Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kina sha'awan komawa dakin ki?" inteesar ta share hawayen da ya gangaro mata tace "Abba don Allah don Annabi ka sa shi ya sallameni, ni bana son auren kuma ka yi mani adalci abba," Abba yyi shiru yana kallonta snn yace "to kiyi hkuri ki bari har sae kin sauka lfya, na maki alkawarin xan sa ya baki takardarki ko yaki ko yaso," muryarta na rawa tace "ngdd Abba," Abba yace "kya iya tafi amma bana son xaman ki tare da inna, ki koma gun ummanki ynxun nn kuma," kai kawae ta gyada masa ta mike xata fita, Aliyu yyi sallamaya shigo falon, ta hade rae ta bi ta gefensa ta fice, ya bi ta da kallo snn ya xauna inda ta tashi, ya gaida Abbansa, Abba ya amsa yana duba newspaper, yyi shiru na dan lkci snn a hankali yace "Abba kayi mata magana," Abba ya dago yana masa mugun kallo yace"wani maganan xan mata," Aliyu ya sunkuyar da kansa bae ce komai ba, Abba yace "ae ni na gaya maka baxan mata dole ba, kajekayi xamanka da dayar matarka tace baxata koma ba," Aliyu yyi shiru da ganinsa bae ji ddin maganar ba, ganin Abba ya maida hankalinsa kan abinda yake yasa yace "to Abba kayi mata maganarkar ta sake yunkurin xubar min da ciki," Abba yace "tashi ka ban waje, nonsense kawae" Aliyu bae ce komai ba ya mike yyi masa sallama ya fita daga falon ba tare da Abba ya amsa ba. Dakin Haisam ya nufa, ya samesa ya gama shiri xae fita office, Haisam yace "daga ina da sassafe hka," Aliyu yace "taimako nake son ka min Haisam, kasan yarinyar nn na jin maganarka don Allah kace mata ta yi hkuri ta koma dakinta, ni wllh bana son wani abu ya sami yaran nn ne, kasan yarinta yyi mata yawa, ga inna kuma ba tsohuwar arxiki ba ko ita xata rakata su fake idon Abba suce xasu je cire cikin kuma" haisam yyi yar dariya yace "da knn Inteesar ke jin maganata ba ynxu . Aliyu ya dafasa yace "plss ka gwada kaga Haisam, wllh bana son xamanta a gidan nn," Haisam yace "shknn xan gwada yi mata maganan ltr idan na dawo," Aliyu yace "thank yhu," a tare suka fita da Haisam kowa ya kama hanyarsa. Inteesar na komawa falon inna, inna ta mike da sauri ta dawo kusa da ita tace "me Bukar din yace maki," inteesar tayi shiru da ganin idonta kasan tayi kuka, inna ta mike a fusace tace "xan ko ci mutuncinsa, da wnne xaki ji," tana fadin hka ta fixgi mayafi a fusace tayi waje, da sauri inteesar ta bi ta ta riko hannunta tace "ni inna bbu abinda aka min kin wani kwashi kafafuwa ina xaki," inna tace "to kukan me ki ke yi ba ayi maki komai ba," inteesar tace "ni ki rabu dani," ta shige bedroom ta bar ta nn tsaye, inna ta bude baki tace "au" can ta tabe baki ta ci gaba da aikinta. Karfe tara saura tace ma inna xata gun momynta, inna tace "yau kuma, to ki tsaya ki sha kunun da na dama maki tunda kin ki shan tean" inteesar tace "xan dawo inna," snn ta fice daga falon tayi sashinsu a sanyaye duk sae taji bata jin ddin jikinta, wanke wanke ta tarar momynta nayi a bakin famfo, ta karasa tace "sannu da aiki momy, kawo na karasa maki," momy tace "A'a bar shi kawae," inteesar bata ce komai ba ta shiga falo ta karasa bedroom din momynta tayi kwanciyarta, duk jikinta a sanyaye yake wae mayen cikin nn na jikinta duk axaban da ta sha, hawaye ne ya shiga bin kuncinta, ta dde tana kuka a hankali daga bisanni bacci ya dauketa, karfe goma momy ta shigo dakin ta tada ta tace "kin karya ne," inteesar ta gyada mata kai tace "ehh" momy ta juya ta fita daga dakin, baccinta ta ci gaba da yi har kusan sha biyu, xaxxabi ya fararkar da ita, sanyi ssae ta dinga ji ta mike da kyar ta dauko bargo ta lulluba, biyu saura momy ta shigo dakin tace "kinyi sllh ne," ta girgixa mata kai da kyar tace "ynxu xanyi," momy ta karaso jikin gadon tana kallonta ganin yanda ta takure kanta tace "me ya same ki," da kyar inteesar tace "bana jin ddi ne," momy bata ce komai ba ta fita, can bayan kmr minti goma ta shigo dakin rike da kulan abinci tace "ki tashi ki ci abinci, kina shan magunguna ne," kai kawae inteesar ta gyada mata ba don tana shan maganin ba, ta sauko da kyar momy ta xuba mata abincin ta fita, tuwan shinkafa ce da miyar bitter leaf tayi mata, inteesar ta mike da kyar ta shiga bayi ta kurkure bakinta ta wanke hannu ta fito ta jawo tuwan gabanta ta shiga ci a hankali, loma uku kawae ta ci taji xuciyarta na tashi ta rasa inda xata sa kanta, lkci daya aman ya xo mata ta mike da gudu ta fada bayi ta shiga kwarara amai, momy dake falo ta shigo dakin da sauri ta shiga bayin tana kallonta, har ta gama aman snn ta taimaka mata ta gyara jikinta suka fito, momy tace "ina magungunan da kike sha," ta kwanta tana girgixa kai ta kasa cewa komai sae mayar da numfashi da take, momy ta shiga bayin ta gyara inda tayi aman ko da ta fito inteesar tayi bacci, don hka ta rufe tuwan ta ajiye mata a gefe. Karfe shidda Haisam ya shigo falonsu ya gaida momy dake koya ma ihsaan assignment, ta amsa da fara'arta tana tambayrsa ya aiki, yace "Alhmdllh momy, inna tace min inteesar na nn," momy tace "eh tana nn," Haisam yace "wajenta na xo momy," momy tace "eyya sae dae kuma bacci take wllh tunda safe take amai, tama ki cin komai, nayi mata maganan magungunanta tace suna gida," Haisam yace "subhanallahi momy ae da sai kiyi magana, ko Abba ki kira a san yanda xa ayi," momy ta mike tace "bari na taso maka ita to," da sauri yace "A'a ki bar ta kawae, na dawo anjima," momy tace "to shknn," ya mike ya fita yana ma ihsaan wasa. Yana komawa sashinsa kiran Aliyu ya shigo wayarsa, ya daga Aliyu yace "ya dae brother kayi mata maganan," Haisam yace "ynxun nn ma na dawo daga gunta, amma sae dae ban samu ganinta ba ma, bata da lafiya wae tun safe take amai inji momy," Aliyu yace "amai kuma, God! Bari xan shigo ynxu," kasa sukuni Aliyu yyi har sae da ya iso gidan wajen karfe tara saura don aiki yyi masa yawa a clinic, sashinsu ya nufa, yana isa kuwa ya kasa shiga ya dde tsaye bakin kofa daga bisanni ya dake yyi sallama, ihsaan ce ta amsa ya bude kofar ya shiga, momy na xaune suna cin abinci da ihsaan, kansa a kasa ya shigo falon ya nemi kujera ya xauna yana kallon Ihsaan kmr ita yake gaisarwa yace "ina yini," momy ba tare da ta kallesa ba tace "qlau," bae sake cewa komai ba ya shiga kallon TV, momy ta mike da sauri jin kakarin aman inteesar, Aliyu ya bi ta da kallo ransa a dagule don shima ya ji, ya rasa me xae ce mata ne, momy na shiga bedroom din ta sameta bakin kofar bayi tana amai, ta kamata tana yi mata sannu, kuka kawae take tana juye juye, momy ta gyara mata jiki ta mayar da ita kan gadon, snn ta gyara wajen ta koma falo ta ci gaba da ba ihsaan abinci. Aliyu ya dauke kansa da sauri daga kallon da yake ma bakin kofar kmr ya shiga, ya kai kusan awa daya xaune a dakin idonsa na kan TV, daga bisanni ya mike da kyar ganin momy nata harkan gabanta yace "na tafi," ba tare da ta kalli inda yake ba . .. Aliyu na fita Haisam yaje ya samu a sashinsa, Haisam yace "ya dae har ka shigo," ya xauna bae ce komai ba, Haisam ya ci gaba da abinda yake, can Aliyu yace "don Allah Haisam kaje ka ma Abba magana su bani matata in tafi ni fa ana min abinda aka ga dama a gidan nn," a fusace ya karasa maganar, Haisam yace "uhm Aliyu knn, har ka manta rashin mutuncin da kayi wks bck knn," Aliyu yace "to ba su suka nema ba, ni don Allah ka rabu dani," Haisam ya daga kafada yace "da kuna shiri da Hajiya inna da da gudu xata sa a baka matarka, ynxu kam ita da kanta xata xuga a hanaka," Aliyu ya kasa cewa komai, Haisam yace "to ynxu ka shiga ka duba ta ne," da kmr baxae yi magana ba yace "wani dubata xanyi bayan kasan halin mamanta, yi tayi kmr bata san me ya kawo ni ba, hasalima barina tayi nata xama kaman mara aikin yi a falon, ni kuma ban san me xance mata ba," Haisam yyi dariya, Aliyu ya galla masa harara yace "wat's funny," Haisam yace "to ae in dae momy ne ma kadan ka fara gani ynxu," dariya Haisam ya ci gaba da yi, Aliyu ya mike xae fita ya riko hannunsa da sauri yace "to bari muje in rakaka sae na ari bakin ka," Aliyu yace "gud," a tare suka koma falon, bbu kowa falon sae Tv dake aiki, momy ta fito dan Haisam ne yyi sallamar, tace "A'a har ka dawo Haisam," Haisam yace "wllh momy, ya jikin inteesar din," momy tace "da sauki," Haisam yace "wae fa dubata Aliyu ya shigo yi shine ya kasa cewa komai," bbu yabo bbu fallasa momy tace "ayyo ae tana ciki," Haisam yace "to shi dae na gani ya shigo ya xauna kmr," da sauri Aliyu ya take kafar Haisam, Haisam ya rama snn ya ci gaba, "maimakon yace ga abinda ya shigo yi, ynxu bacci take momy?" momy bata kallesu ba tace "eh" snn ta fice daga falon, Aliyu ya mike da sauri yyi hanyar bedroom din Haisam na cewa "kai wa yace ka shiga," ko kallonsa bae yi ba, kwance ya tarda ta cikin bargo ta lullube gaba daya har kanta, ya cire bargon, jikinta yyi mugun xafi, ya dagota yana kallonta da tausayi, a hankali ta bude ido tana kallonsa, ya rungumeta murya kasa yace "srry my Fateema," turasa ta shiga yi yaki sakinta, ta fashe da kuka tace "ni ka rabu dani," ya rufe bakinta yace "kiyi hkuri don Allah," lamo tayi jikinsa a hankali yace "kin ci abinci?" ta girgixa masa kai yace "sbda me," da kyar tace "amai," yace "ki gaya min inda ke maki ciwo fateema," tayi shiru bata ce komai ba, ya kwantar da ita ya mike ya bude kwanon da ya gani kusa da gadon, shinkafa ce da miya, ya shiga xuba mata snn ya dawo kan gadon rike da abincin xae bata, da sauri ta kauda kanta ta fada kan gado cikin kuka tace "amai xanyi ka ajiyesa," ya mayar ya ajiye da sauri snn ya dago ta yace "to me xaki ci," ta girgixa masa kai, ya rungumeta yana shafa gashinta, mikewa yyi ya shiga bathroom ya dibo ruwa a roba, snn ya fito yana tambayrta ko xae samu dan tawul, tayi shiru bata ce komai ba sae da ya dawo gabanta a hankali ya kara mata tambayar snn ta nuna masa, ya mike ya dauko ya saka cikin ruwan, ya cire mata rigar jikinta da xani snn ya shiga matse tawul din yana goge mata jiki da shi, karfe goma yace xae tafi bayan ya lallabata ta sha tea kadan, har lkcn tana rungume jikinsa, ta gyada masa kai kawae, snn yace "gobe da safe xan xo da magunguna da injectns dinki kinji kanwata," kai kawae ta gyada masa, ya daura mata kiss a bakinta, ta lumshe ido da sauri, yyi mata sae da safe, ta bi shi da kallo har ya fita, ya fita da minti biyar momy ta shigo, xani ne kawae jikinta, kunya ya kamata ta rufe ido da sauri kmr me bacci. Kullum sae Aliyu ya xo sashinsu da safe da dare, ya kan siya masu fruit ko nama, duk da ko kadan momy bata sake masa, sae dae yyi ta xamansa a falo idan ta fita sae ya shiga dakin, laulayin inteesar ya dawo sabo kullum cikin wahala da amai take yana mugun tausayinta har mmki abun yake bata, duk da tasan duk sbda cikinsa ne, wani lkcin idan ya shigo gidan sae karfe sha daya yake wucewa duk da bbu wanda yasan yana xuwa har inna, idan kuwa tayi bacci me ddi to a jikinsa ne, don yana xuwa ya rungumeta bacci yake xuwa mata, wani lkcn ma sae dae ya kwantar da ita kawae yyi ma momy sallama ya wuce, duk dare Abba ma na shigowa dubata hka Haisam, inna kam bata san ashe jarababbun yara na makale jikin inteesar ba, su kansu Hajiya basu sani ba. Yau ta cika sati biyu gun mamanta, momy na kula da ita ssae kuma tana tausayinta ganin yanda cikin ke bata wahala, karfe hudu na yamma Aliyu ya shigo gidan ranar yaci sa'a bbu kowa tsakar gida ya nufi sashinsu inteesar, xaune ya tarda ta da momy a falo ta sata gaba sae ta shanye kunun da ta dama mata don bata cin komai, ya gaida momy tayi kmr bata ji sa ba ta fice daga falon, ya dawo gefen inteesar ya shiga lallabata yana bata kunun har ta sha rabi, snn ya ajiye ya rungumota jikinsa yana buga mata baya kar tayi amai, tayi lamo tana sauke ajiyar xuciya, a hankali yace "fateema," ta dago tana kallonsa ya mayar da kanta kirjinsa yace "gida nake son tafiya dake fateema, nasan sae da amincewarki Abba xae yarda na daukeki, ki tausayamin plss my wife" . Inteesar ta kwace kanta daga rungumar da yyi mata tana masa mugun kallo tace "waye wife din taka? Sae yau da kaga ciki a jikina kasan ni wife dinka ce, to ni ba matarka bace wllh, bari ma kaji abinda baka sani ba ya Aliyu, wllh bana sonka bana sonka, tun ynxu nake son mu ajiye yarjejeniya da kai a kan cikin nn," yyi shiru yana kallonta xuciyarsa na tafarfasa, tunanin me yake hka har ya kai sa ga kiranta da wife dinsa, ya rike temper dinsa yana kallonta bbu yabo bbu fallasa yace "yarjejeniyar me," tana masa wani irin kallo tace "na farko ina haifa abinda ke cikina xaka bani takardata, na biyu kuma ni baxan shayar da danka ba tun ynxu ka sani, idan ka yrda da deal din nn, to na yrda xan bar cikin nn, idan kuma akasin hka, to wllh wlh xan sake komawa a cire min cikin kuma baxa ku sake gani na ba," ya sauke ajiyar xuciya yana kallonta, ransa yyi mugun baci, amma da yake yaransa kawae yake so, sae yace "ok na yrda xan baki takardarki kuma baxa ki shayar da su ba," tace "ka rantse da mahaliccinka," yyi shiru yana kallonta snn yyi wani irin murmushi yace "na rantse," tace "kuma ni daga ynxu ka daina xuwa gurina na yafe maka," yace "ok ngdd," snn ya mike ya fice ba tare da yyi mata sallama ba ma, ta mike ta koma daki da kyar ta kwanta kan gado ta lumshe idonta dake cike da hawaye, yes hkn kadae ne mafita a gareta, Aliyu bae cancanci ta xauna da shi ba ko kadan, idan yana shisshige mata hka xata iya canxa ra'ayinta. Tun daga ranar Aliyu bae sake xuwa sashinsu ba duk da tasan yana xuwa gidan, yau kusan sati knn tayi forcin din kanta xuciyarta taji hkn da yyi yafi burgeta yafi mata ddi amma ta kasa, baccin kirki gagaranta yake duk da ynxu laulayin nata da sauki cikinta ma ya dan fara fitowa, in kaga yanda inna ke ji da ita da cikin sae ka rantse kace ba ita ke jinjina mata xubar da cikin da tayi kwanaki ba, tunda ta gane ciki na nn maimakon a ga inna ta bata rae ko makamancin hka sae aka ga ta buge da murna har da rawanta, kullum ita ke ma inteesar girki safe da yamma wae don yaran suyi karfi, su Hajiya ma ba karamin girgixa suka yi ba da kursum ta gaya masu ae ciki na nn kuma har ya fara fitowa, umma tace "tab, wllh ki san abun yi tun wuri Hajiya," Hajiya da abun duniya ya isheta tace "to umma ya xanyi ni wllh duk jikina ma ya mutu, taya xa'ayi Aliyu ya hada xuriya da marasu asali kuma mugaye, umma ta tabe baki tace "ki shigo anjima da daddare ina da shawara da xan baki," Hajiya taji ddi ssae tace "to umma naji ddi amma, xan shigo anjiman" Yau lahadi inteesar na xaune tsakar gida da inna da yamma wajajen karfe biyar suna ta hira tana cin gyada kursum na kwance kan tabarma a gefensu tana danna wayarta, ynxu kam bbu laulayi sae shegen kwadayi kmr xata ci bbu, sae nauyi da jikinta yyi mata don cikinta ya fito ssae watan shi na biyar knn, duk da tana tattare da damuwar da bata san dalilinsa ba sae kyau take karawa abunta kmr ba ita ba ga wani haske da ta kara a kan nata, cikin ya amsheta ssae yyi mata das das a jiki gwanin sha'awa, ta mike knn xata dauko ma inna tsintsiya ta tattare bawon gyadan da suka ci don kursum tace baxata tashi ba tunda bata ci gyada ba, suka ji an bude gate, gaba daya suka maida hankalinsu ga gate din, Aliyu ne ya shigo gidan safeena na biye da shi a baya, kallo daya tayi masa ta dauke kanta tayi gun inna rike da tsintsiyar a hannunta, ya kasa dauke idonsa daga kanta sae binta da kallo yake, ya sauke idonsa kan cikinta ya sauke ajiyar xuciya, muryar inna ne ya dawo dashi cikin tsawa tace "su waye wa innan xasu fado mana gida kmr tsofaffin arna ba sallama," safeena da ta kasa daina kallon Inteesar ita ma xuciyarta na harbawa ta maida kallonta gun inna tana mata wani shegen kallon rainin wayo, Aliyu ya harari inna yace "ke dae kin banu wllh, ae randa xaki mutu a gidan nn sae na xuba ruwa a kasa nasha," a fusace inna tace "karyanka yaro kuma sae ka riga ni mutuwa," inteesar ta juya da sauri tana kallon inna tace "kai inna," inna ta mike tana gyara daurin xani tana huci tace "ku fita ku ban waje, kar na walakanta ku ynxun nn," Aliyu yyi dariya yace "to mai gidan," safeena ta tabe baki tayi bangaren Hajiya inna ta sha gabanta tana huci tace "ina kike tunanin xaki mahaukaciya," inteesar ta mike da kyar tayi sashinsu Aliyu ya bi ta da kallo har ta bace masa, snn ya maida dubansa ga inna dake fada safeena na fada, bbu tonan sililin da inna bata yi mata ba, yace "ke safeena," ta juya ranta a bace tana kallon Aliyu tace "ka ja ma tsohuwar nn kunne ta fita harkata don ni nafi karfinta wllh," ya daka mata tsawa yace "tunda tace ki fita ba sae ki fita ba, sa'ar kakarki ce aka ce maki wnn" safeena ta shiga hawaye tana kallonsa, yyi tsaki ya karasa gun inna yace "kiyi hakuri inna, bata cika hankali bane yarinyar," inna tana wage baki tace "ae naga alama maxa ta fitar min daga gidan dana, sannu da xuwa Aliyu ina ta cigiyarka" yyi murmushi yace "ae gani innata," tana dariya ta ja sa suka yi sashinta, shi ko sae murmushi yake don yana da dalilin yin abinda yyi Safeena ta juya tana kukan takaici ta bar gidan, da sauri Hajiya da umma dake leke ta taga suna kallon duk abinda ke faruwa suka fito, Hajiya tabi bayanta tana kiranta cikin lallashi tace "kiyi Hkuri safeena ki kyaleni da shi, wancan kuma me ya kai ki musanyar yawu da ita baki san mayya bace," Safeena tace "ae kam naga alama Hajiya, amma ni dae wllh nafi karfinta" ta karashe maganan tana kuka, Hajiya ta ja suka yi sashinta umma na biye dasu a baya suna lallashinta, kursum ta tabe baki ta mike tace "lallai wnn jaka ce mara xuciya," fura inna ta shiga dama ma Aliyu yana kwance kan dogon kujera suna hira, yace "ae idan yarinyar nn ta haihu ke xaki je mata xaman jego," da sauri inna na wage baki tace "haba," yace "eh mana," tace "wayyo amma naji ddi wllh, Allah yyi maka albarka," ya dan tabe baki yace "Ameen, to ma taya xaki je xaman jegon tana nn," inna tace "yo ba sae ta koma ba," ya danyi murmushi yace "to kiyi mata magana, don tafi jin maganarki kan na kowa a gidan nn" inna tace "to bari na aika a kira min ita na gaya mata ynxun nn ma, yo ae wnn ba wani abu bne," dae dae nn khadija ta shigo, ta gaida yayanta snn tace "inna an aiko ni wajen ki," inna tace "waye," khadija tace "wae mamata tace naxo na amshi dari biyar din da kika ara hannunta kwanaki," inna ta bude baki tace "lah ku ji min mata, ki je kice mata taxo ta danne ni ta kwata, naga dae gun dana take samun kudin kajin min fitsararriyarkawae," khadija ta juya xata fita Aliyu ya kirata ya ciro dubu daya ya mika mata yace "gashi ki kai mata," inna tace "ae da ka kyaleni da ita Aliyu, ita don bata da kunya don na amshi wani shegen dari biyar a hannunta kusan shekara daya knn sae ta aiko a karba, maxa kice kuma ta baki canjin dari biyar ki mayar min," khadija har ta fita inna ta kwalo mata kira ta dawo fuskarta a daure tace "wae meye ne inna," inna tace "kije ki kira min inteesar ynxun nn," ta fice daga falon Aliyu ya daka mata tsawa baki ji me tace maki bne "ta leko tace naji ae," snn ta wuce, bayan kmr minti goma inteesar ta shigo falon tana rike da kugunta daga bakin kofa tana kallon inna tace "gani inna," Aliyu dake xaune yana shan fura ya juya yana kallonta, inna tace "to bakin kofar xan xo in same ki," inteesar ta shigo ta xauna gefenta da kyar, sae bin ta da kallo Aliyu yake, tace "me xan maki inna bacci fa nake, inna tace "kai haba, to shiga ki kwanta in kin tashi ma yi maganan," inteesar ta mike xata shiga daki, inna tace "lah baki ga Aliyu bne, naga baki gaidashi ba," inteesar ta juya tana kallon inda yake, har lkcn kallonta yake, yyi murmushi ya ci gaba da shan furarsa yace "ni na isa ta gaishe ni," inteesar ta dan yi tsaki ta shige daki abinta, inna tace "to Allah shi kyauta," hira Aliyu ya kwanta gefen inna yana mata tana biye masa muryarta har waje, sae ka rantse kace ba Aliyu bne, duk inteesar na kwance a daki tana jinsu, rabon da Aliyu ya tsaya suyi hirar arxiki da inna har an manta, yace "ni fa inna yunwa nake ji kin wani hada ni da fura," tace "lah me xaka ci toh," yace "jollof rice nake so da farfesu," da sauri tace "to bari in je in maka," ta mike tsaye tana gyara dankwalin kanta tace "yo nayi ma wasu bnxa ma bare kai," ta fice tana kwala ma kursum kira taxo ta hura mata gawayi, don bata gane gas acewarta bata lkci ne. Aliyu ya juya yana kallon kofar dakin kmr ya shiga ya fasa, yana ta danne dannen wayarsa amma lkci lkci yakan juya ya kalli kofar dakin, inteesar taji shirin yyi yawa, wata xuciyarta tace ta leka taga ko yana falon, a hankali cikin sanda ta isa bakin kofa ta dan bude labulen a hankali tana lekensa, shima ya juya knn yana kallon kofar dakin xuciyarsa na son ya shiga, suka hada ido, ta sake labulen da sauri yyi murmushi bae dae ce komai ba, ganin xuciyarsa ta kasa hakura da shiga dakin kuma baya so ya shiga yasa ya mike da sauri ya fice daga falon yyi sashinsa. Ko da inna ta shigo falon tana kiran inteesar ta fito ta ci abinci da xafinsa, da sauri ta fito kmr jira take, taga inna kadae ne xaune falon, tace "wae ni kika ma girki," inna tace "aa Aliyu nayi ma," inteesar tace "to ina yake," inna tace "ae ni da kaina na kai masa yana kwance a dakinsa yaron kirki." inteesar bata ce komai ba ta dauki furan da ya rage ya rufe ta shiga sha, inna tace "ke dae kin banu da kwadayi, naki ne," ko kallonta inteesar bata yi ba ta shanye ta ajye kofin, snn ta fara cin abincinta, ta gama cin abinci knn, khadija ta shigo dakin tace "wae ina furan ya Aliyu" inna tace ahaf gata nn ta shanye khadija tayi tsaki ta juya ta fice. Karfe tara inteesar tayi ma inna sae da safe tayi sashinsu, har ta wuce bangarensu Aliyu ta dawo tana lekan ko yana nn ko ya tafi, ita dae bata ga alaman ya tafi ba kuma bata ga alaman yana nn ba, ta karasa bakin kofar a hankali da yake basu kunna bulb din wajen ba ta durkusa tana lalube ko xata ga takalminsa, dae dae nn aka bude kofar Haisam ya fito, daga ita har shi sae da suka tsorata. Ashe Aliyun ma na kallonta daga bayanta ya fito daga bangaren Hajiyarsa knn. . Haisam yace "me kike yi a nn Inteesar," ta ji kmr ta nutse wajen don kunya ta fara kame kame, Haisam yyi dariya yace "to ae baya ciki ya fita sae dae in xaki shiga ki jirasa," kmr xata yi kuka tace "wayyo ni ya Haisam abu na ne ya fadi nke nema," bata jira me xae ce ba ta juya da sauri xuciyarta a dagule xata bar wajen ta kusan cin karo da Aliyu dake tsaye har lkcn yana kallonta, gabanta yyi mugun faduwa, tabi gefensa da sauri xata wuce ya rikota, Haisam dae yyi gaba abinsa yana dariya, ta buge masa hannu ta daure fuska tace "meye hka malam," dariyarsa mai kyau yyi snn yace "me kike bukata daga gare ni da kika biyo ni," ta fashe da kukan takaici tace "waye ya biyo ka, Allah ya isa na, da'alla ka sake ni na wuce don naxo neman abu na shine na biyo ka," dariya ya dinga yi har da buga bango yace "ae nine abun naki, ni kika xo nema 4 sure na sani," ta fixge hannunta xata bar wajen yyi saurin rikota ya bude kofar falon ya ja ta suka shiga, kuka ssae take yi kuma na takaici, ka kyaleni ya Aliyu bana son hka, yyi murmushi ya rufe kofar falon da key ya karaso bayanta ya tsaya a hankali yace "am srry fateema, i also feel...." sae kuma yyi shiru ta juya tace "ka bude min kofa in fita nace maka," bae ce mata komai ba ya dauketa sae bedroom yace "ki bari in gaisa da yarana," kuka ta dinga yi tana jin haushin kanta ita kam har ga Allah ganinta kawae tayi a bakin kofar bata san ya aka yi ba, ya rufe kofar dakin ya xaunar da ita kan gado yana kallonta ya durkusa gabanta yace "its High tym mun fahimci juna fateema," cikin tsawa tace "wace fahimta kuma, ka bude min kofa in fice daga dakin nn" yyi murmushi ya kauda kansa yace "ok," snn ya mike ya bude mata kofar dakin da sauri ta fita, ya bi ta baya ya bude mata na falo ma ta fice, snn ya mayar da kofarsa ya rufe. Ko barin wajen bae yi ba ta fara buga kofar da sauri, ya bude yana kallonta ta shigo falon da sauri tace "momy xata gan ni" yace "a ina," tace "wucewa take," bae ce komai ba ya xauna kan kujera, ita ko tana tsaye bakin kofar sae leke leke take, ta kai minti kusan goma a hka snn yace "to ki xauna mana," ta juya ta galla masa harara tace "ina ruwanka da tsayuwata," yyi murmushi ya dauke kansa bae sake cewa komai ba har ta gama tsayuwarta ta bude kofar ta fice, ya sauke ajiyar xuciya, shi kam baxae iya tsayawa rokan karamar yarinyar nn ta koma gidansa ba ta ci gaba da raina sa ba, duk da abun yana damunsa but ya gwammace yyi ta damunsa din. Kullum sae Aliyu ya xo gida da

Chapter 26 of 32