Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ku taya mu addua mama kam ko ta so ko taki doke ta auri Alamin, tunda zabin ta ne na farko bamu muka cusa mata shi ba. Hasali ma bamu san lokacin da suka hadu ba. tsabat rashin kunya ce irin t yayan zamani da rashin sanin mutuncin mutane. saboda. haja hajia karki damu kuma dabarar da kikayi wa alamin tayi daidai sai dai akwai sauran rina akaba domin fadar kalmar ciwon ma ba zai bar shi yayi sukuni ba. Tace zaifi sauki akan a gaya masa gaskiar magana ni na dauki dawainiyar kwantar masa da hankali kullun ya kira waya. Tace to shikenan Allah yasa mu dace ta ce ina sakinar take mu gaisa Ta mike tana fadin Taso muje in kaiki kwance ma take bata iya tashi. Ah me ya faru? ina fatan ba dukanta kukayi ba, ta ce Baban Amira bai gaya maki bude mota tayi ta diro kasa ba? ido waje ta dafe kirji ta diro daga mota? tace ya wuce wai! zo muje ki ganta ta tashi dauke da mamakin tana fadin naga abinda ya ishe ni ni yasu, sakina da gaske take bata son Alamin. suka cusa kai dakin, baraka dake zaune bakin gado ta mike tana gaishe su. umma ta nuna wa mami wurin zama a bakin gadon tace zauyna hajia kinga idanuwan maras kunya ta juya kan mama taci gaba ga hajia nan tazo da kanta inkinga dama ki bude ido ta kudundune kai cikin pilli mami ta dube su tace ku bamu wuri hajia ita baraka suka bar dakin mami ta karasa matsowa tasa hannu ta birkito ta kuka taga tanayi tasa hannu biyu ta tallafo kuncin ta ta sanyaya murya tace sakina dan dubeni kinji? ta dago idanuwa jajur ta dube ta hawaye suka wuce bisa kuncinta. mami ta kara goge su . ta ce na san ba'a siyan so mama da yau nayi cinikin sa ko nawa ne na siya wa alamin, koda zai kasance zani daya zai rage min a fadin duniya. amma kash hakan ba zai taba yuwuwa ba, sai nayi imanin ko dan yaya ne kin san mahimamcin rike alqawari me yasa kika dauki alqawarin da ba zaki iya cikawa ba? me yasa kika yaudari shi kika bari tsananin son ki ya zauna a zuciyarsa? kina so ki kashe shi ne sakina? ki tausaya min ana gaya masa sakon nan zuciyar sa zata iya bugawa ya mutu mama. shi kenan na rasa shi kuma ban da wani alamin na sonki mama sai dai ayi zancen dan adam ssaboda haka ki gaya mani abubuwan da yake miki wadanda baki so har suka sanya ki tunanin fasa aurensa. wallahi nayi maki alqawarin zan masa fada tare da lallashi in kuma. gargade shi kinji? gaya man matsalarki da alamin. hawaye suka ci gaba da ambaliya bisa fuskar mama domin ko sunan alamin bata son ana ambatowa tsawon lokaci bata tanka ba sai kwarara ruwan idonta kamar zai kare mami ta sake fadin da alama alamin dai bai maki komai ba sakina tsuntsun son sa ne kawai ya tashi daga kansa ya koma wa wani ko? ta kara aje ido kasa mami tai wawan ajiyar zuciya idanuwanta suka kawo kwalla baki man halacci ba sakina a iya tunani na mutuwa ce kawai zata raba ki da alamin shi yasa gaba dayan mu muka dora burin mu a kanki. bamu da wami buri face Allah ya nuna mana ranar da zki zama mata danmu sai gashi dare daya kin juya mana baya. A tunani ki kinyi daidai? baki gudun kar amana ta ci ki sakina? kiyi tinani cikin natsuwa duk wanda ya ha'inci wani Allah ba zai kyale shi ba. zan barki kiyi tunani kan magana ta. idan kin canza ra'ayi ki koma minna zuwa gobe Alamin yaji ki hankalinsa ya kwanta kinji? yace in gaishe ki kuma yace inyi maki addu'a. Ta taimaka mata ta kwanta a hankali idanuwanta rufe suke yayin da mami ta dafa kanta tayi mata addu'oi da alamin yace tayi sannan ta kirata ta bude ido. nizan koma sai najiki a minna karki bari shaidan ya rinjayeki ki bar mai tsananin sonki cikin kunan zuciya nakasa zaiyi kinji? ta lumshe idon a natse mami ta wuce ta bar dakin umma ta shiga tare da sallama ta nemi wuri ta zauna yayin da baraka ta fice. ta basu wuri ta saurareki? tace to! bata dai tanka ba sai kuka da zan fito. ma nayi mata addua' kallo na ta dinga yi. da alamun za'a dace tace kwarai da gaske bari in lallaba hajia zan shiga wajen gwaggo sannan mu wuce . to a gaishe ta da kyau Allah ya kiyaye hanya Suka wuce suna fadin"Amin"har kofar gida tayi mata rakiya,motarsu ta daga ita kuma ta dawo gida dakin mama a koma suka taru da baraka suka ci gaba da yi mata nasihohi tana kudundune bata tanka ba,balle su gane me take nufi,Awa guda bayan tafiya mami yaya. Abdul- kadeer ya iso gidan daidai lokacin kuwa Abba ya dawo gidan,yayan tare yake da dakarun sojoji guda uku,duk suka fito,suka toge suna sarawa abba,sannan suka gaishe shi tare da yayan suka rankayo yana ruwan masifa, maganar banza yarinyar nan take yi,mu makace ta kawo shi ko mu muka hadasu wannan ai iskanci ne yanzun nan zan wuce da ita shiya na dauko kuratan nan su yi min gadinta a mota na ga ta inda zata fito,Nonsense kawai" Abba yace kayi daidai domin ni mama ta ginsheni ko ganinta bana sonyi cikin gidan nan,saboda "BAKIN CIKI",abu kamar al'mara yana so ya zama gaske yarinya ta bamu kunya ta zubar mana da mutunci basu ma san sun shigo falon ba sai da umma tace maraba da babban yaya yace sannu umma bamuyi sallama ba ko?raina bace yake ina mama?tana daki ina fatan tafiya kazo yi da ita sosai kuwa umma akwai kurata uku nazo dasu wadanda zasu gyara mata zama muddin tayi yunkurin bata mana lokaci tace yayi kyau wallhi yanzu ma hajiyar al-amin ta bar gidan nan bakaga uwar kunyar da ta lullubeniba na rasa inda zansa kaina Abba yace tazo kikace"tana ma cikin garin nan bata wuce ba"Abba ya nemi waje ya zauna ya kama kai,shi kuwa yaya babba dakin ya nufa kina jina baza ki fito ba"umma tace da wace kafar zata fito bayan ta kusan kashe kanta,yace kadan ta gani amma yau sai kin bar garin nan ko za ki mutu!Useless girl!kina nufin ki zubar mana da mutunci ko,baki. Kai wannan matsayinba,I swear,kin ji na rantse"yasa hannu ya fisgo ta da karfin sa yana fadin"stand up my friend"ta tsandara kara mai garfin gaske saboda gaba gabobain ta suka amsa suka kaiwa kwakwalwar ta zuwa falon dole gabobin suka loma aiki ashe dama wuri suka samu. Ya dankwafar da ita bisa kujera tace wayyo na shiga uku yace"No lokacin bai zoba tukuna sai kin ci gaba da bijire wasu umma I'am telling you! yau abuja zamu wuce ki zauna can, sai lazy doktan ki ya dawo ai ke ki ka zabe shi tun farko so now you have no reason ki ce kin fasa bayan kun kusa aure ya dubi umma yaci gaba karki ji tausayinta ta umma ki fidda ta a ranki har sai tayi biyayya a gareku, Ta kada kai tace tuni mama ta fice min a rai balle tausayinta ko alama babashi cikin raina ka tafi da ita duk abinda ya dace kuyi mata don ta gane kuskuranta yace wannan dole ne Abba bari mu wuce umma ta fara magana bari in hado mata kaya yayin da abba da babban yaya kamar zasu cinye mama a falo kuka take tamkar za a zare mata rayuwa umma ta fito da jakar kayan ta wurga mata gyale bisa jiki,yaya soja ya mike tashi karki bata min lokaci taki mikewa yasa hannu ya maketa sannan ya cafko. ta yana fadin zan iya karya ki u know dat! gara ki shiga hankalinki bai sake taba har kofar gida ita kuwa umma cikin sasa ta shiga ta gayo masu za a wuce da mama don haka suka yo waje ganin yadda za a yi saboda suji dadin karaars wa. A gaban su ya cilla wa kuratan daya zo da su ya ce kusa min ita a mota! kan kace kwabo mama na cikin mota, suka sanya ta tsakiya yayanta na gaba sanda ya jefa jakarta a but yaya ya juya da sauri ya zauna matsayin driver babu bata lokaci ya murza mukulli mota ta tashi ya bar wajen, idanuwan baraka suka cika da kwalla nan da nan ta fasa kuka ta koma cikin gida da gudu. sauran matan na ta fadin Allah ya kiyaye hanya ubangiji yasa a dace. umma ta juya ta shiga gida su suka biyo bayanta . ganin hankalin umma yayi mummunan tashi yasa hajia gaje ta janye hajia hajo cikin gida ta mika hannu suka tafa sannan ta tallafe haba ido waje tace Ashe abin har ya girman haka? wanan sojoji kamar an zo kama gagararren barawo? ta ce ai kamar hakan ne tunda ta gagari iyayenta. zamuga ikon Allah yarinya na neman tayi wa iyayenta bakin cikin daula, sun ga samu zasu ga rashi ai kinga haj halima kamar ranta zai fita sai kace dole suka sake tafawa haj hajo tace Hakki ne nake gaya miki kadan ma suka gani badai danliti ta jajibo masu ba? Allah dai ya kiyaye lalacewa! ta tabe baki Nayaushe kuma? wai ance wa kuturu Allah ya laance ka! shagonsa fa take zuwa tsinancewa ai ba sai an tambaya ba! hajia hajo tace Allah shi kyauta haj gaje ta amsa na gaba domin dai wannan ya riga ya faru anyi abin kunya maga yadda za ayi! sun jima suna yada labaran banza da karairayi kai duniya ina zaki da mu? rayuwa kenan uban dawaki da umma suna kallon ikon Allah suna fama da BAKIN CIKI sai fatan Allah ya musanya masu alkhairi Mama kuwa tun isowarsu Abuja take kudundune cikin daki duk hargagin yaya soja baisa ta dauki lomar abinci tasa wa bakinta ba,al'amari ya daure wa anti amina kai ta zauna ta siga yayyafa mata nasihohi da rarrashi ko Allah yasa ta gane amma ina Alla bai nufa ba tukuna shi kuwa soja babu abinda ya dame shi cewa yayi zai fi kyau da zata bari yunwa ta kasheta a yau hakan kuma shi zai tabbatar masa ta cika mai kunnen kashi,yasa kai ya bar gidan amma kuratan sojojinsa na nan tsare da gidan bayan masu gadi mutun biyu ke nan yanzu sun zama su biyar,kafin yamma mama taci kukan daya fidda ta daga hayyacinta bama ta jin tarin yunwar da ke cikin ta saboda tsananin tashin hankalin da take ciki domin ita kanta ta san ta shigo kurkuku zai yi wuya ta kara ganin dan liti sai dai tunanin ta bai yanke ba duk tsananin da zata shiga baza ta taba auren wani ba dan liti ba. [12/01 17:26] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 2***5(TRUE LIFE STORY) Saboda haka taci gaba da zama cikin kunci da yunwa har bayan sallar isha'I yayanta ya shigo gida kamar shi alamin ke kira wayar sa ta hau bugawa falon kai tsaye kan wayar ya nufa ya dauka yayain da malami ya sheko da gudu don yi masa oyoyo.anti Amina ta biyo bayansa daga jin muryar al'ameen kasa yana cikin farin ciki da doki cike da zuciyarsa ina yini yaya,yace lazy dokta ya karatu?"Yana yar dariya ya amsa Alhamdulillahi ai na kira can minna don in tambayi jikin mutunniyar sai aka ce min ta sami sauki harma ka taho da ita, yace haka ne amma kasan yana yin rashin lafiyar sai a hankali cikin dan kankanin lokaci sai ta birkice bari in turo maka ita,koda kaji sauyi daga gare ta kar ka damu haka yanayinta ya sauya,jikin sa yayi mugun sanyi duk a lokaci guda gabansa ya ci gaba da faduwa murya dishe yace to yaya Allah dai ya bata lfy,ya amsa da amin ya aje kan wayar gefe ya amsa gaisuwar iyalinsa sannan ya haye sama ya fada dakin mama yana shiga ta kara kudundinewa cikin bargo yasa hannu ya kwashe bargon ya watsar gefr yace tashi zaune sai ga antin ta shigo ta matsa bisa shimfidar ta birkito ta tana fadin yi mata a hankali ke mama tashi kinji! Ta ciccibo ta ta tashi zaune kamar wacce ta shekara tana ciwo saboda tsabar fita hayyacin da tayi Tausayi ya lullube antyn a hankali tace kinaji na? Ga alamin cen ya kira waya don Allah ki fidda mu kunya ki tashi ki je ki saurare shi badon mu ba sai don girman Alkawarin da kika daukar masa kafin ya tafi tashi kije kudinsa na bin iska kinji? Tamkar antyn na magana da dutse don ko motsi batayi ba sai idanuwa ta ke ambaliyar ruwan hawaye . Haushi da takaici suka rufe yayanta ya daka mata tsawa mai tsanani sai ta zabura bazaki tashi ba? Alamarin ya kara kure su cikin mamaki sukaji wannan kalmar ta fito bakinta Nifa yaya ba zanyi magana da kowa ba Gaba daya suka ware ido baki sake sai dai shi soja baya tsayawa yana kallon raini don haka ya cira hannu ya tsnke ta da wawan marin da yayi sanadiyyar daukewar numfashinta karkaf,ta zube sumammiya ya nuna cikin zafi yace ni zakiyi wa rashin kunya ba na wasa da ke ni zan iya karya ki wallhy anti amina da tuni take kwasar salati tace ai maganar karyawa ta kare tafa suma yallabai yanzu me za a cewa Al'ameen din Yace ta mutu ni tayiwa rashin kunya bata isa ba wallahi!Mtsw"ya ja dogon tsaki ya bar dakin falon ya sauka ya dauki kan wayar ya kanga wa kunnensa hello al'ameen naji na ya amsa ina kinka yaya yace kayi hakuri da mama al'ameen ya katse shi me ya faru yaya ina take yace ta suma al'ameen kayi hakuri da ita domin mama ta riga ta sami matsala....". Ya sauke salati ya katse shi yaya bazan iya hakura da sakeena ba kowane irin hali ta shi ina son ta haka koda kuwa ciwon hauka ne ya kamata,Roko na gare ku shine ku taimake ni ku kai ta asibiti don Allah ko nawane zan kashe yaya please ku taimake ni ya goge hawayen dake zuba bisa kuncinsa yayin da jikin yaya soja yayi mugun la a sar cikin taushin murya yace kar ka damu al'ameen zamu kaita kar ka damu kaji sai da safe. Ko kamin ya gama amsawa ya kife kan wayar al'ameen sai da ya lalubi wuri don baya gani yadda ya kamata sauran abinda ke zuciyar sa kuwa biro na ba zai iya rubuce shi ba domin al'amarin gagarumi ne maras misaltuwa sai dai muce Allah ka kiyashemu sharrin masu sharri amin summa amin Anti amina keta faman neman ran mama shi kuwa yayanta bai sake komawa ta kanta ba dakin sa ya shige don yin abubuwan da yake ganin suna da muhimmanci a gare shi ita kuwa mama zafin. Mari da tsananin yunwa tare da tarin damuwa su suka taru suka jefa ta cikin doguwar suma awa daya da rabi ta kwashe babu motsin rai sannan ta dawo duniya,ta fasa kuka tana fadin wayyo Allah na zan mutu wayyo Allah! wayyo!" Nan da nan hawaye suka tsunkewa anti amina saboda tausayin da ya kamata murya na rawa ta tarairayo ta tana fadin mama ki tausaya wa kanki wannan mugun halin da kika jefa kanki kin kuwa ga yadda kamannin ki suka sauya wane irin masifar so ne wannan na bala'I. Akan da namiji kike wahalar da kanki a banza a wofi ki mutu ya nemi wata ya aura,wannan sakarci ne mama kiyi wa kanki fada tun dare bai miki ba sannan ki sani idan kika ci amanar al'ameen Allah ba zai kyale ki ba,ta fizge jikin ta ta sake faduwa bisa shimfida ta kara fasa kuka, malami ya budo kofa ya shigo cikin sanyin jiki ya karasa gun su yace mami uncle al'ameen ya bugo waya, kafin anti amina tace wani abu tuni mama tayi wuf ta tashi zaune cikin sababi take fadin ba za a zo ba kaje ka gaya masa bazan dauki wayar ba dole ne sai na aure shi nace. Ba zan aure shi ba duk ku taru ku kashe ni kowa ya huta ta sake komawa ta dase ciki anti amina da malami suka saki baki suna kallon ikon Allah. Jimawa kadan ta dube shi tace,Mu je falon." suka fice jiki babu kwari,musamman Malami da sababin ya bashi tsoro ba kadan ba.Anti Amina ta dauki wayar tayi sallama,suka gaisa kafin yace, Ya jikin sakeenar? Ta farfado kuwa? 'Ta farfado Al-Ameen, har ta samu barci. Ya sauke numfashi,'Allah ya kara mata lfy. To amin.yace Anti,don Allah ki taimaka ki tuna wa yaya tafiya asibitin.Ni ina ganin babu abinda zai gagari asibiti koda matsalar junnu din ne, akwai ta su irin gudumawar da zasu iya badawa. Please Anti a kai ta asibitin a gwada." Idanuwan ta suka kara tara kwalla,jin yadda muryar sa ke rawa,ta tabbata hawaye ne ke zuba bisa kuncin sa.Ta numfasa tace "karka damu Al-Ameen,duk wani iya kokari ana yinsa.inshaAllahu Allah zai dube mu ya yaye mata wannan lalura.ka kwantar da hankalinka kaji? Ya amsa,Hankalina ba zai kwanta ba Anti,har sai naji muryar sakeena da bakinta ta gaya min tabbacin samun saukin.Ban san halin da sakeena ke ciki ba Anti,kowa cewa yake tana samun sauki,amma ni ban ji alamun ba a jiki na.zuciya ta tana min sake-sake iri-iri akan sakeena kuma tana nuna min ita acikin mummunan hali.jin muryar ta ne kadai zata warware min rudun dana fada.....Anti Amina ta amshe,komai yayi zafi mgnin sa Allah Dokta.ka tsaya wa addu'a kawai ita ce kadai zata taimake mu.shi kenan Anti,ngd.Idan Allah ya kaimu gobe zan sake kira ko na dace jin muryar ta.Tace To Allah ya yasa a dace.ameen Sukayi sallama ta aje waya ta koma bisa kujera ta kama kai hannu biyu ta matse kwallan ta tace wannan masifa Allah ka yaye mana,muryar mai gidan taji yana fadin kema zai zauna kina bata lokacinki yau mu ma bazamu ci abinci ba ke nan Ta share fuska ta dube shi yallabai ba ka ki kalaman dokta bane su suka kara dafani wallahi ya ya zamuyi da yarinyar nan ne yace oho!ni kizo ki ban abinci ina jin yunwa ta mike ta nufi kicin shi kuma ya wuce ebur yana kiran malami ya sauko da gudu yana amsawa gani dadi kaima yau baza kaci abinci. Bane yace ai na ci dadi to koma daki kayi barci sai da safe,ya juya ya haye saman yayin da anti amina ta fito da jerin kayan abinci bisa tire ta jera bisa tebur sannan ta zuba masa taja kujera ita ma ta zauna yana ci tana maida masa kalaman al'ameen sai da ta kare ya kurbi ruwa ya dube ta, Yace ni kinga duk wannan shiriritar ina yi ne kawai saboda hajiyar sa ta roki a rufe masa amma ni ban ga dalilin yawo da hankali ba yanzu ina fa'idar yin shirun tunda hankalin sa da ake so ya kwanta bai kwanta ba?mama ko zata mutu shi zata aura to me ne ne abin jin tsoron gaya masa matsalar da ake ciki banda shiriritarku ta mata,ta ce ai ba haka bane yallabai kaga kuma shi kansa marafa ya goyi bayan hakan"shi ke nan sai ki yi ta rarrashinta kafin gobe idan ta amince yin maga da shi shi ke nan idan kuma taki kya nemi wata karyar ki shirya masa kinga sharo karya ya same mu ke nan sai abinda Allah yayi ina amfanin sa Ta numfasa tace al'amarin hakuri zamuyi tayi rokona gare ka don Allah ka daina dukanta wallahi taurin kai zai kara mata ido waje yake magana muddin tayi min rashin kunya zan tabbatar da na hukunta ta yadda ya kamata don ni ba sa'an ta bane,you know that so ba zan dauki iskanci ba kina iya hawa sama idan kin kare maganar,tace ran maza ya huce yallabai ba ina nufin wani abu bane yaci gaba da cin abincinsa bai tanka ba ta zura masa ido tana dan murmushi ta san halin yan kayan ta idan kayi magana kaji yayi shiru to kaima ka tsuke dan bakin ka ka kama kanka shi zai fi zama alkairi. Garin Allah ya waye,baya ga sallah babu abinda Mama ta aikata,ta yada kai bisa kafet tayi lamo kamar sumammiya.Gaba daya ta rame,fuskar ta ta tsuke duk ta bushe idanuwanta sun kode sun firfito waje, sbd tsabar kuka.Malami ya fito wanka ya tsugunna gabanta yace "ìna kwana Anti?Tayi banza dashi,ya zura mata ido,Baki da lafiya ne Anti? Tunda ku ka zo da Daddy baki min mgna ba. Ta ballo masa harara,sai na tsinka mka mari ka sake min magana! Ta ja tsaki,ta juya kan ta wani gefen.Haushi ya kama shi,ya tashi ya ci gaba da shirin sa. Wannan karon kam bai gane kan gadon Antinsa ba. Me ke faruwane? Karfe bakwai daidai Anti Amina ta shigo,tana shigowa Mama ta rintse ido. Anti Amina ta dauko bisa kanta,ta dan dafa ta na san ba barci kike yi ba,ki tashi don girman Allah ga Dokta can ya kira. Kamar yadda na gaya miki jiya so yake yaji muryar ki,hankalinsa ya kwanta ko da gaisuwar sa ki amsa,zai ji dadi Mama. [12/01 17:32] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 2***6(TRUE LIFE STORY) Ku da baku wurin in kun amsa.To Mama ta amsa. Haushi kamar ya kashe anti Amina.ta mike tsaye tace, kar ki tashi Mamaa,idan kin sake jin nayi mikí mgn akan Al-Ameen,duk abinda kika so kiyi min! Mts....... Ta ja tsaki ta wuce. Mama ta rakata da nata dogon tsakin anti amina ta waigo rike da kugu ta zubo mata ido,lallai mama,ni kike yiwa tsaki? Yayi miki kyau! Taja kofa ta fice.kan wayar ta duka rai bace. Tace, hello! Yace hello anti,ta tashi? Bata tashi ba dokta.(nace"dokto ka fiya nace dolene?) "ba matsala,ai barcin ma yana da amfani a gareta.zan sake kira,ngd antí. Cike da tausayinsa ta amsa,kar ka damu sai anjima. To suka aje waya. Ta haye sama shake da haushi,amma bata nuna wa yallabai ba,don ta san ita zai tsatstsage danya. Iyaka tace da shi bata tashi barci ba Wasa wasa mama fa har ta sake kai bayan la'asar batasa kwayar abinci a bakinta ba hankalin anti amina ya tashi kwarai da gaske mama kam bata cikin hayyacinta gaba daya ta galabaita yunwa na neman tayi mata illa koma in ce tayi matan,shiyasa tana jin waya na ta bugawa taki dagawa don tasab mai kiran kuma bata da abinda zata gaya masa a hakikanin gaskiya ma hankalinta yafi rinjaye akan mama dake ta zama da yunwa tun safiyar jiya Tayi fada tayi rarrashi duk a banza misalin karfe biyar ta hada tea ta shigo da shi dakin wai ko Allah ya bata sa'a ta dan kurba me zata gani mama ke ta madedewa tsakar daki wata irin farar kuffa na hauhawa bisa bakin ta,tasaki kofin tea ta tarairayo ta tana sallalami kinga irinta ko mama nayi nayi dake kice abinci kin ki kina so ki kashe kanki a banza a rude ta sake bazamowa falo ta dauki waya ta kira wayar ofishin yaya abdul kadeea ta shaida masa halin da mama ta shiga Amma yanzu za a fara wucewa da ita asibiti nan take ya bata izini yace zai same ta asibitin babu baa lokaci soja daya ya sakata mota anti amina na tare da ita a gidan baya tana shafa mata ruwa a fuska sojan na jan motar an bata gado ga ledar ruwa na aiki a jikinta, wucewa minti talatin yayan ya iso ya same su jugum jugum,suna kallon ta rai bace ya watsa hannaye aljihu yace dama haka take so ba kuma shi zai taimaketa ba muddin tana motsin rai al'ameen ne mijinta so idan ta farfado ki fara gaya mata kafin na dawo zan koma ofis muna da mitin,tace to adawo lafiya ya wuce cikin kuzarinsa kuratan sa na biye da shi har bakin mota suka koma sannan guda ya bude masa ya shiga direban yaja suka wuce,anti amina ta ci gaba da zama dauke da tagumi zuciyar ta na mata saka iri iri haka wayar al'ameen ke ci gaba da bugawa cikin gidan ba a dauka ba malami ya shigo gidan dawo war sa ke nan daga maka ranta,kicin ya wuce kai tsaye saboda yunwa ce ta koro shi ya debo abinci ya zauna ya fara ci waya ta sake daukar ruri ya mike da filet din a hannunsa yana kara lomar shinkafa da salad ya dauki waya baki cike da abinci ya ce hello hello malami al'ameen ne ba kowa ne a gidan yace eh nima yanzu na dawo school mai gadi ya gaya min sun tafi kai anti mama asibiti wai ta suma. Jikin al ameen Ya kara mutuwa ya ce gaskiya Uncle duk ta rame kamar ba ita ba bata magana sai kuka Tunda suka dawo da dadi ba ta ci komai ba ko ni bata. Yi min magana ba sai yau ta ce za ta mare ni idan na sake gaishe ta wane irin ciwo take yi uncle hawaye suka tsunke wa Al Ameen. Bai san lokacin da ya kife kan wayar ba malami yabi ta hannunsa da kallo. Bai gane komai ba dan haka shima ya aje ya dauki abincinsa ya cigaba da ci yayi sallar magariba dadinsa ya shigo yayi masa sannu da zuwa ya amsa ya haye sama ya cire kaki yasa kana nan kaya jaket da wando ya sauko ya shiga kicin ya hada kayan abinci cikin dan matsakaicin kwando ya kira malami yace kai mota ya jirashi can su tafi asibitin,yace dadi yauwa uncle al'ameen ya kira waya dazun me kagaya masa na gaya masa anti ta sume kunje kai ta asibit to ke ka kirani a mota ya dauki kwando yayi waje jim kadan dadinsa ya fito suka tafi har zuwa lokacin mama bata gane kowa yayan ta ya zauna nan zuwa goman dare sannan suka koma gida da malami Anti amina ta kwana tare da ita kiran asubahin farko ta dawo hayyacinta ido ta zurawa anti amina kafin ta fasa kuka anti amina ta matsa gare ta ta dafa ta saman goshinta tace me yasa kike wahalar da kanki bayan ki na sane da cewa aure tsakaninki da al'ameen babu fashi,ta goge hawaye wallahi wallahi anti bazan. Taba cin abinci ba har sai yaya ya maida ni inda ya dauko ni kinji kuma na rantse bazan kaffara ba,baki sake take kallonta tama rasa ta cewa mama ke ci gaba da fadin na gwammace na mutu da a raba ni da dan liti sabo da haka mu zuba nida yaya idan jan idonsa zai sa in daina son dan'liti anti amina tace gadkiya ne kuma yanzu kika tabbatar min kinyi nisa ka kya jin kira To abinda zan gaya miki shine ki guji bacin ran iyaye rayuwa ki ba zatayi kyau ba muddin kika bar mahaifanki da BAKIN CIKI sannan dole ki fuskanci kalubale tunda kika ci amanar dokta bazan rufe miki ba mama koda nan gaba in ta Allah ta kasance zaki tuna dani kice na gaya miki a asibitin nan wallahi yadda kika sanya al'ameen kuka da radadin zuciya kema sai dan liti

Chapter 11 of 28