Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shiga kasuwa tayi kaca-kaca da kudin, a dole ita wae sae ta kyautatawa kawartata tunda bikin jikarta ce. Su hajiya kam sun ji ddin xuwan inna gidan bikin don kwana biyar tace xata yi, ko ba komai xasu dan samu sarari a gidan su sheka tsiyarsu yanda suke so. Intisaar na daki wajajen karfe goma na safe tana duba wani Novel na turawa taji hayaniyarsu hajiya a tsakar gidan, ba shiri ta fito ta tarda su hajiya sun saka momynta a gaba sae maganganu suke gya mata fadila na taya su, "idan banda rainin wayo tun asubar fari take ta facakala da ruwa sae kace ita daya ce a gidan, ynxu idan ruwan ya dauke mu da wanne xamuyi ayyukan mu, mun xo muna mata mgna kuma ta maida mu mahaukata, to dae mai daure maki kugu a gidan bata nan, idan kikayi wasa...." xainab ce ta karaso wajen da sauri ita ma tana cewa hva hajiya meye yyi xafi hka da sassafe xa ku sa momy a gaba kuna..." kyakkyawan mari hajiya ta watsa ma xainab din tana cewa "wuce ki bni waje munafuka kawai, dama tun ba yau ba kike nuna ni ba komai bace a wajenki, idan bnda hka taya xa a maida ni mahaukaciya baki xo kin tsaya min ba xaki gya min mgnar bnxa, baki ga yanda fadila take yi bne don ubanki," intisaar ta kalle momynta da ta tsaya tana kallonsu kawae bata ce komai ba, umma ta hankade xainab tana cewa bace mana da gani mara xuciya kawae warce bata san ciwan kanta ba. Girgixa kai momy tayi kawae taci gaba da wankin da take yi a bakin famfon, hajiya ta fixge bokitin a fusace ta xubar da ruwa da kayan dake ciki sannan tasa kafa tayi ball da sauran bokitan tana cewa "don babanki baxa kiyi wankin nan ba yau wllh, mu ma muna da bukatar ruwa" umma ta kashe famfon tana kwadawa rahma kira ta kawo mata kwado su kulle. Intisaar ta goge hawayen idonta ta dubi momynta da ta tsaya kallonsu kawae ba tare da tace uffan ba, tace "momy ki bari anjima xan je waje na debo makii ruwan wankin, xo mu tafi" ta fara jan hannun momyntata su bar wajen, momy kam kasa barin wajen tayi, ta xubawa fadila dake ta faman xaxxaga mata xagi tana cewa "mutum ya xame mana annoba a gida, kuma idan ana magna ya dinga yi kmr kurma don tsoro, wllh hajiya ni kawae da kun bari watarana na lallasa ta na nuna mata....." ji kke tass! Momy ta xuba mata tagwayen mari masu rai da lfya, hava wa! Nan fadila ta gigice ta fasa ihu don batayi xaton marin ba, cike da mamaki hajiya da umma suka dinga salati suna cewa ita fadilar kika mara? Hajiya ta fixgo fadilar tace "xage ki rama fadila, wllh sae kin rama," umma kam tuni aka shige gida da gudu anje shirin dambe, don tace wllh sae ta rama ma 'yar ta. Fadila ta dage xata mari momyn, intisaar ta fixgota da karfi tana cewa "ke yar karamar 'yar iska, ni xakiyi facing ba momyna ba," nan intisaar ta dage ta dinga xuba mata mari tana tana cakume da kwalar rigarta. Nan fa gida ya hautsine, umma ta fito da gudunta bayan ta canxa kaya, tayo kan momy da gudu tana cewa "ae yau sae dae ni ko ke?" tam nan fa momy ta xage ta kai umma kasa suka dinga cin dambe. Su rahma da kursum suka hadu suka dinga dukan intisaar din da taki sakin fadila har ynxu bayan ta kaita kasa ta haye kan ruwan cikinta tana jibgarta iya karfinta. Hajiya na ganin an kai umma kasa ana ta nakada, ta fice waje da gudu tana kiran jama'ah su xo su ga xainabu xata kashe Shafa. Xainab na shiga daki da kukanta dama abba ta kira amma yaki xuwa, ya Haisam ya tafi kaduna tun jiya, don hka kawae sae ta kira Aliyu tana kuka ta gya masa, sannan ta fito taga irin damben da ake ci, kuka ta dinga yi sosae ta ma rasa abinda xata yi ga muryar Hajiyrsu can a wje tana aibanta momy, mata suka dinga tururuwa cikin gidan duk da wsu gulma ya shigo dasu, ihsan ma kuka ta dinga yi a kusa da xainb tana cewa "Anty kice momyna ta bari." da kyar matan suka kwace umma a hannunm momy, sannan aka raba su intisaar shi ma da kyar don intisaar komawa tayi kmr mahaukaciya duk tayi ma fadila kaca-kaca hka ma kursum dake.. Xainab ta karasa kusa da intisaar da hanxarinta bayan an rabasu, ta fara janta ixuwa palonsu, fadila kam ihu ta dinga yi tana fixge fixge daga rikon da akayi mata wae a barta sae ta kashe intisaar yau, momy ta ja bokitin ta ta tara a famfon tana cewa "kuma wanki yanxu na fara, bnga uban da ya isa ya hanani ba, kuna tunanin shirun da nake maku tsoro ne, wllh duk wanda yace baxae kame girmansa ba a cikin ku xai ko sha mamaki." rirrike hajiya aka shiga yi wae sae tayi ma momy duka, hka ma umma ko kunya bbu. Wata yar dattijuwa da tashigo gidan ta dube momy tace "to ke 'yar nan tunda gaba suke dake ki bari anjima kiyi wankin mana, ina ce sunce aiki suke son suyi da ruwan su ma" momy tace "ki bari kawae baaba wllh munafukan mutane ne, idan bnda hka famfofin gidan nan sun kai biyar pa, kuma ko wanne na da nasa pampon a bangarensa, nan bangarena ne amma sbda neman mgna suka kwaso jiki suka xo wae baxanyi wanki ba, kuma wllh baaba tank din gidan nan babba ne, ko xan kai washegari ina wanki bbu abinda xae ragu a ruwan amma dayake jirana sukeyi shi yasa nayi laifi, toh bari kuji, wllh tllh daga yau duk shegen da yace xae sake takani a gidan nan sae ya sha mamaki." hajiya tace "mu kke gyawa magana hka xainabu, dama ashe kina mgna hka amma don munafurci idan kinga Alhaji sae ki dinga yi kmr na kirki? Don Allah ku sakeni na gwada mata hnkli." momy tace "ku kyaleta don Allah" umma ta dinga dura mata ashar ta uwa ta uba tana daga inda take, don bata sake gigin matsowa kusa da ita ba, a dai-dai lkcn Aliyu ya shigo gidan, ya girgixa kai cike da takaici ya jingina gefen gate din rungume da hannuwansa yana kallonsu, muryar momy yaji tana cewa "don Allah don Annabi ku kyaleta ta dokeni, wllh tllh Aisha sae kinyi da kin sanin sani na, don laga-laga xan maki kuma ba lallai ne mijin ki ma ya gne ki ba. A fusace Aliyun ya karaso cikin tsakar gidan yana kallonsu daya bayan daya, basu ma san yashigo ba, ya dubi fadila da bata da maraba da hauka gashin nan yyibuya-buya, daga ita sae leggings, intisaar ta dube fadilar dake xaginta ta uwa ta uba tana kiranta da 'yar tsintuwar innarsu, tace " duk da hkn dae ban xage ina karuwanci ba, na fita tun asuba na dawo karfe takwas din dare." fadila ta kara rudewa ta shiga galla wa masu rikonta cixo wae sae sun saketa ta mata duka, sae kace ba ita aka kwata da kyar daga hannun intisaar din ba ynxu, Aliyu ya karaso wajen ya sa kafa ya kwashe fadilar ta xube kasa sannan yashiga ball da ita yana cewa "yau xaku ci ubanku gaba daya, go down on ur kneels, i said go down on ur kneels." ya fadi cikin tsawa sannan yyi kan intisaar din da tuni ta juya a guje xata bar wajen ita ma ya cafkota ya watsa mata mari lafiyayye, momy ta karaso inda yke da sauri tana cewa "kai! Kai! Wllh kar ka kuskura ka taba min 'ya, cika ta, ta fixge hannunsa daga rikon da yyi wa intisaar din, cikin tsawa tace mata shiga ciki, ta ja ihsaan ma suka bar wajen" binta yyi da kallon mamaki, ya juya kan su hajiya dake ta cacan baki amma an rasa wanda xae tunkareta yace "wllh hajiya kina bni mamaki, ynxu meye amfanin irin wannan abun, don me baxa ku kama girmanku ba, dube yanda yar cikin ku tasa ku gaba tana gaggaya maku maganganu, sae faman kumfar baki kuke," kai Aliyu kasan me ya faru ne? Kasan irin abinda tayi ma umma?"hajiya ta fadi tana xaxxaro ido, yyi tsaki yace koma me tayi maku kuka siyar wa kanku. Ya dube su kursum da har ynxu suka ki yin shiru ya daka masu tsawa yana cewa "bna son naga ko wani dabba a tsakar gidan nan ryt now, get out" da sauri duka suka watse suka yi sashinsu, shima yyi nasa bangaren ya bar umma da hajiya a wajen.. Gaba daya mutan gidan sun hallara a falon Abba washegari da safe, Momy na xaune kan 1seater fuskar ta a daure ta xuba ma plasman ake manne jikin bango ido, intisaar na gefenta a kasa a xaune, hajiya da umma na xaune a 2seater suma rai a hade, sauran 'yan matan ma gaba daya sun nemi gu sun xauna a palon, ihsaan kadae ce ke gefen abbanta a xaune, Aliyu ya shigo da sallamarsa a dalilin kiran da abba ya aika ayi masa, ya nemi gefe shima ya xauna. Abba yyi ajiyar xuciya ya dubi intisaar yace "fateemah ki gya min abinda ya faru a gidan nan jiya bayan na fita" nan intisaar ta koro masa duka abinda ya faru a jiyan, ya jinjina kai yace "ikon Allah" hajiya ta yi saurin cewa "kaji munafuka amma ai baki gya masa irin fitsarar da uwartaki ta dinga mana ba" abba ya daka mata tsawa ransa a bace yace "ki shiga hankalinki." ta ja bakinta tayi shiru tana hararar sa. Abba yyi shiru sannan ya nisa ransa a bace yace "xainab ban san ki da irin wannan halin ba, amma gskya jiya kin ban mamaki, a tunanina ko da ace abinda yafi xagi shafa ta maki bata cacanci ki rama ba bare har ki hau ta da dambe ba, kinga kina da laifi a nan tunda dae shafa ba sa'arki bace, don me baxaki jirani na dawo ba ko ki kirani a waya? Har xagi dubi tsabagen idon Aisha baki ji kunyar 'ya yanta ba kice mata karuwa.?" tsam momy ta mike tayi masa wani irin kallo tayi hanyar fita daga palon ba tare da ta ce komai ba, kiranta abba ya shiga yi amma ko waiwayowa bata yi ba har ta fice daga palon. Hajiya tayi murmushin takaici tace "ka gani wa idon ka ko? Wllh jiya na dde ina naxarin anya kuwa xainabu ce wannan, rirrike ta fa aka dinga yi xata min duka bayan an rabata da umma. Umma ta tabe baki tace "uhum ae ni naga abun mamaki jiya, yarinyar da mutum sae ya rantse ya dada rantse wa yace ko kuda baxata iya kashewa ba, amma ashe duk wannan shiru shirun da take yi don taga inna na nan ne, jiya ta nuna mana ko ita wacece." Aliyu kam tunda ya shigo falon yake ta daddanna wayrsa bae ko daga kai ba. Abba ya dube su intisaar din gaba daya yace "daga yau na sake jin abu makamancin hka ya faru a gidan nan wllh tllh sae na karya mutum, kuma bna son naji wata magana ya fita daga nan har yaje kunnan inna, idan na kama mutum da karya wannan dokan sai na saba mashi kwarai da gaske, ku tashi ku ban waje shashashan bnxa kawai" duka suka mike suka bar palon, intisaar kam jikinta yyi sanyi sosae. Hajiya tace tana nuna intisaar "har da 'yar mitsitsiyar 'yar nan, ta dubi tsabagen ido na tace min mayya" sae kuma ta fashe da kuka tana girgixa kai tace amma bbu komai ai tun farko idan muka ce mka ga abinda xainabu tayi bka yarda ynxu kam ai ka gani da idonka, Aliyu ya mike yana kallon abban nasa yace "kayi hkuri abba," sannan ya fice. Nan hajiya da umma suka dinga aibanta momy, hajiya sae matse kwalla take, abba kam tv ya xuba ma ido bai tanka masu ba, umma tace "har ca tayi wae fadila ba 'yar ka bace karuwan....." tsawa abbaya daka masu ya mike yana cewa "ku fitar min a palo don Allah, sannan ya shige bedroom." hajiya ta bude baki hka ma umma, hajiya tace "da yake ran matan so, kuma yar gwal ya bace dole duk ka fice hayyacinka ae. " nan da suka gaba babatunsu su mike suka fice daga palon kowa da takaicinsa. Intisaar na xaune kan darduma bayan ta idar da sllhr isha'i, Abba yyi sallama ya shigo palonnasu, ta ce "sannu da xuwa abba, ina yini" yace "lfya lau fatima ina momyn taku?" tace "tana cikin daki" bai ce komai ba ya shiga dakin da sllma, ba kasafai Abba ke shigowa bangaren matan nasa ba sai da babban dalili, ta mike ta kwashe kwanukan da suka ci abinci ta fita dasu ta wanke don momynta ce tayi girki, sae da tashiga kicin ta kwaso sauran kwanukan wanke- wanken mutan gidan sannan taje bakin famfo tana wankesu don tana tsoran wankesu a kicin kar 'yan gidan su rutsa ta, tun da safe dama momy bata barta ta fito ba, ita tayi duka ayyukanta sae xainab da ta fake idon hajiyarsu ta dan kama mata. Tana gama wanke kwanukan ta kwashesu tayi kicin din don ta ajiye ko wanne a maxauninsa, Aliyu ta gani tsaye yana hada coffee, ta juya da sauri xata bar wajen taji yace "one more step, yhu are in trouble." mutuwar tsaye tayi a wajen xuciyarta na dukan uku- uku, yau ta shiga uka dukanta xai yi tasani " ya karaso inda take ya xagayo ya tsaya gabanta yana mata wani irin kallon, tuni kwalla ya taru a idonta, yyi murmushin mugunta yace "yaushe kuka fara samun liver a gidan nan daga ke har uwarki," amsar ki kadae xata ceceki yau a nan, idan ba hka ba wllh tllh sae na fasa kanki a nan wajen, save my tym ki bani amsata, am ol ears. Ya fadi da tsawa " kuka ta fara yi tace "ni dae don Allah don annabi kayi hkuri ka....." muryar Abba suka ji yana cewa "wat's goin on in there?" ya fadi da xolaya, Aliyun ya kirkiro murmushi ya fara kame-kame, No Abba.. Kawae taimaka mata nke ne... Sae kuma ya karbi kwanukan dake hannunta ya fara kkrin ajiye su inda suke, Abba yace "uhum ok yyi kyau hkn, idan ka gama kaxo ka sameni, we hve an issue 2 discuss" Aliyun yace "yes sir" batare da ya kallesa ba sannan abba ya bar wajen, da gudu intisaar ta juya ta bar wajen bayan Abba yyi gaba, wae juyawar da xai yi sai ganin wajen yyi wayam ba kowa, ya cije lebe cike da takaici sannan ya ajiye kwanukan hannunsa ya juya ya bar kicin din yana tunanin irin abinda xae mata idan ya kamata. Bayan kwana biyu komai ya dawo nml a gidan, da momy ta dauki xafi sosae amma abba na xuwa ya bata hkuri sae ta ajiye fushin da tayi da tace masa komai ae ya wuce, ya ji ddin hkn sosae don idan ba wannan karan ba ma bai taba ganin bacin ranta ba kuma ya gano ita ke da gskya bayan yyi bincike sosae a kan lamarin, su hajiya kuwa ya je yyi masu kashedi mai girma akan su fita harkar matarshi, idan xaman gidan da suka je sukayi na kusan wata hudu bai ishesu ba to xasu koma ne, hkn yasa suka kame kansu don sun san shi sarai. Ranar laraba inna ta dawo gidan da mota shake da kaya, har gida aka kawota aka ajiye, su intisaar da xainab suka dinga shigowa da kaya kowa na murnar dawowan ta, ita kuwa baki har kunne ta dinga fadin irin yanda aka dinga karramata a gidan bikin don inna akwae son girma, bakin kofarta su hajiya suka tsaya sukayi mata sannu da xuwa sama-sama suka yi gaba. Ta ja dogon tsaki tace "munafukan bnxa kawae da alamar ma basu yi farin ciki da dawowa na ba." intisaar dake ta faman bubbude kayan da suka shishshigo da bata tanka wa inna ba. Momy ma taxo tayi mata sannu daxu suka danyi hira sannan ta wuce, falon ya rage daga ita sae jikokinta tana ta faman kullawa kowa tsarabarsa a leda. Intisaar ta kai nasu gida, hka ma xainab da kursum. Fadila ta shigo gaida inna, inna ta saka sallati tana kallon fadilar tace "hatsarin mota kika yi fadila?" ta tambaya ganin yanda bakin fadila ya kumbura da fuskarta, xainab dake cikin bedroom tana gyara ma inna daki, ta toshe bakinta ganin dariya na neman subce mata. Fadila ta harari innar tace "hatsarin jirgi nayi ba ta mota ba." ta juya ta fice fuuuu. Inna ta kwashe da dariya tana cewa "ikon Allah," xainab na gamawa ta fito tana dariya tace "inna ki min alkawari idan na gya maki maganar nan xaki barshi a cikin ki" inna tace "hva Abu, sae kace wata yarinya sae naje ina cewa ga abinda xainab tace min." xainab tace "yauwa inna." nan xainab ta xauna ta xayyane wa inna abinda ya faru kwana hudu da suka wuce a gidan." bata kai karshe ba inna ta mike tana cewa " kut! Ae yau sae sun gya min ko pampopin gidan nan na ubansu ne, sae sun gya min me xainabu ta tsare masu a gidan nan" xainab ta mike a rude tana cewa "nashiga uku inna don Allah ki rufamin asiri abba yace kar wanda ya gya maki, ballani xai yi wllh" shi bukar din yace kar a gya min? to xai dawo ya sameni shima," inna ta fadi a fusace ta fice daga palon." da gudu xainab tayi sashinsu ta shige bathroom ba tare da ta bari hajiya ta ganta ba jikinta na bari. Inna ta karaso tsakar gidan cikin daga murya tane cewa "ina munafukan gidan... To don ubanku ku fito ku gya min ko ubanku ne ya dasa ma da'na famfofi a gidan, ku fito ku gya min ko nairan ku nawa ne a ciki na biya ku. Sbda me xaku sa min 'ya a gaba a cikin gidan nan, uban me ta tsare maku? Ku fito ku gya min me xainabu ta tsare maku nace matsiyata " cikin daga murya inna ke ta xuba masu rashin mutumci. Momy ta dube intisaar fuskarta daure tace "don ubanki sai da kika je kka gyawa inna wannan mgnar bayan abinda....." intisaar ta xaro ido a tsorace tace "wllh momy ban gya ma inna komai ba, tana bani tsarabar mu ae ban sake komawa ba ma." abin ya daure wa momy kai, to waye ya gya ma inna wannan mgnar? Hajiya kuwa kasa xaune tayi sae kaiwa take tana komowa a palonta, ynxu xainabu sae da taje ta gya ma tsohuwar nan wannan mgnar. Hka ma umma dake ta lekar innar ta taga da 'ya yanta, tsinuwa kam sun sha shi ba adadi . Ganin inna taki barin tsakar gidan ne tana ta masifa yasa momy ta fito ta dinga bata hkuri ta koma sashinta, amma kememe inna taki ta dinga xunduma masu ashar tana cewa ae yau sai tasa sun bar gidan nan, momy tayi sumsum ta koma sashinta ganin ba sauraranta inna xatayi ba. Tun a kofar gida haisam da Aliyu suka dinga jin muryar inna kmr speaker, Aliyu ya tabe baki ya koma mota ya ciro apple dinsa da ya manta a ciki, haisam kadae ya karaso gate din ya shiga gidan ransa a bace, wannan wani irin masifa ce hka, kullum sae anji hayaniya a gidansu sae kace makaranta, yana shiga gidan ya ga irin rashin mutuncin da inna ke xubawa a gidan ya juya ya bar gidan kawai. Dariya Aliyu yyi ganin yanda Haisam ya fito daga gidan, ko kallonsa Haisam bai yi ba ya shige motarsa yyi gaba. Aliyu ya shiga gidan ya dauki farar kujerar roba ya xauna gefen wani flower yana ta kallon inna yana cin apple dinsa with much interest. Tana ta masifa har da kukanta, "wllh kwado xan sa wa duka famfofn gidan, duk shegen da xae yi amfni da ruwa yaje waje ," tana kai wa nan ta fice daga gidan tana gunjin kuka. Dariya Aliyu ya dinga yi har da buga kafa, hajiya ta fito jin muryar dan nata, ta rike haba tana cewa "ka ga makirci ko Ali, ynxu bayan duk abinda Alhaji yace sae da wannan tsinanniyar matar ta gya wa wannan mayyar tsohuwar ko?" shi dai bai ce komai ba yana ta cin tufarsa. Umma ta fito ita ma tana cewa " wannan anyi makirar mace....." shigowar inna ce ta sa su yin tsit. Kananan kwadunaye inna ta shigo da har guda biyar, su ka bita da kallon mamaki. " idan akwae shegen da ya isa ya matso kusa da famfofin da na ya gani." hka inna ta dinga dasa wa famfofin kwado tana mita, sashinsu intisaar da nata kadae ne bata je ba, Aliyu binta yke tayi da kallo har ta gama, ta dawo tsakar gidan ta dauki kujera ta xauna tana girgixa kafa. Sumsum su hajiya da umma suka shige gida, Aliyu ya mike yyi hanyar kicin sae gashi ya fito da tabarya, yyi hanyar daya daga cikin taps din, bugu uku yyi ma kwadon ya balle, inna ta taso da gudu tana cewa xan ci ubanka wllh idan ka sake shiga gonata Aliyu.... Tsawa ya daka mata yana cewa "to me kke nufi hajiya, baxan wanke hannuna ba kuma ko meye?" yyi tsaki ya bude tap din yana wanke hannayensa, ranar dae hka Aliyu ya maida inna mahaukaciya a tsakar gidan, tana yi, yana ta kyalkyale dariya, hkn yasa ta dinga rusa kuka wae bukar take jira a tsakar gidan. Abba yyi jigum yana sauraran maganganun uwartasa da bae da ma'ana kuma bai da tushe, ya jira har ta kai aya sannan ya mike yana kallonta rai bace "to wae baaba meye na tada maganar da ya wuce kwana da kwanaki, meyasa kike yin hka ne fisabilillahi, ynxu ca akayi maki xainab din bata hkura bne ko kuma su hajiya basu amsa lafin nasu bne?" inna ta marairaice fuska tace "to ni ina nasani, ca nke ae maganar tana nan ne har ynxu," Abba yyi tsaki yace "wannan wani irin abu ne don Allah, ko ma bai wuce ba ina ruwanki cikin maganar, tsakanina ne da iyalina," inna dae sae wuri-wuri take da ido, su hajiya kmr su yi shewa don murna, ya dube gaba daya 'ya yan nasa dake falon fuskarsa a tamke yace "cikin ku waye ya gya ma baaba wannan maganar? Kuma duk wanda yyi min krya sae na yi mugun saba masa wllh" yasan momy baxata taba gyawa inna wannan mgnr ba duk da su hajiya sun ce masa ita ta gya wa innar amma bai tanka masu ba, don yasan wacece ita. nan xainab ta dinga cunkulin inna alamar ta rufa mata asiri jikinta na bari, hankadata inna tayi tana cewa "ke don ubanki ki rabu dani sae shisshigeni kike yi sae kace yarinya," xainab saura kadan ta saki fitsari don ca take inna tona mata asiri xatayi. Aliyu ya daka ma kanninnasa tsawa yana cewa "ba magana ake maku ba wawaye kawai," inna ta kalle Aliyun kmr me naxari, can sai tace "to ni Aliyu ne ya gya min wannan mgnar ba kowa ba." Aliyu ya firfito da ido yace "ni inna," ta galla masa harara tace "munafuki kawai, shine ya gya min bukar, ko karya nayi mka?" Abba ya juya yana kallon Aliyun ransa ya dada baci, Aliyu xai yi magana abba ya daka masa tsawa yana cewa "karya knan tayi mka," inna tace "Atoh dae, ina xaune yaxo ya sameni ya gya min, intisaar ae tana wajen lkcin, ko krya nayi intisaar?" ta tambaya tana kallon intisaar din. Intisaar tayi narai-narai da ido cikin karkarwar murya tace "don Allah don annabi inna ki rufa min asiri ni wllh ina gidanmu lkcn, bn san kun yi ba" inna tace "au hka ne kuma, daga ni sae shi a palon lkcn." haisam ya kalli Aliyun da ya ma kasa cewa komae sae kada wa da idonsa yyi yana kallon innar ko kifta ido baya yi, sae dariya ta subce masa, abba ya juya yana kallonsa a fusace, ya mike yyi saurin barin palon yana yar dariya, shi dae yasan inna sharri tayi ma Aliyu don Aliyu bai da surutu kawae dae yasan ramuwar irin abinda Aliyu ke yi mata a gidan tayi ne. Ranar kuka ne kawae Aliyu bai yi ba, don wanki babban bargo Abba yyi masa "tashi ka bni waje karka sa na watsa mka mari, abinda yaci ace kanninka ne sukayi sai gashi wae kai da knka kayi" Abba ya fadi cikin bacin rai bayan yyi fadan har ya gaji, Aliyu ya mike kmr xaki ya fice fuu daga palon, inna ta rakasa da cewa "munafuki kawae." hajiya ta mike a fusace ita ma ta fice daga palon, sae bayan ya fita su kursum suka fashe da dariyar da suke hadiyewa tun tuni, inna ma ta taya su dn ta rama iskancin da ya dinga mta a tsakar gida jiya, har xainab sae da tayi dariyar, intisar kadae ce bata yi ta ba ta hade rai. Intisar na tsakar gda tana taya xainb tsifan kanta aka bude gate din gidan gaba daya suka maida hnklinsu wurin gate din su ga wanda xae shigo, Aliyu ne da safeenah su ka shigo gidan, xainab tace "tab, amma wannan yarinyar jaka ce mara xuciya, ynxu sae da ta sake xuwa gidan....." da sauri intisaar ta katse ta da cewa "kinga ni ba ruwana ki bar xancen nan xainab" bangaren hajiya suka wuce bayan intisaar da xainab sun gaisheta tayi masu bnxa, shi ko ya watsa masu harara. Xainab ta fashe da dariya a hankali tana cewa "ina ma Allah ya kawo inna nan mu ci dariya wllh," intisaar tace "ki dae ci dariya amma bnda ni" xainab tayi dariya tace "shegiya matsoraciya, dubi fa kayan da tasa yau har gwanda na ranan nan," intisaar ta mike tace "kinga idan baki son tsifan nan ne na wuce don ni bbu ruwana wllh karki ki jaxa min" xainab ta fixgota tana dariya tace "to yi hkuri nayi shiru xo ki karasa min." suna wajen har bayan kusan awa biyu sannan suka fito, hajiya sae wangale baki take yi tana cewa "Allah yyi maki albarka safeenah, mun gode sosai, ki gaishe min da hajiya kice sae naxo, umma ma tafito tana cewa "Allah dae ya nuna mana wannan abun arxikin" leda kato su hajiya da umma suka cika mata da tsaraba khadija na rike da ledan kmr xata shige jikinsafeenar dake ta murmushi tana gdya, hajiya ta hade rai ganin xainab da intisaar tace "don ubanki kin xo kin gaida antynki ko sae na taka ki a nan," ta galla wa intisaar harara tace "tashi ki ba mutane waje munafuka kawae." da sauri intisaar ta mike ta bar wajen tayi sashinsu, safeena tana yatsine fuska tace "wae hajiya wacece wannan yarinyar?" hajiya ta tabe baki tace "agolar gidan ce" safeenah tace "tabdijam" umma tace to ya muka iya. Aliyu ya fito da makullin mota don maida ta gida xai yi yace "ta yi maki wani abu ne dear?" ta tabe baki tace "muje kawae" har gate hajiya da umma suka rakota suna sa mata albarka, hajiya tace "ki fa ba wa hajiya sakona," tace "xan bata hajiya" sannan suka wuce ita da Aliyun. Umma tace "gskya amintakan ku da hajiya mairo yyi, tunda har ta dauki tilon 'yar ta xata ba danki," hajiya tayi murmushi tace "ae ni bbu abinda xance da mairo, baki ji yanda naji ba ran da ta kirani take gaya min irin rashin mutuncin da tsohuwar nan tayi ma safeenah da bama gidan, wllh naji takaici sosae" umma tace "to ae laifinsa ne, don me yasan bama gidan xai daukota ya kawo ta bayan yasan yan hassada ne a gidan, idan kin bibiya ma xainabu ce ta xuga innar tayi ma safeenar hkan." hajiya tace "ae ba takanas ya dauko ta ya kawo ta gidan ba, hanya ce ta biyo dasu ta nan shine yace bari ta gaida kakarsa, ae tasan bama gidan." muryar inna da suka ji tana kwada wa fadila kira ne yasa suka yi tsit, kursum tace "bata nan" inna ta rike haba tace "ohh ni rahmatu yarinya ta maida kanta gantalalliya kmr akuya anki tsawatar mata, amma ba laifin kowa bne, na bukar ne, ae da ya aurar da ita da duk hka bata faru ba." tayi gaba tana ta mitocinta. Hajiya da umma suka tabe baki, umma tace "randa wannan tsohuwar xata mutu ae sae na xuba ruwa a kasa nasha," hajiya tace "ae ba ke kadai ba shafa." Abba yace "gani inna," bayan yaje kiran da mahaifiyar tasa ke masa. Dama bukar dubu ashirin xaka bani nayi ma yaran Nafisa tsaraba don gobe xanje gidanta, Abba yace "to inna bari haisam yaxo ya ciro maki." tace "yanxu fa nake so ni dae wllh, don bn yarda da wannan wayon naka ba, sau dayawa hka kke min" Abba ya jin jina kai yace "ynxu xai kawo maki baaba." cike da jin haushi yyi maganar ko sati uku ba ayi ba da ta saida masa fili sannan ya kara mata da dubu hamsin amma har tana tambayar wani dubi ashirin din. Haisam tasa ya kaita sukayi shoppin din, ta jida kayan kusan dubu talatin, dole shi ya cika sannan ya maido ta gida. Washegari ta samu Abba wae ya samo wanda xai kaita, haisam baya nan, don hka dole yasa a kira masa Aliyusukayi Aliyu na shigo wa palon Abban nasa ya nemi gu ya xauna ya gaida shi a ladabce sannan yace "gani Abba" Abba ya hade rai yace "ka gaida inna ne yau?" inna ta tabe baki tace "ae ni rabon da Aliyu ya gaida ni tun ran da na ce shi yyi min wannan gulman" Aliyu

Chapter 6 of 32