Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bane? Tace, kwana yayi baiyi barci ba, sai bayan sallahr asuba barcin ya sace shi. Tana rufe baki ladi na sallama da tiran abinci ta dire gabansu. Tace ga shi hajiya dr, Iya tace in gaida ka, yanxun xata shigo. Yace ina amsawa. Ta fita ta bar dakin. Mami ta jawo tiren ta hada masu shayi ta mika masa, ungo nan dan iya. Daute ka sha kaji karfin jikinka. Ya sanya kofi a baki ya kurba kadan. Wlh daci mami ba xan iya sha ba. Tace don me? Ka cigaba da sha za kaji bakin ya washe. Ga kuma farfesun, bude bakin in xuba maka. Ya bude 'yar kular ta debo a cokali ta mika masa, karbi ka gani mana. Ya bude bakin ta xuba masa tace, yauwa ko kai fah? Yanxun idan Abba ya zo maganar auranta kankama, haka za'a ga ango a rame? Dadi ya lullubeshi yayi wani lallausan murmushi yace, mami na rame ko? Kai baka ji ajikin ka ba? Bana so kayi angwanci a rame, don haka ma za ka kama abinci ka ci. Nan da nan ta ga ya gyara zama ya hau shan farfesu yana kurban shayi, kinsan wani abu Mami? Sai ka fadi, shayin nan ya daian min daci. To yi sauri ka shannye. Ya kuraba ya sake kallonta, yanxu Mami idan aka daura auran anan xan barta? Eh mana, ko ba xan iya kula da ita bane? Yayi dan murmushi, a'a mami na, amma ni na fison mu tafi tare can, kin ga kafin mu dawo ta mance da sakaran Yaron da ya hure mata kunne. Ko ma muyi xaman mu can tana karatunta ina aiki na, ko kuwa? Ta dafa kafadarsa, gaskiyya ne, ina goyan bayanka, sai dai in ta haihu ka kawo min maigida ko kishiya. Ya kyalkyale da dariya, kwalla suka cika idanuwan mami ta bisi da kallo tana gyada kai. Yayi gyatsa kafin yace, ina son twins mami, ko? Sai dai an mai son su baya samun su? Da sauki ya katse ta, no duk canfi ne Mami, ni dai ina so kuma Allah xai bani ameer da ameera. Tayi 'yar dariya tace, duk naji, idan ma 'yan hudu ne Allah ya kawo masu albarka, yanxun tunda ka koshi, kaje ka yi wanka kafin dadin ka ya tashi. Xai ji dadi idan ya ga ango shar! Yace haka ne mamina. Ina xuwa, ya tashi da sauri ya fice. Mami ta ta tallafe kunci ta ce nikam tawa.... Nikam tawa ta sameni, ni Ya su, Allah ka duba mana. A bakin kofa suka hadu da iya suka gaisa. Sannan ya wuce bangarens, ya fada bayi ya sheko wanka, ya kimtsa jikinsa da wani lafiyayyen farin boyel mai taushin gaske. Ya fesa turare, ya dawo dakin Mami, ita ma wanka yi ta sauya kaya. Ta dube shi tana fara'a tace, haba yanxu na ga daidai. Ina ganin ma dai daga yau aka angwancin nan. Ya xauna kusa da ita yana dariya. Tsokanata kike sonyi Mami, me kika gani yanxun? Sai ma ranar kenan. Ki gane Mamina, ranar ba zaki shaida ni ba. Ta ware ido tana 'yar dariya zai hana? Sai dai ko amarya ta kasa shaida kai, amma ina mami zata mance da dan tilon dan ta. Dadi ya kara lullube shi, ya rungumo ta yana fadin Allah sarki mamina, Allah ya bar min ke tare da Dady na. Dadin ne kansa ya amsa, amin amin. Ya kara sa shigowa suna masuayar fara'a. Dadyna ya tashi lfya? Na tashi lfy Doktna. Suka gaishe shi cikin annushuwa, duk da bai san sirrin ba, xuciyarsa tayi masa dadi. Don haka ya xauna aka kawo masa abincinsa su ka fara ci tare suna kara kwantar masa da hankalin. Sosai kuwa hankalinsa ya kwanta, yana ganin tamkar an daura auransa da mama, tunda yana da magoya baya ta kowanne bangare [12/01 18:24] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 2***9 Abba bai ga ta zama ba, 7:30 suka kama hanyar minna shida Alh. Adamu tare da Umma, domin ita tana bukatar ganin likita. Saboda ha ane aka tafi da Inna saude don ta rinka taimaka mata. Basu iske abdulkareem a gida ba, ya riga ya fita aiki. Hankalin Aunty Rabi ya dugunxuma nan da nan ta dauki waya ta kita wayar ofis dince, Yaya abdul yaji kamar zai mutu, saboda tsabar bacin rai, amma ba yadda zaiyi ya fito saboda tsarin aiki irin na banki. Daga nana aunty amina ta kira, itama ta shaida mata, kafin ayi haka labari ya gauraye ko'ina. Asibiti suka fara aje Umma tare da inna saude. Aunty Rabi itace jagora domin asibitin da banki ke da reg da su ne. Daga can da Abba da alh. Adamu suka dumfari gidan marafa. Da ganin su, gaban Mami ya fadi, fara'ar karfin hali kawai takeyi. Bayan su natsu a falo. Abba ya tambayi marafa? Tace, ai kuwa yayi sammako ya tafi Lafai, don shaidawa mutannan gida maganar daurin auren, shi kuwa ango na san ya ma kai zariya yanxun Insha Allahu. Kasan a can yawancin abokansa suke saboda can yayi krt. Ina fatan lfya? Ya sauke numfashi idanuwan sa suka kara juyewa yace, babu lfya Hjya, Ki Innalillahi Wa inna ilaihir raji'un! Alh. Adamu ya gaya mata. Ya gayara xama, yace hajiya wannnan al'amari babu dadin ji, a takaice dai sakeena ta gudu tun jiya har yanxu ba mu san inda take ba. Tsaye ta mike dafe da kirji, ta yi me? Ta kame a hakan bata iya kara komai ba. Abba yace, nayi iya yina Hajiya, amma mama ta nuna min ta karfina, hanyar da zabarwa kanta ta wuce da sani nan. Kuyi hkr hajiya, ni ban ma san da kalmar da xan gaya maku ba. Ta koma a hankali ta zauna cikin kasala tace, ai shikenan, duk abinda Allah yayi daidai ne, mu mun hkr, Allah ya musanya wa Al- ameen da mafi alkhairi, sukayi ji. Shiru kafin Abba yace mu na nan garin nasan har Alhji ya dawo. Itama hajiya tana nan na kawo ta asibiti tun jiya ciwon ta ya tashi abin sai yadda Allah yayi. Ta maida tagumi tace, dole Umma tayi ciwo, ubangiji Allah ya bata sauki ya kuma shirya mana zuri'a, suka amsa amin. Suka mike sukayi mata sallama suka tafi. Hawaye suka kubcewa mami, hannunta a kunci tace, ta faru ta kare kowa sai ya hkr! Tab, wannan yarinya ta daure min kai. Allah kayiwa Al-ameen sakayya! Iya da ladi suka jiyo hajiya na sambatu, suka fito suka taushi xuciyarta, babu bata tym ta sa driver ya kaita Lafai. Gado aka ba Umma, saboda yanayin jikin nata, yana bukatar kulawar likita sosai domin jininta ya hau, har ya haye yadda ko alama ba 'a so. Anan su abba suka ci gaba da zama har karfe 4. Yaya abdulkrm ya samu ya baro ofis. Kai tsayr asibitin ya nufa a sukwane. Da ka dube shi, kasan ransa a nbace yake, yana ganin Umma kuma al'amarin ya kara gigita shi. Ya dubi Abba ido jajur! Yace, yanxun wane mataki aka dauka? Abba yace, ni na sallama mama, tunda ta iya toazarta ni haka. Na kuma je gidan su Al-ameen, matslar kawai ban same su bam duk sun tafi raba goron gayyata, sai hajiya na samu shaida mata. Alh. Adamu yace amma ni ina ganin zai fi kyau abada cigiyar a gidajen Radio da Tv. Abba ya amshe, da kudin wa? Saceta akayi? Ba xan kara asara ba, yadda ta sa kafa ta bar gidana, ta tozarta ni, ta wulaknata ni, ta nuna min ban isa da ita ba. Wlh ni ma na hkr da ita. Ba xan yi mata baki ba, dan ko bance wani abu, tabbas ita da kanta ta kai kanta mkrntar koyo hankali. Za ku ce na gaya maku. Taje duniya cem ta ishi kowa riga da wando har da mayafin yafawa. Ya abdulkrm ya numfasa, yace ta yiwa knata, Allah ya shiryar da ita, yasa ta gane, suka amsa da amin. Jimawa kadan ya ba Aunty Rabi mukullin mota ta wuce dauko su Ameera daga sch. Kai tsaye ta wuce da su gida. Ta kama hidimar shirya abinci. Tana gamawa ta kwashe gaba daya da yaran suka koma asibiti. Ta iske kofar dkin da Umma take dankam! Da Jam'a, ashe bayan tafiyarta kadan su ya Abdul kadir da abdulrhmn suka iso. Can kuma sai ga dady da mami. Al-ameen ne kadai bai dawo ba. Duk tabisu ta gaida su. Dady kam yama rasa yadda xai fassara al'amarin Allah ya sa bai riga ya yayyada xancen ba ko 'ina, iyakar sa cikin babban gidansu. Allah ya kawo Mami tayi masa birki. Shi kansa yadda yakeji a tym din, idan xa'a gwada jininsa dole ace ya hau, amma daya iso ya dubi halin da iyayen Mama ke ciki sai yaga ashe shi nafila ne, tashin hankali na inda yake. Shi yasa ya nutsu sukayi magana ta fahimta da abba...... Ya Dubi halin da Iyayen Mama ke ciki sai ya ga ashe shi nafila ne, tashin hankali na inda yake. Shi yasa ya nutsu sukayi magana ta fahimta da Abba. Suka dauki komai suka barwa Allah tare da rokon Abba daya amince ya bawa mama wanda ta sake xaba. Abba bai ce komai ba anan. Don baya jin zai iya ba Danliti 'yarsa su hada zuri'a da mutuncin sa da komai a gari. Yanxun tunaninsu dan gogan. Yaya al'amarain zai kasance? Bayan abba ya kauda masa duk wani shakku, ya bashi tabbacin babu wani face shi, shi ya kara karfafa masa gwiuwa har ya sami kafar tafiya gayyato abokan taya shi murnar angwanci? Wannan amsa sai wanda ya gani da idanuwansa. Gab! Da kiran sallah magriba duk suka bar asibitin, aka bar Inna saude ita kadai tare da Umman, wacce har yanxun barci takeyi, domin allurar da akayi mata mai karfi ce sosai, saboda ana son ta samu hutu kwarai da gaske. Su dady na isa gida, kamar tare suke da Al-ameen. Bai fhimci komai a fuskokinsu ba, don basu yarda yaga sauyi ba ya baje a kujera yace, wsh! Ai fah an fara kenanm kinji yadda naga ji Mami? Ta danyi murmushi tace, dan Iya kena, to abinda ya kamata ka hanzarta yin wanke ne, don gab ake da kiran magriba. Haka za'ayi Mami na, dadi ya aka baro mutanan Lafai? Ina fatan zaka jaddada musu su taso da wuri? Wannan ai dole ne, kama san kawunka ba shi da wasa. Yana ta far'a gaskiyya ne ni ma frnds dina ne ce masu kai tsaye su wuce Fandagori, ai gidan Uban dawaki ba boyayye bane, suna tambaya za'a nunna masu. Dadi yace, kayi daidai, yanxun tashi ka shiga wankan nnima shi xanyi aga wanda xai riga fitowa cin abinci. Ya mike xumbur! Yana dariya ni ne xan riga Dadi, to shikenan, mami ki na ji ko? Idan kuma na riga shi bulala tara, tace ni kuma xan cikashe dayar, su zama goma. Na yada. Bai jira komai ba ya kwasa da gudu, ya shige bangarensa. Mami ta bishi da kallo. Dadi ya sa hannu ya cire mata tagumi yace, ke ma tashi ki daina damuwa. Ta sauke numfashi, amma ba tace komai ba, ta yunkura ya taimaka mata ta tashi suka wuce. Kowa ya shige dakinsa. Al- ameen ya fara fitowa falon, ya nufi gefen tebur inda ya hangi ladi na jera abinci. Ya isa wajen yana fadin, angaida Maman abinci. Tayi dan murmushi. Tace ni ma na gaida dr. Yace na kusa dina cin abincinki Ladi, ina ganin daga yau nai masa bye bye. Tayi 'yar dariya, to aci gaba ne dr. Amma ina ganin akwai gobe kafin amaryar ta iso ko? Ya gyada kai, yana dan murmushi, wa ya gaya miki xan dawo ni kadai? Tana 'yar dariya ta amsa, au can xaka zauna? Kafata, kafarta, zata sake magana, ya dakatar da ita, shisshhh... Tayi tsit! Tana kallon sa yana boyewa bayan kujeru. Dadi ya fito mami na biye dashi, madalla, kinga bulala ta hau kan danki, kira shi na tsatstsala masa. Tace, yanxunn nan ma xaka ganshi a sukwane, kwai ganin sa sukayi yana gyara xaman kujera xai xauna. Gaba daya suka kwashe da dariya. Ladi na tasya su sannan ta bar wajen. Dady yace, gaskiyya ba haka ake yi ba, ai dai sai ya bari mu fito tare ko mami? Dariyar Al-ameen ta karu, yayin da Mami ke fadun, kaji wayau! Ta xuba wa kowa abinci yaci, suka kashi suna ta biye masa, suna labarin biki. Bukatarsu ya cika cikinsa, kuma ya ci sosai. Bayan su kammala Dady ne ya fara barin tebur din Al-ameen ya byi shi xasu yi wata magana, nan da nan ya mike ya bi bayansa. Mami ta kwala wa Ladi kira tace ta gyara kan tebur din, ita ma kai tsaye ta wuce, ta iske su xaune bisa kafet. Dayan gefen ta xauna, suka sanya shi tsakiya. Dadi yayi gyarn murya yace, wasu 'yan tamnbayoyi xan yi maka Al- ameen, ina fatan xaka nutsu ka bani amsa shakikiya. Da farko dai shin Al-ameen wa yake badawa, wa yake hanawa? Yace, Allah. To idan ya baka, sannan ya dawo ya karba, me yakamata kayi? Ya amsa, nayi masa gdya, watakila ya musanya min da alkhairi, ko Mami? Tace, Gaskiyya ne! Dadi yace, Madalla, abinda nake ka sanya wa ranka kenan. Idan har ka tabbata tsakanin ka da Allah ka amsa min tambayoyi na. Ka kuma san imani shine cikar dan musulmi, ko ba haka ba? A salube yace, sosai dady. Yauwa, to kayi hkr maganar da xan gaya maka. Nasan ka na son sakeena, sannan kayi imani Allah ne ya hadu ku ya sanya maka sonta, a da mu na ganin kamar itama tana sonka, kamar yarda kake sonta. Amma yanxun ta nuna yaudara ce kawai, saboda haka ka hkr da ita. Kamar yadda kace Allah xai musanya maka alkhairi. Ya dubi Mami, ya juya ya dube shi, Dady ban fahimce ka ba, ai sakeena na so na, xuga ce kawai kuma na tabbata da xarar aka daura auranmu, ni masan yadda xan da hankalinta gareni. Dady ya ka kada kai, maganar ka dawo da hankalinta gareka duk ya kau. Al-ameen sakeena ta gudu tun jiya babu wanda yasan inda take saboda haka nake rokonka arziki da ka kwantar da hankalinka, kayi imani da furucin da kayi daxu, Allah ba xai bari kasha wuya ba. Ya Dubi Mami fuska kunshe da tashin hakali yace mami ban fahimci ta gudu ba? Me dady yake nufi? Tace iyakar kiyayya sakeena ta nuna maka, tunda ta xabi ta dauki akwatinta ta bar gidan iyayen ta ada ace ta aure ka. Ta xabi ta ci mutuncin mahaifanta akan auranka. Wulakanci ya kai makura Al-ameen, ya kamata ka nuna mana ka haihu dan halas, kace kai ma ka hkr da sakeena. Ya xura mata ido, du sun kadu, mami kina nufin an fasa daura auran gobe? Tace abinda Abbanta yayi sammakon xuwa shaida mana kenan, ia ske ba ku nan kun riga kun tafi gayyata, ni na bi dadynka Lafai na dakatar da shi. Kai ma ina so ka dauki waya ka kira abokin ka dr. Lawal ka gaya masa an fasa, don ya gaya wa saura kar su yi wahala. Ya kada kai yace, baxan iya ba mami, na rantse da Allah sakeena na so na, ina xata gudu taje? Ban yarda ba mami sace min ita kayi, don a raba mu.... Rufe min baki! Mami ta daka masa tasawa mai karfi, daga nan ta balle da masifa, kar ka yarda Al-ameen, amma ina son ka sani, babu maganar auranka gobe da sakeena! Idan kuma ka sake tak a wurin nan sai na tsinka mata mari, don ka gane ba wasa muke yi da kai ba! Yaya ana rarrashinka ana numaka gaskiyyar magana ka naso ka akrya ta mu? Sakeenar banxa sakeenan wofi? Ita kadaice mace a duniya? In sake jin xancen ta abakin ka sai na saba maka! Ku ma ka sani, daga daren yau ka fara shiri gobe xuwa jibi xaka koma sch! Kaji ko baka ji ni ba? Ya aje kai kasa. Dadi yasa hannu ya dago fuskarsa. Tuni hawaye suka wanke masa kunci, shi ya fara fadin, me yasa zata gudu ta barni Dady? Ko baxan hkr da ita ba, ai bai kamata ta gudu ba, hatsari ne babba ga diya mace, wa ya san hannu da take yanxun? Mami tayi caraf? Ta cafke, tana hannun wanda take so. Dama ka daina bata hawayenka a banxa. Sannan kama kunnunwanka da kyau ka ji ni, tun daga ranar da ka daina jin muryar sakeena awaya ta daina sonka, ta mance da kai, ta share ka a rayuwarta. Saboda kin da ta ke ma. Sakeena ta diro daga mota, da abin ya zo da karar kwana da yanxun an kusa mata sadakar arba'in. Sakeena tayi kwana da kwanaki tana yajin cin abinci, tayi ta suma ana mata karin ruwa a asibiti. Kai saboda kiyayyar ka, gabada dabi'iun sakeena suka sauya, bata gannin kowa da daraja, nballe ta saurari fada, da iayeynta da 'yanuwanta ke mata ba dare ba rana. A karshe sakeena ta aikata abinda yafi komi muni akan diya mace. Duk saboda bata sonka, ashe ya kamata ka hankalta kasan halin da kake ciki, don kai ba yaro bane, kuma ba alfahari ba, ilimi muhammadiya da boko sai dai a yiwa wani gori ba dai kai ba Al-ameen, duk kuma wanda yayi imani da kaddara, baya tabewa Al-ameen. Ka maida al-amarin ka wajen Allah shi xai maka magani. Ya dube su daidai tamkar karamin yaro, murya na rawa yace, gaskiyya ne Mami, duk abinda ki ka fadi na yarda, kuma na hkr da sakeena, sai dai son ta ba xan iya cire shi cikin raina ba, saboda ba ni na aje shi ba, kuyi hkr, ku yafe ni, idan furuncin danayi ya muku xafi, sannan ina rokon ku don Allah da son Manxonsa, kar ku kullaci sakeena cikin xukatan ku akan wannan maganar. Wlh har yanxu ina ji ajikna sakeenna tawace. Dady ya rungumo kafadunsa yace, shikenan,ya Isa, munji rokonka mun amsa. Zamu cigaba da taya ka addu'. Yanxun abinda nake sonka da shi shine, ka kira Dr. Lawal ka gaya masa, don su sani. Sai dai in baka lambobin ka kira shi dady, bakina ba xai iya furta mummunan labarin nan ba. Ya mike ya jao durowar dadi ya dauki biro da paper ya rubuta ya bashi, ya mike xai fice, ya kusan kaiwa kofa mamy ta kira shi, ya juyo tace kayi nafilfilu cikn dare. Allah zai saurareka, ya nisa kafin yace xanyi mami. Ya sa kai ya fice. Mami ta dubi dady ta hadiye hawayenta, tace gobe in Allah ya kaimu xan koma Lafai wajen baba liman in samo masa ruwan addu'a ya sha ya sami sanyi cikin ransa. Yace hakan ma yayi, Allah ya sa mu dace. Tace amin. Ta jawo wa dady kan waya ya nemi Dr. Lawal, ya sanar masa. Yace an fasa? Subhanallahi? Wannan abu baiyi dadi ba. Don girman Allah dady a samu a daidaita, wlh Al- ameen yana son yarinyar nan ba kadan ba. Ya ce ba sai ka rantse ba Lawal, ni kaina nasan hakan, amma fadan da ya fi karfinka dole ka maida shi wasa. Mu nan muna ta addu'a Allah ya zaba mafi alkhairi. Ya numfasa, yace amin. Ina Dr. Yake? Ai sai da ka neme shi xuwa gobe, yanxun kam babu sukuni yana dakinsa. Yayi dan jim, kafin yace Allah shi kyauta, amma ayi kokari Dadi idan xai yuwu a sasanta. Ba komai mun gode a gaida Iyali. Zasuji, ya aje wayar tare da tsananin mamakin wannan abu? Me ya faru haka da xafi? Haka ya kwana da tambayar kansa, don babu alamar wata mishkila a tattare da soyayyar abokinsa da sakeena, ko daya zo sanar da xancen auran ma babu alamat akwai matsala babba. Labarin barci dai babu shi a wajen Al- ameen kuma xuciyarsa bata daina karyata masa xancan ba. Ko alama ta ki amsar sakon, saboda tsabar shakkun da yake ciki, wai sakeena taci amanarsa? Har 8am yana kan sallaya, ba don wai yana sallah ba, a'a kasala ce ta hana masa tashi. Mami tayi sallama ta shigo da tiran kayan karin safe. Ya xubo mata ido. Mami tayi sallama ta shigo da tiran abinci, ya xubo mata ido, ta aje a agbnsa, ta xauna gefe, sannan yace, ina kwana mami? Lfya lau, ina fatan ba ka tsananta wa kan tunani ba? Ya kada kai, ya xanyi mami? Kin san ba yin kaina bane? Ta dafa shi a sanyaye, kllm ina kara gaya maka Al-ameen, kai kadai ne garemu, kuma ka zama tamkar dubu, ba gare mu kadai ba, gabadaya al'umma za su so rayuwarka ta daure cikin fciki da walwala, saboda muhimmancinta, ina so ka san wani abu yau. Wlh na yi maka rantsuwar da ba kaffara da rayuwarka ta salwanta, gara ni in mutu, don na..... Ya rufe bakinta, a hankali, idanuwansa taf, da hawaye yace, kiyi shiru mamina! Da ni dake zamu rayu da yardar Allah cikin farinciki da kwanciyar hankali. Har ga Allah na hkra da sakeena mami, kawai ciwon fitar son ta ke azabtar da ni. Ka kwantar da hankalinki mamina, a hankali zaki gan ni yadda kike so. Tayi dan murmushi tace, Allah yayi ma albarka! Da sauri ya kwanta a kafadarta yana fadin amin mamina. Zauna da kyau na hada maka brkfst. Kaga masa na sa iya ta shirya maka da sassafe, na san kana so kuma kana kewarta, don ba'a samu a Rasha. Ya bita da kallo dauke da tausayi. Yace nagode mamina, amma tare xamu ci ko? Ta jawo fileta tana fadi ah! Me zai hana? Bari ka gani. Ta loda waina a plate tana xuba miya ya ware ido, yace mami kin cika abincin nan! Ita ma ta ware idon tace injiwa? Ni da kaine fa? Sa hannu ka gani ko asa man shanu? Ya kada kai, a'a kinsa banso kayan karni. Ka bar dadi yaro. Yayi 'yar dariya yace Allah ko? Ta tura masa a baki tace, haba ai ba sai na fadi ba. Dady yai sallama dakin ya karaso da sauri yana cewa iye! Masa kuke ci kuka nuna min 'yan ubanci? Gaskiya ba ha akeyi ba, ai sai ku kira ni ko? Ya tambaya yana kallon al-ameen cikin ido. Ya gayara masa wwuri, yace laifin mami ne, xauna abinka Dadyna. Ya xauna yasa hannu ciki, yace ai mami akwai rowa, Allah dai ya tsaga da rabona. Suna dariya ta bashi amsa, ka san kuwa da na kawai, na aka yi ma. Kaji ko? Tafi son ka akaina. Yayi wuf ya rike hannu da yake kokarin kai loma yace, ba xaka ci ba sai ka fadi! Gaya min, mami ta hau dariya shima ita yake yi. Dady na ga dai da ta rikice kanka. Tace babu wani sai kai, sannan aka sameni, ko ba haka bane mami? Tace ni xaka tambaya? Dady ya karbe yanki wainar daga hannunsa ya tura masa baki, yace cinye dana, ka bani amsa daidai. Bai gama cinyewa ba ya dauko cinyar kaza ya tura msa, ka ra da wannan kayi brush! Duk suka sa dariya, ganin al-ameen na neman kwarewa, kan kace kwabo sun yaudari Al-ameen ya cinye wainar da mami ta zo da ita, domin dai shi suka yi ta turawa da wasa da dariya ya take cikinsa. Bayan sun kare, mami ta dube shi tace yanxun ka tashi ka shiga wanka ka kimtsa, muje asibiti ka gaida Umma.... Umma? Me ya sameta? Tashin hankali ya sa ta sami hawan jini tuntuni, maganar jiya kuma ta kara birkita ta jininta yayi mugun hawa. Tana nan asibitin sun bata gado. Jiyan abba ya taho da ita. Ya marairaice yace, Umma na asibiti tun jiya baku gaya min ba? Ban dadin hakan ba, dady yace kayi hrk, ganin kai ma baka da sukuni ya sa muka kyaleka, kaji da guda 1. Ya mike yace ba sai nayi wanka ba, yanxun xan tafi, idan na dawo nayi, bai saurara ba ya wuce ya jawo dirowa ya dauko key ya fice. Mami ta biyo shi tace Al-ameen, ya tsaya cak! yana dubanta, ta matsi sosai ta dafa shi, ka tafi a hankali, idan kaje kace ina gaishe ta, ni ma xan biyo in na dawo daga Lafai, ya dan lumshi ido, ya bude yace xan kula mami, amma me xaki je yi Lafai? Tace uzurina xai kaini. Allah ya kiyaye hanya, ta amsa amin. Ya daga kai dubi dady dake tsaye yace, sai na dawo dady, to ina jin ma xan sameka asibitin. Yace shikenan sai kazo. Ya juya yayi waje, su iya na kokarin fitowa su gaisa. Amma ina saurin da yakeyi, ya hana su su same shi falon, tuni ya kai ma'ajiyar motocin, ya murza ya bar gidan. Umma na xaune an jera mata filo, ruwan lipton kawai ta iya kurba, ya xuna cikinta. Likitan ne yace ta dan jingina kadan ta huta. Duk 'ya'yan sun kewayeta, abba na xaune gabanta bisa kujera. Gaba daya tausar xuciyarta suke yi don ta fidda abin a aranta. Sallamar al-ameen cikin dakin ita ta dauki hankalin kowa, suka amsa kona masa duban tausayi, ganin yadda ya xabge kamar mai ciwo, wai don ma su mami na yin iya kokarinsa akansa. Ya bisu daidai sukayi musabaha, sannan ya tsugguna gaban Abba suka gaisa. Tuni ganinsa ya sa hawayen Umma suka tsinke, yayi shiru a tsugunne. Abba ya dafa shi, yace sai ka dawo ka sami labari maras dadi? To ina so ka kwantar da hankalinka kayi imani da kaddara, ka sani yau da ace mama na da 'yar uwa xan baka ita, don in nuna maka iya kaunar da muke maka. Mama ta zabi ta wulakanta mu, shi yasa na ke son kowa ya cireta a ransa, mu manta da ita mu kyaleta duniya ta hora ta. Kayi hkr kaji? Ya goge kwalla yace naji abba, kuma nagode akan iya kokarin da kukayi min, amma abba ina rokon ka, don girman Allah ku ya fe mata, sannan ku sanya mata albarka, a auran da xatayi. Duk sukayi shiru, kowa ya xuba masa ido. Tausayin sa na ratsa su, umma ta goge kwalla. Tace Mama ba abar tausayi bace Al- ameen, don haka ka daina rokon ayi mata afuwa laifin data aikata. Ya kata matsowa gaban gadon yace, ba haka bane Umma, ki san sharrin shaidan, sannan xuciya bata da kashi, ba 'a son ran mama zata aikiata wannan abin ba, xuciya ce ta saka mata, na tabbata duk ranar da ta nutsu tayi tunani xata gane lallai bata kyauta ba. Don Allah Umma ko ina nan ko ba nan, idan Mama ta dawo ku amshe ta hannu 2, ku samata albarka. Insha Allahu shaidanin daya rinjaye xuciyarta, xai kyaleta, ta dawo diya ta gari kamar yadda take da. Abba ya kara dafa shi, yace idonka ya riga ya rufe a son mama, shi ya sa baka kallon girman laifin da ta aikata. Ya juya ya dube shi, ba haka bane Abba nasan ina son mama kuma har na mutu ba xan daina son ta ba, amma ku yafe mata, don rayuwar ta, tayi kyau

Chapter 14 of 28