Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nan gaba, ba farin cikin mu bane ace mama ta lalace tabi duniya, tunda gaba dayan mu nan, muna son ta. Kun yafe mata ko Umma? Tace kayi hkr Al- ameen ba xan iya cewa komai ba tukunna, ya abdulqadeer yace, ko mu bamu goyi bayan su Umma suyi afuwa gareta ba, har sai ta sauya zabin da tayi da. Tunda tace ba kai ba, to ka kawo wani dan mutunci tamkar kai, amma ba Dan liti ba. Wanna itace shawarar da muka yanke. Yana rufe baki dadi ya turo kofar ya shigo tare da gaishe-gaishe. Ya dubi al-ameen yace, dr na jiranka. Da mamai ya dube shi, dr. Lawal? Yaushe ya zo? Bai dade ba, muna shirin fitowa, sai gashi shine nace ya xauna xan biyo na gaya maka. Ya mike yayi sallama da su ya bar asibitin. Bai sami mami ba, don itama driver ya wuce da ita lfya. Dr. Lawal na babban falon gidansu, ladi sun adana shi da kayan kusa da baka, amma da ka dube shu kasan baya cikin sukuni. Yana shigowa ya mike da sauri ya tarbe shi suka kama juna. Dr. Lafai! Yace banyi xanton xaka xo ba. Dole na xo, wannnan mummanan labari ya hanani barci jiya. Yayi dan yake, kai dai bari, mu xauna aboki na. Suka zauna kujera daya, dr lawal yace, me yayi zafi likita? Idanuwansa suka kada yace, bansan me ke faruwa ba dr sama da sati 4 ina can na daina jin wayar sakeena, aka ce min bata da lfya ne, dalilin da yasa na dawo kenan don hankalina yaki kwanciya ita kawai nake son gani. Ina xuwa na iske labari ya sha bambam, wai sakeena ta sami wani ya hure mata kunne, har ta mance da manyan alkawuran da ta daukat min. Kowa yayi iya kokarinsa wajen nuna mata gaskiyya, amma sam tace ba san wannan ba. Abban ta kuwa ya sha alwashin ni da ta fara kawowa akayi mana baiko, ya sani ba xai daura mata aure da kowa ba, face ni don haka yace ba xan koma sai an daura auran. So da kaunar da nakewa sakeena yasa bana tunanin komai Illa xumudin a daura mana auran, shi yasa koda naje jiya bana nuna maka komai ba.a xato na bai kamata in tona kwanne sirri na sakeena ba, do kar a zage ta matsayin maci amana, ina ganin kamar idan muka kebe matsayin miji da mata, xan iya rinjayar ta. Son da take take min ya sake dawowa xuciyarta. Ashe duk abin da nake zato ya wuce nan dr.lawal kawai na dawo jiyan su dady ke gaya min sakeena ta gudu cikin dare ba a san inda take ba. Al-ameen ya jingina da kujera ya runtse ido sai hawaye shar... Na malala, hankalin dr. Lawal ya kara tashim ya xura masa ido jim sannan ya sauke numfashi ya dafa shi, yace, kana cikin tashin hankali aboki na amma Allah yace duk inda tsanani yakem to tabbas da akwai sauki. Pls ka zama jarumi a cikin jarabawar nan, ka bari hkr ya xama sanadin samun saukin tashin hankalin nan. Ya bude ido taf da kwalla, yace inason sakeena Dr. Kai kasan hakan, yace kwarai da na sani kuma xato na itama tana tsananin sonka. Ya matso shi sosai yace haka ne, wlh sakeena tana sona, to me yasa ta kini tym 1? Yace mata kenan Dr. Lafai. Balle sakeenna na da kyau da xata iya wasa da hankalin kowane da namiji. Watakila kuma wancan yafi ka duk abubuwan da take bukta. Dan wani minister ne a abja? Yace ban nemi sani ba, a yau ne nake jin sunansa bakin yaanta wai shi Danliti, danliti? Daga jin sunan kasan ba wani bane. Da sauri ya amsa ai kuwa wani ne.... (Hahaha Allah sarki lazy Dr.) tunda ya sace min sakeena. Ko da kuwa kwara masai yake yi. Inda ace xan gan shi xan iya durkuwa gwiuwa 2 in roke shi, ya bar min sakeena ta. Wlh itace rayuwata dr. Ya kada kai yace, ka daina fadar haka Dr. Lafao kar fa ka mance wani hani ga Allah baiwa ne, xa iya kasancewa sakeena kyan dan miciji gareta.... Ya dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu.... Yace gaya min kowace kalma dr. Amma kar ka aibata min sakeena, ba xan taba ganin farinka ba. Ya xura masa ido, kunshe da mamaki, kafin yace, ba nufi nake nan ba aboki na, ina so ka gane cewar bakomai da kake bane yake kasancewa alkhairi a gareka, shi ya sa kullum ake son bawa ya roki alkhairi wajen Allah. Yace sakeen alkhairi ce gareni, tuni mafarkai na suke nuna min hakan, har xuwa yanxun kuma jiki na yana bani sakeena tawa ce, mishkila aka samu wani wurin, bana so musu da su Dady ne kawai, shi ya sa nake nuna musu na hkr da ita. Yace to idan baka hkr ba, yaya xakayi yi? Tunda batayi da kai? Babu abinda [12/01 18:24] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 2***10 Amma nan da iya shkrun da xanyia duniya ba xan daina son ta ba har na koma Ubangiji. Ya xura masa ido, yace Al-ameen kar ka manta akwai gagaruminn aiki gabanka wanda kowa ya xura ido don ganin rawar da xaka taka, kasancewar kai kadai ake tunanin xaka iya taka ta kuma mutanenan arewa suna jiran daya tamakar dubu ya dawo masu da abin alafahrin a duniya baki daya. Ina ka sami nutsiwa ka fuskanci abinda ke gabanka ka tare da jadda imani a cikin ranka, lallai Allah xai iya baka wata. Ina fatan xuwa na ba xai xama abnxa ba ba, kuma addu'ar duk masoyanka a zariya ba zata fadi kasa banxa ba. Kowa yace Allah ya musanya maka da lakhairi, na tabbata Allah xai duba ya kawo sauyi na fadi daidai? Ya numfasa yace ka fadi daidai abokina na, na gode ma kowa bisa addu'ar da suka yi min. Xan koma rasha da yardar Allah cikin yardarsa xan dage na fidda kowa kunya. Sai dai abinda nake so ka sani har in mutu ina son sakeena. Yace tuni na sani, sannan ina da ilimin xuciya daya gareka, duk abinda Allah ya xuba cikin ta, babu me iya dauke shi. Ya koma ya jingina da kujrea, rungume da hannayensa, ya dan numfasa ya kada kai, dr. Lawal ya bubbuga kafadarsa ya sake fadin, ka manta kawai abokina, ya wuce, ya bishi da kallo kawai baice komai ba su dade tare. Dr. Lawal na kara kwantar masa da hanakili tare da nuna masa mahimmancinsa ga al-aumma. Bayan azahar suke asibiti ya gaida Umma, daga can ya wuce zariya, shi kuwa Al-ameen gida ya dawo, don shima ba ya son yana ganin Umma kwance tausayinta yana kara karya masa xuciya. Ya rinka jin kamar su abba ba xa su yafe wa sakeena ba. Wannan shine babban tashin hankalin sa. La'asar ta kawo jiki yana xaune shi kadai bisa gadonsa, tym-tym ya kan dauki hoton da ke bisa kirjinsa ya duba. Hotonsu ne shi da mama wanda sukayi a dakin Mami, xuwan ta farko gidan. Karo barkatai kenan daya daga hoton ya xura masa ido tsawon lokaci, sannan ya mike ya sake kife shi. Ya laluba aljihunsa ya dauko xoben da Mama da dawo masa dashi, ya xare na hannunsa ya hada su waje daya, ya xura masa ido. Sannan ahankali yake wasa da su, ya rike kowanne yana hada su karo. Cikin idanuwansa yake ganin ita ke rike da wanda ya bata, suke karawa juna. Wannan karon da karfinsa ya kara mata, na hannunta ya karye nan da nan ta shagwabe, gaskiya ba hake ake yi ba! Ba haka ake ba Dr. Al- ameen! Al-ameen tsananin kiran ya dawo da shi tunaninsa duniya. A firgice ya dubi Mami dake gabansa xaune. Ba xai iya cewa ga tym da ta shigo ba, don haka yake mata kallon mamaki, haka itama ta xura masa ido mai dauke da questions. Mami! Yaushe kika dawo? Ta sauke numfashi ta kada kai, kafin tace, tsoron na Allah tsorona kar ka xaunce al-ameen ka dawo cikin hankalinka mana! Yai sauri ya runtse ido yana fadin Hasbunnallu wa ni Imal wakil, Allahuma ajirni fi musibati wa akhlifini khairan minha. Ya bnude ido jajur ya dubeta, kiyi hrk mami.... Takatshe shi ba xan bari rayuwar ka ta salwanta ba Al-ameen sai inda karfi na ya kare, Allah na gani yarinyar nan ta xalunce ni. Kafin yace wani abu, ta mike da sauri tai waje, ya bita yana kira, ba su hadu ba sai a dakinta... Mami.... Ta daga masa hannu. Ban son jin komai, ta mika masa wani ruwa da ke hannunta tace shnaye shi ka bani kofi. Yace na menen? Ban son tambaya ni na umarce ka kashanye, ka bani kofin. Ya daga kofin da sunan Allah, ya kafa aabki ya kwankwade. Ta karbi kofin ta aje gefe. Ya sake tambaya mami ruwan me nasha? Tace baba liman ya bani taimako na kawo maka, anjima zaka sake sha, gobe ka kara da safe da yamma. Jibi in Allah ya kaimu lfya za ka koma sch, domin fitar da dadin ka yayi bookin ya je maka, ina fatan kajini? Jikinsa yai sanyi, ya kamo hannnayenta 2 ya ja suka xauna bisa kujera yace Allah sarki mamina. Allah bar min ke. Nagode da karfafa min gwiuwar da kukeyi. Idanuwanta taf da hawaye tace, hankalina bai taba tashi ba irin na yau. Ban taba jin faduwar gaba ba irin ta yaukai da zobuna kake hira kana dariya, Al- ameen ban same xai faru ba nan gaba. Kafadunta 2 ya dafa yace sai alkhairi mamina, kawai xancen xuci ne ya fito fili mami... Tace daga haka sai tabin hakali al-ameen , yayi dan murmushi yace Allah ba xai sa ba mamina, ya san ni kadai ya baki, kuma shi mai tsananin tausayi ne. Allah sa ruwan da kika bani ba wanda xai cire min son sakeena bane. Ta xura masa ido cikin xafi tace, shine Al-ameen Insha Allahu sakeena ba xata zama ajalinka ba, ya numfasa yana murmushi da bai kai ciki ba mami kenan, wa ya gaya miki sakeena xata kashe miki tilon danki? Kuma wa ya gaya miki danki xai ji dadin rayuwa ba tare da soayyar sakeena ciknin xuciyarsa ba? Duka 2 tafiya suke kafada da kafada mami, Allah yayi hukuncinsa, don haka ban ji Baba liman xai iya cirewa. Bayin kaina bane, kiyi hkr mami. Tayi masa xuru duk jikinta ya mutu a hankali ta ce ko bai fita ba xaka ji sanyi cikin ranka. Tunaninn ka xai daidaitu da aikin kwakwalwar ka ta yadda xaka yi mu'amula kamar sauran mutane. Wannan shine farinciknm. Yace, Allah ya taimake ku akan burin ku. Nima ya taimakeni akan nawa..... Tace xamu ci gaba dayi da fada idan har kana gaya min irin wadannan kalaman. Ya kada kai ba xa muyi ba mami. To ka daina. Ya lumshe ido, ya bude yace na daina, Allah yayi maka albarka. Ya dora kansa kafadarta ya amsa da amin. Ta ciga da yi ma nasiha yana sauraronta sai dai can kasar xuciyarsa cike yake da xulumi, Allah ya sa ruwan da mami ta ba shi ya sha ba wanda xai sa ya mance da sakeena bane. Da wannan xulumin ya tafi yin sallah la'asar hankalinsa bai kwanta ba, sai da ya tura yatsansa ya arce makogwaronsa ya kirkiro wa kansa aman dole. Bayan sallar magriba dady ya shigo ya tsare shi yaci abinci. Sannan mami ta debo ruwan addu'arta ta mika masa, ya shanye. Allah Allah yake yi tashi ya koma dakinsa ya jawo aman, amma kmar dady ya sano ya ki barinsa tashi. Yayi ta jansa da hirarrakin duniya, wai don ya rage tunanu. Kafin ya bar wajen ya kwashe awoyi sama da 2 takaice ya ishe shi, don ya tabbata ruwn nan ya gama bin jininsa. Wannan karon bai nemi yin aman ba, gado ya fada ya fara tunanin iska, har bacci ya samuyi, da alama an fara samun nasara. Shi kansa yayi mamakin irin barcin da yayi bugu da kari ya rage jin xugin xuciyarsa ke y, hankali kwance suka yi karin safe. Mami ta kara bulbuo ruwan addu'ar ta a gora, ta mika masa. Ya kwankwada duk ba a son ransa yake sha ba, a yau takardun komawarsa Rasha xasu kammalu, haka dady ya gaya masa. Saboda haka ya umarce shi daya kasance cikin shiri koda yaushe xa'a iya basu tym din tashi. Jikinsa babu kasala ya koma bangarensa ya jwo jakar kayansa yayi ta lda kaya har da wadanda ya dade bai anfani da su ba. Ya wuce dirowar madubinsa ya jawo ya kashe takardun cikin kaf, dinsu ya dauko xai xuba jaka, wata ambula ta fado duk hotuna ciki suka watse bisa kafet daidadi shigowar mami dakin. Ya aje takardun gefen gadon yana amsa sallamarta, sannan ya tsugunna ya kwashe hotunan, akasarinsa duk na mama ne, sai kalilan wanda suke tare. Tayi tsye tana kallon katuwar jakar da yake lodawa kaya, ya akayi mami na? Tace kamar bada jakar nan ka xo ba? Ya mike dauke da hotunan a hannunsa yana amsawa, xan kara wasu kayan ne, shi yasa na sauya jaka. Ya matsya xai cusa hotunan, tayi wuf ta karbe ina xaka da dasu? Ai wadannan hotunan wuta ya kamata ka cinna musu. Wuta mami? Me ya san xan sa wa sakeena wuta? Saboda nan gaba xata xama matar wani, ka ga haramun ne gareka kallon hotonta. Ina fatan ka gamsu? Yayi shiru na 'yan dakikai kafin ya numfsa, ya dubeta idanuwan har sun kada, yace kin fadi gaskiyya mami, amma baxan iya cinna wa jikin sakeena wuta ba, sai dai ina rokonki dan girman Allah ki adana min su har xuwa tym din da xata halasta gareni. Tayi masa xuru tana shakku cikin ranta, addu'ar Baba liman batayi tasiri bane ko kuwa bata fara aiki bane tkunna? Ta kada kai ta dubi hotunan ta sake dubansa, amma shi ya riga ta magana. Mami pls ki ajeye min su inda ba xa su salwanta ba. Ta sauke numfashi, xan boye maka sun tunda kafi son hakan, gwaggo ce ta xo tana daki na. Ya ware ido sosai. Gwaggo? Da sasssafen nan? Dole tayo sammako, hankalinta a tashe yake, ka fito tana daki.Tayi waje da ambulan din a hannunta, shima ya biyo bayanta. Tana xaune a shimfida bisa kafet ya xube gabannta dauke da murmushi, uwargida ran fida, kuma sai ki bugo min sammako kamar ban aika da cefane ba? Duban tausayi take masa, ta dafa kafadarsa tace dole nai sammako, in xo in ga halin da kake ciki. Ina fatan xaka sanya dangana cikin ranka. Ka mance da yarinyar nan, domin dai.... Ya katse ta, ya kamata mu gaisa gwaggo kinxo lfya? Ya tsufa? Tace tsufa na nan kuma lfya lau na xo. Amma me yasa ka katse min magana? Babu komai gani nayi bamu ko gaisa ba, alhalin ya dace na fara gaisheki. Haka ne to ina fatan duk shawarwarin da kowa ke ba, kana ji ka kuma dauka? Ka manta sakeena... Da sauri ya katse gwaggo tuni na hkr da ita, hasalima yau ko geb xan koma sch. Ban xan dalilin katseni ba Al- ameen akwai abinda baka so na fadi. Mami ta amshe, sosai kuwa kina so ya mance da sakeena, kunnunwansa ba sa son ji, shi yasa yake katseki. Tace oho, to wahalar banxa kakeyi, domin dai labari ya tabbata tare da shashashan saurayinta suka tafi, kaga kuwa sai abinda Allah yayi. Gara ka kama kanka ka san inda ke maka ciwo. 'yan mata dai ga su nan birjik duk wacce kace kule xata ce cas. Rayuwa kawai sakeena ta xaba, don na tabbata yaron nan baxai aureta ba, nawa ya lalata, ya watsar tana gani kuma ta bishi, inm banda ita ma, rayuwarka ta sha banban da wacce sakeena ta dauka, kaga kuwa tafiyarka ba xata xama daidai da tata ba. Ka fahimce ni? Wasu kwalla masu xafi suka sauka bisa kuncinsa, hakan ya jawo mamaki ga gwaggo da Mami suka xuba masa ido baki sake. Xugum sukayi, daga bisani mami ta numfasa tace ikon Allah! Gwaggo ta xare tagumi tace, akwai sauran aiki, kuma ina mai tabbatar maka , bata tym dinka kakeyi. Ya jawo hankaci ya share fuska, yace, ko kadan gwaggo, labarin ki tsananin tausayin sakeena ya cusa min, sakeena ba haka take ba, nayi rayuwa da ita sosai na fahimci halayenta, xan iya cewa nafi kowa saninta, na fahimci halinta. ,Zan iya cewa nafi kowa sanin ta hakika ya zalunce ta tunda ya sauyamata rayuwa ya bata tarbiyarta ya gurbata mu'amalarta da iyayenta da yan uwanta ya datse tasananin soyayyar dake tsakaninmu ka ALLAH bazai kyale shi ba ta ko wace hanya ya bi yayi nasa a kanta sai ya ga sakayya,"ya mike da sauri zai bar dakin gwaggo ta kwala masa kira ya tsaya bakin kofa yana goge kwalla tace dawo ka zauna ai ban gama magana da kai ba yana daga tsaye gaskiya gwaggo kunnuwa na ba za Su iya sauraron irin wadannan labarurrukan akan sakeena ba,tausayin ta bazai barni sukuni ba gara a bar ni cikin bakin duhu ina laluben inda ALLAH zai sake hada fuskokin mu har ta zama mata a gare ni," jikin gwaggo yayi mugun sanyi tace dawo zauna nan ya dawo ya zauna gefenta ya hade kai da guiwa ta dafa kansa tace idan nayi kuskure kayi min afuwa amma ba laifi na bane ka sani ko wace uwa tana kishin danta kuma abinda ya faru da kai dole mai kaunarka yayi bakin ciki balle mu da muka fi kowa kusa da kai, na san kana son sakeena sai dai ba na son idon ka ya rufe ka kasa ganin aika aikar da ta aikata a garemu, ya cire kai ya dube ta ni kuwa hakan na fi so gwaggo domin na yi imanin ba yin kanta bane sace min ita akayi hure mata kunne akayi da kalmomin shaidan addu'a zatayi maganin abin, da zaki taimake ni da ita ma zan fi farin ciki akan wadannan labaran da ki ke son bani," gwaggo " mami ta karbe za a yi maka in dai addu'a ce ka samu tashi kaje kaci gaba da shirinka bai tofa komai ba ya yunkura ya bar dakin,kamar daman can ya kosa ya barshi,"gwaggo ta dubi mami hankali tashe tace bai kamata ku kyale yaron nan ya koma haka kawai ba tare da wani taimako ba tace tun jiya na je lafai na samo masa wajan baba liman wai nan yama sha ruwan addu'ar ke nan tafdijan ki na kallo fa ko laifinta baya son a fadi wannan so yayi yawa gara ma da auran bai yuwu ba da muna kallo zai zama mijin ta ce,abin haushi nama na jan kare, mami tace me ki ka gani gwaggo?ALLAH dai ya zaba alkairi abin cewa ke nan anan gwaggo ta wuni, Shi kuwa Alameen a dakinsa ya wuni don baya son ana daga masa hankali da labaran sakkena kazantar da baka gani ba tsafta ce,kai a yadda yake jin mama cikin ransa koda ya ga kazantar da idanuwansa zuciyarsa ba za ta amince masa ba bai fito ba sai da gwaggo zata koma suka yi sallama daga nan dakin iya ya shige ya kudundune kamar maraya sama da awa guda tana tausar zuciyar sa da kalamai masu dadi,ya kuwa ji dadin cikin ransa saboda kalaman iya sunfi rinjaye ga. Bashi tabbacin idan sakeena matarsa ce duk rintsi duk wuya sai ya aure ta karfe shidda dai dai dady ya dawo masa da takardun tafiyarsa sun kammalu kuma gobe da yardar ALLAH sha biyu ranan zasu tashi don haka yana gama cin abincin dare mami ta ba shi ruwan addu'a ya kwankwada kai tsaye asibiti ya wuce don yin sallama dasu abba,kowa yayi masa nasiha kuma sun jaddada masa ya maida hankalinsa akan anibda ya kaishi kar ya tsaya bata lokacinsa. Akan tunanin iska wanda ba zai fisheshi ba,sai dai abin yana basu mamaki yadda lafuzzan alameen ke nuni da tsantsan son mama a zuciyarsa. Wanda ko alama na bayyana har yanzu bai yarda sakeena. Taci amanarsa ba, akwai mishkila wani wuri shiyasa yake ta rokansu dasu taya shi addu'a ALLAH yasa wata rana sakeena ra zama mata a gare shi,gaba daya ya kwabe masu guiwa har suka yi masa alkawarin yin yafiya a gareta idan har ta dawo ta nemi gafara,kowa ya dubi alameen sai ya ji tarin kwalla cikin iadanuwansa lokacin da yake barin asibitin yana gugar fuska shi kansa yaya soja a yau zuciyarsa ta karaya,tausayi ya kwarara cikin jikinsa ya nemi haddasa masa abin mamaki domin kwalla ya ji tam da idanuwansa suna zubowa da saurinsa ya bar wajan bai gama ganin wucewar alameen ba [12/01 18:24] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 2*** 11 Karfe 8am suka dauki hanyar abj tare da mami. Hankalinsu bai gama tashi ba, sai da tym ya cika aka kira passengers. Al-ameen ya rungume su, idanuwan sa cike da hawaye, bakinsa na son yin magana amma kasa, haka su ma Allah ya doro masu nauyin baki, kallon juna sukeyi. Da sauri ya juya ya wuce, yana goge fuska da hankici. Shi yasa suke tafe cikin mota kowa shiru. Mami dauke da taguminta. Tunaninta yay rayuwar dan nata xata kasance a kasar da babu wanda ya damu da wani balle ya sami wata kulawa ta musamman. Dadi yayi tana share hawaye ya dan dube ta, kada kai. Amma bai iya cewa komai ba don ya san mami tana mukatar zubda hawaye ko ta ji dadi cikin ranta, amma da ya ga abin yaki karewa, dole ya tanka, ina ganin bai dace ki ci gaba da bata ranki ba, wanda kika yi ai ya isa, ko sai ya jefa ki wani hali ni in rasa da wanda xanji? Ta goge kwalla, tace Alh. Ba haka bane ganin Al-ameen na da abin fadi, amma yakasa ya wuce da damuwar cikin ransa? Wa zai gaya mawa a can? Kai tsaye ya bata amsa, Allah zai gaya mawa, kin kuwa san ya fini, ya fiki, yafi duk wanda kike tunani zai ba Al-ameen wanni taimako, saboda haka ki bar shi da buwayin sarki, shine xai masa dukkan gudunmawa. Ta zare tagumi ta numfasa, haka ne, Allah ya taimake shi, to amin kuma na tabbatar zai taimakeni shin, tunda kika furta, addu'ar uwar yankan wuka ne, don haka ki kwantar da hankalinki. Ina fatan kin ji ni. Tace, naji alh. Allah ya shige mana gaba, yace amin. Daga nan Mami ta saki jikinta suka ci gaba da hira. Suna shigowa gari, asibiti suka wuce gano jikin Umma. Alhmdlh, Umma na samun sauki, watakila ma xuwa gobe a sallameta. Ba su iske yaya abdulkadeer da Abdul- rahman ba, duk sun koma a wannan yammacin. Sun dan jima asibitin, sannan suka dawo gida. Mami ta dukufa rokon Allah cikin sallolinta, Allah ya sanyaya wa Al-ameen xuciyarsa, ya cire masa wannan makahon so sa ya ke wa Mama. Haka ta kwana tunaninsa har barci tayi mafarkinsa xaune yana wasa da xobunan guda 2. Shiyasa da ta fara tayi ta da na sanin da ta raba shi da zobunan kafin ya tafi. Suna karin safe karfe 8:30, waya ta dauki kuka, mami ta baro tebur ta zo duka tayi sallama. Muryar dan lelenta taji ya amsa. Farin ciki ya lallube ta tace, Allah sarki Dr. An sauka lfya? Yace lfya lau Mami, ina dadina? Ga shi nan, ya taso ya ji kaini, ina fatan ba matsala? Babu mami, na ma iske time table din jarabawar mu ya fito, karatu kawai xa mu fuskanta, ni da abokan karatuna. Dadi ya tsaya wajen tana fadin, kai naji dadi sosai, to Allah ya baku sa'a baki daya. Ga dadinka. Ya ce, to nagode Mami. Dadi ya amsa suka gaisa. Dady time table ya fito a taya mu addu'a. Yace kullum a cikinta muke, amma xa mu kara kaimi. Ubangiji Allah ya taimako. Yace amin. To xan wuce cikin sch, sai kun sake jina. Yace, yayi kyau, all d bst! Cike da fara'a ya amsa. Nagode Dadina. Ya aje waya ya dubi mami yace hankalinki ya kwanta? Bakinta har kunne ta amsa. Kai bari Allah ya kara masa hkr. Yace amin, muje muci abinci ko? Suka koma tebur. Mami tace abinci hankalinta kwance. Ba Haka al'amarin yake wajensu Umma ba, domin yau sun koma Fandagori sun iske da kuara da suka bari baya. Hankulansu su kara tashi yadda xance ke ta yamadidi a agari. Zagi iri-iri babi irn wanda ba'ayi ba wasu suna ba iyayen Mama laifi, amma da dama sunfi zargin mama akan rashin hankali da ta aikata. Wani abinda yafi daga wa Ubandawaki hankali shine, wai gaba daya gundarin labarin daga bakin 'yan uwansa da matayensu ya fara fitowa. Bayan gaskiyya ga tarin karya da karairayin da suka yiwa labarin kawanya, don haka ya tara su falon sa bayan sallar isha'i. Wannan shine karo na 2 da na tara ku akan wasu maganganu na batanci da suke fitowa daga gareku. A zatona ku masu rufa min asiri ne ko bayan raina a matsayin ku na 'yan uwana da muka fito ciki daya. Amma bansan abinda nayi muku ba kuke min bita da kulli, ko kuma ince kuke farinciki don wannan abin ya sameni. To abinda nake so ku gane shine, da frko dai bamu mukayi kanmu ba. Allah ne yayi mu, mu kuma shi ya rubuta duk abinda zai faru da mu. Babu wanda yasan kaddarar mu2m bnalle ya share masa mummuna kafin tazo. Da anayi da na gogewa Mama, don na duk fadin duniyar babu wanda zai kaini BAKIN CIKI, sai kuwa mahaifyar ta. Idan kuwa hakane, bai kamata ace ku da matayenku, ku dauki wannan al'amarin ya zamar maku abin hira a gari ba. Kaddara na kowa, idan baku duba kusancin mu ba, ya kamata ku duba wannan. Allah yai sani ban zalunci kowa ba cikin ku ba, haka ban xalunci mama ba, kamar yadda kuke yadawa cewar mu ne muka dage sai mai kudi xata aura, alhalin kun san komai a game da alkawarin auran ta da Al-ameen. Kun fi kowa sanin gaskiyya, amma kuka boye ta, saboda son rai to na bar kowa da Allah, yayi min sakayya, Da yardar Allah BAKIN CIKIN Mama bazai kashe mu ba, haka zalika ina mata fatana shiriyar koda yaushe. Mai surutu da dariya kuma Allah ya bashi sa'ar yi. Amma kar ya mance kaddara bata fatan shiryar kowa! Yana sa aya, ya mike ya bar falon ba tare da wani yayi magana ba, ita ma umma tashi tayi ta bi bayansa, yayi sauran ke mazuran rashin gaskiya. Haj. Gaje ta buga tsaki, ta bar falon. Daga bisani Haj. Hajjo ta lallaba ta sulale, Alh. Basiru ya dubi Alh. Adamu. Yace mutane munafukai ne, wai daga dawowarsa, an sami wani kusugurmin ya feshe shi, don neman fada. Alh. Adam yace, wai me akace? Au ya faru ba za'a maida yadda akayi ba? Me za'a baoye bayan ta gudun kowa kuma ya sani tare da shegen yaron nan suka tafi! Ai ko ba 'a fada ba, amsar a bayyane take. Tace, bata so, ba sai a kyale ta ba, ta auri dan iskan da ake ganin ba shi da asali ba, ba ita zata

Chapter 15 of 28