Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kudinsu suke a banxa a kansa, amma abu sae kara gaba yake, tayi kwafa ta haura sama, yana shiga motarsa ya kama hanyar asibiti, bae damu da gaisuwan da nurses ke masa ba har ma da patients ya haura sama kawae ya wuce office dinsa, ya bude glass din da magunguna suke ya shiga xaban wanda ya kawosa, tabs kala biyu ya dauka da ruwan allura daya ya rufe glass din ya fito ya rufe office din, ya sauko kasa xuwa reception, sae a snn ya shiga amsa gaisuwan patients din da ke gaishesa, yyi murmushi ganin matar da yyi ma theatre kwanakin baya da yaranta da babansu, ya karasa kusa dasu yana kallonsu yace "madam me ya sami twins" matartace "wllh tari suke doctor, ya aiki?," ya karbi dayan yana masa wasa yace "aiki Alhmdllh anyi attend din maku ne," tace "A'a ynxu dae xa a duba mu, madam fa," yyi murmushi yace "tana lfya," tace "to a gaida min ita, yau kana wkend ko," yace "wllh kuwa, Allah ya sauwake, i wil b on my way," ya ba mijinta hannu suka yi sllma snn ya juya, yana isa kofar fita sai da ya juya ya sake kallon kyawawan yan biyun da suka girma ssae, ya dauke kansa da sauri ya fice ya shiga motarsa ya bar asibitin. . Aliyu na shiga gida ya tarda Safeena kwance a falo tana kallo, ta bisa da kallo har ya haura sama snn ta mike xaune tana bubbuga kafa a hankali ta shiga maganar xuci "lallai its high tym she wake up frm her slumber, ya kamata ta tashi tsaye daga xaunen da take ynxu, Aliyu ya gama kawota bango, xata cire sonsa ta ajiye gefe guda tayi abinda uwarta ta dde tana son tayi taki yi sbda so ya rufe mata ido, ita kuma inteesar ynxu suka sa kafar wando da ya da ita" tayi murmushin mugunta ta mike ta haura sama xuciyarta na tafarfasa. Aliyu na shiga dakin ya tarda ta tana bacci ya xauna gefenta yana kallonta ya ciro magunguna da alluran da ya dauko a asibiti yana kallonsu, snn ya juya yana kallonta tayi wani irin haske ta kuma kara kyau, yyi murmushi ya shafi gefen fuskarta ya mike ya dauko syringe a dakinsa ya dawo ya shiga hada alluran, sunansa yaji ta kira, ya juya da sauri yana kallonta ta sake maimaitawa "ya Aliyu," sae kuma yaga tayi murmushi ta juya, ya ajiye alluran hannunsa ya dawo dab da ita ya xauna yana shafa labbanta da yatsa yace "fateema," cikin baccin ta amsa "na'am," yyi murmushi ya daura mata kiss a bakinta, murmushin yaga ita ma tayi, yyi still yana kallonta, to wae meyasa yake son xubar da cikin nn, shi dae yana son yara kuma xae so yaga kyakkyawan bbyn da xata haifa masa mai kama da ita, ya dauke kansa ya daura hannu a goshinsa kan na juya masa, y? Meyasa yake son xubar da bbynsa gudan jininsa, ya girgixa kai yace "No," da sauri yaga ta mike xaune ya kamo ta ta fara turasa xata sauka yaki sakinta yana tambayarta mene, amai ta shiga kwarara masa a jiki yana rike da ita har lkcn, sae da ta gama snn ya dauketa ya shiga da ita bayi, sae kuka take tana cewa ita ya kaita gida, wanka yyi mata ya nannadeta cikin towel ya fito da ita ya cire xanin gadon snn ya kwantar da ita, shima wankan yyi don duk ta bata masa jiki ya saka xanin gadon cikin washn machine da shirt din jikinsa snn ya fito daure da towel, ranar ce rana ta farko da ta taba ganinsa daure da towel don ko singlet Aliyu bae yrda ta gansa da shi bare short nicker, ta rufe idonta da sauri, shima bae ce mata komai ba ya kwashi magunguna da alluran da ya hada ya fita da su, dai dai lkcn da Safeena ta fito daga dakinta, ta bi sa da kallon mmki shi kam ko kallonta bae yi ba shiga dakinsa. Alluran da yyi mata bayan ya tilasta ta sha tea ne ya tsayar mata da aman, amma duk da hka sae da ta gwammace dama aman ta dinga yi taji ddi, don rasa inda xata sa ranta tayi sae kuka take tana juye juye, ya rungumota cike da tausayinta yana lallabata tayi bacci, da kyar ta samu baccin ya dauketa, yyi shiru yana kallonta duk ta rame lkci daya, da yamma wajajen karfe biyar ya fita pharmacy siyo mata magunguna da drips din da xae sa mata.Yana fita ko minti goma ba ayi ba Zainab ta shigo gidan ko kallon safeena dake ta busar da gashinta da hand dryer bata yi ba ta wuce sama, safeena ta bi ta da kallo snn ta ja dogon tsaki, bacci ta tarar Inteesar ke yi ta shiga tashinta da xolaya tana cewa "ke kasa kinyi bakuwa maxa tashi" inteesar ta shiga juye juye ta mike xaune da kyar tana kallon Zainab, Zainab tace "hmm lbri na xo maki da mai ban kunya," inteesar xata yi magana taji yawu cike bakinta, ta mike tsaye da kyar ta shiga bayi ta xubar da yawun ta dauraye bakinta da freshner ta dawo, Zainab tace "meye hka," Inteesar ta langwabe da kyar tace "bana jin ddi ne," Zainab ta bude baki "iyye kar dae bby xa a samo mana," inteesar tayi shiru da mamaki tana kallonta snn tace "bby kuma, wani bby," Zainab tayi dariya tace "lalala kinga yanda kka yi wani irin haske da kyau kuwa, shknn xa a sama ma yayana bby," inteesar ta hade rae xata yi magana taji yawu kuma a bakinta ta mike da sauri taje ta tofar wnn wani irin jaraba ce, ta tambayi kanta, kuka ta fashe ma Zainab ganin Zainab ta kuke sae murna take xa su samu bby, tace "ni fa bana son hka Zainab wllh bani da komai," Zainab tace "ki daina wllh, ga signs a jikinki," kuka ssae take tana cewa na shiga uku ni Zainab ki bari bani da komai yarinya da ni xaki ce ina da ciki, Zainab tayi dariya ssae tace "tunda ko kina kwana daki daya da yayana ai ke ba yarinya bace," dai dai nn Aliyu ya shigo yana ma Zainab mugun kallo yace "ke wae wace irin mutum ce, ban hanaki shigowa gidana ba, xo ki fita," cikin daga murya ya karasa maganar ta mike da sauri tana xumburo baki ta dauki mayafinta ta bi ta gefensa ta fice ya kai mata rankwashi, inteesar ta hade kanta da gwiwa tana kuka, ynxu ciki ne da ita yar yarinya da ita, to da wani ido ma xata kalli su inna, ae Allah ma ya kyauta kuma ya rabata da haihuwa ynxu kuma ma wae dan Aliyu. Ta mike da sauri tun kan ya shigo dakin xata yi hanyar bathroom jiri ya debeta ya shigo dakin da sauri ya kamota ta fada kansa suka xube kan gado, ya fada gefenta da sauri ganin ynda take mayar da numfashi ya dagota ya rungumeta yana mata sannu, cikin kuka tace "wllh ka cire min cikin nn bana so," ya toshe bakinta da sauri yana kallon cikin idonta yace "ni ina son abu na . Kuka ssae Inteesar ta shiga rera masa, shi kam saekallonta yake yana murmushi, ta fara kkrin mikewa xata sauka daga kan gadon ya riketa da sauri yace "ina xaki," cikin kuka tace "wllh sae ka cire min cikin nn bana so," ya rufe bakinta ya hade rae yace "kar ki sake cewa na cire maki bbyna, sae kace wani kaya," ta buge masa hannu, ya harde kafarsa cikin nata tayi yar kara, ya rungumota yana kallonta ya shiga shafa mata cikinta yace "me xaki ci, dubi fa yanda kika rame tun kan ba mu je ko ina ba, a hka xa muyi rainon cikin kika san ma ko yan biyu ne kanwata," ta fashe masa da kuka tana kiran Abbanta, ya rankwashi kanta yace "ki daina min kmr ihsaan a nn, ke baki san kin girma ba tunda ga bby nn cikin cikin ki" bata san lkcn da ita ma ta rama rankwashin ba tana kukan da xa a iya kiransa da na shagwaba duk da har ga Allah ba shagwaba take ba, ya wara ido yana kallonta, ta koma baya da sauri nn da nn ta tsorata ya lakaci hancinta ya ja kunnenta yace "kin ci sa a bbyna na jikinki da yau na maki shegen bugu, ya Aliyu kike rankwashi " bae jira me xata ce ba ya kwantar da itaya mike ya fita, ta mike xaune da sauri ta hade kanta da gwiwa ta fashe da wani sabon kukan ynxu wae ciki ne da ita da gske yar yarinya da ita, ba a dau lkci ba ya dawo dakin rike da kofin tea yace "maxa tashi ki sha na saka maki ruwa aman ya tsaya," kallon tean kawae tayi taji xuciyarta na tashi ya kai mata baki ta mike da sauri sae cikin bayi ta shiga kwarara amae, ya isa kusa da ita ya durkusa ya dafata yana kallonta yana mata sannu, sae da ta gama snn ya gyara mata jiki ya maidota cikin dakin, a hankali ta kamo hannunsa tana hawaye tace "don Allah ya Aliyu ka tausayamin ka cire min cikin nn bana so," ya galla mata harara yace "wllh idan kika sake gaya min wnn maganar sae na bata maki rae, ki cire ynxu na gani mana," tayi shiru tana kallonsa xuciyarta na tafarfasa, ita ko ta fi sa iskanci xae gani kuwa, ta juya tayi kwanciyarta tana mayar da numfashi, tean da bata sha ba knn har bacci ya dauke, sae kusan sha daya na dare ta farka yana gefenta a kwance, shima amai ne ya farkar da ita, ya cire mata ruwan dake hannunta ganin a gigice ta farka tana neman sauka ya raka har bayin ta shiga kwarara amae, gashi dae ba komai cikinta, ya xuba mata ruwa a kai ya fito da ita, daga ita har shi ranan basu yi baccin kirki ba, jikinta yyi xafi ssae ta rasa inda xata sa ranta sae kuka take masa yana rungume da ita, da kyar bacci mai nauyi ya dauketa kusan asuba. Washegari monday bae je aiki ba sbda ita, tana kwance jikinsa bayan ya lallabata ta sha tea kadan yyi mata allurorinta wajen karfe goma safeena ta kwankwasa kofar tare da sallama, yace ta shigo, ta bude kofar ta shigo sae da xuciyarta ya kusan harbawa yanayin da ta gansu, shi singlet da 3qtre ne jikinsa, ita kuma rigan bacci iya cinya, ta kirkiro murmushi ganin allurori a bedside drawer tace "Ayya bata jin ddi ne dear," ba tare da ya kalleta ba yace "eh, ya akayi?" tace "Allah sarki, Allah ya sauwake fateema sannu," inteesar ta dago kai da kyar ta watsa mata harara, ta mayar da kanta, safeena ta dauke kanta da saurixuciyarta na tafarfasa tace "yauwa dear Momy ce ciwonta ya tashi shine xanje ynxu, amma ba ddewa xanyi ba dan da sauki," yace "ita kuma kullum ciwon nata ke tashi, baku da abinci ne a gida, ae yunwa ce ke kawo ulcer " tayi shiru tana kallonsa ya tabe baki yace "Allah ya sauwake, ki duba side drawer can bedroom dina ki dauki dubu goma," tana murmushi tace "to ngd dear," snn ta juya ta fice tana murmushin mugunta. Da yamma safeena ta shigo gidan, har lkcn Aliyu na dakin Inteesar, lkci lkci yakan yi tunanin ko dae kawae ya rabata da cikin nn ne ta huta shima ya huta, don ba karamin wahala yaga take sha ba tun kan cikin ya kai ko ina, ynxu ma da kyar ta samu bacci ya dauke, irin masu shegen laulayin nn ne me wahala, ya dan yi tsaki, ita ma ragwancinta ne kawae yyi yawa, duk ta fige lkci daya sai kace wacce tayi wata tana ciwo, safeena ce ta bude dakin ta shigo ya daga kai yana kallonta, tayi murmushi tare da lumshe ido tace "Aliyu so nake kaje duba mum dita ynxu, kuma ka tafi mata da wnn maganin nn da ka bata ranan nn wae taji ddinsa," yyi shiru yana kallonta,snn taga ya sauke ajiyar xuciya yace "wae ynxu?" ta dan yi fari da ido murna fal cikinta, amma ta hade rae tace "to da yaushe kke tunani," yace "ok," snn ya kwantar da Inteesar dake jikinsa ya mike tsaye ya juya yana kallonta bacci take, kan yace komai safeena tayi saurin cewa "to kaxo ka wuce," ya juya ya fice daga dakin, ta bisa da kallo tana murmushi, dakinsa ya shiga ya shirya snn ya fito da makullin mota, tana hararansa tace "to haka xaka je mata hannu rabbana," ya koma ciki sae gashi ya fito da kudade, ta rakasa har jikin mota snn ta manna masa kiss a baki, yyi murmushi ya lumshe idonsa yace "sae na dawo bbyna," snn ya ja motar ya fice daga gidan, ta doka uban tsalle tashiga kiran layin uwarta cikin murna tace "wayyoo mum, saura naki gashi nn xuwa. Aliyu na fita gidan ya wuce wani babban super market ya yayiwa mum din safeena siyayya bata wasa ba akalla ya kashe kusan 50k. Ya fito ya shiga motarsa ya dau hanyar gidan mum xuciarsa duk a cushe ya rasa dalili,gashi yana son kiran inteesar a waya ta wayar sa dake hannunsa amma ya kasa a haka dai ya cigaba da driving har Allah ya kai shi lpy. Yana isa gidan su safeenar maigadi ya bude masa get yana washe baki kasancewar aliyu na hannun damansa ne yana da yawan kyau,ko kula da gaisuwar da me gadi yake yi masa bai yi ba ya mika masa 2k aiko maigadi ya hau godia da kiraki hannu kawai ya daga masa yai hanyar parkin shade dinsu ya ajiye motarsa ya duba seat din baya cikin magungunan daya ajiyewa a a first aid box dinsa ya dauki na ulcer ya jefa a cikin ledar magunguna da safeena ta bashi. Sallama yayi cikin nutsuwa ya shiga falon dai dai lokacin mum ta fito aiko ganin aliyu yasa ta dan yatsina fuska shiko jiki na bari kamar yayi gamo ya sauko dg kan kujera yana kwasar gaisuwa,fuska ba yabo ba fallasa suka gaisa yai mata ya jiki sannan ya mika mata ledojin hannunsa ya mike xai mata sallama kenan tace "aliyu baxaka tsaya ko ruwa kasha ba?" Sai ya tsinci kansa ya kasa yi mata musu alhalin bai taba cin komai na gidan ba. Komawa yai ya xauna xuciarsa na cikin dumuwa yana buqatar ya duba inteesar kuma ya san by nw ta tashi dg baccin da ya barta tanayi. Tunanin haka yasa ya ajiyar xucia tare da fesar da iska mai xafi hade da lashe labbansa da suka bushe. Mum ce ta shigo riqe da jug a akan tray da cup da roban ruwan c'est bon,ta tsiyaya masa xobon ta mika masa ya kai hannu biyu tare da yin godia.... zai kai bakin shi kenan wayarsa tai ringing hakan ya dakatar dashi da sauri ya ajiye xobon ya karkace ya xaro wayar dg aljihun jeans dinsa duk a tunaninsa ko inteesar ce ta kira shi... Sae da Aliyu ya fara xuwa asibiti ya dauki maganin da xai kai ma mamar safeena snn ya ja motarsa ya kama hanyar gidan jikinsa a mace, ya na isa yyi parkin a waje, ya fito da maganin yana kare ma gidan kallo snn ya shiga, suka gaisa da mai gadin ya karasa balcony ya danna bell, yar aiki ta bude masa kmr jira take ya shiga falon ta nuna masa kujeran da xae xauna da sauri shima kmr wnda ake contrl ya xauna inda ta nuna masa yana bin ko ina na falon da kallo, yar aikin tayi sama kiran Hajiya, yana kallo Hajiyar ta shigo falon ya dan dukar da kansa ya gaisheta ta amsa da fara'a kmr gske snn yyi mata ya jiki, ya bata maganin da ya kawo mata, ta amsa tana gdya tana jujjuya maganin, ya ciro kudin da ya dauko daxu ya mika mata yace "ni xan koma Hajiya" ta karba da sauri tana gdya ta mike tace to bari na kawo maka ruwa kasha mana, yace "A'a Alhmdlh ae daga gida nke," tace "to bari na baka sako ka kaima safeena," yace "to," ta mike ta yi sama, sae ga ta ta sauko da dan wani parcel, ya karba yyi mata sallama, ta rakosa har bakin kofa tana sa masa albarka snn ta koma murna fal cikinta, yana barin anguwar yaji hka kawae yana son ganin abinda ke cikin parcel din, parkin yyi gefen titi snn ya shiga budewa, wani ruwa ne ya xuba jikinsa ya matsar da parcel din daga jikinsa da sauri amma duk da hka sae da ruwan ya taba kayansa da farko wari yaji, ya yatsine fuska kawae kuma sae yaji wni mugun kamshi me ddi ya xiyarci hancinsa, ya rufe da sauri ya ajiye parcel din ya ci gaba da drivin dinsa. Safeena ta kasa xaune ta kasa tsaye sae kaiwa take tana komowa a falo, wayar uwarta ya shigo nata ta daga da sauri jikinta na rawa tace "ya xauna kan kujerar mumy, kuma ya karbi ledan," uwar ta kyalkyale da dariya tace "wllh kuwa dota, ynxu fatanmu kawae Allah yasa ya bude," safeena ta doka tsalle tace " Alhmdllh amma naji ddi momy, budewa kuma ba matsala bace ko a gida xan sa ya bude bare ina da yakinin ma ya bude naji sighn din da mutumin yace xan ji a jiki na," budewar gate din da safeena taji yasa tace "wayyoo momyna ya dawo xamu yi waya anjima," ta katse kiran tana murmushin mugunta, shknn ynxu sae yanda tayi da Aliyu," yana shigowa gidan ta karasa cikin kissa ta rungumesa ya dagata sama ya manna mata kiss a goshi yace "bbyna sae kyau kike karawa kullum," ta hararesa tace "sae yau ka sani," yace "A'a bbyna ina sane," kinsan me bbyna na dan maki barna wllh momy ta ban turare na kawo maki da karambani na na bude ya xuba jikina," ta kankamesa ta rasa inda xata sa kanta don murna, tace "da gske bbyna, wllh sae ka biya ni," yyi hanyar stairs da ita yana cewa "naji xan biya bby nawa ne," inteesar kam na xaune ta jinginar da kanta jikin gado, ji take kmr ba ita ba duk ta rasa inda xata sa ranta taji ddi, ga alluran hana aman da yyi mata duk ya bi ya dameta, tana neman yin aman ma ko xata samu sauki amma ta kasa, yunwa take ji ssae amma bbu abinda ke ranta, ko wani abinci ta tuna sae taji amai na taso mata jikinta yyi mugun xafi ga kishin ruwa da take ji kuma tana tsoron shan ruwa, ta sauko kasa da kyar ta kwanta kan tiles din dakin ko xata ji ddin ranta, kasa daure kishin tayi ta mike xaune tana mayar da numfashi ta rarrafa ta bude fridge dinta taga ba ruwa ciki sae lemo, tana daddafa bango ta fita daga dakin ta sauka kasa da kyar ta bude fridge ta dauki ruwa ta sha, snn ta koma sama, dae dae kofar dakinta taji amai frm no where ta xube wajen ta shiga kwarara aman kmr ranta xae fita, suna daki shi da safeena duk ta gama rikitar da shi, ya turata da karfi ya mike tsaye ya karasa kofa ya bude ya fita safeena ta bi bayansa da sauri, durkusawa yyi gabanta yana kallonta, ta fashe masa da kuka abun tausayi ta xube jikinsa muryarta na rawa tace "don Allah ya Aliyu ka kai ni gida, ni wllh na gaji ko ina ciwo yake min wayyoo mutuwa xanyi," ya rungumeta cike da tausayi xae yi magana safeena tace "dear," ya juya da sauri yana kallonta, kallonsa kawae ta tsaya yi bata ce komai ba, ya sauke ajiyar xuciya yana kallon Inteesar yace "ke kuma mahaukaciyar wace gari ce xakiyi ma mutane amai a nn, idan kina jin amai ba sae ki shiga bathroom din ki ba, wnn ae kaxanta ce," Inteesar ta daga kanta tana kallonsa, da kyar ta shiga kkrin mikewa daga inda take wani aman ya taso mata ta shiga kwarara sa a wajen, kuka ssae ta fashe da ta jingina jikin bango tace "wayyoo Abbana," kallonta kawae ya tsaya yi ya kasa cewa komai, ta rarrafa ta shiga dakinta ta xube kan tile tana mayar da numfashi, safeena da sae kallon inteesar take da mugun mamaki lkci daya jikinta yyi sanyi ta ma rasa tunanin da xata yi, a xuciyarta tana cewa amae kuma? to me hkn ke nufi, ta sauke ajiyar xuciya tana kallon Aliyu tace "me ke damunta???? . Aliyu ya mike tsaye yana kallon safeena yace "bata jin ddi ne," bae jira me xata ce ba ya bude dakinsa ya shiga sae ga shi ya fito da mop ya gyara wajen aman, safeena ta koma daki da sauri hannunta na rawa ta shiga kiran uwarta, tana dagawa tace "momy wlh ina ga fa kmr cikine da yarinyar nn," uwar ta mike daga xaunen da take da sauri tace "mene? Ke wa ya gaya maki," a rude safeena tace "gashi nn tana ta amai," uwar tayi salati tace "bari xan kiraki," ta katse kiran. Da daddare Inteesar na kwance kan tiles ya shigo dakin ya durkusa gabanta yana kallonta yace "tashi ki sha kunu na karbo maki a gida," ta kasa dagowa ya dagota yana kallonta ya kauda kansa da sauri, ya kai mata kofin baki, ta kauda kai da sauri muryarta na rawa tace "xafi," ya girgixa mata kai yace "ba xafi," ta maido da kan jikinta na rawa ta daura hannunta kan kofin taji ba xafi ta kai bakinta yana rike da kofin ya shiga bata, da sauri ta cire bakinta tace "baxan yi amai ba? ya gyada mata kai ya ci gaba da bata, yunwa take ji ssae don hka rabi tasha ta koma tayi kwanciyarta kan tiles, yace "kin koshi ne ta gyada masa kai tace ruwa xan sha, yace "aa baxa ki sha ba," bata ce komai ba ya dago ta mayar kan gadon duk abinda suke safeena na lekensu, ta koma da sauri daki har da hawayenta ta kira uwarta tace "kai ni momy wllh na gaji, gashi can wajenta yana lallabata yana bata koko," uwar tace "yi shiru safeena, daxun nn na dawo daga wurin mutumin, ca yyi wae duk abinda xa muyi masa a kantabaxae taba tasiri ba sbda yana mugun son cikin nn dake jikinta," safeena ta dafe kirji tace "ynxu ciki ne da ita da gske ina xaune momy," uwar tace "ki tsaya ki saurareni mana," safeena na share hawaye tace "to ina ji momy," uwar tace "yauwa, to ynxu ca yyi dole sae an lalata cikin in har muna son muga aiki yyi mugun tasiri a kansa, ynxun ma ba wae bae yi tasiri bane, don xae dinga lallaba ki kuma sae abinda kika ce masa xe yi, sae dae fa hankalinsa gaba daya na gunta sbda wnn shegen cikin, kuma fa baki isa ki hanasa xuwa gunta ba amma, don hka kawae ki kwantar da hankalinki jibi ki xo mu koma kauyen yace yana jiranmu, ciki kuma kmr ya bare ne," safeena ta share hawayenta xuciyarta fal murna tace "to ngdd momyna," ta katse kiran tana murmushin mugunta. Da safe Aliyu ya bae ma safeena i.v din bikin Zainab, ta tabe baki tana hararansa tace "to ca nayi maka ban sani bane," yyi shiru yana kallonta snn yyi murmushi yace "to Allah ya baki hkuri bbyna, amma ni dae ban san me nayi maki ba kika canxa min kwana biyu," ya mike ya karasa kusa da ita ya xauna yana shafa gashinta yace "haba yan matana," ta hararesa tare da buga masa hannu tace "ni ka rabu dani," ya rungumeta yace "haba bbyna," kmr xata yi kuka tace "to ba kai bne ba baka ma damu dani da lamarina ba a gidan ba," yace "inji wa yace maki hka," kakarin Aman inteesar yaji, ya saketa da sauri ya mike tsaye ya fice daga dakin, safeena ta bi sa da kallo xuciyarta na mugun kuna, kasan dakin ya tarar da ita tana ta amai ya kamata har ta gama snn ya gyara mata jikin ya gyara dakin ya kwantar da ita kan gado, ta rikesa muryarta na rawa tace "sanyi nake ji yaya," ya lulluba mata bargo snn ya dauki I.v din da ya ajiye gaban madubinta xae fita ya juya yaga kallonsa take, ya dawo yana kallonta yyi murmushi yace "kina san wani abu ne," ta girgixa masa kai yace "kinsan bikin Zainab saura kwana goma ko," ta mike xaune da sauri tace "da gske yaya, ni ba a gaya min ba to," ya kamo hannunta yace "ae sun san baki da lfya, ki bari nxt wk sae mu tafi gidan kafin nn jikinki ya kara kwari," ta marairaice kmr xata yi kuka tace "to ba kila xuwa tayi ranan ta gaya min ba ka koreta," yace "ba ta ji ne," tace "to yaya wa xata aura" yana kallonta yace "faruuq," ta wara idonta ta fada kansa cikin jin ddi tace "don Allah da gske yaya, kai amma naji ddi wllh, ka bani nmbr ya faruuq din" yace "to anjima xan baki, xanje gida ynxu me xan ce inna ta girka maki?" tayi shiru sae kuma ta bata rae ita da ba ma son cikin take ba, yace kinyi shiru, tana hararansa tace "kace mata ina da ciki ne," ya daga hannayensa da sauri yace "A'a" yana girgixa kai, ta koma ta kwanta tace "dan wake nake so ni," yace "to, sae na dawo, kar ki sha ruwa kar amai ya takuraki," bata ce masa komai ba yayi hanyar kofa, duk wnn abinda suke safeena na labe tana jinsu, tana jin xae fito ta bar wajen da sauri ta shige dakinta tana murmushin mugunta, yana fitowa ya shiga dakin safeenar . Bayan kwana biyu safeena ta samu ta lallaba Aliyu wae xata gun wata yar uwarta, ya ko barta har da bata kudi da makullin mota dayake ta iya drivin tana ta murna a xuciyarta tana cewa lallai sae yanda tayi da Aliyu, ynxu kam ta yrda yana tafin hannunta amma dae ba duka ba, tunda bata isa ta hanasa xuwa gun Inteesar ba, amma komai ya kusan xuwa karshe, ta fada a fili tana murmushi, cikin kwanakin nn Aliyu na da aiki ssae a clinic don hka ya gwammace da ya bar Inteesar kadae a gida gwara ya dinga tafiya da ita don tana bukatar kulawa ssae, hka ko ya dinga yi kullum shi xae shiryata da safe yyi ma safeena sallama su wuce asibiti, hkn yyi mugun tada ma safeena hankali to ta ya xa'a yi ta aikata abinda suka sha wahala kafin su samu bayan baya barinta a gida., ita kam Inteesar ko kadan abinda Aliyu ke mata baya burgeta don dai dae da second daya bata son cikin jikinta, kuma tasan sbda cikin yake mata hka, wani mugun tashin hankali ke xuwa mata idan ta tuna cikin Aliyu ne jikinta, Ana saura kwana uku bikin Zainab ya kai ta gida duk da ba a son ranta ba don bata son su san tana da ciki, amma ashe duk ya gaya masu uwarsa ce kadae be gaya ma ba sae umma, inna duk ta rikice masa wae cutar jikarta kawae yake

Chapter 21 of 32