Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kujera itama sai mussadiq kusadashi sai Habeeb sai Ahmad daga qarshe kuma Aymaan kowannensu kansu aqasa suna sauraron kaka da dakyar ta iya bude bakinta tafara magana....✍? Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/10/21, 8:09 AM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *097* *WAIWAYE* "Asalin sunana Asma'u Mamman, ni marainiyace banida uwa banida uba don agidan marayu natashi na tsinci kaina a garin komasi dake qasar ghana. Acikin gidan marayu natashi kamar sauran yan uwana marayu damuke rayuwa a cikin gidan baza'a kira rayuwarmu da ingantacciyar rayuwa ba don gaskiya bama samun kulawa yadda ya kamata, abinci ma kanshi bama samun ingantacce saidai kame2 ga rashin ilimi daga na bokon har na arabi bama samu (gwara gwara na arabin tunda munsan wasu abubbuwan kamar yadda akeyin sallah da yan gajerun surori) ga rashin suturun kirki gidan marayun kasancewar anyi yawa sosai aciki yasa babu kulawa sosai gashi da dan tallafin da gomnati ke badawa duk wata aka dogara saidai idan allah ya taimakemu yajefo mana taimako daga ire iren mutane masu sadaka dasuke tunawa da yara marayu irinmu zama gidan marayunmu zama ne marar dadi don kowa burinshi allah ya rabashi da gidan ko ta hanyar adoption (daukar yara don rainonsu) kokuma aikatau don har taya wadanda xasu bar gidan murna mukeyi munaji dama mu Haka nataso nima kamar sauran yaran babu ilimin arabi ba na boko sai qwarewa a iya aikace aikace da rainon yara don yawanci marayun dasuka tasa suke komawa masu kula da qanannu qanannun cikinsu haka muka tashi cikin wata irin rayuwa marar alqibla, kullum a aiki da raino muke qarewa bamu fita daga gidan ko nan da wajen gidan, duk wanda kaga ta fita to ko ansamu masu daukarta ne ko tasamu aikin aikatau kokuma tayi aure don babu laifi akwai masu zuwa neman aurenmu agidan wani lokacin kuma marayu yan uwanmu maza ke auranmu haka natashi agidan kullum inama kaina fatan fita daga gidan watarana nima nasamu ingantacciyar rayuwa koyaya ne rayuwa awajen gidan na matuqar bani sha'awa musanmman idan ina ganin mutanen dakan shigo gidan marayun namu don daukarmu sai inji sunbani sha'awa ina kuma qara jin kwadayin son fita daga gidan inason jin yadda wajen yake saboda kwadayin son fita daga gidan yasa duk lokacin da akazo dauka har addu'a nake aza6eni nima, bandamu ba ko aikatau xanje inyi burina Kawai nafita daga gidan duk lokacin da akazo akayi dauka ba'a daukeni ba kwana nakeyi kuka bama ni kadai ba harda wasu acikinmu saboda yadda zaman gidan ya ishemu, burinmu Kawai mufita aganinmu rayuwarmu awaje saitafi tacikin gidan inganci ahaka harna girma naxama budurwa, ina shekara 20 wani mutum yazo neman aure na agidan da gudun tsiya na amince dashi batareda duba yanayin shekarunshi ba don babbane sosai don a haife ya haifeni gashi yanada mata biyu da 'ya'ya kusan goma sha ban damu da duk wannan ba alokacin na amince nan da nan aka daura aurenmu bayan anyi dan bincike dasukeyi na sanin mazaunin mutum da sana'arshi inda aka gano sana'arshi qera tukane na qasa da tulu dadai sauran kayan qerawa na qasa bayan daurin aurenmu aka damqani ahannun mijina daga ni sai yan kayana sai dan ihsani da manyan gidan suka hadamin wanda betaka kara ya karya ba nabi mijina bakina har kunne don tsabar murna muka bar gidan da tun haihuwata banta6a fitowa ba abin hawa muka hau dani da mijina har gidanshi wanda yakasance na qasa ne duk ya tsufa ya zaizaye gidan zagaye yake da yar gajeriyar katanga ta qasa inda idan kashiga ciki saika fara cinkaro da wani washeshen fili mai girma sosai inda daga nesa xaga hangi yan qanannu qanannun dakunnan dake gidan dakuna hudu ne gidan masu yan qanannun taga (window) daga can sama daki nafarko na maigidan ne sai biyu na kowanne matarshi daya kuma na yara inda na qarshen wanda da alamu saida akayimashi kwaskwarima saboda qamshin sabon shafen qasan dayakeyi nawane ni amarya babu kitchen gidan don a tsakar filin gidan suke girki sai makewayi dake daga can qarshen gidan. ahaka nashiga gidan ina kalle kalle inda yarane sosai tsakar gidan duk yan kuya kuya kusan duk kai daya kowa na,binmu da na mujiya, daga tagar dakunnan matan gidan kuma ina iya hango kawunnan mutane ana leqomu ahaka muka shiga dakina wanda yasha gyara ga tabarmi anbaza takoina sai dan tulu dake daga can kusurwar dakin ataqaice nan yazama dakina kuma ranar nazama cikkakiyar mace ta hanyar raya sunnar aure da mukayi da mijina da farko farkon zamana gidan komai na tafiya min lafiya lau don sosai.mijina kesona don yamafi fifitani akan kingin matan baya yarda inyi wahala don ko girkin gidan da sai andora qatuwar tukunya baya bari nayi kullum abinci na shi ke kawomin wanda duk yawanci kayan dadi ne hakan yaqara sani jindadin auren don ina samun kulawa sosai fiyeda wanda nake samu agidan marayunmu hakan yasa kan kace me nayi 6ul 6ul naqara kyau haka naita rayuwa mai dadi agidan mijina inda nalura kamar mijina bayason kingin matanshi saboda yadda baya shiga harkansu don becika shiga dakunnansu ba kuma maganar arziqi bata hadasu kullum sai fada ga yaranshi suma banga yana wani kula dasuba don suma rayuwarsu suke kara zube ina mammakin abubbuwan dake faruwa agidan dakuma yadda yake watsar da sauran iyalenshi saidai ganin ni bayamin haka yasa Kawai nashare na cigaba da more rayuwata acikin wata na hudu dayin aurenmu nasamu ciki inda sai anan nagane waye ainahin mijina tun lokacin dayaji batun cikina ya chanzamin kwata2 inda yafara tsiromin da wulaqanci iri iri inda tun bangane dalilin hakan ba harna gane ashe haihuwace bayaso lokacin nasha wahala sosai saboda cikin yazomin irin mai shegen laulayinnan ne gashi mijina yajuyamin baya abinci kanshi yabar bani sai alokacin nagane ashe matan gidan suke ciyar da kansu ma gashi matan gidan dama duk haushina sukeji saboda yadda mijinmu ke nuna kulawa agareni abaya hakan yasa alokacin babu mai tausayamin saima allah qara dasuke yimin da qannanun habaice habaice ahaka naita kashe yan kudadden hannuna a lokacin inasamu inci abinci don ko shekara zanyi banci abinci ba babu wanda zai damu da hakan agidan haka naita wahala ga laulayi ga rashin kula har na qulla wata biyu sai alokacin na yanke shawarar fara sana'a ganin idan nazauna hakanan yunwa zata kasheni ne abanza gashi duk na cinye yan kudaddena ahaka nafara aikin wankau dukda yadda banida lafiya haka nake daurewa nayi wanki don samun abinda zansaka aciki ahaka har cikina yayi wata biyar inda lokacin muka wayi gari mukaga ana tada daki daya a gidan cikin qanqanin lokaci aka gama ginin yaji shafen qasa kamar nawa inda sai anan nakejin labarin ashe aure zaiyi naji baqinciki sosai a lokacin don sai a lokacin nakejin ashe mutum ne shi daya saba da aure2 cikin sati biyu aka daura aurenshi dawata ta tare inda itama yakoma yimata duk abubbuwa na kyautata dayake yimin abaya ahaka naita rainon cikina nikadai yau fari gobe baqi inda har lokacin babu wani jituwa atsakaninmu da matan gidan don kowaharkar gabanta takeyi, kowa kanshi yasani da 'yayanshi ahaka naita rainon cikina da tun kafin na haifeshi allah ya dasamin qaunarshi sosai a zuciyata don koyaya nake cikin baqinciki na dan cikina ya motsa sainaji sauqi sauqi, kullum burina na haifeshi lafiya nima inga wanda zan kira nawa cikina na shiga wata takwas mijinmu ya6ata da amaryarshi kasancewar itama ta dauki ciki wulaqanci yafara mata itama kala kala hardamu ma yana cewa bamu iya komai ba sai haihuwa ahaka ya watsar daita itama tafara dandana abinda muke dandanawa ana hakan watarana yashigo dakina daya rabu dazuwa don har saida nayi mammakin ganinshi don rabonda yashigo dakina tun ina amarya ashe shigowar ma bata alhairi bace don yana shigowa babu cass bare ass ya sakeni saki irinna jahilci wato uku gabadaya yakuma ce na tattara nafitarmashi agida aure zai qara sosai naji ciwon abin sosai don abin nashi babu ko tausayawa, ga tsohon ciki ga saki sakin ma na wulaqanci ahaka nabaro gidan bayan kwana biyu saboda budemin wutar dayayi na nabarmashi gidanshi sanin babu inda zani don babu wanda nasani yasa ban zarce koina ba sai gidan marayunmu koda naje nafadama manyan wajen yadda komai yafaru sai Kawai suka bani hqr don dama sunsaba irin wannan case din don yawanci ana sako wadanda sukai aure sukuma dawo gidan marayun su cigaba da rayuwa haka nakoma cikin gidan da rayuwa har lokacin da allah ya saukeni na haihu lafiya inda na haifi d'a namiji saidai ko kwana beyiba yakoma sosai naji rashin d'ana don na kwallafa rai akanshi sosai kuma inasonshi sosai tunma kafin na haifeshi hakan yasa har ciwo saida na kwanta kafin daga baya na hqr na cigaba da rayuwata dukda har lokacin d'ana na maqale a zuciyata haka na cigaba da rayuwa a gidan har tsawon shekaru takwas inda ana tara nasamu wata tazo daukar yan aikatau aka hada dani matar munsanta sosai don tana yawan zuwa dibar yara agidan inda take rarrabawa aikatau kamar dai wata dillaliyace ta masu kudi mai kaimasu yan aiki kasancewar angaji dani a gidan yasa aka hada dani dukda na girma don lokacin shekaruna talatin aka samu akatafi dani don dama yawanci abinda yasa suke badamu aikatau don susamu sauqin yawanmu ne don bawani iya riqemu sukeyi ba nima dai naji dadin daukata da akayi agidan don nima nagaji da zaman gidan ahaka aka tafi damu inda aka rarrabamu wa masu kudi inda ni dawasu guda biyar ne za'a tura saudiya aikatau don matar har qasashe take tutturawa mutane yan aiki sosai naji dadi jin zanbar qasar gabadaya naje qasar da kullum nake burin ganinta koda a mafarki ne hakan yasa naita doqin tafiyar don har hangoni nakeyi acan ina shiga da fita da cud'anya cikin larabawa cikin qanqanin lokaci akayimana shirye shiryen tafiyar inda mukabi jirgin ruwa (6arauniyar hanya) har muka samu muka shiga qasar tunda nake ban ta6a ganin haddaden waje mai kyawun gaske irin na qasar. haka aka tafi damu munata zuba qauyanci har muka isa masaukinmu anan muka kwana Washegari kuma aka rarrabamu a gidajen dazamuyi aiki ni gidan wani attajiri aka kaini don kai koda ganin gidan kasan gidan masu dashi ne saboda haduwa, anan aka hadamu nida wadansu da suma aka kawo aikatau da matar gidan mai tsananin wulaqanci kwata2 mutan gidan basa qaunar baqar fata don afili suke nuna qyamarmu ahaka aka rarrabawa kowa aikinshi dakuma fadamana kudin albashinmu rayuwa agidan amatsayin yar aiki rayuwace ta wahala da qasqanci don kwata2 basa qaunarmu kamar ma ba kallon mutane suke mana ba don kuskure kadan idan kayi saika yabawa aya zaqinta ahaka muke wannan qasqanttaciyar rayuwar wanda saida na gwammaci zamana a qasarmu akanta don abin nasu ba iya kyama da hantara ya tsaya ba, abin haryakai harda cin mutuncinmu na 'ya mace inda mazajensu keyimana kallon dabbobin dazasu iya zuwa sujuye qazanttaciyar buqatarsu akai suyi tafiyarsu hakan dana gani yasa hankalina tashi ainun don abin abin tashin hankaline inda nan take nafara danasanin zuwana qasar haka naita lalla6awa kullum cikin roqon allah ya kareni daga sharrin mutanen don naga yadda sukeyima kingin yan uwana masu aiki inda suke maidasu kamar karuwansu idan kuma baki yarda ba a laqamaki wani sharrin da za'ayi miki hukuncin dazakiji inama tunfarko kin yarda da buqatunsu (hakan nafaruwa a real wlh, mutane yan Africa masu zuwa wasu qasashen don aikatau dadai sauransu ba qaramin tashin hankali suke fuskanta ba acan saboda tsananin qabilanci da ake nunawa acan inda yawanci ake maidasu sex machine don yawanci sunfison Africans don acewarsu sunfi satisfying dinsu, allah ya kyauta) ahaka nayi wata uku agidan ina kaff kaff dakaina ina addu'ar allah ya ku6utar dani saidai ba'a dauki lokaci ba wani d'an gidan yafara kawomun hari sosai hankalina yatashi da ganin hakan, hakan yasa naita kakaucemashi ina addu'ar allah ya ku6utar dani daga sharrinshi alokacin sosai zaman qasar ya gundureni don da nasan yadda za'ayi nagudu danayi gashi wacce takawomu tun ranar data kawomu bansake sata a idoba ahaka har watarana saurayin yaso raping dina lokacin babu kowa gidan don saida yayi yan dabarunshi na yadda zaisameni yaci karenshi babu babbaka ranar naga tashin hankali don da tsiya yaso afkamin saidai allah yabani ikon makeshi da vase din tangarau mai nauyi akai inda nan take ya silale yasume jini nabin kanshi ganin hakan yasa na rude don nasan shikenan tawa,ta qare don muddin akadawo aka taddamu haka shikenan nagama shaqar numfashi hakan yasani fitowa agigice don ni duk tunanina mutuwa yayi, cikin sa'a kau ban tadda mai gadi a gate ba hakan yasa na afka waje nafara gudu irin gudun fanfalaki burina Kawai intsira da rayuwata haka naita gudu shiga nan fita can batareda nasan inda na nufaba, kuka kau tun inayi harna kasa saboda muryata databar fita ahaka dare yayimin nasamu qarqashin wata gada na ra6a saboda yan kame dake kame da daddare na raku6e ina kyarmar sanyi ina addu'ar allah ya kawomin dauki ahaka har dare yayi sosai koina yadauki shiru, motoci nawucewa jefi jefi asaman gadar dana 6uya ahaka tun ban iya barci saboda sanyi da cizon sauro har wani barci marar dadi ya figeni can cikin barci naji motsi sama2 abinka da dama atsorace nake sainayi firgigit na tashi ina zare idanu ganin yadda hasken fitilu keta walainiya awajen yasani qara la6ewa ajikin bangon gadar ina toshe bakina don duk tunanina mutanen gidan danake aiki suka biyoni suna nemana kokuma yan kame daga saman gadar suke haskowa da fitilarsu mai mugun haske kamar masu neman wani abu nidai qamewa nayi wuri guda inata hawaye ina kyarma bayan kusan minti daya da haske hasken naji qarar abu tsindum sunjefo cikin ruwan gadar dake gudana yana tafiya atsorace nasake maqalewa ajikin bangon gadar ina qara toshe baki don atunanina su suka duro ciki can sainaga nabar ganin hasken can kuma naji tashin mota tasaman gadar aka tafi dukda antafi hakan besa na iya komawa barcin ba haka naita zaxzare ido cikin duhu ina kyarma saboda sanyin da akeyi gashi ina qarqashin gada ahaka har haske hasken alfijir yafara ketowa inda anan na yanke shawarar barin wajen don nagaji da cizon da,sauro keyimin hakan yasa na lalla6a ina qoqarin fita daga gadar kamar ance in kalli gabana saina hangi wani box mai dan girma daga nesa da inda nake kasancewar akwai tazara,da inda nake yasa nakasa hango ko menene sosai harzan wuce saina tuna da mutanen dasuka zo jiya suka jefo abu acikin gadar hakan yasa naji inason ganin koma menene ahankali nake bin gefe gefen gadar ina tattaka dutsinan ciki gudun karna afka cikin ruwan ahaka harna iso wurin kwalin daya jiqe jagab shima don dutsi ya tokareshi ne da,tuni yabi ruwa tsayawa nayi ina kallon kwalin cikin dan hasken safiya daya farayi ina saqe saqe zuciyata nabani qila sharace aciki suka jefar saidai kuma dukda hakan sainaji inason budewa inga me keciki ahankali nasa hannuna dake kyarma kyarmar sanyin danake ji nabude kwalin inda ganin abinda yake ciki yasa numfashina daukewa cakk na wucin gadi wani farin yaro nagani aciki hannayenshi da qafaffunshi a quqqule da igiyoyi bakinshi toshe da tsumma an daureshi tamau idanunshi alumshe babu alamun numfashi ko kadan attatare dashi....✍? *manage banida charge, qila gobe inyi* Ummin fasihu🧚🏻‍♀? 8/11/21, 2:03 AM - Buhainat😝: *🙍🏻‍♂️DEEN🙍🏻‍♂?* *cigaban 097* ja baya nayi amugun tsorace don ban ta6a tsanmmanin abinda zan gani kenan nan take jikina yahau rawa nafara yin baya baya hannu toshe da baki atsorace najuya nabar wajen dagudu ina bi ta duwatsun cikin ruwan harna samu na koma hanyar danabi nashigo qarqashin gadar nasamu nafita daga saman gadar na tsaya ina kallon kwalin danake hange daga nesa har lokacin zuciyata banda bugawa babu abinda takeyi sonike intafi amma kuma nakasa sai kallon kwalin nake batareda na iya motsawa daga inda nakeba kamar wanda aka jawo saina tsinci kaina da komawa cikin gadar kuma ina tafiya ahankali nasake nufar kwalin jiki na rawa nasake leqawa naga abinda nagani daxu yaro ne da bazai wuce shekaru uku ba, farine dukda ba irin tass dinnan ba na larabawa don nashi irin farin nanne mai jajaja, gashin kanshi ajiqe kamar yadda sauran jikinshi yake ya kwanto yarufe rabin fuskarshi nafi minti biyu atsaye ina kallonshi zuciyata na bugawa kafin cikin qarfin hali dasa hannu nadan ta6ashi ko motsawa beyiba hakan yasa naqara ta6ashi duk atsorace ganin be motsa ba yasa cikin qarfin halin na hau kekketa kwalin har ya ida fitowa fili sannan najuyoshi nasa hannu ina qunce mugun daurin da akayima bakinshi saida nasha wahala sannan na kwance na zazzaro tsummunan da aka cuccusamashi cikin baki ina kuka sosai don an daure mashi bakinne cikeda mugunta ga bakin da kumatunshi sunyi jajur alamun kwanciyar jini bayan nagama kunce bakin nakoma kan hannayenshi da qafaffunshi dake daddaure nahau quncewa, suma saida nashi wahala sosai kafin na samu kuncewa saikuma narasa abinda zanyi mashi daganan gashi gari yawaye don haske yayi sosai ganin hakan yasa nafara qoqarin daukarshi saidai yayimin nauyi sosai hakan yasa nadan kwantar dashi kan dutsin wajen nahau daddana mashi cikinshi daya dan yo sama akau saigashi ruwa sunshiga fitowa ta hanci ta baki, haka naita dannawa har suka daina fitowa saidai har lokacin ko motsawa beyiba hakan yasa na cije na cicci6eshi dukda lokacin yadan rage nauyi nasamu dakyar nadorashi abaya na don har inayi ina faduwa sannan nashiga takowa ahankali don barin cikin gadar dashi koda nafito rasa inda nanufa nayi gashi har lokacin ina tsoron kar ace yan gidan danake aiki nacan na nemana gashi nasan shima wannan yaron wadanda suka jefashi a gada sunyi hakan ne don son ganin bayanshi hakan na nufin daga ni har shi muna cikin hadari hakan yasa maimakon nayi titi nashiga cikin mutane saina yanki daji kawai batareda nasan inda muka nufaba burina Kawai na tseratar da rayuwarmu dukda har lokacin banida tabbacin ba gawace goye abaya na ba ahaka harna samu nayi nisa sosai harsaida naji ban iya tafiya sannan na haqura muka zube awajen ina sauke numfarfashi dagowa nayi ina kallon yaron wanda farat daya yashiga zuciyata ina jinshi fiyeda nakejin d'ana dana haifa yakoma bansan ko yana rayeba ko ya mutu don kwata2 baya motsi kuma natara yatsuna a hancinshi nidai banji yana numfashi ba kunnena nasa a saitin zuciyarshi ina sauraro ko zanji bugun zuciyarshi saidai shima shiru saida na dade ina sauraro sannan naji bugun zuciyar can qasa qasa sosai nayi murnar hakan don dafarko harna fara sadaqarwa dacewar yamutu tashi nayi ina kallonshi batareda nasan wani taimakon dazanyi mashi ba, nasan asibiti yakamata na nema na kaishi amma zuciyata taqi bani hadin kai don gani nake kaishi asibitin daidai yake da jefashi cikin hadarin daya fito don qilan hakan yazamo silar dazaisa mutanen dasuka so ganin bayanshi dafarko susake dawowa haka mukaita zama awurin cikin rashin sanin abinyi ga yunwa ga sanyi don daga ni har shi kayanmu ajiqe suke haka mukaita zama har rana tafara fitowa inda anan nasamu nacire mashi jiqaqiyar rigarshi ko yadanji sauqin sanyin haka natusashi gaba nabuga uban tagumi ina kallonshi batareda nasan abinda zanyi ba ahaka har rana ta take sosai ganin hakan yasa nasake miqewa na daukeshi nasake goyashi nacigaba da tafiya acikin dajin ranar naci baqar wahala don haka nawuni ina tafiya babu ci gwara gwara ruwa idan nahadu da matattarar ruwa ina dan kwalfa in jiqa maqoshina ahaka harna qarasa wani qauye qauye anan qarfina yaqare bansan ya akayi ba kawai sainaji lumm idanuna na rufewa dakansu kaina na juyamin nazube awajen dani da d'an dake bayana bansan iya adadin lokacin dana dauka ba asume saidai Kawai nafarka naganni cikin wani daki mai dan duhu duhu firgigit nayi na miqe zaune ina waige waige anan nagane kamar ma cikin bukka nike agarin waige waigena na hangi wannan yaron shima kwance daga dayan gefen dakin bansan sadda naqarasa wurin ba da rarrafe nayi saurin tattaroshi ajikina na rungume ga mammaki na sainaji yayi motsi yana yatsuna fuska saboda motsashi danayi saikuma yafara tari ahankali cikin wata iriyar dakussashiyar murya dabata fita sosai farinciki ne ya lullu6eni ganin ya motsa hakan yasani sake rungumeshi ina jin wani irin sonshi har qasan zuciyata sai kallon kyakyawar fuskarshi nakeyi babu ko kyaftawa kamar nasamu madubi ahaka wasu mutane suka shigo bukkar jin motsinsu yasani dawowa daga duniyar kallon yaron naja dabaya atsorace ina binsu da kallo kamar yadda suma sukemin suma larabawa ne saidai dagani yan qauye ne duba da yanayinsu mace ce da namiji duk sun manyanta sun tsaya daga bakin kofa sun zubamana idanu nima dai kallonsu nake amma atsorace sai qara rungume yaron jikina nakeyi qamm a qirjina yadda kasan za'a kwaceminshi kallon juna naga sunyi sunyi murmushi sannan suka qaraso ciki suna kallon yadda nake qara jabaya ina mannewa da jikin bukkar ganin yadda na tsorata yasa suka bar nufomu inda anan matar cikin murmushi don kwantar min da hankali tafara cemin na kwantar da hankalina babu abinda zasuyimin cikin larabci dukda banajin larabcin sosai amma nagane abinda take nufi saboda gwadawar datakeyi da hannu hakan yasa hankalina dan kwantawa miqomin hannu tayi akan nabata d'an nikuma saina qara matseshi jikina ina jada baya alamun ban badawa, murmushi sukayi sai mutumin cikin harshen larabci yake tambayata d'ana ne? dan zaman danayi agidan danake aiki yasani dan sanin wasu guntayen larabci hakan yasa nagane abinda yace min hakan yasa na kada kaina cikin sauri murmushi suka sakeyi nan suka hau nunamin baxasu cutar damuba taimaka mana zasuyi dakyar dai suka samu suka lalla6ani na yarda dasu nabasu shi suka mayar dashi shinfidarshi suka kwantar dashi inda anan naga sun cigaba dayimashi wani hayaqi wanda yaita sashi tari da shaqaqiyar muryarshi nidai ina gefe ina kallonsu harsuka gama yimashi duk maganin dasuke mashi suka kyaleshi yanata barcinshi abinci suka bani wanda kamar jira nake na amsa hannu narawa nashiga ci saboda tsananin yunwar da dama nakeji saida naci na qoshi sannan nadawo nutsuwata inda anan sukaso sanin wacece ni mekuma yakawomu qauyensu dayake duk bajin yaren juna muke ba yasa maganar kurame (demonstration) duk tafi yawa a maganarmu inda anan nake kwantantamasu cewa gudowa mukayi za'a kamamu mu ba yan qasar bane nakuma nuna masu sonike mubar qasar shiru sukayi suna kallona hakan yasa gabana cigaba da faduwa don duk a tunanina sungano yaron ba nawa bane don shi farine nikuma gaskiya baqa ce dukda ba irin qirin dinnan ba amma dai kwata2 bamuyi kama da yaron ba kuma gashi shi sak balarabe dukda jikinshi ba irin farinnan tass ba yake kamar na jikin kajin turawa amma farine irin mai jajaja wanda anasamun daidaikun masu irin fatar a Africa tambayata sukayi wacce qasa nake nace Ghana a Africa sai suka sake tambayata ina uban yaron cikin qwarin gwiwa nabasu amsar yamutu nima nan aikatau yakawoni saboda tsananin rayuwa saina tsinci kaina da gayamasu duk abinda yafaru a tsohon gidan danake aiki da silar gudowata, abu daya ne ban gayamasu ba shine yaron tsintarshi nayi sundade suna jujjuya maganata kamar dai basu yarda dani ba don saidai su kalli yaron su kalleni can sukace karna damu zasu taimaka min nakoma qasarmu can Africa amma sai yaron ya farfado tukunna yasamu lafiya ba haka nasoba amma babu yadda na iya haka na haqura ina addu'ar allah yarufamin asiri mubar qasar lafiya saida muka kwana uku agidan kafin yaron ya farka kuma abin mammaki yana farkawa yafara waige waige yana kiran ummie cikin muryar dabata fita munayin ido hudu dashi ya rarrafo wajena dasauri ya maqalqaleni sosai na sauke ajiyar zuciya ganin yadda yaron yayi don da yaqi yarda dani da qila mutanen sun zargeni duk yadda mutanen sukaso ta6ashi qiyawa yayi ya lafe ajikina yayi lamo kamar dagaske ni mamarshi ce ahaka muka qara kwanaki biyu inda na matsa ni sonike nakoma qasarmu don har lokacin hankalina be kwanta da zamanmu qasar ba izuwa lokacin sungama gamsuwa cewa d'ana ne saboda yadda yake liqemin kodayaushe yana maqale dani duk yadda sukaso muqara zama ko don jikinshi dabe ida warwarewa ba qiyawa nayi nace idan naje can zankaishi ayimashi magani ahaka suka haqura ranarda muka cika sati daya awurinsu namijin ya rakamu mukayi tafiya sosai bisa raqumma har mukazo wani qauye shima anan ya hadamu dawani wanda aikinsu fitarda mutanen qasar ta 6arauniyar hanya anan yabarmu bayan yadan bamu dan guzurin tafiya nikau naita godiya kamar zan ari baki anan aka hadamu da wasu mutanen dasuma qasar za'a fita dasu rabi da kwatansu duk yan Africa ne inda aka lodamu awani qaton jirgin ruwa cikin dare muka daga daren ranar ko rintsawa banyiba ina qanqame da KAMALDEEN kamar yadda nasamashi suna hankalina be kwanta ba saida naga mun qetare iyakar saudiya sai lokacin naji sanyi sanyi araina alokacin nakuma lura duk yawanci mutanen cikin jirgin yan Nigeria ne sannaniyar qasarnan datayi suna duk fadin Africa dama duniya bakidaya hakan yasa nima jin hankalina karkata acan ataqaice dai saida mukayi kwana uku muna tafiya sannan muka iso Nigeria aka jibgemu garin lagos lokacin jikin Kamal yaqara rikicewa saboda yanayin tafiyar tamu ga sanyin daya bibbigemu hakan yasa muna sauka na dangana da asibiti wanda dakyar dagano ta hanyar kwatance ganin mawuyacin halin dayake ciki yasa aka kar6eshi cikin gaggawa inda anan likitoci suka shiga bashi taimakon nikau nakasa zaune nakasa tsaye saboda yadda

Chapter 78 of 81