Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shakka ta muhammad. Allah yatabbatar da lkhairi. Tace, amin. Suka kara tafawa, ai zaki ganshi, dan kyakkyawa shi ga addini. Tace, baikai Aminu na ba dai. Ta tabe baki tace, naki kikasani, ni kuma nawa na sani. Kowa da gwaninsa.Tace, gaskiyarki, kuturu ma sarki ne a gidan sa. Shikika raina ma wayau? Tace, ba haka bane wlh, aimisali ne kawai. Tace, na gane kowa jin kamsa yakeyi a inda yake takama? Mama ta gyara zamatace, har kin tuna min, wai yahse wannan me masunansa? Wannan da aka jefe babansa wajenkwartanci? Tace oh! Kina nufin Dan liti? Yauwa shimyaushe ya dawo gain? Tace, ai ya jima zai kai satibiyu. Ta tabe baki, na gaua bude wani shago ne? Kai mutane ba su da tunani, menen na barin Dan liti yaxauna garin nan har da ba shi hayar katon shago?Tace, manyan gari ma basu kore shi, wai zai koreshi? Wai kin san ma wani abu? Yanxun nana xan wuce,wai sannu 'yan mata yace dani. Tace, haka yake,anyi gadon banza ido a mata. Shi jinsa yake mai kyau, marasa tunani na binsa yana lalata su. Kingashekarunsa shida rabonsa da garin nan, amma yanadawowa 'yan mata na masa layi, yana tijara su. Takaici ya ishi mama tace, kwadayi, ba an ga ya dawo daabin duniya ba? Ai mata mun shiga ciki, kwadayi kekai mu ya baro mu. Allah ya shiryemu, tace ameen dai. To wai shi da yayi miki magana menene nufinsa?Ido waje tace oho! Shi ya sani, ke da baki wajen, idankin tanka, nima na tanka masa. Allah ya isa ma nayimasa, daya katse min tunanin dokta na. Suka tafa,Baraka ta mike ta dauki kwandon kayan ta shige dashi kicin. Mama ta dauki tsintsiya ta sa ruwa ta kora wurin, ta share tas! Suka koma dakin Baraka. Hirar takoma can tare da tsara shagalin biki. Gab da akekiran magriba. Mama ta baro gidan Baraka tayo matarakiya, suna rike da hannauen yaran har bakin titi.Anan Baraka ta tsaya tace, to sai na zo goben ko?Tace, ina jira, don Allah ki zo da wuri. ISA, lah! Kinga mutumin naki da zai rufe shago, ya hango ki ya fasa.Kar ki bi ta wajen sake hanya. Kinsan Allah bai isaba, bazan dauki nisa saboda shi ba, idan ya matsamin sai ya sha mamaki, don xan yi masa wnkinbabban bargo, kafin nan bar garin nan. Ina son kimatar likita, amma ki tsaya bata lokacinki wajen danliti asara ce, ki wuce kawai, shi ya fi. Allah kokawata? Don dai ba ke yake wa magana ba, shi yasahaushin bai damunki. Tayi 'yar dariya, haka ne, ammaina rokon ki, karki kula shi, ba don ni ba sabodaDokta. An gama, kinsan wani abu? Cewa yayi idanwani yaji murya ta kawai, ya cuce shi, abinda na tuna kenan. Saboda haka kwalelensa, ba zaiji ba. Suyi 'yardariya. Kuje, yanxun xa'a kira sallah, sai goben. Allahya kaimu. Ta sallamu su ameer, ta tsaya sukatsallaha, sannan ta juya ta koma. Kai tsaye mama tazao zata wuce. Dan liti bai daddara ba, ya sake yimata magana, 'yan mata an dawo? Ko kallo bai isheta ba, wannan karon, ya daga murya ya sake fadin,Haba 'yammata ai rika sauraran masoyi mana, don ba'a san inda rana zata fadi ba! Kai, Dan liti yayi sa'atayi alkwarin ba zai ji muryarta ba, amma da yajiamsar da ba zai sake marmamrin kula ta ba. Dawannan haushin ta iso gida. Suka yi alwala da yaran sukayi sallah. Dare ya raba barci, yaki zama cikinidanuwan ta saboda zafi biyu suka hade mata, gakewar muryar sanyin ranta, ga kuma takaicin rashinba Danliti amsa, har yanxun yana mata kaikayi axuciya. Idan ta tuna kalaman sa na karshe, ta kanjikamar zata mutu. Wai ba 'a son inda rana zata fadi ba? Ta kan kuta, ta shanye hwayen idanuwanta. Hakata wayi gari da ramar rashin barci, shi ya sa take jinkasala. Xuwan Baraka ya sa ta gyagije ta mike sosai,suna ta aiki. Ba'a jima ba, ango ya iso. Gida ya karagauraye wa da shewa da guda. Bayan sallar la'asarmutanen Abuja suka iso. Sannu a hankali gida ya cika da 'yan biki na nesa da kusa. Tundaga lokacinake ta dora tukunya ana saukewa.... Ranar juma'a akwai dinner a kd. Don hakaango ya kwashi su mama da baraka tare da su danDanlami ya wuce da su. Mama kam sai da mucetsarki ta tabbata ga Allah gwanin halitta, ka ranste daAllah itace amaryar. Tana gefen Yayanta, ya na ji daita. Samari kowa idonsa na kanta. Cikin abokansa kuwa babu wanda bai taya ba, amma ya ce mus ansanya mata ranar 'yar watanni suka rage bikinta.Kash! Duk wanda yaji sai ya numfasa. Lallai Al-ameen gaskiyya, sai ma yanxu take kara jinjinwatunanisa. Bata gama shan mamaki ba, bayansundawo daga diner, misalin goma na dare, suna sashin baki a gidan ango, inda aka xubawa amarya kayandakinta. Suna tare da Baraka hirar dinner kawai sukeyi. Dan lami ya yi sallam ya shigo yace wa mamayaya Ali na kiranta. Tace lfya? Yace kalau, yana canbaya. Ya fice abinsa. Ta dubi Baraka tace, kinji watasabuwa kuma. Tace, wata tsohuwa dai, ai kun jima da Yaya Ali. Abin ne ta motsa, kin san gyambo ne, tace,Allah ya ba shi sauki. Ameen dai. Ta figi gyale ta yafata same shi a bayan gida yana xaune bisa dakalinsokawe da fara'arta ta tayi sallama, ya amsa. Ganinfusakar ta sake ya sa shi ma jin sanyi cikin ransa,tace wai kana kirana? Yace eh ina kuma fatan xaki saurare ni, ta kara matsowa tana fadin me hana yaAli? Meya faru? Ya mike daga inda yake yace ga gurixauna, tace a'a yay Ali kayi xamanka kawai, no kixauna ai ni nace ko? Ta xauna tana murmushi sannanta dube shi suka hada ido, ya akayi? Yace babukomai Mama, kawai so nake muyi hira. Ta sunkuyar da kai tare da numfasawa. Yace nasan tuni kin mantada ni cikin ranki, amma ni na kasa mama, waccesahwara xaki bani? Ta dago kai ta sake dubansa,tace me xaisa na manta da kai Ya Ali? Karfa kamanta jininmu daya, dubi fuskokinmu kamar mu daya,don me xan manta da mutum kamar ka? Ashe lallai xan iya mantawa da su Ya abdulkadeer. Ya saukenumafshi yace, haka ne, amma kin san ina miki waniso na daban ko? Sao dai ke kinyi nisa da soyayyarwani, har kun kusa aure. Ba wai ina masa ynaka bayabane, so nake ki gane har abada ni mai sonki ne, bakuma xan taba fidda rai da ke ba, sai ranar da na ga an shafa fatihar auranki. Xanyi farinciki, idan har zakiyarda mu yi hira koda labarin Al- ameen zaki rika bani,wlh xan saurareki. Ta runtse ido, tausayin Ya Ali yaryfeta, sai dai runtse idanuwan da tayi bata ganinhotunan kowa face na Al- ameen dinta. Tayi sauri tabude, idanuwanta suka kada, a sanyaye take cewa, kayi hkr Ya Alli, komai mukaddari ne daga Allah. Kayiaddu'ar Ubangiji yayi maka sauyi na alkhairi. Sannankuma ina so ka sani, ban taba kin ka cikin raina ba,kuma ba xan taba kinka ba, shi aure nufi ne na Allah.Shi ne yake shirya abinsa yadda yaso. Ina fatan kafahimce ni? Ya gyara tasyauwa yana kallonta, yace, na fahimce ki mama, na gode da gudunmawarki. Toamma bana so kana damuwa. Yayi dan murmushi, nadaina kanwata. To kai sai yaushe zaka yi auran? Sairanar da na daina ganin Mama a matsayin budurwa.Ta kalle shi tana 'yar dariya, ka tsufa Ya Ali, ka fagirmi ya Abdulrahma. Kana so a fara maka kiran gwauro ko? Hakan bai dameni ba. Ni ya dameni, aceyayana gwauro. Yayi dariya, nace ki bari na tabbatarna rasa wacce nake so, sai in rufe ido in kwaso kowace ce inyi maneji. A'a yayana, tsakani da Allahzaka aureta, ai sunnan ba'ayin ta da maneji. Iba dace,ibada kuwa akwai hakkoki cikinta. Gaskiyane, amma kin san shan kojo kwanciyar rai. Kuma kowane soyana da mizaninsa a xuciya, ni na san babu macenda xan so tamkar yadda na ke sonki. Ya Ali kenan,ka bar maganr nan don Allah, na yi karya ne? Banfada ba. Bari na shiga ciki, kin gaji da surutu na ko?Ta kada kai, a'a wlh kawai barci na ji ya soma kama ni. Kindai gajin kena. Eh, toh da xak duba agogonkakila ka ganr dare yayo. Ya duba agogon ya dubeta,sha daya da rabi ne kawai. Tayi sauri ta mike, wuu! Aikuwa na kawai bane, dare yayi yaya. Kai kankaidanka ganni da wni a wannan lokacin, dole ka koranigida. Uhm hakane, amma banda Al-ameen, don ban isa na rabaki da shi ba, do ne? A matsayinka nayayana, idan bayi dai-dai ba, dole ka hukunta ni kotare da wa nake. Yayi dan murmushi, to na gode. Saiwani lokacin kenan? Uhm..... Sai da safe. Allah yakamu lfya, Ameen. Ya wuce ba tare da sake waigowaba. Shi kuwa kallonta yake tayi har kule ya sauke numfashi, ya koma inda ta tashi ya xauna, shiru jimsannan ya kada kai cike da damuwa. Damuwar mamaba a kan tausayin Ya Ali kawai ta tsaya ba. Ji takekamar tayi abinda ba dai- dai ba ga Al-ameen. Shi yasa xuciyarta ta rasa sukuni ta rika korafo wajenBaraka. Allah ya sani ba tadi tayi da Ya Ali ba, illa ta saurare shi ne kawai don ta kwantar masa da hankali.Yaushe rabon da yayi mata magana irin wannan?Tabbas ta gane yana cikin matsala, dalilinsa da ya sakenan ta tsaya ta saurari kalaman bakinsa, wadandatake ganin amayo su xasusa ya sami sukuni aransa.To ita gashi ta shiga matsalar, gani take tamkar taci amanar doktanta. Ta runtse ido hotunan sa sukabayyana gareta, yana ta cuba murmushi muryarsa nafadin.. [11/01 18:43] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 1***11 Washegari anti amina da anti rabi suka shiryatafiya. Tun dare mama ta hada kayanta tace ita mazata bi su,fasa karin kwanakin da tace zata yi.Gabadaya suka rufe ta da tsokana wai sbda alamin zatakoma.Tace eh sbda shi din ne haramun ne? Ita kadaita san abinda ke damunta. Duk da ta ba danliti amsa,ji take kamar amsar tayi kadan ko alama batason ganinsa balle tahi munanan kalaman bakinsa,shiyasa ta zabi data koma minna tayi zamanta canhar lokacin da alamin zai dawo. Allah da ikonsakuma,anti amina ta kafe tare zasu tafi wannan karon.Gaskia hankalin ta zai fi nutsuwa a minna sbda tana gani bebi alamin tana renon sa yana mata dariya idanta kira shi dokta.Ita kanta anti rabi bata so hakanba,sai dai ba yadda ta iya dole mama ta bi anti aminata nace.Suna ta zuba kayan su a mota.Yara damanya na taya su,bayan sun kare suka kara sallamada kowa duka suka yo musu rakiya har da marya da ango.Mama ta shiga bayan mota ita da malami.Yayaali ya tsaya jikin tagar ya zuro mata ido "wai damadake za'a wuce? Tace eh mana."Na zaci zaki yiwaumma kwana biyu".Tayi murmushi,naso hakan ammaai zan dawo,yaushe kenan? Ni ma sai inzo mugaisa.Tayi er dariya,gaskiya ba zance ga lokacin ba,watakila ma sai alamin ya dawo,"Ke don Allah,kusan wata uku kenan ashe zaki iya tafiya ki barumma tsawon wannan lokacin? Tace ba haka bane Sai ga yaya soja ya fito tare daabba,shi yakatse musu zancen.Abba ya leko,toauta na a kula dakai kin ji? Tace to abba",yayanyace "abba har wanirarrashinta kake yi,jaririya ce? Yaceitace mana,damaina son gaya maka ka dainarankwasar min ita'.Yawaigo gidan bayan yanafadin,rankw ashi abba?Irin wannan?Abba ya bude murfin motaryace,"auta nafito! Fito ki bi abdulkareem. Tafito dage da kai har dakukan shagwaba,masu dariyanayi.Shi ma ya fito dasauri,sorry abba,sorry! Ya kamakunnuwansa yarike,"na rantse ba zan sake ba" tacuno baki tamakale kafada,ni ba zan bi suba.Yaya yace,"za ki tsallen kwado awajen nan,I'm telln you,ki shigamotamu tafi!Ta kara turo bakin,abbayace 'yi hakuri komaki kyale shi".Har ta tura kai zatashige ta sakedagowa ta dubi umman ta tsayekofar gida tanadariya,ta ruga wajenta ta rungumeta,umma zan dawonan ba da dadewa ba.tace wuce kutafi". To Allah ya tsare. Ta saketa,ta kwaso sauri bata san yaddaakeyi ta dawo ta bangaran inda yayaali yake tsayeba,kawai ganinsu tayi daf dajuna,ta bi shi da kallokafin tace,ba zan dade ba,zandawo." Jikinsa yayi mugun mutuwa yace,adawo lafiya"'amin".Ta bude mota ta shiga yataimaka ya rufe kofaridanuwansa na kallonta,Ta sunkuyarda kai,ita kantabata san abinda ya kashe mata jikiba,sannan batasan me take tunani ba,Ji tayi motana tafiya ta dagoda sauri tana daga wa kowa hannuhar suka bace.Ta maida kanta jikinmota ta jawo malami tarungume.suna isowa daidai shagondanliti,daga muryayayi yace "Allah ya kiyaye hanya!Ta ballo masaharara,yaya nta na fadin,"amin""amin".Tana harararsayana mata murmushi har da dagamata gira,ta sakidogon tsaki,"ke da wa? Anti aminata tambaya,tace mantuwanayi.Yayanta yace 'ba zan koma ba!tacenima bance ba yaya ai ba waniabun damuwa bane namanta". Suka fada titi,komadamuwar ne ba zankoma ba lazy girl"tace "lazy soja"ya kyalkyale dadariya yana kallon motarabdulkareem tana bin su abaya yace,ni ko? Za ki shiga guardroom yarinya,jikin ki zai gayamiki".Suka kalli juna ita da malamisukatintsire da dariya haka suka cigabada tafiya. Har suka iso minna anan suka tsyasuka karayiwa juna sallama sannanabdulkareem ya daukihanyar unguwar su,su kuma sukacigaba da tafiya.Sun isa abj lafia,sojoji biyu kegadin gidan suka budemusu get. Bayan sun yi sallolinsukowa yaci abindayake sha'awar ci daga nan mamada anti amina suka shiga gyaregyaren wuri.Karfe tara na darelokacin neda mama ta gama shirin barcibayan wankan datayi.Suna kwance da malami wanilittafin labarin yaratake karanta masa,anti amina tashiga dakin tace,gadoktan ki can akan layi dama yasan yau zaki dawo?Ido waje ta kada kai tace a'a kilasun yi waya da anti rabi ne ta gayamasa,ba mamaki je ki dauka.Tasauko kayan barci ne jikin ta rigada wando ta rugafalon kasa ta dauki kan wayar dakeaje gefe,tayimasa sallama,ya amsa muryarsa nabayyanar dafarin cikin zuciyarsa.Watau abj kikagudo ko?me kikenufi da kika baro dokta acan?'Yardariya tayi tace,shi ma yaji yaddanake ji.Baki da hujja yarinya kikomagun sa kafin mami taci ki tara.Zankoma yallabai,toya karatu,ya rasha?To ba laofoamma rasha kin sansai maneji da nake yi,zuciyata nagun ki myprincess.Tana murmushi nima inatuhumar kadokta,waya gaya maka ina nan?Yace kawai na kira ne inji ko suanti sun dawo,inyi musu barka dadawowa.Sai take gaya min kemakina abj,ta dannumfasa tace ta kyauta.Ko?Allah,dama ina tatunanin ina zan ji ka?Allah sarkisakeenta,to ya biki? Tace anyi an gama lafiya amarya na can tare daangonta.da kyau,saura namu ko? Tayi murmushi batace komai ba,ba zaki amsa min ba? Me zan ce?Bayankasan hakan?yace to Allah ya nuna mana,ki karahakuri na kusan dawowa kin ji? Idanuwanta suka kawokwalla.Na kosa dokta,baki kai ni ba sakeena,ni kadai na san yadda nake ji,kin san irin son da nake miki kekanki kin san ina wahala anan tsawon watannin danayi ban ganki ba sakeena yasa idanuwa na sunmakance alhali lafiyar su lau,dul abinda na kalla bayagamsar dani my princess hakuri kawai nake yi. Tagoge kwallan bisa kuncinta,ta numfasa,no sakeena,pls kar ki gigita ni,stop crying,please!M uryana rawa tace dole in yi hawaye dokta,domin na fi kafuskantar kalubale shiyasa na kosa ka dawo ayi takare,Yace kalubale? Wane iri sakeena ta?kowa zuwayake nema na,kare da doki ma,shiyasa na gudo abjdon inyi musu nisa.Yayi hucin zafi,ya fahimci ta shiga damuwa,kar ki saurare su sakeena kullum ki rikakallon zoben alkawarin mu sannan kar ki manta akwairanar auran mu a kanki. Nauyi ne babba a kan ki myprincess pls,kar wani kalubale yasa ki qi saukewa,kitaimake ni dom girman Allah". Ta kara goge hawaye,ka daina roko na doktadomin kai ma kasan cewa ban iya rayuwa da kowaface kai,idan kana roko na sai in ga kamar baka yardadani bane.Da sauri ya amsa na yarda dake sakeenakema in har kin amince da magana ta to ki sharehawayenki ki daina kuka zuciyata ta daina konewa. Ta share fuska tare da kokarin tsaida hawayenta,nadaina dokta,yace good girl!To bani labari me kikashirya a bikin mu? Tace me zan shirya baka nan? Nikuwa kinga list din nan anan rubuce,karanto min inji?Da farko akwai immunization day,wasu manyamanyan allurai ne na tanadar don amarya.....Dariyarta ta katse shi shima ya fara dariyar,ki tsaya kiji mana!me zan ji?Wannan shirin naka almara ce kamasake.Na riga na gama shiri na ba zan sake ba,yarinyaallura biyu da safe,biyu da rana,biyu da daddare,shidakenan.Sosai ma,duk a jiki na,ah to,sa wasa kiga aiki.Ta cigaba da dariya hankalinsa na kara kwanciya,kokari nsa ta manta da waccan maganarshiyasa ya dage da bata dariya har dare ya fara nisabasu sani ba,ai kuwa yayi nasara don ko data je takwanta bata yi tunanin komai ba,tace labarin dayarika bata har tayi barci mai rai da koshi ne. Kwanabiyu cif!yau zuwanta abj kuma ko a daren yau alameen ya kira sun sha hira tana ta kewar bebialameen ta kwanta barci,sosai take son ganinsashiyasa ta kwaso hotunansu ta tsibe tana kallo hakata bata lokaci tana kallon doktan ta sannan tasumbace shi,ta tattara hotuna ta maida cikinjakarta,ta dawo ta kwanta ta zurawa malami ido amma a zahiri ba shi take kallo ba,wani tunanin candaban take yi,bata san lokacin da barci ya sace ta ba Tsintar kanta tayi tare da danliti bisa benci akofar shagonsa cikin wani irin nishadi na banmamaki.Wani abu suke ci wanda bata tantance komenen ba.Ta sanya masa a baki ya cinye,shi ma yadauko yasa mata?Ta sake daukowa ta kai masa bakishi ma ya kara mika mata sai ta hade da yatsun sa ta cije,ya rika yarfawa yana fadin,"wash! Sakeena! Wlhda zafi! Ita kuwa dariya take yi har da kama ciki,yakawo mata duka ta tashi da gudu ta mika hanyargida,tana gudu tana waigensa tare dayi masadariya.shi kuwa kwala mata kira yake mai karfi yanaamsa kuwwa "sakeena! sakeena!! sakeena!!! Ta yunkura ta tashi zaune dafe da kirji tana fadin,innalillahi wa inna ilaihir rajiun!sharkaf tayi da zufa kumatana ta numfarfashi tamkar wacce ta sha gudunfamfalaki. Ta lalubi fitilar tebur ta kunna ta cigaba dazare ido tana dube dube,mamaki ya isheta tanatambayar kanta 'me ya hada ta da danliti? Barcin da bata sake komawa ba kenan har gab da asuba alokacin ne wani sabon barci ya dauketa,ji tayi ana tabubbuga ta,ta bude ido a natse ta dubi mai tashi Malami ne a tsaye yana mata dariya,gari yawaye anti ki tashi mu yi sallah.Ta tashi da sauri tadubi agogo karfe shida daidai,ta duro ta fada bayi tayoalwala tayi sallah,wani abinda ke daure mata kai shafta mance da mafarkinta,a zahiri ta san tayi mafarkiamma ta kasa tuna irinsa. Haka ta wuni tunani babu kuzari a jikinta kuma ta kasa gayawa kowa. Hattaalamin da bata iya boye masa duk wata damuwartayau ta kasa gaya masa mafarkinta mai ban mamakiballe ya taya ta addua.Dare yayi sosai lokacin dabarci ya sake dauketa kamar jiya haka ta sakeganinta da danliti. Babu bambanci da mafarkin jiya,ta farka a firgice hankalinta ya tashi,gaba daya kanta yayamutse tana jin muryarsa yana kiran sunanta cikinkunnuwanta,shiya ta zuwa yatsunta,ta tashi ta runtseido tamau!Tana fadin inna lillahi wa inna ilaihir rajiun!Sannu a hankali ta daina jin kiran. Ta makure a gadota rasa abinda ke mata dadi a duniya,gab da asuba wani barcin ya sake sace ta,yadda take zaune amakure gefen gado.Malami ke tashinta ta bude ido tadube shi,yace a zaune kika kwana anti? Da kyar tatashi sosai ta zauna,wuyanta yayi mugun rikewa,yakage,ta kasa motsa shi,tace ya aka yi na tashizaune?Yace oho nima ynzu na tashi na ganki a zaune. Ta jujjuya wuyanta tace,wash! wuya na ya rikemalami ban iya motsa shi.yace in kira momi? Tace aa kyaleta, yanxu zai warware in na tashi,yana tsaye yana kallonta tana ta juya wuyan har tasamu ya saki, ka yi alwala ne? Ya ce aa . To jekayimana ka fito, ya wuce ya yayo, ya dawo itama dashiga toilet, ta kama ruwa tafara alwala, Sakeena! Tajian kira ta. Ta waigo da sauri, bata ga kowa b, tayi jim, a tsaye sannan ta ci gaba da alwala ta kare ta fito taysallah. Wannan yinin tayi tunanin Dan Liti, gaba 1mind dinta, ta koma fandogari. Har Anti Amina ta lurabatab cikin sukuni. Yau da wuri Al-Ameen ya kirawaya 8:30 ma bata gama yi b, tana daki ta idar dasallar isha. Malami ya shigo ya gaya mata yaya Al Ameen ya kira, takalleshi up n down tace kace masaina zuwa.. Ya juya ya fice, shi kansa da yake yaro,yaji mamaki , don bai saba gani b, Da taji waya harrige rige sukeyi wajen rcvng. Tay guntun tsaki ta tasorai bace ta sauko falon suna ta hira da malami yanabashi daria. Tayi tsaye, tana kallon sa, kafin yace gata. Ya miqa mata , ta amsa ba fara'a, tace hello.Yace Amincin Allah ya tabbata gare ki my princess...Kai ma hak. Yau kuma yanga kike ji, kika barni damamaki? Ko amarci ne ya fara tun yanxu? Tayatsuna face tace " sallah na ke," Oho yau na bugoda wuri ko? Na kosa inji ki ne my wife.. Tayi far da eyez tace ka kyautah wa kanka...... Banda ke? Watakila, banson gulma. To yakike? Kalau, aa ba kalau b, kamar sakeenata batacikin walwala, waya taba min ke? Wa zaitabani kuwa? To ai ban saba jin ki haka b my princess ko bakida lfyne? Lfy lau nake. Ina shakku gaskia, karki boye minsakeena, gaya mi meke damunki? Ta danyi shiru, hawaye suka cika eyez dinta,murya na rawa Lnibansani ba Dr. Kayimin pryr raina yana baci nekawai"jikinsa yay sanyi karki damu mama in shaAllah zan miki, kinsan Dan Adam ajjizi ne, 9 yake baicika 10 b, dole wata rana kaji ba daidai b. Haka lyftake,so karki damu, ok? Nagode, ki manta kawai. Kinsa wani abu? Kishin kishin naji wai skul dinnansuna son rike ni, kamar yaya? Wai in zauna anan inyimasu aiki.... Banjin zan iya ko da sunyi man tayin.Don me? Ke kingoyi baya ke nan. Baci gaba bane? Niban ga wani abu a cikin sa b.... Ni nagani, wayau nekawai suke mana , a haifi mutum a kasar sa, yayi girma ya gama whlar studyng a kasarsa, tashi 1 watakasar ta gwada masa money ya bar kasar sa. Alhalinal umar sa na matukar buqatar gudunmuwarsa. Ni banda sha'awar wannan, na fi so inyiwa kasa ta bauta, badon kudi b sakeena , sai don tai mako ga masubukata kin gane????? Uhm.... Uhm?? Haba sakina ta, na ce ki sakiranki, ko naji dadi, kina so in shiga damuwa ne? Tayihamma,gaba 1 taji slp ya rufe mata eyez, yayi yardariya ya ce, wannan uwar hamma, ai sai ki cinye ni,barci kike ji? Wlh kuwa gaba 1 eyez dina sun rufe,. Aikuwa ya kamata ki kwanta kiyi slp, in kyale ki ko? Tadan nunfasa, kuma bana son kwanciyar. No pls kijeki kwanta, Allah na yafe, ok? Sai 2mrw zankira inAllah ya yarda, sai da 2mrw ko? Shi ke nan. Ki fa yibarcin, kar ki tsaya tinkng komai. Ta amsa,to. Gudgirl I lov U my prncess. A hnkli ta ce Me too... YaceSo much? Tace So much! Murmushin sa ya kari yace to ayi slp lfy. To. Ta fadi tare da aje kan wayar ta jimatsaye tana tunanin iska, ta tako ta dawo daki 9pmdaidai. Malami har yayi slp. Bata sauya komai jikin taba ta kwnta,shirun da tayi, bawai Al amin take tnkba , fandagori kawai take tink,can mind dinta ta koma,tana matukar son ganin Dan liti. Yayin da shima al amin yake zaune bisa bed yana tinkn yanayn sakinarsa take ayau,don hka ya roki Allah daya yaye mataabinda ke bata mata rai. Dukkansu sun raba darebasuyi slp b... Yau mafarkin mama ya sauya salo,domin a yau kiran da ya kwala mata yasa ta tsayacak,! Tana kallon sa, tafiya zakiyi ki barni??? Ta kada Kai.. Ya ware hnds dinsa yace, Kizo nan don Allah. 2acigaba da kallonsa bata motsa b, kizo mana nace,! Taruntumo da gudu ta rungume sa, ta fasa kuka, ya riqeta tamau! Yna fadin, ko ke fa? To kidaina cryng, donbanga dalilin yin sa ba... Ya dago fuskarta yana sharemata hawayen, ya isa haka, ki daina bata hawayen ki? Kuka take yi sosai, tana kwance rashe rashe bisagadon, ta jima tana kuka kafin ta yunkura ta tashizaune,taja jikinta,ta jingina da akanta kan gado tacigaba da tsiyayar hawaye ana sharewa. Bata sakekomawa barci ba har aka kira asalatu. Ta sauka tafada bayi tayo alwala ta bada faralo,ta zauna shiru bisa sallaya. Zuciyarta tana azalzala mata son ganinDan liti...... Muryar malami taji yana fadin, har kinkinyi sallah ne anti? Shine baki tashe ni ba? Tadanruntse ido, ta bude,yi hkri malami,na manta ne. Je kayo alwala,. Ya wuce bayi yayi alwala ya fito yayisallah. Yana idarwa, wanka yaje yayo yayi shirin skul. Bisa gadonsa ya koma ya kwnat.jim yayi shiru cankuma ya dago kai yace anti kifa tashe ni karki manta.Tace bazan manta ba,ya koma ya kwanta.ya bartazaune bisa sallaya. Anti Amina ce ta shigo,karfebakwai da rabi wai barci ne ya dauke ku? KaiMalami!... Ta bubbuga shi,yayin da mama tay firgigi ta bude ido, skul din fa? Ka kwanta kana ta slp?? Yasauko a firgice yace , nace anti ta tashe ni fa! [11/01 18:49] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 1***12 Tace, Ita ma aunty ai ta bingire, dube ta aza zaune take yinsa. Ta so kayi breakfast dadin kana jiranka. Ta juya inda Mama ke xaune tana famanxuba mika, Yayan ki zai fita ne, ki fito ku gaisa. Tace,Gani nan. Suka fice da Malami, ita kuwa mama bayita shiga ta wanko Fuska ta fito. Suna bisa tebur ta same su fuska ba walwala, ta ja kujera ta xauna, inakwana yaya? Yace kalau, ya lazu Doktan ki?Murmushin bai kai ciki ba tace, ai ni ban shi ba Yaya.Yace a Yau kuma? Zamuyi waya ai, zan gaya masaabinda kikace. Tayi shiru Aunty amina tace, me yasami idanuwanki? Kamar sun kumbura? Ai ba sa min ciwo, tace, to meyasa? Da alama dai sun kumbura.Ta murje idon. Yayanta na cewa, ke me zai dameki?Ita da take tare da lazy Dr. Suka fara dariya, ita kuwayake takeyi. Ta sa abincin, sai juya masa cokalitakeyi, ta kasa ci, da alama tana son tayi matamagana ne. Amma ta kasa, aunty amina ta kare mata kallo, tace wai menene? Ta dago ido ta dubeta, tadubi yayanta, jim kafin tace, Fandagori nake sonxuwa. Fandagori? Me zakayi? Yayan ta ya tambaya.Idanuwan ta suka yi rau- rau! Da kwalla tace, ina sonxuwa ne kawai. Ya xura mata ido yace, xo nan bebi.Ta taso a hankali ta zo gaban sa ta tsaya. Ya kamo hannnayenta biyu yace, me zaki yi a can? Bayan yaukwanan mu bakwai da dawowa? Tace Umma na keson gani. Ya dubi Aunty amina, yace kinji shagwabarbanza! Ke kadai ke da Umman nan ne wai? To ba zaiki ba ki ba, nan zaki zauna sai karshen wata. Ta karamurtuke fuska. Don Allah yaya kayi hkr ka bari in tafi. Ni wlh ko a motar haya xan iya tafiya, ba sai direbaya kaini ba. Yace, motar haya? Baki a tunaninki bebi,banso in sake jin wannan maganar, karshen wata inada hutu zamu tafi tare. Is dat clear? Ya fadi tare damatse yatsunta da karfi. Tayi tayi ta kwace amma takasa. Ya kara girgiza ya, ya kara fadin Is dat clear? Ta kara cunno baki ta kauda kai. Ya saki hannun yace je ki ci abinci, ta juya da gudu ta haye sama.Aunty amina ta kwala mata kira, Mama! Ya dagamata hannu, a kyaleta! Iya shege takeji kwana biyu,ko baki lura ba? Tace haka ne fa, ni ma ban ganemata ba kwana biyu. Ya dubi malami yace, lazy man ayi sauri mana. Yace na gama Dadi. Mu tafi kenan?Ya ce eh. Suka bar tebur. Madam ta kwaso masajakar sa da hularsa. Malami ya goya, ta sa jakar suka fito tayi musu rakiya xuwa mota. Sai da suka fita,ta dawo cikin gida. Kai tsaye wajen mama ta nufa,tana xaune bakin gado ta kumbura suntum! Idanuwan ta sun kada jajur! Ta kare mata kallo, sannan taxauna gefenta, wai Mama me yake damunki ne? Komunyi miki laifi ne? Ta kada kai. To me zai sa ki tashihankalinki haka? Wajen Umma nake son inje. Ai bahana ki akayi ba, tunda yace ki bari karshen wata kutafi, sai kiyi hakr xuwa tym din. Tayi shiru ba tace komi ba. Ta rungumo kafadarta, wannan abu na banimamaki, kamar yau kika fara xuwa garin nan? Dabakinki fa kika ce kin fasa kara kwanankin da kikacexakiki, balle ace matsa miki akayi. Tace sai da na zokuma naji bana son zaman. To kiyi hkr, tundaYayanki yace ba xaki motar haya ba. Shikenan, yauwa autan Umma. Ni bari in je inyi wanka, in dankwanta kafin rana tayi. Tace to, auntyn ta bar dakin takoma nata. Ta aiwatar da duk abinda take son yidaganan tabi lfyr hafo. Bata jima ba, ta sunkuci jakarhannu ta rataya ta yafa mayafi ta debo takalman tarike a hannu ta sadado ta sauko kasa. Shigar ta falon ke da wuya, wayar Al-amen ta shigo falon, gabanta yayanke ya fadi, ta tsaya cak! Tana zare idanuwan.Tsoron ta Allah, tsoronta kar karar wayar ta tashi antyamina. Saboda haka tayi azama ta nufi wajen wayar,ta daga kan taaje gefe, ba tare da tayi magana ba,balle ta san waye akan layi. Ta dan kara tsayawa, jim shiru bata jin wani motsi ba, tayi hamdala ga Allah. Taaje takalmanta ta xura tayi waje abinta. Babufargaban komai ta doshi gate har tana gaida masugadi. Suka amsa tare da fadin a dawo lfya. Taceameen. Tayi waje cikin sauri ta bar sashin unguwar tafito a sarari a inda ta samu shatan tashi ta kai ta tasha. Tayi muguwar sa'a fasinja daya akejira motarta tashi xuwa Minna. Inda daga can zata sami MotarFandagori. Sha biyun Rana Aunty amina ta farkabarcinta, ta sauko falon kasa, tin daga nan ta faraganin abinda bata sa ba ba, kayan abinci na aje bisatebur yadda ta barsu. Mama ta bata kwashe ta gyara wurin ba. Cikin ranta take fadin, lallai yau Mama tsiyatakeji. Haushi ya isheta ta nemi kujera tsakar falo taxauna ta shiga kwala mata kira. Shiru bata amsa ba.Mamaki ya isheta, t yunkura zata tashi idanunwantasuka kai bisa waya, Ah ji wani sabon iya shege. Sumama! Ta nufi kan wayar ta dauka ta mayar yadda take. Tana jan tsaki. Ta hawo saman ta fada dakinmama cikin zafinta. Ganin babu kowa a dakin yasatayi turus! Cikin sanyin murya take kiranta, mama! Kokina toilet ne? Shiru? Wai malam yaci shirwa. Tabude bayin vata ciki. Hankalinta ya tashi ta sauko dasauri tana kiran Mama! Har waje. Daya daga cikin masu gadin yake gaya mata ai ta jima ta da fita.Al'amarin ya daure mata kai. Ta dawo falo..... Tana mamakin mama. Karar waya yadawomata da hankalinta, ta tashi taje ta dauka, hello! Muryar aunty Rabi taji ta amsa. Hello aunty amina,Rabi ce, tace nagane ai ya yara? Lfya lau wlh. Waime ya smu wayar ku ne? Al- ameen ya kirani, wai tunsafe yake neman layin, amma yana engage. Tace, uhm.... Ke dai bari, ina nan ina ganin abin mamaki.Kamar yaya? Tace, Mama ce daxun da safen tacewaYayanta ita gida zata koma, yace ta bari karshenwata ya kaita. Nima na rarrasheta, har fa ta amince,wai kuma na tashi barci yanzun, bata ba dalilinta cikingidan nan. Sannan ina zaton ita ta cire mana kan waya ta aje gefe. Cikin al-ajabi tace, to saboda me? Oho! Kuma ba ayi mata komai ba? Wai zai yi mataRabi? Ko da ma anyi matan ai be kamata tayi hakanba ko? Tace gaskiya ne ka, ah to, ita da yayanta ne.Ni ba babu ruwan. Tace, amma ai mama bata dawannan halin, me yasa za tafar shi yanxun? Wlh bakiji ba duk Al-ameen ya damu, nace masa ya barizanyi tryn inji. Tace watakila don taga kowa na rawarjiki ne da ita, shi yasa take son ta lallace. Zata kuwayiwa kanta sakiyar da ba ruwa, idan ta bari yaron nanya kubce mata. Aunty Rabi ta numfasa tace, to yanxumenene abinyi? Tace, yayan nata zan kira Yanxun in gaya masa ta gudu, Allah

Chapter 7 of 28