Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bae tambaya ba. kwanansu hudu a asibitin aka sallamesu badon likitocin sun so ba sae don Aliyu ya takura a sallamesa, duk da har lkcin yana yawan complain ciwon kai, gidansu Abbanmu suka sauka don likitocin sun ce kar ya bi hanya ynxu duk da bae so hkn ba, tuniAnty Nafeesa ta koma Nigeria da Faruuq, Haisam ne kadae ya rage tare dasu, Hajiya ma washegarin ranar da ya warke ta koma duk don taje ta sami safeena da uwarta, daki daya gari guda aka ba inteesar da Aliyu a gidan Abbanmu, ta ci gaba da kula da mijinta tana tilasta shi yana shan magungunansa, don baya son shan magani, komai ita ke masa, duk da sun dawo gidan Ant, Anty bata takurata da yaran ba stil gunta suke wuni su kwana sae dai ta kai su kawae ta basu nono ta kuma karbansu ta wuce, kirkinsu Anty da mijinta ya wuce misali bbu abinda suka ragesu da komai enuf kmr suna gidansu, amma duk da hka Aliyu duk ya damu xae koma gida, hkn yasa Abbanmu yace to su bari ya gama abinda yake nn da sati dayasae su tafi gaba daya, bae yi masa musu ba ya yrda ya kara sati daya a india, suna daki ana jibi xa su tafi bayan ta gama basa abinci ya sha maganinsa ta rungumesa jikinta don hka take masa har yyi bacci, sae dae yyi murmushi baya ce mata komai, yau kam shafata kawae yake kansa na kan kirjinta idonsa lumshe kuma bata hanasa ba duk da gabanta faduwa yake amma bata nuna ba, bubbuga kofa aka yi hade da sallama ta xabura da sauri, shima ya bude idonsa da suka canxa launi ya amsa sallaman jin kukan twins, yar aiki ce ta shigo dakin ta karasa kusa da gadon ta kwantar dasu da yake ta saba da inteesar ssae don ita ma yar Nigeria ce tana dariya tace idan an gama ji da baban bbie, Anty tace aji da bbies," inteesar tayi murmushi tace "to Anty," matar ta fita ta kullo masu dakin, ya kankameta jikinsa fuskarsa a kan kirjinta yace"i love yhu my inteesar," a hankali tace "i love yhu 2 my Hydar," ya dago yana murmushi ta rufe idonta da sauri ya daura bakinsa kan nata ya shiga kissn dinta, bbies nata kuka, da kyardon ita ma ta fara dauke wuta ta turasa daga jikinta tace"bbies suna kuka" ya fada gefen gado ya kwanta yana mayar da numfashi yace "ni ke na sani ba bbies ba," ta hade rae tana kallonsa tace "tunda kaga yaran nn baka taba daukarsu ba, sae naga kmr baka sonsu," ya juya yana kallon yaran da suka xama wasu manya abun sha'awa wata daya da haihu, bbu abinda suka bari nashi kmr an tsaga kara, ya dan yi murmushi ya kwasosu ya xuba su jikinsa 4 d first tym, yana kallon inteesar yace "da haushinsu nake ji bbyna sae naga kmr sune suka cutar min dake suka baki wahala" inteesar tayi shiru batace komai ba don har lkcn bae san safeena bace tayi mata asiri wae kmr ynda Hajiyrsa da inna ke fada. Da kansa ya ciro masuabincinsu yana kallon cikin idonta ta kauda kanta sakamakon wani yarr da taji, ya rungumeta ta baya ta rike Hassan din da ya daura mata a cinya, dayan kam ya hkura yyi shiru, da kansaya shiga basa nonon ta bayansu, yana kissin din wuyarta ta turasa da kyar ta kwace breast dinta tace "ka bari kar ya kware," ta rungume danta ta shiga basa nonon a nutse. Yyi tagumi hannu bibbiyu yana kallonsu yana murmushin da shi kansa bai san dalilin ba . ... Ranar da xasu bar india inteesar nata shirya kayan bbies din da Anty tace ta hada gaba daya su tafi dasu don da bata yi niyyar su dauki ko wani kaya ba, Aliyu ya fitada Abban Najeeb da ya taso tun daga Nigeria yaxo india sbda shi kuma tare xasu bar india ranar, inteesar ta gama shirya kayanta da na bbies gaba daya da na Aliyu, suna kwance kan gado suna ta rigima duk sun isheta ita kam tana ganin kkrin Anty da bata gajiya da su, gashi bata iya daukansu gaba daya lkci daya ba don nauyinsu tubarkallah in ka gansu kmr yaran da suka yi wata uku, Hassan ta fara dauka xata kai ma Anty kafin ta dawo ta dauki Hussainin ta duba daki bata ga Anty ba hkn yasa ta sauko xuwa falon, Anty na xaune da bako a falon, ta karasa cikin falon da sallamarta kmr xata yi kuka tace "Anty ni wllh yaran nn sun isheni sae suyi ta kukan karya suna damuna kuma ba yunwa suke ji ba," Anty tayi dariya ssae ta karbeshi daga hannunta tace "ni basu isheni ba da ma ki bar min su wllh," inteesar tayi dariya ta juya xata je ta daukodayan suka yi ido hudu da wani mai kama da Aliyunta a xaune a falon, ta kasa daina kallonsa, he looks familiar, ta dauke kanta da sauri xata bar wajen taji yace "fateema" da mamaki ta juya tana kallonsa, sae a snn ta tuna sa, ofcourse Dr din da yabata maganin cire ciki ne a Nigeria, gabanta yyi mugun faduwa, ta bar falon da sauri, Anty ta shiga cewa "A ina kasanta Sadeeq," ya bita da kallo har tabace masa snn yace "Anty ina kika san yarinyar nn,"inteesar bata sake saukowa ba har ya bar gidan gabanta sae faduwa yake, Anty ta shigo dakin tana kallonta ta xauna snn tace "meyasa kika yi hka Fateema," inteesar ta sunkuyar da kanta sae hawaye, Anty tayi shiru snn tace "to Allah shi kyauta ya kuma yafe mana kurakuranmu, Sadeeq kanina ne uwar mu daya ubanmu daya, a Nigeria yake aiki, yyi min bayanin komai," inteesar ta share hawayenta tace "baxan ma sake ba Anty, ki basa hkurin karyan da nayi masa nasa ya aikata abinda bae dace ba, duk da gashi at lng lst sae da na haifesu," Anty ta rungumeta tace "shknn ya isa fateema ki daina kuka, nima nayi masa fadan abinda yyi bae dace ba," kai kawae inteesar ta gyada mata ta dauki Hussain ta fita tana cewa shima yau xae koma Nigeria jirgi daya xamu shiga idan Allah ya yrda. Ranar lahadi karfe goma saura su inteesar suka sauka kano daga lgs, a airport suka rabu da Abban Najeeb, Sadeeq ma daga nn suka rabu bayan yyi ma Aliyu alkawarin xae kawo masu visit, shi yyi ta rainon Hassan a jirgi yaran sun shiga ransa ssae, inteesar tayi masa gdya ya shiga taxi ya wuce, Haisam ne yaxo daukansu daga airport, ya gaida abbanmu cikin ladabi snn ya gaidaAnty, inteesar ta gaida shi tana murmushi ya juya yana hararan Aliyu dake murmushi suka kama hanyar gida gaba daya, falon Abba Abbanmu ya sauka, inteesar da Anty kuma gun inna suka sauka Hajiya tayi welcmin dinsu ssae ta rasa inda xata sa inteesar da ya'yanta ita ta hada masu breakfst aka kai ma Abbanmu nasa can falon Abba, inteesar da Anty suka yi tare, inna sae xuba take masu ta rasa inda xata sa bbies da suka xama kmr wasu yaran larabawa don kyau, momy ta xo tayi masu sannu daxuwa cike da fara'a mai sunanta na nane da ita, bata yi wani miss din iyayen nata ba, yarinyar ta rungume inteesar snn ta rungume uwarta tana yi masu sannu da xuwa ta dauki twin, Anty Nafeesa ma ta xo yi masu sannu da xuwa baki har kunne, karfe biyar na yamma gaba daya suka hallara falon Abba don Anty sunce ranar xasu tafi kaduna don suna da gida a can, har dasu inna gayyar sodi tunda ba'a gayyace ta ba, inteesar na dakin Aliyu lkcn kursum ta kwankwasa tace Abba na kiransu, a tare suka shiga falon sae kunya ya kama inteesar taxauna gefen Anty, shi kuma ya xauna gefen Haisam,Abbanmu yace "ina twins suke," inteesar tace "sunagun momy," Abba yace "ina momyn take je ki ki kirata," inteesar ta mike ta fita xuwa ta kira momynta, ta gama shirya yaran knn ta shigo tace"momy Abba na kiranki," momy tasa hijab ta dauki daya ita ma ta dauki dayan suka fito tana cewa"momy ihsaan fa wae," momy tace "tana gidan Zainab anjima xasu xo da daddare, ita ma laulayi take," inteesar tace "Allah sarki Zainab, Allah ya bata lfya," inteesar tayi sallama ta shiga falon hka ma mmy, cak momy ta tsaya daga bakin kofar idonta a kan Abbanmu da shima nasa idon na kantamurmushin da yake dauke da a fuskarsa sakamakon hiran da suke yi da Abba ya bace nn da nn, ya mike tsaye da kyar yana kallonta cikin wani irin yanayi yace "Zai zainab," nn da nn hawaye ya cika idon momy ta juya da sauri ta bar falon, Abba ya mike yana kallonsa da mamaki, da kyar dae yace"Alhaji umar ina kasan Zainab din," Abbanmu da ya rikice lkci daya yace "wllh wllh matatace," ya juya yana kallon inteesar, da sauri ta mike ta fice daga falon, Abba yace "a ina ta xama matarka" Abbanmu ya girgixa kai yana kallon Anty dake kallnsa da mmki yace "matata ce wllh" inna ta mike tayo waje da ido tace "yau naga tsiya a ina ta xama matarka ni Rahmatu, Bukar ina Kaso wanna tabbaben. Inteesar_____2*16 . Khaleesat Haiydar . Abba ya juya yana kallon inna don takaici ya ma rasa me xae ce mata, ita ko ta dage sae an gaya mata inda aka samo Abbanmu, a fusace Anty Nafeesa tace "don Allah idan baxa kiyi shiru ba inna xa mu bar maki falon nn, haba don Allah" shi kam Abbanmu kallonta kawae yake daga tsayen da yake, Abba yace "to Alhaji Umar ae bayani xaka mana ta ynda Zainab ta xama matarka," Abbanmu ya koma ya xauna ya kasa cewa komai har lkcin idonsa na bakin kofa kmr xae bita, sae da Abba ya kuma maimaita masa tambayar snn a hankli yace "matata ce," a fusace inna tace "yau naga abinda ya isheni don Allah a fitar min da wnn mutumin na daina ganinsa," Abba ya hade rai yace "don Allah baaba ki fita ki bamu waje, dama bbu wnda ya gayyato ki nn," ya maida dubansa ga Abbanmu yace "to ae bayani xaka mana," Abbanmu ya dan yi shiru snn yace "matata ce kusan shekaru sha takwas da suka wuce baya," kowa yyi shiru yana kallonsa, Abba yace "to me ya raba ku," ya girgixa kai yace "wllh bamu rabu ba," Abba yace "a wani garin kuke lkcn tana matarka," Abbanmu yace "Misra," Abba yace "to me ya dawo da ita Nigeria," Abbanmu yyi shiru na dan lkci snn yace "wllh nima ban sani ba," Anty ta mike ta fita waje, Abba bae kuma cewa komai ba ya juya yana kallon inna da ta cika tayi fam sae huci take, Abba ya mike yace yana xuwa ya fita, a daki inteesar ta tarar da momynta xaune tana kuka, ta sulale gabanta xuciyartana bugawa tace "momy waye shi," sae da momy ta dau lkci snn tace "shine mahaifinki inteesar," inteesar tayi shiru hawaye na bin kuncinta tana kallon momynta da kyar tace "shine Abbana," momy ta gyada mata kai, inteesar ta fashe da kukan da bata san dalilinsa ba, kukan farin ciki ne, na bakin ciki ne ta kasa ganewa, ynxu Abbanmu shi ya haifeta, sallamar Anty yasa gaba daya suka juya sun kallon bakin kofa, har daki ta shigo ta xauna tana kallon momy tace "kiyi hkuri Zainab, nasan da lbrinki da ddewa, amma karki ga laifin Umar, kullum kina ransa, kuma bbu inda bae shiga ba don nemanki though nasan ba lallai ki yrda da abinda nake gaya maki ba," momy ta kasa ce mata komai inteesar kam sae kuka take, Anty ta rungumeta tace "Allah sarki inteesar dama yace min yana ganin Zainab dinsa a idonki," Abba yyi sallama ya shigo falon snn ya karasa cikin dakin, mikewa Anty tayi ta ja inteesar suka fita, falon ta mayar da ita Abbanmu sae kallonta yake da ganinsa kasan yana cikin damuwa a lkcn, inteesar ta kasa daga kai ta kalleshi sae hawaye take, Aliyu ya girgixa mata kai alamar ta daina kukan, inna ta tabe baki tace "to yau dae xan ga karshen wnn tsiya," bbu wanda ya tanka mata a falon, bayan kmr minti goma Abba ya dawo falon da momy, Abbanmu sae kallonta yake, Abba ya juya yana kallonsa yace "to ynxu Alhaji Umar ya kke son ayi don dae ynxu Zainab matata ce," inna tace "ya ko xa'ayi," da sauri Abbanmu yace "ni bance ayi komai ba," Abba yace "to me ya rabaka da Zainab can misira, har ta dawo nn Nigeria" Abbanmu yace "wllh wllh ban sani ba, ni dae nasan auren soyayya muka yi kuma a katsina na aurota ta dalilin wani abokina, amma lkcin ina da mata a nn egypt, danginta suka bani ita bayan anyi komai muka tafi egypt, iyayena yan can ne amma sun rasu, to a gskya nasan matata ta farko bata da kirki ko kadan, kuma Zainab tana da hkuri fiye da ynda mutum xae yi xato, snn ni din Allah yyi ni mai dukiya watan mu takwas da Zainab na rasa abinda ya faru...." da sauri inna ta dakatar da shi a fusace tace "karya kke, ca tayi guduwa kayi ka barta," Abbanmu yace "wllh baaba ni ban san ya akayi ba," ya sauko kasa yana kallon inna hawaye cike idonsa yace "ki tambayeta mama, ni ban taba cutarta ba ko sau daya a xaman da muka yi, wllh bbu inda ban shiga neman Zainab ba can katsina da naje danginta ca suka yi basu ganta ba, don Zainab marainiyace," sae a snn inna ta fara matsar kwalla tace "to nice nn na tsinci Zainabu da tsohon cikin inteesar, na kuma taimaka mata don na gaji taimako a wajen ubana, kuma duk wanda baya taimako ya tabe, ni nn bbu abinda bn yi ma Zainabu ba har ta haihu nasa dana yyi mata suna, tace min bata da kowa sae Allahnta se kai, nn na tilasta Bukar ya biya mana kudin jirgi muka je nemanka amma sae muka tarar ma wae har ka sayar da gidan" Abbanmu sae yi magana inna ta dakatar dashi a fusace tana kuka wiwi, "yi min shiru, to wae ma tunanin uban me kke ka gudu ka bar mata da tsohon ciki," ta share hawaye ta tsuke fuska ta rungume hannayenta ta rike haba tana Kallonsa tana jira ansa . .... Abbanmu ya rasa me xae ce ma inna ya sunkuyar da kansa kawae, Abba yace "haba inna ynxu ai komai ya wuce, don Allah ki bar maganar nn hka," Inteesar ta kasa xama a falon tana kuka har lkcn ta mike ta fita, Abbanmu ya bita da kallo shima hawaye a nasa idon, Momy kam kanta na kasa bata dago ba tunda ta shigo, mikewa Aliyu yyi shima ya fita daga falon, bangarensu tayi don hka ya bita da sauri har ya isketa ya jawota jikinsa yace "haba bbyna don me kika fita," kasa ce masa komai tayi sae kuka take, ya kama hannunta yyi bangarensa da ita suka shiga bedroom dinsa ya xaunar da ita kan gado yace "yau ranar farin ciki ne a gareki kanwata, bae kamata kiyi kuka ba gode ma Allah xaki yi," bata ce komai ba ya rungumeta yace "kar ki sake wnn kukan dear," gyada masa kai kawae tayi tana kirjinsa, kursum tayi sallama bakin kofa, ya mike ya fita xuwa falo snn ya bude kofar, Hussaini ne a hannunta yana kuka, ya karbesa tace "ina xuwa na dauko dayan shima kuka yake," ta juya da sauri ya shiga daki ya mika ma inteesar shi, ta karbesa, snn ya koma ya karbo dayan ya rufe kofar ya dawo ya xauna gefenta yana kallonta tana ba Hussaini nono, a hankali yace "wani suna xamu sa masu Wife?" tayi shiru bata ce komai ba, ya jinginar da kansa jikin nata yace "na lura kin kasa sakin jikinki da ni ko fateema," tayi murmushi tace "eh mana, ae kai ko...." da sauri ya rufe bakinta yace "no fateema, let bygones B bygones, plss," ta kwantar da yaron hannunta ta juya tana facin dinsa xata yi magana ya rungumeta a hankali yace "ban san me xan maki ki yrda ina sonki ba fateema" hawaye ya cika idonsa yace "ki yrda dani inteesar ni din me sonki ne da gskya wllh," ta gyada masa kai tace "na yrda," ya dago kanta yana murmushi yace "thank yhu fateema," ita ma tayi murmushin snn tace "Sunan Abba nake son a sa ma Hassan, Hussaini kuma ka xabi sunan da kke so" yyi murmushi ya rungumeta bae ce komai ba. washegari da safe inna tasa inteesar taje gun mahaifinta su gana da kyau tunda momy ma tace ta yafe, bata yi mata musu ba taje ta samesa a falon Abba, shi kadae ne xaune a falon da yan biyu, ta karasa ta xauna ta gaishesa kanta a kasa, ya amsa yana murmushin jin ddin ganinta, sun dde suna hira da Abban nata tana basa lbri iri iri yawanci duk akan inna har lkcn sllhn azahar yyi yace xae tafi masallaci ta dauki yaranta tayi gun momynta dasu. Washegari da safe aka rada ma twins suna, Hassan aka sa mashi Abubukar Sadeeq, Hussaini kuma aka sa mashi Umar Faruuq, sunan Abbanmu, rago hudu aka yanka masu, kuma ba ayi taron suna ba, su Anty da Anty Nafeesa da wasu kawayen Hajiya ne suka yi aikin naman, kwanan Abbanmu da Anty uku a gidan suka fara shirin komawa india bayan komai ya daidaita, ya ba twin kyautan million daya, inna ta karbe wae xata ajiye masu har su girma, yyi ma inna ma kyauta mai yawa, snn ya mallaka ma inteesar gidansa dake kaduna, Anty Nafeesa ta shiga gyara inteesar don itama xata koma dakinta kmr ynda Abba yace, ranar da Abbanmu da Anty suka wuce ranar Aliyu ya dauki matarsa da yaransa da daddare suka koma gida bayan Abba yyi masu nasiha ssae kan sun xauna lfya, yana rike da yaransa tana biye dashi a baya suka shiga gidan, ya kwantar dasu kan kujera ya rungumeta yace "New life inteesar," murmushi tayi bata ce komai ba ta haura sama, komai na gidan sabo ne, har dakinta ma an canxa mata furnitures, ta fito daga wanka ya shigo dakin rike da twins yana mata wani irin kallo yace "yunwa suke ji dear," ta karbi Hussaini a hannunsa, ya taimaka mata ta hada masu madara tana ba daya, shima yana ba daya. Wani sabuwar rayuwa me cike da tsan tsan so da kaunar juna suka bude a gidan, Aliyu ya xama kmr bawanta gashi bae kaunar yaga ta bata rae nn da nn yake rikicewa, duk yamma sukan shiga garden da twins dinsu su xauna, yana karanto mata diary dinsa tun daga farko, wani guri tayi dariya wani gun kuma tayi kuka, wani kuma taji haushi, abun dae ba'a magana, tunda suka dawo gidan Aliyu bae taba nuna mata yana son kusantarta ba sbda tsoranta, duk da daurewa kawae yake don mugun sha'awarta ke dawainiya da shi. Ko kadan ba ita ke wahala da yaran ba komai shi ke masu, nono kadae ne tsakaninta dasu duk da tasan ba dorewa hkn xae yi ba don dole xae fara aiki, satinsu hudu a gidan ita dae bata ji yyi mata maganar safeena ba kuma bata ganta ba, kasa daurewa tayi suna xaune da daddare ranar ta tambayesa safeena, ba tare da ya kalleta ba yace "Hajiya tasa na bata takardarta," inteesar bata ce komai ba taci gaba da kallonta, karfe sha daya ya dauki twins da suke kira da Sudais da Shuraim, yaje ya kwantar dasu snn ya sauko falo ya xauna gefenta yana kallonta a hankali yace "na lura wahala kawae kike bani a gidan nn inteesar," ta juya ta hararesa tace "ta yaya nake baka wahala," ya dagata sama yace "bari in nuna maki," kan tace komai ya haura da ita sama ya bude dakinsa ya shiga ya kwantar da ita kan gado yana kallonta yana murmushi yace "yau xamuyi 1st nyt dinmu bbyna, Jst assume it to b so. Inteesar ta mike xaune da sauri tace "A'a ni bana sooo" bae ce mata komai ba ya juya ya fita ta bi sa da kallo jikinta yyi sanyi, a nata tunanin ransa ne ya baci, ta dde xaune har lkcn idonta na kan kofa snn ta mike ta shiga bayi a xuciyarta tace ita xata bi sa, wanka ta kuma yi ta wanke bakinta, ta fito ta xauna gaban madubi daure da towel ta gama shafe shafenta na turarrukan da inna da Anty Nafeesa suka bata snn ta ciro wani kayan bacci pink colour mara nauyi mai hannun singlet iya cinya ta saka ta daure gashinta da ribon, tayi still tana kallon kanta gaban madubi tayi kyau ssae komai na jikinta a bayyane yake sae taji kunya ya kamata ta girgixa kai, aa baxata iya fita hka ba, ta bude drawer ta fito da da wani kayan baccin tana kallo ta ji an bude kofa ta juya da sauri tare da sakin kayan hannunta don sae da taji tsoro, singlet ne da short nicker jikinsa yana rike da bakar leda da plate, ya wara dara daran idonsa yace "kai amma amaryar nn tawa bata da kunya" inteesar ta juya da sauri ta durkushe wajen ya karaso gabanta yana mata wani irin kallo ya dagota yana kare mata kallo kunya ya rufeta ta kasa kallonsa yana rike da ita suka dawo tsakiyar dakin ya xaunar da ita kusa da gado yana kallonta snn ya mike ya bude drawer dinta ta bisa da kallo mayafi ya fito da pink colour ya dawo gabanta ya durkusa ya lullubeta da shi har fuskarta, snn ya xauna yana murmushi murya can kasa yace "Assalamu alaikum ma'abociyar kyau da hkuri," bata ce komai ba sae kallonsa take ta cikin mayafi duk jikinta yyi sanyi, a hankali yace "baki amsa sallamata ba cweet wife," a hankali ta amsa masa, yyi murmushi, ya dan bude mayafin yana kallon fuskarta ta sunkuyar da kai da sauri ta kauda kanta, ledar ya bude ya ciro kaxa da hollandia yoghurt ya mike ya dauko cups ya xuba masu drink din ya bude kazar yana kallonta yace "bismillah amaryata," bata ce komai ba ya matso kusa da ita ya daga mayafin ya daura kanta snn ya shiga bata naman, bata yi masu ba ta karba, yasa taci naman ssae shima yaci snn ya dauki drink din ya kai mata baki ta bude a hankali ya shiga bata har sae da ta kauda kanta tace ya isheta snn ya sha nashi, matsar da ledan kaxar yyi da drinks ya dago ta ya xaunar da ita kan gado ya durkusa gabanta a hankali yace "kada Allah ya nuna min ranar da xan bata maki rae ko nayi maki ba dai dai ba inteesar," bata ce komai ba ya mike ya duka dab da fuskarta ta dauke kafafuwarta daga kasa ta daura kan gadon snn ta koma can tsakiyar gadon ta xauna har lkcn mayafi na jikinta, yyi murmushi ya kashe wutan dakin ya hau gadon shima ya xauna kusa da ita yana kallonta kanta a kasa, a hankali ya cire mayafin jikinta ya ajiye ya tsura mata ido ta rufe fuskarta da tafin hannunta, ya jawota jikinsa a hankali yace "i love yhu my inteesar," ta kasa cewa komai ya kwantar da ita a hankali ya shiga yi mata rada a kunne, "kiyi min kuka bbyna, kice min baki so kina tsoro bbyna, ki rikice min bbyna, kisa na rude naji tausayinki amma na kasa kyaleki nayi ta rokanki har na kai ma cimma burina bbyna, i just want 2 imagine yau na fara saninki xan dauki wnn moment din kmr daren farkon mu bbyna, don Allah ki bani hadin kai" bae jira tace komai ba shiga kissin dinta nn da nn jikinta ya dau rawa kmr sabon shiga, bae damu ba don dama hka yake so, ranar taga ta kanta a hannun Aliyu, bae sarara mata ba sae da yaga ta fara kukan gske don ta gaji, duk ya rikice mata ya kankameta yana lallashinta ynda kasan amaryar gske, yyi ta sa mata albarka, ko kulasa bata yi ba taja bargo abunta don bacci take ji, ya mike ya shiga bayi kan ya fito har ta fara bacci ya dagota yana kallon kyakkyawan fuskarta ta bude ido a hankali tana kallonsa yace "kar kiyi bacci bbyna bari na gasa maki jikinki xaki fi jin ddin baccinki," ta galla masa harara tace "ca nayi maka bani da lfya," ya kashe mata ido yace "to nasani ko na ji maki ciwo ne naji kina ta ihu kina kiran inna," sae abun ya bata dariya tace "kaji ka da sharri, ko dae kai ne ke ta ihu ni tsoro ma ka bni," ta fashe da dariya, yyi murmushi yana gyada kai yace "yyi maki kyau, amma ynxu tashi nayi maki wanka kafin kiyi bacci," ta juya tace "ni ka kyaleni ba ynxu xanyi wanka ba bacci nake ji," yace "idan yara suka tashi anjima kiyi ya dasu," ta juya tana kallonsa da mamaki tace "abincin su xan basu mana," ya girgixa kai yace "baxa ki taba min yara da janaba a jikin ki ba," bae jira me xata ce ba ya kinkimeta sae cikin bayi, ya sakata ciki ruwan xafi, ta dan yi ihu a tsorace tace "meye hka ya Aliyu," ya kashe mata ido yace "kin manta ke amarya ce gasa ki xanyi," dariya abun ya bata, ranar a tare suka yi wankan taki bude idonta don mugun kunyarsa take ji, ya daura towel snn ya nadeta da wani towel din ya fita da ita suka xauna gefen gado ya rungume abarsa a hankali yace "i promise 2 love yhu 4 ever my inteesar," kasa ce masa komai tayi kanta na kirjinsa. Bayan shekara biyu inteesar ce tsaye kitchen tana girka ma su Sudais indomie wajajen karfe tara, Aliyu na sama da yake ranar lahadi ce, twins kuwa na balcony suna build din castle da bricks din wasan su sae surutu suke da turanci duk sun cika gidan da hayaniya, yaran sun girma ssae kyawawa dasu kmr yaran larabawa komai nasu abun sha'awa ne, gasu da shegen wayo kmr ba yaran shekara uku ba, daurewa kawae inteesar take don tana dauke da karamin cikin da take ta boye ma Aliyu, shi kam kallonta kawae yake sae ma take basa dariya bata san ya riga ta sanin abunsa ba, tsit taji bata sake jin hayaniyarsu a balconyn ba, ta danyi murmushi ta leko falo don tasan baxae wuce Aliyu ne ya sauko suka yi shiru ba don baya toleratin noise makin dinsu discipline dinsu yake ssae,, bata ga Aliyu a idan tayi tunanin xata gansa ba wato bakin kofar falo, don hka ta karasa balconyn da sauri taga ko sun fita xuwa garden ne, safeena ta gani durkushe gabansu tana kallonsu su ma sun yi shiru suna kallonta, Sudais yace "yhu re interruptin our play" Safeena tayi murmushi a sanyaye tace "am srry neva meant 2, where is yhur mom?" Shuraim ya juya da sauri xae je kiranta ya ci karo da ita bakin kofa, yace "Anty we have a stranger in here," Safeena ta mike tsaye tana kallon inteesar a hankali tace "ina kwana," inteesar ta kasa cewa komai ta dauke kanta gabanta na faduwa, hawaye taji ya cika idonta ganin ynda Safeena ta koma kmr ba ita ba, daga bayan ta taji Aliyu nacewa "bbyna baki gama hada kayan ba fa, ko kin gaji ne," shiru

Chapter 31 of 32