Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mikewa amma ta kasa, a hankali muryarta na rawa tace "yunwa nake ji ya Aliyu," ya juya yana kallonta kmr ya rufeta da duka ya girgixa kansa xuciyarsa na suya, cike da takaici yace "ta kasheki," snn ya juya yyi kwanciyarsa. Da rarrafe ta fita daga dakin ta shiga nata ta hada tea jikint a na rawa, amma duk yunwan da take ji sae ta kasa shan tean, hka ranan ta kwana a wahale. Washegari monday bbu yabo bbu fallasa ya shigo dakinta da safe yace ta shirya xasu gida, gabanta ya shiga faduwa, tana kallonsa daga kwancen da take tace "baxan iya ba ya Aliyu" wani tsawa ya daka mata yace "kada Allah yasa ki iya din, jahila kawai, Allah ya baki sa'a na dawo naga baki shirya ba," ya fice daga dakin, kuka ta shiga rerawa a hankali, ta kasa tashi daga kan gadon duk jikinta yyi tsami, cikin ikon Allah ta mike da kyar ta shiga ta wanke baki ta canxa pad, don bata da karfin wanka, ta fito jikinta na rawa ta xura doguwar rigarta snn ta saka hijab ta sauko yana falo yana jiranta bae ko kalleta ba ya mike yyi hanyar fita tana biye da shi a baya kmr iska xae kadeta ta fadi, duk tayi mugun rama daga jiya xuwa yau, a sanyaye ta bude bayan mota ta shiga bae ko kalleta ba ya shiga driver sit ya ja motar suka fita daga gidan, har suka isa gida bae ce mata ba ita ma bata ce masa ba, gabanta ya shiga faduwa don bata san me xata shiga ta tarar ba, da kyar jikinta a mace ta fito daga motar ta jira shima ya fito, bae ko kalleta ba ya nufi gate xuciyarta na harbawa da sauri da sauri ta bi bayansa suna shiga gidan falon abba taga ya nufa, ita dae tana ta biye da shi a baya kmr jela, a bakin kofar Abba suka ci karo da momy xata fito daga falon, inteesar ta koma baya da sauri kuma a tsorace, momy ta bi ta ta cafketa, ihu ta fasa a tsorace momy ta shiga xuba mata mari tana duka kmr an aikota, kuka ta dinga rusawa tana ihu a gidan Abba ya fito da sauri yana kallon momy a fusace yace "kina da hankali kuwa Zainab, meye hka kike yi," ko kallonsa bata yi ba sae jibgarta take tana tumble da ita, ita ko bata fasa ihu da kukan da take ba, Aliyu ya dauke kansa ya koma gefe ya tsaya ya lumshe idonsa, su Hajiya da umma duk suka fiffito daga dakunansu su Rahma duk sun tafi sch, duk irin masifar da Abba ya dinga yi ma momy ransa a bace kan ta sake inteesar kin sakinta tayi, har sae da ta kai ta kasa, su Hajiya da umma dae na tsaye sae murmushi suke, Hajiya na cewa "to wnn abu dae idan bakintsa mata aka yi ba taya yar mitsitsiyar nn tasan wani cire ciki" daga nisa suka ji Muryar inna tana tahowa da gudu tana cewa "muryar waye nake ji hka kmr ta Inteesar uban me ake mata," ta karaso tana haki, tana ganin abinda momy ke yi ma inteesar tayo waje da ido ta fasa ihu "meye hka xan gani Zainabu, akuya kika samu ko me? kashemin ita xakiyi don uwarki," sae a snn momy ta saketa, inna ta fashe da kuka tana kallonsu gaba daya tace "amma dae Allah ya isa ban yafe maku ba, ynxu Bukar har da kai aka taru xa a kashe yar mala'ikan Allahn nn don ta xubar da wani wahalallen cikin Aliyu dake neman aikata lahira, to duk shegen da bae fasa dukanta ba bae haifu cikin uwarsa ba " ta dago inteesar dake ta rusa kuka ita ma tana nata kukan ssae tace "Allah ya isar maki kuma ciki kin isa ne yasa kika xubar da shi, mu je ga ruwa can na daura xan maki wanka" taja ta tana dingishi suka yi sashinta tana huci, Aliyu ya juya yana kallon Abbansa da ya bi su da kallo shima, snn ya girgixa kai kmr xae hadiye xuciya yyi hanyar fita daga gidan Abba ya kirasa. Allah sarki Babana Aliyu, but ol d same Allah shi kara, na ma tuna ko waye kai da. . Inteesar na xaune falon inna tana cin tuwa da lafiyayyan miyan vegetable da inna tayi mata yaji nama da kifi da ganda, sae tura abunta take, ga farfesun kayan ciki da na kai gabanta ga fura mae sanyi shima duk a gabanta, inna ko na xaune gefenta tana tayi mata hira tana kyalkyala dariya, inteesar dae hankalinta na kan abincinta har ta manta rabon da ta ci tuwo sae indomie kmr mayya kullum, tun safe da inna ta ja ta tayo sashin ta da ita bbu wanda yaga fuskar xuwa ya samesu har Abba, Aliyu kam Abba ne ya hanasa xuwa don yasan halinsa, Haisam ma baram baram suka yi da inna daga yaxo yi ma inteesar fada, ransa a bace ya bar falon, sallamar faruuq yasa inteesar ta jawo hijabinta da sauri don daga ita sae yar shimi, suka amsa masa sallaman inna na washe baki ya nemi guri ya xauna ya gaida inna ta amsa cike da jin ddi ta mike ta kwaso masa lemo a fridge dinta, inteesar ta gaishesa tana murmushi ya amsa ba tare da ya kalleta ba, tace "ya faruuq Zainab fa?" yace "tana lfya," ta ci gaba da cin tuwonta inna nata yi masa hira mara tushe sae binta yake da uhm, sae da ya jira don kanta tayi shiru snn ya hade rae yana kallon inteesar yace "inteesar wajen ki naxo," ta dago tana kallonsa hka ma inna, yace "am vry disappointed in yhu inteesar, never knew yhu 2 b foolish...." da sauri inna tace "meye wnn kke cewa, ka fada wanda xanji mana," ya juya yana kallon inna yace "Haba inna, ynxu abinda inteesar tayi ta kyauta knn da ba ki son a mata fada, rae biyu fa ta hallaka dan wauta irin nata, kuma ace baxa a mata magana ba" a fusace ya karasa maganar, inna ta dafe kirji kmr xata yi kuka tace "rae biyu fa kace, dama yan biyu ne knn?" faruuq yace "au ke da duk abinda ake baki sani ba inna," inna tayi narai narai da ido tace "ni ina nasani, ynxu yan biyu ta xubar faruuq, ko daya bae rage ba," ta juya tana kallon inteesar dake ta tura tuwanta abunta fuskarta a daure, can ta juyo tana kallonsa tace "to hka Allah ya kaddara sae a dau na annabi, yarinya dae bata gama mallakar hankalinta ba bare ace xa a mata fada ynxu, kawae sae dae ace Allah shi kyauta, su kuma Allah ya ji kansu," faruuq don takaici kasa cewa komai yyi, can dae yace "meyasa xaki dinga cewa hka inna, inteesar din ce yarinya ynxu," inna ta hade rae tana kallonsa tace "naga dae alamar kaima ka fara xama munafuki, tashi ka ban waje idan har wnn maganar ce ta kawo ka, to jefar da ita kuke son nayi kome, dama Allah yyi yaran baxa su wuce wata uku a cikinta ba, don hka ku shafa ma jikata lfya" faruuq ya mike ransa a bace yace "to inna, Allah ya baki Hkuri ni xan koma," tace "eh Allah ya kiyaye," ya juya ya fice daga falon, inna ta ja dogon tsaki tace "munafukan bnxa kawae, ci ki koshi kije ki kwanta ina fatan dae jinin ya tsaya gaba daya ynxu." Da daddare inteesar na kwance gefen inna duk da fankan dake aiki a falon tana tayi mata fiffita suna hira, Abba yyi sallama, inteesar ta mike xaune da sauri tana kallon inna, inna tace "tsaya tsaya kar ka shigo min," ta juya tana kallon inteesar murya kasa kasa tace "maxa tashi ki shiga daki," da gudu inteesar ta shige daki ta rufe kofa, inna ta rungume hannuwanta tana sakace hakori tace "yauwa xaka iya shigowa" Abba ya shigo dakin da sallamarsa ya xauna ya gaidata yana kallonta, ta amsa bbu yabo ba fallasa, yyi shiru na kusan minti biyar snn yace "baaba fateema fa" inna ta hade rae tana kallonsa tace "ya aka yi," cikin fada Abba ya fara magana "haba baaba, ni ynxu kina gwada ma yaran nn bani da iko da su ne kome, ya yarinya tayi laifi irin wnn nasa a kawo min ita gida ki kunshe ta a daki bbu wani bayani, kuma ke ba yi mata xaki yi ba, ynxu kina gwada mata abinda tayi tayi dai dai knn kome," inna ta marairaice ganin yanda ransa ya baci tace "to wae Bukar maganar nn bata wuce bane ko me, naga dae ya ya ba dawowa xasuyi ba," Abba ya shiga kiran inteesar a fusace "fateema fateema," kmr munafuka ta fito da hijab har kasa, inna se ca take baxata fito ba koma inteesar, Abba yace "maxa ki wuce falona ki jira ni," a fusace yyi maganar don hka bata saurari inna ba ta fice kmr munafuka gabanta na faduwa, inna tace "to wllh sae na bi ku," bae tanka ta ba ya fice, ta fixgi gyalenta da sauri ta fice ta bi bayansu, gaban inteesar yyi mugun faduwa ganin su Hajiya da ma momynta har ma da Anty nafeesa da ta bi ta da harara a falon ashe ta xo gidan, ko inna ma bata sani ba, inteesar ta saci kallon Aliyu dake xaune gefen Haisam, ta rasa inda xata xauna don kowa haushinta yake ji a falon, Abba ya shigo ya xauna yana kallonta ta sunkuyar da kanta har lkcn tana tsaye, cikin ikon Allah sae ga inna ta shigo falon tana haki, tana kallon Hajiya tace "ke tashi ki ban waje in xauna," Hajiya bata yi musu ba amma in ranta yyi dubu ya bace, ta mike inna ta xauna tace "xo xauna nn inteesar," inteesar ta xauna gefen inna, Hajiya kuma ta nemi wani wajen ta xauna ranta a bace. Inteesar ta daga kai a hankali ta saci kallon Aliyu taga kallonta yake, duk ya koma kmr wani mara lfya, ta dauke kanta da sauri shima hka . A nutse Abba ya kira sunanta "fateemah," ta dago a hankali tana kallonsa, ya sauke ajiyar xuciya yace "ko da yake ma bari na fara ta kanki baaba," inna na kallonsa tace "eh ina ji," yana kallonta yace "Baaba kar ki fara magana nn ba tare da ance kiyi ba, duk me xaki ji a nn don Allah karki bude bakin ki, idan ana bukatar cewar ki xa'a sanar da ke, don Allah dae nace," inna ta tabe baki tana girgixa kafa, ya maida dubansa ga Inteesar da ta sunkuyar da kanta yace "fateema," wnn karan kasa dagowa ta kallesa tayi, bae damu ba ya ci gaba "Ashe ke dama mara hankali ce bansani ba," inna tayi karaf tace "kmr yaya," Abba ya hade rae yana kallonta, ta daga hannu da sauri tace "to nayi shiru," Abba na kallon Inteesar yace "ynxu abinda nake so dake shine kawae ki gaya min asibitin da kika je," Hawaye ya cika idonta ta kasa cewa komai, cikin daga murya Abba yace "ba magana nake maki ba," a hankali Aliyu yace "ae Safeena ce tayi mata jagora wae," a fusace inna tace "ga magana nn xaku tsaya kuna wani lauyewa, ni dae nasan jikata baxata iya aikata wnn danyan aikin da kanta ba" Abba yyi shiru yana kallon Aliyu snn yace "kae wa yaga maka hka," Aliyu yace "ita da bakinta ta fada," inteesar ta watsa masa harara tace "ni ba muyi hka da kai ba, kuma safeena bata yi min ko wani jagora ba ni da kaina na tafi inda naje, hasalima bata sani ba," Aliyu ya yo waje da ido da mamaki yace "kika ce me?" ta xaro masa ido tace "ehh" ya dafe kansa yace "innalillahi wa inna ilaihi raji un, kika sa naje na ba yar mutane takarda ashe sharri kika mata" Abba yace "takardar ka kai mata?" Aliyu ya kasa cewa komai sae kallon inteesar da yake, a rude Hajiya tace "kana da hankali kuwa Aliyu, ka saketa fa kace?" Abba yace "saki nawa kayi mata," Aliyu ya sauke ajiyar xuciya yace "daya," snn ya ciro pen daga Aljihunsa ya mike ya shiga dakin Abbansa duk aka bi sa da kallo ya fito rike da farar takarda ya isa study desk ya duka xae yi rubutu Abba yace "meye hka kke yi Ali," ya dago bbu yabo bbu fallasa yace "ita ma rubuta mata nata xanyi Abba" Abba ya daka masa tsawa "kana da hankali kuwa, a gabana don baka da kunya xaka dauko takarda kana gaya min maganar bnxa," cikin daga murya Abba yace "dawo nn ka xauna," Hajiya tace "kambu, ae wlh baka isa ba Alhaji, ita wancan din da ya saka ance maka gata ne bata da, ae ita ma Wllh sae ya rubuta mata nata, na rantse," Abba ya mike a fusace yace "fice min a falo Aisha, nace ki fita," ta mike tace "ae ko baka fada ba fita xanyi, amma wllh kmr yanda tayi makirci tasa ya saki matarsa ta arxiki ita ma sae ya saketa, ae dama idan bata xama makira ba sae Allah ma ya tambayeta, abu a jini," ta fice tana huci, inna tace "shegiya yar wahala, ae in Aliyu ya saki Inteesar yau duk kuma sae nasa dana ya rubuta maku takardarku wllh wllh," inteesar ta fashe da kuka tace "Abba ni ka bar shi ya rubuta min takardata don Allah don Annabi," Abba ya daka mata tsawa a fusace "rufe min baki, stupid" Anty Nafeesa kam kasa cewa komai tayi sae kallon inteesar take, momy dama hankalinta na kan TV, Abba yyi shiru na wani dan lkci snn yana kallon Aliyu yace "sae kaje ka mayar da matarka," Aliyu bae ce komai ba sae da har lkcin kansa a kasa yake da ganinsa kasan ran maxa ya baci, Abba ya hade rae yana kallon inteesar yace "ynxu dalilin cire cikin jikinki kawae nake son ki gaya mana gaba daya mu ji," hawaye ya cika idon Inteesar tayi shiru kanta a kasa, har sae da Haisam ya daka mata tsawa, "ba magana ake maki ba," a fusace inna ta mike tace "ohh ni yau naga tsiya xasu kashe min jika, kuma sun hanani magana " ta fashe da kuka xata bar falon, Abba yace "haba baaba ki dawo muji daliin da yasa tayi hka, ae bbu wanda yyi mata wani abun a nn," da kyar aka lallaba inna ta dawo ta xauna tana share hawaye, Abba yace "muna jin ki Fateema," inteesar ta dago kanta a hankali tana kallon Aliyun, taga shima kallonta yake, ta kauda kanta tace "sbda bana sonsa shima kuma baya sona yasa nayi hkn Abba," ta fashe masu da kuka ssae tace "Abba tunda na taso ya Aliyu ke cutata a gidan nn, tun ban san kaina ba, ban san me nayi masa ba ko dan ba gidan ubana bne, ya tsaneni kuma baya son bude ido ya gan ni cikin gidansu, ko uwar da ta haifeni ma bae bari ba, idan an manta randa ya daga hannu xae mareta to ni ban manta ba, kuma har gobe baxan manta ba, ban san me muka yi masa ba, duka bbu wanda ban sha a hannun Aliyu ba, idan ba a manta ba wani rashin lfya da nayi na kwana da kwanaki shi shine sanadin sa, amma ban fada ma kowa ba, har ka hada mu aure Abba, kuma tunda ka hada mu abba ko sau daya ban taba jin ddin xaman gidansa ba, sae nayi sati biyu ban daura idona a kansa ba, bae san ci na ba bae san sha na ba, kullum a wahale nake cikin gidan, to a hka yake son na haifa masa yara, wllh Abba bana sonsa ka taimakeni kasa ya bani takardata ynxun nn, biyayya kawae yyi maka yake xaune da ni gida daya a matsayin matarsa," ta fashe da matsanancin kuka takasa ci gaba, tun da ta fara magana Aliyu ke kallonta baki bude. Ganin bbu wanda ya iya cewa komai a falon don duk jikinsu yyi sanyi ya sa inteesar ta tsagaita kukan da take ta cigaba "snn Abba ni bada yardana ya sake aure ba, hasalima ni ban san xae yi aure ba sae ranar da ya kawo ni gunka da daddare kke tambayata ko nasani, to a nn ne ma nasan aure xae yi, kuma dama tun a hanya yyi threatn dina kan cewar ko me xaka tambayeni nace nasani, kuma Abba har yau yaki daukar batun karatuna da muhimmanci da nayi magana sae ya dinga hantarata wae baxan iya course din da nace nake so ba, kuma Abba da yake cewa na xubar masa da ciki a tambayesa ko kula dani da cikin yake, Abba sae nayi kwana uku ban gansa ba gashi bbu abinda nake iyawa kullum a wahale nake kwana nake yini a gidan ga kuma yunwa, tunda ba iya girkin nake ba," tayi shiru tana share hawayenta snn a hankali tace "lastly Abba kayi hakuri ba rashin kunya nake maka ba, amma ka tausaya min kayi masa magana ya sauwaka min, don baxan koma gidansa ba wllh na gama aurensa," Aliyu ya mike yana mata wani mugun kallo yana huci yace "munafuka, makaryaciya kawae, ki xo ki shake ni na baki takardar taki kuma wllh sae kinyi da kin sanin xubar min da ciki," ya juya xae bar falon Abba ya dakatar da shi a fusace, inteesar ta fashe da kuka tace "wllh Abba kace ya bani takardata bana auren kuma, bana sonsa," Abba yana kallon Aliyu yace "dawo ka xauna," ya kai minti kusan biyar a tsaye kmr baxae xauna ba, sae da Anty Nafeesa tace "ba magana ake maka ba ka tsaya ma mutane kallon rainin wayo," ya juya ya kalleta, snn ya koma inda yake ya xauna yana ma inteesar wani irin kallon, da ganinsa kasan ran maxa ya gama bacewa, Abba yace "cikin maganganun da Fateema tayi a nn akwae wanda xaka karyata," ya kauda kansa bae ce komai ba sae huci da yake, Abba yace "gud, dama tun ba yau ba nasan halinka, na kuma san xaka iya aikata duk abinda fateema ta lissafo a nn, kai kam ban san wani irin mutum bne Aliyu, kuma gwara da Fateema ta gaya min abubuwan da ta dde tana boyewa a cikinta tana cutar kanta," ya juya yana kallon Inteesar yace "amma fateema ke abinda kika aikata a ganin kinyi dai dai knn, me xaki ce ma mahaliccinki, ashe dama karamin tunani gare ki ban sani ba" inteesar dai kanta na kasa tana hawaye ta kasa cewa komai, Abba ya ci gaba, "a nan kin nuna kmr rashin kulawar da yake nuna maki ne yasa kika aikata abinda kika aikata, to Fateema baki san hanyar gida bne, ko in kin xo akwae wanda xae ce maki don me" a hankali tace "Abba banyi wnn tunanin ba," Abba ya girgixa kai yana kallon Aliyu yace "to malam rubuta mata takardarta, Allah ya hada kowa da rabonsa, ni nayi kuskure tun farko na baka auren fateema duk da ka nuna min baka sonta" Aliyu ya juya yana kallonta, ita ma kallonsa take, ya maida dubansa ga Abbansa yace "srry ba rashin kunya nake mka ba Abba, amma taxo ta shake ni ta kwata, ko kuma ta saki kanta da kanta," yana kai wa nn ya mike yana huci xae bar falon, Abba ya daka masa tsawa yace "don uwarka ni nayi maka magana ko fateema" Inna ta mike a fusace tace "yau naga tsiya, yarinya tace bata son aurenka ka sallameta mana ko ana yi dole ne, ae ba rasa manema tayi ba, ko gobe ta fita titi santalelen yaro me katuwar mota wanda ya fi ka komai ne xae biyo ta wllh, yo tsami gaye da kai idan ba tsautsayi ba ma me xae kai ta aurenka sai tsayi ba hankali kmr bishiya," abun dariya abun takaici, a walakance Aliyu na kallon inna yace "ae sae ki rubuta mata sakin ki bata, ko kuma ku hadu ku shake ni ku karba," yyi tsaki a fusace ya juya xae fita Abba yace "kar ka kuskura ka fita daga falon nn, kanka rawa yake Aliyu, ita mahaifiyar tawa kke gaya ma magana" inna ta fashe da kuka tace "yo sabon abu ne wnn, ae sae Allah ya mana hisabi da Aliyu" Haisam ya mike ya fice daga falon, hkn ma Momy, ran Abba a bace kuma a nutse yana kallon Aliyu yace "bani takardar Fateema ynxun nn Ali kar na nuna maka d odza side of me," cikin tsawa ya karasa maganar, Aliyu yyi shiru yana kallonsa yana huci, inna tace "ba magana ake maka ba salubabbe kawae," ya juya yana kallon inna tace "daina kallona Munafuki kawae," inteesar dae kanta na kasa, ya juya ya kalleta snn yyi huci me xafi ya ciro takardar da ke Aljihunsa da pen ya daura takardar kan hannun sofa, snn ya duka ya fara rubutu a jiki. Inteesar ta dago a sanyaye tana kallonsa hawaye na bin kuncinta, Abba ma kallonsa yake ko kiftawa baya yi, hka ma Anty Nafeesa, inna tayo waje da ido ta dafe kirji tace "lah rubutawa xae yi Bukar" . .. Inna ta fashe da kuka ta mike tsaye tana cewa "Bukar kayi shiru, kaga fa rubutawa yake, lah ha ila ha ilallahu mahammadur- rasulillahi sallallahu alaihi wassallama, Bukar kayi wani abu mana" Abba kam kasa cewa komai yyi sae kallon Aliyun yake, Anty Nafeesa ta jinginar da kanta jikin kujera tana kallon ikon Allah, har Aliyu ya gama rubutunsa ya mayar da pen din cikin aljihunsa yana kallon Abbansa yace "gashi nn na rubuta mata," Abba yyi murmushin takaici yace "to ka kyauta," ya dauke kansa ya shiga linke takardar neatly yana kallon inteesar dake kallonsa har lkcn tana hawaye, ya karasa gabanta yana mata mugun kallo ya jefa mata takarda snn ya juya xae fita inna ta bi sa da gudu ta cakumi kwalarsa tace "don uwarka jikartawa ka mayar baxawara, to Allah ya isa bamu yafe maka ba, sae Allah ya saka mana," Abba yace "ki rabu dashi baaba," inna tace "naki din, dama nasan har da hadin bakinka ae," ta fashe da wani matsanancin kuka ta xube wajen tana daddaga hannu sama, Aliyu yyi yar dariya rainin wayo ya juya ya fice daga falon, sae a snn umma dake xaune har lkcn bata ce komai ba ta mike ta bar falon xuciyarta fal murna don dama abinda take jiran gani knn, kuma ta gani, ynxu kuma xa taje tayi break din ma Hajiya gud News din, Abba ya sauke ajiyar xuciya yana girgixa kansa, Anty Nafeesa ta mike ta nufi gaban inteesar ta dauki takardar da Aliyu ya jefa mata ta koma ta xauna tana warware wa, inteesar kam hade kanta tayi da gwiwa tana rera kuka a hankali, Anty Nafeesa ta gama karanta content din takardar ta ajiye kan kujera kusa da Abba ta mike ta fice daga falon, inna ta mike ta dago inteesar tace "tashi mu je, sae me don ya sake ki, abinda ynxun nn kina fita masu mota xa su biyoki, uban waye xae kalleki yace kin taba aure idan ba dan bakin ciki ba, ae gwanda da kika kwabar da cikin don da ganin jarababbun yara ne, mu je kawae Allah ya isar mana" sae a snn inteesar taji sanyi ta mike tsaye inna ta shiga share mata hawayenta, Abba kam idonsa na kan takardar da Nafeesa ta ajiye masa bayan ya dauka, yana gama karanta cntent din ya sauke ajiyar xuciya tare da jinginar da kansa jikin kujera yace "gashi nn fateema," inna ta ja hannunta xasu fita tace "rabu da shi da'alla muje me xaki yi da shi su da suka sa shi ya sake ki ae sae su cinye," Inteesar ta kasa bin inna ta koma a sanyaye ta karbi takardar a hannun Abba, Abba yace "kiyi hkuri Fateema ni na ja maki komai," ta kirkiro murmushi ta karbi takardar inna tayi tsaki ta ja ta suka fice daga falon tana cewa "yo idan bata yi hkurin ba ya ake son tayi dama bayan an gama cutarta," inteesar dae jikinta a mace suka isa falon inna, inna ta karbe takardar hannunta da ta kasa dubawa har lkcin, tayi michi michi da ido tana kallon rubutun ita nn karatu take kmr tasan me aka rubuta jikin takardar tayi tsaki ta cukuikuye takardar ta jefar bakin kofa tace "shege kawae rubutun ma kmr ta agwawa," ta juya tana kallon inteesar da ta xauna kan kujera ta kura ma TV ido tace "maxa je ki kiyi wanka ki xo ki kwanta, kar ki sa komai a ranki kinji" a sanyaye inteesar ta mike ta shiga dakin inna tayi kwanciyarta kan gado kawae don baxata iya yin wankan ba. . Washegari da safe inna na share falo ta ga takardar da ta jefar bakin kofa, tace "na share wn shegen takardar Inteesar," inteesar da har lkcn ke kwance a daki tayi shiru kmr baxata ce komai ba sae kuma tace "ki ajiye kawae kar ki share," inna na gama sharan ta hada mata ruwan wanka ta kai mata bayi duk tana kwance, inna tace "maxa ki tashi kije kiyi wanka kadda ruwan ya huce," ta mike xaune da kyar ta fara cire kayan jikinta xata shiga wankan inna tace "to me xan hada maki na kalaci kan ki fito," inteesar ta dan yatsine fuska tace "ni waina kawae xa a siyo min," inna tace "yo ae wnn ba wani abu bne bari na kira kursum kan su tafi makaranta su siyo maki," inteesar na shiryawa a dakin inna taji muryar momynta ta xo gaida inna, ta hanxarta ta gama abinda take ta fito da sauri don ta gaidata don ba xuwa sashinsu xata yi ta jibgeta ba, gefen inna ta xauna tace "ina kwana momy," ba tare da ta kalleta ba ta amsa da "lfya lau," inna tace "ya kina amsa mata kmr ana tilasta ki," momy ta dan yi murmushi ta mike tsaye tace "bari naje na gama kimtsa ihsaan inna," inna ta tabe baki bata ce komai ba momy ta fice, inna tace "wannan wannan da ba dan a gabana ta haife ki ba da sae nace ba uwarki bace, bata sonki ko kadan, to wae da wanne xaki ji," inna tayi tsaki tace "Allah shi kiyaye," inteesar dae bata ce komai ba tana ta kallo abinta, can ganin inna tayi shiru yasa tace "inna ni ina son xuwa gida in kwaso kayana bani da kaya ko daya a nn da xan sa," inna tace "Aa ba sae kin je ba, xan sa su kursum su je su kwaso maki kawae, me xae kai ki gidan nn kuma" inteesar ta hade rae tace "to sanin me da me xasu kawo min xasu yi, ni wllh da kaina xanje bbu wanda xae je dauko min kayana," inna ta bude baki tana kallonta, can ta rufe bakin tace "ke dae wahalalliya ce wllh, don ubanki idan kika je kika hadu da shegen kiyi ya?" inteesar tace "meye ruwana da shi an dde bamu hadu ba, bari ma kiga ynxun nn xan shirya na tafi wllh, kuma kiyi ma Abba maganan yaushe xa a kwaso min kayan dakina gaba daya" inna tayi shiru tana kallonta snn ta tabe baki tace "to ni dae ba ruwana, ki tsaya kuma ki karya," waina uku inteesar taci ta wanke hannunta tace ta koshi, inna tace "to ni dae banda ko sisin da xan baki kudin mota," inteesar tace "ai kam sae ki nemo shi don nima bani da kudi," inna tace "bari naje gun Zainabu na ranto dari biyar to," inteesar tace "oho ni dae ki nema ki bani, kuma fa karki ce mata nice xanyi amfani dashi" inna tace "to," snn ta fita xuwa ranto dari biyar, ko minti goma ba ayi ba ta dawo rike da dubu daya tace "gashi nn har dubu daya na samu," inteesar tace "yauwa innata shi yasa nake son ki," ta karbe kudin ta saka takalminta ta fice daga gidan inna ta rakata har gate snn ta koma ciki.

Chapter 24 of 32