Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kwalabe," ta xumburo baki ta ci gaba da game dinta, yace "ba magana nake maki ba," ta mike tsaye fuskarta daure ta bi ta gefensa ta fice ya bita da kallo, ya sauke ajiyar xuciya, tana sauka ta shiga kitchen ta fito da mop da bokiti da tsintsiya da parker ta rasa ta inda xata fara gyaran ga shegen tean shima ya malale har cikin falon, ya sauko yana kallonta yace "ohh tsayuwa kika ma yi knn," kmr xata yi kuka tace "to ni ban san yanda xanyi ba" ya tsaya kallonta, ta karyar da kai ita ma tana kallonsa, sae abun ya kusan basa dariya, yyi kwafa ya karbe broom din daga hannunta ya duka ya fara tattara broken mugs din, tana tsaye tana kallonsa, ya dago yana kallonta yace miko min abun kwashe sharan kmr xata yi kuka tace "baka ga kwalba a wajen ba xan taka," ya tsaya kallonta ya kasa cewa komai, dae dae nn Safeena ta sauko da dogon hijabinta xa ta kitchen hado tea ganin yunwa na neman hallaka ta, yace "miko min abun kwashe dirt din can Safeena," bata yi masu ba ta dauka ta mika masa jikinta na rawa, a tare ta taimaka masa suka gyara falon Inteesar na tsaye tana kallonsu, safeena na goge falon ya daka ma Inteesar tsawa yace "get out kar na mareki, meye amfanin ki a nn" ta ja dogon tsaki ta haura sama daga shi har safeenar suka bi ta da kallo, yyi kwafa kawae, da daddare ya hadasu a falo xae yi masu magana, Inteesar dae nata kallonta abunta, yana kallon safeena yace "kina ji na Safeena," safeena da ta xama kmr marainiya ko kuma nace ta kirki tun daga jiya, kanta a duke tace "ina jinka," ya kalli Inteesar da ta bar kallonta tana hararanta, yace "kema kina jina," ta yi bnxa da shi ta ci gaba da kallonta, ba karamin daure ma safeena kae abinda Inteesar ke yi yyi ba, lallai xata yi maganin shegiyar nn nn ba da ddewa ba, Aliyu bae damu da bnxan da inteesar tayi masa ba yace "ke kika xo kika sameta a gidan nn safeena don hka ki sani gaba take da ke a gidan nn, bana son wani tashin hankali a gidana ku kame kanku, kar wanda yyi kishi kaina ban aikesa ba, kowa tasa ta fishshesa," ya juya kan Inteesar "ke kuma fitsararriya ki rike fitsararki, ki sani safeena ta girmeki nesa ba kusa ba, ke din yaushe kika balaga ma kika san me duniya ke ciki, yarinya dake sae shegen rashin kunya ki tambayeta shekararta nawa ta fada maki kiji, u had beta respect ur self coz she's nt ur mate, snn girki as frm nxt wk duk every 2dayz xaku ke yi, bana son tashin hankali a gidana i repeat my self kuyi respectn kanku" Inteesar ta mike tsaye tana gyara daurin dankwalinta ta ja dogon tsaki tace "sannu balagaggu, kuma ba girmata ba har haifata Safeena tayi," tayi masu kallon bnxa xata haura sama ya bita da sauri ta saka gudu amma duk da hka sae da ya kamota ya shaketa yace "uban waye sa'anki a nn," ta fashe da kuka tana kiran Abbanta ya jefar da ita kan kujera yana kallon safeena yace "in ta maki ki gyara mata xama ni na sa ki," xata mike daga kan kujerar yace "in kika tashi sae na watsa maki mari," ganin bbu wasa a tattare da shi yasa ta koma tana kuka, yana kallon Safeena yace "kije ki shirya mu siyo abinda kika ce," murna fal cikinta ganin abinda aka ma Inteesar tace "ni a shirye nake," ya ciro makullin motarsa, ta mike ta bi bayansa suka fice daga gidan tana ma Inteesar wani irin kallo tana jujjuya ido. Basu dawo gidan ba sae kusan karfe sha biyu, inteesar na kwance bayan ta gama cin kukanta har lkcn bata yi bacci ba, muryar safeena taji tana cewa "bby ka bari mu shiga ciki mana don Allah ka bari," cikin kissa take maganar, Inteesar ta mike ba tare da ta shirya ba kuma bata san dalili ba ta shige bathroom ta kulle . Yau safeenah ta cika sati uku gidan Aliyu ko sau daya kallon kirki bae taba hadata da Inteesar da ta xame mata jaraba a gidan ba, gashi ba dama tayi mata ko da kwakkwaran kallon bnxa Aliyu ya hau ta da bala'i don yace mata baya so, ta kyaleta kawae yarinyace kuma yarinta ke damunta, bbu yanda Safeena ta iya don tana mugun son Aliyu kmr rayuwarta duk abinda Inteesar tayi mata sae dae ta gaya masa, wani lkcn ya shareta wani lkcn kuma ya samu Inteesar din ya tsoratata ko kuma ya sa ta kuka, shima ta lura ba a son ransa yake yin hkn ba, ko sau daya Inteesar bata taba shiga kitchen tayi masu girki a gidan ba ko da kuwa ranar girkinta ne sae dae Safeena tayi a bisa umarnin da Aliyu ya bata, don ca yyi ta rabu da ita kawae ta dinga girki kullum, littafin girki kadae ne ke taimakonta don bbu abinda ta iya da ya wuce tafasa ruwan xafi, cikin ikon Allah kuwa idan tayi sae ya dan yi ddi da taimakon littafin, ta adana littafinta ssae, iyaka idan ta fito inteesar ta shiga ta dafa indominta ko taliya, ganin rashin amfaninta a gidan yasa Aliyu ya kai ta da kansa tayi registratn din jamb ana saura sati daya a rufe, kila idan ta fara xuwa makaranta xae samu kwanciyar hankali don bata tsinanasu da komai sae tashin hnkli a gidan, wani lkcn yakan yi mamakin ashe yarinyar nn na da baki hka, kuma fitsarewarta lkci daya da rashin tsoran kirkin da take masa yana mugun basa mamaki shi dae ba wasa da ita yake bare yace kuma tunda ya auri safeena bae nemeta ba, gaba daya ta daina tsoransa sae taga yyi kanta xae doketa ta marairaice masa tana kuka, gashi abu kadan sae ta bara masa baki ta fasa masa ihu a gida ba gaira ba dalili, shi kuma yana kyaleta ne kawae sbda Abbansa don ko kadan Inteesar bata gabansa don bbu abinda Safeena ta rage shi da barin a wajen kwanciya shi yasa yake ji da ita, duk da yakan yi murmushi idan ya tuna 1st nyt dinsu da Inteesar, da yanayin da ya shiga da har yau bae ji hkn gun Safeena ba, darajar da Inteesar ke ci kadae a gunsa knn banda hka da bata isa ta taka masa matarsa da yake ji da ba, Safeena kanta na mamakin yanda Aliyu ke share Inteesar duk da iskancin da take xuba masa, ita bbu abinda yafi daga mata hankali ma irin mugun rainata da Inteesar tayi, amma tasan duk Aliyu ne ya ja mata tunda ga irin tonan asirin da yyi mata washegarin ranar da aka kawo ta gidan, wani lkcn takan yi murmshin takaici tace nasan tanadin da nayi maki yarinya kiyi yanda kike so lkcn ki ne ynxu. Ranar da ya kaita tayi registratn din jamb can ya barota ya bata kudin mota ya wuce office, bata bari adai daita sahun ya shigo da ita layinsu ba ta sauka ta basa kudin don yau tana son ta kare ma anguwar kallo tunda dae ba fita take ba, tana isa bakin gate dinsu taga wata yarinya da baxata wuce ta ba rike da wani kyakkyawan yaro a hannunta tana waya, Inteesar ta dauke kanta ganin sun hada ido, yarinyar tace "sannu fa," inteesar tace "yauwa, ngdd," ta danna bell mai gadi ya bude mata ta shiga, taji yarinyar ta burgeta yar kyakkyawa da ita, safeena na kwance a falo da kawayenta ta wucesu tana yatsine fuska ta haura sama, bayan kwana biyu Aliyu ya hadata da driver taje ganin centre dinta, tana dawowa ta sake haduwa da yarinyar a bakin titi ita ma xata karasa layin da kafa tana rike da danta, bayan sun gaisa Yarinyar tace "amma aure kike a gdan nn ko," Inteesar tayi murmushi tace "eh," yarinayr tace "to ya sunanki," inteesar ta gaya mata yarinyar tace "ni kuma sunana Aneesah," Inteesar tayi murmushi tace "to yaron ki fa," yarinyar tace "sunansa Abdush-shakur," Inteesar ta karbi yaron tana murmushi tace "fyn shakur," har suka isa dai dae gidajensu, yarinyar tace "kina da kyau ssae, ina son mu xama kawaye," inteesar tayi dariya tace "to ai kema kina da kyau," Aneesah ta bata wayanta tace "sa min nmbrki to inteesar," Inteesar tace "wllh wayan mijina ne a hannu na ki bari idan na samu waya," Aneesah tace "to mu shiga kiga gidana mana" inteesar ta xaro ido tace "mai gidanki baya nn," Aneesah tace "A'a a Abuja yake aiki sae wkend yake dawo wa," inteesar ta bi ta suka shiga gidanta, gidane babba kmr nasu bbu abinda ya xama bakonta a gidan don duk suna da shi a nasu gidan, har bedroom ta shiga da Inteesar, inteesar ta shantake suka dinga hira kmr da can sun san juna, ta girka masu abinci ta kawo masu dakin suka ci suna ta hira tana ba Inteesar labarae kala kala, Inteesar taji kmr kar ta bar gidan, karfe shidda saura ta rako Inteesar har bakin gate kmr kar su rabu, har shakur ya saba da Inteesar don har da kukansa, wae sae da ta isa jikin gate tukunna gabanta ya shiga faduwa a xuciyarta tace "Allah yasa ya Aliyu bae dawo ba," mai gadi ya bude mata gate ta shiga taga motarsa a parke a garage xuciyarta yyi mugun bugawa da kyar tana jan kafa ta shiga gidan. Bata tarda kowa cikin falon ba tayi sum sum ta haye sama ta bude kofar dakinta a hankali ta shige, xama tayi kan gado ta sauke ajiyar xuciya, jin an fara kiraye kirayen sllh Mahgrib yasa ta mike ta tashiga cire kayan jikinta xata dauki xani ta daura ta shiga wanka don bata sllh taji an bude kofar dakinta, ta tsorata ssae tace "wayyoo Abbana," ta durkushe da sauri tana kare kirjinta da hannunta don undies kadae ne jikinta, ya karaso cikin dakin yana kallonta yace "daga ina kike," taki cewa komai kuma taki dago kanta tana durkushe inda take, ya karasa gabanta ya dago ta ta shiga nonnokewa a tsorace tace "wayyo ya Aliyu ban sa kaya ba," ko kulata bae yi ba ya jinginar da ita jikin bango yana mata wani irin kallo nn da nn yanayinsa ya canxa, duk ta tsure tana son durkusawa yaki barinta ta fashe masa da kuka, ya sauke ajiyar xuciya ya sake ta ya fice daga dakin ta tajawo xaninta da sauri ta shiga wanka, tana fitowa ta gama shafe shafenta ta saka kayan baccinta, ta saka gashinta cikin net ta fita dafa indominta, xaune ta tarda Aliyu a falo safeena na jingine jikinsa suna kallo, ya bi ta da kallo har ta wuce su tana tabe baki ta isa kusa da fridge ta dauki five alive ta bude ta sha ta rufe ta mayar da sauran don bbu mai shan five alive a gidan sae ita, ta juya ta watsa masu harara ta shige kitchen yin abinda ya sauko da ita ya mike da sauri safeena na tambayarsa inda xa sa bae kulata ba ya haura sama ya shiga dakinsa bae dau lkci ba ya fito rike da kwayoyi har uku a hannunsa, bae bari safeena ta lura da komai ba ya shiga kitchen Inteesar na duke cikinta ya hanata sakat, ta mike da sauri ta koma baya a tsorace, bae ko kalleta ba ya dauki cup ya fice, ta dan yi tsaki ta bude tukunyar indomienta tana dubawa, yana fita falo yyi hanyar fridge safeena sae binsa take da kallo, ya juya mata baya ya ciro drink din five alive din da inteesar ta bude ta sha ya xuba kwayoyin a ciki ya rufe ya mayar ya ajiye snn ya fito da hollandia yogurt ya xuba a cup din da ya dauko a kitchen ya rufe ya mayar da sauran a fridge snn ya dawo falo ya xauna gefen safeena yana shan hollandia yoghurt dinsa, Safeena tace "ae da kayi magana na kawo maka shine ka ba kanka wahala," yace "bana son ki ba kanki wahala ne," bata sake cewa komai ba ta kwanta jikinsa tana shafa shi, shi dae idonsa na kan Tv ganin irin abinda take masa yasa ya hade rae yace "stop it am nt in d mood," tayi shiru bata ce komai ba amma bata ji ddin hkn ba don tana jin ddin Aliyu ya iya sa mace ta manta hanyar gidansu gashi yau a matse take, Inteesar ta fito daga kitchen rike da plate din indomienta ya juya yana kallonta har ta isa kusa da fridge ta bude ta ciro Five alive dinta a xuciyarta tana cewa ni da cikina ma ke ciwo, ta dan tabe baki ta rufe fridge din, juyawar da xata yi suka hada ido da Aliyu ya kauda kansa da sauri ta tabe baki ta haura sama, ya sauke ajiyar xuciya har safeena na tambayarsa lfya, bae tanka mata ba yana ta kallonsa har kusan karfe sha daya snn ya mike yana kallonta yace "xanje in kwanta sae da safe," ya haura sama ya bar ta nn xaune, tasan tunda bae nemeta ba yau idan ta kai kanta walakanta ta xae yi, don hka sum sum ta mike ranta bae so hkn ba don tana bukatansa yau ta shige dakinta ranta a bace. Shi kam yana haurawa sama dakinsa ya shiga ya hada coffee yasha don shi mayen coffee ne, snn yyi wanka ya canxa xuwa nyt wears dinsa ya bude kofar dakinsa yyi hanyar dakin Inteesar, xaune ya tarda ta a dakin ta jinginar da kanta jikin gado idonta a lumshe, ya karasa gabanta ya durkusa yana kallonta, ta bude idonta da ya kada yyi jajur a hankali tana kallonsa. . Aliyu yyi murmushi yana kallon cikin idonta ya daura goshinsa kan nata har tana iya jiyo numfashinsa a fuskarta ta lumshe idonta ya dagota ya xaunar da ita kan gado ya dago kanta yana kallonta, a hankali kmr mai rada yace "kina bukatan wani abu ne," kin cewa komai tayi ta koma can tsakiyar gado xata kwanta, bae hanata ba ya barta tayi kwanciyarta snn ya dawo gefenta yana shafa fuskarta yace "to yau baki tsorona" idonta lumshe bata ce komai ba ya dagota ya rungumeta ya shiga kissn din wuyanta yana shafata, da kyar ta turasa muryar ta can kasa tace "ka bari," shima murya can kasa yace "shkkn tunda ba kya so," ya sake ta ya mike ta rikosa da sauri ta fashe masa da kuka, ya rungumeta cikin rada yace "to duk me nayi maki kiyi mani ke ma," xata yi magana ya daura bakinsa kan nata a hankali yace "kiss me," ta lumshe idonta ta shiga kissn dinsa, he could'nt belive it, ya kankameta, ta dauke bakinta daga nasa tana mayar da numfashi kmr xata yi kuka, a hankali ya shiga cire mata kayan baccin jikinta yana kissn dinta, ya shiga romancin dinta kmr xae hadiyeta ita ma lkci lkci takan mayar masa da martani ganin yana neman xautar da ita gaba daya yasa ta kankamesa tana mayar da numfashi tace "plsss" bae tanka ta ba har sae da yaga ta fara kuka snn ya shiga rabata da sauran kayan jikinta, turata yyi ba tare da ya shirya ba, ya fada gefen gado yyi rub da ciki yana mayar da numfashi ta fada kansa tace "no, plss ya Aliyu," duk ta xama kmr wata mara hankali, da kyar ya dago ya rungumota murya can kasa yace "u re nt clean," ta rikesa tana girgixa masa kai tana hawaye ta kasa cewa komai sae mayar da numfashi da take, ya mike da kyar ya fice daga dakin, ta fada kan gado tana kuka a hankali tunda take bata taba shiga irin yanayin da ta shiga ranan ba, ta ma rasa meke damunta kawae, wnn abun dae da take mugun tsoro yau taji take mugun bukata kmr xata yi hauka, ta rasa inda xata sa ranta, ta dukunkune waje daya kmr mai jin sanyi, Aliyu ya bude dakin ya shigo ya karasa kusa da gadon rike da kofi a hannunsa ya dago ta, ta fada kansa tana kuka tace "don Allah ya Aliyu," ya kai mata kofin baki ta dauke kanta da sauri yace "magani ne" ta maida kanta jikinta na rawa ta shiga shan abinda ke kofi, ruwan lime ne, sae da ya tabbatar ta shanye snn ya kwantar da ita ya lulluba mata bargo ta xama kmr wata mara lfya, yaji tausayinta ssae gashi har uku ya xuba mata, da kyar ta samu bacci ya dauketa, snn ya mike ya dauki juice din ya shiga bathroom ya xubar ya fice daga dakin, dakin Safeena ya shiga ya biya bukatansa. Da safe tana wanka ya shigo dakin, ta kasa fitowa daga bathroom din duk da ta gama wani mugun kunyarsa take ji, to wae jiya wani jaraban ne ya sameta ita kam, tunda take bata taba experiance din abinda taji jiya ba, ya gaji da xamansa a dakin ya fice duk da yasan ta gama wankan fitowa ne kadae baxata yi ba gashi ta sa key, yana fita ta fito da sauri ta kulle dakinta da key, tana shiryawa gaban madubi taji muryarsa da safeena can kasa, ta mike da sauri ta bude curtain din window tana kallonsu, tana sanye da wasu shegun matsatsun kaya, ya bude mata mota ta shiga ya xaga shima ya shiga snn ya ja motar suka bar gidan, ta sake labulen ta koma gaban madubinta amma ta samu kanta da kasa yin komai kuma, ta mike ta koma kan gado tayi kwanciyarta tare da lumshe ido, har rana basu dawo ba, hkn yasa ta mike ta dauki Hijab dinta tasa snn ta sa takalminta ta fice daga gidan, mai gadi yace "ina xa ki," tace "bae gaya maka inda da exams yau ba," ya bude mata gate din ta fice tayi gidan Aneesah. . Aneesah tayi farin cikin ganinta ssae ta kai ta har bedroom ranar ma , snn ta kawo mata lemo, Aneesah tace "to ni yaushe kike son na shigo gidan ki kawas," Inteesar ta tabe baki tace "ae ni ba ni kadae bace, ni da kishiyata ce," Aneesah ta yo waje da ido tace "da gske, ke ce ta farko ko ta biyu," Inteesar tace "ta farko," Aneesah ta bude baki tace "shekaranku nawa da auren? Ko don baki haihu bne har ynxu," Inteesar tayi murmushi tace "watanmu biyar knn da aure," Aneesah ta dafata da mamaki tace "kai Inteesar, to dama ba auren soyayya kuka yi bne ko kuwa kinsan ba ke kadai bace," Inteesar tace "kusan auren xumunci aka mana, baya sona bana sonsa," Aneesah tayi shiru tana kallonta snn ta sauke ajiyar xuciya tace "ke xaki koya masa sonki Inteesar namiji fa wawa ne cikin lkci kalilan xaki ga kin mallake abunki sae kace ba mace ba Inteesar," Inteesar ta tabe baki tace "tabdi me xanyi da shi, hanyar jirgi daban ta mota daban, baya shiga harkata bana shiga tasa," Aneesah tace "to amma kuna plannin ne ko," Inteesar tace "kinga ni ki rabu dani da hirar nn, ina shakur?" ba don ran Aneesah ya so ba suka bar xancen suka kama wani hirar, ranar ma a gidan ta ci abincin rana, bata bar gidan ba sae kusan karfe shidda ta shiga ta tarar sun dawo, safeena na kitchen da dan littafinta da take boyewa tana hada masu girki shi kuma yana xaune falo yana kallo, ta hade rae xata wuce sama ya daka mata wani mugun tsawa da ya raxanata ta tsaya daga inda take tana masa mugun kallo ya mike ya karasa kusa da ita fuskarsa daure yace "daga gidan ubanwa kike," ta tabe baki tace "aikena kayi to," bata rufe baki ba ya watsa mata mari ta fasa ihu ta durkushe wajen tana kiran Abba, safeena ta leko tace "haba cweety nace ka rabu da ita yarinya ce bata san ciwon kanta ba tukun yarinta na damunta, meye kuma na dukanta, nasiha ya kamata kayi mata dear," Inteesar ta mike tana kuka tace "don uwarki sae ki xo kiyi min nasihar munafuka kawae jaka" yyi kanta ta fasa wani ihun ta saka gudu ta bar wajen ta haura sama tana ci gaba da rusa kuka kmr xata tsaga gidan, ranar hka taci kukanta ta koshi bbu mai lallashi ta gaji ta kwanta tayi bacci ba tare da ta ci abincin dare ba, karfe goma ya shiga dakin nata, ko wanka bata yi ba bare ta canxa kayanta karewarta ma kasa tayi kwanciyarta, ya daga ta ya cire hijabin jikinta snn ya mayar da ita kan gado yana kallon fuskarta, ya lulluba mata bargo ya kashe mata wutan dakin ya fita. Washegari kin fitowa tayi daga dakinta tana ta xaune har axahar bata karya ba, ya shigo dakin ya tarar da ita xaune kan darduma ta idar da sllh, ta mike ta shige bathroom ta bar sa nn tsaye, yyi tsaki ya fice daga dakin, ranar ma hka suka fita suka barta ita kadae a gidan, taci kukanta ta fito ganin yunwa na neman hallakata ta nemi abinda xata ci, har da na dare ta tanada don ba fitowa xata sake yi ba, Ana gobe xata je ta xana jamb dinta tun safe take ta karatu har kusan sha biyu bata karya ba, ta rufe biology text book din dake hannunta ta fito xuwa falo don neman abinda xata ci a xuciyarta tana cewa inda wnn mutumin kirki ne da ba shi xae koya min abubuwan da na manta a chemistry ba, tayi tsaki ta shiga kitchen ta tarar safeena ta daura girki amma bata kitchen din littafin da take amfani da tana koyan girki na kitchen din a ajiye da alamar tuwon shinkafa da miyar egusi xata yi ganin irin kayan miyan da aka jera a kitchen din ko wanne a cikin dan plate, inteesar ta girgixa kai tace "dakikiya kawae ynxu ina dauke littafin nn bbu abinda xata iya yi a nn," xata daura indomie kawae wata xuciyar tace ta dauke littafin kawae ta boye, ba shiri ta dauke littafin ta ma fasa girkin gaba daya ta fice da sauri ta haura sama a stairs suka hadu da safeena, safeena tayi mata wani kallon banxa tana karairaya, inteesar tayi dariya can ciki ciki a xuciyarta tace "i jez dey laf," ta shige dakinta, safeena na shiga kitchen ta nemi littafi ta rasa ta fito da sauri ta koma sama ta buga kofar dakin inteesar, inteesar ta fito tana gyara daurin dankwalinta a walakance tace "lafiya," safeena tayi mata mugun kallo tace "maxa fito min da kayana kar na nakada maki shegen duka a nn," inteesar tayi dariya tace "meye kuma kayanki," safeena na huci ta kasa cewa komai don wnn ae abun kunya ne a gunta anata tunanin, inteesar tayi tsaki tana yatsine fuska xata rufe kofar safeena ta fixgota ta kai mata mari, ta fasa ihu tace "wayyoo Abbana, wlh sae na rama," safeena ta kai mata wani marin, inteesar ta fasa wani kukan tace "don uwarki me nayi maki xaki dokeni, bnxa kawae dakikiya, karuwa da ke," Safeena tayo waje da ido tace "ni kike ce ma karuwa," Inteesar tace "ance maki din karuwa yar iska, uban waye bae san kinyi karuwanci ba," tayi kan Inteesar ta rufeta da duka dai dai nn Aliyu ya shigo gidan, ya haura sama da sauri da mamaki yana kallonsu ya fixge Safeena a fusace yace "ke jakar wace gari ce" tana huci tace "karuwa fa tace min Aliyu," ya watsa mata mari yace "ta ce maki din, sharri tayi maki, ko bakiyi karuwancin bane. Safeena ta bude baki da mamaki tana kallon Aliyu, cikin tsawa yace "get out kar na taka ki a nn, don uwarki idan kika ji mata ciwo kice baki sani ba ko me? Yar ki ce xaki kamata da duka hka ko sharri tayi maki" tsui tsui Inteesar ta bude dakinta a hankali ta shige tasa key, Safeena da hawaye ya gama wanke mata fuska don takaici ta kasa cewa komai ta juya ta bude dakinta ta shige da sauri, yyi tsaki ya bude dakinsa shi ma ya shiga, dariya Inteesar ta dinga yi kmr wata tababbiya a daki, kai Aliyu bae yi ba ko ke wacece ya disga ki gaban kowa ba komai bane a gurinsa, girkin da Inteesar bata yi ba knn ta ci gaba da karatunta da ta tuna abinda ya faru sae ta fashe da dariya, Safeena kam xamanta tayi a daki bayan ta kira uwarta ta gaya mata abunda ya faru girki kam ta fasa shi har taje takashe gas din ta komo sama, tana xaune tana naxarin abinda uwarta ta gama gaya mata tana murmushin mugunta Aliyu ya shigo dakin ta dauke kanta ya karaso kusa da ita ya xauna yana kallonta cikin lallami yace "haba bbyna, meyasa xaki kulata bayan nace ki daina, i've told yhu times wit out nmbr yarinyar nn ba ishasshen hankali gareta ba wllh, ni kaina tsoro take bani" Safeena ta mike a fusace tace "dnt tell me dat Aliyu, ynxu so nake kawae ka tashi ka maidani gidanmu," ya mike ya kamo hannunta yace "haba safeena wllh ina sonki kema kin san da hka, dukan yarinyar nn da kika yi ynxu baki san xae iya xaman min jaraba ba,"xata yi magana ya saka bakinsa cikin nata ya shiga kissin dinta ya dago kanta yana kallonta yace "yhu knw i luv yhu dear, ki bari ynxu xanje in mata magana," ya xaunar da ita ya fice daga dakin ta bi shi da kallo, ita kam Allah ya daura mata son Aliyu, tayi shiru xuciyarta na tafarfasa tanatunanin abinda xata yi masa taji ddi yau, ta sauke ajiyar xuciya tace "xanyi maganinka kuwa yau," shi kam yana fitaya buga kofar dakin Inteesar ta mike da sauri duk da tasan waye tace "waye," yace "ni kike tambayr waye," tayi tsaki ta koma tayi kwanciyarta, yyi shiru yana kallon kofar snn yyi kwafa ya shiga dakinsa. Ganin mugun yunwan da take ji yasa inteesar ta bude kofar a hankali ta fita xuwa falo, kitchen ta tarda shi tsaye shima yana hada tea ta juya da sauri xata koma ya fixgota, tace "wayyoo ni ka kyaleni," ya cakumota yace "ke kince kunnen kashi gare ki ko?" ta bata rae kmr xata yi kuka tace "ni ka kyaleni" yyi kwafa ya saketa yace "ni nasan maganinki," snn ya fice, itama tean ta hada taxo ta wucesa a falo tana takunta mai jan hankali ya bita da kallo, a dae dae stairs ta hadu da safeena, ta wuceta da sauri kmr mara gskya, safeena dae bata ce mata komai ba ta sauko kasa. Ganin ba girki safeena xata yi ba kuma yasan yyi mata laifi yasa Aliyu ya fita ya siyo masu abinci da daddare, bata nuna masa komai ba ta xauna suka ci abincin bayan ya kaima Inteesar nata, karfe tara tace masa xata je tayi wanka ta barsa nn falo ta haura sama sae da ta fara shiga dakinsa ta bude drawer dinsa ta dauki kwalin wani magani ta cire pills har guda hudu tana murmushi sanin ko na menene ta fice daga dakin ta shiga nata, tana jin ya bude dakinsa ta fito daga nata dakin da sauri ta shiga nasa yace "shine kika bar ni ni daya a falo ko bbyna," ta danyi murmushi bata ce komai ba ta xauna gefensa, ta kalli agogo tace "yau baxa ka sha coffee ba bby," ya duba agogo karfe sha daya saura yace "to kawo min dear," ta mike tana rangwada da shegun kayan baccin dake jikinta tace "ok bby," snn ta fita daga dakin, tana gama hada

Chapter 19 of 32