ko 'ina jikinta ciwo. Umma ta zauna gefen gadon shi kuma Abba n atsaye kanta, yace Mama barazanar kashe kanki ba zai sauya abinda ke cikin raina ba, idan ma baki sani ba, ki sani gara ki mutu da mutunci na ya xube a idon duniya. Saboda haka fadowar ki a mota bata girgiza ni ba balle ta cire daidai da kwayar zarra na alkawarin da na daukarwa Al-ameen da iyayensa. Mu zuba ni dake, duk wani matakin rashin kunyar da kika hau, ni na fi ki hawa matakin karshe! Ya juya ya bar dakin. Umma ta kura mata ido, hawaye suka cika idanuwanta, tace Mama zaki iya tashi ki saurare ni? Ta shiru bata motsa ba, ta sake fadin, idan har ni na haifeki kuma na isa dake, to ki tashi zaune ki fuskance ni. Ta jima kafin ta yunkura ta tashi fuskar ta sharkaf da hawaye, kamanninta sun sauya, saboda fitinar da ta daukarwa kanta a tunanin iyayenta. Umma ta zura mata ido, kafin tace, nasiha xan miki, idan kiji ki dauka wahala ta kare miki, idan kuma kince ba haka ba to rayuwa zata cigaba da yi miki kunci, domin Allah ne ya wajabta miki yi mana biyayya, muddin ba mu sa ba masa. Ban jin akwai wani dalili ko hujja da xaki gayawa ubangiji da ace kin mutu sakamon bude murfin motar da kikayi, ki fado lasa. Wannan ya nuna muraran kin kashe kanki ne da gan-gan. Ma'ana kin mutu kafira. Me zai jawo miki wannan masifar da hankalinki da komai? Ko kuwa kina so ki nuna mana kin fi karfin mu cikin dan kankanin lokcine ne? Kina nufin mu sanya miki ido ki zubar da mutuncin ki da mu a garin nan? Ban taba tunanin Mama, ke din nan zaki zama kaza kici share baki a game da irin so da Kaunar da Al-ameen da iyayensa syka nuna miki. Haka kuma ban taba mafarkin ke din nan zaki iya hango wani da namiji ya rufe miki ido har kice kin fo sonsa akan Al-ameen. Kina nufin daman can yaudara sa kike yi ba tsakani da Allah kike sonsa ba? Har yanxun mafarki nakeyi Mama, don ba gaskanya abinda yake shirin fitowa daga gareki nake ba. Ki yiwa girman Allah kir ki bari wannan magana ta zama gaskiyya, ba ke kadai za'a zaga ba har damu iyayenki. Na mu ma zai fi yawa saboda mune muka isa dake. Yanxun abinda na rokonki shine, ki share hawayen ki ki gaya min, laifin me Al-ameen yayi miki kike son ki katse masa rayuwa? Gaya min daga ni sai ke ce a dakin nan kuma share hwayenki, muddin shi ne baida gaskiyya. Ta shre hawayneta wasu suka xubo mata, kalaman ummanta masu taushi ne dashiga xuciya, amma kash Danliti ya riga ya gama da ruhinta. Allah ya bashi sa'a ya kamata ahannu, idanuwanta ba sa ganin kowa sai shi, kunnuwanta ba sa sauraron kowa face kalaman yaudarsa da izgilanci. Dalilin da yasa kenan kalma daya bata tasiri a hrt dinta, a duk tsahon jawabin da Umma tayi, da ka dubi fuskarta, zaka gane bata yarda bane kawai. Murya cunkushe tace, ni babu abinda Al'ameen yayi min Umma, kawai raina yafi kwanciya da Danliti kuma shi nake so na aura. Haushi kamar ya kashe Umma ta mike tsaye. Tace, to baki isa ba! Mu dan Liti baiyi mana ba, idan kina da wasu iyayen da za su dauta miki auran to bismillah! Ya ci gaba da fadin, ai kuwa bata isa ba, ni zanje in dauko ta kuma dole ta auri wannan yaron tunda itace tace tana so tun farko! Yace, Yaya duk yadda kake tunanin al'amarin nan ya wuce nan, amma ka gwada ka gani, kilan kai tafi jin tsoronka, sai dai kafin nan xance Al-ameen din ya kira ka, kuyi magana, don ni gaskiyya ban san me xance masa ba. Yace ba wani abu xan rarrasheshi, ya kwantar da hankalinsa, kaima yaunxun nan ka kama hanya kaje ka yiwa Hajiyansa bayani, kace kar su damu ba wata matsala bace babba. Ya numfasa ya amsa da to kawai. Lallai babban yaya yana dau kara abin wasa ne. Suna aje waya Aunty amina ta nufo shi, me ya faru ne wai? Nan take ya labarta mata abinda ke faruwa. Tun kafin ya kare idanunwanta ke waje, wai kana nufin Mama ta fasa auran Dr? Yace gara da kikace wai, don bata ida ba. Ni xan je na dauko ta, cikin gidan nan zata zauna sai ya dawo. Ta kada kai cikin damuwa, tace amma mama ta ban mamaki, me Dr? Yayi mata? Babu abinda yayi mata, wani ta hango saboda rashin hankali irin naku na mata da butulci! Tace wlh na yadda sai dai matsalar banyi zaton haka ba daga wajen Mama ba ganin yadda take nunwa Dr. So mai tsanani, duk yaudara ce, kai gani kuma a zahiri ai ta nuna. Amma ai tayi kuskure ni zan gyara mata zama, don bata isa ta zubda mana mutunci ba! Tace gaskiyya ne. Allah yasa ta gane. Ya wuce tebur don cin abinci. Shi kuwa abdulkareem, bai sami zaman cin abincin ba gidansu Al-ameen ya nufa ba tare daya san wane irin bayani xai iya yi masu ba, don hankalinsu ya kwanta. A haka ya isa gidan. Nan da nan aka tarbe shi da girmamawa da abubuwan kusa da baka, marafa baya gari, saboda haka mami ce ke tare da shi, ina fatan dai kaci abinci? Yayi dan yake yace, Alhmdlh Hajiya, nagode. Tace amma dai ko Juice kasha ko? Haba, kamar wani bako? Yanata murmushin rashin nayi, yana kallo ta xuba masa ta mika masa, Ungo sha don Allah. Kuma maimakon kazo min da surukartwa, yau in riketa cikin gidan nan sai tayi min sati. Ya aje kofin lemo ya kara gyara zama, Yace Hajiya, hkr na zo in baki, domin ban sami dawowa da Mama ba,... Saboda me? Kodai maganar Al-ameen gaskiyya ce, sakeena na cikin wani hali? Bata da lfya ko? Ya karkada kai.... Tace karka bote min komai Baban ameer, duk tsananin da sakeena ke ciki, nasan yadda xan rarrashi Al-ameen don hankalinsa ya kwanta. Gaya min me ya faru da ita? Jikinsa ya kara sanyi, cikin taushin murya, yace Matsala ce babba Hajiya, wacce ni kaina ban da ita ba, sai da naje daxun. Ashe tun komawar ta gida, wani yaro ya hure mata kunne, shi ya hana ta dawowa. Su abba na ta fama da ita kuma suna kan kokarin su don ganin raba ta da shi. Na yi nayi ta biyo ni, taki hajiya, shine Abba yace in zo in baku hkr kafin yazo. Insha Allahu za'ayi maganin abin. Gaba daya hankulan mu atashe suke, al'amarin yana daure mana kai. Idanuwanta xuru akansa, hannunta bisa kunci. Tace, wyyo Allah! Wayyo Allah! Me xanji yau mai kama da almara? Ta goce da sallalami, yanxun baban ameera kana nufin sakeena tace amanar Al-ameen kenan? Idanuwanta suka cika da kwalla, yayi da yaya Abdul ya kara kasa da kansa. Yace, kiyi hkr Hajiya, a gaskiyya ban san yadda xan fassara wannan al'amarin ba, amma abinda nake so ki gane Abba ba xao rungume hannayensa ya sanya mata ido ba. Haka muma 'yan uwanta. Muddin kuwa tana son albarka dole tabi umarnin mahaifinta. Shi yasa ya fara turo ni kafin ya zo da kansa ya ga alhaji. Haka kuma ku rarrashi Al-ameen ya kwnatar da hankalinsa komai zai daidaita cikin hukuncin Allah da yardarsa. Ta cire tagumi. Tace, a gaskiyya ba zan iya fuskantar Al-ameen da wannan maganar ba, in katsa masa karatu. Na san ya damu kwarai ya san halin da sakeena ke ciki, amma ba xan iya gaya masa wannan mummunan labarin ba, kuma na rokr ku don Allah ku kyaleshi kawai. Gara abar shi cikin duhun da agaya masa sakeena ta sauke alkawarin da ta daukara masa. Na tabbata komai nasa zai tsaya jarabawar su gab take da xuwa. Ni da kaina xan iya xuwa na roketa, ta tausaya wa Al-ameen karta kashe masa zuciya. Kwalla masu zafi suka xubo bisa kuncinta bata re da saninta ba. Hankalin Abdul ya kara tashi, BAKIN CIKI ya dada lulluba shi. Don girman Allah Hajia karki xubda hawayenki akan maganar nan. Da yardar Allah komai zai gyaru. Kamar yadda kika ce kar agaya masa ba, ba za'a gaya masa ba. Gara ace masa bata da lfiya ne, xuwa lokacin da xa'a shawo kanta. Ta goge kwallah, tace ina ganin hakan zai fi sauki iyaka dai yayi tunanin jikinta, mu kuma nan mu rinka gaya masa tana samun sauki. Yace, to shkienan, Allah yasa mudace. Don girman Allah hajiya kuyi hkr, sakarci ne kawai irin na yara. Tace, ya za muyi baban ameer? Dole mu rungumi kaddara. Ya mike babu isasshen laka a jikinsa, yayi mata sallama ya fice, batare da hajiyar ta kara ko motsi ba. Wucewar awa daya da rabi tana zaune xuciyarta cike da sake-sake iri-iri. Ji take kamar a mafarki abdul yaxo mata da wannan mummunan labari, wanda take ganin zai iya salwantar fa rayuwar dant tilon danta da takeji da shi. Duk fadin duniyar nan bata hada shi da kowa. Yaya marafa zaiji, idan wannan labari yake kunnen sa? Tabbas xai fita shga damuwa, domin yafi ta sanya Al-ameen ransa, ko alama baya son yaga ya nemi abu. Waya ta dau ruri a falon, ita ta katse tunaninta tare da haddasa mata faduwar gaba mai tsanani. Ta mika hannu ta dauka ba tare da tayi hasashen mai kiran ba. Tayi sallama cikin raunin murya. A raunane taji muryar Al-ameen ya amsa mata kafin yaci gaba da cewa, mami na, ashe sakeen ba ta da lfiya shine aka boye min? Ni ban ma yarda bata da lfiya bane Mami, kawai ku gaya min idan mutuwa tayi, xan hana Allah ikonsa ne? Ai nasan yafi ni sonta, kuma ta shi ce ban isa in hana shi amsat kayansa ba.... Tace saurareni Al-ameen, kar hankalinka ya gushe.idan baka yarda ba da maganar yayun sakeena ba, ai ni mahaifiyar kace, ba xan rufe maka komai ba, ka yarda ko baka yarda ba? Murya na rawa ya amsa, Na yarda mami, tace to sakeena bata mutu ba, rashin lfya ce ta sameta aka maida ta gida. Bana so ka damu da yawa, domin sosai take samun sauki, gobe ma xan sake xuwa in dubo ta, kaji? Ya numfasa yace, amma Mami me yasa za'a ajiyeta gida? Akaita asibiti mana, ko can xariya xanyi magana da abokina, na tabbata xai kula da ita tamkar ni. Pls mamy ki basu shawara idan kinje goben. Tace ba ciwon asibiti bane, shedanu ne suka tabata, kuma su iyayen nata suna tsye neman magani. Kai ma kasan xa su xauna ba. Ni dai rokona gareka shine ka nutsu ka kwantar da hankalinka, ka fuskanci jarabawar ki mai xuwa. Ka zama mai imani da Allah, shi xai sa ya karbi addu'ar ka idan kayi mata. Ka jini? Ya goge kwalla, yace naji mami don Allah idan kinje ki dafa kanta ki karanta mata ayatul kursiyu, falaki da nasi. Idan har gane ki ko da baxa ta iya miki magana ba, ki gaya mata Al-ameen dinta na gasheta, kuma xan ciga ba da yi mata addu'a har xuwa lokacin da xanji muryar ta a waya. Idanunwanta suka tara kwalla. Tace, Insha Allahu xan gaya mata, tare da dukkan abinda kace, muddin kayi min alkawarin zaka kwantar da hankalinka. Da sauri ya amsa, Allah nai miki alkawari mami, kinsan bani da wani buri daya wuce in faranta maku rai. Tace, Allah yasa dalilin alkawarin da kayi min Ubangiji ya yayewa sakeena abinda ya sameta! Yace, ameen Mami na! Dadina bai dawo ba ko? Bai dawo ba sai zuwa jibi. Yace Allah ya dawo da shi lfya. Ta amsa da ameen. Yace ki gayawa su iya su taya mu da addu'a, Allah ya taimake mu. Tace, xan gaya musu. Al-ameen, karka damu kaji? Murya raunane ya amsa, to mami sai kinsake jina. Bata iya kara komai ba ta aje wayar, domin muryarsa kawai ta isa jefa mutun cikin damuwa. Taci gaba da xama dauke da tagumi tunani na cin xuciyarta fiye da tunanin mai kallonta. Haka al-amarin yake wajen Al-ameen, domin dai rayuwa tayi masa tsauri kuma hasashen rashin lfiyar Mam yafi koma zama cikin ransa. Ba don yayi wa mamy alkawari ba, da babu makwa zai iya baro abinda yakeyi ya dawo ya ganewa idon sa Mama, tana cikin mummunan hali. Kafin kace kwabo, kowa ya fahimci samun sauyin sa, domin ya yamutse ya wayi garim duk kuzarin da nutsuwar sa basu jikinsa. Yana zaune addu'a yana tafe addu'a, haka acikin aji, hankalinsa yafi rinjayea ga addu'o'in da yakewa mama cikin ransa. 12pm washegari lokacin ne motar Mami ke fakin kofar gidan Uban dawaki. Yayin da mama ke kwance rankas ciwon jiki, sakamakon fadowar da tayi daga mota. Can da nan bata iya motsawa, Baraka ke tare da ita tana zazzaga mata nasihohi, duk da ta san bata sauraron ta, sai dai ya zama wajibi gareta, ta kara gaya mata gaskiyya. Mami tayo sallama falon ta shigo, gaban Umma ya yanke ya fadi. Ta amsa tana fitowa daga dakinta. Yake baki kawai takeyi, amma zuciyarta ta shake take da takaici tare da BAKIN CIKI mai tarin yawa. Ga wata kunya da ta yo wa idanuwanta dirar mikiya, mai alaka da ciwon dundumi. Sannu da xuwa Hajiya! Ta amsa mata da fara'ar karfin hali. Ta nuna mata kujera ta xauna, tana kara yi mata sannu da xuwa. Sannan ta debo mata abubuwan sanyi masu ruwa. Ruwan ta fara xuba mata, ta mika mata ta sha. Suka gaisa cikin girmama juna. Ta kara gyara xama, tace, sai kika ganni da rana tsaka ko? Fuska kunshe da tashin hankali. Tace ke dai bari, nasan kin sami sako maras dadin ji. Ta kada kai dauke da damuwa. Tace naji sakon da ya hani barci jiya, wanda ya sanya ni rama kafin safiya. Ina jajantawa shi kansa Al-ameen da ya sallama rayuwarsa kaf kan sakeena. Nayi kuka da wadannan idanuwan nawa, don na tabbatar da amsata ba alkhairi bace a gareni, domin komai zai iya faruwa ga tilon da na, farin ciki na kuma sanyi idona. Shi ya sa nace xama bai ganni ba, tilas inxo in rarrashi sakeena, ta tausaya min kar in rasa Al-ameen. Wadannan kalami sosai suka sanya hawayen Umma suka tsinke nan take, ta rasa me zata ce wa Mami ta sanyaya mata rai? Dole tayi kuma domin dai bata da kwakkwarar mafada, mama na nan akan bakanta babu sauyi. Da kunnunwata ta, taji lokacin da take gaywa Baraka tabbas zata iya kashe kanta, saboda Danliti. Mami ta cigaba da fadin ki daina kuka Hajiya, Baban ameer ya gaya min tashin hankalin da kuke ciki, kukan bashi da alfanu....... [11/01 19:35] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 2***4(TRUE LIFE STORY) umma ta hare kwalla ta katse ta Tabbas mama bata da lafia ciwon daya kamata mai tsanani ne maganin Allah, dole kuwa in yi kuka , don mama ta dasa mana BAKIN CIKIN da ban taba tunani ko mafarkin irinsa ba daga ni har Abban ta mu na cikin rudu tare da mamakin yadda wannan alamari ya kasanze haka, hakuri zakuyi hajia sannan

Chapter 10 of 28