Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tabbatar karatun ya kama bakinta, sannan ta koma dakinta ta ci gaba da nazari. Hakan ya dan kauda mata damuwar da ta tsinci kanta ciki yau. Shi yas ma taki sassauta wa karatun, don bata son ummanta ta fahmci wani sauyi a game da ita. Sun Sallaci Isha'I sun ci abinci tana like gefen Abbanta Umma ke fadin wann karon kuma ina zaki hutu? Kanta tasye ta bata amsa wajen Ya abdulkareem zani. Baki sake take kallonta wai! Wai! Yau kuma aljanun can suka buga? Tayi yar dariya umma kenan ai dama ba wai bana son zuwa minna bane kawai Anti rabi ce matsalata kayita aiki kamar boyinta. Ta dan harareta uhumn ke kuma malalaciya uwar son jiki ba a haka ake koyo ba? Ta kada kai a'a wllh naje hutu kuma inyi ta aiki ina amfanin hutun ko Abba? Yace kyalle Umman nan kema kike zuwa gunsu kiyi zamanki wajen Abbanki inga me samin ke aiki. Umma tace oho! Shi zaki goya miki baya? Ta ai gidan wani zata aiki kam dole tayi shi ko anan dinma. Yace ok hakane? Kinga kiyi tafiyarki Abj wajen soja. Ta kada kai bari dai in tafi minnar Abba, kasan shima yaya yana ta korafi wai ban zuwa gun sa. Yace amma nasha mamaki..... Name Abba? Son zuwa minar nan koda yake duk yarinta ce take saki zuwa hutun nan da zarar kin fara jami'a ajewa zakiyi, Umma tace likita ba! Dokta Sakeena! Ta langwabe jikin Abbanta tana dariyar dole amma cikin ranta tausayawa junan su takeyi musamman Al-Ameen da kansa yake rawa yana ganin matsalar me sauki ce abin ya kara kashe mata jiki data dubi Abbanta taga yadda muraran fuskarsa ta nuna alfahari da kalaman Umma. Kwance bisa gadonta amma barci yaki yuwuwa dabarar ta taje hutu minna ko Allah yasa su kara ganawa da Al-Ameen koda Uban Dwk ya soke bukatarsa. Shin yaya zatayi ne? Mafita kam babu sai abnd Allah yayi. Ta kuwa kwana gayawa Allah don ya zaba mata abnd yafi alhairi. Ko karatu ko auren Al-Ameen wanda zamu iya kiransa mai sa'a gwarzon da yayi nasarar ciwo zuciyar Mama da yaki har take tunanin dama ace burin Abban ta aure ne bason zama likita ba. Shawara ta zauna kan jibi da yardar Allah zata wuce minna. Sha biyun rana daidai tana shimfide bisa gadonta tare da muguwar kasala, shigowar Uban Dwk gida dawowarsa kenan daga kewayen gonakinsa. Ya daga labulen dakinta tare da fadin yaya dai yar gidan Abba? Ta tashi zaune tana murmushi, babu komai Abbana har ka dawo? Yace na dawo Mamana lfy dai? Naga kamar jikinki a mace yake. Ta amsa Allah ya taimaki mai martaba lfy kalau Mamanka take bacci ne bai isheni ba. Ya karasa shigowa dakin ya tsaya akanta yace ni kuwa banason ki saba da yawan bacci Mamana kin fa san karatun da zakiyi mai wahala ne bayason lalaci ko kin manta ne? Ta dan rausaya kai tana murmushi ban manta ba Abba ko yanzun ma rashin abin yine yasa. Rashin abin yi? To taso muje in dai abin yine ni zan baki shi yanzun nan. Ta fara dariya meye shi Abbana? Yace ki zagaye tsakar gidan nan sau 12, ta kame baki wuuu! Abbba a tsakar ranar nan? Ai sai in zube sumammiya, duk suka dauki dariya yayin da wani matashin yaro yayi sallama sassan yace ana sallama da Alhaji. Umma dake waje ta karaso da sakon. Shi mutum ne me girmama bakinsa don haka bai bata lokaci ba ya fice don ansa sallama, wata zungureriyar marsandi ya fara cin karo da ita a kofar gidan sannan idanuwansa suka kai ga bakinsa maza su 2 a tsaye wanda kallo daya zakai musu ka tabbatar manyan mutane ne. Kai! Guda a cikinsu ma Uban Dwk ya sanshi farin sani kuwa domin fitaccen mutum ne a gwamnatin data shude ambassador ne 10yrs back, watau Alh Saifullahi Sodangi Lafai kuma marafan lafai. Take nan mamaki ya saukarwa Uban Dwk ganin cewa babu abnd ya taba hadasu na mu'amala. Cike da mamaki ya bisu da sallama cikn fara'a suka yi musabaha, sannan ya kira yaronsa Kalla yace maza ya bude masa falon baki. Can suka rankaya da bakin nasa, ya nuna masu kujeru yana fadin "bismilla! Kai sannunku da zuwa!" Sun fara gaisawa kenan kalla yayi sallama ya shigo da gorunan ruwan (Swan) bisa tire da kofuna, ya aje gabansu. Ya sake dibar gaisuwa ya fice ya bar falon. Uban dawaki ya shayar da bakinsa suwan sanyi. Bayan sun natsa Ambasada ya soma da cewa, "watakila ka shaida ni, watakila kuma baka taba sanina ba". Uban dawaki ya cafe, "farin sani kuwa, mai girma marafan lafai". Suka yi 'yar dariya, "babu shakka, to wannan kuma kanina ne uwa daya uba daya, alh. Nuhu lafai". Uban dawaki ya jinjina kai, "tabbas kuwa, ga kama nan, sannunku da zuwa" Suka kara amsawa, sannan alh. Nuhu ya zarce da bayani, "Allah mai yadda yaso, kuma shi yake shirya al'amuransa yadda yaga dama. Watau jiya yaron wajenmu yazo garin nan, domin mahaifiyarsa, ya kuma ga 'yar wajenka wacce ta tabbatar masa cewa ita 'yarka ce. A hakikanin gaskiya dai yaro ya gani yana kuma so da aure, shi yasa yana zuwa ya sanar mana, mu kuma muka ce ai babu bata lokaci dole mu kawo gaisuwa, tare da neman izini. Domin a haln ynzu bamu da wani buri da ya wuce Allah ya nuna mana aurensa, tnda ya kammala karatu har aiki ya samu. Don a gaskiya mun yaba da bayanin da yayi mana, yarinyar ta fito daga babban gida. Ina fatan za'a karbi kokon barar mu? [11/01 12:44] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 1***3 Admin KbShow Uban dawaki yayi jim, shiru yana tunanin me zaice da manyan bakinsa da suka wanko kafa takanas takano suka zo da babban alkhairi gidansa? Girma da kwarjinin Marafa sun cika masu ido, har ya rika ji ckn zuciyarsa bazai iya kabar da kokon bararsu ba. Amma abin tambayar shine, ina burinsa na tuntuni da ya kwallafa akan mama? Tun tana ckn zanin goynta? Muryar ambasada yaji yana fadin, "nasa daliln shirunka alh., Al'ameen yayi min bayanin komai game da burinka na sakeena tayi zurfin karatu. Wannan kuduri ne mai kyau, kuma ni kaina ina sha'awar hakan. To amma ina son in tunasar da kai cewar aure baya hana ilimi. Ina roknka da ka tausayawa halin da al'ameen ya shiga na fadawa tarkon son sakeena. Shi kadai gareni alh, kuma daidai gwargwado soyayyar da na nuna masa bata gurbata tarbiyyarsa ba. Yaro ne mai ladabi da biyayya ga kowa, tare da tsananin bin dukkan abnda muka umarce shi. Dalilin da yasa kenan nima nake tsananin son abnda yake so. Bana sanya wajen taimaka masa da addu'a, a duk lokacn da ya tsinci kansa cikn wata matsala kamar ynda na lura ya shiga wani hali daga jiya zuwa yau da muka baro shi. Babu sukuni a zuciyarsa, alh. Ka taimaka ka amince wa al'ameen auren sakeena da zarar ta kammala sakandare, karatu kuwa ko wane iri ne, ko a ina ne sakeena zata yi shi da yardar Allah" Wannan dogon bayani na marafa ya kwabe wa uban dawaki guiwa, zcyrsa tayi rauni, ba zai iya ja da nufin Allah ba. Ya gyara zama sosai yace, "ba shakka naji duk abnda kuka fadi, kuma nayi farin ciki kwarai da gaske, sbd haka na amsa kiranku, duk da cewar ya kamata in shawarci sauran 'yan uwana, amma babu komai zan yi musu bayana idan muka zauna. Al'ameen ya ci gaba da neman sakeena, Allah ya tabbatar mana da alkhairi" Kawai gani yayi marafa ya daga hannu sama yana fadin, "Alhamdu lillah!" ya maimaita har sau uku, sannan ya dubi uban dawaki, "bansan kalmar da zan fada ba alh......." yayi murmushi, "ai ka fadi alh., tnda kayi godiya ga Allah". Ya jinjina kai, "haka ne, to mun kara godiya gareka Allah, ka nuna mana lokacin" duk suka amsa da amin. Alh. Nuhu ya zarce da fadin, "yanzu dame-dame ake bukata na gaisuwa da baiko?" yace, "kar ku damu da wannan, da zarar mun zauna da 'yan uwana zaku ji bayani insha Allahu". "to babu laifi, muna saurare. Ina sakeenar take? A kira min ita mu gaisa, don in cika alkawarin da na dauko......" "alkawari?" "kwarai kuwa, har mota ya biyoni yana fadin, don Allah daddy in kunje ku isar da gaisuwata ga sakeena, koda mahaifnta bai amince min auranta ba. To kaji, dole in cika wannan alkawari. A kira min ita inga farin cikn al'ameen" Farin ciki ya lullube uban dawaki, bakinsa har kunne ya mike, "Allah sarki, to tana zuwa". Yayi ckn gida da hanzari ya sami Hajiya Halima, "ina mama? Ashe bakin nata ne" tare da mamaki ta tambaya, "bakinta? Kamar yaya?" "zan miki bayani, je kice ta shiryo tsaf ta sameni falon baki". Ya juya ya koma. Ita kuma dakin mama ta wuce, gaban madubi ta sameta zaune tana shafe-shafe, fitowarta kenan daga wanka. Ta matsa gareta tace, "dama kinsan da zuwan wasu baki gunki?" "baki?" ta kada kai, "daga ina umma?" "ni zaki tambaya? To kiyi maza suna falon baki inji abbanki". Ta juya ckn juyayi ta fice. Mama kuwa kasake tayi tana tunani, "baki?" Al'ameen ya fado mata a rai, nan da nan farin ciki ya rufeta, ta mike da gudu ta nufi dirowar kaynta, ta zuba ado ta rufa mayafi, ta fito ta doshi falon baki gabanta na harbawa, amma zuciyarta fara sol! Duk da cewar bata tabbatar da hukuncin da abbanta ya yanke ba. Sai dai tana da yakinin akwai alamun nasara, tnda aka ce taje da gaishe su . Tayi sallama ckn kunya ta shiga, ta sami wuri gefe ta tankwashe kafa, "sannunku da zuwa". Kai bakin marafa da kaninsa kamar gonar auduga, su kansu mama ta girgiza su, sun tabbatar da al'ameen ya darzo, fatan da suke yi Ubangiji yasa kyanta har ckn zuciyarta yake. Cikin ladabi da tsananin kunya ta gaishesu, su kuma suka amsa ckn farin ciki da nuna kauna a zahiri. Marafa ya taso yazo gabanta, ya tsuguna yace, "al'ameen ya zabe ki, nima haka. Sbd haka sai ku rike juna amana. Har Allah ya nuna mana lokacin da muke dakon zuwansa, kin ji?". Ta kara yin kasa da kai, sannan ta amsa da kai. Yace, "madalla, to mun gode". Yasa hannu a aljihu ya zaro sababbin bandir 'yan wazobia ya aje a gabnta, "wannan kyauta ce don nuna farin cikina gare ki, sbd zabar dana ya zama mijinki". Kunya kamar ta nutse, da kyar ta iya fadin, "na gode. Allah ya saka da alkhairi". Yace, "to me zan ce wa al'ameen idan mun koma?". Ta yunkura a guje ta bar falon, suna mata dariya. Shi kansa Uban dawaki yana mamakin kansa, irin farn ckn da ya tsinci kansa. Alh. Saifullahi ya mike, "to bari muyi harama, mun gode kwarai, Allah ya tabbatar mana da alkhairi". Suka yi musabaha, uban dawaki na fadin, "amin". Yayi musu rakiya, sai da yaga tashnsu sannan ya shigo gida. "Saboda Allah mama haka kuka yi da abbanki?" ummanta ke tambaya, ta kada kai, "wlh umma ba laifina bane. Babu abnda ban gaya masa ba, yaki yarda. Kinga wannan turowar ma ni bansan da ita ba, kawai ce min yayi shi yasan ynda zai bullowa al'amarin, don haka in sa masa ido". Tace, "ke din ma kina sonsa ne, ai nasan halinki sarai mama, ba don haka ba ko kallo bai isheki ba. Kin bani mamaki wlh, watau shi yasa jiya kika ce minna zaki hutu, ashe da manufarki....." Abbanta ya cafe, "tabbas haka ne....." ya karaso ciki ya zauna, yana dubanta yaynda gabanta ke ci gaba da harbawa da sauri. "ya aka yi haka mama na? Ki turo min babban mutum irin marafa, bayan kisan zai yi wuya ince a'a ko?". Hankalnta ya kara tashi, ido tam da hawaye tace, "wlh abba ba haka bane, hasali ma ni bansan shine mahaifnsa ba, domin ni bai gaya min ba, ka yarda dani abba, don bani da nufin saba maka. Duk hukuncn da ka yanke akan wannan al'amarin bazan bijire ba". Tasa hannu ta goge kwallan da suka zubo bisa kuncnta. Yace, "matso nan mamana". Da rarrafe ta isa gunsa, ya kamo kafadarta yace, "dubeni nan". Ta dago manyan idanuwnta da suka fara jirkita ta kalle shi, "na yarda da ke dari- bisa-dari mamana, sai dai abnda nake hangowa watakila ke ba zaki hango shi ba. Bayn aure mata sukan fuskanci 'yan matsaloli musamman idan Allah ya kawo rabo ckn gaggawa, wanda idan ba ayi sa'a ba sai ya jawo koma baya ga komai nata, ba ma karatu ba kadai. Amma bazan matsa ba mamana, ya kasance nayi jayayya da shirn Allah, don haka ina muku fatan alkhairi". Ta rufe fuska da tafin hannunta, fuskarta na bayyanar da murmushi. Jiknsa ta langwabe, dadi kamar ya kasheta. Yace, "ho 'yar nema! Watau kice kina son al'ameen ko?". Ta tashi a guje ta bar musu dakin. Uban Dwk ya numfasa sannan ya dubi Umma to ya kika ce? Kinga dai yanda al'amarin ya kasance. Fuska sake tace yaya kuwa za'ayi Alh? Tunda ka amince ai shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, yace Ameen. Baki ma sani ba wai shima likita ne mun fito ina musu rakiya shi baban nasa ke gaya min. Nace itama abnd take son ta karanta din kenan. A hakikanin gsky ya tabbatar min babu damuwa I.S.A zataci gaba da karatunta, kinji inda muka tsaya dasu. Sauran maganar gaisuwa da baiko nace su bari mu zauna da yan'uwana. Ta numfasa gsky ne hakan kuma yayi kyau saidai kana ganin bazasy dora wani abu a zukatansu ba? Kasan fa su Ali sun so ta ka hana kace karatu zatayi. Yayi dan shiru jim, kafin yace kinyi magana amma ba komai nina san bayanin da zanyi musu. Tace shikenan sun dan jima suna maida zancen. Mama kuwa tana dakinta rayuwa ta zame mata sabuwa. Duk. Inda tajefa ido Al- Ameen din take gani kwarjininsa murmushinsa salon maganarsa da taushin murya mai dadi. Bayan sallar la'asar lokaci ne da kannen Uban dwk ke dawowa daga gonakinsu. Yaran nata daukar darasin Muhammadiyya kamar kullum. Uban Dwk ya tara kannensa a falonsa ya zayyane musu komai game da abnd ya faru, nan taje ransu ya sosu ba kadan ba kallon juna suke cikin al'ajabi suna tambayar zukatansu. Ina karatun da akace Mama zatayi? Ya kara gyara zama yace nasan zakuyi wa zukatanku wann tambayoyu a game da magana ta, sbd Aliyu da Sa'aeed dama sauran samarin da suka yo caa akan Mama, suna neman aurenta amma na hana, sbd dalilin zurfin karatunta. Wannan magana wllh haka take cikin zuciyata kuma shine buri na saidai marafan lafai ya cika min ido kwarai da gaske, banjin kuma zaku goyi bayan na bada masa kasa a ido ba, alhalin da kansa yayi tattaki neman alfarmar da bata fi karfina ba. Abnd nakeso in rokeku shine donAllah don son Manzon Allah SAW kuyi min uziri akan wann hukunci dana yanke karku zargi komai sai alkhairi, ina fatan zaku bani hadin kai dari bisa dari. Alh Basiru mahaifin su Aliyu kuma yafi kowa yaya a gidan ya gyara zama yace Alh ai wann al'amari na Allah ne kuma abin alfaharinmu ne ace Mama ta sami cigaba domin cigaba ne samun irin wann hamshakin zuriya ta marafan lafai. Mama yar mu ce kuma muna farin ciki tare da fatan Allah ya tabbatar da wann abu kome kace Adamu? Alh Adamu karamin cikinsu ubansu Sa'eed yace wann magana haka take Alh mu munsan cewa Mama bazata auri kowa ba sai wanda Allah yace shine mijinta sbd haka muna murnar samun wann babban rabo daga Allah. Cikin jin dadi Uban Dwk ke magana "godiya ta tabbata ga Allah da yasa na sami hadin kanku cikin sauki nayi godiya sosai, abu na gaba shine sunyi maganar gaisuwa da baiko nace su dan saurara min muyi shawara da yan'uwana. Me zaku ce akai? Alh Basiru yace hakan shi ma yayi kyau sai ta gama sakandiran ne ko kuwa yanzu suke so? Yace a'a sai ta gama tukunna. Idan haka ne zaifi kyau a bari ta gama din sai ayi baiko a sa rana ko kuwa? Alh Adamu yace haka yayi daidai. Allah ya nuna mana lokacin lfy. Kowa ya amsa da ameen. Uban dwk ya shaida musu kyautar kudin da Marafan yayiwa Mama na tsabar kudi naira dubu hamsin. Aha! Gsky ta bayyana abnd Uban Dwk yake so kenan ruwan kudi. Haka zuciyoyinsu suka saka musu, ya fiddo kudi ya nuna musu kafin yace saidai maganata gsky wann kudi ko sisi bazan taba a cikinsu ba zanci gaba da ajiyarsu cikin banki da dukkan wata kyauta dazata zo daga baya har sai wann abu ya tabbara iidan kuma an sami akasi ba fata muke ba sai a mayar musu kayansu. Ko yaya kuka gani? Sasan alh. Basiru suka tasu da matansu suka kwnce musu abnda ya wakana a falon uban dawaki. H. Hajo matar alh. Basiru ita ta fara tsoma baki, "amma kuwa idan baka mutu ba zaka ga abin mamaki kala-kala. Ynzu da gske alh. Babba ne ya iya tararku da wannan maganar? Ko ya mance abnda yayi a kan su ali ne?" Alh. Adamu yace, "ya manta? Babu abnda ya manta. Hasali ma sai da ya kara maimaita zancn su". "tafdi!" inji h. Gaje, matar alh. Adamu. "kai dai kaga dan-uwa kawai, ai dama tun farko na fada, ba wani karatn da ake so tayi, burnsu mai kudi ko basarake, sbd su ganin mama tafi kowa kyau a duniya. Shi yasa suka dauketa a matsayn wani jari gare su. Ai shikenan, Allah ya bamu lfya. Muma namu 'ya'yan bamu fidda ran Allah zai azurta su ba. Ba Dai kowannensu ya kama aiki ba? To muje zuwa wai mahaukaci ya hau kura. Harda wani za'a tara kudi a banki, don kawai kar ya baku wani abu ne a ciki, shine yake muku 'yan dabaru" "ni dama bance a bani ba, me zanci da su?" inji alh. Basiru. Alh. Adamu yace, "balle kuma ni, ai tuni na haramtawa kaina komai na alh, tnda ya nuna mana kiyayya a fili". Ya tashi yayi waje, alh. Basiru yabi baynsa. Yaynda h. Gaje ke fadin, "sai musa ido mu gani, da wane bakin h. Halima zata gaya mana zancan". H. Hajo tace, "kema dai da son jin baki kike. Tnda mijnta ya furta, ai ba sai ta maimaita ba, tana nan tasa ido muje mata murna 'yarta tayi farin jin". Tayi 'yar shewa, "Allah mai iko, kiri-kiri an raina mana wayau?". H. Hajo ta ja tsaki, "mtsww! Kina mamaki kenan, dama kin daina wlh, domin an jima ana ruwa kasa na shnyewa. Ba girin-girin ba dai, tayi mai. Ba auran gidan kudin ba, kwancyar hnkali!" Tana rufe baki tare da sallamar umma, suka amsa suna wani yatsina suna yarfarwa. Ta zauna tana fadin, "na shiga sasanki yara suka ce kina nan" "uhm! Ina nan" "dama maganar 'yarku ce, ban sani ba ko su alh. Sun gaya muku halin da ake ciki?". H. Hajo tace, "sun gaya mana, yanzu haka ma shirn zuwa sasan naki muke, sai kuma gaki. Ashe kuma mama an fasa karatu aure za'ayi?" Tace, "to yaya zamu yi, mutane sun cikawa alh. ido, sannan da alama ita ma maman tana son yaron. 'ya mace kuwa idan ta nuna tana son aure, to yi mata auran shine mafi alkhairi ga iyaynta". H. Gaje tace, "gaskya kuwa, gidan hutu ai dole a so shi. Ai kinga wadancan da yake ya ku bayi ne bata ce tana so ba". Umma ta dube ta sosai, "me kike nufi gaje?" tace, "me kuwa? Ita gaskya ai daya ce, sannan arziki na Allah ne. Daga ali har sa'eed bamu fidda masu rai ba". Ta tsura mata ido cike da mamaki, kfn tace, "na wuce kiyi min habaici gaje, domin ni ba sa'arki bace. Kasancewar ali da sa'eed 'yan uwa ga mama bai zama dole wani a cknsu ya aureta ba, domin shi aure nufi ne na Allah. Shi ke kullashi, kuma duk fassarar da zaku yi man kun dade ba kuyi ba. Allah yasan zcyrmu akan komai". Ta tashi ta bar sasan. Wata uwar shewa suka kwasa hannu bibiyu suka tafa, "tabarmar kunya....," inji h. Gaje, "da hauka ake nade ta!" h. Hajo ta bata amsa.! [11/01 12:44] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 1***4 Sasan alh. Basiru suka tasu da matansu suka kwnce musu abnda ya wakana a falon uban dawaki. H. Hajo matar alh. Basiru ita ta fara tsoma baki, "amma kuwa idan baka mutu ba zaka ga abin mamaki kala-kala. Ynzu da gske alh. Babba ne ya iya tararku da wannan maganar? Ko ya mance abnda yayi a kan su ali ne?" Alh. Adamu yace, "ya manta? Babu abnda ya manta. Hasali ma sai da ya kara maimaita zancn su". "tafdi!" inji h. Gaje, matar alh. Adamu. "kai dai kaga dan-uwa kawai, ai dama tun farko na fada, ba wani karatn da ake so tayi, burnsu mai kudi ko basarake, sbd su ganin mama tafi kowa kyau a duniya. Shi yasa suka dauketa a matsayn wani jari gare su. Ai shikenan, Allah ya bamu lfya. Muma namu 'ya'yan bamu fidda ran Allah zai azurta su ba. Ba Dai kowannensu ya kama aiki ba? To muje zuwa wai mahaukaci ya hau kura. Harda wani za'a tara kudi a banki, don kawai kar ya baku wani abu ne a ciki, shine yake muku 'yan dabaru" "ni dama bance a bani ba, me zanci da su?" inji alh. Basiru. Alh. Adamu yace, "balle kuma ni, ai tuni na haramtawa kaina komai na alh, tnda ya nuna mana kiyayya a fili". Ya tashi yayi waje, alh. Basiru yabi baynsa. Yaynda h. Gaje ke fadin, "sai musa ido mu gani, da wane bakin h. Halima zata gaya mana zancan". H. Hajo tace, "kema dai da son jin baki kike. Tnda mijnta ya furta, ai ba sai ta maimaita ba, tana nan tasa ido muje mata murna 'yarta tayi farin jin". Tayi 'yar shewa, "Allah mai iko, kiri-kiri an raina mana wayau?". H. Hajo ta ja tsaki, "mtsww! Kina mamaki kenan, dama kin daina wlh, domin an jima ana ruwa kasa na shnyewa. Ba girin-girin ba dai, tayi mai. Ba auran gidan kudin ba, kwancyar hnkali!" Tana rufe baki tare da sallamar umma, suka amsa suna wani yatsina suna yarfarwa. Ta zauna tana fadin, "na shiga sasanki yara suka ce kina nan" "uhm! Ina nan" "dama maganar 'yarku ce, ban sani ba ko su alh. Sun gaya muku halin da ake ciki?". H. Hajo tace, "sun gaya mana, yanzu haka ma shirn zuwa sasan naki muke, sai kuma gaki. Ashe kuma mama an fasa karatu aure za'ayi?" Tace, "to yaya zamu yi, mutane sun cikawa alh. ido, sannan da alama ita ma maman tana son yaron. 'ya mace kuwa idan ta nuna tana son aure, to yi mata auran shine mafi alkhairi ga iyaynta". H. Gaje tace, "gaskya kuwa, gidan hutu ai dole a so shi. Ai kinga wadancan da yake ya ku bayi ne bata ce tana so ba". Umma ta dube ta sosai, "me kike nufi gaje?" tace, "me kuwa? Ita gaskya ai daya ce, sannan arziki na Allah ne. Daga ali har sa'eed bamu fidda masu rai ba". Ta tsura mata ido cike da mamaki, kfn tace, "na wuce kiyi min habaici gaje, domin ni ba sa'arki bace. Kasancewar ali da sa'eed 'yan uwa ga mama bai zama dole wani a cknsu ya aureta ba, domin shi aure nufi ne na Allah. Shi ke kullashi, kuma duk fassarar da zaku yi man kun dade ba kuyi ba. Allah yasan zcyrmu akan komai". Ta tashi ta bar sasan. Wata uwar shewa suka kwasa hannu bibiyu suka tafa, "tabarmar kunya....," inji h. Gaje, "da hauka ake nade ta!" h. Hajo ta bata amsa.! Umma na shiga sasanta ta iske baraka, shigowarta kenan suna murnar ganin juna ita da mama. "a'a baraka ce?" "nice umma, ina yini?" "lfya kalau. Ya babanki da innar taki?" "duk suna lfy. Tace a gaisheki. Wai dinkunan sunyi miki kuwa?" "wle sunyi kyau" Mama ta cafe, "baki ga ta cabawa abba ado ba yau tun safe?". Ta yo mata dakuwa, "gidanku!". Ta wuce suna mata dariya har da tafawa. Janye ta mama tayi ckn daknta, "kamar kinsan ina nemanki kawata" tace, "nima haka kawai naji ina son ganinki, nacewa inna zanzo nan. Har tana min tsiya, wai anyi hutun kenan, bama gajiya da bin hanya". Suka yi 'yar drya, kafn mama tace, "kinsan wani abu?" ta kada kai. "kawai dazu da rana sai ga mahaifn al'ameen........" ta katseta ido waje, "don Allah? Sai aka yi yaya?" tace, "uhm! In gaya miki Abba ya amince! Kimji ynda nake ji yau a duniya?". Ta cika da mamaki, "tafdi! Allah ya saka masa da alkhairi" "ameen ke dai. Ni ynzu al'ameen din nake son gani, idan yaji wannan albishir din. Kinsan Allah, da ni duk na hakura ina 'yar dabara inje hutu minna, idan Abba ya hana ma rika gaisawa a can" Tace, "amma idonki ya rufe, wa ya gaya miki a minna yake da zama?" "nasan a zariya yake, amma dole yaje minna, musamman idan yasan zai ganni a can". "ke mama......" "meye?" "meye kuwa? Allah dai ya nuna mana lokacn lfya". "to ynzu zaki je hutun ko kin fasa?" "Gobe insha Allahu zan tafi, amma dole in dan saurara in ga ko zaizo goben" Tace, "kema kinsan dole gobe ya dauko hanya, wannan babban albishir ina zai tsoma ransa, idan bai zo ya ganki ba?". Suka tafa suna 'yar driya. Har gab da magariba suna tare, sannan mama tayi mata rakiya ta koma gida. Inna saude kanta tayi farin cikin jin wannan labari.! Duk da cewar maganganun su Haj Gaji sun bala'in batawa Umma rai sam bata gayawa Uban dwk ba gudun tashin hsnkali da sabani, hakan yasa bata kwana da zancen cikin ranta ba taci gaba da sabgoginta kamar ba abnd ya farau. Mama kuwa ta kintsa kayanta a jaka tare da sakonnin Umma wanda zata tafi dasu don yin tsaraba, Abba da kansa yake gaya mata kar tayi gaggawar tafiya watakila Al-Ameen yazo kada suyi sabani, ya wuce gona da kazzin idan har ya dawo daga goba bai zo ba shi zai kaita, ba karamin dadi Mama taji ba sbd a zahiri Abbanta yana nuna jin dadinsa da sauyin da Allah ya kawo musu a lokaci guda. Mama ta caba kwalliyar mamaki irin wacce take gigita samarin gidansu duk sanda sukai tozali da ita duk da cewar basanan Ali yana aiki da karamar hukumar birnin gwari shi kuwa Sa'eed dan-sandan-bada-hannu ne a Kd. Shi Sa'eed Mamansa ce ta dauki abin da zafi tuni ya gane ta wuce ajinsa ya fara neman wata anan Kd. Can sassan ta shiga don gaishesu tare da shaida musu zata tafi hutu kamar yanda ta saba idan zata tafin. Tana shiga danlami ta samu yana wankin kayansa ya zura mata ido harta iso gunsa tana murmushi duk da cewar shi tasa fuskar a daure take "wanki kakeyi?" "Uhmmn..... Kuma a zaune don lalaci yaushe zai fita.. Yace ni banson iyayinki.. Tace iyayi?? Wai naga sai wani cin magani kakeyi baka koshi bane halan? Ya dubeta sosai Yace Eh yunwa nakeji.. Saiki kawo min abinci matar masu kudi! Baki sake take kallonsa "matar masu kudi? Ban gane nuffinka ba? Yace jeki abnd ya kawoki karki hanani aiki na.. Ta gyara tsayuwa tace maganarka tana da manufa danlami me kake nufi da matar masu kudi? Sai taji magana daga bakin Haj Gaje ai ba karya bane yaga kinyi kalar matar masu kudi ne shiyasa ya fadi haka ai kinga masu kudin suna zuwa aure ya tabbata! Gaba daya ta daburce ta rasa ina wann magana ta dosa ba shiyasa tayi tsaye tana kallon Haj Gaje. Tace ki daina kallona idan baki gane ba ki tambayi mai hankali yayi miki bayani. Ta wuce abin ta cikin daki. Take nan ran Mama ya baci. Ta juya cikin sauri ta bar sassan, kicibis sukayi da Salisu ya dubeta da kyau yace ashe dama duk abun yaudara ce koda yake dama kin gaya min su Ya Ali basa gabanki, ta kalleshi tace kwarai haka ne ko akwa me yi min dole? Sannan yin kwadayi ma ai dace ne wani idan zai like yayi kwadayin ma bai samu mtsewww... Taja dogon tsaki tabar gurin yayin da Haj Hajjo ta tsaya gabansa amma kai sakarai ne tsayawa kayi tana gaya maka magana son ranta? Kai tsaranta ne? Sakarai kawai. Itama taja tsakin ta wuce shi. Haushi kamar ya hadiyi zuciya cikin sauri ya fice kofar gida. Gaban Ummanta ta zube idanuwa cike da kwalla tace Umma meke faruwa ne cikin gidan nan ake yada habaici? Tace shine zakiwa kuka? To ina ruwanki da abnd ke faruwa? Tunda ba matsalar mu bace. Umma kinsan ban son abin haushi idan su salisu sukaci gaba da yi min habaici wllh zan basu mmk gara ki gayawa Abba yayiwa tufkar hanci tun kafin gidan nan ya yamutse. Ta zura mata ido kinga babu abnd ya shafeki da surutunsu domin ba shi zai hana abnd Allah ya shirya ba, biye masu zakiyi duk ku haukace gaba daya? Ina so ki dauke kanki daga gare su tamkar yadda nayi. Ta goge kwalla tace kema sunyi miki ne? Tace tun jiya iyayensu suka fara amma bai dameni ba don nasan wann abu bani na shkirya shi ba ba kuma Abban ki bane balle ke. Shiyasa ko shi Alhajin ban gayawa ba sbd bana son hayaniya kin gane? Ta dan yi jim sannan ta amsa da ka tana goge kwalla. Tashi ki je ki wanke fuskarki. Ta mike zata wuce yaro yayi sallama yace wai ance Sakeena tazo Al-Ameen yazo. Gabanta ya yanke ya fadi ta zurawa yaron ido ta rasa me zatace? Umman ce ta bashi amsa to kace tana zuwa. Ya juya ya fita, kin tsaya ki kam kije ki shiryo mana. Ta shige dakinta sanyi na kwarar zuciyarta. Ta tsaya gaban mudubi ta gyara fuskarta ta suro gyalenta ta yafa tayo waje. Umma na tsakar gida ta mika mata makulli tace ki kaishi falo karku tsaya a waje. Fuska sake ta amsa ranta ya kara sol. Tayi kofar gida cikin sauri amma cikin sanda ta leko yana tsaye jingine da motarsa ya zurawa zauren ido shiyasa tayi arba da idanuwansa masu haske da girma. Sbd haka kunya ta lullubeta ta koma zauren ta lafe tana maida numfashi kawai muryarsa taji bisa kanta yana fadin sallama gareki ma'abociyar kyau! Jim tayi shiru kamar ruwa ya cita hannunta daya rufe da fuskarta haka shima ya tsaya ya

Chapter 2 of 28