Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gidansu zee tashigo hospital din Wata dattijuwa cikin ma'aikatan gidansu zee ta tafito ita da bala driver daya kawota Hannunta dauke da basket din abinci wanda mummy tasa akawo musu Saida suka gagaisa da kowa sunamasu ya jiki sannan daddy da zee suka tashi akan zasubi bala ya ajiyesu gida, ita kuma dattijuwar mai aikin saita tsaya dasu Godiya su matar mallam Nasiru da baaba abu suka shiga yimashi saboda sosai ya nuna hallaci duba da yadda ya tsaya akansu sosai batareda yayi la'akari da matsayinshi ba na babban mutum Itakau kaka batama san da tafiyarsu ba don tunda tadawo ta zauna ta buga tagumi ba tace komaiba sai Kafe waje guda da ido datayi Bayan tafiyarsu daddy ne dattijuwar yar aikin mai suna Inna Binta ta gabatar masu abincin datazo dashi, duk sunci sai kaka da sukayi juyin duniyar akan taci amma taqiya haka suka haqura suka kyaleta A bangaren zee kau koda suka isa gida mummy ce ta tisata gaba tayi wanka da ruwan masu dumi sosai ta gaggasa jikinta sannan ta tilasta mata taci abinci dukda bada wani yawa taciba sannan tabata maggugunanta tasha tasata ta kwanta Ko minti biyar ba'ayiba da kwanciyarta barcin gajiya ya saceta Tasha barci sosai wanda ke cike da mafarkan Deen kala2 wanda tana tashi duk ta mance mafi yawa a cikinsu Sosai taji dadin jikinta yanzu duk wata gajiya ta tafi sai dan abinda ba'a rasaba saikuma murar datake fama daita haryanzu Miqewa tayi tashiga toilet ta dauro alwalla sannan tazo ta gabatar da zuhr daya wuceta ta dora da asr da ake cikin lokacinta yanzu Ta dade tana yima Deen addu'ar samun lafiya sannan ta nemi sakayyar allah akansu nurr dasuka ci amanarta da su master dasuka nufeta da sharri Saida tagama sannan takoma kan gado ta zauna ta lula duniyar tunani Ahaka wata maid tashigo kiranta inji mummy Tashi tayi bayan ta yafa veil din gown dinta ta bita Kamar yadda ta hasaso abinci mummy zata sata ci Saida ta gaidata mummy ta amsa tana mata ya jiki ta amsa da da sauki sannan mummy ta zubamata farfesun kan rago wanda yaji kayan yaji sosai ta turamata a gabanta Babu musu tashiga sha don itama tana buqatar abinda zai dan warware mata toshewar hanci datake fama dashi sai gashi kuma ya taimaka sosai don taji dadin jikinta bayan tasha Haka taita kasa kunne taji ance ta taso su koma asibiti amma shiru Gashi batada waya yanzu bare takira daddy ta narkemashi yasa akaita gakuma batason ta tambayi mummy, haka taita jira amma shiru Daga baya ma saita daure taje tasamu mummyn da maganar sai cemata tayi ba yanzu ba Abin ya 6ata mata rai sosai Hakan yasa takoma daki ta kulle taita kuka Sai bayan isha'i mummy ta aika agayamata ta shirya suwuce hospital din Tuni ta mance da zuciyar datake tayi saurin chanzawa tana addu'ar allah yasa su tararda ya farka Da ita da mummy dawata maid dinsu suka tafi wannan karon ma da abinci a basket A asibitin taga daddy Hakan yasa tawuce wajenshi da sauri ta Rungumeshi tana tura baki Dagota dadi yayi yajamata hanci yana tsokanarta yana kiranta cry cry baby ita kuma sai qara zunbura baki take Binsu mummy dasukayi gaba suma sukayi suka shiga dakin dasu kaka suke Saida su mummy suka gama gaisawa dasu kaka sannan itama zee ta gaidata cikin jin kunya kuma ba kunyar komai bace saina tasan tanamata kallon itace silar rashin lfyar jikanta Amsawa kaka da yanzu ta dan kwantar da hankalinta tayi tana tambayar ta ya jikinta, Amsawa tayi da dasauqi sannan itama ta tambayi lafiyar mai jiki itama ta amsa da dasauqi daga nan kowa yayi shiru Mummy ce ta gabatar musu da abinci, amsa sukayi suna godiya suka ajiye ko don anjima don basu dade dacin abincin da matar mallam Nasiru takoma gida tayi musuba Sosai mummy tasaki jiki dasu sukaita fira kamar dama sunsan juna, yadda mummy tasaki fuska tanata fara'a yasa suma suka saki jiki daita sunata hira harda kaka dake tofa nata akai akai Zee kau tun bayan gaisuwarnan bata qara cewa komai ba saima sadda kai datayi tana wasa da zoben hannunta tana sauraronsu Hankalinta gabadaya baya tareda su kawai dai tana wajen ne amma ko wuqa za'asa mata bazata iya recalling kalma daya a abinda suke cewa ba Hankalinta gabadaya na kan Deen, idan akwai abinda tafiso yanzu to sanyashi a ido ne Sun dan jima a Hakan sannan tadan dago taga haryanzu firarsu suke hankali kwanta Dan Hadiye yawun bakinta tayi sannan tayi gyarar murya wanda Hakan yasa duk suka kallota, sai kuma taji ta takura da kallon amma saita basar tace "zan dan je wajen daddy" tafada tana qirqirar wani busashen murmushi Da to saita dawo su baaba abu suka amsamata suna kallonta yayinda mummy batace komai ba sai kauda kai datayi Tashi tayi tana dan satar kallon mummy sannan tanufi hanyar fita ta fice Duk binta da kallo sukayi harta fice sannan baaba abu tayi fuska kalar tausayi tace "baiwar Allah, kai allah ka cigaba da karemu da zuri'armu wannan abu da me yayi kama? Yarinya nitsatsa amma anason wargazamata rayuwa, allah kacigaba dayimana katangar tsari da ire iren wadannan azzaluman bayin naka" Duk da amin aka amsa banda mummy da tadanyi murmushi kawai Wai nitsatsa, Yarinyar da shegen rawar kai yayima yawa wataqila garin Hakan taje ta tsokano ma kanta su don ita haryanzu bata yarda haka kawai zasu nemi wargazamata rayuwa ba Nan akalar hirar tasu takoma kansu, inda suketa addu'ar tonuwar asirin su master da kuma yin allah wadai dasu sumee dakuma fatan waraka wa Deen *ZEE* Ajiyar zuciya ta sauke bayan tafito tana dan juya manyan idanunta Wawaigawa tayi don ganin inda zata hango su daddyn amma bata gansu ba Har tayi hanyar office din Dr dinsu saikuma tafasa Dawowa tayi ta nufi recording room dasuka shiga dazun dasafe Saida tayi knocking sau hudu sannan aka bude kofar mutumin wata mata ta bayyana Dan murmushi matar tayimata tace "hi" Itama maida mata murmushin tayi tace "hy" "how may I help you miss?" inji matar tana kallonta Rasa abinda zatace tayi Hakan yasata fara kame2 Ganin Hakan yasata cewa tashigo ciki sai suyi maganar Shiga zee tayi tana wondering ina wancan mutumin yake na dazun? Saida ta zauna sannan matar tace "yes miss? How may I help you?" inji matar tana folding hannunta tana kallonta Taking deep breath tayi sannan tace "amm.. Dama sonake ayiman viewing wani dake kwance a room 12 ne please, patient ne amma anhana shiga ganinshi shine nakeso please kiyimin viewing dinshi" Shiru matar tayi tana kallonta na dan wani lokaci sannan tace "am sorry, amma ba'a zuwa ganin mutum anan, kiyi hqr kijira har abaku izinin shiga ku ganshi Hakan ma zaifi" Shiru zee tadanyi tana kallon zoben hannunta sannan tasake dagowa ga matar "please, kawai ganinshi zanyi koda flashing dinshi zakiyimin nadan ganshi ki kashe, I want to know how he is please" tafada pleadingly "idan kinason sanin yadda yake likitanshi zakije ki nema ba nan ba, am sorry but it's strictly against the law, da ana yin haka da kowa ma nan zaizo don ganin nashi, kiyi hqr please ki jira har lokacin da za'a baku izinin shiga ganinshi, am sorry" Kada kai zee tayi a sanyaye tana qoqarin maida hawayenta sannan ta miqe tsaye "thank you" tafada ta nufi kofa Binta da kallo matar tayi har Saida tadora hannu akan handle zata murda "wane ward yake?" zee ta tsinkayi muryar matar Juyowa zee tayi da sauri kamar dama jira take tace "12... Ward 12" Murmushi matar tayi tace "ok zo kiganshi na seconds biyar kiwuce kafin azo akamamu anan babu ruwana" tafada tana operating din mouse din hannunta Da sauri zee tadawo ta zauna tana murmushin jindadi dabatasan tanayiba Kunnomata matar tayi tayi mata zooming dinshi sannan ta kaucemata don tagani Tsayawa zee tayi tana kallonshi Kwance yake kamar dazu haryanzu abin oxygen a hancinshi Saidai yanzu babu qarin ruwa a hannunshi da alamu an cire "Don.. Allah ma, kidanyimin zooming face dinshi" tafada cikin sanyayar murya Murmushi matar tayi tayi yadda tace, nan take fuskar Deen yafito daro2 a screen din majigin Kafeshi tayi da idanu tanajin zuciyarta na kumbura don shauqi Dukda abin oxygen din ya kare kaso mai yawa na fuskar Hakan be hanata ganin yanda fuskar tayi fayau ba Idanunshi a lumshe sai lashes dinshi dasukayi zara zara suka hade dajuna sanadiyar lumshe idanun dayayi, ga girarenshi masu cika da baqi dasuka kusan hadewa Maida kallonta tayi akan ciwon dake akanshi wanda aka nannade da banda sannan akan tulin lallausan sumarshi dake tuje as usual Kafeshi da idanu tayi bako kyaftawa tanajin kamar zai bude idanu at any moment Batasan iya lokacin data dauka a haka ba sai jitayi an dafa kafadarta hakan yadawo da ita daga duniyar kallonshi Dariya matar tayi tace "haba madam? Daga ganin marar lafiya saikuma a bige da kuka?" Sai a sannan tasan ashe kuka takeyi Hanki din hannunta tasa tana tsane fuskarta tana murmushin jin kunya "to ai kiganshi yanzu, 5 seconds na neman zama 5 minutes, allah yabashi lfy insha allah very soon za'a barku kushiga wajenshi kiyita ganinshi babu mai takura maki" tafada tana Dariya Dan murmushin kunya tayi tana tashi "thank you very much" tafada tana murmushi "Don't mention.. Amm, nace dan uwanki ne?" tafada tana qumshe Dariya Kada kai kawai zee tayi sannan ta nufi hanyar fita tana mata sai anjima Cikin Dariya matar tace "to allah yaqara donqon zuminci, allah kuma yaqaro afuwa" Itadai zee fitowa tayi murmushi a fuskarta Tana fitowa daidai su mummy ma na fitowa da niyyar tafiya gida Hakan yasa suka wuce bayan itama zee din tayimasu kaka sallama suka shige mota harda daddy suka wuce gida *BAYAN KWANA UKU* Cikin kwanakin nan abubbuwa da dama sunfaru ciki harda nasarar damqe su master da akayi a gidan wani abokin huldar kayan mayensu inda wani dan leqen asiri yakawoma yan sandan rahoto sukuma basuyi wata wata ba suka yiwa wajen tsinke inda sukayi ramm da dukkansu aka kwashesu sai magarqama Ciki kuma harda sauqin da Deen yasamu dukda ba farfadowa yayi ba Amma an chanza mashi daki inda ana iya shiga aganoshi Saidai kwata2 ba'ason ayi hayaniya Tsakanin zee da kaka saina rasa wanda yafi farinciki da wannan cigaban dukda ita zee nata farincikin be bayyana ba kamar na kaka amma a badini tafi kaka murna da Hakan Kullum sai sunje asibitin Sau biyu, dasafe da kuma bayan isha'i Sosai su daddy ke hidimtamasu kaka wajen abin da yashafi lafiyar Deen don haryanzu ko sisin kaka beyi ciwon kai ba da sunan maganin Deen Hakan yasa kaka ke ganin girmansu sosai don ita kaka dama batada babban masoyin da yawuce mai nunawa dan jikallenta qauna A bangaren zee kau duk lokacin dasuka zo daga gaisuwa da tambayar mai jiki bata qara cewa komai sai kallon Deen da zata cigaba da yi Su kaka da mummy sunsha kamata ta kafeshi da ido dukda yadda take kallon a fakaice Izuwa yanzu babu wannan abin oxygen din a hancinshi Hakan yasa fuskar shi ke afili Saidai tayi fayau taqara haske lips dinshi kuma sunqara pink sosai Yau sunyi baqi yan dubiya sosai ciki harda yan makarantarsu dama mallamai, Cikin mallaman harda mr ibrahim Rasa inda zata sa kanta tayi don kunya lokacin da mr ibrahim ya yimata jaje da fatan Allah ya tsare gaba Haka dai ta amsa da amin batareda ta iya hada idanu da ko daya daga cikin su ba Haka akaita zuwa ganinshi, a yan kwanakin nan tasan Deen mutumin mutane ne don sai zuwa dubanshi ake takoina kuma duk wanda yazo da kalar yabon da zaimashi na kyawawan hallayenshi Hakan yasa taji ya qara burgeta akan nada kuma take kwadayin itama watarana tasamu mutane masu yaba hallayenta, wadanda zasu nuna damuwarsu sosai idan wani abu ya sameta Ahmad mai adaidaita ma yazo dashi da matarshi ganin din, Saidai lokacin dasukazo su zee basukai ga zuwa ba saida sukazo sannan aka gayamasu Zaune suke suna dan fira jefi jefi Kaka ce da baaba abu sai mummy da zee a dakin Can su ukun ke firarsu yayinda zee ke gefe tana yan danne dannenta a sabuwar wayar da daddy ya siyamata tanayi tana dagowa tana kallon Deen lokaci bayan lokaci Dagowa tasakeyi ta dan kalleshi saitaga kamar yatsun hannunshi sun dan motsa Qara dan waro idanunta tayi tana kallon hannun sannan ta maida kallon ga fuskarshi amma bataga yakuma motsin ba Bata Janye idanun ba akanshi ta cigaba da kallonshi babu ko blinking don idan idonta ba qarya sukayi mata ba tabbas taga yatsunshi sun motsa Qara girma idanunta sukayi ganin idanunshi sunfara motsi a runtsen dasuke Cigaba da kallonshi tayi idanu a ware bata ko kyaftawa don gani take idan ta kyaftasu zataga akasin abinda take gani yanzu Cigaba na motsi idanun sukayi da alama soyake ya budesu Can eyelids din suka fara rabawa idanun suka shiga budewa ahankali Biji2 yafara gani Hakan yasa yashiga kyafkyafta idanun Ahankali ganin nashi yafara clearing tun yana ganin abubbuwa blurring har ganin nashi yadawo clearly Be sauke idanunshi koina sai cikin nata large pure white eyes din... âœï¸ Ummin fasihu 🧚ðŸ»â€â™€ï¸? 8/2/21, 9:35 PM - BuhainatðŸ˜: *ðŸ™ðŸ»â€â™‚ï¸DEEN ðŸ™ðŸ»â€â™‚ï¸?* *026* Cak komai nata ya tsaya ta kafeshi da idanu kamar yadda shima nashi ke kafe da ita Sotake ta tashi tayi ihun murna ta nufeshi ta kamo hannunshi tayi mashi magana amma duk ta kasa, ko kyafta idanu batasonyi don gani take data kyafta ta bude zataga idanunshi a rufe kamar kullum Mummy ce kema Zainab magana akan ta miqo ledar kusada ita amma shiru ko motsawa batayi ba "bakiji ba?" inji mummy tana kallonta bama ita kadai ba harda su kaka Still bata motsaba ko ta nuna alamun taji don bama lallai ne intaji dinba Ganin ta zaune ta kafe wuri guda da ido yasa suma bin inda take kallo da ido Atare duk suka miqe kowa bakinshi bude "Deen!!" Duk suka fada atare Kaka ce farkon qarasowa gabanshi tana riqo hannunshi cikin tsananin farinciki Sai a lokacin ya janye idanunshi da basu ida washewa ba daga kan zee ya maidasu kan kaka dake kuka da Dariya lokaci guda "kyakyawa na, katashi? Alhamdullilah! Alhamdullilah! Allah mun gode maka, allah mun gode maka" tafada tana Rungumeshi qamm Lumshe oily idanunshi dasuka dan dishe yayi ya bude yana qara narkewa a wuyan kaka Dago idanunshi yayi a hankali ya saukesu akan zee da yanzu take tsaye tana kallonshi itama idanun na kyallin hawayen dasuka taru aciki "wai bazaki tafi ki kira Dr din bane?" inji mummy ganin tayi tsaye taqi gaba taqi baya Magana mummy ya dawo da zee daga duniyar kallon Deen tayi saurin Juyawa ta nufi kofa Binta da kallo Deen dake rungume still ajikin kaka yayi kamar yau yafara ganinta Harta dora hannu a handle din kofar saikuma taqara juyowa ta kalleshi Lumshe idanu yayi ya qara budesu akanta wani slight murmushi wanda yayi mugun tsayawa aran zee ya su6ucemashi Saurin bude kofar tayi tafita ta rufo Saidai maimakon tayi gaba saita koma ta jingina da kofar ta Lumshe idanu wanda Hakan yaba hawayen dasuka taru a idanunta damar gangarowa Ahankali ta silale awajen tana dafa saitin zuciyarta datakeji tana kumbura da sacewa Hawaye sosai take wanda ita kanta batasan na meye ba yayinda murmushin Deen na yanzu yaqi 6acemata a idanu Rabashi kaka tayi da jikinta ta dago fuskarshi tana shafawa tana murmushi da hawaye a lokaci guda Shima mayar mata da martanin murmushin yayi yana Lumshe idanu tareda budewa Suma su mummy qarasowa sukayi cikin farinciki suna miqa godiya ga Allah (s.w.t) daya tasheshi "sannu son, ya jikin?" inji mummy tana kallonshi tana kuma qara hango zallar qaunar da kaka kemashi Dan kafeta da idanu yayi saikuma ya Lumshe idanu ya bude alamun da sauqi Itakau baaba abu cewa tayi "Allah mun godemaka, raggon maza an leqo lahira an dawo, to ya hanya?" tafada cikin sigar tsokana don dama haka takemashi Itama murmushi yadanyi mata sannan ya maida kallonshi kan kaka da haryanzu ta tisashi gaba tana kallo kamar tasamu t.v Murmushi yasake mata Hakan yasa takai hannunta a kumatun haggunshi tana shafawa, Lumshe idanu yayi ya sake budesu yana son dago hannu ya dora akan nata dake dafe da kumatunshi amma yakasa don kwata2 beda wani qarfi ajikinshi "kyakyawa na, nayi zaton tafiya zatayi ka barni, nayi zaton barina zakayi ni kadai a duniyar nan, da katafi ka barni da bansan yadda zan kuma cigaba da rayuwa babu kai ba, rayuwa batareda kai ba rayuwar kunci ce Hade da dawwamammiyar kewa" Girgiza mata kai yayi ahankali alamun ta daina kuka Hakan yasa taqara rungumeshi tanajin farinciki na huda zuciyarta takoina Share qwalla mummy da baaba abu sukayi na tausayinsu, mummy na qara jingina soyayyar dake tsakanin wannan kakar da jikan Jin shirun yafara yawa yasa mummy cewa "bari naje na dubo likitan narasa abinda yasa basu qarasoba Tundazu" Bata jira komai ba tanufi kofa Murda handle din tayi ta tura sai taji abu ya tokare kofar cikin mammaki taqara turawa taji har lokacin atokare Cikin mammaki tace "ikon allah" taqara turawa wannan karon da qarfi Firgigit zee ta dago daga hada kanta da gwiwa datayi Jin ana turo kofa tabayanta yasata saurin miqewa tana ja baya Gani tayi an bude kofar mummy ta leqo Wara idanunta zee tayi don sai yanzu ta tuna abinda ya fiddota Saurin yin u-turn tayi ta nufi hanyar dazata sadata da office din Dr din Binta da kallo mummy tayi baki sake sannan ta ida fitowa itama ta nufi hanyar office din Dr din don bazata qara jiran gawon shanu ba Tana shawo kwanar dazata sadata da office din Dr din sukayi kici6us da Drn da zee Batabi takan zee ba tace ma Drn "yauwa Dr, yafarka yanzu yanzunnan" "ok muje mugani" inji Drn Nan tajuya suka koma ta hanyar dasuka taho zee a bayansu Shigowarsu yasasu duk dagowa suna kallonsu Qarasowa Drn yayi ciki fuska a washe "masha allah, alhamdullilah! You're back" yafada yana dan dafa goshinshi Murmushi kawai Deen yayi kamar yadda yake tun lokacin daya tashi Ciro abin wuyanshi Dr din yayi yasa a kunne sannan ya dora a qirjinshi yana feeling heartbeat dinshi Duk tsit akayi a dakin ana kallonsu kowa fuska bayyane da farinciki Saida likitan yagama duka gwaje gwajenshi sannan juyo gasu kaka, kaka bakinnan kamar gonar auduga "to kaka ina tayamu murna, yatashi kuma alhamdullilah jiki da sauqi sosai sai dan abinda ba'a rasaba, yanzu ayimashi brush asamar mashi abu mai dan ruwa ruwa da zafi zafi yasama cikinshi Ayanzu beda qwarin jiki sai ahankali qarfinshi zai dawo kuma don Allah banda hayaniya, please" Duk amsa mashi sukayi da insha allah Yan rubuce rubuce yayi a memo din hannunshi sannan yace "abashi wani abin yasa a cikinshi kafin indawo mashi da maggungunan dazai dinga sha, Allah yaqaro afuwa" Duk da amin suka sake amsawa sannan yafita Waya mummy ta dauka bayan fitar Dr itama tafita don kiran daddy Ita kuma kaka ta shige toilet don tarar ruwa itakuma baaba abu tafita sai dakin ya rage daga zee dai Deen Kafe juna da ido sukayi expressionless Ahankali Deen ya dago hannunshi ya miqomata yana dan murmushi Hakan yaqara tsumata tayi saurin qarasawa wajenshi ta kama hannun ta damke gaam takifa fuskarta akai tana shesheka Binta kawai yake da kallo not saying anything Saida tayi mai isarta sannan ta dago da watery eyes dinta ta kalleshi taga shima ita yake kallo "am so sorry.. Am sorry for everything, nina jawo komai, nakusan sanadin rayuwarka, daka tafi da bansan yadda zanyiba don bazan ta6a yafewa kaina ba, am sorry for causing you pain upon pain, forgive me.. Please" ta qarashe tana lumshe idanu hawayenta na gangarowa Dora dayan hannun yayi akan nasu dake wuri guda sannan ya girgiza mata kai yana murmushi saikuma ya bude baki kamar zaiyi magana amma taqi fitowa Ganin Hakan yasata cewa "menene? Baka iya magana ne?" Murmushi yayi ganin yadda take tambayar cikin damuwa saikuma ya nunamata cikinshi yana yamutsa fuska Ganin Hakan yasata saurin tashi tana raba hannunsu tanufi wani flask dake kan wata locker wanda dama ana ajiyeta ne da ruwa ciki incase ya farfado don dama Dr yariga ya fadamasu zai iya farfadowa a kowanne lokaci Tana cikin fiddo cups din kaka tafito hannunta riqeda bowl da dogon kofi dake dauke da ruwa Daidai nan baaba abu tadawo ita da mummy dasuka Hade a waje Maclean din da baaba tasiyo ta matsa a sabon brush data siyo ta miqama kaka da zatayi mashi brush Daukan cups din zee tayi taje ta daurayo sannan ta dawo ta jawo flask din da kayan shayin dake cikin leda tashiga hadawa Sosai tasa ginger powder aciki tayimashi hadin mai citta Deen da kaka kema brush sai 6ata fuska yayi kaka nata qara lalla6ashi har aka samu aka gama brush din Daidai nan zee tagama hada tea din taba kaka Cikin jindadi tashiga sama zee albarka sannan tazo tafara ba Deen din shayin Ana haka daddy yashigo tareda Dr Tashi zee tayi tanufi daddy da sauri ta fada jikinshi cikin tsananin farinciki Shima daddy riqeta yayi fuskarshi awashe suka ida qarasowa ciki Deen tunda zee ta ruga wajen daddy yake binsu da kallo harsuka qaraso wajenshi, yama bar amsar shayin hankalin yakoma can "masha allah, sannu kaji?" inji daddy cikin kulawa Kada mashi kai Deen yayi yana dan murmushi sannan ya kalli zee da itama murmushi yaqi barin face dinta "Allah ya sauwaqe ya qara lafiya, allah yakuma kiyaye gaba" inji daddyn Duk da amin suka amsa banda Deen din dayayi murmushi kawai "Gaskiya kayi mana hallacin dabazamu iya sakamaka da komai ba, ba don kai ba da yanzu wani zancen ake, babu abinda zamuce illah allah yasaka da alhairinsa" inji mummy tana murmushi "hakane kam, babu abinda zamuce face allah ya sakamaka da alhairi, ka ceci rayuwarmu don rayuwar Zainab tamuce idan muka rasata komai na iya faruwa, words can't express how gratefull we are kuma insha allah saimun tabbatar an hukunta wadannan shaidanun daidai da abinda suka aikata don yanzu haka magana takai kotu on monday za'a fara zama" inji daddy "Allah yakaimu, ai abinda yakamata kenan dama, yaran yanzu ka haifesu ne baka haifi halinsu ba, kuduba qannanun yara irin wadannan sun iya munafurci ni Zainabu, kuma wai qawayenta ne na qut da qut, duniya ina zaki damu? Idan wadanda ka yarda dasu suna maka zagon qasa ta bayan fage dawa zaka yarda ni Abu?" inji baaba Abu tana riqe ha6a "shiyasa ai qawayen basuda wata amfani, ni dama basuyi minba tunda nafara ganinsu nakuma yimata magana amma taqi rabuwa dasu ai ga irin abubbuwan danake guje miki nan kinfara gani" inji mummy tana eyeing dinta "wlh kam, qawayen yanzu ko bam (bomb)? Ke kina nan kin saki jiki dasu kina zama dasu da zuciya daya amma su basuda maqiyi daya wuce ke kuma basuda burin daya wuce suka bayan ki, ai da akayi abota ba wannan zamanin ba" inji kaka tana ajiye kofin shayin ganin besha "To allah ya kyauta, yaranma naji ance cocaine dealers ne suna safarar miyyagun qwayoyi da hodar iblis yanzu haka da akaje gidan da aka kamasu akayi bincike saigasu nan birjik anata zaqulosu yanzu kunga abin yaqara tsawo ga wannan ga wancan" inji daddy Riqe ha6a baaba abu tayi tace "danqari! Ashe yan kwaya ne? Ca6 aikau sun aikata tunda dasun shawu suka bugu tafara gayamasu qarya kome yazo kansu yi zasuyi" "To allah dai yashiryasu idan masu shiryuwa ne" inji kaka "fatan kenan" inji mummy tana Kada kai Dr ne yaqara duba Deen sannan yabasu maggungunan shi bayan ya gayamasu yadda qa'idar shan yake Da zasu tafi zee jitayi kamar karta tafi kamar tayita zama anan Don dole tabisu daddy tana waigen Deen dashima yake kallonta yanajin kamar karta tafi Ranar nan zee ta dade batayi barci ba, duk motsin da zatayi saiya fado mata arai duk kuma lokacin daya fadomata a rai saita tsinci kanta da murmusawa Barci 6arawo ne ya sadado batareda ta farga ba ya saceta A bangaren Deen kuwa saida ya rama sallolin da ake binshi cikin daren nan sannan yasha maggungunanshi wanda Dakyar aka samu ya hadiyesu don dama shi kwata2 beson magani duk lokacin dazaisha magani sai kaka

Chapter 18 of 81