Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
cikin satin nan. Saboda haka ki kwantar da hankalinki, ki na dasauran 'yal3an da suke bukatar ki kusa da su a koda yaushe. Kinji ni da kyau? Ta goge 'yar kwallan da suka xubo mata, tace naji alhji, Allah yayi musu albarka baki dayansu. Yayi murmushi yana fadin, amin kina iya dauko abincin yanxun. Ta tashi da saurinta, ta wuce, ya raka da ido tausayinta ya kwarara cikn ransa. Ya numfasa yace, mun gode maka Allah da wannan jarabci. Ta fito masa da abin, ya gaugauta ci, domin gab ake da kiran la'asar. Ya kammalawa kuwa tym yayi, ya mike yana fadin, ki shiga ki tasheta tayi sallah. Ta amsa da to, ya wuce dakinsa. Umma ta kwashe kayan ta maida kicin, sannan ta nufi dakin Mama, don tashinta. Tana kife ruf da ciki, Umma ta dada mata duka ta tashi a firgice. Umma ta xura mata ido, tace, in kin ga dama ki tashi kiyi sallah! Tayi waje ta bata wuri. Da kyar ta mike zaune, kanta ya sara mata, ta dafe shi hannu biyu, gaba daya miyan bakinta ya kafe. Makoshin ta ya bushe. Tana daga xaune, amma jiri ne ke dibar ta.... Idanuwanta na ganin duhu, don haka ta runtse su tamau! Tana maida numfashi, ta wuce minti sama da goma ahaka, sannan ta iya tashi a daddafe ta shiga bayin. Tunaninta kawai tayi wanka ko tafi jin dadin jikinta. Nan da nan ta kwashi ruwa a bokiti ta fara wanka. Kamshin sabulun( Joy) Ya gauraye bayin, ba xato ba tsammani taji xuciyarta ta tsani kamshin, kan ka ce kwabo ta goce da amai. Ta kwarara mai isarta, wai don ma babu komi cikin nata. Tana gamawa ta dauki bojitin ta juye ruwan ajikinta, tun daga kai. Ta jefar da shi ta yayo xani ta daura, ta banko kofa ta dawo daki, ta bar bayin face face da amai. Ruf da ciki ta sake fadwa gado fadi take, wash! Wayyo Allah xan mutu! Tun daga tym din al'amura suka kwance mata, ta rasa kanta ta rasa meke damunta tana rashin son abinci da yawan tashin xuciya, ga wani cikin safe da jiri wani tym din jikinta yayi xafi, don kansa kuma ya sauka ba tare da tasha magani ba. Duk ba wannan bace babbar Matsalarta ba, Ina Danliti ya shiga kwana 2 babu labarinsa? Me kuma yake nufi da tafiyarsa? Duk da cewar tasan dole ya dawo, idanuwanta da xuciyarta sun gaza jure rashin sa na 'yan kwanakin 2. Shi yasa koda yaushe tana kunshe a dakin matsalolinta masu yawa na neman xautar da ita. Umma da kanta bata gane kanta ba, musamman rashin xuwanta neman abinda xat ci. Amma yawan xaman daki umma ta jingina da rashin ganin Danliti da ta rataywa xuciyarta, balle ayi maganar jingina shi da wanccan Matsalar. Ta kan kada kai, tace, kaico! Abincin wani, gubar wani! Allah ka raba mu da muguwar kaddara... A yau asabar ake sa ran xuwan yayyin Mamma, ga shi babu magana mai kwari ko kuma muce uban gayyar baya gari, shi da kansa abba xaune yake shiru dakin ta same shi, ta xauna gefensa tace, kana xaune baka shiga wanka ba? Yayi gajeran tsaki, yace maganar nan ke damuna, da yarinyar nan xata gane da ta amince cewar Dalinti ba xai turo kowa ba. Banda aikin rashin gaskiyya, menene na kama hanya kabar gari, kai da aka ba damar ka aiko a baka mallakar abinda kake so. Wane bata tym xakayi saboda Allah? Ta numfasa, tace yaushe xata fusknaci hakan yadda ta makance gaba daya, bata ganin kowa sai shi? Ai na gaya maka ko abinci bata ci, duk ta fige saboda bala'i, ni yaran nan ma dasu wahala suke nake tausayawa ba su gama warware gajiyar biki ba, ga aikinsa mai dan banxan wahala, da da halin da xa'a ce da su dakata, wlh da ance suyi xamansu. Ya gyara xama kyale su suzo ko hira mukayi, ai maji dadi, ko ba haka ba? Haka ne, Allah ya kawo su lfya. Amin ke ki kira min Mama ta zo yaushe, dan liti xai dawo? Ta mike ta nufi daki Mama ta tura kofa kakarin amai ya fara dibar hankalinta, cikin fargaba ta nufi kofar bayin ta murda ta bude, Mama! Tana durkushe kame da ciki, kamar xata mutu. Kan Umma ya kara daurewa, domin bata taba ganin Mama na kwarara amai haka ba. Ko rashin lfya takeyi, bata amai, sai dai xafin xaxxabi. Don haka ta nufe da sauri ta dafe ta, me xan gani haka Mama, baki da lfya ne ko yaya ne? Bata iya amsa mata ba, tana tsaye kame da haba, tagama kakarinta, ta kuskure baki hade da fuska, tayo waje abinta, ba tare da kula Umma ba. Bisa gado ta fada ta datse ciki tana numfarfashi. Umma ta biyo a fusace tasa hannu ta birkito ta, ba kyajin ina magana ne? Nace lfya kike sheka amai? Ido jajur! Cike da kwalla tace, cikina ke min ciwo, tun yaushe? Yau 3days. Ta jawo ta waje cikin haske sosai, ta kama hannayenta ta dudduba, sannan ta gwale idanuwanta, ta duba cikinsu, a tsorace ta tambayeta ke, kina yi al'ada kuwa? Tayi shiru tana xaxxare ido, baki na rawa tace, nima ban sani ba Umma. Ba ki sani ba? Ke xaki gaya min ko sai na farfasa bakinki? Ta goce da kuka, don ita ma ta kideme, ta mance rabonta da a'alada. Umma ta xura mata ido, jinin ta na kara hauhawa, da sauri ta wuce ta bar mama tsaye. Dakin abba ta koma ta xauna, ta rike kai tana maida salati. Me akayi? Tace alh. Magana takare ka dauki mama ka kaita asibiti ayi mata gwajegwaje! Gabansa ya fadi gwajegwaje? Name kuma? Na komai Alh. Ina shiga na sameta tana sheka amai a bayi, wai cikinta ke ciwo, amma alamu a bayyane sun nuna Mama juna 2 gareta........ Tsaye ya mike tare da fadin me? Hawaye suka kara tsunke mata, ya koma a hankali ya xauna bakin sa na karanto salatin Manxon rahma. Gaba dayansu tsit! Sukayi tsawon lokaci sai Umma ke shatatar hawaye, baiyi aune ba kawai ya ga ta dungura ta fadi a sume. Ya xabura ya tarairayota, yana kiran Halima! Halima!! Don girman Allah karki kara min tsahin hankali akan wanda nake ciki, ya jawo goran ruwa ya xuba a hannunsa, ya yarfa mata, ya cigaba da shafa mata ruwan bisa fuska, ahankali har ta dawo hayyacinta. Ta bude ido, jim tana kallonsa, sannan ta sake fashewa da kuka, nan take tausayinta, yasa kwallan Ubandawaki suka fara sauka bisa kuncinsa. BAKIN CIKI kamar ya aika shi barxahu. Kiyi hkr, ki kwantar da hankalin ki Halima, wannan jarabawa daga Allah Ubangiji take, babu wanda ya isa ya kankare mana ita, bana son tsanin damuwar nan da kikeyi, tana jefa ni mummunan matsayi, ko dogara da Allah Halima shine xai magance mana komai. Ta goge hawayenta tayi, iyayinta don ta tashi xaune amma ta kasa. Yace kar ki damu da sai kin tashi yanxu kiyi kwanciyarki ki huta, bari in kwaso magungunan ki in duba wanda ya dace kisha. Ya mike da sauri wani duhu ya rufe masa idanuwansa, bai ganin komai face wasu miliyoyin taurari kanana, tilas ya dawo ya xauna ya fadin Hasbinallahu wa nimal wakil. Yayi ta maxa ya sake mikewa. Umma tace ka xauna Alhaji kar kaje ka fadi ka nakasa. Bai tanka ba, ya fice. Jimawa kadan ya dawo da kwanndon magungunan ta ya xauan yana bincikawa, jikinsa na rawa saboda bacin rai. Sallama sukayi daga falo kuma babu tantama muryar Ya abdurahman ce, abba Ya amsa, ya kara da fadin gamu nan, ku karaso ciki. Ganinsu jugun2, Yaya take ya rasa kuzarinsa. Yaya dai Abba? Jikin nata ne ya tashi? Yace shine abdulrahman, nan da nan ya xube gabanta, da dauko kanta ya dora bisa cinyoyinsa, sannu Umma! Sannu! Ta matse kwalla, ta dube shi, kaxo lfya? Ina safiyya? Ya amsa lfya lau take, tace in gaisheki. Ina amsawa, me yasa baka xo da ita ba? Ya goge mata kwalla, tayi nauyi ne Umma bata jin dadi, idan tayi doguwar tafiya, koda muka koma, bayan daura aure sai da tayi xaxxabi. Ta dan kada kai, tace Allah sarki, Allah ya raba su lfya. Amin. Ya amsa sannan ya dubi Abba suka gaisa. Kafin su kama wata maganar, muryar Manyan yayin ta gauraye cikin falonm. Abba ya gaya musu suna ciki, kowa ya shigo da kuzarinsa, ya ga Umma a kwance sai yayi turus! Bayan sun gaisa tasha magani. Abba ya kwashe abinda ke faruwa kaf, ya gaya musu, kowa yayi shiru, kawunansu sunkuye tsawon tym kafin Ya soja, yace, yanxun Ina Maman take? Oho inji Abba, gaba daya sukace oho? Ta bar gidan nne, Umma tace tsakar gida na barya tsaye, ban sani ba ko ta koma daki ko ta fice don ba sani xamuyi ba. Duk tym din ta so fitarta, ficewa ta takeyi. [12/01 21:55] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 2***14 Ya soja ya dubi Ya abdulrahman, yace je ka kawo mana ita nan! Ya miki cikin hanxari, ya nufi dakinta, tana kife bisa gado aikin kuka kawai takeyi. Ya sa hannu ya fisgota, ba karamin tsoro ya bata ba, ta kwala ihu, wani BAKIN CIKI ya kara turnuke shi, bai san tymda yasa hannu ya doke bakinta ba, yace rufe mana baki shashasha. Da sauri ta kame baki, wanda take kyautata xaton hakoranta xasu iya xaxxagow idan bata dafe shi ba. Ahaka ya ciga da jan ta har dakin abba. Gaban babban ya direta, ta xube har tana karo da guiwarsa. Ya xuro mata ido kamar zasu fado kasa. Yace matsa kdaga kusa dani, xan iya tokarinki, ki mutu idan baki matsa ba. Ta janye jikinta baya, ahankali hawaye na ambaliya, sunfi minti 5 babu wanda tanka saboda takaici, kafin Ya abdulkrm yace, gaba daya kin rusa rayuwarki Mama kin lalata cikar asalinki da martabar iyayenmu. Yanxu wa ya isa ya kankare bakin fetin da kika shafawa kanki? Wa ai daura miki aure da ciki? Wa kuma xai jagoranci kisan kai? Wannan cikin dole ki haife shi, domin yunkurin xubda shi, ya fi yinsa barna da tarin xunubi. Kin ga tun daga nan idan kinyi tunani cikin hankalinki, xaki gane babu soyayysa tsankaninki da Danliti. Burinsa dama ya ruguxa rayuwarki, burinsa kuma ya cika tare da hadin kanki. Saboda haka dabara ta rage wa mai shiga rijiya, sannan karki xargi Danliti, idan ya tsallake auranki, gaba daya abinda yake bukata ya samu, abinda yai saura shine ki haife masa wannan ckin, in ya ga dama ya karbi dan, idan bai yarda ba ya kyaleki da shi, ku wulaknta. Dama wannan shine karshen son xuciya. Babu uwar kudi balle riba ga mai cinikin son xuciya. Kuma duk wanda ya hau motar kwadayi da son xuciya, babu tantama tashar kunya da nadama xata kaishi ta aje. A koda yaushe karshen danasani, ina fatan wannan xai xama darasi gareki, ki gane cewa abinda Babba ya hango, yaro ko ya hau gwauron dutse ba xai hango ba. Ya goge 'ya kwallan da suka xubo bisa kuncinsa sannan ya sauke numfashi ya dubi sauran, yace yanxun mene abinyi? Abba yace abinyi babu shi abdulkrm, tunda maganar aure ta rushe a halin yanxun. Ya Soja yace duk da haka, dole ya san tana dauke da cikinsa, bayan ta haihu xa a daura musu aure, su tare da yaronsu! Su karata can da abin kunyarsu! Ya abdul rahman ya kara sanyaya muryarsa mai taushi, yace wannan dole ne, amma abu na farko shine, ina xata xauna? Ta kula da kanta? Umma dai ba xata jure ganinta a wannan yanayin ba, ya soja ya gyara zama yace, gaskiya ne, kuma waje na ya kamata ta xauna, sai dai ba xan iya daukarta ba saboda xan iya yi mata dukan mutuwa yadda nake jin na tsani ganinya. So a cikinku, wanda yake ganin xai iya hkr da ita, yana iya tafiya da ita Allah ya shiryeta, mu kuma kullum addu'a muke mata, idan ta dauki wannan mtsayin darasi a gareta, xamu fi kowa farin ciki. Ya Abdulrahman, yace ni xan tafi da ita, no ka bari ni in wuce da ita Minna. In ji Ya abdulkrm. Abba yace ba xata biki ba nan da xata xauna... ban ce mata yin ku za su yadda ta ba amman yau da gobe sai Allah. gara ta zauna anan, domin anan ne suke aikata abin kunyar u kun ga ganinta da juna biyu ba zai girgiza kowa ba sanin cewar daman can sakamkon da zai biyo baya kenan. in ba wani gyaran Allah ba. saboda haka ku kwantar da hankalinku kuci gaba da yi mata addua sannan ku kwantar da hankalinku ku tallafa wa mahaifiyar ku ta kowace fuska don ganin ciwon BAKIN CIKIN bai tagayyara ta ba, dukkan su suka jinjina kai alaman uban dawaki gaskia ne. yaya soja yace da yardar Allah umma ba za ta tagayyara ba, idan mama bata son ki mu bamu da wacce ta fi ki. bamu da wani buri. da ya wuce mu rayu tare da ke. kar bacin ran mama yasa mu dakatar da dukkan farin cikin mu. mu ukkun nan mun ishe ki kallo ki samu sanyi a ranki ko umma? hawaye na suka malalo mata yaya abdul yayi maza ya rungumota ya na share mata hawayen ki daina kuka umma in kina kuka mama ba zata taba ganin haske ba, duk adduar da zamu mata tace ba komai wallahi bana jayayya da ikon Allah amman ku sani BAKIN CIKIN ba zai goge cikin raina ba, domin FARin ciki da bakin ciki duk halitta ce cdaga Allah fata na kawai Allah ya bamu ikon cinye jarabawarnan Allah yayi maku albarka Kowa ya numfasa, yace amin, abba ya dubi mama da hawayenta yaki yankewa yace, ina fatan kin ji abubuwan da 'yan uwanki suka fadi, idan kinyi anfani da su, ki ga daidai, idan kuma kin ce ba haka ba, mu babu abinda xamu iya yi, sai mu kyale ki, ki ci gaba da rayuwar da kika xaba. Ko dama kin riga kin ruguza ta, karashe ne kawai. Allah ya shiryeki, ki na iya bamu wuri mu sha iska, ki jira dawowar Danliti, amma ki sani auran ku ba shi yuwuwa, sai bayan kin haihu. Tashi ki bamu wuri. Ta kara makurewa, kukanta ya karu, duk suka xubo mata ido. Ya soja yace wa yace kiyi kuka? Cewa akayi mun gaji da ganinki, ki koma dakinki. Ta yunkura kamar xata tashi, amma ta kasa, da sauri ta rarrafa jikin Ya abdulrahman, ta kudundune ta rushe da kuka. Nan da nan ta karya masa xuciya, ko dama shi akwai sanyi da saurin jin tausayin mutum. Idanuwansa suka cika taf da kwalla, tun baya son kulata har ya kai hannunsa, bisa knta muryarsa na rawa yake fadin, imani kawai xai sa akalleki Mama, amma ke ba abar tausayi bace, tunda baki tausaywa kanki ba...... Ya soja ya katse shi, pls abdulrahman, fita da ita, Umma tace sai ma ya fita da ita? Gata kenan, ya kyaleta, ta tashi da kanta ta wuce. Ya tarairayo ta suka mike tare, ya janyo ta xuwa dakinta ya xaunar da ita bakin gado. Ya tsugunna gabanta yace, dube ni Mama. Da kyar ta dube shi, hawayen ta na xuba, yace kukanki bai da wani anfani, muddin ba nayin nadama bane. Nadamar ma ta gaskiyya, tsakani da Allah. Saboda haka ina shwaratar ki da ki kama kanki, wannan ya xama na farko kuma na karshe. Ba soyyaya vace wannan, ki dauki jikinki ki ba da ga namiji, daga ranar da ya sanki a waje. Wlh kin gama yawo, duk wulaknci da ya ga dama xaiyi miki, ko da kinyi sa'a ya aureki, abanxa xai rika kallonki, sannan wulakanci ba xai daina shi ba, a karshe ki ga auran ya bantale, tun ba aje koina ba. Kuskure ne, kin riga kin yi Mama, irin wanda bamu taba xato ba, babu yadda xa muyi mu gyara shi, sai dai kiyi tuba wajen Allah, sannan ki nemi afuwarsu Abba, kin jini? Ta xura masa ido, hawaye na ta bulbula ta kasa fadin komai, domin ita kanta bata san ainihin abinda ke damunta ba, cikin ranta agame da samun ciki ba tare da aure ba. Saboda haka, sake fado masa tayi, ta kankame shi, kukan ta kamar xai fasa xuciyarta. Ba karamin rikita shi tayi ba, domin nan take ya goce da kukan shi ma. Da kyar ya banbare ta ya mike da sauri ya bar dakin, ya dawo falo ya cigaba da gugar kwalla, xuciyarsa na masa ciwo. Kai! Sun dandani BAKINCIKI, da akwai yadda xasuyi su goge wa Mama wannan bakin fentin da sun goge mata shi, ko da shi xasu rasa komai nasu. Sai dai kash! Babu hali, shi ya sa ko abinci tsakurarsa sukayi suka ci, ba don yayi musu dadi a baki ba. Haka suka juya bayan sallar la'asar makare da BAKIN CIKIN da baya misaltuwa. Haka zalika sun bar Mama cikin wani yanayi na kunci rayuwa, wanda ya wanxar mata da cututtuka masu dama ajikinta. Kafin yamma ta fadi, kamar ba ita ta dawo Legos dambasheshiya ba. Sati 2 kenan yau babu labarin Danliti, yayin da rashin lfyar mama ke cigaba da yaduwa tamkar yadda labarin samun cikinta ya gama baza gari, ta bakin Hajiya Gaje. Amma don tsabar yaudara su suka matsawa Mazajensu su akan su kai ta asibiti ko ta sami dan taimakon da xai rage mata larurar jikinta. Da kyar abba ya amince. Alh. Basir ya kaita babban asibiti da garin Kagara. Suka ga likita, yayi gwaje gwajen sa ya gano, lalurar shigar ciki ne ke wahalar da ita. Saboda haka ya bata 'yan taimakon da xasu rage abubuwan da take ji a jikinta, sauka dawo gida. Sun wuce kofar shagon Danliti shi kuma yana karasowa wajen. Yayi fakin ya fito tare da yin daguwar mika mai isar da sakon gajiya. Ayuba ya fito ya tarbe shi, sai dai fuskar sa babu fara'a ko alama. Yaya dai mutumina? Naga kamar kana ciwo? Ya numfasa, amma bai tanka ba har suka shige shagon. Ya dube shi da kyau, yace ina magana ka kyaleni, lfya nace? Ya kara sauke numfashi. Yace ina fa lfya, magana ta cika gari..... Ya katseshi Mama na da ciki ko? Gabansa ya fadi ya saki baki yana masa kallon Mamaki, Dan liti ya kece da dariya, kwalla na gangara bisa kuncinsa kafin yace, shiege ni, dan buzu mai shayi. Raina kama gaiyya, ka tabani ka ga tsiya. Watau labari har ya bazu ko? Kaga burina na farko ya cika, amma har yanxun akwai saura, don na san dan xagin kalilan za'ayi mata. Ido jajur! Ayuba yace, kaji tsoron Allah Danliti, ka kyale yarinyar nan haka. Tunda ba xaka aureta ba, ka barta taji da wannan bala'in! Ai ka gama ruguzamata rayuwa, babu sauran wulakanci da yafi wannan..... Ya ja Kujera ya xauna, yace haka kake gani, nasan akwai saura, sai dai ba xan shanye maka dadin labarin ba, idon ka nake son ka gani kamar yadda ka ga wannnan. Ya bishi da kallo, yana kada kai. Murmushin keta Danliti yayi, ya sake fadin, babu wani abu mutumina, kai kanka kasa ramuwar gayya, tafi gayya xafi. Dadin abin a gabanka mama ta xageni, ta xagi Mahaifina, ka manta kawai! Yace wannan ba hujja bace Danliti, ina gaya maka barnar da kakeyi tayi yawa. Allah ba xai kyaleka ba. Ya ja dogon tsaki ya mike tsaye, kai wannan ya dameka, ni yanxun gidan ma xani kuma lfy lau xaka ga na dawo, see you! Ya juya ya daga kanta ya fice abinsa, ayuba ya koma a hankali, ya xauna ya dora tagumin mamaki da takaici. Danliti ya sake gani ya dire masa bakar leda tare da kwalin juice kato bisa kanta. Yace ga sauran kazar da na ci a mota nan, idan ka gama laulayin, ka ci. Ya juya ya wuce mota, yayi tafiya sa ya bar shi da tagumi. Kansa tsaye yayi fakin kofar gidan Uban dawaki, akwai yara gidan suna wasa, don haka bai yi wahalat neman yaro ba, take nan ya aika yana kiran Mama. Yarinyar ta shiga, jim kadan ta fito ta gaya masa tana xuwa. Yana nan jingine da mota yana kada makullai. Abba ya fito. Nan da nan ya tsuguna kai sunkuye, mummunin kare kenan. Yace, ah! Sannu abba, ina yini? Abba ya bishi da kallo, amma kash, ya kasa ganin bakinsa balle ya gaya masa bakaken maganganu. Ya amsa gaisuwasa, sannan yace mike ka biyoni. Ya wuce kofar falon bakinsa, ya murda ta bude suka shiga, xauna, ya nemi waje ya tankwashe kafafuwa. Abba ya xauna ya dube shi da kyau yace, yanxun saboda Allah Danliti abinda kayi, ka kyauta kenan? Me ya sa duk abinda xakuyi baku sa tsoron Allah a xukatanku? Ya xa kace kana son yarinya da aure, sannan ka aikata mata abinda ba shine ba? Danliti ya kara sunkuyar da kai, kamar xai tsaga kafet din falon ya shige don gulma, abba ya ciga da cewa, to ta faru takare, ahalin Yanuxn Mama juna 2 gareta, kaga xancen auranku ya rushe kenan dole tayi zaman istibra'i xuwa tym da xata haihu. Wannan abu ya bani kunya kuma kun xubar min da mutunci da kima a garin nan. Hannaye 2 Danliti ysa ya rufe fuskarsa yayi xugum, ko mtsi ba yayi. Abba ya numfasa ya kada kai ya cigaba, ni bani da abinda da xan iyayi, tunda kaddara ta riga fata, abinda kawai nake soka sni, shari'a ce ta tsara haka, saboda haka dole ku kauracewa juna, don gudun karku kara maida hannun agogo baya. Ina fatan kaji? Sai ka koma jira ranar da xata haifamaka danka, kaga kun sami dan aike, ba sai kun nema ba. Kana iya tfiya, mu jira abinda Allah xaiyi. Shawara da xan baka kawai, ka nemi tuba wajen Allah, domin ka saba masa, ka keta rigar mutuncin yarainya. Shiru yayi ya kasa tashi, abba yace tashi mana, ni nakare magana, ya dago kai da kyar, amma bai kalli fuskar abba ba, cikin sanyin murya yace, abba kayi hkr ka yafe min? Wlh sharrin shaidan ne. Ya goge kwalla, abba na kallonsa kafin yace, haka ne, amma wani tym har da son xuciya. Si yasa nace ka nemi tuba wajen Allah, don ta ni mai sauki ne. Ya kara rankwafawa yace, je ka kawai. Ya tashi simi simi ya fice babu ko waige. Abba ya raka shi da ido, sannan ya numfasa ya kada kai, yace Allah ya shirya mana. Shi kuwa Danliti yana fita yayiwata 'yar girgiza ta jin dadi, ya wuce motarsa cike da farin ciki ya koma shagonsa. Ledar kazar da ya ajewa ayuba suna nan bisa kantar bai taba ba. Wai don ya ba ayuba haushi sai ya dage kantar kayan suka watse kasa. Ayuba ya bishi da kallon kafin ya ce ni baka ban haushi ba don ka xubar kudinka ne, ba nwa ba, gaskiyya ce dai ba xan daina gaya maka ba, watakila ma baiji shi ba, domin bai tsaya ya saurare shi ba, cikin daki ya shigr. Yayi kwance yana tunanin shirinsa na gaba akan mama. Abba kuwa ys jima falon xaune yana tunani rayuwa kawai. Sannan ya mike da kyar ya koma cikin gida, ya maida wa Umma yadda sukayi da Danliti ta kada kai tace , shikenan, Allah yasa ta nutsu ta xauna gidan. Yace amin, amma ina mai tabbatar miki muddin tace ba xata nutsu cikin gida ba, xan bata mamaki, domin, dole ta xaba ko mu ko shi. Umma tace gaskiyya ne, ace wannan abu ya sameka, baka yi nadama, ai kuwa sai a sallama mutum asa masa ido. Allah yasa mu dace. Ya amsa da amin. Tunanin uwar gayyar ba anan yake ba, domin kuwa jin ga Danliti yana kiranta, ya tabbatar mata da cewar ya dawo kuma taso ta ganshi, su Abba suka taka mata birki. Duk da haka taji karfi a jikinta kwarai da gaske, har wasu daga cikin cuttuttukan da ke damunta suka yaye nan take. Sai dai tana ganin babu adalci a hukuncin dasu abba suka yanke. A zaton su zan iya zama tsahon tym banga masoyina ba???????? Ta tabe baki tana daga kwancw tace, ba xan iya ba gaskiyya, sai dai suyi hkr wlh. Ai dai maga juna, ya san halin da nake ciki, ya tausaya min. Ta goge kwalla ta cigaba da sakar xuci. Ana ta sallar magriba, tym ne da ita mama ta sami damar satar jiki ta sulale ta isa shagon danliti. Shi kuma kaida ke xaune cikin shagon. Ayuba ya shiga sallah. Yana ganinta ya dafe kirji ya wani lumshe ido. Yace wayyo Allah na gode maka! Ta daga kanta ta shiga, ta nemi t barma ta zauna, saboda bata jure tsayuwa. Tana xama ta hade kai da guiwa ta fasa kuka ya kare mata kallo, a dage yana dan murmushi, sannan ya taso ya dawo gunta yace haba bebina! Meye abin kuka? Ya xauna gefenta ya rungumota jikinsa, bana son kukan hakan nan....... Ta cira kai da sauri ta dube shi, ba xanyi kuka ba? Ciki fah gareni, kowa ya tsaneni ana ta zagina. Shine xaka ce ba xanyi kuka ba? Yayi dan murmushi yace, bebi kenan, to don kowa ya tsaneki shine me? Bayanni ina son ki kuma ina son ciki na! Kina so yi kukan ne, wata kila kuma na dadi ne yayi miki yawa. Ta mako masa harara tace, jin dadi? A zageni, a tsaneni shine jin dadi? Son ka ne kawai yake sawa bana damuwa, amma kai ina ganin abin baya damunka, daya dame ka, da baka wanke kafarka ka bar garin ba, tsawon sati 2, alhalin an ce ka turo a daura mana aure. Da ka maida hankali ka turo din, ai da duk hakan bata kasance ba, koda cikin xai bayyana adakinka xai fito. Tunda ni ban ma taba nuna wa akwai wani abu tskanin mu ba. Sannann.... Ya da ka mata tsawa, ya ida don Allah! Haba! Wannan maida xancen na menene? Ko kuwa turo ki akayi ki zo ki batan rai? Ko dan kinga ina ta rarrashinki? Babu fah dole, kin ganne? Abban ki cewa yayi ba dole bane ya bani ke, ko bayan kin haihu. So pls ki daina damu na da irin wadannnan surutun banxan, ban son jinsu, idan har kin son mu shirya! Kin gane? Ta xura masa ido hawaye na xuba, ta ma rasa me zata ce? Ayuba yayo sallama ya shigo ya riske su cikin wannan halin. Shi ma yayi tsaye yana kallon su, jim kadan Danliti ya buga tsaki ya tashi ya shige daki ta goge hawayen itama ta tashi ta bishi, ayuba yaa kada kai ya ja kujera ya xauna yana fadin Allah ya kwaci yarinyar nan. Tana shiga ido ya xubo mata. Yace au biyo ni kikayi? To ranki xai baci kuwa, gara ki koma. Ta marairaice tace, kayi hrk Danliti, ba don ranka ya baci bane ya sa na gaya maka abinda ke damuna. A xatona xaka tausaya min a halin da nake ciki. Bani da wani gata wajen iyayena. Tun ranar da na nuna kainake so Danliti, ka tausaya min. Yayi lum da ido ya bude, ya cigaba da kallonta

Chapter 18 of 28