Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
in koma gida, dama lekowa nayi mu gaisa kisan na dawo. Tabita da kallo, ki na san kin dawo wajenki xano? Menene anfani kawancen mu? Bayan ko na gaya miki gaskiyya bakyaji. Allah ko? To Allah ya bamu alkhairi ki gaida mohd dinki, in yazo. Yaushe xasu kawo gaisuwane? Ko bai shirya aure bane? Wlh ban masa zargin komai ba, amma sonsa bai rufe min ido ba, ina bukatar in gama sanin ko shi waye tunda ba gari daya muke ba. Ta tabe baki, Baraka ke nan, Miss kakale! Ba kakale bane, gaskiyya ce kawai, daga kinta sai bata. Shi ya sa nake nuna mikita, don banson ki bata. Ta mike hannu daya kame da kugu, tace, nagode, ni nayi gida, kar Umma ta neme ni. Tasa kai tafice. Baraka ta biyota, ta sallami Inna ta rako ta iya zaure ta juya. Ta shige gida, tabar mama dauke da mamaki. Tai kwafa tace, kiyi da gwana yarinya. Ta kama hanya ta koma wajen Danliti, wasa-wasa sai da ta bata mini talatin anan, sannan ta karasa gida. Umma na zaune tskar falo ta sha tagumi, ta gaji Mama ta shigo babu ko tsoro ko fargaba tace, sannu da gida Umma. Inna saude na gaisheki. Ta zura mata ido ba tare da cire tagumin ba, jima kafin tace, da izinin wa ki ka bar gidan nan Mama? Ta mimmike kafa sosai akujera. Tace ai kinshifa wanka ne Umma shi yasa banyi miki magana ba. Umma ta numfasa, tayi hucin BAKIN CIKi tace, lallai kin isa mama, duk son danliti ne yasa kika zama maras kunya? To kibi a hankali, duniya zata koya miki hankali, muddin kika dauke ta kika goya. Ta figi gyalenta, ta mike cikin sauri tana fadin, Uhm.....! Ta wuce ta fada dakinta, tayi kwanciyarta. Umma ta kada kai, kwallah suka xubo mata, ta share tace, Allah kana kallo, munyi iya yinmu, amma shiriya na wajenka, kayi mana gaji Ya Allah. Nan Umma taci gaba da zama tana shan BAKIN CIKI tare da takaici mai tarin yawa har aka kira azhar, ta tashi tayi sallah. Abba ya dawo ta labarta masa, hannaye biyi ya kama kai, takaici kamar ya kashe shi, bai niyyara kara yiwa Mama wata magana ba akan Danliti, amma dole tasa ya kira tazo dakinsa ta xauna. Yayi mata kaca-kaca, sannan ya sa mata dokar fita ko'ina, duk da yasan ba dole bane tabi umarninsa. Tabbas hakan ne, yadda Mama ta fito dakin bakin nan nata ya kai wani gari wai shi ZUNTU. Shi kasna ya san rashin kunyta Mama ta kai wani mataki na kololuwa kwatance, ta xauna bakin gadon ta tana fadin a fili, wannan shine bature ke kira Impossible! Tunda kuka hana shi xuwa guna, dole inje gunsa mu ga juna. Ta saki wani lafiyayyen tsaki, ta yada kai bisa filo......... Maganar mama dutse. 7days kenan babu abinda ta fasa, muna iya cewa al'amarin kara haukata yayi. Domin a halin yanxun Mama bata shayi, agaban Umma zata dauki mayafinta, ta fice. Umma na kira, tana fadin tana xuwa yanxu xata dawo. Sau uku Umma na xuwa da kanta kofar shagon Danlinti, tana taso keyarta. Jama'a na kallon su, gwanin ban kunya. Sai da Abba ya hanata xuwa. Yace tasa mata ido, tunda ta zama gagararriya. Wannan abin kunya ya zama abin yayatawa awajen su hajjo, duk inda suka xauna xancan kenan. Babu abinda bai dawowa kunnen Umma ba, sai dai tayi kuka ta share hawayenta ta barwa Allah komai. Mama fa ta gagari kowa, suna ji suna gani mummunan labari na ta yaduwa har gidan Gwaggo Hausi. Daga can labarin ya mika gidan Marafa. Nana take mami ta tsani auran mama da Al-ameen. Shi kuwa Marafa nuna mata yake su daina kama jita-jita. Aure dai nufi ne na Allah, idan sakeena matar Al- ameen ce, bbu makawa xai aureta, idan kuwa ba matar sa bace si barwa Allah yayi masa zabin alkhairi. Duk da haka al'amarin yana jefa Mamai cikin tunani ba kadan ba, kuma da Al-ameen zai ji shawarar ta, da ta umarace shi daya hakura da sakeena, tunda shasahnci tasa gaba. Sallar la'asar ta kammala, amma bata bar sallayar ba, saboda gabatar da lazimi takeyi. Wata tasi tayi fakin kofar gidan, direban ya fito ya bude but, yana fido jakar kaya. Yana rufe but din, idanuwa na suka nuna min Al-ameen a tsaye ya cusa hannu gaban riga ya zaro kudi ya mikawa direban, yace, ka rike chanji. Ya sunkuci jakarsa ya wuce. Direba na xuba gdoiya. Ya tura karamin gate ya shiga, bakin mai gida har kunne ya taso da gudu ya amshi jakar yana fadin Maraba da oga! Fuskarsa babu walwala sosai, yace ya kuke? Lafiya lau oga. Ya shige masa da kaya falo. Al-ameen yayi sallama, muryar sa ta dauki hankalin duk wanda ke cikin gidan. Iya ta riga kowa fitowa, wa nakehi kamar dan Iya? Ya nufo ta fuska sake, ni ne iya, surprise ko? Ya dan rungumo tana fadin, ai kaki koya min turancin nan, da yanxun na gane nufinka. Yana murmushi ya rabu da jikinta, ya dubi Ladi, Hajiya Ladi ina fatan kunje kun duba min jikin sakeena ta? Tace muna dai shirin tafiya da hada tsaraba. Ya ce, baku da tsraaba? Gaskiyya kunyi min babban laifi. Tace, mun san hakan amma tuba muke. Ta ya kuke? Ta amsa lfya lau ya hanya? Yace, Alhmdlh. Yana juyo wa sukayi ido hudu da mami tana masa kallon mamaki. Ya nufe ta da sauri ya rungumeta, Mami na! Idanuwanta suka tara kwalla, ta kasa cewa komai har ya dago ya dubeta, yayi dan murmushi. Yace, nayi muku laifi Mami, kuyi min hkr na kasa daurewa ne. Tace nagode Allah da ya kawo ka lfya. Amma banji dadin xuwanka ba Al-ameen. Yace, na tuba Mami, ki duba halin da nake ciki, kiyi min uzuri. Ta dan kada kai. Tace, muje ciki ka sha ruwa ka yi sallah. Suka wuce yana tambayar Dadinda. Tace, xai dawo anjima daga kd. Yana xama Ladi ta shigo masa da ababen sha masu sanyi. Bayan ya jika makoshi, ya dubi Mami yace, ya jikin sakeena? Na daina kiran waya, don kunnuwa na ba za su jure jin mummunan labari ba, koda yaushe. Dalilin da yasa kenan, nace ya xama wajibi in xo inga halin da take ciki da idanuwa na. Dan hutu muka samu na sati daya, shine na yi anfani da wannan damar. Yaya yanayin jikin nata yake? Ta numfasa sosai kafin tace, jikin ta har yanxun a rikice yake, xan so ace Allah ya saka maka hkr, da dangana akan sakeena, domin kwakwalwarta ta jirkita Al-ameen..... Hauka Mami? Kina nufin sakeena ta haukace? Inna- lillahi wa Inna-illaihiri Raji-un! Idanuwansa suka tara kwalla, ba xan iya hkr da ita ba Mami, ko ba zata taba warkewa ba, sai na aureya. Alkawari ne wannan Insha Allahu ba xan karya wa sakeena ba. Tana ina ne yanxu? Ita ma nata idanuwan suka kawo kwalla. Ta ce, tana Fandagori, kuma ni ma xan so hakan Al-ameen, domin duk abinda kake so, nima shi xuciyata take matukat so da kauna. Amma al-amarin ya sauya salo, ka dauki kaddara kayi hkr da ita, hankalina zaifi kwanciya Al-ameen. Da gudu hawayen sa suka wuce bisa kyakkyawar fuskarsa, ya matso ta a hankali, ya dauko hannayenta biyu ya matse, ya dubeta ido cikin ido. Yace, har abada bana fatan in saba umarnin ku mama, amma ina rokon alfarma ki ban izini in cikawa sakeena alkawarin da daukar mata. Zan tafi samun nutsuwa, idan ina kallonta a matsayin mata ta kowane irin yanayin take. Ina rokon ki Mami ki taimaka min. Ya jingina goshinsa bisa kafadar ta, ya matse hawayensa tare da ajiyar zuciya mai karfin gaske. Haka maminsa ke cikin irin wannan yanain. Ta jima shiru tana tunanin zuci, tana son gaya masa gaskiyya, amma bakinta ba xai iya furtawa ba, saboda tausayin dan tilon dan ta. Ta yi ajiyar zuciya. Tace, nayi maka Umarni akan duk abinda yafi xama alkhairi Al-ameen. Mike ka je kayi sallah kaci abinci. Ya dubeta yana share kwalla. Yace, nagode Mami. Ta danyi murmushin dole. Jeka yi sallah. Ya tashi da sauri ya dauki jakarsa, ya fice. Mami ta raka shi da kallo, hannunta a kunci. Ta nunfasa kafin tace, Allah gamu gareka. Yana shiga, bangarensa ya isa ya yar da jakar hannunsa ya xauna gefen gado Ya kama kai hannayensa 2 yana yiwa Allah tasbihi. Jim kdan ya tura hannu aljihunsa, ya xao wallet dinsa ya bude ya xurawa dan karamin hoton Mama ido, nan da nan hwaye suka goce masa, bai ma san tsaninin kukan da yake ba har da shassheka, kamar xuciyarsa zata tsago kirjinsa. Allah da ikonsa, tamkar mami na da masaniya ta taso ta biyo shi dakin, don ganin a wane yanayin yake? Da sauri ta karaso ta zauna kusa ta shi ta rungumo abinta, idanuwan na tara kwalla. Komai ya sami bawa daga Allah ne Al- ameen, bai kamata ka xauna ka rinka kuka ba! Jin muryarta yasa hankalinsa ya dawo jikinsa, sannu-sannu hawayensa ya tsane. Ya dago ido jajur! Ya dubi Mami, yace mami ki amince min inje in dubo sakeena Yanxun. Ta goge masa guntun kwallan dake bisa kuncinsa. Tace, na baka izini Al-ameen, fargaba na kawai dare. Yace, kar ki damu Mami. Allah xai tsare. Shikenan, Ubangiji Allah ya sa ganinka ya xama waraka gareta, hankalin kowa yakwanta. Yace, Ameen Mami. Tace , To kayi sallah Maza-maza, don Allah kar ka zauna dogon tunani. Yanxun xan fito Insha Allahu. Ta mike ta bar dakin. Al-ameen Ya sauke numfashi, shima ya mike ya fada bayi, nan da nan ya watso ruwa ya dauro alwala ya fito. Bayan yayi sallah ya kimtsa, ya fito Mama ta matsa yaci wani abu, amma bai iya zama ba, gaba daya hankalimsa ya koma Fandogari. Sai dai ya sha Mamaki daya ga Mami ta nace dole ya tafi da direbanya, bai yi musu ba. Kai tsaye ya shiga mota direba ya ja shi suka dauki hanya suka bar Mami cike da damuwa tare da tunanin yaya al'amarin zai kasance idan Mama ta juya wa Al-ameen Baya? [12/01 18:24] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 2*** 8 Ba su ido Fandogari ba, sai karfe 8pm, babu bata tym gidan Uban dawaki suka dosa. Ya shige sassan sa tare da sallama. Umma ta amsa ba tare da ankara da mai muryar ba. Sannu Umma. Ta dube shi da kyau, gaban ta yayi mugun faduwa, ta mike tsaye tana fadin, Al- ameen! Saukar yaushe? Yace, yau din nan Umma. Ikon Allah. Sannu da xuwa! Zauna mana, ya zauna yana amsawa. Kafin yace, ina yini Umma? Ta amsa, lfya lau ya karatu? Mun gode Allah, ya jikin sakeena? Tayi dan shiru, kafin tace wani abu. Abba yayi sallama ya shigo, duk suka amsa amsa Abba! Yace, ah! Al-ameen! Saukan yaushe? Yace daxun da la'asar Abba. Ya xauna suka gaisa, sannan ya sake tambayar jikin mama. Abba yace ciwo na nan Al-ameen. Halima kawo masa abinci ya ci, kafin muyi magana. Abba bana jin yunwa, domin na riga na saba da ita, tun tym din na sami labarin tashin hankalin da kuke ciki. Abin daya hana ni jurewa kenan, nace dole in xo inga halin da Mama take ciki. Abba yace, gaskiyya ne. Mama na nan cikin lularar da ta sameta sai dai al'amuran zai ba ka mamaki idan na gaya maka alabari ya sha bambam Al-ameen, nasan an boye maka komai coz of karatunka, amma yanxun dole ka sani, tunda ka zo. Jikinsa ya kara sanyi, yayi xuru yana sauraron abba, al-ameen rayuwa ta sauyawa mama, wanda muke ganin sa tamkar a mafarki, daga ni har 'yan uwanta kaf! Babu wanda ba shi ckin alhinin wannan abu. Balle kuma kai da soyayyah ta hada ka Mama, kuma ita da kanta takwo mana kai cikin gidan nan. Shi yasa nayi rantsuwa, idan mama xata mutu, sai dai ta mutu a dakin ka tunda tun farko ita ta kawo ka. Ashe kuwa babu wani dalili ko uzuuri da xata kawo mana mu saurare ta. Nasan har yanxun kana jina a hagunce ne, baka gane inda na dosa ba. To bari na fito maka a mutum kada ka wahalar da kanka, Magana daya ce, mama ta gano wani kuma idanuwanta sun rufe ta manta cewar tayi xafin farko kuma na karshe a swajena. Ka fahimce ni? Gaba daya kansa ya kunce, daga yadda yayi kuri idanuwan sa kafe yana kallon Abba, suka gane bai fahimci su ba. Saboda haka yace, dole ka shiga rudu fiye da wanda ka shuga a baya, amma ina so ka sani, mu muna tare da kai, ba mu san kowa ba face kai, ba don komai ba sai don tun farko kai tafara kawo mana. Abinda nake son ka gane shi ne, xuwanka ya sanya ni farin ciki. Domin kai kadai nake jira in tabbatar wa Mama cewa lallai ni ba tsohon banxa bane, kuma bana magana 2. Ina mai tabbatar maka ba xaka koma ba sai na daura auranka da sakeena da yardan Allah. Na gama magana ta, ka tashi hankalinka kwance, kashiga wajenta tana nan cikin dakinta. Ya mike ya bar falon. Umma ta dube shi tace, Al-ameen! Murya dishe ya amsa, na'am Umma tace kayi hkr, ka kwantar da hankalinka. Mama bata isa ta xubar mana da mtunci ba. Kai zata aura da yardar Allah, domin da kai ne akayi mata baiko. Tashi ka shiga wajenta ku fahimci juna. Ta mike tabashi guri, don yaji dadin tashi......... Me kunnuwan Al-ameen ke ji yau? Ya runtse ido tamau! Ya girgiza kai wai ko barci yakeyi ne? Abba ya xo masa a mafarki. Ya bude idanuwan ya ware su sosai, tabbas zaune yake cikin falon su Mama. Kenan dagaske ne maganganun da Abba ya gaya masa? Kirjinsa ya soma bugawa ji yake kiris! Yarage ya zare masa rai, saboda wani gagarumin ciwo da yaji cikin xuciyarsa, nan take ya kama shi. Motsin kirki ya kasa yi har Umma ta sake fitowa da nufin dauko wa Abba abincinsa. Ta danyi jim, tana masa kallon tausayi, sannan ta matso tayi kiransa, ya dubeta firgigi idanuwa sun juye jajur! Tace, ka na xaune, baka shiga ba? Tashi ka shiga mana, ka kwantar da hankalinka, komai xai wuce Insha Allah, ya mike a kasale, ya nufi dakin ba tare da yasan me xai je yayi ba. Tana zaune tsakar daki ba ta hade kai da guiwa, tsiyayar hawaye kawai takeyi, domin tana jin duk kalaman da Abba ke fadi. Daf! Da ita ya tsugnna, bai san lokacin da yasa hannu ya dago fuskarta ba. Sukayi wa juna xuru tsawon lokaci kafin yace, kin ganeni sakeena? Al-ameen ne, kin gane ni? Ta kau da kai abinta. Da sauri ya kara juyo da ita, kiyi min magana sakeena ko na sami nutsuwa saboda ke na dawo kasar nan, don na duba jikin ki. Ina can tunani da xulimmi sun addabe ni, idan kin gane ni, ki amsa min, ya jikin ki? Ta watso masa harara, hawaye na kwarara. Tace waya gaya maka banda lfya? Yace, haka kowa ke gaya min tun tym din da na daina jin muryarki a waya, komai nawa ya tsaya sakeena, radadin ciwon daya sameki, ya hanani sukuni. Ina fatan gani na ya zama sanadin samun saukin ki. Ta goge kwalla. Tace duk wanda ya gaya maka banda lfya, ya maka karya, kalau nake, gani kuma kana kallo na xaune, sai dai na tabbata dawowar ka zata iya zame min cuta! Ya kara xura mata ido , kina nufin abinda Abba ya gaya min yanxun gaskiyya ne? Tace ka daina kokwanto. Ya langwabe kai gwanin ban tausayi. Yace dole nai kokwanto sakeena, don nasan akwai alkawarin a tsakanin mu, kuma bana tunanin zaki yaudare ni, wannan ya tabbatar min da tsantsan son da kike min. Ban taba kallonki da xuciya 2 ba sakeena. Shiyasa har halin yanxun da nake magana dake ban yarda kin karya alkawarin mu ba. Ta kalle shi a dage, ta watsar tace, ya kamata ka amince, tunda gashi da bakina ina gaya maka, tsutsun soyayyarka yayi fiffike yayi dogon tashi. Ya dafe kirjinsa a natse idanuwansa tam! Da wahaye, yace, bai tashi ba sakeena, nayi rantsuwa kina so na. Akwai miskhila dai a wani wuri, ki gaya min laifin da nayi miki. Wlh da kaina xan hukunta kaina, koda da jinin jikina ne xuba, idan har zai zama fansar tarin laifin da nayi miki. Gaya min da sauri inji. Ta ya mutsa fuska, hawayen ta ya bushe tace, Al-ameen ka farka daga barcin da kakeyi ka saurareni, ni sakeena na gaya maka a da naso ka, amma yanxun ban son ka, ba kuma zan aure ka ba, idan sama da kasa za su hade! Kaji ni ko? Sai na maimaita? Ya matse ido, kwalla masu zafi suka yo waje da gudu, ya dan kada kai murya shke yace, kin xuba min dafi, kin xuba min dafi sakeena. Baki tunanin amana? Yasa hannu ya kamo yatsunta, ya kura wa zobensa ido, ya ciga, baki kallon zoben alkawarin mu? Me yasa kika mance da dimbin kalaman da kika sha gaya min? Wadanda suka jaddada imani na akan son da kike min? Ta kwace yatsunta a hankali ta zare xoben, ta jefa masa, ga tsiyarka nan, idan shi kake kallo a matsayin alkawari, ni ma cire min nawa ka bani. Yaci gaba da kallonta, kafin ya dauko zoben yace, kiyiwa Girman Allah ki maida zoben nan sakeena.... Bazan karba ba! Idan ma ka aje shi, zan jefa shi masai! Kuma nima dole ka ban nawa! Yace sai dai ki kashe ni, sannan ki zare shi, wannan din ma zan ciga da boye shi, har xuwa tym din zaki sami nutsuwa dakin auranmu. Ta kwada masa harara, sannan tayi wani dan murmushi na kaico, ta kauda fuska, y mika hannu ya kamo habarta, ta sa nata da karfi ta doke nasa, kafin tace, karka sake tabani, idan ba haka ba kuma sai na kurma maka ihun dan iska! Ta mike da sauri ta bar wajen, kai tsaye bayi ta shige, ta maida mukulli ta kulle. Yayin da Al-ameen ke cigaba da kiranta. Ya tashi ya tsaya kofar bayin yana fadin, ki fito ki saurare ni sakeena, ya kamata mu fuskanci juna, mu gane inda matsalar mu take. A zatona har duniya ta nade ba zaki taba juya min baya ba! Tana daga ciki ta amsa, bazan fito ba. Daman kasan inda dare yayi maka, yace ki tuna alkawari sakeena, don Allah karki bari ayi min dariya. Idan na rasaki zan iya rasa komai nawa, ki tausaya min sakeena, kar damuwa ta kasheni. Tace, kan ka akeji! Ni na gama magana da kai. Ko za'a kashe ni ba xan sauya ba, dama ka kama gabanka zai fiye maka alkhairi. Ya tsaya jim, shiru goshin sa jingine da kofar ya rasa inda zai tsoma ransa yaji dadi. A hankali ya soma karannto Innalillahi Wa inna ilaihir Rajiu'un. Ya fi 10mins tsaye. Sannan ya juyo da sauri ya fito yana share fuska da hankaci. Kawai arba yayi da su Abba zaune falon. Ya rage sauri ya nufi gunsu ya tsugunna, abba zan koma. Gab dayan su ido suka xuba masa, jim Abba yace, amma dai ba minna zaka nufa ba yanxu ko? Ya dan kada yace, kuma ka kwantar da hankalinka Insha Allahu Mama matar kace. Kar ma ka bata tym din wajen xuwa goben, kai tsaye ka wuce gida, ka gayawa Marafa ina tafe da kaina, muyi magana. Yace to, Abba na barku lfya. Ya mike ya fice suka raka shi da kallo. Ummma kam bata sami cewa komai ba, saboda tsabar tausayinsa. Yana fitowa Gambo direba ya balle murfin mota ya fito, ya tarbe shi ganin ogansa na ta share fuska, yaya jikin nata? Ya dube shi ido jajur yace ba sauki Gambo. Mu shiga mota, ka maidani gida. Yace yallabai ai dare yayi sosai, nayi zaton gidan gwaggo xamu kwana. Ya miko hannu yace bani keys, kai ka wuce gidan Gwaggon ka kwana! Ya dan sunkuyar da kai, yace yi hkr yallabai Allah ya sauke mu lfya. Shi tuni ya bude gidan gaba ya fada. Gambo ya xauna mazauninsa da sunan Allah ya murza mukulli yaja suka wuce, a tym din agogon motar yana nuna 09:45pm. A daren nan nake son ganin Dady na. Gambo yace Allah ya yarda mana, ita kuma Allah ya bata lfya. Ya kama kai ya runtse ido, ya jingina sosai da kujera yana fadin amin Gambo. Direba na ta tsula gudu cikin dare. Shi kuwa Al-ameen kurwarsa na can cikin tunanin baya. Itin tsantsan son da Mama ke masa, shi yake gani cikin idanuwansa, har xuwa ranar da ya xo sallama da ita a sch, kawai gambo ji yayi Al-ameen na sambatu, sosai kikace kina sona sakeena, dama yaudara ce? Me yasa sakeena? Me yasa? Hnkalin Gambo ya koma gunsa yayi kiransa sau uku, kafin yaji kiran. Ya xuba masa ido yayi da direba ke fadin, kayi hkr yallabai, yace sakeena ta yaudareni Gambo, ta xuba min dafin da xai wuya na sami maganinsa. Xan iya mutuwa Gambo, domin gaba daya na sallama kaina gareta. Ko kasan inda nake da mishkila ka gaya min in gyara? Gaba daya tausayin sa ya lullube gambo, ya kada kai da sauri, yace babu inda kake da mishkila Yallabai, sai dai ko ajizanci na dan adam. Ni kaina ban yarda sakeena bata sonka ba, watakila ciwo ne rudata yace, kai ma ka yarda bata da lfya ko? Amma kowa yace kalau take, ni nasan sakeena bazata ki ni haka kawai ba, zuciya na wasi-wasi. Gambo yace , kar ka damu Yallabai, Allah zai warware komai, sakeena zata zama matarka. Ya sauke numfashi mai karfi yace, wannan shine babban burina a duniya, komai Allah ya bani na gode masa, saura wannan burin ya rage min. Shima zaka sameshi Insha Allahu. Yayi dan shiru, sannan ya kada kai yace, laifi nane, rashin kasancewa ta kusa da sakeena, shi ya jawo shaidani ya shiga tsakanin mu. Lallai mata na da rauni Gambo, ba taba tunanin sakeena zata iya hango wani har ya rikita ta amince dukkan amanar da muka damka ma juna. Al'amarin na daure min kai, na rasa yadda xan fassara shi. Yace, haka ne yallabai, amma idan ka barwa Allah komi na tabbata xai maka zabin alkhairi. Ka sani ko wata jarabawa ce Ubangiji yake yi ma don ya gwada imanin ka. Kar ka damu Yallabai, Allah ba zai hana ka sakeena ba, idan har kayi imani shine mai hanawa da badawa. Ya sake jingina da kujera, ya runtse ido ka fadi gaskiyya Gambo, na gode. Bai sake tankaea ba haka kuma bai daina tunanin xuci ba, ma'ana sakeena bata daina xuwa cikin idanuwan sa dauke da lallausan murmushinta mai sanyaya masa rai, tana tura hularasa gaban goshi bakinta na fadin, so much! Shi ya sa baya aikin komai face ajiya xuciya. Gambo na jinsa tausayinsa nakara zama cikin ransa. Karfe daya dai-dai na dare motarsu na tsayuwa kofar gate din gidansu. Gambo yayi hon, nan da nan Mai gadi ya shaida hon din motar mami ne, ya taso a guje ya bude kofar, motar ta shige kai tsaye kofar shiga ya tsaya. Al-ameen ya fito, sannan ya wuce ma'ajiya motaci. Tun kafin ya kwankwasa, yaji ana kokarin budewa, don haka ya dakata hannayensa biyu cikin aljihu. Marafa ne da kansa ya bude kofar, suka zuba juna ido, daga bisani ne mami ta bayyana wajen har ta riga marafa magana, Al-ameen . Idanuwansa suka yi tam da kwalla, ta yi azama ta jawo shi ciki, daddynsa ya maida kofar ya rufe. Don me ka iyo daren nan Al-ameen? Sai kace babu inda zaka raba ka kwana! Ya zauna dabas! Ya kama hannaye biyu, Marafa ya xauna kusa shi. Ya rungumo kafadunsa, yace baka kyauta min ba Al-ameen, da ka dauko hanya cikin daren nan dan kuskure kadan za'asamu, shikenan ka ajwo mana tashin hankali, karfa ka manta, kai ke nan guda daya muke kallo zukatan mu na wankewa daga radadin rashin da. Ya dube shi ido jajur! Yayin da Mami itama ta xauna daya gefen suka sanya shi tsakiya. Yace, na kosa in ganka Dady, sakon Abba xan gaya maka, yace gobe yana nan tafe maganar aure na sakeena, kafin in koma yake so a daura shi. Mami tace, kun daidaita da sakeenar ne? Ya dan kada kai yace, sakeena ba warke ba Mami, hasalima bata gane ni ba, shiyasa tun farko nace a kaita asibiti, kowa yaki amincea da ni, ga shi nan kwakwalwarta ta tabu. Sakeena ta kasa ganeni Mami, ni kuma bazan fasa auran ta ba, domin shine babban buri na a duniya. Su abba sun goya min baya, kuma ku taimaka min buri na ya cika don girman Allah. Gaba daya ya kara daga musu hankali babu kamar Marafa da ko alama baya kaunar yaga dansa na kukan neman wani abu, shi yasa nan take ya ji ko ana ba maza ha mata, sai Al-ameen ya auri mama. Amma ita Mami bata an ta dosa ba, don haka tace. Al-ameen bania ron hankalin kanan, na ga alama baka yarda Sakeena lfy lau take ba.... Ku kuka gaya min ai Mami... Yanxun kuma ni na gaya maka lfya, kawai cin amanar ka tayi, tunda kaje bata saurare ka ba, kai ma ka manta da ita kawai, ka roki Allah ya musanya maka da mafi alkahiri. Bafa sakeena kadai ce ta yalwatu da dukkan abubuwan da kake so ba. Saboda haka ka kama kanka, ka nutsu ka gane cewa ko an daura auran, ba zaku zauna lfya ba, tunda idon ta ya bude, tana takamar tana da kyau, kowa na kallonta, kajini? Ya girgiza kai, idonsa xuru yana kallonta, tace au baka ji ni ba? Menene nufinka? Marafa ya amshe don Allah, don Annabi ki kyale shi, ba yace Uban dawaki na taf ba? Allah ya kaimu goben lfya, shi aure ai nufi ne na Allah. Yanun kaje ka kwanta mu saurari goben, kaji? Yace naji dady, don Allah ku tayni da addu'a sakeena kadai nake so. Yace na sani, addua kuwa kullum munayi, kayi alwala ka sami koda raka'a 2 ne kafin ka kwanta, na tabbata zaka sami nutsuwa ok? Ya amsa da kai ya dan bubbuga kafadarsa yace, yau dan Dady, Allah ya bamu alkhairi. Bai dai tanka ba, ya mike ya bar falon. Mami ta cire tagumi tace, sai Allah yayi wa yaron nan sakayya! Yadda tai masa haka Allah zai mata. In banda idon Al-ameen ya rufe a kanta, me zaici da ita? Yarinyar da gwaggo tace shagon saurayi take su raba dare suna.... Marafa ya katse ta, don son Annabi, ki bar wannan magana haba. Ki yi masa fatan alkkhairi kawai. Cikin bacin rai ta mike ta koma daki. BAKIN CIKI kamar ya kasheta. Shi kuwa Al-ameen yana can yana nafilfili kamar yadda dadinsa ya umarce shi. Da safe ya fito gaba daya ya zabge, kallo daya za kai masa ka tabbatar da hakan. Gaban mami ya fadi ta kwala wa Ladi kira ta zo a gigice. Tace, to hajiya. Ta juya da sauri ta fice. Mami ta dube shi tace, matso nan kusa da ni. Ya kara matsowa yace, ina kwana? Ta amsa tana shafar kansa. Ina dadina, bai tashi

Chapter 13 of 28