Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wani abu. Motsin fitowar yayanta yasa tayi firgigi, ta wuce da sauri ta bude mota ta fada. Muryar anti rabi taji bisa kanta tana fadin, "to matar likita a sauka lfya, ace ina gaida umma da kyau da kyau". Tace, "zata ji". Ameera kuwa kuka take yi zata bi ta. Hnkaln mama ya kara tashi, tace, "yaya mu tafi dasu mana" yace, "islamiyya ce bana son suyi missing, kyale su kawai sai wani lokaci". Ya ja murfin mota ya rufe, yayi mata key. Al'ameen ne ya dauke ta, "yi hakuri kawata, anjima kadan muma zamu bi su". Bata yi shiru ba, amma ta rage sautin kukan. Suna kalln motar ta bar harabar gidan, ameera kuwa ta kara wage baki. Al'ameen ya jefata a kafadarsa ya rungune, kirjnsa shima sai bugawa yake. Shi kansa yana bukatar rarrashin, shi yasa yayi tsaye jiki ba kwari. Tsawn lokaci sannan ya dagota ya share mata hawaye. "Manta da anti, ba ma yi da ita, tnda ta tafi ta barmu. Yi shiru, yi shiru. To jeki wajen momi, sai na dawo ko?". Tace, "yaushe zaka dawo?" "duk lokacn da nazo garin nan zanzo insha Allahu". Ya ajeta gaban mominsu, yace, "anti zan wuce, sai wani lokaci". Tace, "to mun gode kwarai da gaske. A gaida mutan gidan". "zasu ji". Ya wuce yana dagawa yaran hannu. har suka iso fandogari mama bata cikin sukuni ranta bace yake kwarai. Ganin Ummanta yasa ta saki jikinta. Kowane sassa umma ta turata, tace taje ta gaishesu kuma ta gaya mata an sulhunta. Gab da sallar magrib uban dwk ya dawo daga Kd gaba 1 siyayyar skul yai mata bayan isha' suka taru a falo suna cin abnc. Umma ta baje masa kayan data sami a gidansu al-ameen yasa abarka,sann yace ta aje su tukunna. Umma tace a'a Alh naga akwai abubuwan ci wadanda zasu iya lalacewa, yace banason amsar kayayyakin nan amma bakomai ki bata wadanda kike ganin zasu iya lalacewa kibar sauran. Tayi murmushi Alh ho! Abdulkareem yace danAllah kubar mata kayanta tayi amfani dasu. Menene? Aiba fata akeyi ba kuma sani kanka ne Abba babu abnd zai gagara koda an sami akasi karka da mu Abba. Nasan surutai sunyi yawa akan mama cikin gidannan haka bazai hana ta amsar kyauta daga masoyinta ba. Yace Allah ya shige mana gaba suka amsa da amin. Yayan yaci gaba da fadin gsky yaron nan yana son mama kullum waya sau 2 sau 3 wkend kuwa idan yazo tun safe sai yamma. Umma tace ai ta kare kuma tunda ba a waya a makaranta Abba yace baki tausayinsu kenan? Tace ina ruwana? Suka fara dariya mama ta hada rai. Abba yace ni inaji kyaleta kinji yar Abba? Ta kara matsawa gunsa ta lafe. Yaya yai yar dariya yace abin harda shagwaba? Ido kamar an matse kwado ba inji Umma. Duk suka fashe da dariya ita kuwa kukan shagwaba takeyi. Washe gari da sassafe karfe 8am tare da yayanta suka iso gidansu baraka sbd shima yanason ya gaida innarsu. Ta kuwa ji dadin zuwansa ita da megidanta su kuwa kawayen suna can kebe lbr ya tsunke kamar kurna na zuba. Ita dai baraka wangame baki kawai tayi tana mamakin wann kasaitacciyar soyayya data kullu cikin kankanin lokaci. Tabbas ta shaida domin itama na tattalin kayan skul da mama ta kawo mata sun ishe ta tafiya skul. Jaka inna tasa albarka banda alhairin da AK yai mata da megidan. Kafin ya gama sallama dasu inna mama da baraka sun sulale sun tafi gidan goggo wato kakar alameen. Harda manya goro guda 10 suka satowa inna cikin wanda take siyarwa Goggo ta nuna nata murnar taga kishiya suka bata goro ta amsa ta jujjuyashi tace na toshiyar bakine wann? Lallai kinsa in bar miki mijin. To naki wayon kenan? Suna ta dariya suka fito ta rakosu har zaure tana sa musu albarka. Suna fitowa suka hangi yaya tsaye yana jira suka karasa da sauri, yi hakuri yaya. Ina kukaje masu yawon tsiya? Baraka tace mun danje wajen wata kawarmu ce. Yace I see.. Daga zaure inna ke fadin kaji karya ko? Ni nasan gidan goggo Hausi sukaje kakar alameen. Ya kama baki yace Allah ya shiryeku. Inna sai wani lokaci. Ya bude mota ya shiga inna na fadin Allah ya tsare agaida Rabi da yara. Mama da baraka suka rungume juna sannan ta shiga mota tana yiwa inna sallama yaja suka wuce. [11/01 13:02] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 1***8 Suna isowa gida, me mama zata gani? Motar al'ameen aje gefe guda. Gabnta ya yanke ya fadi, haka ma yayanta ke mamaki, "wannan ba motar al'ameen bace?" "ita ce yaya". "mama biyoki yayi?". Tayi shiru tana 'yar drya. Yana fakin yabe fadin, "kai wannan mutum yana damun kansa da yawa. Pls ki gaya masa ya rage sonkh, kaq ya zame masa illa". Ta sauke ido kasa tana murmushi, tana kuma murzar zobensa da ke yatsanta". Yace, "je ki mana, tnda ba zaki iya gaya masa ba". Tace, "yaya kenan". Ta fito yaynda yayan ke fadin, "nayi laifi ko?". Ta kada kai, "a'a wlh". Ba shi ckn motar, sbd haka ta tabbatar yana falo. Don haka ta wuce ckn gida. Ido waje tana magana, "umma sai naga motar al'ameen a waje?" tace, "nima haka abbankuya gaya min. Yana can falo tare da alhajin"". Ta nemi waje ta zauna har da tagumi. "au zama kuma zaki yi?" "ummi kince suna tare da abba, sai kuma imje?" tace, "to zauna. Amma kinsan dama ku yake jira ku dawo ya maida ki makrnta ko?". Tayi shiru. "saura kije ki shantake da surutu. Sannan ki gaya masa don Allah ya rage sonki, zai iya zame masa damuwa". Tuni take kallon umma ido waje, har ta wuce ta bata wuri. Ta zabga tagumi hannu biyu zugum! Tunaninta yaya zata yi ta dumfari al'ameen da wannan maganar? Tabbas ita kanta tasan al'ameen ya makance a sonta, da zai rage din da zata so hakan, don bata son duk wani abnda zai raunana mata shi. "Mama!" taji an kwala mata kira, ta dawo daga duniyar tunani firgigi, ta dubesu tsaye bisa kanta. Abba yace, "tunanin me kike yi?" tace, "ba komai abba". "to yana falo, kiyi sauri ki ganshi muce. Wai rokona yake in barshi ya kaiki, tnda duk hanyar daya ce. Nace masa a'a, ya barshi yaje gun aiknsa". Jiknta ya kara mutuwa, ta juya salalau-salalau. Yayanta na fadin, "ni dai nace ta gaya masa ya rage sonta. Dis is 2 much!". Abba yace, "duk wannan ma bai taso ba, amma a ganshi tare da ita a mota, ai zan shiga bakin duniya, kuma daga ckn gdn nan maganar zata fara. Ba ni a ckn wannan tsarin, ba wai kuma don ban yarda dashi bane. Je kayi wanka kayi shirn komawa". Ya wuce, shi kuma ya wuce sashn da ya kwana don yin wanka. Kwalla ta tsaya take sharewa a kofar falon, zallar tausayn al'ameen ne ya tilasta mata zubar su. So ba zai taba zama laifi ba, amma ya kamata al'ameen ya rika bi a hnkali, kar son da yake nuna mata ya zama laifi a wajn iyaynta. Sai da ta natsu sosai ckn ranta, sannan ta tura kofar ta shi shiga tare da sallama. Ya amsa yana kallnta, ta wuce ta zauna rai bace. Da sauri ya matso gunta ya tsuguna, "da inga irhn wannan fuskar taki gara na kwanta gadn asibiti sakeena. Gaya min waye ya taba min rayuwa ta?". Gaba daya tsigar jiknta sun tashi, ta dan numfasa tace, "kai da kanka ka tabani Dr." "ni? Me nayi?" "nasan kana sona Dr, ni kaina zan iya dafa Kur'ani in rantse. Wlh yadda kake ji haka nima nake ji. Bana son kana tsananta damuwa ckn son da kake min, domin ina jin tsorn kar wani abu ya illata min kai. Ganinka da nayi yau ya fadar min da gaba ba kadan ba. Wnda ya tabbatar min cewa zaiyi wuya jiya in kayi barcin kirki, sbd ba muyi waya ba. Me yasa? Kar ka mance makrnta zan koma, inda ba waya, sai fa in kazo visiting. Kana nufin ba zaka yi sukuni ba tsawn wannan lokacin? Rashn sukuni ba shi zai tara maka damuwa ba? Kai fa likita ne. Ka gaya min me yawan sa damuwa a rai yake haifarwa?" Yayi zuru yana kalln ynda idanuwnta suka kawo kwalla. Ta kara fadin, "tmbayarka nake, ka gaya min?". Ckn sanyin murya yace, "abubuwa masu dama da kan iya nakasa lafyar mutum. Amma kar kiga laifina sakeena, sonki nake yi". Kwalla suka malalo bisa kuncnta, lebe na rawa tace, "yayi yawa Dr.! Ka rage don Allah, bana son na rasa lfyrka". Tasa hannaynta da sauri ta rufe fuska, ta ja numfashi mai sarke da kuka mai tsuma rai. Wani kululu ya tokare masa wuya, kansa ya dau zafi, zcyrsa na zugi tare da tashn hnkali. Da kyar ya kalato miya a baknsa, ya iya fadin, "SA... SAKEENA!". Ta dago ido jajur! ta dubeshi. Ya mika mata hankicif, "don girman Allah ki gnge hawayn nan Sakeena. Kin kuwa san ciwon da kika dasa min yazu? Komai zai iya faruwa dani, muddin hawaynki ya ci gaba da zuba". Tasa hannu ta karba ta goge kwallan ta numfasa ta dubeshi a hnkl alkawarin da mukayi wa juna Allah zai tabbtr mana dashi nima ina sonka Dr. Ya koma dirshan ya zauna farin ciki ya mamaye zuciyarsa yace duk jawabin ki na yarda dasu sakeena. Kuma zan kiyaye shawarwarin da kika bani, tare da yin adduar Allah ya sanyaya min zuciyata duk lokacin da ciwon son ganinki ya kamani, rokona gareki shine ki taimakeni ki daina zubda hawayen ki ko alama banason ganinsu. Tace daga yau bazan sake ba, muddin ina ganin ka cikin nutsuwa. Yayi dan murmushi an gama my princess. Tace to yanzu ka tashi in rakaka ka kama hanya ka isa wajen aiki da wuri. Yace a'a kar muyi haka dake kije ki shirya ku fito kina gaba a motar Abba ni kuma ina take miki baya. Kash! Saidai babu jiniya dana makala kowa yaji ya kauce hanya gimbiyata zata koma skul. Ko ba haka ba? Ta dan shagwabe gsky ba haka akeyi ba, ba haka akeyi ba Dr! Aidai zaka sa Abba yayi min fada. Ya zura mata idanu yana dariya to shikenan bari inyi gaba tunda kin amince min..... Ka zama prince ba ta tari numfashinsa. Ya kara rausaya kai ah! Lallai ngd. Ya mike to muje ki rakani. Ta tashi suka jero na shiga na gaida goggo. Ah haba yaushe? Dazu da mukaje gidan Inna ta da yaya. Amma kin kyauta naji dadi nima idan nabar nan zan shiga in kai mata cfane karfa kiyi kishi. Tayi yar dariya aini bana kishi da goggo, sbd me? Ya tambayeta yana kallonta ido cikin ido ta bashi amsa sbd aronka na bata! Ya fashe da dariya zan kuwa gaya mata idan ta zauneki ba ruwana. Sukaci gaba da dariya har gaban mota ya bude ya shiga ta rufe nasa "take care" Allah ya tsare. Ameen kikace arona kika ba goggo ko? Ta tura masa hula gaban goshi ta ruga cikin gida yabita da kallo duk kasala ta rufeshi. Ya sauke wawan numfashi ya gyara zaman hular yana kada kai fuskarsa dauke da murmushin kauna. Yayiwa motar key yayi ribas zai wuce kamar walkiya ta bullo ta daga masa hannu da sauri ya dago nasa fara'arsa ta karu. Hanklinsa ya kwanta yaga abar sonsa. Bayan ya gama da goggo da kanta ta kaishi ya gaida inna daga nan ya tambayi baraka don ya sha jin lbrnta a bakin mama. Ta fito suka gaisa babu wanda baiyiwa hasafi ba musamman baraka da yake ganin zuwa wajenta shine silar haduwarsa da mama yarinyar da yakeji tamkar itace ransa. yana fitowa ya shige mota ya doshi babban titi yana kawo kai motar Uban dwk na hayewa kwalta. Abba bai sahida shi ba Amma ita mama tuni suka hada ido sukaiwa juna murmushin mmki nan da nan ya takewa motarsu baya wann sa'a da yawa take (dan anace saida ya bitan kuwa). Cikin kuzari yake tukinsa suna tafe yana biye dasu a hnkl har zariya daidai shataletalen kofar doka take cewa Abba ko kasan Al-ameen na binmu a baya? Ya dan dubeta kadan ya juya bansani ba ina yake? Tace gashi can bayanmu ai tun daga fandogari tare muke. Yace oho! Nidai ina ganin mota tana bina a baya- baya ban ganeshi ba. Kofar get din asibitin (A.B.U.T.H ZARIA) daura da kamfanin maizar nan sukayi fakin kowa ya fito. Ashe kai ke bina a baya? Ya dan sunkuyar da kai yace ai ina fitowa gidan kakata na ganku. Yace yayi kyau to bari mu wuce aikai ka iso gida ya amsa eh yana satar kalllon mama. To shikenan mama mu wuce . Ya koma cikin mota itama ta shige yayi azama ya rufe yana fadin a sauka lfy Abba. Ya amsa amin. Idanusa na kan mama sukaja suka tafi. Alameen ya kama aiki kamr yanda mma ta maida kai ga karatunta amma zukatan suna cike da tunanin junansu. 43 days cif da komawarsu kasancewar sun koma a tsakiyar mnth shiyasa ba ai musu visiting ba sai nxt mnth ending. Kai sun sha wuya musamman dr da yake ganin kamr 43yrs sukayi ya kosa sosai yazo domin lahadin ce yake rawar jikin zuwa yaganta. Isowarsa kenan da safe ogansu na sashin Doctors ya kirashi ya mika masa takarda tare da cewa zai representing dinsa a taron fida na arewa wanda za*ayi a bauchi. Nan take hnklinsa ya fita daga jikinsa a kasalance ya dawo office dinsa ya cilla paper din on table ya dora hannu aka kamar ya kurma ihu sai innalillahi kawai yake furtawa! Wayyo Allah na shiga 3! Tamkar ya mutu. Jiyayi anyi knocking table dinsa ya dago ido jajur! Ya dubi mutumin dake tsaye yaya dai? Yayi guntun tsaki yace dr lawan yaushe ka shigo? Yace jst nw menene? Yace noting kawai banson zuwa bauchin nan ne gsky ina da abinyi wkend dinnan kuma idan ta raya min zanki zuwa saidai mu kwashi yan kallo da prof! Tofah. Ya ware ido sosai yace kai lallai kana neman barin kujerarka! To don me? Yace ba damuwata bace..... Ya katseshi look Alameen ban taba jin haka a bakinka bana tabbata uzurinka me karfine amma karka bata 10 1 bata gyaru ba. Kayi hakuri kawai! Kai tsaye yace bazan iya ba! I want to see her! Raina namin ciwo sosai konaje seminar nan oga bazai sami bayanin da yake bukata ba. Ya bude baki yace mutumina kace U re in luff kawai! To menene prob din? Nxt wk basai kaje ba. Yace bazai yiwu ba boarding skul take sunday za'ai musu visiting day idan ya wuce sai nxt mnth, mundade bamuga juna ba. Cool dwn dr naga ka harzuko dayawa amma shawarata kawai kayi hakuri. Itama bazata so taji ka sami prob da aikinka sbd ita ba, I believe she wl understand ur excuse duk ranar daka gaya mata.n Yaysi shiru yana nazarinmaganganun hakika yace wani abu daya tuna irin nasihar da sakeena take masa akan ya daina matsantawa akansa akan soyayyarsu somin sun amince da juna. Ya numfasa yace na hakura dr lawal, sky da hnklina yayi mugun tashi ina bukatar ganita dr. Aikai kana da mata kasan sirrin abun. Yayi yar dariya ya buga kafadarsa mutumina ka tashi daga dr ka koma mr lover-lover tunda dai ka amince bari na koma office. Yaushe zaka tafi? Idan mun tashi I.S.A. To a dawo lfy ya amsa ameen. Ya wuce yana me lover-lover! Yayi dan tsaki yace kp quite my frnd! Yayi dariya ya fice. Ranar lahadi cikin skul kowacce kagani tana cike da farin ciki sbd yau zasu ga mutanen gida wuri ya rincabe da baki kala kala sun zauna ana hira da ciye ciye kusan mama ce kadai ke kaiwa da komowa tana bilayin neman ta inda dr zai bullo. Wanda dalilin zuwansa ne yasa ba wanda yazo mata daga gida. Amma har la'asar ta bada baya ba lbrnsa. Tun tana fitowa har tay zamanta cikin hostel. Tunaninta meya hana shi zuwa? Babu amsar data fara zuwa ma ranta sai wata gagarumar matsala ce ta rashin lfy. Anya kuwa rashin lfy zata iya hanashi zuwa yau? Kai babu makawa yana kwance ranga ranga baisan hakin da yake ciki ba nan take hawaye suka tsnike mata harda na zuci kanta yayi dum! Har cikin idonta takejin ciwon har dare tana kudundune a gado duk iya rarrashin da frnds dinta sukayi a banza. Bata iya cin komi ba sai jiri ke dibarta idan ta tashi sallah ba bacci jikin yaci gaba da dumamewa kafin safiya ta kwana a skul clinic. Wasa wasa fa mama jiki yaki dadi. Kwananta 2 a asibitn makarnta, amma abu kullm kara gaba yake. Zazzabi, ga rashn cin abnci. Ko an matsa mata amayar dashi take yi, duk ta galabaita ta fita hayyacnta. Ganin haka yasa shugabar makrnta ta tura babban asibtin koyarwa dake zariya don ta sami kulawa sosai. Nan take aka bata gado, metiro din hostel ke jinyarta. A wannan ranar biyar na yamma Dr. Al'ameen da Dr. Lawal suka hadu a ma'ajiyar motoci, kowanne yayi fakin ya fito, "Ah! Mr. Lover!". Fuska ba walwala yace, "Don Allah ka daina, kar ka ynka min sabn suna". Ya matso yana masa drya. Suka tafa, "to ya aka yi? U look very weak, me ke faruwa ne?" "menene ma bai faru ba? In gaya maka tnda na dawo Bauci bani da lfya, kawai bankadar magunguna nake yi kar in kwnta warwas!". Ya nuna shi yana masa drya, "bebinka ko? Come on kar ka damu, zaka ganta da zarar wata ya kare. Zaka rnd ne?" "no, kawai na fito ne sbd bana son kwnciya a gida, tunani ke damuna" "ok, to zo ka raki ni female ward in duba wata yarnya da na kwntar dazu da safe. Na barta uncncios, ban sani ba ko ynzu ta fara gane mutane". Yace, "ba matsala, muje". Suka wuce yana fadin, "ai naji oga yana ta fada, wai report din nan kamar ba kai ka rubuta shi ba". Yace, "kyale dan rainin wayau, nima ina jinsa tn jiya ya fara conplain. "Dr. Lafai ka kuwa zauna wajn seminar nan? Naji kana kame-kame ne?". A raina nace, "ai sai kayi, wa yace kaki zuwa da kanka? Ai kadan ma ka gani ckn aikn magudi". Dr. Lawal ya kama drya, "bansn ka da haka ba mutumina, gskya wannan baby ana ji da ita" "sosai ma". Suka fada dakin ckn natsuwa. Kai tsaye wajn gadn sabuwai mai jinyarsa ya dosa, al'ameen na biye dashi. Tana kwnce rabin jiknta na rufe, gaba daya ta rame, fuskarta ta tsuke kwarai. Alameen bai gasgata idonsa ba shiyasa ya runtse ya sake budewa yayin da dr lawal ke tambayar mai jinyarta yaya dai mama? Ta kuwa tashi? Tace har yanzu dr amma da aka yi mata allurar dazu ta motsa. Dokta lawal bai kara fadin komi ba sbd mamakin yadda Alameen ke zare ido yana takawa a hnkl bakinsa na ambatar Sakeena! Jnkl tashe ya kalli dr lawal yaushe aka kawota? Yace dazu da safe kasanta ne? Sakeena ce. Yace yes sunanta kenan. To ai itace nake baka lbr. Baki sake yace kai danAllah? Ya dubi mama kamar yayi kuka meya faru da ita mama? Tace kawayenta dai sunce tun ranar lahadi wai ko babu wanda yazo wajenta visiting shine take ta kuka taki cin abnci har abin ya zame mata ciwo. Ina ganin ma principal ta aika aka gayawa iyayenta don suzo suga halin da take ciki. Tuni ya nemi kujera ya zauna yana fadin Innalillahi......! Kaga irnta ko dr lawal? Yace be a man karka manta acikin ward muke ido jajur yake dubansa dame-dame ka shirya mata? Yace karka damu duk abnd ya dace na riga na bata duba folder din kagani. Ya karba hannunsa na rawa ya karanta abnd ke rubuce dole tasa ya gamsu da abubuwan da dr lawal ya shirya mata don yasan abnd yake. Amma da son samu ne a bata maganin da zata warke yanzu yanzun nan shi yake so. Ya mika masa folder yace is this ur only plan? Yace zomuje daga waje... Hodijan! To nima zanyi daga wajen office sai kuma naje gida In Shaa Allah! Al'ameen yace, "no! I cnt go any where. Dr. Lawal je ka gama aiknka ka koma gida". Maman mkrnta bata gane ba, don haka ta tambaya, "haka dai kasn sakeena ne?" Dr. Lawal ya bata amsa, "shine wnda zata aura, kuma likitnmu ne a nan asibitn". Da mamaknta tace, "ba shakka! Lallai baiga ta tfya ba, sai yaga mata ta mike. To Allah ya taimake mu, ya kawo sauki da gaggawa". Suka amsa da amin. Ya kai hannunsa ya dafa saman goshnta, ya zuqa mata ido, ckn zcyrsa kuwa tambaya yake, "why? Why Sakeena?". Ya kada kai yayi dan tsaki ya sauke numfashi mai dauke da hucin zafi. Anan Dr. Lawal ya bar shi, haka maman makrnta ta bashi wuri, ta fito ta baza tabarma tayi kwnciyarta tana hutawa. Ya maida kallnsa bisa ledar ruwan da ake kara mata, kamar yasa hannu ya kara gudnsa ko zaisa sakeenarsa ta mike. Ya rike kai hannu 2-2, zufa yaci gaba da kwarara ckn jiknsa. Ya dago kai a hnkali ya ci gaba da kallnta, yana hadiye hawayn idanuwnsa. Ji yayi an dafa shi, muryar Dr. Lawal ke magana, "an kira sallah Dr." ya dube shi gwanin tausayi yace, "har ynzu fa bata farfado ba". Dr. Lawal yace, "come on al'ameen, ka barwa Allah komai mana. Taso muje muyi sallah mu dawo" ya mike yana ajiyar zcya, suka fice yana waignta. Cikn sujada ya dade yana addu'ar neman agaji wajn Allah. Tare da Dr. Lwl suka sake dawowa. Tun daga shigowarsu suka hngo maman mkrnta dafe da hannun da ake kara mata ruwa, kamar baknta motsi yake? Al'ameen ya kwaso sauri iya dire gabnta. Dr. Lwl na biye da shi, fadi yake, "matsa! Matsa mama." maman makrnta ta kauce da sauri. Ya zauna ya kamo hannun sakeena, yana kira. Ita kuwa sai zare ido take tana dube-dube. Bata gane inda take ba. "yaya dai?" Dr. Lwl ya tambaya. "she is back!" ya bashi amsa, jiknsa na rawa. Gaba daya suka dauke hnkaln masu jinyar dakin zuwa gare su. Kowa sai kallo yake yana Wa kansa tambayoyi. Alameen kuwa kira yake sakeena! Sakeena! Ta zura masa ido sannu a hnkli brain dinta ta ta dawo aiki idanuwanta suka fara washewa face din da takeson gani ta bayyana a idonta shiyasa ta rage kallon da take masa yace nine sakena! Kiyi magana naji hawaye suka tsinke mata shar! Shar! Ya zaro hankici ya shige share mata. No pls karkiyi kuka my Queen! Dr lawal ya yafito maman skul da hannu ya juya suka fice ita kuwa sakena kallonsa takeyi har yanzu bata gasganta abnd take gani ba. Nace ki daina kuka nine Alameen dinki. Kwallar basu daina sauka ba tace a ina nake? Ya hadiye hawayen da suka cika masa ido yace asibiti ne sakena me yasa zaki kwanta ciwo? Tace dama lfyrka kalau ka kasa cika min alkawari? Ba haka bane sakena ogana ne ya turani seminar bauchi ba yadda zanyi ne kinsan yanayin aikin kuma dole nayiwa shugabana biyayya. Ta runtse ido ta matse hawaye sannan ta bude tana kalllon sama tace Allah nagode maka daka sa tunani na ba gsky bane. Ta maido kallonta gareshi taci gaba, gaba 1 tunanina ya tsayane ga rashin lfy ce kadai zata iya hanaka zuwa guna na yarda na amince da hakan kuma zuciata tana kara tabbatr min kwance kake magashiyan. Bansan ciwon nan ya kamani ba dr amma nasan yawan tunanina da tsananin da zuciata ta shiga.jikinsa ya kara mutuwa tausayinta ya kara lullubeshi ki yafe min sakena ISA bazan sake ba ni kaina naji ajikina na tsananin rashinki, tace ba laifinka bane Allah na yarda daka kai farin ciki nakeyi da Allah ya nuna min kai cikin koshin lfy. Yadan numfasa yace ngd sakenata zaki sami sauki a hnkl dr lawal ya shirya miki magaunguna masu kyau da zasu taimaka ki samu sauki kuma ga Alameen dinki a kusa dake. [11/01 13:07] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 1***9 Ta dauke kai tana murmushi. Ya bita da kallo yana jin kamar ya tsaga zcyrsa ya saka ta. "sakeena!" yayi kirnta, ta juyo ta dube shi, "ya zaki juya baki ce min komai ba?" ta lumshe ido. "ko ganina ba zaisa ki warke ba?". Bata bude idon ba ta amsa, "sai dai in jikaka likita in sha". Yayi 'yar drya, "ko? To in shiga bokitin can kenan?" "Um" "zan shiga fa! Da gske nake yi. Kin wani rufe ido, ko labari zaki bani" "uhm...." ta sake fadi. Ya gyara zama yace, "to ina jinki, bani in sha". Tayi shiru, "ko barci kike ji?" ta bude ido ta kalleshi, idanuwn ta sun dan kada. Ya kura mata ido, "yaya dai?" ba komai" "a'a sakeena. Me ke miki ciwo?" "kar ka damu" Ya kara matsowa, "ba zaki gaya min ba? To wa kike so ki gaya wa wnda ya fi ni? Ki gaya min shi in kira miki shi" tace, "cikina ne kawai ba wani sosai bane. Dr. Nasan zai daina". Rai bace yace, "ya aka yi kika sani?" tace, "sbd ina ganinka Dr. Allah kar ka damu, ba sosai bane". Ya dafe goshi tare da sauke numfashi, "da akwai maganin da yafi wannan da na baki sakeena!". Ta yunkura tana kokarn tashi, "ina zaki?" "zan tashi zaune ne, don in nuna maka na ma warke" "no, ki kwnta na yarda kin warke". Ya sa hannu ya maida ta, ya kara ja mata mayafi, "kinsan abnda nake so da ke?" ta kada kai. "duk snda aka sami mishkila baki ganni ba, don Allah ki daina mummunan tunani a kaina. Kin ji?". Tace, "insha Allahu bazan sake ba". "kinga haka ake yi, idan ban ganki ba inyi hakuri, haka kema in baki ganni ba kiyi hakuri. Shikenan baza muyi ciwo ba ko?" "gskya ne. To bani labarin Bauchi. Ya garin yake?" "bansan komai ba game da garin, domin nima a yamutse na shige shi. Bansan ko'ina ba, daga dakin taso sai dakin barci na......." "gaskya ba haka ake yi ba, ba haka ake yi ba Dr.". Ya dan murmusa, "ya ake yi sakeena?" "ni dai ka bani labari" "ok labari? To saurara kiji". Ya lumshe eyes ya zazzage mata halin da ya shiga, kaf a bauchi. Ya bude idon a hnkali, suka kura wa juna eyes, "kinji labarin?" "naji, amma wane bayani ka rubuta a wannan shiriritar?" "me kuwa banda shiriritar. Kinga shi bai sami abnda yake so ba, nima ban samu ba" "magudi ko?" "ba shi bane. Allah haushi ya bani" "nima haka" "Allah ko?" "ah! To bambance min zukatan" yayi drya ya lakuce mata hanci, "kin kureni". Ta kauda kai tana murmushi. Hira fa ta tsinke, sun ma mance inda suke. Dr. Lwl ne ke tsaye hannaye ckn aljihu, sannan al'ameen ya dago ya dube shi. Yayi murmushi, "mr. Lover lover, kace ba haka ba, ynzu sbd Allah bayn likita, kai wanene?" yace, "al'ameen ofcourse! Ko my princess?" "ahaf! Ita tana ma da bakn magana ne? Ta dare min gadn patient, ashe duk karya ne lfyrta lau". Suna drya yace, "banda sharri" "tsakani da Allah haka mai ciwo yake? Well ku dai kuka sani. Ni zan wuce gida" "da wuri haka?" "da wuri? Lallai ne. To duba agognka ka gani". Ya dubi agogo cike da mamaki, "12 saura kwata?" "kana tmbaya ne? Baka yarda ba kenan". Yayi shiru yana kalln mama. Dr. Lwl ya kara matsawa yana duba ta yana fadin, "ina fatan dai kayi issha'i?" "ina fa! Shi yasa nake mamakn gudun lokacin". Yayi rubuce2 ckn file din, ya rufe "ina zaka san lokaci na gudu, kana kalln mai kyau. Nan zaka kwana?" "yes, amma bari muje nayi sallah. Sakeena inje inyi sallah ko?" tace, "maza hnzrta". Suka yi sallama da Dr. Lwl yana ta yi mata tsiya, sai da taja mayafi ta rufe fuska sbd kunyar maganganunsa. Sun fito dr lawal ke tambyrsa donAllah ina ka samo wann sarauniyar kyau haka? Yana murmushi yace itama yar niger state ce iyayenta yan fandogari, yace gsky yarinyar tayi ko kasan na kusayin barmbabama? Kamr yaya? Yace aini nan na dage ne iya karfina in samu ta warke saina gabatr da kaima. Yaja ya tsaya ya watso masa harara me kake nufi? Ya kamoshi yana dariya a'a dr maida wukar pls! Aini an wuce nan wajen tunda dara taci gida. Trust me wllh tuni na janye kudurina kasan ni banda rufi ya fizgoshi come on mu tafi mana ai ya wuce. Yace bakikkirin nake ganinka bazan iya jerawa dakai ba in banda iskanci ma last year kayi aure hange-hangen me kakeyi? Ya kyalkyale da dariya karkayi zato ba daina son matata nayi ba nikaina bansan abnd ya rikitani ba amma ina baka shawara ka gayawa sakena ta rika sa nikab kyaunta is too mcuh gsky! Ya murtuke duk kishi ya cikashi ya dunkule hannu ya nunashi "kayi sa'a kaine wllh dana farfasa maka baki!" Yace fasa mana nima nasan I deserve it but is nt my fault. Alameen yace u noe wat? Ka kyalemin ita ni zan dinga duba kayata. Kaga kuma inda baka isa ba kenan, ya zura masa ido yace I noe wat to do! Ya wuceshi da sauri yana kwafa. Dr lawal ya bishi da gudu yana fadin do ur best my frnd ina maka fatar Allah yasa sakeena matarka ce. Suka jeru suna kaoon juna ya amsa ameen ameen kuma ya isheka haka! Ya fashe da dariya suka tafa mr lover lover! Suna tafe yana tsokanarsa. A taikace Alameen nan ya kwana duk da mama ta roke shi akan ya koma gida abinsa amma ya kafe

Chapter 5 of 28