Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wanene, cikinfushitace "wannan gantalallen da na ke gya maki ne, tun ranar yake sintirin xuwa gidan nan, nace ya rabu dani bana yi yaki saurarana, wannan wani irin jaraba ce?" intisaar ta tabe baki tace "ae duk hka suke kmr mayu," sannan ta mike ta dauke cup din da kanwarta tasha corn-flakes ta fita dashi tana taya xainab mita. Tana fita tayi hanyar gate, ta ko gansa a tsaye tayi masaiso har wajen inna, tayi sallama inna ta amsa daga can kuryar daki, ta shiga tana cewa "inna bako kikayi," inna tace "hva don Allah, daga ina? Gani nan xuwa" intisaar na 'yar dariya tace "saurayin xainab ne," inna ta sake kabbara daga cikin dakin tana cewa "gani nan xuwa, ya shigo don Allah," intisaar na dariya ta juya xata fita tayi masa iso xuwa palon, suka hada iso da Aliyu dake gefen kujera a xaune yana danna laptop, wani mugun faduwar gaba ya xo mata, ita bata ma gansa ba, wani irin kallo yyi mata yana girgixa kafa, ya hade girar sama da ta kasa,jikinta a sanyaye tace ma bakon ya shigo, ya shigo yana gdya, ya mikawa Aliyu hannu suka gaisa Aliyun ya dan saki fuska,inna ta fito ta dinga wangale baki tana masa sannu daxuwa, kusan duka lemukanfridge dinta ta dire masa a gabansa sannan ta xubo masa cin-cin da alkaki, tana cewa "ci ka koshi yaro nan ma gidanku ne, ae xainab jikata ce, ni na haifi ubanta, kmr an baka ita an gama kaji ko," gdya ya dinga yi shima yana murmushi, intisaar kuwa dama tuni ta nemi lungu ta xauna tana satan kallon Aliyun da shi din ma satar kallon nata yake, suna hada ido ya galla mata harara, ta mike jiki a sanyayexata bar palon, inna dake ta faman xuba da Abdurrahman, tace "aa ina xaki," takirkiro murmushi tace "xainab din xan kira, inna tace "yauwa maxa kije ki kira min ita yar kwal uba, ashe dama tana da santalellan yaro kyakkyawa hka taki gya min, maxa kira min ita," ta fice da sauri tana yake, Aliyu ya mike inna tace "ina xaka malam bayan kaga munyi bako," ya kirkiro murmushi yana kallon Abdul din yace "ina xuwa ynxun nan ae xan dawo," sannan ya juya da saurinsa ya fice, shit, ya fadi da karfi ganin har tayi kwana, bae san ta fisa wayo ba, dama tasan sae ya biyo ta don hka da gudun ta tayi sashinsu, tana shiga palon nasu, xainab tace "ina kika je ina kiranki tun daxu kixo ki ga abu," intisaar ta tabe baki tace "kicin na tafi, inna tana kiranki fa." xainab ta kalleta tace "a ina kikaga inna?" tsakar gida tana neman ki, intisaar ta fadi ba tare da ta kalle xainab din ba, xainab ta mike tayi sashin innar, intisaar ta dinga dariya bayan ta wuce, ita ma ta rama abinda xainab din ta mata ranar da faruuq ya fara xuwa gidan. A hanya taga ya Aliyu ya watsa mata harara ta kauda kai tare da xumburo baki tayi gaba da sauri, yyi kwafa tare dacewa "xakuci ubanku gaba daya ae, ke mai saurayin da me kawo shi cikin gidan dukxan kama ku, yara basu kai ko ina ba amma sun san su ajiye samari," shi daya ke maganarsa don tuni xainab ta ma kusa sashin inna. Da daddare intisaar taje siyo masu table water momy ta aiketa, tana ganin xainab tasaka gudu ta fice daga gate din tana dariya, xainab bata ko kalleta ba tayi sashinsu, ta dawo rike da ruwan a hannunta ta shiga cikin gidan tana adduar Allah yasa xainab bata nan, mutum taci karo da a bakin gate din ta koma baya da sauri ta ga ko waye, taji an riketa gam, gashi wajen bbu wuta kuma bata fito da torch ba, tana jin kamshin turaren ba sae an gya mata ko waye ba, kankamesa tayi jikinta na bari tana cewa "wayyo momyna, me nayi kuma" tura ya shiga yi amma taki sakinsa ta dada rungumesa gam tanai masa magiyan yyi hkuri..... . Cikin murya kasa-kasa take rokansa ya rufa mata asiri kar ya doketa, bae ko saurareta ba cikin xafin nama ya fara kkrin banbareta daga jikinsa amma hkn yaki yiwuwa sbda irin rikon da tayi masa, jikinsa yyi sanyi kafarsa ya kasa daukarsa, murya can kasa- kasa yace "get off me, ko kuma na baki mamaki," wayyo dukana xaka.... Ji tayi ya daga hijab dinta ya shige ciki, cikin muryar da ba tata ba tace"nashiga uku...." da sauri ta sake shi daga rungumar da tayi masa tana neman guduwa, ya fixgota hade da kankameta ya mannata da bango,kuka ta saki a rude ta fara kkrin turasa, ya matse ta da karfinsa fuskarsa wuyarta tana jin numfashinsa, tayi kicin-kicin ta galla masa cixo a kirjinsa, ya dada kankamta kmr xasu dawo daya yana magana a hnkli yace "dnt utry dat again...." murmushin mugunta yke yi, hkn ya kara tsureta jikinta ya shiga bari tana cewa "don Allah don annabi ka rufa min asiri kayi hkuri," buga bakinta yyi da karfi yana cewa "kar ki sake hada ni da Allah" gyaran murya suka ji an yi daga dan nesa dasu, ya saketa da sauri tare da juyawa, haisam ya gani xaune kan plastic chair ya kauda kansa yana kallon taurarin dake sama, jikin intisaar yyi sanyi, ta gyara hijab dinta, ta durkusa ta dauki ruwan da ta ajiye a gurin tana satan kallon haisam din da har yanxu bai juyo ya kallesu ba, ta bar wajen da saurinta tayi sashinsu, Aliyu ya karasa kusa da haisam din yana cewa"yane?" ba tare da haisam ya kallesa ba yace "nothin" sannan ya mike ya bar wajen, ashe tun daxu yke wajen a xaune yana kallon duk abinda sukeyi, duk da dae ba jin abinda suke cewa yyi ba, haisam yyi murmushi bayan ya bar wajen yace"Intisaarr"Aliyu kam binsa yyi da kallo har ya bace masa, yyi tsaki mai sauti ya bar wajen yana tunanin irin abinda xae yi wa yarinyar nan idan ya kamata, tun ba yau batake seduce dinsa dama, gashi yau har sae da taci galaba a kansa, to wae ma garin yaya hkn ta faru. Intisaar kam har washegari jikinta a sanyaye yake, ko abba kasa xuwa gaida shi tayi don bata sonhaduwa da haisam, har taje islamiyya ta dawo bata je gun inna ba, sae da yamma ihsaan taxo tace mata inna na kiranta, ta dae daure tayi sashin innar tana adduar Allah yasa baxata hadu da haisam ba, don ko tunanin Aliyun ma bata yi ita kmr haisam, tana shiga palon inna ta ko tar dashi a xaune, kunya ya kamata taji kmr ta nutse a inda take, "ina yini ya haisam" ta gaidashi ba tare da ta kallesa ba, ya amsayana cewa "sae ynxu kika fito knan" ta kirkiro murmushi kawae tace"uhum" gyaran daki tayi ma inna sannan ta ce mata tana xuwa xata dauko abu ta dawo, hnyr gudu dama take nema, tana fita kuwaya bita,ta rasa yanda xatayi har ya karaso kusa da ita, "me ya hanaki fitowa yau?" ya tambayeta suna tafiya tare, ta kirkiro murmushi tace"bakomai" yace "hmm, Aliyu fa?" ta xaro ido tace "nima ban sani ba" ta marairaice fuska da sauri ta fara magana ganin inda ya dosa tace"kaga ya haisam wllh jiya aikena akayi shine ya tsareni a gate wae xae dokeni" murmushi haisam yyi bai ce komai ba, hkn ya kara daga matahankali tace "Allah da gaske nke ya haisam" yace "uhum shine kika rungumesa knan" ta xaro ido tace "aa rikesa nayi kar ya dokeni" suna shan kwana suka ga Aliyun a xaune yana waya, yana ganinsu ya kashe wayan, gabanta ya fadi muryarta na karkarwa tace "ya haisam don Allah rakani kar ka barni a nan," ganin a nan xasu rabu ne yasa tace masa hka, yyi dariya yace "aa Aliyu dae xae rakaki ni ba ruwana,"hannunsa ta kama tana rokansa, aliyu ya bisu da kallo har suka wuce,haisam na dariya, ya mike yyi tsaki yace "ikon Allah kadae ne xae sa baxaki suma a hannuna ba idan na kamaki " dagaita har haisam bbu wanda ya kallesa bare ya amsa masa. . Yau juma'ah tana xaune palonsu ita da xainab, suna hira bayan sun dawo dagadubiyar wata yar ajinsu farida da bata da lfya, kusan karfe biyar ce ta yamma, daga intisaar din har xainab material iri daya suka sa purple nd pink sunyi kyau kwarai, kursum ma tana palon nasu tana cin abincin intisaar da momy ta ajiye wae ba aajiye mata abinci ba, intisaar tace taci natadon a koshe take ita, kirar wayar faruuq ne ya shigo wayrta, ta daga suka gaisa sannan yace mata gashi a wajen inna, ta shiga daki ta nemi ixini gun momynta, sannan ta fito tace ma xainab ta rakata, xainab ta galla mata harara sannan tace"anki!" intisaar tayi 'yar dariya sannan tace"karki raka ni din ma to sae me" xomuje kursum," ta fadi tana kallon kursum din, kursum ta tura kwanun abincin tace"muje," suka fice tare intisaar nai ma xainab dariya. Suna shan kwana fadila ta kwada ma kanwartata kira, kursum ta haderae tace "meye" umma ta leko tana cewa"don ubanki kanwar uwarki ce kota ubanki wannan shegiyar?" kursum ta xumburo baki, uwar ta daka mata tsawa cin bacin rai tace taxo ta wuce, dole intisaar ta kama hanyr sashin inna ita daya. Tana isa tayi sllma murya can ciki inna ta amsa da karfinta tashiga palon tana addu'ar Allah yasa ba surutunta na bnxa takewa faruuq ba, tana shiga palon suka yi ido hudu da Aliyu, gabanta yyi mugun faduwa har ta mnta lst tym din da ta gnsa ita kam,sanye yake da shadda fara kal, ashe dae su Aliyu ana sa manyan kaya, ta kalli haisam ma dake xaune a palon shi din ma shaddar ce fara, hka ma faruq dinta, gaba daya dae anko sukayi, ta nemi gefen inna ta xauna, bata bari sun hada ido da faruuq din dake ta kallonta ba, inna tace "sae ynxu ku ka dawo?" tace "eh" a takaice kawae, sannan ta gaida haisam da har lkcn kallonta yke yi,yyi murmushi yace"lfya kanwata kinga yanda kika yi kyau kuwa yau" ta sunkuyar da kai tana murmushi tace "kai yayana kullum sae ka xolayeni wllh" sannan ta sata kallon Aliyu, kallonta ykeyi amma fuskarsa a hade, ta dauke idonta da sauri ta dube faruuq dake ta faman kallonta kmr xae cinyeta, ta galla masa harara da wasa tace "wannan kallon fa" dariya yyi ya kashe mata ido yace "naga kin kara kyau ne yau bby," ta xaro ido tana kallon inna data bude baki tana kallonsu, dariya suka yi gaba dayansu har da haisam, innar ma ta taya su, Aliyu dae ya maida dubansa ga plasma, lallai yarinyar nan ta rika, ko gaishesa ma bata yi ba, faruuq ya dubi haisam yace "big bro, plss tel her nt 2 let me down, coz i'm blindly in love" haisam yyi dariya sosae, ya kalli intisaar dake ma faruuq din wani irin kallo ya dawo gefenta ya xauna yace "hope u heard wat he said cweet sis, i wont love 2 c anythin bad goes wrong wit my frnd" tayi 'yar dariya ta daura kanta a kafadar haisam din tace"ok cweet bro, help me let him knw dat...... Am his nd his alone,nd i promise nt 2 let him down," ta karasa mgnrta tana satan kallon faruuqdin, dariya sukayi gaba daya, haisam yace yana kallon faruuq "hope dat's clear besty" inna da tuni ta hangame baki tana kallonsu ta mike tayi narai-narai da ido tana cewa "yau de xagina ake tayi, tunda gashi Aliyu bae ce komai ba, bari kawae na bar maku palon" dariya intisaar tayi ta riketa tana cewa "kaji mana wannan tsohuwar mu soyayyar mumuke yi don Allah ki xauna ," inna tace "lah" bari de nashiga ciki idan kun gama xan dawo, faruuq yyi dariya yace "inna ta tsargu," ya dawo gefen intisaar ya xauna yana mata wani irin kallo kmr maye, cake ya dauka ya kai mata baki yace "bude bakin na baki kanwata" ta hararesa tace "bna ci," haisamyyi dariya ya mike ya koma kan kujera yace"kila don dae ina gefenku ne amma na tashi karbi kayanki ke dae"dole sae da faruuq ya tilasta mata yasa mata cake din a baki, ta kauda kanta a kunyace, kawae suka hada ido da Aliyu da ya xuba mata ido yana kallo, gabanta yace dam, taga ya kauda kansa yyi murmushi, mikewa tayi dasauri tana kallon faruuq din tace " lah! ina xuwa ya faruuq minti biyar na daura abu a kitchen," ta mike da sauri ta fice, ta kinkimitakalminta ta ruga a guje, tana fita kuwa Aliyu ya mike shima ya fice. Shit! ya fadi dakarfi yana huci, ya girgixa kansa yabar wajen kawae. Ita kuwa tana isa sashinsu ta shige palo gabanta nafaduwa, ta shiga wanka kawae, ko da ta fito xainab ta tafi, tayi sallah, sannan ta saka kayan barcinta ta jawo abincinta taci, ta koya ma ihsaan assignment dinta wajen karfe takwas knan, ta idar da sallahn isha'i knan faruuq ya kirata kunya yasa ta kasa daga wayan don tasan bata kyauta ba, daga karshe dae ta daga, yace "uhun to ai kya xo muyi sllma ko kanwata" tace "lah bka tafi ba dama yaya" yace "yea mun danyi wani abuda haisam ne a laptop, ynxu xan tafi ki fito ina ma bakin gate, daxu dae nasan babanki yasa ki barin falon" ya fadi cikin xolaya, taji kunya sosae, tace "hm to ka shigo ka gaida momy mana idan yaso sae na raka ka gaba daya kaga ni kunya nke ji baxan iya ce mata xan fita ba kuma" yace"ohk gani nan xuwa kanwata. . ... Har parlor faruuqya shigo ya gaida momy, ta amsa masa da fara'arta tana tambayrsa mutanen gidan yace duk lfya momy, sun danyi hira kadan sannan ya mike yace "ni xan koma momy, dare yyi," tace "to ka gaida mutanan gidan mun gode kwarai," ya ciro kudi mai yawa ya mikawa ihsaan da ya xaunar a gefensa momy tace "hva don Allah kar ayi hka umar," yace "aa momy xata siya chocolateko ihsaan?" ya fadi yana kallon ihsaan da tayi dariya ta gyada masa ka, ihsaan momy ta aika ta kira intisaar a daki, ta fito sanye da hijab dinta har kasa, sannan ta fita rakasa, suna isa bakin gate ya dauko kujeru biyu ya ajiye yace "hira xamuyi kanwata, don daxun wayo kika min kika gudu" ta dan xaro ido tace "ya faruuq abbafa ya kusan dawowa," ya bata rai yace "to shknansae da safe," ya mike xae bar wajen ta riko hannunsa tace "wayyo yi hkuri yayana, xamuyi hirar amma ba da yawa ba" yyi murmushi ya koma ya xauna yace "to na yrda kanwata, xo ki xauna," ta xauna kan kujerar kanta a sunkuye, ya tsura mata ido yana kallonta, a hnkli yace"i love yhu intisaar," ta rufe fuskarta da tafin hannunta bata ce komai ba, ya sa hannu ya cire hannayen nata daga fuskarta yana kallonta, duk da wajen ba wani hasken kirki bne dashi, kunya ya kamata sosai tace a hnkli "kaga nafara jin bacci yayana," yyi shiru bai ce komai ba sae kallonta da yake yi, can dae ya mike tsaye yana cewa"to shknan kanwata sae munyi waya knan," kudi ya ciro ya mika mata taki karba ya bata rai yace "kin raina knan ko" ta wara ido tace "hva deyayana wllh kawae de ngd ne" yyi fuska ya ajiye mata kudin kan cinyarta yace "ki watsar dasu to," tayi shiru takasa cewa komai, yace"ina xuwa bni 2 mint," ya fita waje saegashi yashigo da leda a hannunsa ya mikamata yace "ummi tace a kawo maki," tace"kai hva de yayana, ni wllh da baka karbo ba....." ya ajye mata shima a gefenta yace"to shi din ma ki jefar" sannan yace mata sae da safe, ya fice daga gidan, ta bisa da kallo har taji tashin motarsa sannan tayi ajiyar xuciya, Allah dae ya gani tana son faruuq fiye da yanda take tunani, jiki ba kwari ta mike ta dauki ledar ta maida kujerun gun da suke sannan ta juya xata yisashinsu taji taci karo da mutum, tashiga uku talalace, ta saki ledar hannunta ta juya da sauri xatayi hanyar gate don nan kadae ne xata tsira idan tabi, ya fixgota, xata fasa ihu yasa hannua bakinta sannanya juyar da ita, "ya Aliyu ka taimakeni, ni bnmka komai ba wllh" cikin kuka da rawar murya take maganan, ya kai mata tagwayen mari masu lfya, sannan ya buga ta a bango da karfinsa, fuskar nan tasa bbu alamr rahma, kuka mai tsuma xuciya ta saki tace"don darajan iyayenka kayi hkuri plsss" buga mata baki yyi da karfi harsae da bakinta ya fashe, yasa kafa ya kwasheta, ta mike da sauri agigice tana cewa "nashiga uku, don Allah....." wani mugun naushi ya kai ma cikinta ta firfito da ido tare da saki wani irin axababben kara damuryar da ba tata ba, ya kai mata wani marin tare da daura yatsunsa a bakinsa alamr tayi shiru, ta sa hannu ta toshe bakinta tana karkarwa ta girgixa kanta hawaye mae xafi na xuba a idonta. Aliyu bae kyaleta ba sae da yaga ta kasa tsayawa sannan ya fixge kudin dake hannunta yasa a aljihu, a karo na farko ya bude baki yyi magana"kadan knan kika gani, Wllh tllh ni Ali sae na sumar dake watarana a gidan nan idan baki fita hanyata ba" ya juya ya barta nan a durkushe kanta a kasa, da kyar ta iya mikewa ta bar wajen tana ganin double koledar da faruuq ya bata ma bata dauka ba don ji take kmr xata suma awajen, tayi bangarensu tana daddafe bango don wani irin jiri dake kwasarta. Ko da tashiga palonsu ma momy shafa'i da wutr take ta shige bedroom kawae ta fada kan gado tana juye juye kmr xata mutu, wani irin ciwo cikinta ke mata ta dalilin naushin da ya kai mata, hka ma kanta da ya buga da bango, cikin ikon Allah bacci ya dauketa amma can cikin dare ta farka da matsanancin ciwon kai ga mugun xaxxabin da ya rufeta, juye-juyen da takeyine ya tada momynta, ta mike xaune ta kunna wutan dakin tana kallonta tace"lfyarki kuwa intisaar," kasa magana tayi momy ta kai hannunta jikinta taji kmr wuta,"me ya sameki hka" ita dae ba baki sae kuka da ta fashe da, paracetamol momy takawo mata ta bata ta karba da kyar tasha, sannan ta kashe ac dake dakin ta lulube tadalilin rawar sanyin da takeyi, ranar dae daga ita har momy basuyi bacci ba, momy ta rasa abinda ke damun 'yar tata, duk ita ma hnklinta ya tashi. Gari na wayewa momy taje ta sami abba ganin yanda jikin nata yyi tsanani, gashi sae aikin kuka take, duk ita ma tabi ta daga hnklinta don akwae soyayya da shakuwa mai karfi tsakaninta da 'yar tata don ita kadae take gani taji ddi idan ta tuna mijinta na farko umar, har daki abba ya shigo duba intisaar din, "me ya sameki fatima, ina ke maki ciwo?" ya tambayeta dadamuwa yana yaye bargon da momy ta lullubeta dashi, ita dae ba baki sae kuka, abba yashiga lallashinta yana cewa"damabaki da lfya ne fatima, kuma bakiyi maganaba tun jiyan?" ta girgixa masa kai kawae, xainab tashigo dakin hankalinta a tashe bayan ta tambayi ihsaan ina intisaar don ita har tayi shirin islamiyya da yake tare suke wuce, ihsaan tace mata "my aunty is sick," hkn yasatayo bangaren nasu da saurinta, abba ya dubi xainab da tashigo yace"je ki ki kiramin Ali xainab," tace to sannan ta fice da sauri, a hanya suka haduda kursum take tambayrta ko intisaar ta shirya don ita ma shirin islamiyyar tayi, tunda Aliyu yyi masu mugun duka ranannan suka fara xuwa makaranta gaba dayansu dama, xainab tace "bata da lfya baxa taje ba," kursum tace "hva de me ya sameta," xainab ta yarfehannu tace nima bn sani ba ynxu ma ya Aliyu xan kira abba ma yana can, kursum tayi sashin nasu da sauri xainab kuma ta tafi kiran Aliyu, tana isa tayi sllma ta shiga palon, baya nan, tayita kwada sllma ko yana cikin daki amma shiru, sanin halin yayan nata ne ya sanyata karasawa cikin bedroom din nasa yana ko xaune laptop a gabansa yasa earpiece kunne daya yana danna laptop, ya daka mata tsawa a fusace yana cewa"baki da hnkli ne don ubanki ko ke jahila ce,baki san idan kika yi sllma a waje kika ji shiru gaba xakiyi ba, xaki afko min cikin daki, ban hanaki wannan habit din ba," au ashe ma yana jinta, ta tabe baki cikin rashin damuwa tace "dama abba ne ke kiranka" ta juyafuu xata wuce ya mike da sauri yana cewa "xainab, xainab," amma bata tanka masa ba, ya fito palon da sauri har ta fice ya bita da sauri yana kiranta, ta dawo tana kallonsa fuskarta a hade tace"gani," me yasa abba ke kirana, ya tambayeta yana kallonta don dae yasan sae da dalili ake kiransa, don kan abba ya kirasa sau daya ya kira haisam sau goma,"nima ban sani ba, intisaar dae ce bata da lfya shine yace naje na kiraka" ta fadi tana kallonsa, gabansa ya fadi yace "to menayi ake kirana" tace "ni kuma ina xan sani" hnklinsa ya tashi yace "me tace wa abban?" tace "oho, ni ina shigowa abba yace nayi maxa naje na kiraka" don ta gaji da tambayoyin nasa, bai damu da ohon datace masa ba ya kara tambayrta "ya mood din abba yake" tace a kage "kai yaya ni ma ban sani ba abba nacan yana jiranka," ta juya ta yi gaba ta barshi nan a tsaye. Ya bita da sauri kuma yana kiranta, ta juya rai bace tana kallonsa yace "ina abban?" tace"yana can dakin momy" ya xaro ido yace"yana me?" tace "oho! tayi gaba abinta" ta fara suspect dinsa ita kam. Tana komawa sashinsu intisaar abba ya tambayeta meya tsayar da ita kuma ina Aliyun, tace"nemansa nke a gidan abba amma gashi nan xuwa" ya dubi momy da ta xauna tayi jigum yace "ki hado mata tea xainab," ta mike tace to sannan ta fita, tana fita sae ga inna, tun daga waje suka dinga jin muryarta kmr speaker tana cewa"me ya samu intisaar din, ni rahmatu," abba ya juya rai bace yana kallonxainab yace "donuwarki ca nayi ki ji ki gaya wa inna taxo ta daga mana hnkli a nan ynxu?" xainab ta mike da sauri ido a waje tace "wllh tllh abba ban je wajen inna yau ba ni," abba bae sake cewa komai ba har inna ta shigo dakin, "bukar me ya sameta wae" abba ya dubeta yace "shine ae xa a dubata don bbu wanda yasani," inna tasaki salati tana girgixa kai tace "Allah ubangiji dae ya bata lfya wllh duk hankalina ya tashi da aka je aka gya min," abba bae sake tanka mata ba tana ta surutanta, illa Aliyun da yake jira, murya can ciki Aliyu yyi sllma, duk jikinsa yyi sanyi, ynxu yarinyar nan sae ta iya bude baki tace yyi mata wani abu dama, inna ce ta amsa masa da karfinta tana cewa "maxa shigo," hankalinsa ya kara tashi ya shigo palon ya tsaya yana waige-waige kmr munafuki, abba yace"karaso mana" da kyar yyinamijin kkri ya shiga dakin, ya rusuna ya gaida abba don duk yau bai je gaisheshi ba gashi har karfetara, ya juya ya gaida inna ma sannan yace"abba gani," . Dama fatima ce bata da lfya, shine nace a kiraka ka dubata, abba ya fadi yana kallonsa, Aliyu ya saki ajiyar xuciya, sannan ya maida dubansa ga kangadon yana kallonta, idonta a lumshe yake, duk da dae ba bacci take ba, ya karaso kusa daita yace "meke damunki?" tayi shiru kmr mae bacci, hkn ya bata masa rai don yasan idonta biyu, a dan fusace yace"kinajina xakiyi min banxa?" inna cikin tsawa tace "kai mahaukacin wani gari ne, baka ga bacci take ba yarinya tana fama da kanta xaka dinga mata ihu," xainab ta karasa kusa da ita tana bubbuga kafarta a hankli tana kiran sunanta, ta bude ido tana kalln xainab din, Aliyu ya juya yana kallon abban nasa yace "ko dae a wuce da ita clinic kawae abba" inna tayi karaf tace"wllh bbu inda xa a kaita, gamu da likita a gida kace xa a wuce da ita wani wajen, meye amfanin ka" Aliyun ya dubeta rai bace yace "to ni din Allahn musuru ne da xan san abinda yke damunta," cikin tsawa inna tace "shiyasa naga an kai fadila asibitida bata da lfya, don ubanka ba kai ka dubata ba ka bata magunguna da allurori ba kuma gashi nan ta warke," Aliyu ya dubeta a walakance ya kauda kai kawae, abba yace "shknan bari a kaita asibitin ka iya tafiya" da sauri yace "aa abba bance baxan dubata ba ae, guri nake jira su ban na dubata," ya fadi yana kallnsuinna, haisam ya shigo dakin da sllmrsa ya karasa kusa da intisaar din ya xauna cike da damuwa yana kallonta yace "intisaar me ya sameki, dama jiya baki dalfya baki yi magana ba," ta sunkuyar da kanta kawae sae hawaye, nanya shiga lallashinta, ya dube abba yace "asibiti xamu wuce abba?" inna tace "asibitin lfya ga likita a gida, ynxu xae dubata ae" sllmrsu hajiya da umma ne yasa kowa yyi tsit a dakin, momy ce kadae ta amsa masusuka shigo suna cewa ashe abinda ya faruknan, momy ta basu waje suka xauna sannan suka gaisa, suka tambayeta mae jiki tace masu da sauki, hajiya tace Allah sarki duk ta rame sae kace warce tayi sati tana jinya, umma tace wllh kuwa baiwar Allah, inna ta tabe baki tace "ikon Allah" xainab ta girgixa kai cike da takaici, ynxu har anje an barbada masu shine suka kwaso jiki suka xo gulma, kumatasan baxae wuce kursum ba ko rahma, abba ya dubi gaba dayansu yace "to ae kwa bashi waje yyi aikinsa de ko" hajiya ta mike tana cewa"me xae hana, Allah dae ya bata lfya yasa xakkan jikine," suka mike gaba dayansu har da yaran xasu bar dakin, Aliyuyace "to..to abba ya xa ayi treatin din nata?" abba da har ya kai bakin kofa xae fita ya juya yana kallonsa cikin rashin fahimta yace "kmr ya fa?" yace"aa...dama...emm, to to ae naga sae da magunguna da allurori xa ayi treatn din nata, kuma ni...." sae kuma yyi shiru yana kallon tagan dakin, abba yyimurmushin takaici ya girgixa kai yace "to nawa xa a baka?" inna ta mike ta saki salati tana girgixa kai tace "ita intisaar din sae....." da sauri abba ya katse ta yace "aa baaba ae hakkinsa ne bari a basa" nawa ne kudin treatment din gaba daya? Abba ya tambaya yana kallonsa, cikin bacin rai haisam yace "abba ka bari na wuce da ita asibiti kawai," abba yyi saurin cewa "aa haisam ka bari xae dubata," abba ya sake tambayrsa nawa xae basa, yyi shiru kmr me lissafi sannan yace ba tare da ya kalli abban nasa ba "dubu takwas da dari biyar gaba daya," abba yyi murmushi, haisam cike da takaici yace "to yyi kyau, ka dubatani xan baka," da sauri ya juya yana kallon haisam din rai bace yace "to da baki na xan siyo kayan ne koya? Ko kuma ina da kudin xan tsaya cewa abba ya bani," inna cikin ihu tace "Allah ya babbake mae krya sannan ya tsinemasa," Aliyun ya juya ya galla mata harara sannan ya dauke kansa, haisam ya ciro dubu biyar daga aljihunsa ya mike xae fita abba

Chapter 8 of 32