Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a kawo min mana" nan ya shiga bubbuda ledojin yana kallon kayan baki bude inna tayi maxa tace "maxa kuje can guriin xainabu gani nan xuwa" da sauri kuwa suka juya suka bar wajen, sannan inna ta dinga kwasar kayan tana shiga dasu dakinta Aliyu na binta da kallo "Allahu akbar.. Yanxu har da maltina aka kawo min?? Lah har da madara ni rahma, amma mutanan nan anyi mutanan kirki."Aliyu ya bude baki yana kallonta sae kace warce bata taba shan madara ba ko malt, ita da duk wata abba ke jido mata su dayawa, amma ko sati biyu ba sayi take shanyewa da yara. "kai Allah ya shima wannan yaron Albarka" Aliyu ya dubeta yace "wani yaro?" au na manta ne Allah ya shima maimuna Albarka xance, ko da yake ma duk Daya ne, don dan ta da ya dawo daga waje ne yayo min tsarabar. Aliyu ya tabe baki ya jawo Abincin gabansa xai fara ci akayi sallama faruuq ya shigo palon bayan inna ta amsa da karfinta, Mikewa tayi ta rasa inda xata sa shi sae ca take "sannu da xuwa dan Albarka," ya nemi guri ya xauna ya gaidata ta masa cike da jin dadi, sannan ya ba Aliyu hannu sukayi musabaha, da dan fara'arsa Aliyun ya karba don bai san sa ba. Inna ta Mike ta bude fridge ta jido masa lemo kusan kala hudu da ruwa roba uku, ta dire masa a gabansa Tana tambayensa ya hanya, sannan ta shige ciki ta fito da cin-cin da alkaki bakin nan nata yaki rufuwa. Godiya ya dinga yi mata, don yana jin dadin yanda inna ke nan nan dashi, ko xaka ci abinci ne, bari na kawo maka cokali kuci tare da Aliyu, wannan shine Aliyu jikana da nake baka labari, dariya ma abin ya ba Aliyun, ta dauko cokalin ta saka masa tace suci tare. Aliyun bai yi musu ba ya sauko yana cewa ki dae yi a hankali karki fadi da wannan barin jikin da kike yi. Bata ko tanka masa ba tace "wannan shine faruuq saurayin intisaar ae nasan baka san shi ba, Haisam ne ya san sa," dago kai Aliyu yayi yana kallonsa, nan da nan dan fara'ar dake fuskarsa ya bace, inna tace to kuci abincin mana kar ya huce, ajiye cokalin hannunsa yayi fuskar nan tasa a yatsine yace "ya dae ci, amma ni wannan ba isar mu xai yi ba," faruuq ya dago yana kallonsa, ya gane nufinsa,don hka sae yayi murmushi yace to ni bari naci tunda bako ne ni, da sauri inna tace eh hakan ma yayi sae ya hakura ayi na dare. Hade rai Aliyu yayi yana kallon inna yace "kamar ya na jira na dare? Ban gane nufinki ba?" Inna ta mike ta tabe baki hade dacewa "maida wukar dan nan" sannan ta shige daki sae ga ta ta Fito da garin rogo da suga ta xube masa a gabansa tace "ka debo ruwa a pampo ka jika kasha don ruwan kenan na kwaso wa faruuq. Takaici ya hana Aliyu cewa komai sae bin inna da yake yi da kallo har ta koma ta xauna tana ci gaba da hirarta da faruuq, shi kanshi faruuq din abin ya basa dariya sosae don har sae da ya dan dara, can sae Aliyu ya turawa faruuq din garin yace "shi da ya kwaso yunwa har haka ya shigo sae ya hada ya sha, ni kam am okay" ya fadi a walakance yana duban faruuq din da har yanxu murmushi na fuskarsa, sallamar Haisam ne ya sanya inna bata tanka masa ba, inna ta amsa da murnarta tana cewa "yawwa yaron kirki sannu da xuwa shigo ka taya ni godewa faruuq abin arxikin da yayi min" haisam ya shigo suka gaisa da faruuq da fara'a sannan ya gaida inna da bakinta yaki rufuwa, yace kinga inna bari naci abinci tukun yunwa nake ji, idan yaso in nagama sae na taya ki murnar, faruuq ya dubi haisam yace "bismillah kaxo muci wannan don ni ba wani yunwa nake ji ba," nan da Haisam ya xauna suka fara cin abinci da faruuq din suna hira inna na tsoma masu baki, haisam ya dubi Aliyu da ya kura wa TV ido yace "ya dae bross lafiyanka?, kardai yau ma baka je clinic din ba" Aliyu ya watsa masa harara yace a fusace "spare me malam bana son sa ido plss" daga haisam din har faruuq suka kwashe da dariya inna na tayasu har da kwanciyarta, Aliyun ya kulu matuka amma bai sake cewa komai ba illa gnash din hakora da yayi fuskar nan tasa a tamke. Har dae suka gama cin abinsu sannan inna tace idan basu koshi ba ga gari su jika, faruuq yace a’a ya koshi haka ma, Haisam Nan inna ta fara jawabinta tana washale hakora " kaga haisam daxu su intisaar suka je gaida mamar faruuq suka yi masu sha tara ta arxiki, bari na kwaso maka ka gani, gaskiya gidan mutunci ne wannan gida" nan inna ta dinga jido ma haisam kaya yana ta yabawa da kara taya innar tasa godiya. Ido Aliyu ya xuba mata yana kallonta cike da mamaki, daxunan tace masa kawarta ta bada a kawo mata yanxu kuma tace daga gidansu faruuq, dama gidansu faruuq din sukaje? "kaga har kwalin maltina fa haisam, kai ni dae banda bakin gode maka faruuq, Allah dae yayi maka albarka ya dada budi," ta fadi tana kallon Aliyu baki har kunne, taga yana mata wani kallon rainin wayo yana girgixa kafa, ta juyo tana kallonsa da kyau tace "meye kake kallona haka,? Ka taba kawo koda gwangwanin madara daya ka kawo min gidan nan ne bare maltina? Kuma Don yanxu na samu me min sae ka dinga min bakin ciki? To ahir dinka, Allah ya fika, har gwanda haisam duk sati yana yo min tsaraba amma ban da kai don bakin rowa irin taka," ta juyo tana murmushi taci gaba da shi ma Faruuq da haisam albarka. Ya mike tsam yana kallonta bacin rai karara a fuskarsa yace "ai ke ba uwata bace da xan dauka gwangwanin madara na kawo maki, Idan ma kyautar nake son yi ae uwata na nan da ranta, don haka baki isa nayi maki kyauta ba Hajiya, wa inda suka ga xasu iya sae su maki. Aikin banxa kawae aikin hofi, mutum ya tsufa bae san ya tsufa ba" yana kaiwa nan ya fice Ba tare da ya jira cewarta ba, sashin hajiyarsu ya nufa, yana shiga ciki rae bace ya fara Magana "mumy kina gidan nan xaki bar 'yar ki ta fita raka wata banxa can gidan saurayi? Hajiya ta mike da sauri tana cewa wa kenan? Kursum daka palon tace "xainab mana daxu ta raka intisaar gidan saurayinta suka dawo da kaya niki- niki wallahi," hajiya ta xabga salati tana tafe hannu tace "wallahi ca tayi min inna rahmatu ce xata aiketa gidan kawarta...." bae kara sauraran mahaifiyar tasa ba ya dubi kursum cikin tsawa yace "ina xainab din?" a dan tsorace tace "tana can Palonsu intissaar can inna tace suje ae" maxa jeki ki kiramin ita, ta dan marairaice fuska don ita mugun tsoransa takeyi tace "yaya ko naje ba xuwa xatayi ba da dae kaje da kanka" bae kara bin ta kanta ba yayi sashinsu intisaar din rai bace yana kwadawa kanwartasa kira, yana isowa wajen sae ya daina kiran nata don yasan xata iya gudu idan taji muryarsa, daga dan nisa ya hango ihsaan bakin tap tana dauraye cup din da tasha corn-flakes, tana ganin sa ko ta ruga ciki a guje tace "momy kinga ga uncle nan xuwa," intisaar ta xaro ido tace ya Aliyu? Ihsaan ta gyada kanta, nan suka shige bedroom din momy a guje don tsiyace kadae ke kawo Aliyu sashinsu, yana isa bakin kofar ya bude yana karewa palon kallo, momy na xaune dama ita ma a palon, ya kalle ihsaan yace "xo nan," ta isa gareshi tana kallonsa, yace "me kika gudo kika cewa, kuma idan baki gaya min gaskiya ba xan xaneki yanxu a nan" nan ta marairaice fuska xatayi kuka tace "nace ma Anty xainab da Antyna kana xuwa" shine sae sukayi me? Ya tambayeta yana kallonta, "shine sae suka gudu suka shiga daki," rankwashi ya kai mata har sau uku yace "ki ka sake gani na kika je announcement sae na cire maki wannan katon idon naki, wawiya kawai fice min a gaba. Ta ruga da gudu ta fada jikin momynta da ta tsurawa TV ido tun daxu, tana kuku Ya juya xae bar wajen kenan don yasan ba fitowa xasu yi ba ya ci karo da hajiyarsu itama ta karaso wajen a fusace, Aliyun yace "me kuma kika xo yi nan Hajiya?" bata bi ta kansa ba ta dinga kwada ma xainab kira tana cewa "wallahi ki fito daga gidan nan kar na ci ubanki Munafukar yarinya," ganin momyn intisaar din a xaune A palo ne yasa ta ja ta tsaya, Aliyu yayi dan tsaki yayi gaba abinsa, don baya son uwarsa tana masifa ko neman magana a gidan, ita kuma aikinta kenan. "Zainabu! Ki gya min dalilin sa 'yata bin watsatsiyar yarki gidan saurayi don a bata ta?" hajiya ta fadi fuskarta a tamke, ko kallo bata ishe momy ba da ke ta aikin kallonta tana rungume da 'yar ta, hakan ya kara hassala hajiya don tana matukar bakin cikin sharesu da momyn ke yi a gidan, kenan ma mahaukata kawae ta maidasu don ba dai amata abu ta tanka a gidan ba, cikin daga murya hajiya tace "wae ba da ke nake ba ko kurama ce ke?" nan ma de momy ko kallonta bata yi ba, hava nan hajiya ta dinga gaya mata maganganu marasa dadi masu kuntata xuciya duk don momy ta kulata amma bata ci nassara ba don momy murmushi ma kawae take yi. Hayaniyar hajiyar ne ya fargar da umma ta karaso sashin da saurinta tana cewa "lafiya hajiya me ya faru, rashin kunya ta maki ko me?" ina fa,, yawon iskancin da da ta sa 'yar ta take yi, shi xasu koyawa xainab dita, tunda gashi yau har shiryata tayi suje gidan saurayin 'yar tata. Umma ta xabga salati tana jujjuya kai tace "wallahi kursum taxo ta sameni wae xainab ta bi intisaar gidan saurayi ya cika su da kaya duk na tsamman shirmanta ne shiyasa ban tanka mata ba" hajiya tace "Allah ya isa tsakanina dasu," umma tace "to yanxu ina shegiyar xainab din take" bata jira amsa ba ta afka palonsu intisaar din ta tsaya gaban momy tana cewa "ki fito mana da 'yar mu kar mu aki abinda baki xata ba gidan nan yau," tana magana ne tana nuna momy da dan yatsa, momy tayi murmushi mai sauti, ta kama hannun ihsaan suka shige bedroom ta kulla kofar. Galala umma ta bita da kallo, hajiya ma ta shigo palon tace "idan ba tsoro ba dan uban mutum meyasa bae tsaya ba" nan suka dinga xaxxaga mata rashin mutumci kwando-kwando suna xage-xage, gori kam ta sha shi kala-kala, abinda ya fi bata masu rai bae wuce yanda ta barsu su kadae suna ta haukansu ba, don a da can idan suna mata tayi shiru har dadi sukeji a nasu tunanin tana tsoransu ne,. Ido Aliyu ya xuba masu yana kallonsu, yayi murmushin da xa a iya kiransa da na mugunta sannan ya hade rai yana kallon xainab din yace "ina kuka je jiya?" ta yarfe hannu hawaye na sintiri a fuskarta tace "don Allah kuyi hakuri..." wani irin tsawa ya daka mata yace "it seems kina wasa dani ko?" cikin kuka tace "aa yaya" gud! Gaya min inda kuka je jiya. Ta juya tana kallon intisaar dake kuka wiwi sannan ta kalle abban nasu da ya Aliyun tace "gidansu faruuq muka je gaida mahaifiyarsa" abba yace "waye faruuq din?" saurayin intisaar ne," ta fadi, kanta a sunkuye. Cike da mamaki abba ya tsaya kallonsu, Aliyun yace "amma ina kika ce mun xaku jiya?" "aa Inna ta...." wani irin tsawa ya daka mata yace "rufe min baki kar na taka ki" yayi hakan ne don baya Son Abba yasan da ixinin inna suka je, kawae so yake ya lallasa su barin intisaar. Xainab na ganin hakan tasan yau kam sun banu, nan Aliyu ya dinga tsarawa abba yanda suka yi jiyan da irin karyar da sukayi mashi, xainab ta san inna ce kadai gatansu yanxu don abba yayi fushi matuka, da dubara tashiga yi ma kursum tex da wayan dake hannunta kan cewa ta kira masu inna suna palon abba xa ayi masu duka, duk a rude take, ganin yanda Aliyu ke tayi wa abba tsari yana dada bata masa rai. Ba a jima ba, kursum ta maido mata reply, ta bude da sauri hannunta na karkarwa taga me tace, "NO" abinda ta gani knan boldly wato baxata turo innar ba. Ta kara sautin kukanta tana kallon intisaar da ta kife kanta ita ma tana yi, tun ba yau ba tasan kursum muguwa ce. To wa xata kara yi ma tex yanxu? Don kursum ce kadae hope dinsu, ita ma tace no. Yaya haisam ta tuna, don haka da hanxari ta shiga yi masa tex duk da baya gidan, ya taimaka ya kira masu inna taxo. Kafin tayi sendin Aliyu ya ganta ya fixge wayar da sauri yana cewa "you re vry stupid, wat do yhu fink yhu re doin?" abba ya karba wayan ya ajiye gefensu yana kallonsu. Haisam yyi dariya sosai da yaga tex din, don sbda tsabagen masifa Aliyun yyi sendin bai sani ba. Ai kam yana kiran innar ya gya mata ta taho da gudunta tana salati. Tun daga bakin kofa ta dinga kwada wa abba kira, hkn ba karamin bta wa Aliyu rai yyi ba, don yyi niyar yyi masu laga- laga ne, sai yaji kmr ya hankadata ta koma, nan ta sake masu kuka tana cewa "ynxu Bukar don na tura yaran nan su gaida uwar yaron nan me kirki shine nayi laifi?" Abba ya girgixa kai yace "dama ke kika ce su je?" ta goge hawayen dake idonta tace "eh mana," basu gaya min ke kka ce suje ba ne." ya kallesu yace "ku tashi ku tafi." yyi hkn ne don baya son uwartashi ta daga masa hnkli. Aliyu ya dan bugi kafarsa a kasa yace "shit" inna ta dubi hajiya da umma dake xaune a palon kmr su hadiye xuciya don takaici tace "to munafukai ae sae a tashi a bashi waje kuma ko," tayi tsaki ta wuce tana surutanta, don ana ta tunanin su suka gya masa, duk da su din suka gya masa. . Suna fita Abba ya girgixa kai cikin damuwa yace "ni bn san me ke damun inna ba, tana tsufa ne hnklinta na komawa na yaro," hajiya ta mike ta tabe baki hade dace wa "kawae de ta kare matarka ne, amma ka dae yi bincike da kyau." tana kai wa nan ta fice, umma ma ta bita a baya tana cewa "mu dae Allah ya rufama 'ya yan mu asiri kar a sa su a hnyar da bae dace ba, don wannan lamarin akwae abun dubawa a ciki" momy de bata ce komai ba, amma tasan da ita suke, ta mike itama xata bar palon Abba ya kirata ta dawo, Aliyu ma ya tashi ya bar masu palon cike da jin haushin inna, ko waye yaje ya gya mata ma oho. Suna tsakar gida a tsaye ita da xainab suna ta dariyan abinda ya faru jiya da safe, hajiya da umma sun je barka, inna tana can sashinta, su biyun kadae ne a tsakar gida, shirun da intisaar tayi ne fuskarta ya bayyana alaman tsoro ya sa xainab ta dakata daga surutun da take yi tace "me ya faru," tana waige-waige, da sauri intisaar ta fixgota da gudu suka je bayan wani flower suka buya, xainab na maida numfashi a tsorace tace "wae menene?" ita din ma numfashin take mayar wa tace "ya Aliyu." xainab tace "a ina kika..." tsit tayi ganin Aliyun ya doso ta inda suke, cikin kasaita yake tafiyar tasa, yana sanye da t'shirt fara kal, da 3quatre shima fari tas, intisaar ta bi shi da kallo da idanuwanta kmr xasuyi magana, farar kujerar roba ya dauka ya ajiye ta opposite inda suke ya xauna. Basu da wata fargaba don sun tabbatar idan ba kusa da flowern ya xo ya tsaya ba baxae gansu ba, ya ciro wayrsa daga Aljihu yana dubawa, suka ga yyi murmushi mai kyau har sae da dimple dinsa ya nuna, ya lumshe manyan idanunsa ya sake budesu, ko me ya gani oho. Ashe dae ya Aliyu na murmushi, tambayr da intisaar tayi ma knta knan a xuciyarta, nan dae ta tsaya ta kare masa kallo sosai, don ita kullum kallon tsoro take masa a gidan. A xuciyarta tace "ashe dae yana da kyau har hka," ta tsura ma sajensa da ya kwanta luf- luf a fuskarsa ido, daga sama xuwa kasa ta dinga kallonsa ko kifta ido bata yi, ashe dae shi din kyakkyawa ne sosai, amma duk da hka faruuq dinta ya fisa kyau tasani, xainab ta xungureta tace "ke wannan kallon fa?" a tsorace intisaar din tace "da'alla dubi yanda kika bani tsoro."xainab tace "to naga kina neman cinye min yaya da ido, intisaar ta tabe baki tace "ni kallon mamaki nkeyi masa" to wae taya ma akayi kika san yana xuwa? Xainab ta tambaya tana kallonta, kamshin turarensa, intisaar ta bata amsa ba tare da ta kalleta ba. takun da suka ji yasa suka kara labewa sosai, momy ce taxo ta wuce, bai ce mata ba, bata cemasa ba har ta wuce sa, da alama sashin inna xata, sae da ta wuce shi sannan ya bita da kallo har ta kure masa, yyi murmushin da intisaar ta gaxa gane ko na menene, sannan ya cigaba da danna wayarsa, xainab tace "yau mun shiga uku hka xamu ta tsayawa ni kam na gaji wllh" intisaar bata tanka mata ba ta dan kara satan kallon Aliyun, taga kara hakikincewa yyi ma kan kujerar. Ihsaan ce taxo wuce wa tana kuka, kila ta tashi bata ga momynta ba da yayarta, don bacci take yi, xata wucesa ya fixgo ta yace "cum hia, wa ya dokeki?" bata ce komai ba sae kallonsa da takeyi, ya daura ta kan kafarsa yana cewa "idan kika sake kuka xan maki allura" ba shiri tayi shiru ya dago wayrsa yana ta nunamata ko pix ne ko meye ma oho dae, su dae hka suka dinga lekosu har daga karshe suka ga ya sauke ta ya mata mgna a hnkli ta ruga sashinsa da guda, ba ajima ba ta dawo rike da chocolate, suka ji yace mata "run.. Momy tana wajen inna je ki sameta," da gudu kuwa tayi sashin innar. Idan ba don intisaar da ta dinga rike xainab ba da tuni ta mike ta bar wajen, ita kam tsoran abinda xai yi masu ne yasa ta dinga rike xainab kar ta tona masu asiri. don sun gaji sosai gashi aliyu yaki barin wajen har sunyi kusan awa biyu a durkushe, momy da ihsaan ma tuni suka xo suka wuce. Ba su suka bar bayan flowern ba sae da aka kira la'asar Aliyu ya wuce massallaci. Tana xaune gefen inna da ta dage tana ta kirgan kudi 'yan dubu daddai, da ta kirga sai ta mikowa intisaar ta duba ko dai dai ne, intisaar kam ta xuba mata ido don bata san inda ta samu kudin ba, har dae daga karshe suka gama kirgan kudaden inna ta dubi intisaar din bakinta a wangale tace "nawa knan gaba daya?" intisaar tace "dubu dari biyu da hamsin, ina kika samo su inna?" ba tare da inna ta kalleta ba tana kkrin hada kudaden waje daya tace "fili na na saida." intisaar ta xaro ido hade da bude baki tana kallon inna. Sallamar haisam ya sanyata rufe bakinta, inna ta amsa mashi ba tare da ta lura da halin da intisaar ta shiga ba ya shigo, suka gaisa yace "kina sha'aninki inna, ina kika samo kudi hka?" ya tambayeta yana karewa palon kallo, a xuciyarshi yana cewa kar dae wani abun inna ta kuma saidawa, don saranta knan, in dae bata da kudi to bata ki koh plaxman palonta ta saida ba, hkn kuma na bata wa abba rai sosai ba kadan ba, don duk abinda yke mata bata gani sae ta saida wani abun palonta ko daki, "wllh fili na na saida haisam" haisam yace "mene?" Ba tare da inna ta kallesa ba tace "nace mka fili na na saida. Ko bka ji ne" ya nemi kujera ya xauna yana kallonta cike da mamaki yace "wani filin inna?" don dai shi yasan a ynxu hka inna bata da fili, idan ba dae wanda ake mata gini taje ta saida ba, "wannan din da babanku ya siya min" ta fadi tana mikawa intisaar kudaden ta kai mata daki. Haisam ya yo waje da ido "yace wani filin abba ya baki?" inna ta hade rai tace "na jan bulo mana" haisam ya saki salati yana kallon innar, inna tace "kai ni don Allah ku rabu dani, ina da bukatar kudi kuma baxan saida kaddarana ba?" haisam yace "ya salam! Ynxu inna abba ca yyi maki filin naki ne? Daga ya baki takardu ki ajiye masa sae ki je ki saida fili? Wai ma nawa kika saida filin?" "ni dubu dari biyu da hamsin aka siya," inna ta fadi a marairaice. Haisam ya mike da sauri yana kallonta ya ma kasa cewa komai," filin abban kika saida masa dubu dari biyu da hamsin? Kin san nawa ya sayi filin inna, haisam ya girgixa kai yana kallon innar cike da takaici, ita kam sai wuri-wuri take da ido. Aliyu yyi sallama ya shigo yana cewa "har kin dawo daga yawon inna?" ya kalli haisam da yanayinsa ya sauya xuwa bacin rai yace "me ya faru guy?" Aliyu filin abba taje ta saida dubu dari biyu da hamsin wae" haisam ya fadi cike da jin haushi, Aliyu ya xaro ido yace "wat?" filin da yke cewa xai fara gini cikinsa nxt yr?" dariya Aliyu ya dinga yi har da dafa bango, intisaar kam ido ta xuba masu tana kallonsu ita ma tasan inna bata kyauta ba, tuni inna aka fara hawaye, irin dariyar da Aliyu yake yi ne ya kara kullar da haisam, to meye abun dariya a nan, ta rangada wa abbansu asara, don ko shi bai sayi filin hka ba, cikin karkarwar murya inna tace "to ni ina nasan filinsa ne, da naga bai sake min mgna ba ai nayi xaton ya bani ne, kuma Aliyu ba kai ka bani shawarar ba to?" Aliyu ya xaro ido yace "wa? Aa karki sake saka ni cikin wannan case din Hajiya" inna tace wllh kai ka sani, kana ji ko haisam, jiya ya shigo da daddare nake ce mashi bnda kudi kuma ga bikin jikar aminiyata ya taso bari bukar ya dawo na tambayeshi kudi, sae Aliyu yace min ae Bukar bai da kudi ynxu hka sae dae idan xan saida kujeruna ne na biya bukatata, to naga dae taya xa ayi na saida kujerun palona, palo ya xamo wayam, kuma kwanakin baya ma da na saida fridge dina ma ae sae da bukar yyi min masifa, to yana fita a jiyan sae na tuna ai akwae takardun filin da bukar ya bani......" Aliyu ya daka mata tsawa yana cewa "ke inna rahmatu wllh kar ki saka ni cikin wannan case din na gya maki, idan dae mutum ba hauka ya fara ba ta ya xai kin kima kujerunsa ya saida don an bashi shawarar, ni dama wasa nke maki, kuma magana ce na gya maki." tuni inna aka fara kuka wiwi, Aliyu ya fice yana dariya, Haisam kam kasa cewa komai yyi, tun ba yau ba yasan Aliyu mugu ne, idan ba hka ba taya xa a saida kaddarar mahaifinsa mai muhimmanci yayi ta dariya. Ya juya ya fice kawae ba tare da yace da inna komai ba, to waye ma yyi mata jagora taje tayi wannan aika aikan, Aliyu na fita yaje ya sami hajiyarsa yana ta dariya ya bata lbrin abinda inna tayi, ta hade rai tace "to meye abun dariya a nan Aliyu, gadonku fa ta walakanta kke dariya hka?" ya mike yana kallon umman tashi yace "ni banyi depend a gado ba mum, Allah ya hore min don hka, 4 ol i care," ya fice yana ci gaba da dariyarsa don yasan drama xa ayi a gidan yau idan abba ya dawo. Abba ne tsaye kan inna yana faman bambamin fada kmr xae maketa, inna ba baki sae idanuwa, "kinsan nawa na sayi filin ne xakiyi min hka inna, daga baki ajiya sae ya xama naki, ina aka taba yin hka? Bbu shawara bbu komai xaki je ki walakanta min abun da akalla xan iya saida shi miliyan daya da rabi." hajiya da umma dake palon ji sukayi kmr su shide don murna, Aliyu ya kasa hadiye dariyar dake cinsa ya fasheta, abba ya juyo kansa ya dinga masifa kmr xai maresa, ba shiri ya kame kansa, don ran abba yyi mugun baci ranar. Ganin ba sarki sae Allah yasa inna ta fashe masu da kuka tana cewa "tunda yusufa ya rasu dama nake shan wahala a duniyar nan, daga kai har 'ya yanka bakwa tsinanani da komai, ni ke yi ma kaina duk bukata, Abba ya bude baki yana kallonta ya ma kasa cewa komai, shi din ne baya mata komai? Gnin ta dage sae rera msu kuka take ne yasa ya shiga bata hkri, tce "hka kawae baxan kyautatawa aminiyata ba jikarta xatayi aure, kuma nasan idan na tambayeka ba bani xakayi ba," Abba ya girgixa kai yana mamakin uwartashi, duk juma'ah sae ya bata dubu goma bayan abubuwan da yake siyo mata duk karshen wata sannan ya damka mata dubu ashirin ko tana da bukatar kudi, amma yanxu kiri-kiri tace bbu mai taimaka mata a duniyar nan sae Allahnta, komai ita take ma kanta. Abba yace "to shknan inna, Allah yasa hkn shine mafi alkhairi, kudaden sun isheki de ko? Ta dan fara kame kame tana goge kwalla tace "ni idan san samune akara min dubu hamsin, ko kuma dari ma." takaici yasa abba gyada kae kawae, ya dubi Aliyu yace anjima ka ciro mata dubu hamsin Ali, xan bka, "tab! Ai ni abba accnt dina ko dubu goma bai kai ba ina ga ma." ... Inna ta galla masa harara tace "Allah ya dauwamar dasu a hka," Haisam yace "anjima xan ciro na kawa maki inna." nan ta dinga sa masa albarka, abba yyi mata sallama ya fice daga palon nata cike da jin haushin hali irin nata, Aliyu ya bi bayansa yana cewa "wannan ai sata kiri-kiri ne kawae, daga an baki ajiye sae ki maidashi naki" bai jira me xata ce ba ya fice da sauri yana dariya. Haisam na fitowa daga palon innar umma ta aika a kira mata shi yaje, nan kuwa ta balbalesa da masifa tana cewa" kai dinnan soko ne wllh, Aliyu ya fika wayo nesa ba kusa ba, kana tunanin idan ka dauki kudin naka har dubu hamsin ka bata Alhaji bka xai yi ne? Kai dae bn san wani irin yaro bne Allah ya bani, don meyasa baxakayi koyi da Aliyu ba, duk ka bi ka tare gurinta sae kce ta asirce, wllh idan baka yi gaggawan sauya wannan mugun halin naka ba sae na saba mka" haisam ya girgixa kai cike da takaicin hali irin na uwartasa yace "Allah ya kyauta! Sannan yafice a fusace. Shi kam Aliyu hajiya yaba masa ta dinga yi tana sa masa albrka, shi dae bai tanka mata ba. Da yammacin ranar Haisam ya kaita gidan aminiyartata bayan ta

Chapter 5 of 32