Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tana tsiyayar hawaye kusan 3mins sannnan ya yafito ta da hannu, yace xo nan! Da sauri ta isa gunsa, ta fada jikinsa ta kara fashe da kuka. A'a, kinga ni fa kukan ne bana so. Yanxu menene damuwarki? Ta goge hawaye, tace kullum in rinka samun kulawarka, hakan shi xai tabbatar min da kana sona kana son abinda ke cikina. Yayi dan murmushin nan nasa, ya kara janyo ta jikinsa, yace, kin samu bebi, karewa ma da kewarki na dawo. Kin ci abinci? Ta kada kai, saboda me? Bana iyawa ne, jikina gaba daya ya canza, sai amai kamar xai kasheni. Yace ayya sorry ko? Amma duk da haka ba za a rasa abinda kike sha-awa ba, gaya min in nemo shi, na kosa in kore kishirwata. Ta mako masa harara, ya kyalkyale da dariya, meye na harara ta? Ko ke ma xaki min BAKIN CIKI ne, irin na 'yan sa ido? Masu shiga tsakanin masoya suna son suga bayansu. Haushi su nake ji wlh. Tace ai ko ni din ma haushin su nake ji, ah haba? Wlh kaji na rantse. Ya cacume ta tana dariya tana fadin, ban da lfya Danliti, bai saurare ta balle ya tuna ya nemo mata abinda take son ci. Karfe 8 ya fito ya barta can kwance tana murkukusun ciwon ciki, ya wuce waje wani mai suyan nama, ya karbi danyan naman da yasa ya aje masa. Ya dawo ya bade shi da magani, ya maida cikin leda ya nade. Yana xaune bakin shgo bisa benci, yana tunanin tafiya yayi wanka ko ya samu yayi sallah. Mama ta fito tana yafa mayafinta, ya bita da kallo yana murmushin keta, ya cikin? Tace yayi sauki ni xan koma gida sai gobe. Haba haka da wuri? Yanxun fa 8 ta wuce? Kar a neme ni ne. Wa xai neme ki? Don Allah xaumna muyi hira, ba wanda xai nemeki, bayan sun san kina nan. Bata da xabi, don haka ta xauna kusa dashi, ya shiga bata labaran banxa. Jimawa kadan wani kare ya xo gilmawa nan take ya hau kiransa, tace me xakayi da kare kake kiransa. Kasan karen okundiri fada gareshi ko? Yace bai sami nama bane don ubansa okundiiri, ya kece da dariya, okundirin ne ubansa? Lallai ka samo shi. Yacee to da waye ubansa? Kinga bude ledar nan nama aciki dauko ki ba shi. Yana magana yana shafar kan karen. Tace, taf ya cafke min hannu? Kai dai ka bashi kai da ka siyo masa,don raka asara. Yace karki bani kunya mana, me xai sa ya cije ki, bayan yasan ke bebina ce, ko kare? Ai ka santa ko? Sweetheart dina ce kar ka cije min ita. Tuni kanta ya fasu, ya jawo leda ya bude ta dauko katon yanka ta mika masa tana fadin, abin har da yaji? Sangarta! Ya kwashe da dariya, yace ina ruwanki? Ke dai mika masa gudan. Ta dauko ta mika masa, ya cafke, Dan liti ya runtse ido yace yes! Ya xarce da dairya. Ta xuba masa ido tace, menene abin dariya har da wani cije labe? Yace ji nayi kamar ya hade da hannunki ya gartse. Takai masa bugu a kirji tace amma kai mugu ne! Yace sosai ma ashe baki sani ba yarinya, to tashi kije gida an gama hirar, kinga karen yayi tafiyarsa. Ka gaida okundiri kaji? Ta ci da kyakyata dariya. Yace, ah! Tashi karki sa yarona ya fito yana fito yana kyakyatawa kamar dolo. Ta shi kije gida sai safe. Don Allah kiyi hkr, so nake nayi wanka inyi sallah. Ta fido lah nima har ka tuna min banyi ko magriba ba. Ta juya da sauri tana cewa, sai da safe! Yace Allah ya kaimu. Ya bita da kallo, yace yarinya kin gama yawo kin shiga 3 kin lalace, ya daga murya ki fa sami abinci ki ci. Ta juyo ta amsa, kar ka damu xanci. Suka ja hankalin mutane, don haka yama didi ya biyo baya, masu tsinuwa nayi, masu addu'ae shiriya nayi. A tsakar gida ta iske su Abba na jiran dawowar ta, shi da su Alh. Basiru. Tana shigowa tasha jinin jikinta, ta shiga bin bango, tana so ta shige falo. Alh. Basiru ya daka mata tsawa, ke dawo nan! Simi simi ta matso gun su ta durkusa guiwa 2, batayi aune ba, taji saukar wani wawan mari. Gaba daya ya ratsa kanta, ya gigita ta, ta dunkule ta fasa kuka. A cikin ba tace ga wanda ya xabga mata wannan marin mai tsanannin xafi ba. Sai dai taji muryar Abba na fadin wannan shine gargadi na karshe da xanyi miki, shi ya sa na tara kowa su xama shaida! Idan har ba xaki bi umarni na, ki xauna a gida ba, to wlh sai dai ki xaba, ko mu ko Danliti! BAKIN CIKIn nan ya ishe mu mama. Gara in sallama ki, in tabbatar da kinfi karfina xaman kanki kikeyi. Saboda haka daga yau kika kara sa kafarki kika fita kikaje gun yaron nan, to kar ki dawo, ki yi zaman ki can wajensa ku sha shagalinku yadda kuke so. Duniya ce Mama, mai dauke da axuxuwa babu adadi! Ina fatan kinji kuma kowa ya shaida! Alh. Basir ya karbe karuwa kike so ki xama ko? To Allah ya baki sa'a, mu dai ba xa mu hana shi ba, duk ranar da koreki. Alh. Adamu yace dama saboda me xamu hana shi? Cikin shege ne fah ajikinki, amma bai sa kinyi nadama ba, to me xai sanya ki kuwa? Karkiji da wai, mun tsame hannun a kanki, haka xuri'ar gidan nan kaf! Kar ki ce kin san daya daga cikinsu, duk ranar da wuya ta koro ki! Ta shi ki bace mana da gani shashasha sakarya. Ta mike da gudu ta fada dakinta, ta dasa kukanta, a fusace abba ya bar wajen kowa ya kama gabanmsa, suka cigaba da yada xancan a sasan su. Daren nan su ma Umma basuyi barci ba, musamman Umma da tabbatar wa kanta ciwon xuciya ya kamata. Da safe ta atashi xuru-xuru baki daya idanuwanta sun xurma, shi kansa Abba ya rame ta maxa kawai yakeyi yana wa Umma fada kar ta salwantar da rayuwarta akan Mama. Ita Mama ba wannan ta aje ranta ba, kawau burinta kasance tare da Danliti, don haka take ganin kowa ya tsangwame ta saboda kiyayya. Kafin safiya ma ta mance duk kalaman su Abba da kawunninta. Allah Allah takyi ta sami saukin laulayin safe dake damunta ta lababa taje ta gano Danlitin ta. Xuwa 12noon ta iya shiga kicin, ta dan tsiyayi ruwan lipton, ta dawo ta shanye. Xufa ta keto mata, danji dadi ajikinta, kana ta shiga bayi tayi wanka da sabulun wanki maras kamshi. Ta kimtsa, tsaf, duk da tayi haske sosai, ta kuma rame kwarai, kana iya gane kyanta na asali mai daukar hankali. Ta koma ta kwanta yana kllon agogo 1:00 ta tashi tayo alwala tayi sallah, ta dauko gyalemnta ta xura takalma ta leko falo bataji motsin kowa ba, ta kwahi sauri ta fice abinta. Yara suna ce mata sai kin dawo aunty Mama! Jin haka yasa Umma yanke sallah, ta fito da sauri ta tambayi yaran ina maman? Sukace yanxun ta fita. Tabi xauran, yaran suka biyota ta tura su tace, ku kira min ita. Yara suka fice da gudu suna kwala mata kira, Aunty Mama, ki zo Umma na kira! Haka suke ta gudu suna fadi har suka isketa, ta dube su tace, sai na ci ubanku in kuna kwala min kira haka! Ni sa'ar kuce don Ubanku? Ku tafi ku ban wuri kafin in fallawa yaro mari! Mts..... Taja tsaki, ta wuce abinta, yara suka dawo a guje suka iske Umma a xaure sukace, wai sai ta ci ubanmu idan muka sake kiranta! Ta dafe kirji tace, ta kyauta, kuje wasan ku. Ta dawo cikin gida a salube tare da mamakin taurin kai irin na Mama, me take nufi kenan? Ta xauna a falo tana juyayi. Da kyar ta sake mikewa ta shiga dakin Abba, ta tashe shi barcin ramakon da yakeyi. Ya farka yana kallonta...... Yace, azahar tayi ko? Tace tayi alhaji. Ya yankura ya tashi yace menene na ganki a salube? Tace tasake fita, wa? Mama mana. Cike da mamaki yace ta fita? Yanxun nan kuwa, kamar fako na takeyi, har yaran nasa su kirata, ta dinga kunduma musu xagi, taki dawowa. Ita Maman ta zage su? Tayi murmushin takaici, tace kana mamaki ne? Bai kamata kayi ba alhji. Ta kuwa tafi kenan, kinsa Allah ba zata dawo ckin gidan nan ba. Kiyi hkr, duk abinda ke ranki na so da kaunar Mama, ki cire ki dangana da ita, nima na hkr da ita. Umma ta fasa kuka, ta tashi da asauri ta bar dakin. Hankalin Abba ya kara tashi, ya taso ya biyota dakinta, tana xaune bakin gado kukan kawai takeyi. Ya tsaya kanta, yace saboda Allah ya kike so nayi Halima? Ta cira kai murya na rawa. Tace har ga Allah ba korar Mama ke sanya ni kuka ba, tausayin rayuwarta ke bani, yadda ta ka sa gane cewar mu ba tsangwamarta mukeyi ba, saboda tana son Danliti. Yanxun shikenan ba xata gane cewar alabarkar mu itace kwanciyar hankalinta ba, duk tsananin son da Danliti ke mata, shikenan ta xabi cigaba da xaman shashanci akan ta nutsu, dn tym kankani a daura masu aure? Wannan rayuawar tana cike da tausayi da ban Mamaki, kamar Ya asirce Mama? Ta kada kai ta ciga, ba haka Mamar mu take ba alhji, ta sauya saboda soyayya, kenan ta fi son shi a kanmu? Ina xan samo amsoshin nan Alhji? Ina xan..... Ya rufe bakin da sauri, ya ace ya isa haka! Kar ki jefa kanki damuwar da xata tada miki ciwo, ki kauda kanki ki akan komai, sannan ki nisanta xuciyarki ga irin wadannan tambayoyin da kike wa kanki. Xaki xautu saboda yarinyar da bata damu da lfyarki ba, xamani ne Allah ya kawo mu da yara ke rufe idanuwan su akan abinda suke so. Suyi ta fada da iyeyensu har xuciyoyin iyayen su fara xargin asirce su akayi. Xan ji dadi da farin ciki idan xa'a ce, duk wannan abubuwan da suke faruwa, ki dauke shi amatsayin mafarki mai wucewa, tamkar baki taba haihuwar wata mai suna sakeena ba. Ta dube shi xai yuwu ko? Mai hana? Idan har zaki dage da adduoi, ubangiji ba xai barki haka ba, ta goge hawayenta ta sauke gwauran numfashi tace, xan yi iya kokarina Alhji. Ya jinjina kai. Yace haka nafiso sadiya, kin san ina jin dadin xama dake, kuma tun ina saurayi ban taba son wat 'ya mace ba sai ke. Ban fatan abinda xai salwantar min da rayuwarki, ya kasance wata kaddara tasa kin fara barina cikin duniyar nan. Kullum nayi sallah, sai na roki Allah ya fara daukar raina saboda ba xan iya ganin gawarki ba halima. Idanuwanta suka kara tara hawaye. Tace ka daina fadar maganar nan Alhji..... Ya katse ta, ni ma ba ason raina na fadi ba, domin sirri nane wanda nake xaton shi kdai ne ban taba gaya miki ba, sai yau, dole ce ta sanyani, don ina son ki sami nutsuwa sadiya. Ta matse ido kwallatana suka kwararo ya mika hannu ya goge mata yace, sha kurkuminki Maman abdul 3, gwarazan samarin nan masu takama da baiwar Allah. Ta numfasa tace, Allah yayi masu albarka baki dayansu. Kina nufin har da sakeena ko? Ta amsa da kai, kafin tace, ai mu na mata fatan shiriya ko? Yace haka ne, toh Allah ya shiryta. Amin ta amsa. Haka yayi ta rarrashinta, ta samu nutsuwa, sannan sukayi sallah suma mika kukan su ga Allah. Na san kilan kuyi musu ko mamaki idan nagaya muku Mama bata dawo gida ba, sai bayan sallar magriba. Abu na farko da ta fara cin karo da shi a kofar sasansu dake kulle, shine akwatin kayanta. Taja cak! Ta tsya ta xura masa ido tsawon tym, kana ta matsa ta tura kofar taji ga,! A kulle. Ta tabe baki tare da jan tsaki, ta figi akwatin ta juya tana fadin a ranta, sai aga na kwana a titi. Kai tsaye Danliti ta dosa, yana xaune kofar shagonsa, inda ta basa. Yana hangota da akwati, ya mike ya shige daga ciki yana gayawa Ayuba ga mutuniyar can tafe da akwati, ko maganarta tace ta tabbata? Ayuba ya murtuke fuska yace ni xaka tambaya? Au haushi kaji? Amma dai kana ji na gaya mata kar ta kuskura ta bari su koreta, don bani da wurin ajeta, ko ban gaya mata ba? Yace oho! Wai kai wani irin banxa ne? Yace Ni banxa bane, ai rainin wayau yasa ka gaya mata hakan. Wa ke jan ragamar rayuawarta, in ba kai ba? Ai sanin bata da xabi shi yasa ka raina mata hankali. To ya isa malam, sai gata tsaye gaban kanta, tana kokarin dagawa, duk suka xubo mata ido, ta karasa shigowa, ido waje ya dubi shirgegen akwatin, ya ce ya dai? Bata saurare shi ba, kofar dakin ta tasarmawa xata shige. Yayi azama ya shawo gabanta, magana fa nake yi, kona kokarin shigewa kamar gidanku? Ta xubo masa ido a marairaice tace, me na gaya maka? Ni kuma me na gaya miki? To yaya xanyi? Ina komawa na iske akwatina akofar gida sun kulle gidansu. Ya gayara tsayuwa, da yake kuma ke sakarya ce sai kaka kamo hanya kika taho baki tsaya kika nemi sulhu ba! Yanxun menene nufinki? Anan xaki xauna? Cikin shago? Lallai kin cika dakikiya, Jaka! Kuka sosai ya kwace mata, ta tsugunna ta rungumi kafafwansa, murya na rawa tana fadin, karkayi min Haka Danliti! Saboda kai suka koreni, ina kake so naje, idan ba nan ba? [12/01 21:58] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 2***15 Ayuba ya daga kanta, ya fice hankalinsa tashe, shi kuwa ko gezau beji ba ajikinsa, a dage yake kallonta, tsawan tym sannan ya fizge kafarsa ya kama hanya xai fita, da sauri ta mike ta cukuikuyo rigarsa, fadi take, kayi hrk don girman Allah. Wasu samari 2 suka iso wajen siyen taba sigari, ai sai suka buge da shari'a, kaya-kaya hayaniya har waje Danliti na daga murya shi ba xai aje ta cikin shagonwa ba, ta koma ta nemi sulhu da iayeynta. Kan ka ce kwabo jama'a sun cika makil a gun. Kai Mama ta sha zagi da la'anta, Allah shi kara kwando- kwando. Kalilan ke cewa Allah ya shiryeta, Dan liti ya gacciye banci kofar shagoin ya xauna yace yaga uban da ya tsaya mata agarin nan, wnada xai sashi ya ajeta. Baiwar Allah kuwa na tsugene gaban akwatinta, tana ruasar kuka har karfe 10pm. 'yan ganin kwakwaf suka gaji suka koma gidajen su dauke da labari mai ban al'ajabi. Wasu suna ganin bai kamata Uban dawaki ya koreta ba a matsayin sa na Uba, kuma babban mutum mai sarauta, wasu kuwa suna ganin hakan shine daidai, imna xai sa BAKIN CIKI? Idan bai sallame ta ba, tunda ta tara masa, ya cika masa xuciya, tana neman fashewa ta hallakashi? Ai gara da ya sallamata duniya ta koya mata hankali. Ga darasi na farko nan ta fara gani, duk iskancin Danlitim yace baxai aje taba. Alhalin saboda shi aka koreta. Wannnan ya nuna a fili ita ta nace masa kamar sauran 'yan mata marasa xuciya. Mutane na mamaki abinda Danliti yake da shi wanda yake tsonewa 'yan Mata ido. Su mutu cikin soyayyar sa. In bata ga kyau me yake da shi? Shi babu hali babu kwakkwaran asali. Amma duk wacce ta fada tarkonsa sai gagari iyayenta. Ko don kudi da ya ke kashe mus ne? Shiya sa suka dauki laifi kacokan suka dorawa 'yan Matan masu biye masa don kwadayi da kyalekyalen jikinsa. Wayyi, kai bai san dawan garin ba, dai bai yi tunanin kutsa kansa ciki ba. Tun ciki dare surutai kala-kala suka fara baza gari. Shi kuwa gogan da ya ga kowa ya watse sai ya matso ya xunguri Mama da kafa, ta dago kai da sauri ta dube shi, matso mana nan kiji, ta matsa gareshi, tana hawaye. Ya dubeta da kyau yace, ke banxa ce wlh, shi ya sa kika bani haushi. Nace ba xaki xauna anan ba. In banda hauka irin naki, ya xa'ayi ki xauna tare da mu cikin shago? To ina sane da abinda nakeyi, kin gane? Saboda haka ki koma ki nemi wani wurin ki xauna, ki bani nan da sati xan san abinyi. Murya dushe tace, ni bansan inda xani ba, a'a ko gidan 'yanwanku ba xaki je ba? Ko baku da su ne? Sai dai inje gidan su Baraka, yace ko gidan su Mubarak xaki, sai kinm dawo matsalar kice. Amma ba xaki kwana shagon nan ba. Yauwa, tashi ki sungumi akwatinki, ki wace kar su kulle gidansu. Tace to nagode, sai da safe, Allah ya kaimu 'ya bebine. Muyi fada mu shirya ko? Kar ki damu xan ganki goben. Tayi murmushi, dadi ya rufeta, ta mike tana kara masa godiya, taja akwatinta ta nufi gidansu Baraka. Ya mike janye da benci yana kyalkyala dariya, ya shige shago. Kai mugu dan gidan buzu mai shayi! Yayi wa kansa kirari ya shige daki. Ayuba na kallonsa yana kada kai. Gidan su Bara akulle yake, saboda sha dayan dare tayi ma. Ta shiga bugawa har aka xo aka bude mahaifin Baraka ke tsaye cikin xauran, ya dubeta da kyau yace, Mama ce? Daga ina haka? Ta fara kuka yace shigo shigo ciki! Ta wuce da uban akwati ya maida kofa ya rufe. Tana gaba yana biye da ita yana fadin, subhanalillahi! Dakin Inna saude suka shiga tana tsaye tsakar daki, lfya? Ta xube sharaf! Cikin kuka tace, abba ne ya koreni..... Ina saude ta nemi waje ta xauna, yayin da malam kasim ke fadin, me ya sa Uban dawaki xaiyi hak? Inna saude tace BAKIN CIKIN ta ne ya ishesu. Ace kamar Mama ta gagari kowa duk abinda ya sameta da abinda ake gaya mata ba su isheta nadama ba, idan ba su koreta ba me kike so suyi miki? Ba shashanci kike sha'awar yi ba? To sun baki hanya, meye kuma na kuka? Mal. Kasim yace hakan ba hujja bace, duk abinda xatayi, gara tana gabansu suna tsawata mata, yau da gobe ana hada mata da addu'a, sai Allah ya taimaketa ta gane illar abinda take aikatawa. Saboda haka ta xauna, gobe Allah ya kaimu lfya, xanje in ganshi. Ke kuma je ki kwanta kiyi tunani, meye amfanin lalata rayuwarki da kikeyi? Har jikokinki sai an yi musu gori, wannnan abinda kika aikata! Kina da babban laifi mama, sai kin tuba kin bi Allah kin bi iyayenki sannnan xaki ga daidai a rayuwarki, kinji ni? Ta amsa da kai, yace ta shi ki shiga wajen 'yar uwarji kafin Allah ya kaimu goben. Ta mike simi-simi ta ja akwatinta, inna saude ta xuba mata ido tana mamakinta. Ta kada kai, taca baka ce xata aikata ba, yarinya kyakkyawa, ta lalata rayuwarta. Allah ya shirya mana, yace amin albarkar annabi. Atsakar gida taga Baraka tsaye tana share hwaye, ta matso ta kama mata akwatin suka shiga dakin, kowacce ta nemi wuri ta xauna bakin katifa. Baraka ta dubeta......... Tace anya mama abubuwa da kike yi kanki kalau? Ke bakijin kinya? Baki tunanin gaba daya idanuwan garin nan sun dawo bisa kanki? Baki da martaba da darajar Abba agarin nan? Haba Mama, kamar ba tare muka taso ba? Tarbiyarmu iri daya, nutsuwa da kamun kai, kowa na yabon mu. Mutane na rububin mu, da son hada xuri'a tagari. Ta daga kai sama, idanuwa cike da hawaye ta cigaba, Allah ya isa tsakaninmu da Danliti! Ta dube ta sukayi ma juna xuru kafin Mama tace kar ki sake xagin Danliti Baraka, alhakin sa xai kamaki, laifin mune? Tun tym din da mukace muna son juna, ya kamata su Abba su rungume mu hannu 2 amma suka ki, suka gwammace in kwashe kayana in bishi. A tunanin ki wane sakamako ya kamata su gani? Bayan wannan dake jikina? Baki sake take kallonta, kafin tace, maganar Banza ce, idan duka jina kunnuwa ne xai taba sauraronki ba, wa kika burge don kin aikiata wannnan sakarcin? Shi kansa Danlitin adage yke kallonki. Kin dawo an yi miki afuwa, cikin nman ya bayyana, duk sun hkr, sun shanye, amma ki ntsu xuwa tym din da xaki haihu, a daura maki aure, kar fa ki manta xaman nan naki agida ibadane tunda Allah ya shifida hakan, sai ki ga dalilin xaman, duk xunubunku sun kankare, auran ku yayi karko tare da xuria masu albarka. Ki kwanta kiyi tunani mama, ko asiri Dan liti yayi miki, xakewar taki tayi yawa. Ta sualala kafita ta kwanta, tace, na kwanta shekiya Baraka, sai da safe ko? Ta bita da kallo ta numfasa, tace Allah ya sa ki gane. Amin, ta amsa da gatse ta juya baya abinta. Baraka ta mike ta rufe daki ta dawo ta kwnta. Ta jima bata sami barci ba, saboda juyayin halin da 'yar uwarta ta shiga. Da farar safiya M.kasim ya usa gidan Ubban dawaki yasa aka yi masa sallama da shi, jin cewa shine ke sallam ya sa yace ya shigo cikin gida. Bayan su gaisa. Umma ta fito suka gaisa. Sannan ya maida jawabinsa, a karshe yace, alhaji kar bacin rai yasa ka yanke wannan hukunci, ni ina ganin gara yarinyar nan ta xauna agaban ku, kuna tsawata mata, sai Allah ya taimakemu ya shiryar da ita. Don girman Allah ka yafe mata dawo gida, tunda tayi tunani taxo wajenmu, ta kawo mana kukanta. Abba ya gyara xama yace, a tunanin ka a kashin kanta, ta yanke shawara taje wajen ku? To ba haka xancen yake ba, kila ba xaka sani ba ne, saboda kuan cikin lungu. Amma ni tun jiya na sami labarin wulakancin da yaron nan yayi mata, ya tara mata jama'a, ya tozarta ta, ya kuma ce ba xata xauna masa a shago ba, kaji dalilin nemanku, amma ba nadama tayi ba. Yace, duk da haka ina son ka duba girman da martabar ka agarin nan. Kayi hkri ka amshi rokona, ba don ni ba, sai don girman Allah da darajar iyaye. Ya sunkuar da kai yana kadawa, kafin yace, M.kasim ban ki ta taka ba, amma ba xan iya xama da yarinyar da ban isa in bata umarni ta bi ba. Ta fita tayo shashancinta, ta dawo min gida ta wanke najasa ta kwanta. Mts! Ban jin idanuwana xa su iya jure gainin wannan kaxanta. Gara ta tafu su cikashe. Wlh na hkr da ita, kuma ina rokon Allah ya sanya mana dangani nida Mahaifiyarta, ba kuma xamu gaza ba wajen yi mata addu-ar shiriya. Watakila wata rana taga uwar bari, ta dawo da kanta ta neme mu. Kaga a tym din xan tabbatar da tayi nadama. M. Kasim yayi shiru, jawabin Uban dawaki na cike da tausayi, ya numfasa, yace, na yarda da kai Alh. Sai dai har yanxun ina rokonka, da ka sake bata dama ta karshe, mu gani.idan bata daina ba, to muma sai mu tsame hannayen mu. M. Kasim ya cikwa Abba ido kwarai da gaske, ya jima kafin ya numfasa, yace, shikenan ba komai nagode. Yace nima nagode, Hajiya akara hkr, a bata damar karshe, tace babu komai M. Kasim, Allah saka da alkhairi. Yace amin, barin in koma in turo saude ta dawo ita. Tace to ka tsaya kaga abin kari akawo maka mana, ya mike cike da fara'a, yana fadin alhmdlh, kar ki damu nagode, to nabr ku lfya, Allah ya shige mana gaba, suka amsa amin. Yaka hanya fice. Bayan tafiyarsa kamar da hadin baki, jama'a sukayi ta xuwa suna ba uban dawaki hrk tare da rokonsa ya daure ya maida 'yarda gabasa xai fi kyau agareshi. A cikin su har da abokansa da yaron gidansa, watau kalla. Duk ya karbi rokonsu, kuma yaji dadin kulawar jama'a gareshi tare da tausaya masa akan kaddarar da ta fada wa iyalinsa. Karfe Tara saura, Inna saude ta taso Mama xuwa gida. Bata ma biyo da ita ta shagon Danliti ba, balle ya gansu, haka suka taru da matan gidan kamar zasu cinye ta danya, sannan matza suka shigo suka dasa nasu. A gaban kowa suka tilasta, ta dauki alkawarin ba xata sake xuwa ko ina ba, kidan kuwa ta saba, to a yanke mata hkunci da yafi wannan. Kwana 2 hatsaniyar nan ta kwnata, mama na xaune cikin gida bata fita daidai da tsakar gidan sasansu. Muna iya cewa Danliti bai murda kambunsa bane haka? Saboda haka xuciyar Mama ta sami 'ya nutsuwa. Bata ita kadai ba, su abba ma sun sami 'ya nutsuwa har tana debo 'ya'yan itatuwan da Abba ya ka siyo ta kawo mata, tace ta sha saboda rashin cin abinci da take fama da shi..... ***************** A wannan asabar din ma abdulkrm ya xo daiyalinsa duka. Su ameera nata murnar ganin auntynsum domin sun jima basu ganta ba. Dr. Na ta dabo, yana son ya taka, sai 'yar banxar kuiyam shi ya sa yaki yarda Mama ta daukeshi. Aunty Rabi ta tasa ta da nasihohi, ayoyi, hadisan Manxo SAW akan ta dage ta yaki xuciyarta ta dawo kan kanya, sannan ta nuna mata wannan ba shine soyayya ba, duka saurayin da ya nemi lalacewa da yarinyar da yake so, a hakikanin gaskiyya ba son gaskiyya yake mata ba. Sha'awar sassan jikinta kawai yakeyi. Haka yayanta ta tsatsagge mata gaskiyya, har yayi mata alkawarin idan ta nutsu ta xauna gida kamar yadda aka umarceta, to bayan ta haohu za'ayi bikinta, duk abinda take so, shi xai sayo mata. Mama ta wani kuka tana ba su ameera tausayi. Anann suka kwana, washegari lhadi karfe 12noon suka juya. Su ameera nata tambayar antyn su yaushe xata xo? Tace kar su damu tana nan xuwa nan bada dadewa ba, suna isa gida, yayan ya kira 'yan uwansa, ya labarta musu abinda ya gani game da Mama, idan har ya dore a hakan, alhmdlh! Ana iya cewa an fara samun nasara. Kowa yayi farin ciki jin wannan labarin da fatan Allah ya shige mus gaba. Allah, da ikonsa a yammacin yau din, tun bayan sallar la'asar mama ke cike da kewar Danliti, kafin 5pm ra mance kaf! Da alkawuran da dauka, babu abinda take so face gain Danliti, kewarsa ta gigita kwakwalwarta, ta birkita ta. Kamar an tsikare, kawai ta tashi ta suri gyale da takalmi ta fito kanta tsaye ta fice abinta. Dan gogan ta samun cikin dakin barcinsu, tana shigowa yana xubawa wani kaskon rushi ruwa, ya dago ido ya dubeta, yace ba xan miki sannu da xuwa ba. Ta xaune gefensa tana murmushi, saboda me? Ya xubo mata harara, yace kwanaki nawa rabon ki da nan? Sabo da nayi miki fada ko? Ta rungomoshi tana dariya, ayya nawan ba haka bane, kowa yasa min ido, sai surutai sukeyi kamar ni kadai na fara soyayya agarin nan. Amma kana cikin raina, kaima ka sani, bani da burin da wuce in kasanxe tare da kai, ta bae baki yace tsarani, au baka yarda ba? T yanxun ba ni na xo ba? Dana kiraki ba? Ka kirani? Kamar ya? Ya ture kaskon ba xaki gane. Sai dai na yarda kina sona, tunda kika amsa kiran. Ta xura masa ido tace

Chapter 19 of 28